Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

his lion voice" sai ta ji magana daga bayanta ana cewa what are u doing there?juyawa tai tana sorry sir i came to see malam umar but unfortunately i forget his office number!here i'm ya fada yana mai kokarin matsowa kusa da ita!'yammata taho muje office ai tsayuwa da irinku a waje hadari ne!binsa tai abaya tana ok sir!karamin office ne ba laifi sai takaddu daya cika kan tebur din nasa ga warin sigari sai tashi yake yi"!'yammata zauna ya fada yana bin ta da kallo me zan kawo miki ki sha? No! ka zauna kawai ba damuwa!kujerar dake kallonta ya zauna!toh ina jinki ki fadi damuwarki!
Murmushi ta saki kafin tace ba komai bane maganar da mukai a waya ne yanzu nazo akanta"!au dama ke ce mukai waya dake lallai Allah yayi halitta!ai dole kudinki ya karu yanzu duk aiki daya 50k!kin amince??hmmn amma ai ba haka mukai da kai ba?ada kenan wane malami zai ganki bai k'yasa ba ni ma dai...katseshi beauty tai saurin yi da hannu"kaga mubar wannan maganar yanxu dakko min task file d'ina sauri nake!tashi yayi ya dakko wani file yace gashi duk wani malami na department dinku akwai sunansa,lambar wayarsa kai har da ta mota akwai ciki"nagama nawa aikin saura naki!murmushi beauty ta saki alamun ta ji dadin aikin!to shike nan ga wannan 50k ne baya cikin kudinka kawai somin tab'i ne!ta ja kujerar baya ta mike tana fadin yawan aikinka yawan kudinka"so sai ka ji ni a waya!me yake yi malam umar in banda dariya ai karki damu beauty don kuwa aiki ai kin zo gidanshi" !kul karna kara jin wannan sunan a bakinka sunana *YAR JAMI'A* daga yau ko ka manta ga jami'ar nan a hannu na daga haka tabude kofar tai waje murna fal cikinta!!
📓📓

08 'YAR JAMI'A

_By_ *HERWWERH JIDDERH*
*A.K.A*
*PRINCESS'QUE~DEE*


Da fara'arta beauty ta fito daga faculty din wajen xee-xee ta dosa bude motar tai ta shige"cike da son jin labari xee-xee ke tambayar irin wannan fara'a haka tawan kodai prof. Ya hakura ne?yamutsa fuska tai beauty lokaci d'aya tace pls kar fa ki b'ata min rai daga laifi d'axu se bada hakuri yanxu?dama nai haka ne kawai dan ki rako ni nan"ai shi ya kamata ya bani hakurin don shi yayi laifin ba ni ba" ya baki hakuri fa kika ce beauty?eh mana ko kina ganin hakan baxai yiyu ba?lallai baki san wace hajara ba ma"amma ina ganin wannan abin na hannuna shixe kara wayar miki da kai"kan sitiyarin motar xee-xee ta dafe ta mai da dubanta ga titi tace"agaskiya beauty kin yi min nisa kuma ina ganin tafiyarmu tare a jami'ar nan baxai yiyu ba"duk iskanci na baya wuce na cikin unguwa ko tare da wasu bebs da tsagerancinsu be kai naki ba"amma ke naga kamar kin aje karatu a side"kamar xe fi kyau ki kara duba class ko Allah xe sa ki samu dede ke"ajiyar rai beauty ta saki jin xee-xee ta kai karshen maganarta"hannu takai ta juyo da face dinta suna facing juna tace"xee-xee ashe kallon 'yar iska ma kike min wacce bata damu da karatu ba?kina tsammani ba karatu naxo yi ba?karki yaudari kanki toh wallahi karatu ya kawo ni amma ta hanya me sauki xan bi don na samu"sanadin ni da wahala bamu had'a hanya ba"se kuma wasu 'yan kananan dalilai nawa"so karki damu baxaki tab'a dana sanin kasancewa tare dani ba".
Yanxu haka kinga yinwa nake ji bari naje motana sai muje capteria xqki ji wani abu daga file din nan ko hankalinki ya kwanta"bata jira cewanta ba bude marfin motan tai waje xuwa nata".
*******

Waje ne ya cika da jama'a inda aka fi sani da *stop & chop*duk wani ko wata mai ji da kanta kai hatta wasu daga cikin lecturers sukan zo nan don cin abinci bude kofar tai suka shiga!kujera biyu ta gano a can front side da alama da mutum a zaune ya tashi don ga jakar laptop nan a saman table din!har wani sauri take ta cimma wajen ta isa wajen ta zauna!xee-xee ma taja d'ayar ta zauna!waiter!waiter!beauty ke kira tana d'aga masa hannu!ina xuwa ya fad'a yana tahowa!me kike so akawo?matso kusa kaji!matsowa yayi tsammaninsa fad'a masa zata yi!nan tace kaga so nake daga yanxu har ku rufe wajen nan yau duk wanda yazo cin abinci ka zuba masa kace ya bar kudinsa *'YAR JAMI'A* ta biya kuma ka tabbatar ka nunoni yayin da kake fad'a har nabar wajen!ga wannan naka ne!5k ta saka a cikin tissue wacce take ajiye a wajen ta mika masa!nawa ne??naka ne ta fad'a tana masa alamar ya wuce!!amma ka miko mana maltina musha!toh ya fada yana shigewa ciki!
Kusan minti uku da faruwar haka sai ga wani saurayi wanda bai wuce shekara 30 ba ya shigo ciki sanye da wani coffee brown suit!cikin sauri daliban dake wajen suka fara morning sir!wasu uku daga ciki suka biyo bayansa!tafiya suke basu tsaya a ko ina ba sai a gaban su beautyl!d'aya daga cikin daliban ne yace"excuse me gals ku d'an ba da seat wa sir zai zauna!har xee-xee na kokarin tashi beauty ta riko hannunta"ta murgude baki gefe tace ka fad'a masa *'YAR JAMI'A* ta zauna a wajen kuma ita bata tashi sai ta gama abinda take but in xai iya jira"better for him"kawai sai ta ci gaba da shan maltinan ta hankali kwance!a fusace wani student ya taso jin maganan beauty d'aga hannu yayi da zummar zai mareta cikin sauri Prince ya rike hannunsa!karka soma batta kawai fuskan nan cike da murmushi!karka damu kan ka amma ka fad'a mata ta zama mai kamun kai!cikin sauri ta dago kai don ta ga wanda ya fad'i hakan akaro na biyu kenan"amma ina tuni ya xari jakanshi ya juya ya fita! binsu tai da kallo su kuwa daliban suka juya suna ta cece kuce!xee-xee kawai binta tayi da kallo tana fadin kin burgeni wallahi na zaci zaki ce muta shi nai wani d'anyan aiki yanzu!ai da mikewa nai xan d'au jakar na buga masa a kai don atunani na ya samu mental problem"kinsan tunda kikace na saki jiki dake karatu xe xo min da sauki toh nasan xaki yi hakan"gauran numfashi beauty ta saki hmmn kema ai kinsan haka bazai taba faruwa ba!ace wai ni hajara ina xaune wani ya tashe ni a seat"haba never"!
*****
Dalibai kuwa duk wanda yashigo siyan abinci sai a xuba mishi a kuma ce yaje kawai *YAR JAMI'A* ta biya kuma a nunota abinka da dalibai ai kafin kace me waje ya cika makil! ganin haka yasa beauty kallon xee-xee toh yanxu zan iya baki kadan daga cikin labari na amma fa karki dauka komai"s dan ki xauna tare da ni" tunda hayaniya ta cika wajen ba mai jinmu!!







📓📓09 *'YAR JAMI'A*📓📓
_By_ *HERWWERH JIDDERH*
*A.K.A*
*PRINCESS'QUE~DEE*

Ni dai sunana *HAJARA ALIYU KABIR MAI-DOLLAR* kamar yadda na fada miki ranar da muka fara haduwa!na kasance Yarinya d'aya tal ga mahaifina alh.Aliyu mai-dollar wanda ina ganin ba sai na gaya miki wanene mahaifina a jahar nan ba tunda shahararran attajirin d'an kasuwane kuma na hannun dama a gwamnatin kasa!Asalin mahaifina dai d'an garin yola ne wanda shine na 4 a wajen iyayensa!alh. kabir mai-dollar da hajiya ramatu madaki sune mahaifansa (Wato kakanni na) allah ya azurtasu da 'ya'ya hudu 3mata 1 namiji!aunty fatima itace babba!sai aunty khadija da kuma aunty Aisha!mahaifina shine auta acikin su ya samu cikakkiyar kulawa da gata daga iyayensa duk da wannan mahaifinsu baiyi sake wajen basu ilimin addini ba don dukkansu sunyi karatunsu a england in banda daddy wanda yake a china kasancewar kakus bai fiya zaman kasarba!Da zarar sun gama jami'a suke dawowa gida dan aure haka rayuwar gidan kakus ta ci gaba cikin farin ciki da jin dadi!har izuwa lokacin da ya kamata aunty aisha ta dawo gida don ta gama karatunta na jami'a anan ne tai burus da maganar kakus har take ikirarin can yafi mata nan hankalin kowa ya tashi a gidan nan musamman hajiya wacce sanadin hawan jininta kenan!alokacin daddy bai san abinda ke faruwa ba har sai da tayi shekara 2 acan wanda yayi dai-dai da kammala karatunsa!lokacin da ya dawo ne ya sami wannan mummunan labarin hakan yasaka shi kiran wani abokinsa da sukai makaranta tare dan kasar england da ya taimaka masa wajen sanin halinda take ciki sakamakon rantsuwar da daddy yayi bazai nemetaba tunda ya bata dukkan tarbiyyar da uba zai ba 'yarsa amma tai watsi da hakan!daddy ya shiga matsanancin hali da kiranda abokinsa yayi masa yana shaida masa aunty aisha tabi wata kungiya ta mawaka yanxu haka dasu ake damawa acan england!tunda Alh.kabir ya samu wannan labari yayi wa daddy gargadin idan har yakai 'ya'yansa mata waje toh bai yafe masa ba!
nan beauty ta d'an tsagaita da labarin nata ta dan surb'i maltinan gabanta ta ya mutsa fuska tace kinji fa abu irin na tsoho yaci duniyarsa dan bala'i baxe bari mu jikoki muci tamu ba".kina ji de ko xee-xee
A da daddy ya fara aiki a kamfanin kakus sai daga baya karfin kasuwancin yadawo kano inda daddy ke lura da kasuwancin kano!kakus kuma na can yola!da haka har kakus yabar masa kamfanin tunda bashi da wani d'a a gabansa"kin ga dai aunty fatima tayi aure har da d'anta itama aunty khadija tayi aure amma bata haihuba!kiga tun lokacin fa kenan gashi yanxu duk sun tara family nasu"! Karar wayan beauty ne ya katseta da hiran dole ta tsaya ta dauko wayan a jakanta"number ta gani kawai nan ta katse kiran ta dago kai tana kallon xee-xee da itama ita take duba tace wannan kenan amma,
Kiyi hakuri xee-xee bazan iya baki labarin mahaifiyata yanxu ba da yadda mahaifina ya aure ta saboda baki da hurumi akai!kawai de nasan hankalinki yana ga file din da kika gani dazu na karbo a faculty!toh bari na shaida miki wani abu xee-xee tun lokacin da daddy yasama min admission a jami'ar nan nake jiran fara shigowarta don kuwa
Ranar lahadi da daddare wancan satin daddy yake shaida min zai yi tafiya ta sati biyu amma ya fada wa wani malami gobe zan fara shiga don an gama yi min registration amma zai bani wasu takaddu ya kuma bani file dina akan na kai department dinmu ya kuma she damin wannan mutum xe kara mun bayani sosai akan makarantar da haka kenan muka rabu yana min sai da safe!



📓10 *'YAR JAMI'A*📓📓
_By_ *HERWWERH JIDDERH*
*A K.A*
*PRINCESS'QUE~DEE*

Safiyar litinin da misalin 9:a.m na shigo scul bayan daddy mun rakashi airport ni da ummah a inda ya bani lambar wayar malamin da xa xan nema!kira daya cikin ikon Allah ya dauka!nai masa bayanin kai na" cikin kankanin likaci ya gane!yaron office dinsa(massenger) ya turo ya tafi damu!
office ne babba muka shiga zaune yake dattijo d'an kimanin shekara 45 kansa kasa yana latsa laptop!shigowarmu ne yabashi ikon tsayawa da mai da dubansa garemu!'ya ta kin iso?haka yafada yana mai sakin murmushi a fuskarsa!eh na fada ina kallonsa!toh ga waje nan zauna!cikin nutsuwa na zauna!muka gaisa!sai naji yana cewa!mun gama magana da mahaifinki kuma nasan ya gaya miki!eh kawai nace!yawwa toh yanzu ga wannan takaddun ki hada cikin file dinki zan saka a nuna miki inda xaki kaisu!haka na karba na saka !yaron office dinsa ya kira ya kuma umarceshi da ya nuna min faculty dinmu da office din umar!daga nan nai masa sallama inda yake cewa in har kina da wata matsala karki nufi kowa kizo nan 'yata don bada kowa ake sabo a *jami'a* ba!amma kinsan kawai na ji shine xee-xee!
Baba habibu sunan masinjan nashi"gaskiya naji dadin hada ni dashi da yayi don ya nuna min komai wanda ya kamata na sani in banda malam umar da muka je baya nan !anan ne fa baba habibu yake ta maganganu ciki-ciki wai watakila yaje biyewa shashashan 'yan iskan yaran makaranta ne!wani abu ya faru baba?na fada ina mai da duba na gareshi!hmn ke dai 'yata ki kama mutuncin kanki kawai amma kinga *jami'a* mahadar gyara ko b'arna ce dole zaka zabi daya amma narasa dalilin da yasa yaran suke biye masa wajen ashararanci ga bala'in san kudi a cikinsa kamar dan kasuwa!dagaske baba?na fada ina zaro ido!kedai bari kawai ai shi jariri ma zai iya masa aiki indai zai biya shi cewar baba yana tab'e fuska!ni gaskiya baba har na tsorata dashi kawai ka bani lambarsa in na samu kawa a ajinmu sai ta rakani wajensa don kar naje kai file din ni kadai yazo min da wata maganar!da yake ranar babban mayafi na saka cikin ikon allah kuwa sai naga ya zaro waya!yana fadin kin san da yake duk yawancinsu ina da lambarsu kasancewar ni din na jima dasu anan!cikin sauri na dakko wayata na saka lambar !5k na zaro na mika masa amma kin san bawan Allahn nan sai yak'i karba sai da na nuna masa dan allah na bashi sannan mukai sallama dashi da haka na dawo gida!!
📓




11 *'YAR JAMI'A*📓📓
_By_ *HERWWERH JIDDERH*
A.K.A
*PRINCESS'QUE~DEE*


Nisawa beauty tai daga bada labarin ta dago kai tana kallon xee-xee tace
Bar batun haduwarmu da malam umar yanxu dai bari na bude file d'in nan na gano mana abinda ke ciki!kofin dake gabanta me dauke da maltina ta d'aga tasha sannan ta dauki file din!bismillahi xan bude sirrin jami'a ta fada tana kashe wa xee-xee ido d'aya!matso da kujerarta tayi ta hau nuna mata nan! kinga sunayensu ne da lambar wayarsu ke harda ta mota kin ga kuwa iyakar wayona iyakar nasarata!ko ba haka ba?Washe baki kawai xee-xee take tana fadin kice nima xa'a bani wadansu na lasa!hmmn yanxu ba lokaci bari naga wannan yaron sai mu wuce kin san fa gobe nake birthday na manta ban gaya miki ba don haka sai ki san da wane gayen zan ganki!don allah na ga bai min ba dauke kai zanyi kamar ban sanki ba!daga haka ta tashi tqna dariya ta shige ciki tana leken inda yake don tasan nawa zata biya!zaune ta ganshi gefen wasu mata suna had'a kayan girki!baka jiba" ta fada tana matsowa kusa dasu!cikin sauri ya mike yana fadin hajiya har kin gama ai da kin sa an kirawo ni"shigo mu karasa ga waje can ki zauna!no" ba sai na zauna ba fadi kudin kawai sauri nake!hajiya ai duka abincin wajenfa har ya kare!ai na san zai kare kudin na tambaye ka malam" ta fad'a cikin d'aga murya!gaba daya dubu sha uku da dari biyar ya kama!ok gashi amma gobe kukara hannu wajen girkin don zan baka na kwana biyu nan gaba dan bazan kara zuwa ba sai juma'a !hannu tasa cikin jaka ta zaro dubu talatin ta mika masa!ku nawa ne ma'aikatan wajen?mu biyar ne hajiya!ok ga wannan ka raba muku kuma ka kiyaye kada matar wajen taji don naji ance ba zama take ba!daga haka ta juya tayi waje!cikin mota ta tarar da xee-xee sautin waka ya cika motar!ta bude ta shiga tana kallonta!sai ina yanxu?beauty ke tambayarta"habeeb zan kai wa ziyara gidansa bayan la'asar sai na wuce!dariya kawai beauty tai ta fice daga motar!har ta juya kamar ance ta waiga cikin motar ta hangi hijab!wancan fa ta fada tana nuna mata!em!em !kin san baba sai a slow shiyasa nake yawo dashi da na shiga layi nake sawa kin san shi ba kamar mama ba"kinsan abin ne se kana basaja" koya kika gani?shegiyar gari ni na wuce ke dai ga son dadi ga tsoro kuma!dariya suka sa duka sukai sallama ta wuce!


Mota beauty ta shiga sai gida!horn take baba me gadi ya bude mata gate yana mika gaisuwa! Hannu kawai ta d'aga masa ta shige"cike da rera wak'a ta fad'a falon ganin ba kowa yasa ta hayewa sama!ta bude kofar falonta!me zata gani ladiyo ce ke tsaye tana goge tv!ke me kike min a falo?cikin sauri ta juyo tana kallonta!sannu da zuwa beauty dama umma ce tace....! Yi min shiru munafuka wallahi k'arya kike mata kawai halinki kika zo yi kuma wallahi yau zaki bar gidan nan bari daddy ya dawo!jiki a sanyaye ladiyo ta dauki tsimman nata tayi waje!cikin fushi ta shige d'aki!jakarta ta aje ta saka file d'in cikin drawer !yawwa bari nai wanka na kwanta na huta kuma"towel din dake sarkafe gefe ta janyo tayi bayi"lokaci kankani se gata ta fito"karamin riga ta xurq ma jikinta ta fad'a saman gado se bacci"!




📓📓12 *'YAR JAMI'A*📓📓
_By_ *HERWWERH JIDDERH*
*A.K.A*
*PRINCESS'QUE~DEE*


Buga kofar da daddy yake ne yasa ta farkawa daga baccin da take"! sanin daddy ne kad'ai ke mata haka ya sata saurin bude ido"tace swit daddy gani nan zuwa! Karamar riga ce iya kar kwiwa ke jikinta ta bude kofar tana bude hannayenta!matsowa daddy yayi ya rungumeta jikinsa!daddynki yayi miki laifi beauty na!ya fad'a yana kama hannunta suka koma cikin dakin!laifin me kayi daddy na?Dama Na gayyaci 'ya'yan abokaina don su zo su tayamu murnar birthday dinki gobe mantawa nayi ban sanar miki ba d safe"!kara kwantar da kai tai jikinshi murya cikin shagwab'a tace ok"daddy ba damuwa hakan yayi ai ba laifi bane!
ehh toh dama bawai wannan ne kadai ba ibmn baki manta ba ina wannan aminin nawa alh.Mukhtar'wanda na tab'a baki labarinsa wanda yake abuja da zama!d'ago kai beauty tai tace eh daddy na ganoshi!
yawwa beauty dady ya fad'a cike da fara'a"shine d'azu ya kira ni yake shaida min d'ansa an turo shi service nan kano kuma ya kama gida"shine nafa be kamata ace ga gidana ace har yakai ga xaman gidan haya"duk da dai nasan bak'yasan ganin kowa gidan nan my beauty kiyi hakuri ya zauna damu just 4 a year kinji my bea.........saurin janye jikinta daga nashi tai ta hau buga kafa kasa tana fadin no!no!no daddy ni dai bana so kawai kaji daddy bana so kace ya je wani gidan ya zauna!beauty bazan iya ba aminina ne fa"nasan shi baxe nemi ya kawo shi ba amma tunda yace min yaronsa na kano ai ya kamata ni na gane me yake nufi"kuma ba anan zai zauna ba wancan bangaren zai zauna kinga bazaima takura miki ba kinji beauty!turo baki tayi ta wani had'e giran sama dana kasa tace'toh daddy zan yadda indai zaka kori ladiyo daga aiki!
ladiyo kuma? mai tai miki daddy ya fada yana mikewa tsaye!tana yi min sata a dakina!duk da daddy yasan ba halin ladiyon bane amma haka ya biye mata!basai na koreta ba amma yau zata gane kurenta na shigo miki daki!fita daddy yayi ya nufi kitchen ya tararda umma da ladiyo suna ta aikin kwashin tuwo ai ta inda ya ke shiga ba ta nan yake fita ba!sai da yayi mai isarsa sannan ya juya ya haye sama!kallo ummah kawai ta bishi dashi ita kuwa ladiyo tunda daddy ya fara kanta k'asa yake!
Kallo ummah ta kai gareta kafin tace ladiyo kiyi hakuri kinji!ummah ta fada tana mikewa zata bar kitchen din!
Kai sunkwi ta amsata da bakomai hajiya yarinta ce kuma zata daina!yarinta?wannan haukane ba yarinta ba!dan allah ke ma karki b'ata min rai cigaba da aikinki kawai!tana kaiwa nan ta nufi sashenta duk rai ba dad'i".
Ranar haka beauty ta wuni bata ko lek'o k'asa ba don bata son fadan umma!




📓
13 *'YAR JAMI'A*📓📓
_BY_ *HERWWERH JIDDERH*
*A.K.A*
*PRINCESS'QUE-DEE*


💕


Washe gari Tun bayan sallar asuba ladiyo ta hada kan sauran k'ananan ma'aikatan gidan don fara shirye-shiryen birthday na beauty kamar yadda daddy ya saka ayi,bayan data gama hada breakfast ne a dining table ta koma cikinsu dan cigaba da hidima!hayaniyar aiki kake ji ta ko ina a gidan sai gyara yake d'auka" a d'aya bangaren kuwa har daddy da ummah suka gama cin abinci beauty bata ko lek'o falo ba gudun fad'an ummah take!cikin tsanaki suka gama cin abincin nasu har ummah ta mike tsaye tana shirin shiga kitchen don kai flask na ruwan xafi! daddy ya kira sunanta! Ta amsa tana mai komawa ta xauna!fuska ba yabo ba fallasa yake kallonta"sai kuma yace"ina ganin lokaci yayi da zaki canja halinki don axama na dake sam ba haka kike ba"bansan yanxu waya d'oraki bisa wannan d'abi'arba?ace kawai dan nayi ma wata 'yar aiki fad'a shine kike fushi dani da 'yata ko?bama wannan ba ai ko ba komai yakamata beauty na'ta zama anan wajen!yanxu tana ina?nasan fad'anki ta gudar ma!ace 'yar cikinki baxaki iya sakar mata mara a duniyar nan ta huta ba"toh meye anfaninmu a gurinta banda ganin farin cikinta"baki ummah ta hau motsawa tana kokarin magana daddy ya katseta da hannu"kul ban son jin kome yanxu maxa aje kayan hannunki ki hau sama ki nuna mata farin cikinki da wannan ranar tata duk da nasan kin manta yau birthday d'in ta toh ni ban manta ba"dan na damu da kayana!toh kawai ummah ta amsa dashi ta mike ta nufi sama abinta!ta jima bakin kofar tana bugashi amma beauty bata bude ba!can take itakam beauty saman gado rik'e da waya tana ta faman chart da frnds suna tai mata murnar xagayowar haihuwarta"wasu kuma wanda tasan 'yan abi yarima asha kida ne se gayyatansu take xuwa shagalinta na ranar"!tunanin bugun baxe wuce na ladiyo ba shi yasa tak'i amsanta"!cikin k'aguwa tace"bacci kike ne hajara?ummah ta fada tana murda hannun kofar!tuni tai wurgi da wayan hannun ta gefe jiki na b'ari ta nufo kofa"a'a ganinan xuwa!cikin sauri ta taso ta bude kofar tana 'yan boye-boye jikinta"!ina kwana ummah!sakin fuska ummah tai ta amsheta da lafiya lau ya kika kwana?alhmdullah!ta fad'a tana d'an sakin murmushi!hannunta ummah ta kama ta had'e da nata tace ina miki murnar xagayowar haihuwarki ina fatan kuma xaki yi shagalinki cikin farin ciki!
Cike da d'an guntun fad'uwan gabanta ta k'ara sakin fuskan tace
tnx ummah!sakin hannun nata tayi ta d'an gyara tsayuwanta had'e da dubinta"naga daddynki ya gama tsara kome naki da fatan de bakya bukatar wani abu daga gareni ko?eh ummah babu kome se de pls ke ma ki gayyaci frnds naki"naga daddy ya gayyaci nashi"kallo ta watsa mata me cike da tuhuma kafin tai k'arfin hali ummah tace xan duba na gani"!daga haka ta juya baya tai waje ba tare da ta jira wani cewa na 'yarta ta ba!dafe kai beauty tayi ta muxgune fuska"cike da tunani fal cikinta ta shiga hakaito wacce irin uwa allah ya bata haka?"wacce ita a lissafinta babu socialization ko kad'an"ganin bata da amsar hakan ya sata sakin rai ta shiga sabgar gabanta

Haka wunin ranar ya kasance beauty bata saka daddynta a ido ba har gashi ana maganar la'asar ganin haka ne yasa ta shiga neman number auntyn 'yan gayu kamar yadda suka tsara"bugu biyu ta d'auka"itama de wishes d'in tayi mata kafin beauty ta bata full address nata ta kashe wayan".
Sallah ta fara gabatarwa sannan ta shiga ta watsa ruwa"tun tana cikin toilet take wilk'iyo maganganu a d'akin nata cikin xumud'i kuwa ta sheka ruwa jikinta ta fito"auntyn 'yan gayu ce xaune cikin wasu kaya riga da skirt sun hadu sai wata bakuwar fuska gefenta"da fara'arta ta k'arasa wajensu suka k'ara gaisawa nan take shaidawa beauty cewa wannan itace me gyarata ga kuma kayan sawarta nan an tanada mata kud'i kawai xata bayar"tsalle beauty ta saki had'e da rungumota tana fadin ok! ba damuwa yanxu dai tashi a fara shirin nan k'adan xqki ji jama'a sun fara hallara"!.




📓📓14 *'YAR JAMIA*📓📓
_BY_ *HERWWERH JIDDERH*
*A.K.A*
*PRINCESS'QUE~DEE*

Gyal-gyali na wasu kyawawan ababan kwalliya kake iya ganowa ya cika ko ina na harabar gidan"ga kujeru da tebura an jera su da kaya na tand'e-tand'e da lashe-lashe"wasu kananan fitilu masu kala launin j'a da shud'i su ke ta walkiya a wajen"a hankali motoci na alfarma suke shigowa kowa ka gani cikin kaya na keta raini"daga maxan har matan sam babu na bari dan kowa yayi ma wannan ranar shiri na musamman"sanadin sanin waye Alh. ALIYU KABIR MAI DOLLAR" a gefe guda kuma makid'a ne ke ta sakin sauti a hankali irin me tsuma jiki din nan"sai masu rawa da suke ta nishad'antar da wajen"daddy da tawagar abokansa tuni sun hallara wajen"inda ummah na gefensa itama dai da nata xugar"shagali ake tayi ainun amma har kawo yanxu mai gayya me aiki bata k'araso ba".
Ummah ce ta d'an tab'o daddy da hannu tana nuna masa agogo da xummar lokaci na tafiya"kai ya gyad'a mata kawai ya nemi uxuri daga wajen

Please Login or Register in order to submit comment