Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ai ko ta saki uban birki a bakin wajen ji kake keeeeeeeeeeee"na k'arar tsayuwar mota"cikn sauri mutanen dake bakin wajen kowa ya dawo da hankalinsa gareta don ganin ko lafiya?hankali kwance take bud'e glass na motan tare da fiddo hannu rik'e da k'aramin kati(exit) a hannunta ta mik'a ma security man d'in"tun tsayuwar motar agun duk ma'aikatan gurin sun fahimci motar wace shiyasa ma basu wani d'aga hankali da abun ba don inda sabo su kam sun saba"hannu ya mik'o had'e da amsa da haka ta maida glass nata sama ta ja motanta gaba".
******

Mutumi na kana ina ne?cewar sameer wanda yake zaune cikin mota yana tuk'i ga waya a manne a kunnensa yanayi hankalinsa a tashe kana gani kasan cike yake da damuwa"daga d'ayan b'angaren aka bashi amsa sannan yace owk toh gani nan k'arasowa ina hanya".katse wqyan nashi yayi ya ci gaba da tuk'insa,kusan minti goma kenan da yin haka sai gashi a bakin wani makeken gida"horn biyu yayi mai gadi ya lek'o gami da bud'e gate d'in fahimtar wanda ya zo da yayi",a parking Space na gidan yaje cikin jerun motocin gurin ya aje nashi gami da fitowa ya nufi cikin gidan".a falo ya tarar da mama wato mahaifiyarameenu inda cikin girmamawa ya gaisheta sannan ya nemi izinin shiga cike"cikin wannan takun nasa na isa da tak'ama yake takawa kamar wani wanda ke tsoron k'asa haka ya riski d'akin".da sallamarsa sameer ya bud'e d'akin"amsanshi ameenu yayi a nutse"amma sameer ko ta kansa bai bi ba ya nufi gado abinsa"kwanciya yayi ya juya baya had'e da rufe ido kamar wani me bacci"
Ameenu Dake zaune saman 2 seater rik'e da magazine yana karantawa, cike da mamakin yanayi irin na aminin nasa dole ya ajiyeta gefe guda ya nufo gareshi"
Prince lafiya? Meke damunka haka?mtsssssss......... wani dogon tsaki da sameer ya saki ne ya k'ara tabbatar masa cewa da abinda ke damunsa"hannu yakai ya d'an dafa kafad'ansa a hankali ya shiga bubbuga masa ita yana fad'in pls be lyk a man"fushi fa ba naka bane"koma waye ya b'ata maka just forget about it & let us chill like nothing do you man pls"wani wawan juyi sameer yayo nan take kuma yabi shi da kallo cike da b'acin rai kafin ya iya mosa lips na shi a hankali yace"kasan kuwa me kake cewa?kana so kace na manta da abinda ya faru yau?that is unbearable"ba ran iya hak'ura ba wallahi"nan da nan kuma yanayinsa ya canja jijiyoyin gaban kansa duk suka riga suka mik'e cikin zafin nama ya d'ago jajayen idanunsa yace"se na koya mata hankali"sena tabbatar mata cewa jami'a ba gidan iskanci bane gidan koyan karatu da ladabtarwa ne" wai ni sameer yau wata banza har zata kalleni ta fad'a min magana"by the side ita 'yar gidan uban wace take jin kanta haka?
Sai a lokacin ameenu ya fahimci inda sameer ya dosa"duk ta k'are dama yasan hakan na iya faruwa'don ba yarda za'ai matashin namiji kamar sameer ace bai samu matsala da mata ba"sai gashi yau yazo masa da zancen"murmushi mara sauti ya yi kafin ya kai dubansa ga sameer ya iya cewa"calmdown prince yanxu akan wata mace kake d'aga voice naka haka?kamar ba sameer d'in dana sani a baya ba wanda kullum kake cemin mace bata gabanka yau kuma ya abin ya canja?ko de ka fad'a mata wani secret na mind d'in ka tayi rejecting ne?fad'amin naji wace lucky gal ta yi nasara akanka haka?"cike da zolaya yake maganar"mugun duka sameer ya kai masa a cinyarsa ji kake d'asss..dan maganar tai mai ciwo"stop it kaga bana cikin wasa yanzu"ko zakai min wasa karka k'ara had'ani da wannan 'yar iskar wacce bata ma san ciwon kanta ba"may be ma iskanci akai da uwarta aka haifeta shiyasa itama take haka amma kana dangantani da ita?ganin yadda sameer ya d'au zafi na ruwan bala'i yasa ameenu sassauta murya ya hau masa nasiha"
Kaga de prince ba'a haka a rayuwa duk laifin da mutum yayi maka baka ai batashi haka don baka san wanne baiwa Allah ya aje a tattare da shi ba"duk da na fahimci akan mace kake wannan fad'an toh ina so ka sani ita mace k'ara min tunani gareta abu k'an k'ani na iya saka ta ga tafarkin dai-dai haka zalika abu k'arami yakan iya jefata ga halaka"saboda su mutane ne masu rauni"idan mace tai maka ba dai-dai ba rabuwa kake da ita sai kai mata addu'ar shiriya".
Addu'ar shirya?shirya fa kace?lallai baka san yarinyar nan ba kenan? ai ba zata tab'a shiryuwa ba" illah kawai na samu hanyar da zan lalata mata rayuwa ta gane cewa tayi kuskure a rayuwarta data d'auki jami'a tamkar gidan b'atanci zalla"kaji de na gaya maka"yana wani gyad'a masa hannu alamun gargad'i".
Toh naji but meye sunanta?
Cike da harara sameer yake kallonsa" kamar shi yayi masa laifin can kuma ya saki wani dogon tsuka yace" i don't care to know that"all what i know de ana kiranta da *'yar jami'a* kaji wani banzan suna"sameer ya fad'a yana watsa hananye"shide ameenu binsa kawai yake da ido kafi ya nisa ya ce toh Allah de ya sawwak'e amma yanzu muci abinci ka huta se na rad'a maka wata sauk'ak'ak'kiyar hanya ko zaka iya binta may be da haka ka rama wanna abun da tai maka"
Jin haka ba k'ara min kwantar ma sameer rai yayi ba don shi babban burinsa dama be wuci yaga ya rama abinda beauty tai masa ba musamman ya samu hanyar korarta a karatunta".
Haka suka zauna gidan bashi ya koma gida ba se can bayan 10:00p.m.koda ya koma watsa ruwa kawai yayi tare a jero nafilfilinsa na dare sannan ya haye makwancinsa".






📓22 *'YAR JAMI'A*📓📓
_BY_ *HERWWERH JIDDERH*
*A.K.A*
*PRINCESS'QUE~DEE




Tun fitowar beauty bata zame ko ina ba sai office d'in malam umar ko da ta isa ta tarar da dashi tare da bak'o"dole ta d'an dakata a waje"kusan minti goma da haka sai ga shi ya fito don raka bak'on nasa ai ganin beauty tsaye gaban office nasa sai kai kawo take a wajen kamar wata zautacciya"dole yayi sallama da bak'on nashi ya k'araso gaban ta cikin sauri"
"Yar jami'a lafiya?

Da saurinta beauty ta juyo daga zagayen da take yi se wani ajiyan xuciya take saki tace"mu shiga ciki wannan ba maganar waje bace"

Gaba ya wuce tana biye da shi a baya har suka k'ara office nashi"tsaye tai gaban kuje ran"yayi yayi ta zauna amma sam beauty tak'i"
Dole shima ya taso ya dawo kusa da ita ya shiga magana cikin tattausan lafazi don ya lura tabbas yau ran mutuniyar tasa b'ace yake"
Pls kyakykyawa ki d'an saki fuskan ki daga wannan cukulewan wlhi sam be dace dake ba"
Wane abu kike so a makarantar nan baki samu ba?
Ina ce na baki file me d'auke da komai na jami'ar nan'kuma da bakinki kince min kingama samun komi naki"
Wait malam kar ka sake cewa ka bani komi"baka bani ba ni zakai ma wayo"cike da tsiwa beauty ke maganan"
Wallahi a iyakar sanina na gama baki komi, amma fad'a min me kike so yanxu?
Kallo me cike da raini beauty ta wurga me dole ya d'an kauda kai"kafin can ta d'ago kai tace:
"Ina so ka gaya min game da wani wai shi sameer alqaseem"tell me waye shi?kuma d'an gidan uban waye a garin nan da har ze zage ni a gaban prof KAS"?

Wqni gauren numfashi malam umar ya saki cike da fargaban sunan da yaji beauty ta kira nan ya ja kujerar dake gefensa ya zauna dan samun cikekken nutsuwa"
A hankali ya matso da wata kujera dake gefensa kusa dashi yayi ma beauty nuni data zauna ba musu kuwa da zauna ta maido dubanta gareshi tana saurare"

Wato kina ji ko 'yar jami'a bazan b'oyr miki komi ba dan nasan mun zama d'aya kuma ko wane abu zaki iya yi a makarantar nan amma bazan tab'a lamunce wa kaina baki damar shiga harkar wannan bawan Allahn ba"dan shi ba malami bane"aikin bautar k'asa ne ya kawo shi nan garin kuma yanxu yaci rabi zuwa k'arshen shekara zebar wajen nan"ki rabu da shi kawai in ma abu yayi miki kiyi hak'uri a karo na farko de pls"!!
What malam umar kasan ko me kake cewa?ai gara kace min baza ka iya ba kawai na nemi wata hanyar amma ba ka tsaya min wa'azi ba"dan ko wallahi ka rubuta ka aje korarsa za'ai a jami'ar nan confirm".

📓24 *'YAR JAMI'A*📓📓
_BY_ *HERWWERH JIDDERH*
*A.K.A*
*PRINCESS'QUE~DEE*





Ta b'angaren beauty kuwa ranar tun komawarta gida d'aki ta nufa ta kulle kanta haka ta wuni ciki"tun abin be dami ummah ba har yakai ga ya fara don sam beauty bata fiya jimawa haka a d'aki ba ko da kuwa baza ta fito parlo ta zauna ba amma dai ta kan lek'o tym to tym sab'anin yau'se de ko da ummah taje ta tambayeta se ta nuna mata ba komi"
Da misalin k'arfe 8:00p.m daddy ya shigo gida sashensa ya wuce inda ya iske ummah tsaye rik'e da garwashi na turaren wuta tana turara falon"wani a jiyar zuciya dady ya saki sakamakon wani daddad'an k'amshi daya doki hancinsa"cike da murmushi umma ta nufo shi tana me ajiye garwashin gefe guda"
Rungume juna sukai na d'an tsawon lokaci wqnda hakan ya nuna tsantar kulawa da missing na junansu da sukayi"umma ce ta shiga janye jikinta a hankali tare da amsan jakan dake d'auke a hannunsa"
Sannu da dawowa dear"
Yawwa umman beauty"ya kula da gida da kuma kanki hope de baki wahalar min da jikin nan naki sosai ba?"daddy ya fad'i idonsa k'uru bisa nata"
Haba dear kaima kasan ba yadda za'ai na wahalar maka da jikin nan naka da yawa,zaka sameshi yau fiye da kullum"
Allah umman beauty??cewan dady yana washe baki.
Sosai ma kuwa! se de fa wani hanzari ba gudu ba yau na kasa gane kan yarinyar can tun dawowqrta a makaranta take d'aki".what??? Amma kuma kike cemin gida lpy?yoh ba gwara komi ya hargitse ba da b'acin ran gudaliya ta"bari naje naji me ke damunta"cikin matsanancin damuwa daya riski daddy lokaci d'aya haka ya nufi sashen beauty"
Knocking......yes daddy come in"beauty dake kwance can saman gado ta juya ma k'ofa baya tai maganan sanin cewa daddy ne kad'ai ke mata irin wannna knocking d'in"
Bud'e k'ofan yayi had'e da kiran sunanta yana mai k'ara sowa cikin d'akin"k'aramin teddy nata dake mak'ale a jikinta ta janyo gami da wurga ma dadmdy shi kamar yadda ta saba in tana matsanancin fushi irin wannan tace pls daddy go away ni bana son ganin kowa yanxu"just go"tai maganan tana turo baki waje"be biye ta nata ba dady ya haye gadon daf da ita ya zauna tare da sak'ala hannunta cikin nashi ya juyo da fuskanta gareshi murya ciki-ciki dady ke tambayan beauty na waye ya b'ata miki rai ki gaya min ko waye shi & i promise u cewa zan dealing nashi kowaye pls my one and only one"lura da yadda daddy ya damu sosai da halin da take cike da yadda dady ke fad'in ze dealing ma damuwanta yasa ta d'an saki ran nata kad'an ta shiga magana uwa tana rad'a"dady wani lecturer ne baya son cigaba na a school d'in nan duk yabi ya dameni yau fa har ikirari yake wai se ya koreni don kawai na samu result me kyau so shine nake so dady ka saka a koreshi kafin shi ya aiwqtar da nashi akaina"
Jim dady yayi a fari da jin batun da beauty ta zo mai dashi yana tunanin hanyar da zai magance damuwan nata"
Beauty meye ne had'inki da wani malami a makaranta kinsan fa duk wani abu dazai janyo na samu nak'asu a har kar kasuwancina beauty bana so"bana so in ji kina rigima da wasu don duk wanda yasan cewa ke 'yata ce zai so kuyi kyakykyawar mu'amala ba mummuna ba"inda san samu na ne har ki gama karatunki ba wanda zai san ki in ba 'yan ajinku ba"suma d'in se dan ya zama dole amma yanxu ni naje nasaka a kori wani ai se a watsa a kafafan yad'a labarai wanda hakan ba karamin zubar min dq k'ima ze yi ba"pls beauty dadynki na baki hak'uri da ki bar maganar nan tunda kince kinyi nasara a jarabawarki watak'il abu kika mai ba dai-dai ba kawai ki bashi hak'uri duk randa kuka had'u kuma ki fita a harkarsa,kinsan fa bana so ummanki ta fahimci wani abu so nake ki bata mamaki duk da tana ganin bazaki iya karatun nan ba ki taimaka mu bata mamaki"ki fita da flying colours se mu had'a wani gagarumin shagali"koya kika ce beauty??fuska ba yabo ba fallasa beauty ke bin dady da kallo duk da hakan da ya fad'a sam be yi mata ba toh ya ma za'ai kamar ita ace ba wanda zai santa sai mate d'inta ashe bata cika *'yar jami'ar*ba,banda cincirun don malamai gogaggu da beauty ke harka da su"dariyan yak'e ta sakar me tare da langwab'ar da kai a jikinsa ta lafe tace ok dady na ji ba komi zan fita a har karsa amma kai ma de kasan bazan je na bashi hak'uri ba but believe me duk randa ya k'ara shiga har kata Se ka d'au fansa daddy"
Dady promise me mana kayi shiru"
Sanin rigima irinta beauty dole dady ya amsa mata da yes"da haka ya kamo hannunta suna ta hira abinsu duk da beauty ta gama k'udurta bin wata hanyar don ganin ta muxguna ma sameer da haka suka sakko dinning inda ummah ta gama jera kayan abinci nan suka zauna don cin dinner"
Sosai beauty ke cin abincin don wata irin matsananciyar yunwa data wuni da ita nan ummah ta samesu itama tai joining d'insu"bayan sun gama ne dady ya k'ara jan hannun beauty falo inda sukai ta kallo suna hira ala dole dady naso ya ga ya kawar ma beauty da damuwarta"
K'arar horn na shigowan mota suka ji dady ne yace toh ga d'an albarkan nan ya dawo"
Hmmm kai da ka sanshi ba? ace yaro tun zuwanshi gidan nan ban tab'a saka shi a ido na ba"ko tunanin yazo ya gaishe ni be yi ba?cewan momy tana kalon dady"beauty ko kamar jira take nan ta soma"ai wallahi umma shiyasa ni tun farko nace ban yarda kowa yazo mana gidan nan ba don duk basu da tarbiyya dady ya nace se yazo".
Hannu dady ya kai ga bakinta yayi saurin tsayar da ita a magana yana cewa kai beauty na kin manta ke kika ce min kin yarda yazo amma bakya son ganinsa a hara bar gidan nan"shine fa nai masa iyaka da cikin gida dan kar yazo ya damar mun ke".
Dariya sosai kake gani d'auke saman fuskar beauty sorry dady kaga na manta,gaskiya dady na k'ara tabbatar wa kana so na fiye da tunani na me too luv you dady"peck ta kai masa a kumatu' nan suka hau dariya na jin dad'i abinsu nan-da-nan beauty ta shiga yi mai surutai kala-kala wani abun ma duk shirme kamar ba wacce ta mallaki hankalin kanta ba"
Mik'ewa ummah tai don takaicin yadda suka maida ita gefe guda suka watsar suna ta hirarsu"duk abin duniya ya isheta ita ba abin tai kishi da 'yar cikinta ba'dole ta nufi sama abinta ta bar su nan falo zaune"

Ba ita ta shiga d'aki ba beauty se wajen 12p.m haka watsa ruwa tare da haye wa gado"wayarta ta janyo ta shiga laluben numbers na wasu daga cikin lectures din abokan harkarta"a inda duk wanda takai ma batu na korar sameer daga aiki se a nuna mata gazawar hakan,wasu kuma su nuna mata yiyuwar hakan amma indai har zata kai musu ziyara a wajen had'uwarsu"dole take amsa musu da eh tunda bata da wani buri yanxu wanda ya wuce taga ta kori sameer daga jami'a kafin shi yayi kamar yadda ya furta mata".






📓📓25 *'YAR JAMI'A*📓📓
_BY_ *HERWWERH JIDDERH*
*A.K.A*
*PRINCESS'QUE~DEE*

💕





Yau take litinin wanda yayi dai-dai da dqwowar d'alibai daga hutun sati biyu da aka basu na gama zangon karatu na farko (wato first semester),kowa ka ganshi cikin shirinsa tsaf na komawa karatu wasu fuskoki na shek'i na samun nasarar jarabawar baya wasu kuma akasin haka"

Zaune take a bakin wata theater rik'e da takadda a hannu"ta na yamutsa fuska xee-xee ta d'ago kai ta dube ta".wai beauty lapiya naga duk kin wani had'a fuska?banxan kallo me cike da jin zafin tambayar beauty ke kallonta dashi can kuma ta kai ajiyan lumfashi tana fad'in ai dama ke baxa kiga komi ba" amma fa ki kalli time table d'in nan har da statistic bayan kinsan bana son harkar calculation"ni wallahi duk naji karatun ya fita a kaina"baki xee-xee ta bud'e cike da mamaki toh da har wani karatu ma beauty ke yi a haka?a xahiri kuwa tace haba beauty ke da jami'a ke hannunki ai bake ba har ni xan so A1 ko ya kikace kawai first lecture d'in xamu shiga da haka xamu gane wa xe d'auke mu in me xafin kai ne na bar ki dashi in kuwa ruwa-ruwa ne ki watso min number d'insa"
Tabbas beauty na matuk'ar jin dad'in yadda xee-xee ke yawan yabonta haka'suna cikin haka sqllama suka ji an sakar musu cikin wata siririyar murya"yi sukai uwa basu jiba haka aka k'ara rangad'a sallamar cikin kasalanci xee-xee ta d'ago kai tana kallonta"matashiyar yarinya ce kana ganinta kaga kamilar mace me cike da addini basai an gaya maka ba"don sanye take da atamfa d'inkin riga da skirt ga doguwar hijab har k'asa"sannan k'afafun nan an suturcesu da safa"
Sannunku"matashiyar ta fad'a"
Yawwa meke faruwa kika xo saman kanmu kikai mana inuwa kamar wata ice?xee-xee kenan tana magana tana wani taunar cingom"cikin halin ko in kula matashiyar ta saki wani k'aramin ajiyan zuciya tace eh dama naga kamar kuma class d'inmu d'aya kuma naga yawanci duk ba'a da time table shine nace bari na tambaye ku? D'agowa tai cikin sauri beauty daga jinginar da tai da kujera ta d'ago kai a karo na farko tana dubanta"
Me kika ce?time me??time table?? Eyyee kaga director kai koma ince rector saboda ga sa'anninki ko?duk fad'in makarantar nan baki ga maraina wayonki cikin sanyin safiyar nan ba se mu ko?bakusan ku yak'in nema ba se an samu kuyi photo copy ki??toh ga time table d'in a hannu na xo ki karb'a?cikin fad'a-fad'a beauty ke maganan tana gyada k'afa"
Jin yadda beauty ke magana yasa matashiyar k'ara san yaya murya tace kiyi hak'uri ni ba fad'a nazo yi ba"k'ok'arin juyawa ta shiga yi don barin wajen don tasan tsayuwarta kan iya haifar da wani abun" wani dogon tsaki mtsssss... xee-xee ta saki a gurin tare da k'ara kare wa matashiyar kallo ta baya"dubeta kucakar banxa ko an gaya mata nan tsangayace ko xauran wa'axi da xata xumbulo mana hijabi luuuuuu....se kuma ta katse maganar sakamakon wata muguwar dariya da taji ta kufcewa beauty"da sauri ta d'ago tana tambayar lpy de?se da tai dariya me isarta beauty sannan ta waigota tana nuna ta da hannu cike da mamaki"
Dilla can kin ganki wai har kura ce xata cewa kare maye" ko kema ba hakan kike tahowa daga gida ba ki shigo mana jami'a uwa matar malam se an xo abi lungu a canja"se kuma ta k'ara tuntsurewa da dariya tana fad'in gaskiya duk ranar da na ganki cikin kayan zafin can dole na ja ki miyi selfie"
Yanda take dariya abin ya matuk'ar bawa xee-xee haushi"wannan ma ai cin fuska ne"cikin fushi ta mik'e wqnda tuni beauty ta rik'o hannunta nan ta shiga bata hak'uri"zama ta koma tai fuska ba yabo ba fallasa take fad'in ok komai ya wuce yanxu ina ki kai?
Yamutsa fuska beauty ta d'anyi kafin ta saki tace'gida xan wuce dama kinga abinda ya shigo dani ta nuna time table"yanxu haka kuma xan fitq a school sede hanxari ba gudu ba yanxu ma na koma gidan ummah ta hau jero min tambayoyin na dawo da wuri"kai duniya wannan wacce irin uwace"?dafe kai beauty tai cike da damuwa kafin ta nisa tace any way daddy ai nasan be fita ba tunda yanxu 9:00a.m be yiba barq nai sauri na koma na samu me karemin"xumbur beauty ta mik'e had'e da sak'ale jakanta a wuya ta juyo ta kalli xee-xee tace kin gane xan wuce se munyi waya"a haka suka rabu beauty ta shige mota ta fice a jamiar ta nufi gida!.






📓📓26 *'YAR JAMI'A*📓📓
_BY_ *HERWWERH JIDDERH*
*A.K.A*
*PRINCESS'QUE~DEE*





Da isarta gida q haraba ta tadda motar daddy ali driver na wanke masa cike da murna ta k'ara so ciki"falo ta dosa kai tsaye tana shirin bud'e labule ta ji an bud'e cikin hanzari ta ja da baya ta tsaya"ummah ce ta fara fitowa rik'e da brief case"daddy na biye da ita"hajara lpy kika dawo gida yanxu ko kin yi mantuwa ne?cewar ummah tana dubanta fuska had'e" dama tabbas tasan haka xe faru beauty don haka tai saurin kai idonta ga daddy inda tai nare da su"gyaran murya daddy ya saki tare da kamo hannun ummah kad'an ya ja da alamun ta sauke idon ta haka daga kallon da take wurgar beauty dashi"burus ummah tai tambar bata ji shi ba inda ma ta sake jefo mata tambayan"da ke fa nake kikai min shiru ko?? Ganin yadda ummah yanayinta ya sauya ya baiwa beauty damar daurewa murya cike da sark'ewa tace emm..emm dama yau ba lecture se gobe bayan munje ne monitor ya sanar"
Badan ummah ta yarda da xancen beauty ba amma dole yasa ta shareta lura da sauyawar fuskar daddy".
"Beauty nah tafiya ce fa ta kamani yanxu haka,bayan fitar ki d'axu governor ya sanar dani wani taro da zashi jarmany na harkar farfad'owar tattalin arxikin kasuwanci"ya kuma nemi dana shirya muje tare yanxu haka jakata na mota xan wuce"
Yeennnnnnn.....kuka beauty ta saki tuni ta shiga buga k'afa tana wani langab'ar da kai da hannu ta hau magana a shagwab'e"yanxu da bandawo ba haka dady xaka tafi ban sani ba"toh Allah nima ka tsaya na had'o kayana mu tafi tare"yunk'urawa tayi da niyyar shiga ciki dady cikin sauri har yana tuntub'e da labule ya biyo bayanta yana kiran sunanta"
Ya ilahi"me xan gani haka?allahu qadirun ala man yasha'u"ita abin ma dariya ya baiwa ummah yadda dady ke biye ma beauty uwa wani rak'umi da akala ganin da gaske sun haye sama sun barta tsaye bakin k'ofa yasa ta dawowa ciki ta nemi kujera ta xauna tana fad'in kuyi ku gama kwa iske ni nan"ba inda xan biku na tadda takaici"

Beauty kam bata zame ko ina ba se gaban wardrobe d'inta ta tsaya saurin rik'o hannunta dady yayi inda ta fincike da k'arfinta tana murgud'e baki tace"ni allah kar ka ce min wani abu se na bika baran zauna ni kad'ai se ummah a gida ba nasan ba fad'a ba wataran duka na zatai"cike da tashin hankali dady a karo na biyo ya k'ara kai hannunshi ga beauty ya rik'ota"
Murya can k'asa uwa me shirin kuka ta shiga bata baki"_beauty na ki yi hakuri ki banni na tafi ni kad'ai kinsan fa wannan ba personal tafiya bane balle nace zani da ke kuma duka-duka fa bazan wuce 1week ba,bqtun ummah kuma tun da naji maganar tafiyar nan na ja mata kunne sosai akan kar ta takura min ke,kinji ko ki dai na damuwa indan wannan ne"da alamun yarda da maganan daddy'beauty ta gyad'a kai tace are sure daddy kai mata fad'an?yes my daughter believe me nai mata"yanxu de gaya min me kike so na baki kafin na wuce"abin ne ma ya samu ga beauty washe baki tuni ta shiga yi nan ta fara zayyano buk'atunta wanda duk basu wuce kayan sakawa ba"nan daddy ya lalo kud'i himili guda ya aje mata wanda ita kanta se da kud'in ya firgitata don bata tab'a ganin dady ya bata

Please Login or Register in order to submit comment