Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya saki ganin yadda sameer yayi sororo yana kallonsa,tureshi ya d'an yi da hannu da zummar ya bashi waje ya shigo,haka ya matsa masa ya wuce ciki ya bar shi nan tsaye!kunya duk ta gama cika sameer ga mamaki tsagwaronsa da yake yi ta yadda ameenu yasan gidan dady,dole ya katse tunaninsa a daddafe haka yabi bayansa!zaune ya sameshi gefen gado don haka shima ya nemi waje ya zauna,kana ganin sameer kallo d'aya zakai masa kasan damuwa ta gama cika shi,fahimtar haka da ameenu yayi ne yasa ya kira sunansa a sanyaye ya amsa ba tare da ya kallo shiba,bai jira cewar ameenu ba ya yi gaggawar furta,wallahi ameenu ni kam an cuce n....hannu ameenu ya kai ya toshe bakinsa yace kar ka yi sab'o ko ka zargi iyayenka sameer,dady yayi min bayanin komai game da lamarin kuma ni banga wani ai bu ba tunda iyaye sun aminci wannan gyaran tsakaninku zaku yi shi,ba tare da wani yaji kanku ba,ka d'auka duk abinda ya faru tsakaninku a baya k'adsara ce da silar ganawa,wasu zafafan hawayen bak'in ciki ne suka fara kwaranya fuskar sameer,sosai ameenu ya tausaya masa amma ya zaiyi dole ya danne damuwarsa akai yayi masa nasiha kamar yadda dady ya umarce shi,nasiha da lallami sosai ameenu yayi masa wanda tun yana kukan harvya fara sauka a hankali yana biye masa a maganar,in da a k'arshe ameenu ke shaida masa ya rok'i dady da ya janye maganar dinner daya shirya a daren zuwa wani lokaci ba da jimawa ba ta yadda za'ai abu kowa na so ba ana ganin bak'in juna ba" haka kuwa dady ya amince,ya mutsa fuska sameer yayi kawai bai tanka saba don shi baya tunanin da ranar da zai iya son beauty a ransa!haka suka ci hirarsu ta ranar wanda duk akan maganar aurensu ne har dare ya fara ratsawa ameenu yayi sallama da sameer akan gobe zai dawo da yamma!!
[10:26am, 16/01/2017] Àúńţý jîđđĕřh: 📓 *'YAR JAMI'A*📓

_BY_*HERWWERH JIDDERH*
*A.K.A*
*PRINCESS QUE~DEE*

176-180




💕In Devotion to yuh my Dearies:


*ANEESA ABUBAKAR RIMI*
*(NEESAHLURV)*

&

*UMMEE ADNAN*
*(TAWAN)*



Ko da ta fito beauty cikin kaya na atamfa riga da skirt d'inkin umbrella shape kayan sunyi matuk'ar karb'arta sai wani d'an yalelan gyale data bi jikinta dashi bayan jaka da takalmi k'irar vinci data cakare jikinta dashi, cikin nutsuwa da jin kunya haka ta k'arasa bakin motar da taga alamun mutum aciki duk da bata tab'a ganin motar a gidan ba da alama ya nemi anfani da itane don kar a gane suna tare, wanda ta ke da tabbacin tuni yana ciki ita yake jira,a hankali ta bud'e marfin motar,jikinta har wani gyarma yake wanda ita kanta ta rasa dalilin hakan ta shiga ciki ta rufo k'ofar,wani sanyin dad'i daya doki hancinta na turarensa yasa ta lumshe ido a hankali kuma ta bud'e su,ya sameer ina kwana,abinda ta iya furtawa kenan murya can k'asa!shiru taji tare da tada mota kamar bazai amsa ta ba har suka isa fita gate sannan taji yace lafiya,daga haka bai k'ara cewa komai ba har suka yi nisa da tafiyarsu amma da mamakinta maimakon su nufi hanyar jami'a sai taga ya karya kan motar ya shiga wani titi,zagaye ya shiga yi yana 'yan dube-dube da alama wani abu yake nema can taji yace yes tare da take burki,gaban wani kanti da aka rubuta womens parlo a saman shi,fita yayi ya nufi kantin, haka bai wani jima sosai ba sai gashi ya dawo hannunsa d'auke da leda mai layi-layi,haka ya shigo yaci gaba da tafiyarsa,bai zame ko ina ba sai bayan ZAHRAIN TWINS THEATER inda yasan yau lecture d'inta ana zatayi,waje ya samu ya tsaya tare da bud'e ledar kallo d'aya yayi mata yaga kalar kayan dake jikinta don haka wata hijab pink colour ya zaro ya wulla mata,kallonsa kawai tayi ba ikon magana don haka ta d'akko hijab d'in ta bud'e tare da sakawa,duk abin nan da take idon sameer na kanta har ta gama ta shiga k'ok'arin bud'e k'ofa zata fita,ke???ya fad'a wanda ya tabbatar da ita yake,tsayawa tai ta juyo ta kalleshi,kansa ya mayar a titi duk da duhun motar yace ki aje wayoyinki cikin motar kafin ki fita sannan in kin gama ki same ni anan sannan ki saka a zuciyarki yanzu ba da bace!daga haka bai sake cewa komai ba,ganin haka yasa beauty zaro jakarta a hankali tayi kamar yadda ya umarta sannan ta fita!.hannu sameer ya buga da k'arfinsa a kan sityarin motar had'e da cije harshe yace u re my destiny!can kuma kome ya tuno a hankali ya shiga jero addu'oi kafin ya kunna motar ya wuce office d'inshi!




Duk wani iri take jin ta cikin hijab karo na farko kenan da ta tab'a shigowa jami'a da hijab,duk inda ta waiga sai gani take kamar kowa kallonta yake duk ta gama tsarguwa da kanta,haka ta nufi cikin theater d'in can lungu haka ta manne jikin ta da bango,ta kuma kwantar da kai a jikin tebur d'in wajen,ba ita ta d'ago kai ba sai da taji alamar shigowar malami ciki,tana juyo fuska ido hud'u su kai kicib'is da wata d'aliba wacce idan bata manta ba a wasu lokutan baya itace wacce ta watsa wa jan biro jikinta sakamakon yabonta da sameer yayi,saurin kauda kai tayi zuwa gabanta nan ma dai idonta ya sauka akan lecturern da ya shigo Prof KAS ta gani sanye da tabaronsa hannu rik'e da marker yana 'yan dube-duben wasu takaddu,tun da tayi tozali da wad'annan abubuwan biyu beauty ta sadda kanta k'asa a kan wata k'aramar jotter dake gabanta ba ita ta d'ago ba sai da ta tabbatar da an rufe darasin d'alibar gefenta na shirin tashi rik'o hannunta tayi ta zaunar da ita,hak'urin abinda ya faru a baya beauty ta rok'a tare da nuna nadamarta akan hakan,da ya ke yarinya ce mai sauk'in kai nan take ta yafe mata,su beauty dai har da karb'ar lambar waya kafin su rabu!
Kayan karatunta beauty ta had'a itama ta nufo waje da shirin fita inda anan ne kuma kowa ya fahimci wace acikin hijabi sakamakon shigowarsu ba d'alibai kamar yanzu da yawa kafin kace me,cece kuce da gulmace-gulmace suka fara yawo,kowa na tofa albarkacin bakinsa,wasu dan tsabar gulma har lek'e suke dan tabbatar da abinda suke zargi,ganin haka cikin sauri beauty har tana tuntub'e haka ta fito a ciki ta nufi bayan theater kamar yadda sameer ya shaida mata,can gefe ta hango motarshi don haka ta nufi wajen,tana k'ok'arin bud'e motar taji kamar daga sama an kirs sunanta cikin kid'ima ta juya me zata gani? K'unyar nan da suka sameta wani lokaci a baya a stop and chop har sukai mata tayin shiga k'ungiyarsu,take suka shiga nuna mata wani mugun salo suna kashe mata ido,bata jira wani abu ba tai azamar bud'e k'ofar kamar wacce aka wullo ciki haka ta fad'o ta rufe k'ofar tana ta faman mai da numfashi!


K'arewa 'yan matan nan kallo sameee yayi tas sannan ya dawo da kanshi wajenta,ita dai kallon nata yayi bai iya ce mata komai ba ya tada mota ya bar wajen,cikin nutsu haka yake tuk'in motar yana zagaya makarantar har ya kai ga muhalin da yake son zuwa,waje ya samu ya tsaida motar ya fito a ciki sannan ya sunkuyar da kai yace mata fito,haka beauty ta fito don ta fahimci inda ya kawota ta bi bayansa suka nufi ginin dake gine a wajen,basu tsaya ba sai da sameer ya kai ga office d'in Prof KAS,nan yayi sallama aka basu izinin shiga suka shiga,zaune suka sameshi ciki kamar kullum yana nazarin littafi,gaisawa sukayi cikin girmamawa amma fuskar beauty ta kasa b'oyuwa a gareshi,duk da sameer ya bashi labarin komai da safe,don haka sai bai yi mamakin ganin 'Yar jami'a cikin wannan shiga ta kamala ba,sameer ne ya juyo cike da izzah ya watso mata wani irin mugun kallon da ya sa tuni tasha jinin jikinta,sunkwi da kai tayi kafin yace baki iya bada hak'uri ba ne? A sukwane beauty ta zube k'asa ta shiga rok'on Allah prof ya gafarta mata abinda ya faru a tsakaninsu,cike da mamaki prof yake girgiza kai na jin dad'in Alk'awarin da sameer ya d'auka masa na cewa sai ta durk'usa da k'afafunta ta nemi gafararshi,yau ga 'yar jami'a k'asan gwiwoyinta,haka dai prof ya amsa mata sannan yayi musu nasiha sosai game da zamantakewar aure,bayan nan kuma suka fito zuwa gida inda a kan hanyarsu na koma gida ne sameer ke tambayarta akan 'yan matan da ya gani,beauty bata b'oye masa komai ba haka ta kwashe labarinsu ta bashi,tab'e baki kawai yayi da jin haka ya ci gaba da tuk'insa!


Haka rayuwa ta ci gaba tsakanin beauty da sameer kullum shi yake kaita makaranta kuma ya d'akko ta tun jama'a basu gano komai tsakaninsu ba har suka gano,bayan da kuma ya nema mata malamin islamiyya kullum bayan sallar magriba yake zuwa nan gida suyi karatu,haka takan ware wani yanki na dare tana bitar karatunta,duk da babu wata kafa tayin anfani da waya gashi yanzu zee-zee ta daina shugowa makaranta kuma sameer ne ke kaita ya kuma dawo da ita babu damar ziyararta don ba wani hira ke shiga tsakaninsu dashi ba!a b'angaren ummah kam abin ba'a cewa komai don kullum da had'i na musamman da ake wa beauty hakan yasa duk ta ciko tai wani haske abinta!

A kwana a tashi ba wuya, yau ya zama ranar da su beauty zasu farar jarabawar k'arshen zangon karatu (wato 2 semester exams),tun safe ta gama shirinta tsaf,haka suka tafi a mota tana ta bitar karatunta sosai sameer yake yaba kwazo irin na beauty,kullum haka take fama da wannan karatun indai zasu tafi don ranar da bashi da aiki a jami'ar dole don ita yake shiga,da haka har ta gama jarabawarta!
[10:26am, 16/01/2017] Àúńţý jîđđĕřh: 📓 *'YAR JAMI'A*📓

_BY_*HERWWERH JIDDERH*
*A.K.A*
*PRINCESS QUE~DEE*

181-185



💕In Devotion to yuh my Dearies:


*ANEESA ABUBAKAR RIMI*
*(NEESAHLURV)*

&

*UMMEE ADNAN*
*(TAWAN)*

Wayewar garin yau ta kasance asabar,sameer na zaune saman kujera cikin d'akinsa daga shi sai singlet da short yana zuma revenge game hankalinsa sosai ya raja'a a game d'in yaji knocking,k'afa ya d'na buga k'asa da alamun rashin son tsayuwa a game d'in sannan ya danna pause ya mik'e kanshi tsaye ya nufi bakin k'ofar don yasan bazai wuce Ali driver bane da yake jininsu yazo d'aya yanzu kusan kullum suna tare a d'aki yana masa tad'i,hannu yasa ya bude k'ofar lokaci guda kuma yana fad'in you are late... bai iya tsaida numfashinsa ba karaf idanunsa suka sauka akan beauty dake tsaye cikin kamala hankalinta naga hijabin da take 'yan wasanninta dashi,jin an bud'e itama yasa tai saurin d'ago kai,sak'onni suka fara saukarwa junansu ta ido cike da mamaki,har wani kyarma jikinta yake sanin bata tab'a ganin sameer cikin yanayin irin haka ba yasa tayi saurin kai hannu fuska ta rufe tace kazo dady na kiranka!tan kaiwa nan da gudu beauty ta ruga ciki cike da jin kunya,kamar wanda aka tsayar sameer ya bita da kallo har ta shige ciki sannan ya maido da dubansa anan murmushi ya saki mai cike da d'unbin tambaya yana susa kai,komawa ciki yayi ya zuro jallabiya a sama sannan ya fito!


Kwance beauty take saman cinyar dady yana wasa da gashin girarta,inda ummah na gefensu zaune tana binsu da kallo,sameer yayi sallama fallon ya shigo kai k'asa ya k'araso ciki,gefe ya tsugunna ya gaishesu kafin nan dady yayi masa iso daya zauna a kujera!bayan ya zauna ne dady ya kira sunansa a hankali sameer ya amsa shi cike da ladabi,cigaba dady yayi da magana" Dama na kiraka ne badan komai ba sai dan na ji meye shirye-shiryenka game da beauty nah saboda a halin da ake ciki ta gama jarabawa kuma kamar yadda mahaifinka ya shaida min da zarar ta gama zaku tare,wannan shine mak'asudin kiran naka!
Eh dama dady ina shirin da nake nayi sallah azahar dama na shigo nan domin na sanar maka akan cewa sati mai zuwa zamu wuce abuja tunda ranar asabar mukayi passing out na bautar k'asarmu, cewar sameer da har kawo yanzu kansa na duk'e k'asa!jin jina kai dady yayi sannan yace toh Allah ya kaimu lokacin!ummah ta amsa shi da ameen,shiru dai beauty take duk jinta take wani iri tun bayan shigowar sameer wanda kawo yanzu hira suke tayi a tsakaninsu banda ita can taji dady ya lakato hancinta yana fad'in yanzu zan huta da rigima,sai kije can kiyi ta masa shagwab'ar taki!cuno baki gava tayi uwa mai shirin kuka tace dady ni d'in ko?yadda tayi maganar a shagwab'ance yasa dukkansu sakin wata dariya,sameer ne ya mik'e yana k'ok'arin barin waje dady ya kira sunansa,har lokacin dariya na d'auke saman fuskarsa yace tsaya ta biyo ka can ku bamu waje muyi magana da mahaifiyarku!hannu yasa dady ya shiga d'agota tana nok'e kai wani kallo da ummah ta watso mata yasa tuni tasha jinin jikinta tayi tsum ta mik'e tana wani cuno baki gaba ta bishi sukao waje!

Tafiya yake sameer tana biye dashi har ya shiga d'akinsa gaban gado ya samu ya zauna ya barta anan tsaye,ganin bai yi mata tayin zama ba yasa itama neman waje gefe k'ad'an dashi ta zauna har lokacin hannunta na rik'e da gefen hijab d'inta tqna 'yan wasanninta dashi!
Wayarsa sameer ya janyo yaci gaba sa game d'inshi wanda a zahirin gaskiya kana ganinsa kansan hankalinsa da inda ya raja'a yana cikin haka yaji an masa game over,take ya saki wani guntun tsaki yayi cilli da wayar saman gado,sai kuma shiru ya biyo baya!ganin wannan shine karo na farko da masoya biyun suka tab'a keb'e kansu sai ya zamana fargaba ta mamaye su,k'arfin hali sameer ya d'anyi ya katse shirun nasu da cewa?kin yi shiru kamar bakya magana?ganin yadda yayi maganar cike da izzah yasa ta maido masa amsa dai-dai da tambayarsa"ai naga wajen daga ni sai kai kar nai magana yau ma ya zama laifi,shiru sameer yayi maganar ta d'an so ta dake shi don ya fahimci inda ta dosa haka ya ci gaba da magana yana fad'in"ai yanzu kin girma baran dake ki ajiki ba sai dai a zuci?baki bud'e beauty ta juyo tace a zuci kuma?ai dad'in ta dai ita zuciya ba'a ganinta bare ka illata min ita"har wani yamutsa fuska take yayin maganar"wanda hakan ya baiwa sameer damar sakin wani guntun murmushi sannan yace ni ko a gani na kafin na kai hannu jikinki zuciyarki na fara kaiwa,domin idan baki manta ba ranar da kika fara shiga lecture a jami'a bayan kin gama kin shiga econs faculty wanda har ki ka fad'arwa wani kyakykyawan matashi wayarsa,alokacin basarwa kawai nayi na wuce sanin cewa dana jima tsaye zaki iya suma don azabtaccen kamun da nai wa zuciyarki,haka ne?yanda yayi tambayar yasa beauty tsuke fuska tamau tamkar bada ita yake ba, tabbas ta tuna yadda taji lokacin da tayi karo dashi don har tana iya kwatanta kyawun fuskarsa a idonta!dariya sameer ya soma sosai ganin ya gama gano lagwanta,da haka kuma sannu a hankali hira mai k'arfi ta fara shiga jakanin masoyan biyu,damar da sameer ya samu ne yasa shi labarta wa beauty abinda ya faru cikin satin inda ya shaida mata cewa an kori malam umar daga jami'a sakamakon wata sabuwar d'aliba da yayiwa ciki,iyayenta suka k'i yarda sannan ya sanar mata yasa an chafko principal tare da discipline master yanzu haka suna hannun jami'an tsaro kafin a tura su kotu!
Shiru beauty tayi tare da juyar da walwalarta zuwa fushi,tausayi tsagwaronsa kake iya hangowa a idanunta ga wani mak'alallen hawaye dake shirin zubowa!
Take sameer ya dawo gabanta ya tsugunna had'e da tarba hannunsa a fuskarta yayi sauri tarbar hawayenta a hannunsa,a hankali ya shiga share mata yana lallashinta,sai daya tabbatar da samun nutsuwarta sannan ya tallabo kumatunta ya shiga magana"Ban yarda a gaban idona ko abayana ki zubar da hawaye ba,kamar yadda ban yarda ki sake wata rayuwa nan gaba ba tare da ni ba, a baya na jahilci kai na game dake ashe abin ba haka yake ba,shiyasa a kullum nake d'aukar abinda ya faru akanki matsayin k'addara a gareki,a kullum ina godewa Ameenu don ya zamanto aboki na gari shine yayi ta nuna min yin hak'uri da juriya don samun alkhairin abu,yanzu princess d'ina gani tsugunne gabanki ina neman yafiyar laifina!
Da jin haka beauty tayi saurin rik'o hannayensa ta shiga yi masa nuni da ya tashi amma sam sameer ya k'i ala dole ta iya furta masa ta yafe!


godiya sosai yayi mata sannan ya shiga yi mata nasiha"inda aciki yake cewa" hajara yau na kira sunanki akaro na farko ba dan komai ba sai dan na sanar dake abinda jami'a ta k'unsa,ki sani ita jami'a da aka kira sunanta mahad'ace ta kowanne irin abu hala mai kyau ko akasin haka,muhalli ne na kazo nazo da mutumin kirki da na banza duk zuwa suke kuma kowa da manufarsa,yawancin iyaye ko jama'ar gari sukan kawo cewa a jami'a ko wane masha'a da alkhaba'i ke faru,wanda ba hakan take ba,tarbiyya ana fara tane tun daga gida,rashin samun kyakykyawar tarbiyya kamar wata k'ofa ce na bud'e b'arna ga al'umma,kinga wasu matan sukan yi anfani da jikinsu,wasu kuma suyi an fani da kud'i haka ma daga mazan yake shiko malami buk'atarsa d'aya kuma da ya samu toh ya wuce wajen,amma kinga duk da haka akwai na Allah wad'anda a komai nasu tsantsar gaskiya da rik'on amana suka saka a gaba,kamar dai Prof KAS,saboda haka na yanke shawarar canja miki jami'a sakamakon fahimta da nayi yanzu kin kasa sakewa da nan d'in,mutanen ciki kamar dodonni kike ganinsu,sanadin canjawa da kikayi kina ganin kamar kowa na miki kallon 'yar jami'a ta baya,bayan mun koma abuja zaki ci gaba da zuwa jami'a kuma karatu zaki yi har sai kin gaji tun da dai matar tawa ta kira kanta 'yar jami'a!duka na wasa beauty ta kai masa yayin da yayi saurin gocewa yana dariya!jan hankali sosai sameer ya yi mata kafin ya canja labarin zuwa yadda shagalin dinner d'insu zai kasance wani satin!
[10:26am, 16/01/2017] Àúńţý jîđđĕřh: 📓 *'YAR JAMI'A*📓

_BY_*HERWWERH JIDDERH*
*A.K.A*
*PRINCESS QUE~DEE*

186-190



💕In Devotion to yuh my Dearies:


*ANEESA ABUBAKAR RIMI*
*(NEESAHLURV)*

&

*UMMEE ADNAN*
*(TAWAN)*



Kome aka sa wa lokaci toh alal hak'ik'a sai yazo,yau take asabar wanda shirye-shiryen tafiya tsaf sun gama had'uwa,a inda dady yayi musu jagoranci,ali driver ya kai su airport suka wuce abuja,ko da suka isa can sameer ne yayi wa dadynsa waya aka zo aka d'auke su,sai dai ummah tuni ta gama tsara inda zasu sauka gidan babbar aminiyarta inda a can ne 'yan uwanta da abokan arzik'i zasu taru,dole ba don yaso rabuwa da beauty ba sameer ya sauke su acan kafin ya wuce gida,bayan isarsa gida ne sameer ya iske ameenu da tun ranar litinin ya taho don ya shirya masa yadda dinner zata kasance,wanda ya tarar tuni an gama komai lokaci kawai ake jira!

_8:00p.m(na dare)_

Dandazon motoci ne na alfarma kana ganinsu kaga zallar ajiyar naira aciki ke ta faman tururuwar shigowa gidan can tsakiyarsu wata doguwar mota ce bak'a tasha wanki sai kyalli take wanda da alama ango ne aciki,haka suka jero suka yada zango a tsakar gidan,yadda abokansa ke fitowa daga motoci cikin kaya na alfarma wanda suma dai sukai ankon shadda blue wanda ita kad'ai zai gaya maka cewa bikin manya ne,hira da dariya kawai kake iya jiyowa ta kowane yanki,sameer dake cikin mota zaune ne ya fito a tare wani irin ihu suka sake ganin ango yasha wanka na had'uwa shadda black ce sanye jikinshi tasha zubin aiki golden colour d'an senegal,sai hula da takalminsa duka baki,hannun nan sanye da agogo itama golden,tattare a lallausar farar fata irin ta sameer abin dai ba'a cewa komai,zagaye shi suka zo sukayi kowa da irin tashi salon tsokanar can ameenu ya lek'o ta cikin mota da yake shi ya tuk'o sameer yace ango lokaci na tafiya fa akira amarya ko naje na fito da ita!wani kallo sameer ya wurga masa sai kuma can yace toh ai sai kaje ta fito da ita mu gani,gaba d'aya waje aka sa dariya wasu na fad'in jealousy!! Abin shina sai ya dawo yana bashi dariya dole ya zura hannu cikin aljihu ya fiddo waya ya shiga laluben lambarta,bugu biyu ta d'auka nan ya shaida mata zuwansu,ko me ta fad'a daga d'aya b'angaren ya bata amsa da ok my princess;da haka ya kashe wayar aka ci gaba da hira ana jiran k'arasowarsu!

Wani lokaci kad'an bayan wannan hayaniya ce ta 'yan mata had'e da gud'a kake jiyowa wanda duk dangin ummah ne na yola da ta sanar dasu bikin suka xo sai kuma 'yammatan gidan da suka fito ga wani k'amshin turare daya lullub'e gidan tun bayan fara fitowarsu,inda 'yan matan amarya suka sanya beauty a tsakiyarsu duk kan ninsu sanye da anko,baka iya hango komai daga shigarta,tafiya suka shiga yi basu zame ko ina ba sai jikin motar sameer inda suka zagaya suka shigar da ita sannan suma suka nufi sauran motocin suka shiga,duk wani zumud'i da rikicewa sameer ya gama yinshi burinsa kawai yayi ido hud'u da gimbiyar tasa don haka cikin sauri shima ya bud'e motar ya shiga" watabarakallahu ahsanal khaliqeen"abinda sameer ya iya fad'a kenan jikinsa na kyarma ya matso daf da beauty ya kai hannayensa biyu ya d'ago ta daga sunkwi da kai da tayi,karaf suka had'a ido wani shu'umin kallo suka shiga jefar junansu dashi inda ko wannensu baki d'auke da murmushi na farin ciki" a haka ameenu ya ja motar saura na biye dashi suka bar gidan,yayin da a hankali beauty ta maida dubanta k'asa tace ni kam ka bar kallo na haka"daga k'asan zuciyarsa ya sako wata dariyar had'e da k'ara matsowa sosai ya matse jikinta da nashi,shinshina k'amshin jikinta ya shigayi,yanda yake bin wuyanta da shinshina yasata fara janye jikinta tana tureshi taji can kamar mai rad'a yana fad'in ki barni naji k'amshin matata ko kuma yanzu labari ya canja,ya zatayi da sameer ta san halinsa idan ya fad'i magana dole ba dan taso ba ta barshi ya ci gaba da abinda yake inda sak'onsa ke ziyartar kwakwalwarta tana karb'a!




Karya kwanar da akai ne aka shiga wani k'aya taccen hotel ya tabbatar da beauty da an k'araso wajen inda cincirindo na motoci suka rigaya suka cika wajen,a bakin event hall d'in ameenu ya tsaida motar a inda sameer ya fito ya zagayo ya bud'e waa beauty k'ofa ya rik'o hannunta k'am kamar wacce za'a kwace masa take masu nan da nan aka fara ruwan d'aukar hoto sai alokacin sameer ya iya k'are mata kallo wanda ita ma dai doguwar bridal gown ta saka bak'i wuluk ta bi jikin nan nata,sai head d'in ta golden da takalminta,sosai beauty tayi kyau,don duk yawancin hotunan sameer na kallonta ake yi,lura da haka yasa ta d'an b'ata fuska tanai masa rad'a ka kalli mai camera mana !shima ya rad'a mata nak'i wayon!dariya suka sa a tare kamar daga sama taji ana mata magana ta baya inda akace amarya ta sha k'amshi,muryar data doki kunnenta yasa ta saurin juyawa don tabbatar da zargin da zuciyarta ke yi mata,nan tayi tozali da zee-zee dake tsaye cikin ankon da ita kanta bata san dashi ba don ta lura kusan kowa yayi ankon,a d'an rikice ta kira sunanta tana nunata da yatsa,cike da jin dad'i zee-zee ta matso tace mata juya bayan dinner mayi magana,haka beauty ta juya sameer ya k'ara manna hannayensu suka nufi ciki!



Sabon kid'a aka saki inda jama'a kowa ya mik'e don tarbar ango da amarya a nutsu suka

Please Login or Register in order to submit comment