Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

baza ki ba just tell me sai na nemi mafita ama ba ki tsaya kina min wani zance mara anfani ba!



Ajiyar zuciya beauty ta saki can kuma ta mik'e jiki ba kwari ta kad'e k'asa da ta shafi kayanta ta shiga tafiya,bin ta sameer yayi tayi yana kuma k'ara gane hanya sosai har suka iso,har ta sa kai tana k'ok'arin shiga zaure taji yace ke? Da sauri ta juya kamar dama jira take tace na'am ya sameer!wani irin duka ya kai ma bango a zuciya kafin nan ya d'ago kai da tuni sun rud'e sun ja jur yace ba na ce karki k'ara kirana da ya sameer ba?call me wit my real name sameer don bana karb'ar tuban d'an muzuru,sannan kisani in har kina so asirinki ya rufu sai kin min Alk'awarin zaki sanar min da duk wani labari naki da dalilin da yasa kike wannan mummunan halayyar taki!saurin d'ago kai tayi jiki na b'ari beauty ta amsashi tana nuni da hannu wallahi duk abinda kake son ji zan gaya maka amma ba yau ba sai ana gobe zamu koma kaga yanzu lafiyar tsoho ya kamata mu kula da ita,kai kuma in Alhaji ya kiraka sai kasan abinda zaka gaya masa wannan shine kad'ai alfarmar da za kai min!
Kallo mai cike da buk'atar amsa sameer ya jefeta dashi ran nan sam babu alamar annuri haka yasa hannu ya tureta can gefe daya ya shige gida abinsa!
[10:15am, 16/01/2017] Àúńţý jîđđĕřh: 📓 *'YAR JAMI'A*📓

_BY_*HERWWERH JIDDERH*
*A.K.A*
*PRINCESS QUE~DEE*

136-140



💕In Devotion to yuh my Dearies:


*ANEESA ABUBAKAR RIMI*
*(NEESAHLURV)*

&

*UMMEE ADNAN*
*(TAWAN)*



Bai takura mata sameer ba har sai da tayi kukan ma'ishinta don kanta ta tsaya,sannan ta d'ago kai a hankali ta kalle shi,har lokacin sameer kan shi na gareta don haka ya kauda kansa a sanyaye ganin yadda beauty tai narai da ido,murmushin k'arfin hali ta saki mai cike da tambaya sannan ta dai-daita nutsuwarta ta shiga magana,"yau zata zamo rana wacce ban yi tsammanin kasancewarta a rayuwata ba,sai dai ina k'addara ta riga fata,babu yadda na iya dole na bud'e sirrin da bai kamata na bud'e shi ba don kuwa bani da wata mafita,ya sameer kamar yarda kasha kirana da sunan karuwa ban tab'a inkari akan haka ba, don duk wanda yasan hajara da halayya irin tawa dole duk sunan da aka kirani dashi na amsa,sai dai abinda baka sani ba koma ince jama'a basu sani ba game dani shine,wannan d'abi'a dole ta sakani yinta ba don naso ba!don kuwa na samo wannan halin ne"
Adalilin principal d'in makarantarmu ta secondary school,da jin haka k'ara gyara zama sameer yayi sosai yana fuskantar ta don jin abinda ta ambata,nan ta ci gaba da magana,eh haka ne magana ta ba k'arya principal d'inmu itace ummul abaisi na duk rayuwar da muka tsinci kanmu aciki,sanin kan kane dai dady bazai sani makaranta mai arha ba,makaranta ta ajin k'arshe wajen tsadar kud'i wanda duk 'ya'yan masau kud'i yawancinsu nan suke yi anan nayi primary don haka bayan na gama na d'ora secondary,anan ne kuma wata rana muna zaune a aji da yake mun zo s.s.s3, bazan tab'a mantawa ba muna karatun geography sai ga discipline master yazo har aji ya kiramu mu uku,jiki na gyarma muka bishi duk mun gama bayarwa dukanmu zaiyi,sai bayan da muka fita ne yake shaida mana cewa principal ke nemanmu,haka ya samu gaba har office d'inta,bayan daya kaimu ne labari ya fara canjawa dayake mace ce principal d'in tana washe baki ganinmu ta shiga zayyana mana buk'atarta ta hanyar wayo da dabara"ta shaida mana cewa yanzu mune ajin k'arshe sannan tasan fatan kowannenmu shiga jami'a nan ta cigaba dacewa ita jami'a ba'a shigarta haka nan sai an shirya haka dai taitayi mana bayani muna ganewa ta kuma shaida mana da tazab'e mu muyi mata wani aiki ne saboda tasan 'yan gidan masu hannu da shuni kamarmu babu zancen takurawa ko matsantawa ta iyaye a tattare damu!bamu gama gane inda ta dosa ba sai da discipline master ya k'ara wayar mana da kai da cewa duk kanmu yana so mu kar muyi applying makaranta d'aya ta yadda zamu cimma burin janyo hanakalin malamai maza,ko wacce d'aliba ta yi k'okarin kawo nata toh darajarta zata k'aru sannan akwai wasu mak'udan milliyoyin kud'i da bayan shekara hud'u za'a bata!jin yadda suke jaddada miliyoyin kud'in anan yasaka kowannen mu amincewa,hakan ya saka bamu tashi a wajen ba duk sai da aka bamu somin tab'i na naira dubu d'ari biyu da hamsin!tare da yarjejeniyar ya zama sirri a tsakaninmu,toh tundaga wannan ranar kullum sai mun je office d'in principal bayan an tashi a makaranta ta k'ara wayar mana da kai yadda zamu janyo hankalin malaman jami'a yayin da muka shiga!


Hankalin ummah ya fara tashi in ban manta ba tun daga ranar data fara ganin d'abi'u na da tarbiyyata ta canja duk da dama ba wani tsauri nake samu ba tunda dady na nan kuma baya son b'acin rai na,kullum rigimar daddy da ummah bata wuce akai na,haka har mukayi jarabawar waec da neco amma duk ummah ta lura ba wani karatu nake ba illah dai kad'e-kad'e da wak'e-wak'e da suka zama jikina,ga kud'i da nake kashewa baji ba gani,wasu dady ke bani wasu kuma principal ke turamin ta account tunda duk ta bud'e mana account,wata rana dana karb'o kud'i daga banki ko dana shigo gida na taradda dady a parlo dole nima na zauna,dana tashi mik'ewa ne tsautsayi hannun jakar ya bud'e wasu mak'uden kud'i suka zubo,wato a lakacin ba ummah da dady ba harta ni kai na sai da gaba na ya yanke ya soma gyarma,amma da yake dady baya son ganin laifi na sai yayo sauri mik'ewa ya fara kwasar kud'in ya mayar min jaka sannan ya kamo hannu na mukayi d'akina,turani ciki kawai yayi shi kuma ya wuce nashi d'akin a ranar ne ummah ta fara gaba da ni wai na fara samun kud'i daga waje,wanda ni kuma tun daga lokacin na fahimci ummah bata so na,bata son cigaba na arayuwa daddy ne kad'ai ke so na!


Haka rayuwa ta jin dad'i da daula taci gaba da wanzar min har ya kawo lokacin da na samu admission zuwa jami'a ranar ji nayi tamkar na zama millioner gani nake nesa tazo min kusa,da murna haka na kira na shaida musu,wanda suma murnar sukai tayi min!

Tun kafin sati d'aya da fara shigowata jami'a tuni na ziyarci duk wani kanti na kaya,mak'il haka na cika drawers dina kaf da k'ananan kaya,takalma da jakunkuna,duk da naso siyan gyale ko da k'anana ne amma principal ta hanani acewarta zasu rage min kwarjini kuma zasu b'oye min kyaun halitta!
Shiru beauty tayi da ta kawo nan a hirarta ta kai hannu fuska,mak'alallen wahayen dake shirin sauka a kuncinta ta goge had'e da jan majina!tsintar kanta tayi beauty ta k'in ci gaba da labarin har sai da ya nemi da taji gaba sannan tayi gyaran murya taci gaba!




Tun daga ranar dana shiga jami'a tunani na bai wuce ta wacce hanya zan samu na cimma burina cikin sauk'i ba,sai kuwa gashi na samu malam umar,mutum na hannun dama a b'angaren neman mata da kud'i na iya samo kanshi don na sakar masa kud'i iyakar sakarwa kafin ya had'a file guda na duk wasu sirrika na malaman makarantar ya bani,ita kuma k'awata zee-zee tunda na fahimci 'yar abi yarima asha kid'a ne sai na rik'eta na fara sakar mata kud'i don sune matsalarta duk da agidan ma bata tsiraba,mahaifinta mutumin kirki ne ga kula da hak'k'in iyali amma mahaifiyarta 'yar Allah bamu musamu ce,ita dai a bata kud'i shiyasa kullum cikin samari masu mota take wai a haka baban na sa ido kenan!
Ina ganin wannan shine abinda kake son ji ko?
Tana tambayar ne tare da maida dubanta ga sameer tana kallo!d'ago kai yayi shima dai ya kallota don abinda yake da muradin ji har kawo yanzu bai jiba nan take kuwa ya fara jefo mata tambayoyi!

"Daga shigarki jami'a zuwa yau malamai nawa kika had'ata dasu?kuma ke nawa ne sukai anfani dake?
A kid'ime beauty ta zaro ido cike da mamakin tambayarsa ta k'arshe inda shima ya zaro mata nasa da zummar eh amsarta yake jira!tab'e baki beauty ta yi sannan ta kauda kai gefe guda cikin murya can k'asa tace mutum goma na kai mata,ni kuma babu,ban gane babu ba?babu me?sameer ya tambaya! sunkwui da kai sosai beauty tayi don tasan bai zama lallai sameer ya yarda da amsarta ba ta k'ara nanata masa da babu d'a namiji ko d'aya da muka tab'a keb'ewa ko ta minti biyar a wajen makaranta dukkan ninsu a waya muke magana bayan na fahimci yanayin mutum toh sai na bashi address nata,wannan shine silar da ya saka ko wane course bana fad'uwa tun shigata jami'a kawo yanzu!
Shima prof KAS da kaga abu ya had'amu na zagaya kuma na zagayo na ga babu wata hanya da zan iya samun makin da nake so dole sai nayi masa abinda nayi masa shiyasa hakan ta faru,bata kai ga rufe baki ba wata tambayar tabiyo baya"toh abincin da kike rabawa na stop and chop shi kuma sadaka ce ko kuwa zakkah?kai duk'e tana kallon k'asa tace shi kuma neman suna ne kawai da son shahara don sun tabbatar min hakan zai saka kowa ya san da zamana a jami'a!




Shi kuma kamal dana ganku tare a mota wancan satin darasi yake koya miki?
a'a beauty ta bashi amsa sannan tace shima munje can sau biyu!
Wani gauran numfashi sameer ya saki mai cike da tuhuma ta b'angare d'aya kuma yana jin dadin yadda yake kallon gaskiya tsagoronta a idanun beauty !dole ya danne yanayin da yake ciki kwallon hannayensa wanda yake wasa dasu ya watsa mata su cikin zafin nama wanda hakan ya matuk'ar raxanata ta d'ago kai a tsorace ta dubeshi"ta mau fuskar nan babu alamar wasa balle murmushi haka ya shiga binta da wani mugun kallo sai can kuma cikin dakewar murya ya shiga magana yana nuna ta da yatsa"kin cuci kanki wallahi,banza, wawuya, asharariya,wacce bata san ciwon kanta ba balle na wasu shin kina tsammanin da haka zaki samu kud'i da wannan mummunar d'abi'ar,amma dai tur da halin kawaliya mace mai neman maza a gari tana kai wa wata can!kin zama akuya mai komai tq samu ya zama nata!don haka ina so ki sani wannan labarin naki karki tsammani abin so ne a wajena,babu abinda ya haifar miki illar tsantsar k'iyayya a fili wanda in kin lura zaki ganta cikin kwayar idanuna!kuma da kike batun kina samun nasara a jami'a toh ki rubuta ki ajiye wannan semester d'in sai kin samu matsala da course d'ina,don na d'au alwashin haka tun ranar da kika tozarta prof a gabana,kika wulak'anta tsohon da bai ji ba bai gani ba!maganata ta k'arshe a wajenk kuma sak'oni d'an ladi ya bani cewar yana sonki da aure,kuma a matsayina na wanda Alhaji yake ganin girma har yakan zauna muyi wasa da raha na furta masa na bashi ke,sai dai kuma kash ina ji masa takaicin namiji salihi zai auri mace mai hali irin naki wacce take wa kanta kirari da 'yar jami'a!


Yanda ya gama lura sameer da k'ofofin kan beauty sun riga da dun gama kullewa da munanen kalaman da yake jefarta dasu ga wasu zafafan hawaye da suka kasa tsayuwa a kumatunta ya sashi mik'ewa a fusace har yana buge k'afarta ta hagu yayi gaba ya barta nan jikin bishi cike da damuwa!
[10:15am, 16/01/2017] Àúńţý jîđđĕřh: 📓 *'YAR JAMI'A*📓

_BY_*HERWWERH JIDDERH*
*A.K.A*
*PRINCESS QUE~DEE*

141-145



💕In Devotion to yuh my Dearies:


*ANEESA ABUBAKAR RIMI*
*(NEESAHLURV)*

&

*UMMEE ADNAN*
*(TAWAN)*

Cike da damuwa tare da danasani haka beauty ta mik'e ta nufi gida cikin mawuyacin hali"shiru ta samu gidan wanda hakan ya tabbatar mata cewa tsoho sun fita da Alhaji zagayen yamma don ya motsa jikinsa, bata zame ko ina ba sai d'akin su d'an ladi a ganinta wannan shine mafi kyawun lokaci daya dace ta yi magana da sameer,sallama biyu tayi amma duk ciki babu wacce ya amsa mata,ga kuma takalmansa a bakin k'ofa wanda hakan ya k'ara tabbatar da ita cewa yana ciki,ba ta damu da jin haka ba sai ma kamo labulen d'akin tayi ta rik'e ita bata shiga ba,ita kuma bata lek'a ciki ba ta fara magana cikin murya k'asa uwa mai rad'a"nasan ya sameer duk abinda ka kira ni dashi wallahi na cancanta amma kayi wa girman Allah wannan magana ta zama sirri tsakanina da kai don idan har sirrina ya tonu a gidan nan wallahi na mutu,nasan dai zuciyarka akwai Allah a ciki,kaji k'aina ya sameer tunda kaga dai ban b'oye maka komai game da ni ba,kai ma ka tausaya min!dariya sosai ta juyo daga ciki har kana jiyo shak'ewarsa saboda dariyar mugunta can kuma sai ya nisa yace ho ho ho gaskiya yaro a kullum dai yaro ne,ke baki ji kunyar aikata laifi ba sai ni kike rok'on naji kunyar tona miki asiri,ai ki d'auka asirinki a fili yake,yanzu dai ki shirya karb'ar hukunci daga Alhaji kawai!cikin wani mawuyacin hali na jin sunan da sameer ya ambato yasa ta yaye labulen da saurin ta ta afka cikin d'akin tana fad'in kayi wa Allah kayi hak'ur.... chak ta tsaya tsaye idanunta suka kafe waje d'aya sakamakon toxali da idonta yayi da sameer kwance saman katifa daga shi sai vest da k-aramin short,kasa dauke ido daga kallonsa tayi wanda shima a tsorace ya tashi zaune yana d'an kare jikinsa da hannu!ganin abin bana k'arewa bane haka yasa shi saurin mik'ewa ya nemi jallabiyarsa ya zura sannan ya juyo a fusace ya wurgo mata wani mugun kallo yace lafiya zaki shigo min d'aki ko sallama babu!a sanyaye beauty ta iya sauke kanta k'asa don bata da abinda zata iya cewa yanzu!komawa sameer yayi gefe da gadon ya zauna yad'anyi shiru!
Dan girman Allah ya sameer kayi hak'uri mana tun d'azu fa nake baka hak'uri ko dan kaga ana lallab'aka shine kake ta wani ja min rai"cike da b'acin rai beauty ke d'aga murya tana maganar!bata tsaya nan ba taci gaba abinta,toh wallahi kaje duk wanda zaka fad'a mawa ka gaya masa tunda kai baka da tausayi,kaje kai tayi,juyawa tayi ta nufi k'ofa sai faman banbami take ita ala dole rai ya b'aci!tana kai k'ofa bakinta ya furta"bama Alhaji ba kaje ka gaya wa mai garin garinnan shine zaka nuna min cewa kai sunanka sameer!



Yaye labulen d'akin tayi a zuciye zata fita taji tayi karo da mutum tsaye!k'ara kai hannu tayi beauty ta yaye labulen baki d'aya!karaf ta dawo a baya ganin tsoho tayi tsaye gefensa Alhaji duk kanninsu fusa babu annuri musamman Alhaji,k'arasowa cikin d'akin sukayi baki d'aya kafin kowa ya ankara ji kake tasss ... Alhaji ya kaiwa wa beauty wani zazzafan mari! sululu beauty tayi nan wajen ta zube k'asa sumammiya!wani irin tsalle sameer yayi sai gashi gaban beauty yana jijjiga ta!amma ina babu alamar motsi take duk wani launi na sameer ya rikid'e daga fari zuwa ja don rikita,ganin yadda ta kafe bata motsi yasa tsoho fashewa da kuka yana fad'in wallahi zuciyarka ta sa yau ka kashe min jikata d'aya da bani da kamarta a doran duniya!kuka sosai tsoho ke yi yana sambatu,lura da haka da sauri Alhaji yayi waje bai jima ba sai gashi rik'e da butar ruwa a hannu baba yagana na biye dashi domin bacci take tayi abinta kukan tsoho ya tasheta!ruwan sameer ya karb'a ya shiga yayyyafa mata inda baba yagana ke jijjigata,wani gauran numfashi na wahala beauty ta saki a hankali kuma ta fara bud'e idonta wani dishi-dishi ta fara gani har ta kai ga bud'e idanunta gaba d'aya"sannu kowa ya shiga yi mata ita dai ba magana sai gyad'a kai,hannun Alhaji tsoho ya kamo yace tashi muje waje mu basu waje,ba musu haka ya tashi ya bisu ya rage saura su uku,baba yagana itama mik'ewa tace bara je na samo miki ruwa ki sha!tana fad'in haka ta fice!k'ara lumshe idonta tayi can ciki-ciki ta ji sameer ya ce sannu!ido rufe ta amsa shi,daga nan kuma shiru ya biyo baya!


_08:00p.m(na dare)_


Tsoho ne zaune gefensa Alhaji sai sauran mutanen gida in banda d'an ladi da duk yammacin yau baya gida!gaba d'aya suna zaune a d'akin tsoho kamar yadda ya umarta!bayan da suka gabatar da sallar isha'i!" Sallama da salati ga fiyayyen halitta ya farayi wanda hakan ya ke nuna akwai wata muhimmiyar magana da zaiyi sannan ya fara da"na taraku ne ba don komai ba sai dan abinda ya faru ga jikata hajjo,duk da dai bamuji komai akan hirar da kuke d'azu ke da yaron nan sameer ba amma tunda har kike rok'on kada Alhaji ya sani hak'ik'anin gaskiya abin bazai xamanto mai kyau ba,don haka baza mu takura ku da sanin wani sirri game daku ba sai dai yana da kyau duk yanda nake ji dake hajjo in naga kinyi wani abu ba dai-dai ba na tsawatar miki don hakan shine mafi k'ololuwar soyayya da zan nuna miki! haka tsoho ya cigaba da yi musu nasihohi masu tsuma jiki da sanyayasu,bayan ya gama ne Alhaji ya d'aura daga inda ya tsaya duk da Alhaji kusan duk fad'a ne nashi da jan hankali,sosai nasihar ta shige su musamman beauty da taron don ita ne! Inda daga k'arshe tsoho ya rufe taro da addu'a yana musu albishir da su xauna cikin shiri gobe akwai abin al'ajabi A k'auyen nan!Dariya duka suka saka inda anan beauty ta samu bakin magana tace watak'il in tsoho zai raka mu mota in zamu tafi zai mana rawa da k'afa d'aya don ya tabbatar mana ya samu lafiya!baki daya suka k'ara kwashewa da wata dariyar tsoho yana mai bata amsa da in har ta kama gobe na juya jiki ai sai nayi!cikin raha,da wasa da juna haka suka rabu kowa ya nufi d'akinsa don kwanciya shiko Alhaji yayi sallama dasu ya fice!
[10:15am, 16/01/2017] Àúńţý jîđđĕřh: 📓 *'YAR JAMI'A*📓

_BY_*HERWWERH JIDDERH*
*A.K.A*
*PRINCESS QUE~DEE*

146-150



💕In Devotion to yuh my Dearies:


*ANEESA ABUBAKAR RIMI*
*(NEESAHLURV)*

&

*UMMEE ADNAN*
*(TAWAN)*

Bayan fitar Alhaji da kusan awa guda sai ga d'an ladi ya shigo hannunsa rik'e da bak'ar leda guda biyu,zarcewa ya yi d'aki inda ya iske sameer kwance akan katifa yana waya da ummah waje ya samu ya zauna har ya gama sannan sameer ya jiyo yace haba mutumina yau ina ka shige haka daga cewa ka bani waje na kafa soyayyarka azuciyar yarinyar nan kawai sai ka b'ace sai yanzu?murmushi d'an ladi ya saki yana d'an girgid'a kai ya d'ago idanunsa sama yace ai yau babbar rana ce agareni kaga kuwa bai kamata nayi wasa da ita ba,tun bayan rabuwarmu dai ban zame ko ina ba sai wajen aminina d'an mai gari can naje muka sha hira duk na baci labarin komai game da hajara kai in tak'aice maka labari shine ya bani naira d'ari biyar da na siyo mana wannan naman!janyo ledar d'an ladi yayi ya mik'o d'aya yace kaga wannan shine namu shi kuma wancan daka ganshi a k'ulle na gimbiya ne"dariya sameer ya saka can kuma ya nisa yace Allah mutumina?kace yau dad'i zamu ci,ai tana can shiga ka mik'a mata kafin tai bacci,washe baki d'an ladi ya shiga yi yana k'ara gyara zaman hularsa akai sannan ya d'akko ledar ya jiyo ya kalli sameer yace ya ka gani d'an birni!jinjina kai yayi da zummar gamsuwa da yadda ya ganshi yace wannan kwalliyar tayi mijin hajjo!cike da jin dad'in sunan da sameer ya kirashi dashi haka ya bar d'akin!
Wai wa yaga 'Yaar jami'a an yi auren k'auye??ai kuwa da musamman zan d'auki katin d'aurin aure na kai jami'a ko dan asha dariya!maganar da sameer yayi kenan cikin raha bayan fitar d'an ladi!


Kwance take beauty duk da ba bacci take ba, amma kana ganinta kasan hankalinta baya tattare da ita tuni ta lula duniyar tunani,har d'an ladi ya zaune nesa kad'an da ita amma bata san da zaman saba,sunanta daya kira ne ya maido da ita hayyacinta,a d'an tsorace ta d'ago kai gani d'an ladi zaune gefenta yasa ta saki wata k'aramar tsuka ta koma ta kwanta!gyaran murya ya fara yi sannan ya mik'o mata ledar!ganin bata karb'a ba yasa shi aje mata ledar ya mik'e zai fita kenan yaji tace ka dawo ka d'auki ledarka na k'oshi!bai bi ta kanta ba d'an ladi ya fice abinsa yana mai cike da farinciki na ko ba komai dai ta kalleshi kuma yasan abun sune kawai na mata na filako amma tana da buk'ata!
Baba yagana dake kwance can lungu da gado ta rufa da abin rufa ta bud'e tace in kin k'oshu ji mik'o min na lashe tunda abin wariyar launin fata ne bai kawo min ba ya biye miki!yamutsa fuska beauty tayi sannan ta mike zaune ta janyo ledar ta bud'e nama ta gani sai k'amshi ke tashi nan tai faro da ido tace loh tashi baba mu ci nama ne ashe!haka baba yagana ta sakko suka nad'i namansu tas suka cinye shi,ruwa suka sha suka koma gado anan ne kuma hira ta b'arke tsakanisu,tun fara hirarsu babu abinda baba yagana ke wa beauty nasiha dashi in banda sirrin zaman gidan aure,duk wasu hanyoyi na tarairayar miji da neman soyayya wajen mai gida babu wanda baba bata labarta mata ba,har takai beauty na mamakin yadda baba tasan wad'an nan bayanan ita da take k'auye,basu suka tsagaita da hira ba sai can tsakiyar dare suka samu suka bi lafiyar gado!!




_11:00a.m(na safe)_


Tsoho ne tsaye bakin k'ofar d'akinsa shirye cikin farar shadda da malin malin waxce tasha guga,Alhaji yayi sallama ya shigo cike da girmamawa haka suka gaisa suka nufi hanyar fita waje har sun kai zaure Alhaji ya dawo ciki ya nufi d'akin su d'an ladi suna zaune suna hira shi da sameer koda ya shiga suka gaisa nan ya kalli d'an ladi yace maza ka tashi ka shirya ka sameni kai d'aya a babban masallacin juma'a na tsakiyar gari!toh d'an ladi ya bisa dashi da haka Alhaji yayi waje ya basu waje!

A b'angaren baba yagana kuwa tun tashinta asuba take tsaye gaban murhu sai girke girke take yi ga wata tukunya can k'arama da lokaci zuwa lokaci takan bud'e ta motsata,bud'ewar da tayi ne na k'arshe taga tukunyar tayi don haka ta juye ta a k'aramin kwano ta nufi d'aki da ita!
Tana shiga ciki zaune ta tarar da beauty tayo wanka tana kwalliya sosai yau kwalliya take cab'awa abinta na komawa gida,kallo d'aya baba yagana tayi mata ta saki dariya tace lallai yau ana gayu anan ita kuma wannan kwalliyar fa?juyi tai da ido beauty tana d'aure d'an kwalin doguwar riga pink data saka,tace wannan kwalliyar komawa gida ce don ni duk na k'agu mu tafi na huta da surutunki!kwanon baba yagana ta ajiye gabanta sannan tace bari zumud'i nan da awa biyu zuwa uku zaki tafi gida nina na huta yanzu dai gyara zamanki kici wannan!yamutsa fuska beauty tayi sannan takai hannu ta bud'e kwanon,kaza ta gani ciki tasha kayan had'i ga romo jikinta sam babu kayan miki,d'ago kai tayi ta dubi baba tace wannan kuma meye?kaza ce mana!ku kuma haka kuke dahuwar kazarku anan toh ni dai d'auki kayanki na k'oshi,da jin haka baba yagana ta samu waje ta zauna,ai kuwa baki isa ba nai miki dahuwa kice kin k'oshi ko ya ya ne sai kin ci,cewar baba!ba don ta so ba haka beauty ta zura hannu cikin kwano ta d'an d'eb'o kad'an ta saka baki!cauu...taji abu ya kama bakinta,su beauty abin nema ya samu ai tuni ta gyara zamanta ta

Please Login or Register in order to submit comment