Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fara kwasar romanta,sai da taci kusan rabi da kwata na kazar nan banda romo da ta sha ta k'oshi sannan ta ture kwanon gefe guda tace Alhamdullah,cike da jin dad'i baba ta janye kwanon daga gabanta ta fice abinta ba tare data tanka mata ba!

12:00p.m( na rana)
Busa sarewa da ganguna kad'ai ke tashi ta ko ina,duk unguwa ta karad'e da hayaniya,ko da sameer ya lek'o ya tambayi baba ko lafiya sai ce masa tayi itama bata sani ba jiran dawowar su Alhaji take!
Ba'a yi minti 30 da maganar ba sai ga tsoho ya shigo gida da sallama cikin sauri ya nufi ma'ajiyar tabarma ya d'auka yayi waje"zaure yajeya shinfid'a wa manyan bak'i sannan ya dawo ciki,sunan yagana ya shiga kira haka ta fito a d'aki da sauri tana lafiya?abincin bak'i zaki mik'o da alamar fahimta haka baba yagana ta nufi inda ta jere kayam abinci data gama ta jidi mik'a masa yana fitarwa waje har ya gama!
Bayan wasu mintina da basu fi goma ba sai ga Alhaji ya shigo gida yana kiran sunan sameer,sameer dake tsugunne gaban k'aramar jakarsa ta kaya yana k'ok'arin zuge zip d'inta don ya gama shirya kayansa tsaf ya ji muryar Alhaji,amsa shi yayi ya fito hannu rik'e da jaka"sororo Alhaji yayi yana kallonsa sai kuma can yace ina zuwa haka?susa gyeya yayi sannan yace dama zan kaita motane kafin ku dawo muyi sallama!ahiyar zuciya Alhaji ya sauke sannan yace toh ajeta anan gefe kazo muje zaure ana buk'atarka acan!umarnin da aka bashi yabi haka ya bi bayansa bayan a jae jakar suka nufi zaure!
[10:25am, 16/01/2017] Àúńţý jîđđĕřh: 📓 *'YAR JAMI'A*📓

_BY_*HERWWERH JIDDERH*
*A.K.A*
*PRINCESS QUE~DEE*

156-160



💕In Devotion to yuh my Dearies:


*ANEESA ABUBAKAR RIMI*
*(NEESAHLURV)*

&

*UMMEE ADNAN*
*(TAWAN)*


Daga fitar baba yagana bata zame ko ina ba sai d'akinta inda ta tarar da beauty kwance tana ta waya abinta dariya sosai take yi da alamar wayar da take tana jin dad'inta,waje baba ta samu ta zauna tana jiran gamawarta,ba wani lokaci mai tsawo ta d'auka ba sai gashi tayi sallama sa wadda ta kira da zee-zee sannan ta kashe wayar,kallo ta kai wa baba sannan tace ma,aikaciyar tsoho ya kayi ne?harara baba yagana ta watso mata sai tace saboda kin rai na ni nice ma'aikaciyar tsohon?dariya beauty ta maida mata ba amsa,gyara zamanta sosai baba tayi sannan ta juyo ta fuskance ta sosai,sunanta ta kira,beauty ta amsa tana k'are wa wayar ta kallo"hajara ina so ki nutsu kuma ki saurareni da kyau kisan cewa ita wannan duniyar kome muke aikatawa dama muk'addari ne daga Allah sannan mafiyawancin abubuwa na rayuwa da muke ganinsu ba alkhairi bane toh sune mafi Alkhairi a wajenmu amma mu bamu sani ba,don haka ina yi miki umarni amatsayi na na 'yar uwar mahaifiya a wajenki wacce nasan ko ita mahaifiyar taki zan gaya mata taji,daki ji tsohon Allah a zamantakewarki ta rayuwa,sannan yi biyayya ga na gaba dake domin abinda suka hango miki na ci gaban rayuwa ke bazaki tab'a hango shi ba,nasan yanzu baza ki fahimci me nake nufi ba Amma in kika koma gida ummanki zatai miki cikakken bayani,a k'arshe ina miki addu'ar Allah yayi miki albarka! Beauty ta amsata da ameen!
Tana kaiwa nan a maganarta baba yagana ta mik'e ta nufi jerin samirunta dake mak'ale a cikin kwabot ta zaro wata k'aramar samira bud'eta tayi ta janyo k'ullin dake ciki a rufe a bak'ar leda,beauty dai na biye da ita da ido har ta dawo ta zauna,hannun beauty ta riko ta saka mata shi sannan ta maida ta rufe nan tace hajara ki adana wannan zai miki anfani duk ranar da Allah yasa kika tarr a d'akin mijinki ko bayan rai nane kafin mu'amala ta auratayya ta had'aku ki tabbata kin jik'ashi da ruwa kin sha"hannu ta kuma kaiwa k'ark'ashin gado inda ta janyo wani farin mayafi ta yafawa beauty sannan ta saki murmushi tace toh haka yau zaki komawa ummanki nasan zatai farin ciki in ta ga wannan gyalen jikinki!
Kalaman baba yagana duk sun gama d'aurewa beauty kai inda kunya ta gama lullub'eta dan jin maganar baba ta k'arshe na abinda ta bata,don duk wasansu basu tab'a magana irin haka ba!



Suna cikin wannan hali ne suka ji shigowar tsoho da Alhaji,sunan yagana suke kira baki d'ayansu dan haka cikin sauri ta fito tana tambayar ko lafiya?Alhaji ya tambaye ta ina yaran suke?suna cikin d'aki! Yana jin haka ya shiga kiran sunayensu a tare,sameer ne ya fara fitowa d'an ladi na rik'e da hanunsa gaba d'ayansu fuskokin nan babu alamar annuri,sai can ga beauty ta fito rike da jaka a hannu,tsoho na ganin yanayin beauty sam babu alamar damuwa ko b'acin rai a tattare da ita cike da zolaya yace lallai yaran zamani wato ke farin cikin tafiya ma kike ki barni ko?itama dai cikin wasan ta maida masa da ehh mana ni daman duk a k'age nake na koma garin mu,dariya tsoho ya saki sannan ya tsagaita tak'aitacciyar nasiha yayi musu sosai mai tsuma jiki inda duk ciki jan hankali ne da hak'uri ga al'amuran rayuwa sannan ya sanar dasu cewa basu kad'ai zasu tafi can ba har da Alhaji da wasu mutanen!toh kawai suka amsa da shi sannan suka fiddo kayansu baba yagana na rik'e da hannunta har suka fito waje!

Cincirindo na mutane da motoci,beauty ta soma gani tun fitowarta inda nan take gabanta ya yanke ya shiga fad'uwa cike da d'unbin mamaki ta kalli baba tace wannan mutanen fa haka baba?da yake baba yagana ta shirya ma amsa wannan tambayar tuntuni don tasan ba makawa sai ta afku nan take ta bata amsa da nad'in sarauta akayi shiyasa kika ji unguwar ta rikice Alhaji aka baiwa muk'ami don haka in kunje can gida an nutsu sai ki masa tayin murna!toh ta amsa ta dashi da haka ta kaita har inda motar sameer take ta bud'e ta shiga gidan gaba ta zauna,haka tana kallon Alhaji ya shiga wata mota doguwa fara tare da wasu jama'a kana ganinsu kaga mutane 'yan alfarma,inda d'an ladi ya rako sameer har bakin mota sukai sallama beauty na masa bankwana amma yadda yayi shiru uwa bai ji taba don haka itama ta basar don ta lura da yanayin nasu gaba d'aya yai sai a hankali,ko b'acin ran rabuwa da juna ne oho musu!



Tafiya suka shiga yi cikin nutsuwa haka yake tuk'in inda motoci uku ke bayansa a jere,tun bayana shigarsu mota babu wanda ya iya ko da kwakwkwaran motsi baran tana magana,dukkan ninsu tunani tsagwaronsa ke cinsu sak'a wannan kunce wancan haka har suka yi nisa sosai a tafiyarsu,k'ishi daya taso masa ne ya janyo ruwa faro dake gefe dashi ya bud'e a hankali ya shiga sha,d'agawarsa ta k'arshe ne yasa shi kwarewa da sauri ya sauke ruwan ya shiga tari,jin yadda yake ta faman tari da alama ya kware da yawa ya saka beauty d'ago kai ta sauke dara-daran idanunta akanshi ba tare da wani tunani ba tace masa sannu ya sameer!banza yayi da ita uwa bai ji mai take cewa ba yaci gaba da tarinsa,ko zaka tsaya da motar ya fad'a maka?a raunane ya d'ago kumburarrun idanunsa ya sauke su akanta,kallon da yake watsa mata kad'ai ya isa ace tasha jinin jikinta,d'auke kai tayi daga kansa ta maida kan titi wanda hakan baisa ta tsaya da maganarta ba taci gaba,hmmn yanzu dai ba da bane da zaka kashe mota ka jibgeni,kuma kar kai tunanin abinda kai min abaya yanzu zan d'auke shi,wallahi bazan k'ara tsayawa wani namiji ya tab'a lafiyar jikina ba,kar kaga na saurara maka dama can saboda tsorona da Alhaji ne amma kaga yanzu yadda na d'akko hanyar gidan nan komai ta fanjama-fanjam,cikin b'acin rai da d'acin zuciya haka kalaman beauty ke dokar kunnuwansa,wato wani wawan damk'a daya kai hannu yayi mata saman kanta cikin zafin nama ya kai gab da gaban motar kenan zai buga,kamar daga sama ya ji maganganun baba yagana na dawo masa ....kaji tsoron Allah kuma ka sani hajara ta zama abin kiwo a wajenka......a sulale ya iya zare hannunshi daga kanta wanda tuni beauty ta gama sakin jiki taji inda kanta zai kasance taji an sake ta,hannunsa ya buga jikin sitiyarin motar yace"wallahi an cuce ni"an cuceni"why me? Dariya beauty ta saki ganin yadda yake ta faman haki kamar wani mayunwacin zaki,fari tai da ido kamar yana ganinta tace Allah dai ya kiyaye maza basuyi abun kunya ba,in banda matsoraci wake dukan mace?dariya ta k'ara sakar masa,inda abin duniya ya gama cika sameer CD na motar ya kunna ya k'ure k'arar motar k'ira'ar sudais ta hau tashi sosai ya shiga binsa ko ya samu sassauci a zuciya!
[10:25am, 16/01/2017] Àúńţý jîđđĕřh: 📓 *'YAR JAMI'A*📓

_BY_*HERWWERH JIDDERH*
*A.K.A*
*PRINCESS QUE~DEE*

161-165



💕In Devotion to yuh my Dearies:


*ANEESA ABUBAKAR RIMI*
*(NEESAHLURV)*

&

*UMMEE ADNAN*
*(TAWAN)*


Misalin k'arfe 12;00p.m(na rana) a agogon hannun sameer wanda yayi dai-dai da shigowarsu gidan dady a parking space ya aje motar haka sauran motocin suma suka aje nasu!bara dai na wullar da kwallon mangwaro na huta da k'uda haka beauty ta fad'a tare da bud'e marfin motar ta fita abinta,hanyar shiga babban falo ta bufa ta kai hannu kenan zata bud'e k'ofa taji an riga ta turo k'ofa matsawa tai da baya gudun kar ta bige ta tsaya tana jiran ganin mai fitowa,ido ta zaro waje da gudu kumaa ta fad'a jikinsa dady ta gani tsaye ai kuwa ta shiga rero kukan shagwab'a tana bubbuga k'afa a k'asa,idan ran dady yayi dubu tuni ya gama rikicewa don babu abinda ke dagula masa lissafi irin kukan beauty,tambayarta ya shiga yi ko lafiya amma sam tak'i tanka masa,Alhaji da mutanen wajen haka sukai sororo suna ganin ikon Allah ganin abin nasu ba mai k'arewa bane yasa Alhaji yayi k'arfin hali ya k'araso wajen ya daka mata tsawa don yanzu ba halin dukan matar wani,dole ta janye jikinta daga na dady tabi gefe ta shige gida da gudu,babbar rigar jikin dady ya shiga gyarawa yana cike da fara'ar gani amininsa mahaifin sameer da d'an uwansa har da wasu mutum uku daga danginsa,cikin girmama juna haka ya k'arasa wajensu suka gaisa tare da yiwa juna murnar abinda ya had'a tsakani,haka sameer shima ya fito kai a k'asa ya gaida dady ya amsa,iso dady yayi musu dasu k'araso ciki nan suka d'unguma suka nufi falo,sameer dake tsaye yana k'ok'arin yin sashensa kamar yadda ya saba yaji Alhaji ya rik'o hannusa yana nuna masa hanyar falo dole ba don yaso hakan ba ya bi bayansa suka nufi ciki,ji yake a halin yanzu babu abinda yafi buk'ata irin kad'aituwa ba tare da wani ya shiga lamarinsa ba amma ya ya iya da lamarin Alhaji!.


A babban falo suka sauka nan hira sosai ta b'arke a tsakaninsu bayan nan ummah ta fito suka gaisa da yake tun safe tana kitchen da ma'aikata ana had'a abincin tarbar bak'i,nan da nan kuma aka shiga jere kayan ciye-ciye da tand'e-tand'e,sameer dai ido kad'ai yake iya binsa dashi don gaba d'aya tunaninsa baya wajensu,ga wani uban tagumi daya dasa kamar wanda akaiwa mutuwa,lura da hakan dady yayi nan ya kalloshin sosai yace sameer ki zaka je ciki ka d'an watsa ruwa ne?dady bai gama rufe bakinsa ba kamar dama jira yake sameer yace ehh dady!yana kaiwa nan ya mik'e ya nufi waje sai sashensa!


_4:00p.m (na yamma):_
Sameer ne kwance saman gado ya rufa da bargo duk da ba bacci yake ba amma dai idonsa a rufe yake,ya ji an bud'e k'ofar d'akin an shigo,bargon dake rufe a jikinsa yaji an yaye an shiga daddab'ar shi a hankali ya bud'e idanunsa karaf ya sauke su akan na Alhaji,cike da mamaki Alhaji ya k'ara kai hannunsa a wuyan sameer inda yaji zafi, meke damunka sameer?tambayar da yayi masa kenan!lumshe ido sameer yayi nan take kuma ya bud'esu ya sauke akan Alhaji, ya bashi amsa da babu komai!jinjina kai yayi na alamun bai gamsu da maganar sameer don haka yace toh tashi zaune muyi magana,ba musu sameer ya zauna ya zuba ido yana sauraronsa,sunansa ya kira samee sannan ya ci gaba da magana, A hak'ik'a njn gaskiya sameer na lura da rashin amincewarka da wannan abin alkhairi da nayi,tunda duk cikinmu ba yara balle su kasa gane halinda kake ciki,amma kasani banyi haka don na muzguna ma rayuwarka ba a'a sai dan na inganta ta,duk da nasan halayyarka da hajara ba d'aya bace sai dai kuma kai kad'aine zak iya zama da hajara a halin da ake ciki,don kuwa in har zaka iya rik'e sirrinta toh mene kuwa baza ka iya jura nata ba"ka d'auka wannan aure da aka had'a cigabane na rayuwarku baki d'aya kuma in har kayi hak'uri nan gaba zaka ji dad'in abin!
Shiru dai sameer yake,kai k'asa yana jinsa don haka ya ci gaba"sameer a yanzu ne ake auren soyayya mu da mukai namu ina muka san wata aba soyayya ai sai wacce iyaye suka zab'a maka amma kai fa har halayyarta ka sani kuma nasan duk wani abu nata ba wanda baka sani ba ciki da bai,sai dai bazan tauye maka hak'k'in ka ba sameer kai ma d'ana ne yanzu kamar yadda hajara take 'ya a wajena,gaya min meke saka kuka da har damuwa takai ka ga zazzab'i don daga jin jikin nan naka ba lafiya!
Mai makon sameer ya bashi amsar tambayarsa sai hawaye da suka fara bin kuncinsa,nan Alhaji yayi juyin duniyar nan amma sameer ya k'i magana har sai da yaji yace bari ya kira masa mahaifinsa ko shi zai iya gaya masa sannan yayi k'arfin hali murya can ciki yace Alhaji ni fa ina zargin hajara kuma kaga aure ai bazai yiyu da zargi ba?cike da mamaki Alhaji ya ke duban sameer had'e da nanata kalmar zargi a cikin ransa, dayake Alhaji bana yau bane kuma yasan halin da duniya ke ciki nan ya kamo hannun sameer yace,hakane maganarka d'ana aure baya yiyiwa da zargi amma ina rok'onka wata alfarma,nan sameer yace wace irin alfarma kuma alhaji?gyara zamansa yayi yace ina neman alfarmar ka tare da hajara a gidan nan kuma yau d'in nan idan har ka sameta yadda kake so toh shike nan idan kuma ka samu aka sin haka wanda bana fata toh ni zan baka alk'ami da takadda ka rubuta mata saki uku kwarara"d'ago kai sameer yayi yana kallon Alhaji yadda yake maganar da sigar gaskiya ainun!shiru yayi kafin nan ya gyad'a masa kao da niyyar amincewa sannan ya k'aro wani k'orafin yace"a aure na na ci burin yin shagali na gani na fad'a gashi hakan bai yiyu ba!nan ma dai murmushi Alhaji ya sakar masa sannan ya kuma ce waya gaya maka burinka bazai cika ba? Ai tun shekaran jiya dady ya dawo garin nan kuma na labarta masa komai ta wayar mai gari,kuma ni na umarceshi da karya sanar da hajara har sai ta dawo gida ta ganshi,yanzu haka maganar da akeyi yana can ya tarasu ita da mahaifiyarta ni yake jira mu sanar da hajara halin da ake ciki!da zarar ta sani zuwa dare dadynta da mahaifinka sun had'a k'ayatacciyar walima ko dinna ko me?a wani k'aton waje kuma duk sun gama gayyatar duk wasu wanda ya kamata a halarta kaga bayan daren yau duk shawarar daka yanke,inda yiyuwar ka tsara naka walmar daga baya kun tsara kai da matarka!yanzu dai bara naje can naga yadda zamu kasance!yana kaiwa nan ya tashi yayi waje ya bar sameer da wani sabon tunanin!
[10:25am, 16/01/2017] Àúńţý jîđđĕřh: 📓 *'YAR JAMI'A*📓

_BY_*HERWWERH JIDDERH*
*A.K.A*
*PRINCESS QUE~DEE*

166-170



💕In Devotion to yuh my Dearies:


*ANEESA ABUBAKAR RIMI*
*(NEESAHLURV)*

&

*UMMEE ADNAN*
*(TAWAN)*



Beauty dake zaune gefen dady ta d'aura hanneyenta saman cinyarsa yana matsa mata su a hankali sai ummah dake gefe guda saman kujera inda ta bisu da kallo da haka suka ji sallamar Alhaji,k'ara so wa yayi ya samu waje shima ya zauna,wanda hakan ya dawo da beauty cikin hankalinta,take ta janye jikinta ana dady tanutsu sosai kamar ba ita ba,k'ara gaisawa Alhaji yayi da ummah sannan ya kalli dady yace masa toh Alhaji ai ina ganin sai ka sanar da ita komai ko!wasu k'anana muzurai da ido dady ya somayo alamun Alhaji yayi magana kawai shi basai yayi ba,don haka ya d'ora daga inda ya tsaya"hajara"Alhaji ya kira sunanta,cikin sanyayyar murya beauty ta amsashi tana sauke kai k'asa,Alhaji ya soma magana,wannan zama da mukayi anan ko kuma ince wannan taro da kike ganin ana ta yin shi tun daga can k'auye har kawo nan ba ana yi don kowa bane sai don ke"cike da mamaki beauty ta d'ago suka had'a ido da dady nan take dady ya kauda kai gefe,wanda hakan ya baiwa Alhaji damar cigaba a magana ina so ki saurare ni da kunnen basira kiji me zan gaya miki,a matsayinmu na iyayenki wanda suka gi cancanta da mu gina miki rayuwarki kuma mu zab'a miki mijin aure don haka yau mun sauke hak'k'inmu akanki mun had'a ki aure da d'an uwanki sameer !firgigit beauty tayi take kuwa ta mik'e tsaye cikin d'imauta tabi Alhaji da kallo idanunnan sun gama cika da hawaye amma sun kasa samun muhallin zuba k'asa,dumm...taji kanta yayi mata ta yadda take ganin abin uwa mafarki,lokaci d'aya kuma ta saki wata irin k'ara ta shiga shure-shuren k'afa uwa zararriya,dady ne ya yunk'ura zai yo kanta Alhaji yayo saurin tsaidashi da hannu badon ya so ba haka dady ya tsaya shima tuni hawaye ya gama cika idanunsa na tausayin 'yar tasa,wata irin gigitacciyar tsawa Alhaji ya watso mata take ta shiga hankalintabta tsaida shurin k'afar amma ta kasa dai na wayayen don tasan basu tab'a wasa irin haka da Alhaji ba,abinda ya faru tun daga had'uwarsu da sameer,zuwanta k'auye,kai kawo yai da zasu bar garin minjibir babu wanda ya k'ace mata a tunani,yadda baba yagana ta gaya mata nad'in sarautar Alhaji ashe duk ba haka bane,kukan da ya sameer yake yasan da aure na dashi ne?toh waye ya k'ulla abin nan,sameer?Alhaji ko kuwa tsoho?tunani sosai beauty ta duk'ufa yi ganin ba mafita yasa ta sulale wa kasan kafe ta shiga maida ajiyar zuciya mai cike da kukan zuci,ba ummah ba hatta shi kan shi alhaji sai daya tausaya wa halinda take ciki mazantaka kawai ya nuna don yasan aikin gama ya riga ya gama,a karo na biyu ya k'ara kiran sunanta,shiru ta bishi dashi,don haka sai bai damu ba ya ci gaba da magana cikin fad'a"aure d'aurashi yau akan sadaki dubu d'ari,wanda tuni na damk'asu ga mahaifinki,sannan ki zauna da shirin biyayyar aure ba hauka ko wauta ba,in kuwa naji wani abi sab'anin zaman lafiya, zan wanko k'afa har muhallinki na baki mamaki,kin dai san ni sarai?sannan daren yau ki shirya za'a yi walimar biki akai ki d'akinki!

Ko da Alhaji yazo nan a maganar shi sai ji tayi beauty ta kasa d'aukar girman maganar,ace yadda zamantakewa tasu take da sameer yau ita za'a kai d'akinsa?ai tuni ta mik'e wiwi ta shiga kuka tana buge-buge surutai barka tai marasa kan gado,sosai beauty take sharar kukanta kowa ya ganta a halin da take ciki dole ya tausaya mata,kasa jure hakan dady yayi da saurinsa ya k'arasa gabanta bai bi ta kan Alhaji ba tsum ya rungumota ta fad'a jikinsa ta shiga rero wani sabon kukan,kasa danne zuciyarsa shima dady yayi kafin kace me sun had'a kai da juna suna kuka,
Sororo Alhaji yayi yana kallon abin mamaki,takaici duk ya gama cika shi na yadda dady ya gama sangarta beauty,wani dogon tsaki ya saki tare da fad'in toh Allah dai ya kyauta,da haka ya nufi hanyar fita yayi b'angaren bak'i inda aka tanadar wa mahaifan sameer!

Bayan fitar Alhaji ne kuma ummah ta mik'e jiki ba kwari ta nufi wajen da su dady ke tsaye rungume da juna,hannun beauty ta rik'o a hankali ta d'ago kai tana kallonta,janye ta ta shiga yi daga jikin dady nan tayi hanyar d'akinta da ita amma har lokacin hawaye bai bar zuba a idon beauty ba"
K'ofar d'akinta ta bud'e tare suka shiga ciki, ta nufi bakin gado ta zaunar da beauty k'aramar kujera dake sak'ale gefen gado ummah ta janyo ta jinginata gaban gado ta zauna suna kallon juna!
Sunanta ummah ta kira,cikin kuka beauty ta amsata"nan kuma ummah ta fara magana"ya kamata ace kin tsaya da kukan nan hajara don bazai anfanar dake komai ba,tunda Alhaji ya zartar da hukunci,duk da d'an uwana ne amma a zahirin gaskiya ban ji dad'in sigar da yabi ya sanar dake wannan al'amari ba,sai dai ki sani hajara mu iyayenki muna sonki kuma baza mu tab'a aurar dake ga mutumin banza ba!amma abu d'aya da na lura dashi daga ke har sameer d'ib babu mai farin ciki da wannan abu,kamar yadda na lura da ranar tafiyarku minjibir karo na farko da kuka had'u a tsakar gida razanar da ki kayi bayan kin ganshi ce ta tqbbatar min da kun san juna a baya,don haka hajara ina miki magana a matsayina na mahaifiya agareki da ki ji tsoron mahaliccinki ki sanar dani shin meke tsakaninki da mijinki sameer??!!.
[10:25am, 16/01/2017] Àúńţý jîđđĕřh: 📓 *'YAR JAMI'A*📓

_BY_*HERWWERH JIDDERH*
*A.K.A*
*PRINCESS QUE~DEE*

171-175



💕In Devotion to yuh my Dearies:


*ANEESA ABUBAKAR RIMI*
*(NEESAHLURV)*

&

*UMMEE ADNAN*
*(TAWAN)*



Meke tsakina da mijina sameer kuma?yanzu shike nan kowa kallon matar sameer zai na yi min?zancen zucin da ya k'are zagayensa cikin zuciyar beauty kenan,jin kuma ummah ta tab'ota da hannu yasa ta dawowa daga matsakaicin tunanin data shiga,hawaye na bin kuncinta haka beauty ta shiga zayyano wa ummah duk abinda ya faru bata b'oye mata komai ba kama daga kana principal d'insu har zuwanta k'auye'salati da sallallami ummah ta shigayi bayan da beauty ta gama bata labarin cike da mamakin yadda d'iyar cikin jal a duniya wannan abu ya faru da ita,abinda take ji a gari yau gashi a gidanta,ganin hakan bazai anfana mata da komai ba yasa ta share mak'alallen hawayen dake manne idonta ta d'ago kai tana duban beauty kafin daga bisa ni ta ci gaba da magana"hak'ik'a hajara na so tarbiyyarki ta k'arfafu fiye da yadda kike zato,na so na baki soyayyar da ke kanki sai kinyi alfahari dani nan gaba,amma ina kaddara ta riga fata,mahaifinki ya d'auki son duniya ya d'aura miki inda har ya cusa miki wasu d'abi'u da har kike ganin tamkar na tsaneki,baya son ganin laifinki akan komai,yanzu wa gari ya waya?ke kuka shi kuka,don ma Allah ya taimake mu raya sunna zaki ba wani abu ne maras kyau ba hajara da ya zami da kanmu,yanzu kina ganin da wanda zai miki kallon mai mutunci a jamiar da kike ikrarin wai ke 'yar jami'a!hak'ik'a ban ga laifin sameer don yayi kuka da aurenki ba!don shi ya san mai ya gani na aibu game dake!sai dai kuma koma meye hannunka baya lalacewa ka yanke ka wurgar dole nid'in nan dai nice uwa wacce kukan ki dana mahaifinki ya zama dole na share muku,zanyi anfani da kowacce irin hanya ta gari naga na dawo miki da martabarki ta 'ya mace wacce nasan shi kanshi sameer zai dawo yayi alfahari dake!
Yanda kuka ke bin kuncin beauty haka dariya ya bayyana saman fuskarta,da sauri ta matso gaban ummah ta rumgumeta ta shiga wani sabon kukan tana mai jin son uwartata sosai a rai!



_8:00p.m(na dare)_
Bugun k'ofar da ake a cikin gidan ne ya sanya sameer da ke kwance lullub'e da bargo fitowa daga ciki ya nufo a tsammaninshi zai ga Alhaji,saurin ja da baya yayi abin da ya gani yayi matuk'ar d'aure masa kai,amininsa ameenu ya gani tsaye cikin wata dakakkiyar shadda,fuskar nan d'auke da fara'a,dariya ameenu

Please Login or Register in order to submit comment