Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mata kenan,ta jima tana tunanin mafita sai kuma can dabarar kama wajen ta rike da hannu ta yadda zai b'oye jan dake wajen ya zo mata"haka kuwa akayi ta kama bayan hijab ta rik'e ra nufi bayi ta cire sannan ta nemi taimakon wata d'aliba data shiga masallaci ta d'akko mata hijab dake rataye na sallah ta saka"bayan data gama gyara jikin tane batai wata-wata ba ta fice daga jami'ar duk wani karatunta na ranar haka ta rasa shi!






38 *'YAR JAMI'A*
_BY_*HERWWERH JIDDERH*
*A.K.A*
*PRINCESS QUE~DEE*



💕




_Luv is so sweet when u meet the right person to show it out yeeeee! Oh yeeee!_

Wak'ar da beauty ke rerawa hankali kwance kenan cikin mota,hannu ta kai ga jakarta ta zaro wani k'aramin dairy nata,wani shafi mai cike da Manyan rubuta ta bud'e nan da nan ta kai hannunta ga wata da'ira da akai a wani k'aramin akwati da aka zana tayi tick aciki!alamun yiyuwa na cimma wani abu!bayan da ta gama ne ta kalli agogon hannunta taga har lokacin 12:00p.m ba tayi ba!Tsaki ta saki had'i da kunna motar tata, ta sureta da gudu kamar mai shirin tashi sama tai hanyar fita daga jami'ar!anan ne ta gamu da wani malami wanda ya d'auke su a zangon karatunsu na farko,wanda shima ba laifi d'an harka ne don ko ba komai ya bata marking da ta gamsu dashi"hakan yasa ya haska mata fitila itama ta haska masa na alamun dakatawa"waje ya samu gefe yayi parking itama ta samu tayi sannan ta fito tayo wajensa"da yake motar tasa itama bak'in gilashi ne haka ya bud'e mata motar ta shige ciki ta zauna!gaisawa sukayi tare da maida bayan saduwa"sun d'au lokaci mai tsawo suna hira abinsa kai kace don ita ya shigo"daga bisani ta nemi tafiya amma sam yak'i bari ta tafi,sai ma shiga bata wasu labaran yayi masu matuk'ar tasiri a zuk'ata"
kwan! kwan! kwan!k'arar bugun gilas kenan suka ji daga b'angarensa,ba tare da nuna alamar damuwa ba"ya kalle ta ya sakar mata wani kasalallen murmushi itama ta watso masa sannan ya iya sauke gilas d'in motar k'asa".
Baki bud'e har kana iya hakaito hasken fararen hak'oransa ya ji ance c'mon! malam bani laptop d'ina da aikin da zanyi da ita ka barni ina jira ka taho nan wajen......kalaman sameer kenan wanda bai kai ga k'arashe su ba idanunsa suka sauka ga macen dake gefen kujera zaune,wanda itama dai daga b'angaren nata shi take kallo"dimmm lokaci guda suka ji wani irin matsananciyar bugawar zuciya"kasa danne yanayin da yake ciki sameer yayi dole ya katse maganarsa ta farko ya fito da yatsa waje ya shiga nuna beauty yana fad'in"me wannan yarinyar take maka a mota kamal?d'auke da wata siririyar dariya saman fuskarsa malamin wanda aka kira da kamal ya kai duba a karo na biyu ga beauty kafin ya juyi gareshi yace wai wannan?ehhh ita!!sameer ya bashi amsa a tak'aice"ko da yake ka gane ba na buk'atar ma na sani don nasan abinda ya kori shaho daga shek'a bazai wuce yunwa ba!bani laptop d'ina na wuce"cikin fushi kake jin zafafan kalaman sameer na tashi!da yake yasan halin mutumin nasa kamal don ko suna office wani lokacin in ya d'au zafi ba mai iya masa sai in don kansa ya saki!haka ya mik'a hannu kujerar baya na motar ya janyo jakar laptop d'in ba uhmm balle um'um ya mik'a masa"karb'a sameer yayi duk da haka cikin fushi ya sunkuyo da kai cikin glass d'in yana kallonta yace wallahi i hate u to the extend level baki da hali,baki da hali banza mara kamun kai"!bai jira cewar su ba ya sa kai yayi gaba"

kamar a mafarki haka beauty ke jin kalaman sameer na dokar kunnuwanta"duk wasu k'ofofin tunaninta sun riga sun kulle ruf,k'afe ido tai ga sararin wajen da sameer ya bari tamkar mai wani nazari,can kuma sai ji tai ta saki wani irin k'aramin yak'e wanda ya fi kuka ciwo,bata jira jin wani abu daga bakin kamal ba, ta bud'e k'ofar tana shirin fita,cikin sauri kamal ya rik'o hannunta yana fad'in please dear wait ki ji wani abu"cikin zafin nama beauty tai wurgi da hannunsa gefe ta fito da sauri daga motar ta nufo tata"a fusace haka ta fad'a cikin motar kamar wacce hankali yabar jikinta haka ta finciki motar tayi waje!






39 *'YAR JAMI'A*

_BY_*HERWWERH JIDDERH*
*A.K.A*
*PRINCESS QUE~DEE*



💕

Zaune yake cikin office d'insu da alama aiki yayi masa yawa yadda ya duk'ufa sosai akan laptop d'insa dake ajiye saman tebur d'in gabansa yaji an turo k'ofa,sam bai damu da sannin wanda ya shigo ba don kuwa su uku ke zaman office d'in,sallama yayi kamal yayi sannan ya shigo ciki,kujerar dake kallon ta sameer ya zauna yana d'an gyad'a k'afa,alamun daya gani daga sameer na bashi da niyyar kulasa ne yasa shi k'ara gyara zamansa yace"amma dai kaji shigowa ta ko?eh kuma na amsa maka sallama ba!sameer yayi maganar kansa na sunkuye a laptop!murmushin k'arfin hali kamal ya saki sannan yaci gaba da maganarsa"wai shin kuwa sameer ina kasan 'yar jami'a naga tun da ka ganta d'azu tare da ni duk ka sauya gashi kamar ni d'in ma fushi kake dani!
Banza sameer yayi da shi tamkar bai ji me ya ce ba har na kusan minti uku sannan ya d'ago raunanan idanunsa da tuni sun gama k'ank'ancewa saboda gajiyar aiki ya sauke su saman nashi"malam aiki fa nake ka zo zaka dameni,ina ruwa na da kai da ita,tunda kai ma ka zama mai biye ma shashashan mata ai se kaje kai tayi,kar fa ka manta tare muka zo aikin bautar k'asa jami'ar nan kuma ni baka ga ina biye musu ba toh ni ma kenan dana tashi cikin hausawa,nasan illar abin ina ga kai daka tashi a birnin kudu,ya ci ace yanzu kasan me kake,basai an gaya maka ba,amma fa shawara ce bazan hanaka jin dad'inka ba sai dai ka sani yarinyar dana ganka d'azu da ita tun ran da na fara zuwa jami'ar nan na fara had'uwa da ita duk da bata gane ni a lokacin ba amma ni na ganeta saboda mummunar shigar dake sanye jikinta"don haka ina shawartarka please kaje kai dukkan abinda kake so amma ka rabu da wannan yarinyar wallahi bata da tarbiyya!cikin wani irin mawuyacin hali da yanayi sameer ke magana,kana ganinshi zaka fahimci tabbas duk kan abinda yake magana akanshi ba mai dad'i bane!
Ba don kamal ya ji maganar abokin nasa ba amma ya zai yi dole ya nuna masa ya gane komai kuma zai gyara da haka suka rabu kamal ya koma tebur d'insa ya fara aiki shima sameer ya d'ora daga inda ya tsaya!
****
Misalin k'arfe hud'u na yamma 4:00p.m, kenan a agogon dake sak'ale a hannun sameer"ajiyar zuciya ya saki lura da yadda lokaci ya tafi haka"kafin daga bisani ya had'a kayansa ya fito,a harabar office d'in nasu yaga an had'a jam'i ana k'ok'ari tada sallah haka ya aje kayansa gefe yabi jam'i sannan ya shigo motarsa ya fito daga jami'ar!
Tafiya yake hankali kwance har ya kai ga kwanar da zata sada shi zuwa gidan aminin nasa ameenu kamar yadda ya saba wuce wa can kullum sai kuma dare ya koma gida"maganar ummah ce ta fad'o masa na cewa bayan ya tashi daga aiki zasuyi magana"dole ya juyar da kan motar tasa sanin cewa in bai je lokacin ba dare zai zamanto dare yayi nisa watak'il ma tayi bacci a sa'ilin,haka ya d'auki hanya sai gida!
Horn biyu yayi baba mai gadi ya fito don ganin wane ne da mamaki sai yaga motar sameer!har ya bud'e masa gate suka gaisa ya shigo gaba d'aya baba mai gadi mamaki bai sake shi ba!tunani ya shiga yi Allah yasa dai lafiya ya dawo yau da wuri!ko da sameer yayi parking haka ya fito ya k'ara gyara zaman darkblue suit dake sanye jikinsa"sannan ya zura phones nashi a aljihu ya nufi hanyar shiga babban falo!

Assalamu alaikum!Assalamu alaikum! Sallamar da sameer yake yi kenan amma da alama babu motsin kowa a falon"ganin ya d'au lokaci tsaye ya sashi yanke shawarar ya wuce d'akinsa kawai zuwa an jima sai ya dawo"ya yunk'ura kenan zai juya yaji an bud'e k'ofar!dawo da kallonsa yayi wajen,inda hakan yayi dai-dai ga kallon ummah gareshi tace"aufff ashe kai ne? Eh ummah! Ina yini!cike da girmamawa sameer ke gaisheta!haka ummah ta amsa masa da lafiya lau!sannan tayi masa iso da ya k'ara so ciki! Cikin nutsuwa sameer ke bin bayan ummah har suka k'arasa cikin falon, kujera tai masa nuni da ya zauna!
K'ara gaisawa sukai kafin ummah ta umarci akawo masa abin tab'a wa baki!
Duk da ba wani iya cin komai yayi ba don sameer bai saba da cin abinci gaban mutane ba"in ba dole ba, musamman ma yau da ya kasance gaban ummah!haka ya aje juice cup d'in dake rik'e a hannunsa a centre table"ya d'ago kai yana kallonta da alamar son jin wani abu daga gareta"matsakaicin murmushi ummah ta saki sannan tayi gyaran murya tace!
D'azu nace in ka dawo kazo ina nemanka"saboda a ganina yaci ace kawo yanzu nasan da wane irin mutumi muke zaune a cikin gidan nan!jinjina kai sameer yayi da nuna gamsuwa da furucin ummah!sunkuyar da kai k'asa yayi sannan ya fara motsa leb'ensa!




[10:15am, 16/01/2017] Àúńţý jîđđĕřh: *'YAR JAMI'A*

_BY_*HERWWERH JIDDERH*
*A.K.A*
*PRINCESS QUE~DEE*

40-45



💕In Devotion to yuh my Dearies:


*ANEESA ABUBAKAR RIMI*
*(NEESAHLURV)*

&

*UMMEE ADNAN*
*(TAWAN)*



Ni dai sunana.......pinn pinn...k'arar wayar ummah kenan da ta fara ruri a lakacin wanda hakan ya ba sameer damar tsayawa don ta amsa wayar!hannu takai ummah ga wayar dake aje gefenta ta janyota!ta duba sunan wacce ta kira"yagana kuma?ba d'azu muka gama waya ba?ganin kiran yana daf da katsewa yasa ta tayi saurin d'aga kiran ta kara a kunne!k'ara gaisawa su kai amma duk yanayin da ta tsinceta tabbas a lamar tambaya!lafiya dai ko? Jimmm yagana tayi na wasu 'yan lokaci sannan ta nisa tace jikin malam ne ya k'ara tashi yanzu gashi babu wani babba a gida sai ni kad'ai!innalillahi wa innah ilaihirraji'un"toh yanzu yana ina?ummah tayi tambayar,gashi nan a gida na jik'a masa saiwa yasha ya d'an samu bacci!sosai jikin ummah yayi sanyi da jin rashin lafiyar mahaifinta,cikin k'arfin hali tace mata yanzu gashi baya gari kuma waya dashi sai dai cikin dare don aiki yawa yake musu,amma zan gani zuwa anjima duk yanda na yanke zan kira!toh yagana ta amsa dashi kafin nan sukayi sallama t ma kashe wayar!
A sulale wayar tabi jikin ummah ta sauka kan cinyarta inda tuni ruwan hawaye ya gama cika idon ummah"damuwa tsagwaronta kake gani d'auke saman fuskarta"yanayin da ta shiga yasa sameer bin ta da kallo a hankali ya iya furta,lafiya dai ko ummah?sam hankalin ummah ya gushe a kanshi har sai da ya k'ara nanatawa,sannan ta juyo guntun hawayen dake mak'ale a fuskarta suka gangaro,a rud'e sameer ke fad'in"subhanallahi dan Allah ummah menene ke faruwa?naga daga d'aukar wayarki haka ta faru ko dai anyi rashi ne,girgiza kanta ummah tayi sannan ta share hawayen nata ta d'ago kai a dak'uke tana kallonsa,can kum tace ba'ai rashi ko d'aya ba sameer k'anwar mahaifiyata ce ta kirani akan rashin lafiyar mahaifina;yanzu haka yana can kwance jikin ya k'ara tashi kuma ba kowa a wajensa sai ita sa yake mahaifiyata ta rasu,kuma dangin namu mazan ba masu d'aukar zumunci da wani abu bane,shiyasa kaga duk na damu,in dama ace daddyn hajara na nan da da sauk'i zan iya tambayarsa gobe na shirya naje,toh baya nan ita kuma waccen shashashar yaushe zan tura ta jinya,ita da ko hankali bata cika ba,!dafe kanta unmah tayi don wani irin sarawa da taji yayi kamar zai bar jikinta hakan yasa sameer saurin fad'in ya isa haka ummah ki daina damuwa kar kema wani abun ya sameki,yanzu shi yana ina da zama?yana nan kano cikin local government d'in minjibir!minjibir?sameer ya nanata sunan wajen,a gaskiya ummah bansan wajen ba amma in bazaki damu ba ni ki wakiltani indai kinga ba wani abu sai naje ni!da sauri ummah ta d'ago kai tana kallonsa!ajiyar zuciya ya sauke yace eh ummah ni zanje in har kin amince min sai ai mun kwatance!toh sameer Kar na takura maka aikin naka fa?haba umma karki damu da wannan zan sanar kuma ko bana nan akwai masu tallafa min don haka ki kwantar da hankalinki,toh shike nan hakan yayi na gode amma kaga da waccen malalaciyar zata iya ai da kun tafi tare tunda ta san wajen ba sai ka wahala ba!yamutsa fuska sameer ya d'an yi jin an ambaci mace yace wace kuma ummah?hajara mana,kai dai Kawai Allah ya sawak'e ma wannan yarinya wallahi ban tab'a ganin mace sakara irin taba duk ubanta ya gama d'aure mata sai yadda take so ina duniya zatayi dad'i a haka?cikin fad'a-fad'a ummah ke maganar!wani dogon gauron numfashi sameer ya sauke lura da yadda ummah ke zayyana halayem yarinyar sak irin na salaha k'anwarsa,toh amma ya akai duk da jarunta da nake ganin yanzu tattare da ummah ta kasa gyara 'yarta?toh yanzu mene abunyi?ko dai na tallafa wa ummah ne tunda ga dama ta samu daddy baya nan?
Sameer lafiya dai ko naji kayi shiru haka?jin ya lula wata sabuwar duniyar yana tunani yasa ummah tamabayarsa!cikin jin kunya irin nasu na maza nan ya shiga susa k'eya kamar mara gaskiya sannan yace babu komai ummah amma in babu damuwa sai mu tafi tare da ita kawai yadda nima bazan wahala ba,kuma kinga itama ai taga jikin nasa!sosai hakan yayi wa ummah dad'i nan da nan ta amsa masa da ai kuwa hakan za'ai bara ta tashi daga bacci sai na sanar mata zuwa safe sai d'au hanya"kai Allah dai yayi maka Albarka ashe kai rahama ce a gareni amma k'ememe daddy Ya hanaka shigowa ciki,ai daga yau ka zama d'an gida kuma ana tashi daga aiki ka yo gida nan ne mahallin cinka da shanka,ni na tsaya maka naga kuma wanda zai canja hakan!dariya sameer ya saki na jin dad'in kalaman ummah nan yayi mata godiya da hakan ya kuma nemi izinin wucewa sashensa,ba musu ta yarje masa har da kiran ma'aikata da'a mik'a masa abinci sashensa!
[10:15am, 16/01/2017] Àúńţý jîđđĕřh: *'YAR JAMI'A*

_BY_*HERWWERH JIDDERH*
*A.K.A*
*PRINCESS QUE~DEE*

46-50



💕In Devotion to yuh my Dearies:


*ANEESA ABUBAKAR RIMI*
*(NEESAHLURV)*

&

*UMMEE ADNAN*
*(TAWAN)*





Misalin k'arfe 9:00p.m kenan a agogon bangon dake mak'ale saman d'akin ummah kallo ta kai gareshi sannan ta nisa,juyowa tai gefe ta ga hankali kwance beauty na rik'e da waya sai latse-latse take yi?me kike yi da wayar??ummah ta tambayeta,cak beauty ta tsaya da charting d'in da take ta d'ago kai a hankali tace ummah gaisawa muke da daddy!daddy kuma?me kike ce masa?shiru beauty tai ba emm ba em em,toh ki ce masa ya kirani zami magana,toh ummah sannan beauty ta samu damar ci gaba da latsa yawar ta sanar masa,daga haka ta kashe datan nata ta sauka akai gaba d'aya,gefen kujera ta maida wayan ta aje don tasan halin ummah yanzu k'iris take jira ta kwace ta,ba'a d'auki wani tsawon lokaci ba sai ga kiran daddy ya shigo wayar beauty,hannu ta kai ta d'akko wayar ta ga sunan daddy a jikin wayar,juyawa tai ta kalli ummah tace daddy ne ya kira!wani dumm ummah taji kanta yayi mata yanzu kenan bazai kirata a wayar ta ba sai dai ta 'yar ta!haka ta danne damuwarta ta sa hannu ta karb'i wayar!gaisawa sukai kafin nan suka shiga hira ainun suna k'ara nuna wa juna tsantsar kulawa da rashin juna da sukai!acikin hirar ne beauty dake can gefe zaune taji ummah na sanar da dady zancen tafiya har tana ce masa beauty ta rok'i bak'on gidan nan ya kaita ta dubo jikinsa,da mamaki beauty tabi ummah da kallo har ta kammala wayar,ba abin tai magana ba sai kallo da ido,ke lafiya kika kafe ni da ido haka?cewar momy"nasan dai kin ji me nake cewa sarai toh dan haka ki shirya gobe da sassafe zaku tafi minjibir!minjibir kuma ummah?eh minjibir kuma wallahi naji kin kira dady kin gaya masa wani abu ni dake ne,don haka sai kije ki fara shiri tun yanzu don bansan kwana nawa zai ce kuyi ba!ba shiri beauty ta mik'e tsaye ta amso wayarta a hannun ummah ta fice a d'akin!
Da gudu beauty ta fad'a d'akinta kuka sosai ta shiga yi ba ji ba gani sai wani shure-shure take da hannu ita ala dole an b'ata mata"teddyn ta dake ajiye tsakiyar gado ta d'auka tai cilli dashi saman mirrow duk wasu kayan kwalba suka zube k'asa,tun tana kukan da sauti har ta gaji ta fara tsagaitawa dan kanta"kalaman ummah ke ta faman mata yawo akai toh yanzu haka kawai zata bi wani bak'o k'auye bata ma san waye bane,don kawai an ga daddy baya nan,har kusan sha d'aya na dare beauty na kwance sai faman mirgine-mirgine take saman gado"
Can wata dabara ta fad'o mata"tabbas zan had'a kayana da zarar mun fara tafiya sai na nemi na bashi kud'i kawai ya sauke ni a wani hotel d'in in yaje ya dawo sai ya biyo ya d'auke ni mu tafi!!yes yes beauty ta mik'e tsaye tana murna ta nufi drawer d'inta,duk wani abunda zata buk'ata sai da ta kammala su a jerin akwati biyu don ko ta batun karatunta bata yi sanin dama can baya gabanta!


Kiran sallar asuba na farko beauty ta tashi"ita da sallah sai gari ya waye take yi,wanka ta d'auro kafin nan ta fito ta shirya tsaf ta nemi hijab tai sallah"tana zaune kan dadduma kamar daga sama ta ji ta fara tariyo abinda ya faru jiya a stop and chop,yanda matan nan su kai mata tayin shiga k'ungiyarsu,tunani sosai tayi har dai daga k'arshe ta yanke shawarar in har ta samu zuwa hotel an jima zata kirasu ta shaida musu amincewar ta akan buk'atarsu!
Duk yadda tayi saurin lokaci yayi ummah ta kirata sai gani take lokacin baya ja,sauka k'asa tayi ta nemi breakfast tayi amma har yi war haka 7:00a.m batai ba, tsuka ta saki ta k'ara haye wa sama"tana zaune saman stool tana k'ara gyara kwalliyar fuskarta taji turowar k'ofa,ummah ce ta shigo dan haka cikin ladabi ta gaisheta!shigar jikinta ummah ta k'are ma kallo"doguwar riga ce light pink sai yalolan gyalan rigar data nad'e kanta dashi"jinjina kai ummah tayi sannan tace tun d'azu fa ya fito yana mota ke yake jira"jin haka yasa beauty cikin sauri ta aje lip stick d'in dake hannunta kamar ba ita jiya ke b'ata rai ba,ta shiga jan akwatinta,don yanzu ummah ta hana kowa yi mata aiki a gidan in banda wanki da guga,ummah ce ta taya ta da d'ayan akwatin har bakin mota inda ya ajiyeta saitin fitowa daga falo,bud'e taga booth d'in don haka suka zura akwatunan ciki,jiyowa tai su kai sallama da ummah sannan ta nufi k'ofar gaba na motar ta bud'e,da yake motar dimm take da duhu ko ina bak'i ne in banda side mirrow na waje baya ganin na ciki,shiko sameer rik'e yake da waya yana fama zuma revenge game da yake mayan game ne kawai yaji wani k'amshin turare ya doki hancinsa daga bud'e k'ofar!!!
[10:15am, 16/01/2017] Àúńţý jîđđĕřh: *'YAR JAMI'A*

_BY_*HERWWERH JIDDERH*
*A.K.A*
*PRINCESS QUE~DEE*

51-55



💕In Devotion to yuh my Dearies:


*ANEESA ABUBAKAR RIMI*
*(NEESAHLURV)*

&

*UMMEE ADNAN*
*(TAWAN)*


A hankali sameer ya d'ago dara-daran idanunsa ya sauke su akan k'ofar motar har lokacin beauty na tsaye tana k'ok'arin gyara doguwar rigarta don ta zauna,zanen rigar ya k'ura ma ido yadda yake ta shek'i na tamabarin tauraro(star) sosai ya shagala da kallon zanen kamar daga sama yaji k'arar demmmmm...Alamun an masa game over kenan, saurin sauke kansa yayi a phone d'in inda hakan yayi dai-dai da shigowar beauty had'e da tsayuwar ummah a bakin k'ofar tana fad'in toh sameer Allah ya tsare hanya,da saurinsa ya d'ago kai sama don baiwa ummah amsa!dass yaga idon mace kafe saman nasa wanda tun kiran sunansa da ummah tayi hakan yasa ta waigowa taga wannan waye abokin tafiyar tata,what??abinda sameer ya iya fad'a kenan yana nuna ta da yatsa, beauty da tai saroro kamar wata dutse tana kallonsa,can kuma cikin razani lokaci guda ta turo k'ofar motar har tana bige ummah da marfin motar haka tayo waje sai faman haki take kamar wacce tai tseren gudu!ido waje take kallon ummah da take tsaye tana luliye inda ta bug'e tace ke lafiya haka?bata iya cewa komai ba beauty sai nuni da ta ma shiga yi da motar!ganin ta kasa cewa ko uffan yasa ummah sunkuyar da kai cikin motar don ganin ko wani abu ya faru ciki!zaune ummah taga sameer ya dafe kai da hannu!cikin rashin fahimta ummah ta k'ara nanata maganar ga sameer shima dai yayi shiru!k'ok'arin komawa ciki beauty tayi,ai kuwa cikin sauri ummah ta rik'o hannunta!ina zaki?tambayar da ummah ta jefo ta dashi kenan?cikin dak'ilewar murya beauty ta amsa ta da ciki zan koma ummah wallahi na fasa tafiyar nan ya fito min da kaya na kawai!ciki kuma?akan wane dalili?kafin beauty ta iya bata amsa suka ji bud'e k'ofar sameer daga d'aya b'angaren yana fad'in emmm ummah dama ba komai kawai tayi mamaki ne jiya na d'an daki motar ta ban sani ba har ta kasa hak'uri ta fito tanai min fad'a,sai kuma gashi yau Allah ya had'amu amma babu komai,cikin k'ik'ina da sark'ewar murya sameer ke maganar!kana ganinshi kaga wanda ke b'oye da wani abu a rai,k'ara yunk'urowa beauty tai zatai magana nan ma ya k'ara tare ta da cewa,ina ga ummah in ta shirya kawai mu wuce don kar muyi latti ko?jin an ambaci latti yasa ummah saurin kallon beauty tace kin de ji kunya wallahi ko ina se kin nuna halinkina rashin hak'uri yanzu gashi dara ta ci gida,sai ki wuce yanzu ku tafi ai,kasa ko da kwakwkwaran motsi beauty tayi,duk wasu jijiyoyin kanta sun gama tsayawa cak da aiki,tunani fal sun gama cika kwanyar kanta,toh yanzu dama wannan shine bak'on dady?wanda ya gama tozartani a bainar jama'a?anya kuwa burin dana cimma yau zai iya bari na cika shi?toh yanzu ya ma za'ai na iya binshi mu tafi daga ni sai shi?bata dawo daga duniyar tunanin data shiga ba kamar daga sama taji wuf an finciki hannunta da k'arfin tsiya an wullata cikin mota,an maida k'ofa an kulle da key,a razane beauty ta hau jijjiga k'ofar da k'arfi ita ala dole sai ta bud'e,tana kallo haka cikin sauri sukai sallama da ummah ya shigo motar,bai bi ta kanta ba ya hau kunna motar,batai wata-wata ba ta jiyo kamar wata zararra ta rik'o hannunsa da yake kan key tace wallahi ka bud'e min motar nan,kar ka kuskura ka fita a gidan nan ba tare da ka sauke ni ba na dai gaya maka,sauke idanunsa sameer yayi a karo na farko a hannunsa yaga hannun beauty saman nasa,wani irin kukan kura yayi kamar wani mayunwacin zaki yayi wurgi da hannunta gefe,yanda taga jikinsa na wani kyarma tamkar mayak'in soja yasa ta shiga taitayinta ta fara rok'onsa Allah,da annabinsa ya sauketa,da yake motar duhu gareta sai ya zamana ummah duk wannan dramar tasu ba wadda ta gani haka ya tada mota hankali kwance ya fice daga gidan yana gyad'a kai!
[10:15am, 16/01/2017] Àúńţý jîđđĕřh: *'YAR JAMI'A*

_BY_*HERWWERH JIDDERH*
*A.K.A*
*PRINCESS QUE~DEE*

56-60



💕In Devotion to yuh my Dearies:


*ANEESA ABUBAKAR RIMI*
*(NEESAHLURV)*

&

*UMMEE ADNAN*
*(TAWAN)*


Wallahi ka sauke ni, zan maka ihu, Allah zan juyar da kan motar nan kowa ya mutu,wai ba da kai nake magana ba

Please Login or Register in order to submit comment