Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kud'i masu yawa haka ba"wani wawan hugging ta kaima daddy cike da jin daddy tana fad'in thank yuh my amaxing dady yanxu kam xance maka safe journey"
Dariya sosai suke abinsu nan dai su kai sallama dady ya fito ya nufo falo nan ma dai jan kunne sosai ya k'ara ma ummah kafin tarakashi har mota suyi sallama cikin alhini da nuna tsantsar missing ma juna da haka sukai bankwana"ali driver ya tada mota se government house"




📓27 *'YAR JAMI'A*📓📓
_BY_ *HERWWERH JIDDERH*
*A.K.A*
*PRINCESS'QUE~DEE*


Tsaye take bakin window tana lek'en dady har ya fice kafin ta maida wata nannauyar ajiyar zuciya ta maido dubanta ga d'akin"gefen gado ta taka a hankali ta zauna tare da kai hannunta ga ajiyar da dady yayi mata ta janyo su ta shiga k'irgasu"ta k'arashe lissafasu had'e da kwarma wani uban ihu na farin ciki can kuma tai saurin toshe bakinta da hannu tana sak'awa arai"_kai ashe fa dady baya nan nake sakin wannan shewar kar na jama kaina fad'a"a fili kuwa ta furta N200,000 cab lallai yau akwai shiga mall bara na kira xee-xee"nan ta mik'a hannu a haka ta xaro waya ta shiga lalubar number xee-xee"k'ara biyu wayan ta saki kafin daga bisani xee-xee ta amsa wayan da fad'in kina wuta tawan"murmushi beauty ta fara saki sai kuma ta amsata itqma da kema haka k'awas yanxu de ba lokacin hira bane ki shirya bayan sallar la'asqr xanxo har gida na d'aukeki muje shopping dan haka se ki min text na address d'in gidanku" jimm xee-xee ta fara yi a farko dan sarai ta san halin gidansu da yadda mahaifinta yake gashi da xarar anyi sallar la'asar yake dawowa gida,in yazo yaga beauty a gidansu me xe ce don tana da tabbacin da irin shigar da beauty xata xo gidan nasu"toh amma ai mama na nan kuma nasan bazata hanani zuwa ba don haka ba damuwa"nan ta amsa wa beauty da toh se na ganki"sun d'an tab'a hira ba wani sosai ba da haka sukai sallama"



_Yammacin ranar:_
4:15p.m

Tsaye take bakin k'ofar d'aki rik'e da jakar hannu,jikinta kuwa ta zumbula wani dogon hijabi har k'asa"taji sallamar mama d'aki"wai har yanxu k'awar taki bata xo bane zainab?eh mama amma na kira ta tace min ta kusa tana hanya"toh gara dai kuyi sauri dan kina ganin lokaci yanxu gyaji sallamar mahaifinki" ya mutse fuska xee-xee tai tace wallahi mama nima abinda nake ta ji ma tsoro kenan nasan yanxu yana xuwa fitar nan ta fasu"kuma ze iya wulak'anta min k'awa ko ya koreta"saurin katseta mama tayi da inah yaushe xan bari haka ta faru ya korar miki k'awa ba ita ce wacce kike ban labari 'yar babban mutum nan ba?eh mama ita ce"toh kinga ko in zaki huld'a da 'ya'yan masu hannu da shuni a hankali mijin aurenki ma ta nan tsatson xe fito ke dai kawai ki bar min komi a hannuna bari naje na k'arasa wasu ayyuka a can d'aki na" toh xee-xee ta amsa da tai waje"
Zagayen d'aki kawai take tana duban agogo kamar daga sama taji k'arar horn na mota ai cikin sauri-sauri gudu-gudu ta fito a d'akin ta nufi wajen mama ta shaida mata ta k'araso"nan mama ta nuna mata tai sauri toh su wuce dai kafin baban nata ya dawo" da saurinta ta fito inda ta iske motar beauty kafe bakin gate d'in gidan nasu nan ta nufota"

Zaune take beauty cikin mota cikin wasu arnan kaya riga da skirt sai wata k'aramar hula data sak'ale kanta dashi"idannunta kafe a gidansu xee-xee nan ta shiga xancen xuci'gaskia ba laifi gidan yayi duk da dai unguwar lunguna sunyi mata yawa ga hayaniyar jama'a amma ade xaman gidan k'aramun ma'aikacin kwamnati ba laifi yayi k'ok'ari"tana cikin tunani taji an bud'e mota an shigo se a lokacin hankalinta ya dawo jikinta ta maida dubanta ga k'ofan"me zata gani?xee-xee murk'ushe cikin k'aton hijabi har k'asa" ai beauty bata san lokacin da dariya ta kwace mata ba ta nuna ta da yatsa tana fad'in me xan gani haka xee-xee kode kema kin koma matar malam ne?"cikin wasa xee-xee ta watso mata harara tana ci gaba da k'ok'arin yaye hijabin jikinta da yake motar me duhu ce tana fad'in banda lokacin ki ni dai yanxu yi sauri mu fita a layin nan koma meye kya tsokane ni dashi"batabar dariyar ba dai haka ta kunna motar tahau tuk'i'dai-dai kwanar hawa babban titi suka ci karo da baba cikin motarsa honda 307 yana k'okarin karyo kwana"
Na shiga uku"xee'xee ta fad'a tana b'oye kanta k'asa"me ya faru ne?ko kin manta na waje baya ganin na ciki?beauty ke tambayarta"se alokacin ma xee-xee ta tuna da hakan nan dai ta d'ago kai ala dole ta sha mur don kar beauty ta tsokaneta"tace ai na sani kawai de tsohon nan ne se a slow yanxu haka se kiji yace jikinsa ya basa ina cikin motar nan"na rasa me yasa sam ya kasa yarda dani"kome nawa se yasamin ido,ko shi haka akai masa da yana saurayi oho?itade dariya kawai beauty take har sukai nisa da unguwar sannan ta iya cewa dama dady ya auri mamanki se umma mu had'ata da baba suje suyi ta wa'axinsu mu kuma muna jin dad'in rayuwarmu koya kikace k'awas?dariya itama xee-xee ta saka tace ehh wallahi da mun huta da b'acin ransu duka"se de nasan baba ko ana muzuru ana shaho baxe saki mama ba kamar wanda akai wa asirin natau da ita"ke nima fa haka umma ke nanik'ewa dady na ko de su ustaxannan shigewa mutum suke? Xee-xee ta amsata da oho musu su suka san kayansu"har suka cimma shopping mall d'in nan hirar nan dai d'aya ita suke!







📓📓28 *'YAR JAMI'A*📓📓
_BY_ *HERWWERH JIDDERH*
*A.K.A*
*PRINCESS'QUE~DEE*





Katafaren kantin country mall dai-dai nan beauty ta tsayar da motarta tare da fitowa,haka xee-xee ta biyo bayanta,ciki suka shige abinsu nan suka shiga b'angaren kaya suka jidi kaya na axo a gani designers kala-kala don yawancin kayan komai kala d'aya suka d'auka abinda ya kama jaka da takalmi kai harda jewelries abindai ba'a cewa komi ranar kud'i ya sha kayi"ma'aikatan wajen su kansu beauty bata barsu a baya ba se datai musu kyakykyawar sallama bayan sun kawo mata kaya har mota"basu suka isa gida ba sai gab da sallar magrib inda ta sauke xee-xee a k'ofar gida,nan ta janyo hijabinta cikin jaka ta xumbula tare da janyo ledar kayanta ta nai ma beauty godiya ta fita har ta cimma gate beauty ta manna mata horn ta juyo bak'ar leda ta hau nuna mata dake ajeyi a bayan mota,hakan yasata dawowa tana fad'in kinga na manta kayan da kika ce a baiwa mama ko"nan ta karb'a tana mai k'arai mata godiya ta wuce"hakanan yasa itama beauty ta tada mota ta nufi gida"
Kamar yadda ta saba haka yau ma ta shiga gida mota sautin kid'a se tashi yake haka tai parkin a wajen aje motoci tare da manna horn da gudu mai gadi ya taho rik'e da buta a hannu ya xube gefen marfin motar,booth tq bud'e masa ba magana ya nufi wajen dan yasan aikinsa,da haka ta fito ta nufi cikin gida"falon shiru ba alamar motsin kowa hakan ya tabbatar mata da umma da ma'aikatan gidan kowa na wajen sallah sashenta ta nufa itama"murd'a hannun k'ofarta yayi dai-dai da fitowar ummah daga sashenta rik'e da caxbi tana laxumi"daga ina kike?tambayar data fito daga bakin ummah kenan"cikin sauri beauty ta juyo dan har ta tsorata da jin murya bayanta"tuni ta saita nutsuwarta ganin ummah tace shopping naje nayi" shopping??shopping fa kikace awannan lokacin?in har da gaske kike ina kayan da kika siyo"kafin beauty ta iya cewa wani abu baba me gadi ya hawo sama nik'i-nik'i da kaya cike bisa hannu"sanin ummah cewa dady ya d'aure wa beauty bayan rashin aiki se dai ma'aikata suyo yasa bata tanka mata akan hakanba"gaisheta baba me gadi yayi inda beauty jiki sanyaye ta shige d'akinta yabi bayanta"gefe guda ya aje mata kayan ya fice"
Sallah ta fara yi duk da dai cikin sauri aka kaita ana ta d'okin bud'e kaya"tana sallamewa ko addu'a bata samu damar yi ba ta doshi kayan"a hankali ta hau fiddo kayan tana k'are musu kallo"hannu ta kai ga wata doguwar riga kalar sky blue da ratsin bak'i ajikinsa ta d'aga ta sama tana k'are mata kallo se kuma can ta nisa tace tabbas wannan rigar dake xa'ai harka gobe tunda inaga muna da statistic kamar yadda na gani a time table se de kuma long slip ce" ta nisa kamar me tunanin wani abu se kuma ta basar kawai taci gaba da duban kayanta"k'ara wayanta ya shiga yi nan ta mik'a hannu ta d'akko a jaka"xee-xee kuma toh lapiya?tambayar datai kenan sannan ta d'auka"
Beauty dama mama ce tace na kira mata ke a waya"cewar xee-xee"ok toh wani abu de ko?eh godiya dama xatai miki gata ma kusa bari na bata"nan mama ta karb'i waya suka gaisa da beauty godiya ta inda ta shiga ba ta nan take fita ba har ta kai ta ga fad'in ai kullum in kina son rakiya unguwa zainab tana da cikakken lokaci kixo kuje"itade beauty toh shine kad'ai amsarta har sukai sallama mama na ta shi mata albarka kafin xee-xee ta amshi wayar su ci gaba da hira"bayan ta kashe wayar ne ta shiga gyaran kayan ta jere su a wardrobe bayab ta fitarda complete kayanda xata saka gobe a shiga *jami'a* d'aukar lecture!









📓📓29 *'YAR JAMI'A*📓📓
_BY_ *HERWWERH JIDDERH*
*A.K.A*
*PRINCESS'QUE~DEE*

💕





Zaune take bisa stool gaban madubi se shafe-shafe take da alamar fara'a ainun d'auke sama fuskarta"ta d'au lokaci tana ta kwalliya kamar me shirin xuwa wani party ko dinner"bayan ta gama ne ta nufi wajen kayan data aje saman gado ta janyo su ta saka kamar yadda ta ware su daga irin kayan data siyo a fitar su da xee-xee jiya"da kokawa da nishi doguwar rigar nan ta shige jikinta"se faman haki take kamar wacce ta sha wani aiki"rigar tsaf ta amshi jikinta sosai duk wasu sak'o da loko na jikinta ya bayyana matuk'a gashi tai mata cif-cif kamar an aunata"haka ta zura d'an kunne,tare da jaka da takalmi harda k'ara min veil duk black tunda rigar sky blue ce"ko da beauty takai kallonta ga madubi wani irin ihun jin dad'i ta saki don ita kanta tasan yau kam abin ba'a cewa komai"gefen gado ta k'arasa ta bud'e k'aramar drawer dake wajen ta ciro wata jotter me sak'ale da biro ta xura a jaka"sannan ta matsa gefe wajen ma'ajiyar tirare nan ma tai ruwansa ajikinta"kafin ta zari key na mota ta fito kunne dod'e da earpiece se kad'a kai take na jin dad'in yadda kid'in ke tsima ta" a falo suka had'e da ummah cikin sauri ta tsaida kid'an tare da gaisheta a ladabce"da fara'arta ummah ta amsa mata kafin ta nuna mata dinning table dake cike da kayan bud'e baki"fahimtar abinda ummah ke nufi beauty tai ba musu ta nufi wajen nan sukai karin kumallo" bayan ta gama tai ma ummah sallama ta fito"

Ko da beauty ta shigo jami'ar office din malam umar ta fara wucewa sai dai ina lokacin bai k'araso ba da yake safiya ce sosai dan ko 8:00a.m batai ba"dole ta hak'ura bayan ta tura masa sak'on yanemeta in yaxo da haka ta nufi venue d'in su na ranar"ta jima cikin mota zaune tana ta kallace-kallacen jama'a mai shiga dame fita se sak'a zancen zuci take"cikin waigenta ne idonta ya kai ga captain d'insu tuni ta wangale gilashin motar ta shiga kiran sunansa"meenu!meenu!
Da farko ameenu bai lura da kiran da take masa ba sai da wani d'alibi da suke tafiya tare ya ce masa wai ameenu ba sunanka nake jin 'yar jami'a na kira ba da yake kowa yasan beauty yadda ya kamata" hakan ya sashi mik'a ma d'alibin takaddunsa akan ya wuce masa dasu ciki kafin shi ya k'ara so"wajen beauty ya k'arasa nan suka gaisa sai kuma ta nisa tace haba meenu ka shigo mota mi magana mana xakai tsaye a waje"da farko ya d'an yi shiru kamar baxe shiga ba sai kuma ya xagaya ya bude motar ya shiga"
A nutse meenu ya d'ago kai ya dubeta yace toh ina jin ki wani abu ne?ita abin ma dariya ya bata se yayi ta wani mata magana sauri-sauri aduk sanda suka had'u besan yaga suna jimawa a hira"itama kallon nasa tayi cike da murmushi tace ba wani abu bane illah aikin da kaimin watannin baya yau ma shi za kai min"wane aiki kuma?cewar ameenu"sunan malamin da zai d'aukemu statistic nake son ji" wata ajiyar zuciya ya sauke na jin dad'i da Allah yasa ba wani abun zata sakashi ba don shi sam be son abinda zai had'ashi da ita musamman yanxu da kowa yasan wace ita a jama'iar"
Saukar lumfashinsa yaxo dai-dai da bata amsa"ehh toh nima dai bansan shiba amma dai dana tambayi wani tsohon lecturer anan yace d'alibai dai na kiransa sir prince but tak'amai-mai sunansa se ya shigo lecture zai fad'a mana don haka yake yi kafin ya fara darasi"jin-jina kai beauty tayi kamar me wani naxari tana k'ara maimaita sunan a zuciyarta"sir prince"sir prince" ina kuwa na tab'a jin sunan nan a baya?ina ne kuwa?kai bazan iya tunawa ba"may be ma shima na harka ne ban sani ba"
Ganin yadda ta duk'ufa da tunani ne yasa meenu ya d'an buga kujeranta yace zan iya tafiya ko?firgigit ta jiyo tana fadin yes meenu zaka iya tafiya nima ai yanxu xan shigo ka samamin seat kusa da kai bara naje na siyo orbit chewing gum a caferia"toh kawai ya amsa ta ya fice a motan ita ko ta tada mota ta nufi caferia"
A wani k'aramin kanti ta siyo shi tana k'okarin kunna mota kenan ta bar wajen taji ance adawo lapiya?saurin juyawa tqi taga wanda ke mata magana"murmushi ta saki ganin sir Mutallab tsaye a gefen motan ta"wanda yake d'aya daga cikin malaman department d'insu kuma na hannun dama a wajenta dan kuwa lokaci-xuwa lokaci sukan had'u" dole ta fito suka tsaya nan fa hira ta b'arke tsakaninsu har beauty ta manta da wani abu wai shi lecture!

















📓📓30 *'YAR JAMI'A*📓📓
_BY_ *HERWWERH JIDDERH*
*A.K.A*
*PRINCESS'QUE~DEE*










Kimanin minti 30 beauty na tsaye da sir mutallab suna hira can ya nisa yace au kin ga kin sha'afantar da ni da dad'ad'an kalamanki ko? gashi kinsa nayi late a lecture da zan gabatar"sai a lokacin beauty ta tuna da ashe itama fa tana da lecture dole sukai sallama a gurguje ta hau mota ta nufi venue "wayam kake ganin wajen nan ba alamar mutane kowa ya shiga ciki hakan ya tabbatar mata da an fara lecture"motar xee-xee ta hango can gefe guda, haka ga kuma wasu motoci nan sunyi jeri a gefe d'aya"tsakiyar cikinsu inda yayi dai-dai da wata mota ash colour tasha wanki nan ta aje motan nata ta d'akko jakanta ta fito"
A bud'e ta samu k'ofan hakan yasa ta tura kai ciki ta shige"
Juye ta riske shi ya maida kai ga allo yana ta xuba uban rubuta d'alibai na kwafa"don haka bata jira wata-wata ba ta shiga taku cikin gadara ji kake kwas-kwas takalmi na k'ara"markern dake rik'e a hannunsa sir prince ya tsayar da rubutun tare da juyowa yana kallon ikon Allah"inda tuni hankalin beauty ita ko yayi nisa a neman meenu se can ta hangoshi saman theater ga wata mace a gefensa"sauri beauty ta shiga yi don taje tai mata masifa na ta zauna mata a waje"kamar daga sama taji ance"hey lady where are u going there?ba tamabayar ce ta bata mamaki ba sai dai muryar wanda ta ji"don tabbas ko a mafarki taji wannan voice d'in xata gane shi bare a fili"juyowa tai don k'ara gaskata abinda taji"kwatsam sukai ido hud'u da prince"kusan mutuwar tsaye tayi a gun shiko me zai yi prince in ba k'ara had'e fuska ba ya k'ara jefo mata wata tambayar"tell me about your wristwatch?banbara kwai taji tambayar aiko me xatai in ba k'udurta raina masa hankali ba nan ta gyara tsayuwarta sosai ta kai dubanta ga agogon dake sak'ale a hannunta ta shiga magana cikin izzah"wow my wristwatch ix unique and fashionable"as u guys normally call it one in town"& i'm quite sure small money inside a small pocket can't afford to handle it"tana kaiwa nan ta d'ago kai cike da murmushi saman fuskarta tana dubansa"me yarinyar nan take nufi ni talaka ne kome?wato ina tambayar ta lokaci shine zata juya min da haka aiko zata ga dixgi"xancen da prince ke nanata wa kenan arai"ganin yadda aji kowa ke jiran jin me xai ce ma ta"nan ya k'ara matse fuska tamau kamar be tab'a dariya ba sai kuma ya d'an saki murmushi na gefen fuska ya shiga kad'a marker dake dauke a hannunsa yana fad'in alright class let us solve a small work here before moving to our main topic of discussion"ido kowa ya bishi dashi ana kallon ikon Allah"a inda prince ya koma gefe da rubutun shi na farko yayi wani k'aramin arithmetic yace waze iya min solving"wani d'alibi a gaban seat ya d'aga hannu yace sir let me try"prince yace ok come and try"haka d'alibin ya taso ya karb'i markern a hannunsa ya shiga solving"bai d'auki wani lokaci sosai ba sai gashi ya gama ya fitar da amsa da yake d'alibin shi ke d'aukar overall a class din"yace sir na gama"duban board d'in prince yayi a nutse yaga tabbas abinda yake so ya gani yaron ya rubuta"nan yace ko zakai min bayanin yadda akai ka samo amsar"tiryan-tiryan d'alibin yayi bayani abin yayi matuk'ar burge prince nan ya kallo class yace alright class kun gane me yayi ko?class kowa ya d'auka da yes sir"in banda wata matashiya dake gefen dama gareshi wacce ta amsa da no sir"dama abinda yayi tsammani za'a samu me fad'a kenan dan yasamu yayi nasa bayanin nan kuwa ya kallo ta cike da samun karsashi a jiki yace ok lady let me repeat it clearly"gaban allo ya koma ya shiga nunawa yana bayani daya ke quadratic equation ne sai da ya gama bayani tsaf sai yace mata ko kinsan dalilin da yasa x=0 & y=10 nan ma dai ta kara bashi ansa da no sir sai yace toh bara nai miki example da hausa yadda xaki gane sauran aji ma su k'ara fahimta sosai dan nasan akwai wanda ko an bud'e brain d'insu an zuba karatu kan bazai d'auka ba"
📓📓31 *'YAR JAMI'A*📓📓
_BY_ *HERWWERH JIDDERH*
*A.K.A*
*PRINCESS'QUE~DEE*

💕









kallo ya k'ara kai wa sir prince ga sauran d'alibai dake zaune suna jiran cewarsa cikin sarrafaffiyar muryar nan tasa mai cike da kwarjini had'i da izzah haka ya fara magana" Hak'ik'a nin gaskiya ba ya cikin tsarin karatuna yin bayani da hausa don ya zama dole ne shiyasa yau zan mu ku,kun fahimce ni ko?sauran aji suka amsa da yes sir,sannan yaci gaba da magana"yana kai nuni da hannu izuwa ga allo"a duk lokacin da ku ka tashi lissafin irin wannan aiki toh ku d'auki x amatsayin mace mara kamun kai, ita kuma y amatsayin mace mai kamun kai"a yayin da x mara kamun kai ta gama zagayen ta na duniya zakuga ta tara kud'i masu d'umbin yawa (anan yayi nuni ga inda x ta samu maki100 a yanda calculation d'in ya nuna) ,har ta dunga jin cewa kamar ta fi kowa kud'i jama'ar gari kuma suyi ta bibiyarta don neman abun hannunta,har ta kai wata rana kwatsam sai a wayi gari wannan kud'in nata ya k'are a lokacin da zaton mutane bai kai ga haka ba"nan ya sauke hannunsa a inda rubutu ya nuna=0, ita kuma y mai kamun kai za kuga tana ta faman wahala a duniya( ya saita inda aka rubuta y=0) jama'a ko ta kanta basa bi don a tsammaninsu sam babu wata daraja a tattare da ita har sai an cimma gab'ar da zatai arziki alokacin ne jama'a zaka ji suna yabo gareta na k'iddige muku sai ta kai ta kawo wannan x d"in na bibiyar y don samun dacewar rayuwa"don haka jama'a wannan labari dai na san kun fahimce shi don nai muku shi dalla-dalla"bai kai ga rufe baki ba waje gaba d'aya ya d'auka da tafi ji kake raf-raf had'i da ihu kai har da shewa na jama'a,kowa na tofa albarkacin bakinsa akan wannan labari,beauty dake tsaye gaban desk k'afafunta sun kasa rik'eta ga wani matsanancin sarawa da take ji kan ta ya fara duk don wannan d'an iskan labarin da sir prince ya bayar ta san ba makawa labarin nan da ita yake"ganin tsayuwar baza tai mata ba ne yasa ta fara takawa a hankali tana dafe kai kamar wata 'yar giya ta nufo k'ofa dan barin theater d'in,tana takowa dai-dqi da inda yake tsaye nan ta d'ago fuska cikin zafin nama ta shiga k'ok'arin yin magana amma ta kasa sakamakon rad'ad'in da kanta ke mata"saurin duk'ar da kanta k'asa tayi sai ji tai kamar daga sama yana fad'in pls among u ladies someone should help her out kafin ta fad'i anan may be cough syrup ne ya fara mata aiki,ai ko kamar jira suke class suka d'orar da wani sabon ihun kafin kace me wajen ya karad'e da hayaniya,xee-xee da ke can saman theater cikin sauri tai k'arfin halin tasowa ta nufo wajenta nan ta rik'eta adaddafe har wajen mota, bud'e motar xee'xee tayi ta sanya ta ciki tana mai cewa zaki iya tuk'in ko kuwa?hannu beauty ta d'aga mata kawai da alamun ta bar ta haka ta koma ciki"ba dan taso ba haka xee'xee ta barta xuwa ciki don tasan halin beauty indai ta kafe a abu to abarta kawai"

Tunani sosai su kai ta ziyartar beauty ta sak'a wannan ta kunce wancan duniyar duk ta gama yi mata zafi,sam ta rasa me ke mata dad'i a duniyar nan ace wai yau har ita jama'a zasuyi ma ihu duk shaharar da tayi a haka zai k'are inaaa wallahi da sake hakan bazai tab'a faruwa da ni ba"duka takai wa sityarin motar tata da hannu kafin ta kunna motar cikin b'acin rai ta nufi gate ta bar makarantar!Bayan kimanin awa biyu da faruwar hakan ne sauran d'alibai suka fara tururuwar fitowa bayan da sir prince ya rufe karatunsa na ranar inda kowa ka ganshi labarin nan dai d'aya shi ake nanatawa na dizgin da akai wa 'yar jami'a da sanyin safiyar yau, shi ko prince wani dad'i ne ya lullub'e shi tun bayan fitar beauty daga theater d'in yasan ko ba komai yau burinsa ya fara cika akanta!









📓📓32 *'YAR JAMI'A*📓📓
_BY_ *HERWWERH JIDDERH*
*A.K.A*
*PRINCESS'QUE~DEE*

💕








Horn! Take ta faman yi amma ba taga alamar mutum a wajen ba"fitowa tai ta nufo gate d'in ta bude k'aramar k'ofar ta shige ciki tabar motar a nan waje,d'akin baba mai gadi ta nufa nan ta shiga yaye labulen k'ofar!me beauty zata gani? baba ne kwance saman tabarma sai faman gurnanin bacci yake abinsa daga gani kasan baccin nasa yayi nisa"dube-dube ta soma yi can ta hango buta a kusruwar d'akin,da saurinta ta k'ara sa wajen ta janyota,ruwa ne cike cikinta haka ta nufo baba"shaaaaaa kake ji ruwa na malala saman fuskarsa"firgigit baba mai gadi yayi ya mike zaune yana nanata kalmar shahada"cilli beauty tai da butar gefe sannan ta fice a d'akin tana gungunin cewa gobe ma ka sake baccin rana mu gani"bai iya cewa komai ba baba mai gadi illah cire kayan nasa ya sauya da wasu!
K'ofar falo ta murd'a a zuciye ta

Please Login or Register in order to submit comment