Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fara jin kunya gwara ya d’au
matarsa su k’ara gaba”. Tana fitowa dai-dai Aisha na
hawa matakala Hajiya ta ce”ah! Aisha har kun dawo”,
cikin jin kunya ta sun kuryar da kanta ta amsa da “eh
mun dawo”. Hajiya ta ce”to yayi kyau kije d’aki Hasna
zata kawo”. Miki abinci, Aisha ta ce”Hajiya a k’oshe nake
naci abinci a can” Hajiya ta ce” to shikenan”. Aisha ta
wuce d’akinta sai da tasha maganin Haiydar ya bata kafin
ta kwanta sai ido ta lumshe tana mai tuna abunda ya
faru tsakanin su da nan wani tunani ya fad’o mata yanzu
fa in da rabo hala ciki ya shigeki, murmushi tayi kafin ta
shafa cikinta haka har bacci ya d’auketa. Yau Aisha ta
kammala jarabarwata wanda aka shirya musu liyafa
nagani na fad’a Sarkin Fulani da shi da Lamid’o sun
halarci bikin walimar abun dai sai wanda ya gani walima
akayi na gani na fad’a, bayan walima da kwana biyu
Hajiya ta shirya ‘Yarta da kanta ta mayar ta gidan Haiydar
tare da mata nasihu masu sayaya jiki. Da dadare Haiydar
da wuri ya dawo Falmi ya samu a falo tayi d’aurin rashin
mutunci sai kad’a k’afa takeyi. Ganin ko kallonta bai yi ba
zai shiga d’akin sa tazo tasha gabansa ta ce”to muna fuki
wai mai kake nufi ne kasani lokaci yayi da zaka saki Indo,
ko ka manta kai da bakin ka kace baka sonta sai yanzu
kuna neman ku kareta wai tasamu ubanta mtss zaku
raina min Hankali ai ‘Yar shehe ‘Yar she……”. Wani
kyawawan mari Haiydar ya bata nan tafara shirin kama
sa da kokuwa shi kuma bai son yawan dukar mace kawai
ya jata zuwa d’akinta ya kulleta ta baya, d’akin sa yaje
yayi wanka kafin yasaka kayan bacci d’akin Aisha ya shiga
ya ganta cikin wasu mayun kayan bacci wanda dashi da
babu duk d’aya. *®NWA* *DEDICATED TO* *AISHA
MUHAMMAD* *(MAMAN ABDUL SHAKUR)* *RASH
KARDAM * [2:32PM, 9/14/2016] Rash Kardam:
[10:50PM, 7/21/2016] Rash Kardam : BABBAN
KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM.
*®NWA.* *Pg-229~230.* Da daddare haka suka sha
hiransu cike da k’aunan juna sai kusan goma Sarkin
Fulani ya musu sallama shima Lamid’o d’akinsa ya tafi da
ya kwanta yau jinsa yake cikin farin ciki, Hajiya ta kalli su
Aisha ta ce”kuma ku tashi ku tafi d’aki ku kwanta dare ya
soma yi”. Duka suka mik’e tare da mata sallama, Haiydar
ko ya marai-raice fuska Hajiya duk ta d’ago nufinsa ta
ce”kai kuma mai ka tsaya yi da bazaka tafi masaukinka
ba ne?”. Jiki ba kwari Haiydar ya mik’e ya nufi d’akin sa
shima tukun Hajiya ta tafi nata. Aisha tana shiga d’aki
wanka ta fad’a Hasna kuwa kitchen taje had’a ruwan zafi
take so tasha kafin ta kwanta, Haiydar ganin Hajiya ta tafi
d’akin ta ya dawo cikin sand’a ya tura d’akin su Aisha nan
ya ga ba kowa sai da ya rufe k’ofar tukun ya k’arasa ciki
k’aran ruwa yaji a bayi gefen gadon kusa da bayi ya
zauna don kar ma tana fitowa ta gansa, Hasna da take
shirin fitowa ganin Haiydar ya shiga d’akin su tayi
murmushi sai ta nufi dining kawai don ta sha ruwan
zafinta a can. Aisha da ‘yar wakanta fito d’aure da tawul
iya cinya sam bata lura da mutum ba dake ta na goge
kanta zagawa yayi ta bayanta ya rungumeta tare da zare
d’an k’aramin tawul d’in, cikin razana tayi tana shirin
sakin ihu ya toshe mata baki da hannusa a kunne ta ya
rad’a mata” nine mijiki Haiydar kuma d’an uwanki”,
dumm! Taji gabanta ya fad’i juyo da ita yayi duk kunya
ya ishe ta, hannu tasa tana kare k’irjinta, ya saki
murmushi ya ce”mai yasa kike rufe min abunda yake
halal a gareni kuma nake marari ganinsu tare da
begen…”. Magana kunya ta bata sai ta rufe ido hannuta
ya kama ya kawar daga k’irjinta tare da janta zuwa gado
cikin muryan kuka ta ce”Ya Haiydar miye haka? Dan
Allah ka bari mai kazo yi a nan?”. Murmushi yayi ya
ce”yau nazo karb’an hakkina da ya dad’e shekara da
shekaru ana min rowa kai ta gir-giza masa tare da
k’ok’arin turjewa sai da ya kaita kan gado ya kwantar da
ita, salon k’auna iri-da-kala yasoma nuna mata wanda ya
fi k’arfin in tsaya zayya ne mu ku acin nan. Hasna ko
ganin haka da man akwai d’aki wanda da komai a ciki
d’akin hajiya ta koma ta dauko kayan bacci, tazo tayi
wanka ta kwanta a nan. Haiydar ko sai da yayi wasa da
Aisha son ransa ya kuma tabbatar da ya gamsu kafin ya
mik’e cike da nishad’i ya fito cikin sand’a ya koma
d’akinsa wanka yayi ya kwanta yau yana mai jinsa cikin
farin ciki kasa bacci yayi can iya tuna mai ya faru sai ya
saki lallausar murmushi tare da buga hannusa a katifa
alamar jin dad’i. Aisha ma wanka ta sakeyi kafin tazo ta
kwanta tana mai tunano abunda ya faru haka har bacci
ya d’auketa. Da safe bayan sun karya sun dawo falo an
gaggaisa yau Aisha sai wani sunne kai takeyi Haiydar ko
idonsa akan ta yake suna had’a ido zai kashe mata ido
d’aya, Sarkin Fulani ne yayi gyan murya sai da yayi
addu’a kafin ya fara da cewa”hukuncin dana yanke shine
da zaran Aisha ta kammala jarabawan ta zamu tafi Yola a
kaita taga dangin Mahaifiyar ta sanna gonar Lamid’o
inaso zamu mayar dashi kamfanin yin su Madara da
yogurts san nan gefe d’aya kuma a mayar dashi gidan
gona gefe d’aya kuwa zamu k’awata shi ya dawo gun
tutawa zamu zuba k’ananun namun daji don su kawata
gun da d’akunan hutawa da gun abinci mai kyau, hakan
zai kawo kud’i kuma wasu manya zasuna zuwa gun
kasancewar yayi wajen gari kuma ba hayaniya a gun”. Ya
d’ago ya kallesu ya ce”kunaga hakan yayi ko da wani
tsarin da yafi hakan?”. Hajiya da Lamid’o suka amsa da
yayi nan ya ce”to na nasa an muku komai sabida
komawarku Bauchi don gobe Aisha tana da jarabawa”.
Daga nan kuma suka ci gaba da hiransu. Da yamma
kuwa sarkin Fulani har dashi da Lamid’o aka musu rakiya
zusa filin jirgi suka dawo Bauchi. Washe gari Aisha ta nufi
makaranta nan taba masu Sadeey da Sanah labari ba
k’aramin murna suka mata ba da samun Mahaifinta.
Haiydar ko yana komawa gida ya samu Falmi amma sai
me fiskanta yaga kamar alamun nadama da murna ta
tarbesa don ita damuwarta taji ina yaje sai da ya huta
cikin kissa take tambayarsa ko da yabata labari nan fa ta
dira tsalle ta mik’e ta ce”ina wannan k’arya ne kawai baki
kuka had’a don ku rufa mata asiri” nan fa rikici ya kaure
a tsakanin su daga k’arshe falon ya barmata ya koma
d’akinsa. Bayan kwana biyu duk damuwar sa ya ga Aisha
gashi yanzu saura mata jarabawa d’aya ta gama, zuwa
makarantar yayi yasamu suna jarabawa ya tsaya ya
jirata sai da suka fito yasa aka kirata tana zuwa ya ce”ki
shiga mota”, sam fiskan sa ba alamar dariya hakan yasa
ta shiga da sauri ya ja motar ya bar harabar makarantar
gudu yakeyi sosai hanyar UNGUWAN SARAKUNA ya
nufa, cikin razana Aisha ta ce”lafiya yanaga ba hanyan
gida ka nufa ba?”. Wani kallon da ya aika mata dashi yasa
tayi shiru har suka isa wani k’ofar madai-daicin gida mai
kyau horn yayi mai gadi ya bud’e masa yana shiga ya
ajiye motarsa ya zago ta gun Aisha fiska a d’aure ya
ce”matsawan in kika min gardama to kinsan sauran”. Yau
kam ya dawo mata Haiydar d’insa na da tuni wani tsoro
ya shige ta hannun ta ya kama tare da mannata da
jikinsa suka nufi cikin gidan suna shiga ya kulle k’ofar
tare da zare makullin yasa a aljihun sa, wani d’aki ya nufa
da ita, suna shiga ta ja ta tsaya a k’ofar d’akin cikin
dauriya ta ce”wai lafiya yau kuwa mai yasa ka kawo ni
nan gidan?”. Wani mayen kallo ya bita da shi tare da
matsowa kusa da ita ya ce”yau hakkina nake buk’ata a
gunki nagaji da jamin rai da kikeyi”. Janyota yayi ta fad’a
jikinsa tare da rufe k’ofar d’akin tafara k’ok’arin kwace
kanta wani tsawa ya daka mata ai ba shiri tayi shiru sai
hawaye ke sauka, wayarsa ya ciro ya tura ma Hajiya
message kamar haka. *_Assalamu’alaikum_* _Hajiya
barka da rana kar a tura d’auko Aisha naje d’auko ta
muna tare yanzu haka da ita, zamuje unguwa karkuga
shiru sai mun dawo_. Yana tura ma Hajiya yana ganin ta
bud’e sak’on ya kashe wayarsa ya sa a gen gado,
hannunsa yasa ya janye karamin hijab d’in Aisha tare da
sanya hannusa a gashin kanta ya fara shafawa Aisha ko
sai hawaye takeyi, hannusa ya zura ta cikin riganta ya
balle bra d’in ya fara….. *®NWA* *DEDICATED TO*
*AISHA MUHAMMAD* *(MAMAN ABDUL SHAKUR)*
*_RASH LUV_ * [2:32PM, 9/14/2016] Rash Kardam:
[4:09PM, 7/22/2016] Rash Kardam : BABBAN KUSKEREN
DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. *®NWA.*
*Pg-233~234.* Zuwa yayi ya rungumeta ya ce”baby na
kinyi kyau sosai”, murmushi tayi ya lakaci hancinta ya
ce”kullum kyau kike k’arayi ina rok’on Allah banu baby
mai kama da ke”. Da irin wannan kalaman ya lallab’a
Aisha suka lula duniyar masoya. Washe gari Haiydar ya
fita zuwa aiki Falmi ta tattari kawayen ta ‘Yan bariki suka
zo da niyar dukan Aisha kowacce da bulalarta a hannu
ana haka sai ga Haiydar ya dawo ganin su yasa ya kira
jami’an tsaro aka tattaresu ko wacce taji a jikinta suna
kulle a gurin jami’an tsaro, cikin Falmi ya faro ciwo kafin
me sai ga jini wanda hakan yasa aka kira Haiydar da
gaggawa aka kaita asibiti suna zuwa ana dubata cikin
inkon Allah suka zai da jinin suka shaida ma Haiydar
cewa magani Hana Haihuwa ta sha wanda yayi wa
haifarta illa, nan ran Haiydar ya k’ara b’aci sosai, sai da
aka taimaka mata jini ya tsaya, tana farfad’owa ya
ce”Fatima naga abu abunki yayi yawa don haka in kin
samu sauki ki wuce gidan ku”. Ya juya ya fita hawaye ke
zuba afiskansa tabbas Haiydar na son Falmi amma ita
tana bin zugar kawayen banza shi yasa da kishin hauka
dake damunta. Bayan kwana biyu Haiydar, da Sarkin
Fulani dasu Lamid’o da Hajiya suka tafi Yola tabbas Aisha
taga ga tanta da dangin ta ko ina sai murnan ta akeyi.
Batun gona ko Sarkin Fulani ba k’aramin kud’i ya kashe a
gun ba an k’awata gun sosai gwanin burgewa wanda aka
sanya masa suna *AISHA VILLA GARDEN* sai da akayi
bikin bud’e gurin Lamid’o ya damk’a amanar gurin wa
Maharbin nan daga nan kuma aka d’ibi ma’aikata a kauye
da birnin Yola, kafin suka dawo lokacin Aisha ta k’ara
kyau tayi haske ga wani kwad’ayin da takeyi kulum sai
tasha ice cream rigimar yau daban na gobe daban. Yau
ma kamar kulum Haiydar ya dawo Aisha ta tasashi gaba
da shagwab’a dole sai sunje shan ice cream ba yanda ya
iya dole ya fita su tafi, bayan sun saya ice cream dai-dai
zasu shiga mota Aisha ta hango wasu mutane take ta
rud’e tafara kuka ta mak’ale Haiydar yayi ta tambayan ta
duk ta rud’e sai da Haiydar ya sanya bakinsa cikin nata ya
bata wani sassayan kisses kafin ta dawo hayyacinta
rungeta yayi ya ce”mai ya faru wa ya tab’a ki mai ya
tsorata ki”. Cikin kuka ta ce”sune sune”. Haiydar ya
ce”waye su d’in?”. Aisha ta ce”sune suka d’aukeni lokacin
dana b’ata”. Haiydar ya ce”what!!” Gwada min su nan ta
nuna masa su suna shiga gun shan ice cream d’in
Haiydar yasa ta a mota ya ce”ki zauna anan karki fito”,
rikesa tayi ta fara kuka dan Allah ka kyalesu kar su cutar
da kai”. Murmushi yayi ya ce”karki damu kimin addu’a
Allah zai kareni”. Kai ta gir-giza masa wayansa ya d’aga ya
kira ‘Yan sanda da suke kusa ya na zuwa ya bada umurni
aka rufe gun aiko saiga police nan suka shiga aka kamasu
duka, nan yasa aka tafi dasu ya ce”bari ya mayar da
matar sa gida”. Gidan Hajiya ya kaita ya koma gun aiki.
Azaba akayi ta gana wa mutane nan da kyar suka fad’i
wacce ta sa su ran Haiydar ya k’ara b’aci da kansa yaje
har gidansu Falmi yasa aka kamota sai da ta daku a
gunsa sosai kafin ya ce”ki sani na sakeki saki d’aya tunda
har haukan ki ya kai kiyi tunanin kisa”. Falmi taji wahala
har tayi nadama abunda ta aika, ga wahala ga auren ta
ya mutu,.*************** Bayan wata takwas Aisha
na hango da zungureren ciki tana tafiya tana ciza baki ta
dafe cikin ta Haiydar ne ya fito daga d’aki da sauri ya
riketa ganin kamar nak’uda ne da gudu yayi d’aki ya
d’auko akwatin kayan haihuwar ta ya fitar ya dawo ya
sun kuceta sai asibiti cikin ikon Allah bata dad’e tana
nak’uda ba ta haifo baby boy d’inta, nan fa Haiydar yayi
ta kiran ‘Yan uwa yana fad’a musu kasancewan lafiyarta
lau ta haihu hutawa tayi aka sallame su kafin kace me
gida ya cika da ‘Yan uwa da abokan arziki. Bayan kwana
bakwai ranan suna yaro yaci sunan *_ABDUL SHAKUR_*
Yaro kyakyawa gwanin burgewa bikin suna yayi kyau ida
muka samu kyatuttuk’an zannuwa ne mai hoton yaro da
Al- qur’ani mai girma abun sai wanda ya gani haka aka
watse. *®NWA* *DEDICATED TO* *AISHA
MUHAMMAD* *(MAMAN ABDUL SHAKUR)* *RASH
KARDAM * [2:32PM, 9/14/2016] Rash Kardam: [4:42PM,
7/22/2016] Rash Kardam : BABBAN KUSKEREN DANA
TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. *®NWA.*
*Pg-235~236.* 4yrs latter Wani kyakyawan Yaro na
hango rik’e da teddy a hannusa yana gudu yana dariya
ko dana kalli wanda yake bi wani kyakyawa ne fari sol
tamkar shi yayi kansa ko dana kalleshi da kyau sai naga
kaman Haiydar wata kyakkyawar mace ce ta fito ta
ce”Abban Abdul in kun fara wasa kai ma sai kadawo
kamar wani k’aramin yaro ya tsaya jin maganar ta
Abdul~shakur ne yazo ya kama Abban sa ya dariya ya
ce”na kama na kama”. Haiydar yayi dariya ya d’agashi ya
cilla shi sama duka suna dariya, Assalamu’alaikum jin
sallama duka suka juya sai da suka kalli mai sallaman
sosai suka gane Falmi ce da sauri tazo ta durk’usa tana
basu hak’uri Haiydar ya kau da fuska ya tashi zai tafi
Aisha ce tazo ta rungume Falmi ta ce”Aunty na ni
bakimin komai ba na yafe miki Aunty na”, Falmi ta share
hawaye ta ce”nagode ina rokinki dan Allah ki rok’ar min
Haiydar da ya mayarni d’akina wallahi nayi nadama”. Ta
karashe maganan tana kuka Aisha ta rungume ta
tace”Aunty kar ki damu Haiydar zai mai daki kuma
Haiydar na sonki kawai zugan kawaye ne daman”. Falmi
tayi godiya ta tafi, Aisha da daddare tasamu Haiydar da
maganan dawo da Falmi ya nuna bazai dawo da ita ba,
ganin tayi yaki hakan yasa tayi fushi ta juya masa baya
kusan kwanan su uku basa magana kafin Haiydar yaga
bazai iya jure rashinta ba da kansa yazo ya bata hak’uri
ta ce”in ka ga na hak’ura ka mayar da Aunty na”. Haiydar
da kyar ya yarda sai da suka sanar da su Hajiya tayi
murna don ita ma Falmi har gida taje ta bata hakuri.
Aisha ita da Hasna sukayi ta jagale Haiydar shi ya basu
kud’i suka had’a kayan akwati aka biya sadaki ranar
jumma’a aka d’aura aure, dadadare amarya ta tare a
gidan ta Haiydar bayan ya shigo sai da ya tarasu ya musu
nasiha tare da kashedi banda fad’a bare hayaniya suka
amsa, Aisha ita taje ta taya Haiydar shiryawa ta basa
jallabiya mai kyau sabo ta fesheshi da turare ta kama
Hannusa kafin ta rakosa Har d’akin Falmi bayan sun
shiga da sallama Aisha tana ta addu’a a zuciyar ta don
wani irin kishi takeji amma tana ta addu’a ta kori
shaid’an cikin sanyi murya ta ce”Aunty ga Ango ki na
kawo miki ina muku fatan alkairi sai da safe”. Tana fita da
gudu tayi d’aki tanahawaye niko Rash na ce”hmm kishi
kumallon mata”, Falmi ita ta matso kusa dashi ta fara
shafa sa daga haka na fito, washe gari Aisha ta shirya
musu karin kumalo mai lafiya. Bayan kwana biyu zaman
lafiya a gidan Haiydar ba’a magana dukkansu suna
girmama junasu, yau k’awar Falmi ne Gwantsi ta kawo
mata ziyara ganin irin zaman da sukeyi nan ta fara hure
mata kunne tun kafin tayi nisa Falmi ta ce”kee tsaya da fa
da yanzu ba d’aya band in ada kin zugani na d’auka
yanzu na nutsu nasan mai nakeyi, dakam nasan *NA
TAFKA BABBAN KUSKURE* amma yanzu ina cikin hankali
na kinaso in fito muna yawon kan titi tare tare”.
*®NWA* *DEDICATED TO* *AISHA MUHAMMAD* *
(MAMAN ABDUL SHAKUR)* *RASH KARDAM * [2:32PM,
9/14/2016] Rash Kardam: [4:50PM, 7/22/2016] Rash
Kardam : BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA daga www.hausaebooks.com.ng NA
©RASHEEDAH .A. KARDAM. *®NWA.* *Pg-237~238.*
Falmi ta ci gaba da ce wa”a yanzu kam na gane hanya
kuma na rungumi kawaye na na kirki sune Mesha luv da
Zahra BB sune masu sona da gaskiya, kamar yanda naga
‘Yar uwata Aisha bata da kawayen da suka fi mata Sanah
da Sadeey don haka tashi ki fita bana son ganinki”.
Gwantsi ta tsaya tana mata kallon mamaki ganin bazata
fita ba Falmi ta d’auko waya ta ce”ko ki fita ko na kira
Haiydar”, jin haka yasa Gwantsi fita ba shiri tana zuwa
k’ofa taga Haiydar wanda duk abunda sukeyi yaji, Falmi
da sauri taje ta rungumesa ta masa sannu da dawo
hannusa ta kama ta kaishi d’aki tare da rugemasa kayan
jikinsa sai da yayi wanka ta kawo masa abinci a baki take
basa, Haiydar ya kalleta ya ce”Alhamdulilah! Tabbas yau
ina farin ciki kuma na yarda matata Fatima ta nutsu
kuma ina gode ma Allah da ya kawo Aisha cikin rayuwan
mu don yanda nake samun kulawa da k’auna daga Falmi
ba tare da na biya kud’i ba”. Ya karashe maganar cikin
zolaya dukan wasa ta kai masa tare da rungumesa ta na
sha fa kansa, suna haka aka kwan- kwasa k’ofat suka
bada izini a shigo Aisha ce tashi go rik’e da hannu
Abdul~shakur yaro mai kyau da gudu yazo ya haye
Baban sa yana masa oyoyo Aisha da Falmi sai dariya
suke masa nan ya biye masa sukayita wasa.
*ALHAMDULILAH!* Dukkan yabo ya tabbata ga ubangiji
sammai da kassai , nan na kawo k’arshen wannan labari
na *BABABN KUSKUREN DANA TAFKA* kuskuren dana yi
aciki ya Allah ka yafe min ka bani ikon gyarawa Ameen.
*KIRA GARE KU MAKARANTA* Ina fatan kun gane sak’on
da na isar a ciki kusani ba wai ina nufin d’aukar ‘Yar aiki
da matsala ba a’a sai dai kamar yanda Falmi ta sake ma
‘Yar aiki komai na Mijinta hakan ba dai-dai bane, sannan
kuma da masu halayyan hana mijinsu hakkinsu sukuma
nuna cewa sai aun basu kud’i kafin su biya musu
buk’atarsu na Auratayya wannan ba dai- dai bane
haramun ne ke/ni dukkan kowace ta san kanta inda mai
yi sai ku gyara Allah ya bamu ikon bin dai-dai Ameen.
*SADAUKARWA* Na d’auki wannan *LITTAFIN* mai
suna *BABAN KUSKUREN DANA TAFKA daga www.hausaebooks.com.ng*na sadaukar wa
*AISHA MUHAMMAD (MAMAN ADUL~SHAKUR)* Allah ya
bar k’auna. adsense 2 hereBABBAN KUSKUREN DANA TAFKA
Na Rasheeda A Kardam
Complet
Ebook creat by Shuraih Usman
Ebook publish by www.hausaebooks.cf
Ebook din nan yazo maku ne daga shafin www.hausaebooks.com.ng
Kuna ziyartar shafinmu don samun sababbin littatafai
Ga duk wanda ke bukatar ebooks nashi ya samu shiga cikin wepsite namu sai ya turo mana da littafin ta Email namu hausaebooks@gmail.com

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment