Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Kardam: BABBAN KUSKEREN
DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM.
Pg-156~160. Ba yan gama wanan shagalin, Falmi ita da
tawaganta suka koma gidanta. Yayin da Hajiyansu
Haiydar ta kira Amarya d’akinta, ta bata wani abu a cofi
tasha. Hajiya tace”ki k’wanta ki huta sosai. Sai da a kayi
sallan magriba Hajiya tasa ta gaba taci abinci mai yawa.
Hajiya ta saka ruwa a murhu, tare da lalle da magarya ya
dahu sosai, sanna tasaka ruwa daban wanda ba komai
aciki, ta juye farin ruwan a bokiti ta surka ta kai bayi.
Kafin ta d’au wani bokitin ta tace ruwan lallen nan, da
rariyan ta, sannan ta d’auko madaran turaruka kala-kala
tasaka mata madaran turaren wanka acikin ruwan lallen.
(Shi ruwan lallen ba’a cika ruwa da yawa sosai, d’an dai-
dai za’a saka). Ta kai bayi tace”Aisha tashi kiyi wanka zaki
ga ruwan biyu ne, kiyi wankan sabulu da farin, ki
tabbatar ki dirje ko ina. Bayan kingama wankan sabulu,
sai ki d’auki ruwan lallen nan zakiga ba yawa, ki tabbatar
kin game jikinki dashi ta ko’ian. Aisha Indo ta amsa da”to
Hajiya nagode. Saukowa tayi tashiga bayi, wanka sosai
tayi kafin ta yiwankan lallennan. Tun daga bayi k’amshi
ke tashi har falo. Hajiya ta taho da kasko k’arami, Indo
na fitowa tace”zo nan. Fallen zani ta bata, ta lulub’u dashi
kafin ta samata kasko tare da zuba turarukan wuta aciki
masu kamshi.(masu k’aratu amfanin wannan wankan
lallen, da turare yana saka jikin mutun yayi k’amshi,
sannan k’amshin yana kama jiki, yana sa mutum kara
haske da kyau. Sannan a zuba turare aciki zaki ringa
kamshi ne sosai. Idan mutum ya fito daga wanka, bazai
bari jikinsa ya tsan- tsame ba. Da ruwan zaki saka
turaren wuta a kasko ki luluba jikinki, sannan ki tabbatar
kamshin turaren na bin jikinki, in turaren ya k’are ki
k’ara sakawa har sai kin tsan-tsame.zakiji k’amshin ya
kama jikinki). Hajiya ta d’auko atamfa riga da zani, acikin
a kayan Indo ta d’auko kwalban turare yar mai duguri, ta
juje akan kayan, hatta ina wears d’inta saida suka sha
turare masu sanyin kamshi, wanda duk namiji lafiyaye in
ya shaki kamshi, sai ya yaba. Hasna ne ta turo qofa
tashigo, ita ta tsara ma Indo kwaliya, kafin tasaka kayan.
Masu k’aratu tundaga haraban gidan zaku iya jiyo
kamshin da indo takeyi. Waya hajiya ta d’auko lokacin
tara da rabi, Haiydar takira tace”kazo yanzu ina son
ganinka. Cikin girmamawa yace”to Hajiya gani zuwa. Bai
dad’e ba ko sai gashi, cikin shaddarsa ja sai maik’o takeyi.
Ko da yazo Main falo, bak’ine aciki sai tsokanarsa sukeyi,
murmushi ya musu ya nufi cikin d’akin Hajiya. Qofar
tura tare da yin sallama. Tsayawa yayi cak dan ganin
Indo a bakin madubi tana saka sarka. Sam ya kasa d’auke
kansa daga gareta, ji yake kamar yaje ya rungumeta,
amma jinkai da girman kai bazai barshi ba. Wata zuciya
tace”to mai zakayi da bak’ar mace ma. Wata zuciyar ko
cewa take”ai kuma duk randa tayi gayu sai ta fi falmi
kyau. “Mtss kai k’aryane, yama za’ayi tafi Falmi kyau.
Yana wannan tunani Hajiya tashigo da sallama
tace”yauwa Babana ka iso. Sosa keya ya fara tare da
rusunawa ya gaidata, Hajiya ta zauna abakin gado,
Haiydar ya zauna akan dadduman dake kasan d’akin.
Hajiya tace”Aisha zo nan. Cikin nutsuwa Indo ta tako
zuwa kusa da k’afar Hajiya ta zauna. Hajiya tayi gyaran
murya, tare da fara musu nasiha mai shiga jiki. Harda
yan ayoyinta takawo musu, wanda yake nuni hakkin miji
akan matarsa, tare da hakkin mata akan miji. Bayan ta
gama tace”Aliyu!”. Kansa asunkuye yace”na’am Hajiya.
Taci gaba da cewa”ga *AMANA* Aisha na baka, ban
yarda matarka ta takura mata ba. “Itama matarka ce
kamar yarda Fatima take matsayin matarka. Ko da
tagama musu nasiha ta sanya musu Albarka tare da
cewa Indo d’auko gyalenki. Hajiya ta d’auko Hijab
tace”tashi muje da kaina zan kaiki d’akinki. Hannuta
hajiya ta riko suka fito falo, sai tsokanar su akeyi.
Haiydar shi ya jasu har zuwa gidansa, ko da suka shiga
duk yan biki sun watse sai Falmi da taci riga da wando,
tayi shirin ko ta kwana, don yau a shirye take da in
dakuwa ne ma suyi a gidan. Ganim Hajiya yasa ta
rusuna,, bata ko gaida ta ba sai wani hararan da ta aika
musu. Hajiya ta shigar da Indo d’akinta kafin ta fito
Haiydar yazo ya rakata yace”zai maidata gida. Hajiya
tace”a’a na yafe driver ya maida ni. Sai da suka bar gidan,
sannan ya nufi gida. Yana shiga Falmi ta ja ta tsaya a dai-
dai qofar shiga side d’in Indo. Dake shi ba ma niyayar sa
shiga gun bane ko kalonta baiyiba yanufi side d’insa. A
dai-dai bakin qofarsa ta kwanta, wai dan karyazo ya
wuce d’akin Indo bata sani ba, a haka har bacci ya
d’auketa. Haiydar ko yana shiga d’aki kayansa ya cire ya
watsa ruwa, ya sanya kayan bacci ya kwanta. Ko da ya
rufe idonsa photon suran Indo ke masa yawo a idonsa.
Da duk al’amuran dasuka faru a tsakaninsu. Sai juyi
yakeyi gashi duk yana hannu, amma yasan in ya tink’ari
Falmi, bala’i zai ne mo ma kansa haka yayita juyi har
bacci b’arawo ya d’aukesa. *DEDICATED TO* *AISHA
MUHAMMAD* *(MAMAN ABDUL SHAKUR)* *RASH
KARDAM * [7/5/2016] Rash Kardam BABBAN KUSKEREN
DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM.
Pg-161~163. Gari na wayewa Falmi ta tura d’akin
tasamu Indo tana bacci. A fili tace”eyeh lalle fa kin samu
kanki acikin bak’ak’en labarawa. “Har wani lokacin bacci
kika samu. “Lalle ko zanyi maganinki yanzunan. Cikin
hanzari ta juya zuwa kitchen d’inta, ruwa mai sanyi ta
d’auko a fridge, in kunga ruwan har wani tururi yakeyi
na sanyi. Tana zuwa tasamu har yanzu Indo bata farka
ba, cikin zafin nama cike da masifa Falmi ta shek’a mata
ruwan sanyi a jiki. Cikin razana indo ta farka, sai wuk’i-
wuk’i take da ido. Falmi tace”ke waya baki damar yin
bacci a gidan nan ko kin manta matsayinki ne. “Na yar
shege kuma yar aiki maras amfani ke da babu duk d’aya
kuke a gidan nan. “Maza sauk’o ki had’a mana breakfast.
Indo ji take kamar ta kurma ihu, ba wai watsa mata
ruwa, da masifan da Falmi ke ta mata bane ya dameta
ba, ila cemata da tayi yar shege, wannan maganan ya na
k’ona mata zuciya. In dai zagi ne kam inda sabo ya
kamata tasaba. Tsawa Falmi ta sake mata wanda yasata
dirk’owa daga kan gado, da sauri ta nufi hanyan falo.
Kitchen d’in dake baban falo ta shiga ta had’a musu
breakfast, sai da ta jera komai kafin ta d’ibi na ta, cikin
d’akinta ta koma, tayi wanka tare da yin brush kafin ta
karya. Hajiya sai da tabari Indo tayi 3 days tasaka driver
ya kaimata ak’watunanta. Rayuwan Indo ya canza a
gidan ba’abinda ta ke fuskanta ila tsangwama da tsana
daga gun Falmi da Haiydar. Tun da ta fahimci duk ranar
da sukayi karo da Haiydar sai ta gane kurenta. Hakan
yasa indai taji yana falo to bata fitowa sai ya fita.
Kwanaki sun tafi yau ki manin 2 month da yin bikinsu.
Hajiya ce ta had’a goma na arziki tasaka Hasna ta zo
duba lafiyar d’iyarta Indo. Hasna tana zuwa ta wuce
d’akin Indo tasamu tayi tagumi. Ta rame ga wani bak’in
da ta k’ara, cikin hanzari hasna ta yar da jakanta, taje
tace”Aunty na mai ya sameki haka?. “Kinyi rashin lafiya
ne?. Cikin dauriya Indo ta k’ak’alo murmushi tace”lau na
d’anyi zazab’ine amma na warke yanzu. Sam Hasna bata
gamsu da maganarta ba, suna cikin haka, sai ga Falmi ta
shigo tana kiran Indo harda ashar d’inta. Sam bata san
da zuwan Hasna ba kasancewar daga yawonta ta fito.
Hasna ne tace”kar ki amsa wannan kiran yan tashan.
Falmi jin Indo bata amsa ba tasan kuma tana jinta, abun
sai ya kular da ita. Har zata tura qofar ta fasa ta koma
d’akinta, zuk’ek’iyar bulala ta d’auko, ganin jikin bulalan
yasata sakin wani murmushi, don tasan wannan bulalan
in har yashiga jikin Indo zata gane shayi ruwa ne. Cike da
isa da gadara, tana wani wawwaina bulalan a hannuta. Ta
iso falon Indo, Kiran yantasha ta sakeyi. Hasna kuwa ta
hanna Indo amsawa harda tushe ma Indo baki. Falmi a
harzuke tashigo falon, sam bata lura da Hasna ba tayi
kan Indo da bulala. Cikin sa’a ta tsula mata na d’aya, ta
kai na biyu kenan Hasna tayi saurin shiga tsakaninsu.
Falmi ganin Hasna ta razana amma sai ta dake tace”kee
bani guri inyi abunda nayi niya. Hasna tace”ke Fatima
kike kowa, kar ki kuskura tsautsayi ya gifta miki kice zaki
sake dukan Indo. Falmi cikin fushi tace”ke ce mai tare
mata ko. Cike da gadara Hasna tace”eh da abunda zakiyi
ne.. Tsautsayi yasa Falmi ta d’aga bulala wai zata zuba ma
Hasna. Amma kash ina ae ta makara Hasna tayi saurin
k’wace bulalan tashiga tsula ma Falmi, iya karfinta, Kan
kuce mai ta cika gida da ihu. Sai da Hasna ta mata lilis sai
ihu take, karar motan Haiydar ne ya dawo gida, hakan
baisa Hasna ta daina ba, Haiydar jin ihun Falmi ko mota
bai rufe ba ya shigo gidan da gudunsa. Falon Indo yaji
muryanta cike da mamaki yayi side d’in da gudu. Masu
karatu bari mu huta a nan, ina muku murna da zagowan
k’aramar sallah. Allah ya amsa mana ibadun mu ya
kumasa muna daga cikin wa’yanda aka ‘yanta daga wuta
zuwa aljannah ameen. *HAPPY SALLAH IN ADVANCE*
*DEDICATED TO* *AISHA MUHAMMAD* *(MAMAN
ABDUL SHAKUR)* *RASH KARDAM * [2:32PM,
9/14/2016] Rash Kardam: BABBAN KUSKEREN DANA
TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-164~166. Cikin
hanzari Haiydar ya tura qofar d’akin. Cike da mamaki ga
takaicin abunda ya gani, wai Hasna ke dukan Falmi.
Kanta yayi ya bata lafiyayen mari, tukun Hasna ta koma
gefe. Falmi ko ganinsa ta k’ara sautin kukanta. Cikin
b’acin rai Haiydar yace”ke husna mai ya kawo ki gidan
nan?. “Wa ya baki daman dukan matata?. Hasna tace”
Yaya baka abu….. “Ke ni sa’anki ne ina magana kina
magana. Ganin yanda ke huci, ya nufo kanta zai daketa,
ta d’au wayarta da gudu, tayi bayi tasaka key. Ganin ta
gudu Haiydar ya dawo kan Indo yace” wato kece
munafukar gidanan nan ko?. Belt d’insa yasoma zarewa,
nan Indo tasoma kuka tana basa hak’uri. Hasna jin
Haiydar zai daki Indo, da sauri ta kira Hajiya ta saida
mata ga Haiydar zai daki Indo. Hajiya ta kira wayan
Haiydar dai-dai lokacin da ya d’aga belt, zai zuba ma
Indo wayarsa tayi k’ara, yana cirowa sunan Hajiya ya
gani. Ya d’aga tare da fad’in “Assalamu’alaiku. Hajiya ta
amsa masa da”Ameen Wa’alaikumusalamu. “Ali wallahi
karka kuskura ka daka min ‘ya’ya, mai suka maka ne
haka?. “Ka jirani ina zuwa yanzu, tunda Abba ku baya
gari, bare yazo da kansa. Bata jira amsan shi ba ta kashe
wayar, Hijab ta zara da waya ta fito driver ta kira, suka
d’au hanyan gidan. Haiydar ko wani takaici ne ya
tokaresa, tabbas Hasna ne ta fad’a ma Hajiya, cikin
zuciyarsa ko cewa yake”lalle duk randa na rike yarinyan
nan, bansan wani irin duka zan mata ba. Falmi ya
d’auketa, tare da kaita falo. Itako ta wani sakan jiki, da
baki tana kuka kamar yarinya. Hajiya ne ya shigo da
sallaman ta, Haiydar ya amsa mata, kalon tambaya ta
tsaya masa, kai ya sunkuyar k’asa. Hajiya tace”ina
yarana?. “Wallahi in ka duki d’aya a cikinsu, ranka sai yayi
mumunan b’aci. Bata jira amsansa ba ta nufi side d’in
Indo, tana shiga taganta, ta had’a kai da gwiwa, tana kuka
mai ban tausayi. Hajiya da sauri ta yi gunta tana
cewa”Indo ya dakeki ko?. Hasna jin muryan Hajiya yasa
ta bud’e qofa ta fito. Hajiya tace”mai ya kaiki bayi?.
Hasna tace” Ya Haiydar ne ya tashi zai buge mu. “Na
gudu toilet. Hajiyan tace” muje falo tukun inji komai.
Hasna ta kama hannu Indo suka nufi falo, Haiydar na
ganin su Hajiya sun fito, ya sauka kasa ya zauna, Hajiya
ta zauna a kujera, su Indo suka zauna a kasa suma, Falmi
ko tana zaune a kujera taki saukowa. *DEDICATED TO*
*AISHA MUHAMMAD* *(MAMAN ABDUL SHAKUR)*
*RASH KARDAM * [7/6/2016] Rash Kardam BABBAN
KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM.
Pg-167~169. Hajiya ta kalli Haiydar tace”mai ke faruwa?.
Cikin in ina Haiydar yace”Hajiya na dai dawo ne, naji
muryan Falmi na ihu, ko dana shigo gida da gudu, sai
naji sautin kukanta a side d’in Indo. “Ina zuwa sai na
samu Hasna tana dukanta. Hajiya tace”shine ka tashi
zaka da kamin yara?. “Shin kayi bincike akan mai ya
had’asu?. Kai ya gir-giza alamar a’a, Hajiya taci gaba da
cewa”haka babba ya kamata ya yanke hukunci, ba tare
da binkiken mai ya faru ba. “Haiydar bana son ka da
hakan ba adalci bane. “Yanke hukunci batare da bincike
ba. Ta juya ta kalli Hasna tace”ke Hasna mai ya faru har
kika daki matar wanki?. Hasna ta fara basu bayani
tundaga shigowarta, harda kiran da Falmi tayi ma Indo,
bata rage ko wasali ba. Hajiya ta saki salati tace”daman
kuntata ma yar mutane kukeyi?. “Matarka har tasamu
daman dukan yata?. “To bazaiyiwu ba. Hasna tayi sauri
cewa”Hajiya ina rokon alfarma da amayar da Indo
makarantar boko da islamiya. ” Tayi karatunta taga ma,
kuma hakan zai bata daman samun sakewa, da samun
‘yancinta, da wayewa, batare da wata ta takura mata ba.
Hajiya tace”rufe mana baki manya na magana kina saka
baki. Hajiya ta musu fad’a tace”duk randa wani ya sake
ya daki Indo a gidan. “Tabbas zakuga bacin raina. “Kuma
daga yin aure, bazan so yata tafara yaji ba. “Amma
komawa makaranta yazama dole ta koma. “Haiydar
yanzu zan tafi da matarka, za’amata registration sai
angama komai ta dawo. “Inaso gobe kazo ka kaita,
amma sai mun zab’i makarantar da zatayi karatu. Kafin
Hajiya tak’ara magana Falmi tasaki ihu, tana fad’in Hajiya
ki taimakeni karta koma makaranta. Nayi alkawarin
bazan daketa ba, gwara ta zauna a gida, In Har Indo ta
koma makaranta to nakad’e nikam. Magana Falmi takeyi
ba uwa k’wab’a. Hajiya ta mata kalon bakida kunya.
Hajiya tace”Hasna kuje da Indo ta d’au hijab d’inta, da
kayanta kala biyu, kuzo mu tafi. Hasna kamar jira take,
da sauri ta kama hannu Indo suka nufi d’aki. Basu dad’e
ba suka fito, Hajiya tace”mun tafi. Haiydar ya rako su,
har gun mota suka tafi. Haiydar yana dawowa ko kalon
Falmi baiyi ba, ya wuce d’akinsa. Hajiya suna zuwa tasaka
Indo tayi wanka, ta bata abinci taci, sai da suka huta
Hajiya tace”Hasna yanzu wani makaranta ne yakamata a
yi registration ma Indo?. Hasna tace”inaga *SABIL
SUNLIGHT* za’a mata. “Don makaratan yana da kyau ana
karatu sosai. “Kuma sabon skul ne. Hajiya tace”to ba
matsala gobe zamuje tare kawai. “Tunda Haiydar na fita
aiki. Hasna suka shiga d’akin da Indo, suna hira, Hasna
tace”kin san me aunty na? Indo tace” a’a sai kin fad’a.
Hasna tace” ina rokon Allah yasa in anje registration d’in
nan su baki science class. “Kinsan sabida mai yasa nake
son abaki science class. Indo tace” a’a sai kin fad’a. Hasna
tace”sabida ina so Falmi tayi regret cos taki ya auro mai
aikin asibiti. “Ni kuma tun randa aka yi bikinku, na d’au
alwashin da ikon Allah sai nayi hanyan da kika koma
school. “Sannan inaso ki waye ki zama kikakiyar likita ba
nurse ba. Indo tace”nima ina da burin karatu da, sai dai
rashin mai taimaka min. “Gaskiya nagode Allah ya barmu
tare. Hasna tace”Aunty Jiddah tana kirana a waya tana
tambayarki. “Wai tanaso inta dawo zatazo ta koya miki
abubuwa dayawa. “Basa k’asan ne ita da Yaya Ghali sun
fita yin wani course a waje. Indo tace”ayya ni ae suna
burgeni da Ghalinta dukansu Doctors. Hasna
tace”wallahi kam ae sai kinji labarin soyayyan su gwanin
burgewa wanda aurensu, yazo musu a *BAZATA*. Haka
sukayita hira a tsakaninsu. Washe gari Hasna ta jasu a
mota suka nufi *SABIL SUNLIGHT*. duk wani abunda ya
dace suyi anyishi. Anyi interview ma Indo ganin
k’ok’arinta, yasaba suka bata Science class. SSS1 daman
tayi JSCE ta. SSS1A aka bata, nan suka bata uniform da
komai hatta books, da text book suke bayarwa. Malamin
da kansa ya kaita ajin, ya kira wata Sadiya S Adam, bayan
da Sadiya tazo yace”Sadeey ina k’awarki?. Wacce aka kira
da Sadeey tace”yau batazo ba, bata jin dad’i. Uncle d’in
yace”ga frd nan na muku. “New comer ce gobe zata fara
zuwa, inaso ku zauna tare da ita. Sadeey tace”okay sir!.
Malamin yace”sunanta Aisha Muhammad. Nan suka
gaisa Sadeey ta koma aji. Su Hajiya kuma suka dawo
gida, Indo in banda murna ba’abinda takeyi, wai yau
itace ta koma makaranta. Masu karatu ku shirya yazu ne
gurmin zai fara, don Indo zata shigo gari, zata kile. Masu
karatu ya kuke ganin Haiydar zai yi akan Indo nan gaba,
k’iyayar zata ci gaba ko zai k’are?. Shin Indo zata ci gaba
da d’aukan rainin da suke mata?. Shin ya rayuwan Falmi
yake kasancewa nan gaba?. Ku biyo yar *JARAWA* don ji
yanda zata kaya. *HAPPY SALLAH IN ADVANCE*
*DEDICATED TO* *AISHA MUHAMMAD* *(MAMAN
ABDUL SHAKUR)* *RASH KARDAM * [2:32PM,
9/14/2016] Rash Kardam: [7/6/2016 Rash Kardam]
BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA daga www.hausaebooks.com.ng NA ©RASHEEDAH .A.
KARDAM. Pg-170~173. Ko da suka dawo gida, Hajiya ta
zaunar da Indo tayi mata nasiha, game da aurenta,
sanan ta k’ara da cewa”Aisha kiyi hak’uri ina sane, da duk
irin abunda Aliyu yake miki. “Abunda yasa ba zan
takurasa ba a kwai lokacin dana ke jira, zan ramamiki
duk abunda ya ke miki, inaso ki nutsu kiyi karatu nan
gaba sai Haiydar yazo da kansa yana baki hakuri.
“Alokacin ne zamu rama duk abunda ke mana, Hajiya
wani murmushin mugunta tayi, kafin taci gaba da
cewa”zan saki a makaranta islamiya, don ki rage yawan
zaman gida. “Sannan ki k’ara hak’uri da duk abunda zasu
miki, wataran zakici riban hak’urin ki, har sai ni da kaina
nazo, ina cewa Aisha ki d’an ji tausayin Yayanki, ki
sassauta ma Haiydar. Hasna ne tayi murmushi don itama
tanason ta ga wannan ranan. Hajiya tace” a kwai motar
da Abban na, Sarkin Fulani(Gakansu Haiydar ) ya ban
range rover zan baki ita, tadawo naki halal malak. “Zansa
Hasna ta koya miki mota amma sai naga kunyi jarabawa,
da irin sakamakon da kika fito da shi kafin na damk’a
miki motarki a hannuki. “Sai gobe zaki fara zuwa school,
in kin dawo da kaina zan maidaki gida, kuma zansa
driver yana kaiki makaranta. “Ku tashi kuje ku huta Allah
ya muku Albarka. Suka amsa da”ameen. Gidan Haiydar
ko yau ya dawo da niyar ko ta kwana, don yau yayi niyar
karb’a hakkinsa a gun Falmi. Don yayi hak’uri har ya gaji,
rabonsa da ya kusanceta har ya manta. Wanka yayi ya
nufi d’akinta, yana zuwa ya tarar ta baje a gado, tana
sharan baccin ta. Hawa gadon yayi, yazo kusa da ita ya
kwanta. Salon sa da yake rikitar da mace, ya fara aika
mata sak’onsa. Cikin bacci Falmi taji ana shafata, farat ta
farka ganin Haiydar yasa ta rik’e hannusa, tace”mai kake
shirin yine?. “Ko ka manta dokata ne?. “Matsawan kana
son biyan buk’atarka sai ka ajiye min kud’i. Cikin da
shashiyar murya Haiydar yace”haba Falmi anya kina
tsoron Allah kuwa?. “Matar aure na na sunnah, don zan
kusanceki sai na biya kud’i. “Kisani fa hakan haramun ne.
“Kisani mala’iku su tsine miki fa?. Falmi tace”ai yau in har
kaga ka samu abunda kakeso to kasaka min kud’i har
200k. Haiydar yace”Falmi bayan kud’in sadakin dana
biya?. “Ki sani bana son miki ta k’arfi. “Ina rok’onki da kiji
tausayina, ba wai don bana da kud’in da zan baki ba, a’a
saidan hakan baida kyau. “Kuma duk irin k’yautata miki
danakeyi ba k’ya gani?. “Yaushe na baki 300k fa falmi?.
Tsaki ta ja ta mik’e, za ta sauk’a daga kan gadon, ya
fincikota, sak’onni yasoma aika mata dashi. Duk iya
k’arfinta ta kasa kwacewa sai tasoma masa ihu. ( kira
gareku mata masu irin wannan halin, kusani baida kyau,
Allah da mala’ikunsa, suna tsine wa duk matar da mijinta
ya nimeta, ta juya masa baya. Ko kuma ta nimi sai ya
bata kud’i kafin ya kusance, ta kamar yanda Falmi takeyi.
Dan Allah ku kiyaye inda maiyin haka ku daina. Kisani
duk randa kika faranta wa mijinki rai shi da kanshi zakiga
canji a gunsa kuma komai kika roka matsawan na dashi
zai baki, amma ba kice sai ya baki kafin ki basa hakkinsa
ba, hakan haramu ne. Allah ya tsaremu da aikata hakan
ameen). Bai k’yaleta ba sai kusan asuba, wanka yaje yayi
ya kwanta, yana tunani irin halin Falmi sam baida k’yau.
Gidan Hajiya kuwa, da safe Indo tayi wanka tasaka
Uniform d’inta purple da light purple, riga da skirt sai
barret. Hijab ta d’auko ta d’aura akan kayan, Indo tayi
kyau sosai, Hasna ne ta kaita school d’in. Suna zuwa
school d’in registration office suka nufa. Bayan sun gaisa
da uncle d’in jiya, Hasna tace”gata nan mun kawota.
Uncle d’in yace”ok wata yarinya ya kira, yace”ta je SSS1A
ta kira masa Sadeey S Adam da Sanah S Matazu. Ko da
yarinyan ta tafi, bata dad’e ba saiga su sunzo. Nan ya
had’a su yace”su je su zauna tare. Sanah da Sadeey suka
kama hannu Indo suka nufi class. Hasna kuma ta wuce
school d’inta itama. *MASU NIMAN WANNA BOOK ‘DIN
DA WA’YAN DA SUKE MIN MAGANA TA PRVT, PLS KUYI
HAK’URI SAK’ONNI YANA YAWA, BA WULA’KANCI BA.
KUNA TAMBAYA A GROUP DAN ALLAH. KUMA ‘YAN
GROUP MAI SHI KUNA BAYARWA COS MUTANE SUNA
YAWA, KUMA GA MESSAGES ‘DIN MASU YIN COMMENTS,
SUMA ZAN MUSU REPLY, INA HÀU DA NIYAR INA GA
SAK’O IN CIGABA DA TYPING, AMMA SAI NA TSAYA
TURAWA MUNAE, WASU IN BAN TURA MUSU AKAN
LOKACIBA SUNA FA’DAN BAK’AR MAGANA DUK IYA
K’OKARIN DANAKE AMMA BASA GANI, DAN ALLAH FANZ
A TAIMAKA ANA TURAWA A GROUPS IN AN TAMBAYA
PLS N PLS* GA WANNAN KUYI HAK’URI BAYAWA KAINA
YA DAMEN DA CIWONE NASO NAYI YA FI HAKA .
*DEDICATED TO* *AISHA MUHAMMAD* *(MAMAN
ABDUL SHAKUR)* *RASH KARDAM * [2:32PM,
9/14/2016] Rash Kardam: [7/7/2016] Rash Kardam
BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA daga www.hausaebooks.com.ng NA ©RASHEEDAH .A.
KARDAM. Pg-174~176. Sanah da Sadeey suka nufi class
da Indo, ni ko Rash ina biye da su. Tun shigarsu class,
yan aji suka fara tambayan Sanah da Sadeey wacece?.
Sanah suka sharesu ganin sunyi hanyar sit d’in da ke
k’usa dana su, wani yaro yace”kai new comer ce fa. “Jiya
ina gani aka kawo ta. Wasu sukafara cewa ke kizo nan ki
zauna, wani yaro yace”kai gaskiya tana da kyau. “Zamu
zama frds ko?. Wani kalo Sanah ta musu, wanda yasaka
shi yin shiru yana dariya. Sit d’aya aka bata kasancewa
kowa da sit d’insa, had’e da kuma lokansa na ajiye wasu
littafa. Sanah ce a farko sai sit d’in Indo a tsakiya sai
Sadeey a baya. Ana haka Uncle d’in Biology yazo, darasin
da yamusu shine. *CELL* sai da ya gama darasi yayi
bayani sosai, ko da yazo yin Evaluation, ya tambayesu
kamar haka, “class what is cell?. Shiru ba wanda ya d’aga
hannu, sai Indo ta d’aga hannu, ya nuna ta, Indo ta mik’e
tafara cewa”Cell is the fundamental total unit of life.
Cikin salon da take karatun, abun burgewa ne, bare
muryanta tamkar mai yin busa. Tana gamawa tun kafin
malamin ya bada umurni a tafa mata, ‘yan class suka
d’au sowa da tafi. Jikake raf raf raf, sannan malamin
yace”well done good girl clapp for her once again. A
haka har aka tashi. School bus ne ya maidata gidan
Hajiya. Washe gari ta koma gidanta, Haka rayuwa taci
gaba da tafiya, kulum school bus ke zuwa d’aukan Indo
ya dawo da ita. Sannu a hankali sun shaku dasu Sanah da
Sadeey, anan ne ma take sani asai Sanah yar gidan
bababn Malaman nan ne mai wa’azin biki da gyaran
Amare. Sai Sadeey kuma gurin gayu ba’a barta a baya ba.
Niko Rash nace”lalle abun yayi wato kaya, ya tsinke a
gaban mai kaba. Aisha ta soma kilewa, duk da haka ita
take aiki a gidan Falmi, ko kad’an bata nuna gajiyawarta,
Haiydar ko ya saba da girkinta duk randa bata gida, ko ya
je Hotel baya iya cin abincin su. Indo ko mungun kama
kanta take bata bari ma ya ganta bare ya nimi takura
mata. Falmi ko bala’in yau da ban nagobe da ban,
Meesha lurv da Zarah BB sun bata shawaran ta kama
kanta, ta fita hark’ar Indo tak’i, sabida duk randa Indo ta
waye sai ta gane KUSKURENTA amma fir taki, tana bin
shawaran mugayen k’awayenta, hakan yasaka suka zuba
mata ido. *DEDICATED TO* *AISHA MUHAMMAD* *
(MAMAN ABDUL SHAKUR)* *RASH KARDAM * [2:32PM,
9/14/2016] Rash Kardam: [7/7/2016]Rash Kardam
BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA daga www.hausaebooks.com.ng NA ©RASHEEDAH .A.
KARDAM. Pg-177~179. Rayuwan Indo haka yaci gaba da
tafiya, tana zuwa makaranta. Sun had’a kai da su Sanah
da Sadeey, da zamansu ta ga na da kyau, bata b’oye
musu komai na rayuwanta ba, ta fad’amusu. Sanah tace”
mukuma zamu bada tamu gudumawar gurin ganin kin
gyaru. Sadeey ita ta dage gun koya mata k’waliayar
zamani, Sanah kuma gyaran jiki, hatta yanda Indo zatayi
tafiya saida suka koya mata. Bayan kwana biyu suka zo
mata da form d’in makarantar kwaliya ta cika, da kanta
ta biya kud’in kasancewar tana samu ‘yan kud’i, a haka ta
fara zuwa. Hajiya ganin jarabawan Indo yayi kyau hakan
yasaka ta bata motarta, ranar da Falmi tasamu labari
kamar zatayi hauka a gidan, don saida Hajiya ta tsayar
mata ita da Aliyu, don motar Falmi bai kai na Indo ba.
Sanah suna hira da Sadeey da Indo, Sadeey tace”Indo
gaskiya ni bana son ana kiranki, da Indo nan sai kace yar
kauye. Sanah tace”kamar kina raina. “Shawara daga yau
duk wanda yace miki Indo, in ba wanda kike jin
kunyarsa bane karki amsa. Tun daga ranar sunan Indo
ya b’ata yakoma Aisha, nima Rash nace” daga yau na
daina cewa Indo sai Aishat.********* 2yrs later Wata
k’yak’yawan budurwa na hango, tana fitowa da ga cikin
gida ta na k’ok’arin bud’e motar ta, mai k’irar RANGE
ROVER, sanye take cikin wani doguwar riga ya d’an
kamata daga sama, sai d’an k’aramin cikinta dake a shafe
ya fito. Hakan shi zai baka daman gane irin halittan da
ubangiji ya mata, harta shiga mota ko mai ta tuna cikin
damuwa tace”oh shirt! Da sauri ta fito ta nufi hanyan
cikin gidan, gudu-gudu sauri sauri, sam bata ankara da
wanda ke fitowa ba, sai jin garam sunyi karo da mutum.
Ko ta nuna alamar damuw ta d’ago kai tare da d’an zaro
gilashin dake idota, sai da ta d’an rausaya ido, ta wani
kashe murya tace”oh i’m sorry! you guy. Bata jira amsan
shi ba ta sakai ta wuce abunta, Haiydar da tsananin
mamaki kasa motsi yayi, shafa ida ta buge sa yayi,
haryanzu dadda d’an k’amshin ta yana tashi. Wani yawu
ya

Please Login or Register in order to submit comment