Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

d’au
k’una yana mata rad’ad’i. Gashi Hajiya Firdausi tace”ta
hak’ura boka yace, suna da nasara tunda yar aiki ce.
“Kuma Haiydar ya tsaneta Falmi yake matuk’ar qauna, a
zuciyansa. “Kuma bazai tab’a sin Indo ba. A gidan Hajiya
kuwa yau akaje akayi jere ma Indo, d’an kayan rufin asiri
suka mata bak’arya, side d’inta ita d’aya da d’aki biyu, sai
kitchen da store. Komai yaji dai-dai, gidam kam ya tsaru
ba laifi, don a tsakar gidan ga swimming pool, ga garden,
da wajan wasani abun gwanin nurgewa. Yautake Alhamis
duk inda ka leka a gidan su Haiydar, anata kamu ne,
kawayen amarya sunsha kyau, suna sanye cikin wani
material baki da ash colour, sunyi kyau sosai, sai da aka
debi mutane tukun aka kawo wata k’atuwar Jeep ciki za’a
d’au amarya. Niko Rash zuba ido nake inga fitowar
wannan amarya mai ji da kyau. Mutane naga suna ta
d’aukar hoto, da sauri na mik’e, ina zuwa kuwa na hango
amarya cikin kayanta, less ne dark ash da silver colour,
ohohoho masu k’aratu, gaskiya in baku ga Indo a
wannan rana ba, to kalo ya wuceku, don da kyar na iya
gane cewa Indo ne, yar wanke- wanke da shara, don yau
inda Falmi zata ganta, inaga sai zuciyarta ya buga. Cikin
takun nutsuwa su Hasna da Pinky suka rike hannuta,
yayin da Cutie ke gabansu, har suka isa mota. Larema
hotel sukaje, gurin ya tsaru sai wanda ya gani, a cikin
kwanciyan hankali aka gudanar da komai, Sadiq wasu
abikan ango suka kirasa suna yabamasa irin tsabin da su
Hajiya suka masa, gaskiya tayi bana wasa bace. Shiko
haushi suka basa ma, ana haka har aka kammala kamu,
suka dawo gida cike da murna, kasancewan gidansu
Haiydar na da girma side guda aka bama yan biki, basa
ta cikin gidan side d’insu daban. Hajiya ce ta kira
Haiydar, bayan yazo ta masa nasiha sosai, gameda rike
mata biyu, Hajiya tace”Haiydar na sanka da zafin zuciya
ka k’ara hak’uri da halin Fatima. “Don rashin kunya da
kishi suna damunta, amma dan Allah kayi hak’uri. Sai da
sukayi hira sosai yace”zai tafi a kwai wanda suke jiransa,
ya mik’e ya fito. Hasna ko sun dawo sallah sukayi nan
suka soma hiran yanda biki ya kasance, Hasna ta mik’e
barinje na karbo mana sakon da Aunty Rahma ta bari.
Shiru- shiru Hasna bata dawo ba, hakan ya sa Falmi ta
mik’e don taje gun Hajiya taji ko tananan, kanta ko d’an
kwali babu, gashi yasha gyara, gashinan yazubo har
gadon bayanta, cikin karai-raiya take tafiya mai d’aukan
hankali. Tazo dai-dai corridor d’akin Hajiya aka d’auke
wuta, laluben hanya ta fara tana kiran sunan Hasna, sam
bata lura da mutum yana tahowa ba, sai ji tayi ta
rungumi mutum, cikin tsoro da ta gudu, Haiydar dake ya
ganeta, sai ya tsinci kansa da kara rungumeta, harda
sakin ahiyan zuciya. Duk jikin Indo ya d’au bari, ga
k’amshin turarensa ta cikata, da sauri da sauri k’irjin
Haiydar ke bugawa, hannusa d’aya, ya sanya cikin
gashinta yana wasa dashi, cikin zuciyarsa ko cewa
yake”duk da gashin Falmi amma Indo ta fita sosai.
Sunkuyo da kansa yayi dai-dai hab’arta, ya tallabo, yana
mai kalon fiskanta duk da duhun da ke gun, d’an
k’aramin bakinta nan ne ya burgesa, bakinsa ya kai kusa
danata kenan, Nepa ne suka kawo wuta dai-dai lokacin
take wajan ya gauraye da haske, ni Rash ina d’aga kaina
wa zan gani…….. Sai kunji ni gobe in dama tasamu, in
kuma bansamu yin typing ba, sai bayan Sallah in Allah ya
kaimu. Taku a kulum mai qaunarku Rasheedah Abdullahi
Kardam DEDICATED TO AISHA MUHAMMAD (MAMAN
ABDUL SHAKUR) RASH KARDAM [2:32PM, 9/14/2016]
Rash Kardam: BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA daga www.hausaebooks.com.ng NA
©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-126~130. Haskene ya
mamaye ko ina nacikin corridor d’in, da sauri ya kali
fuskan Indo hawaye ke sauka, yana d’aga kai yaga Husna
tsaye zata fito daga d’akin Hajiya. Take ya ji haushin
kanshi, cikin zuciyarsa ko cewa yake”wai me ke shirin
faruwa dani ne?. Hannusa da ke rike da Indo yayi saurin
tunkud’ata, sai data kai har kasa ya tsata mata yawu,
Hasna kuwa wani mugun harara ya wurga mata, wanda
yasata komawa d’aki bashiri jikinta harna b’ari, don ta
san halin Haiydar in ransa ya b’aci bayida sauki. Sai da
taji ya banko qofa alamun ya fita, kafin ta fito da sauri
tayi gun Indo, ta kamata ta d’agota tace”Aunty na dan
Allah kiyi hak’uri da halin Ya Haiydar. “Watarana sai
labari kinji. “Kuma ga dukkan alamu ya Haiydar na sonki
amma shi kansa bai san haka ba. Indo kam in banda
hawaye ba abunda takeyi, haka har suka koma cikin
d’akin, Indo kaya ta cire tasaka na bacci ta kwanta,
amma sam ba bacin take ba, sai tunanin irin wulakancin
da Haiydar ya mata. Wata zuciya tace”Indo ina ke ina
Haiydar. “Inake ina iya kishi da Falmi ko kin manta
suwaye Falmi?. “Ke fa ba kowa bace face yar aikin
gidansu. “Marar asali bakida gatan ki sai Allah. “Bakisan
kowa ba. Wani zuciya kuma yace”a kul d’inki Indo,
guduwa ba naki bane. “Kina d’iya mace kinsan inda zakije
ne?. “Ta iya yuwa kije gunda za’a b’ata miki rayuwanki.
“Kawai dai ki hak’ura har Haiydar ya gaji ya sakeki. Ajiyar
zuciya ta sauke tare da k’ara lumshe idonta, tare da tuna
abunda ya faru dazu. Washe gari da safe, aka tashi da
aiki sosai, don ranane ran d’aurin aure. Abba saida ya
yanka saniya, Hajiya ko baki har kuni, don murna. K’arfe
d’aya da rabi bayan Sallah jumma’a dubban mutane
suka sai da d’aurin auren Aisha Muhammad da agonta
Aliyu Khaleed Baba(AK Baba) da Amaryansa Aisha
Muhammad(Indo). Akan sadaki naira dubu sitin 60k.
Bayan d’aurin aure ne, jama’a suka wuce Sogiji Hotel
don gudanar da Waliha, duk wanda yaje gun yaci ya sha,
sai fatan Allah ya basu zaman lafiya, tare da k’azantan
d’aki. Haiydar tun daga nesa na hango shi, cikin fararen
shadda da gare, ya matuk’ar yin kyau tamkar bashi ba,
fiskan nan tashi ba yabo ba fallasa, duk yanda naso in
gane wani abu, amma dul yanda naso na kasa tan-tace,
yau farin ciki yakeyi ko bakin ciki. Haka suka kammala
kowa ya kama gabansa. Ango ko ya nufi sabon gidansa,
inda Falmi da kyar ta koma, don cewarta ita sai dai ya
barta ita kad’ai, da kyar ya lallab’a ta takoma, sai da ya
zuba mata kud’i masu yawa kafin ta yarda ta koma.
DEDICATED TO AISHA MUHAMMAD (MAMAN ABDUL
SHAKUR) RASH LUV 6/3/2016] Rash Kardam BABBAN
KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM.
Pg-131~135. Haiydar sai bayan la’asar ya nufi gida, tun a
falon Falmi yaji muryan yan’uwanta, sai ya fasa shiga
d’akinsa ya nufa ya cire manyan kayan, ya shiga bayi ya
watsa ruwa, yana fitowa ya tsane jikinsa ya saka kaya
maras nauyi don ba inda zai je. Kwanciya yayi ya d’auko
wayarsa Falmi ya kira, wayar sai ringing takeyi amma
taki dagawa, don wani masifan haushinsa takeji kamar
tayi hauka. Nasiba tace”Falmi ki d’auka kiji mai ze ce
miki, ai yanzu ne lokacin da zaki zuba mulkinki son ranki
a gidan nan. Kowa da kalan nata munanan shawaran,
Falmi ta d’aga wayar tace”hello ina jinka. Cikin isa take
maganar, Haiydar yace”My Luv bazakizo ki ga lafiyata
ba?. “Gani sai tunaninki nakeyi nakasa samun sukuni.
“Mtssss to mai zan maka bacin ga amaryanka ba sai kaje
gunta ba. “Ai tana da abunda kake buk’ata sai ta baka.
Kawshe wayar tayi suka tafa tare da shewa, Nasiba
tace”shawaran da zan baki duk yanda zakisan yanda
zakiyi kar ki bari yaje gun dinner nan. Falmi tace”Nasy
taya zan hana shi zuwa gun dinner?. “Mtsss haba Falmi
sai kace ke ba mace ba. “Kisan duk wani hanyan
danzakibi ki hana sa zuwa. Nuwairay tace”kin san mai
zakiyi Falmi. Cike da k’osawa tace a’a. Nuwairat tace”
yanzu in ya sake kiranki ki d’auka ki gwada masa kin
sauko, amma kice kina tare da baki, ya d’an jiraki. “Sai ki
bari dab da magriba kiyi kwaliya ki tafi d’akinsa, kar ki
bari ko sallah isha’i ya fita waje. “Ki nuna masa salonki ki
kuma nuna masa kina da buk’atarsa yanzu, ko da kunyi
ki nuna bai ishe kiba, kin ga ai dole bai son bacin ranki
dole ya hak’ura. Shewa sukayi da tafawa Nasy
tace”shegiyar kin kawo idea fa. Ana haka ko sai ga kiran
Haiydar haka Falmi ta d’auka ta rinka fad’amasa kalamai
masu dad’i, tace”Honey ina tare da baki barin sallamesu
zanzo mu gaisa. Ko da ankira magriba karka fita kayi a
gida, ko in kaje ka dawo ka jiran zamuyi magana.
Haiydar cike da murna ya amsa mata da”ba komai ni yau
ji nake kamar nafi kowa farin cikin, tunda kin bar fushi
dani. Haka sukayita hira daga k’arshe sukayi sallama. A
gidan Hajiya ko bayan d’aurin aure, da yamma walima
suka shirya na gani na fad’a, komai cas-cas, akayi walima
aka tashi, da daddare kuma zasuyi dinner. Tun bayan
sallah magriba suka soma shirin dinner, amarya na
hango cikin fafaren net yayi matuk’ar yi mata kyau. Abun
gwanin burgewa, ana kiran Sallah isha’i sukayi sallah
suna jiran zuwan angwaye. Falmi bayan sallah magriba
wanka tayi na musamman ta sanya wani riga iya gwiwa,
daga gefen cinyan a tsage yake, bata sanya bra ba, duk
wani sassan jikinta kana gani. Kayan sun haska jikinta
dake fara ne, dai-dai lokacin Haiydar ya fito daga wanka
d’aure yake da towel, ganin falmi da sauri ya k’araso
gunta, janta jikinsa yayi, yace”Honey nayi misin d’inki
kwana biyu. Hannuta tasa tafara wasa da sajensa da ya
kwanta luf-luf gwanin burgewa, cakul-kuli tasoma masa,
dariya yayi yace”wato yau tsokana kikeji ko?. Hannu ta
kai tasoma ware towel d’in da ke jikintsa, wasa yasoma yi
da gashin kanta, ganin tsayuwa ba zai d’aukesuba ya
d’auketa cak sai kan gado, yasoma mata wasani sai da
abu yayi nisa Falmi tasoma jan jikinta, komai ta tuna ta
tashi zata mik’e, ya kamo hannuta cikin dashashiyar
murya yace”Honey miye haka? “Kinsan ina tsananin
buk’atarki a wannan lokacin. Wani banzan kalo ta wurga
masa da niyar mikewa ta fita, cikin azama ya diro tare da
kaimata wani kyakyawan cafka. DEDICATED TO AISHA
MUHAMMAD (MAMAN ABDUL SHAKUR). RASH KARDAM
[2:32PM, 9/14/2016] Rash Kardam: BABBAN KUSKEREN
DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM.
Pg-136~140. Cikin hanzari ya kaimata cafka, yayi sa’an
riketa, Falmi tayi ta kwace takasa, kuka tasoma masa duk
ya rikice, sakowa yayi ya mata nil down ya riko hannuta
yace”haba Falmi na mai na miki kike hukuntani ta
wannan hanyan?. “Shin kaki tsoron kamun Allah Falmi?.
“Kisani ko dai-dai da seconds daya kika tutarni a wannan
harka Allah zai saka min. “Kulum cikin azarbtar dani
kikeyi Falmi. “Ko so kike in fara bin matan banza. Wani
kalon ko oho ta aika masa cikin muryan kuka tace”Aliyu
in ka ga dama ka kama d’aki a bayan gari ba ruwana.
“Kasani da *KISHIYAR GIDA GWARA TA WAJE* na tsani in
gani da wata matsayin matarka. cikin kuka tace” ni daka
auro min Indo gwara ka ringa bin mata a wa…. Bata
k’arasa ba taji saukar lafiyayen mari a fuskanta, cikin
huci yace”Falmi asai baki da hankali?. “Asai bakisan mai
kikeyi ba?. “Tabbas na yarda bakisan ciwon kanki ba.
“Kinga ina lallab’aki ko don kibani hakkina. “To wallahi ta
karfi zan ringa karb’a yanzu, banza kawai. Falmi ba
k’aramin tsorata tayi da yanayin Haiydar ba, qofar d’akin
yaje ya zate key d’in ta sanya a saman Waldrop d’insa, ya
suma bin Falmi tana hawaye suka soma kokawa da kyar
Haiydar ya samu ya wurgata kan gado, Falmi ta fara ihu,
kamar k’araman yarinya, cikin b’acin rai yace”keee baki
da hankali ko? “Yau ko a gaban wakike sai na karb’i
hakkina, Haiydar da iya karfin sa ya zage yake abunda
yakeso. Niko Rash ina ganin haka na tattaro yan matan
kafata na fito. Su Indo sun gama shiryawa shiru ba
labarin ango, har an kai wasu a mare cikin *LAREMA
HOTEL* anan za’ayi dinner, ya rage daga cutie sai Hasna
da pinky suma yanzu saurayin Pinky Nura yazo
d’aukarta, sai Hasna da Cutie Sadiq zai tafi dasu. Ana
haka saiga Haugal ta iso ita da Ghalinta,(masu karatu ina
fatan baku manta da Haughal ba ko?. Nacikin litafin
*BAZATA*). Ghali yaje gunsu Sadiq yace”wai ina Man d’in
ya shiga ne?. “Tun zamu taho nake ta kiran wayansa bai
d’aga ba. Sadiq yace”wallahi muma hakane amma bari
zamuje gidansa muduba shi, daga nan sai mu wuce.
Jiddah da sallama ta shiga gidan, da su Hasna ta gamu da
su, cikin girmamawa Hasna tace”lah! Aunty Jiddah kin
isone? “Jiddah tace”eh yanzu muka zo. “Hasna tace”ina
Uncle Ghalin”yana waje yanzu zanje muwuce kenan.
Jiddah tazo kusa da Indo tace”amaryan mu kinsha kyau
bari mu fara gaba sai kun iso. Indo murmushi ta iya
mata don tana gabda yin hawaye, sabida tasan daman
Haiydar ya tsaneta wahala zatasha ba kad’anba. Haughal
ta fita zuwa gun Ghali don su wuce gun dinner. Sadiq
yace”Ghali bari muje gidansa kawai mu duba sai muga
ko lafiya ne. Ghali yace”ok hakan za’ayi. Sadiq ya kira
Hasna yace”ku fito da amaryan kawai mu wuce. Da kyar
Indo ta fito don hawaye take amma sai kalura ka gane
hakan, suka sakata a motar da za’a kaita Cutie a da Hasna
motar Sadiq Hasna ce a gaba sai cutie a baya. Pinky
kuma Ya Nuranta. DEDICATED TO AISHA MUHAMMAD
(MAMAN ABDUL SHAKUR) RASH KARDAM [6/3/2016]
Rash Kardam BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA daga www.hausaebooks.com.ng NA
©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-141~145. Suka d’au
hanyan gidan sa, Indo ko in banda hawayen takaici babu
abunda takeyi, tana rokon Allah ya kawo mata d’auki a
rayuwanta. Haiydar ko bai kyale Falmi sai da ya tabbatar
ya gamsu sosai, ya mike ya shiga wanka. Bayan ya fito
yayi Sallah isha’i kenan ya d’auko wayarsa, mai zai gani
60miss call na Hajiya 20 na Sadiq 46, sai na Ghali da
wasu abokansa, sam ya manta da zasuje dinner sai a
lokacin ya tuna, cikin hanzari yasa d’anyar boyal d’insa
mai ji da shek’i, ya kawo agogon hannu ya d’aura ya
sanya takalminsa, ya d’auko hularsa itama fara yazo
gaban miro ya na d’aurawa, Falmi dake kwace jiki ba
k’arfi ta mike cikin zuciyarta ko cewa take”nayi ma kaina
gashi ban hanasa zuwa dinner ba, gashi ya gurjeni son
ransa amma dole na b’ata kwaliyan nan kuma bazaije ba.
Tana d’ingisawa tazo ta tare qofan fita Haiydar ya gama
shiryawa yazo zai wuce tace”baka isa ba yau kaje dinner
auren wata marar asali. “Yar titi kuma tsintaciyar mage
bazai yuwu ba. Haiydar yace”kiyi hak’uri ana jira na
kuma kinga mutane sunzo doni ne. “Ni badan Yar aiki
zanije ba. “Sabida mutanen da suka taru domin ni zanje
in fita kunya. “Falmi kinsan ina matuk’ar qaunanki. Falmi
tace”k’arya ne *MAYAUDARI* maha inci kawai. “Da kana
sona bazaka yarda ka auri Indo Yar aiki na ba. “Haydar
yau ko ni ko kai don ba inda zakaje maci *AMANA*
kawai. “Ka kasa rike *AMANA TA* da iyayena suka baka.
Ganin zata b’ata mishi lokakaci ya d’auko key zai bud’e
qofa tazo ta rike hannu qofar. Ganin bata da nutsuwa a
tare da ita, kuma ya mata magana duk taki fahimta.
Wata zuciya tace”bata k’yak’yawan mari zata fi fahimtan
wannan yaren. Sai da ya gyara hannusa ya bata lafiyayen
mari, take Falmi takoma gefe don sai dataga wasu Stars
suna mata shining. Haiydar ya bud’e qofa har yafito
harabar gidan yana shirin sanya k’afarsa waje kenan, Sai
ga su Sadiq nan suka fara tambayamsa lafiya?. Sadiq ya
fara masa surutu Haiydar yace”mutafi lokaci ya kure.
Yazo sai shiga mota kenan, Falmi ta fito da gudu ta rik’e
murfin motan tana cewa”yau ba inda zakuje indai
inanan. “Alo tsiya alo danja ba mai fita da kai. Cikin
takaici ya tureta ya rufe motar. Falmi batayi k’asa a
gwiwa ba ta je ta tatare gaban motar tabaje tana
cewa”yau sai dai in ta kaina zakubi ku fita ehe. “Sai ku
kasheni in huta. Haiydar bai ma lura da Indo da take gefe
tana hawaye ba. Takaici duk ya ishesa da kunya, gashi a
gaban abokansa. Sadiq ya mata Horn amma taki
matsawa sai ihun da take kurma musu kamar masu
satan mutane. Cikin zafin rai Haiydar ya bud’e qofar
mota. Ga d’an wannan ina samu lokaci zakujini da
daddare in nasamu lokaci, in bansamu ba kuwa sai
bayan *SALLAH* In Allah ya kaimu da rai da lafiya.
DEDICATED TO AISHA MUHAMMAD (MAMAN ABDUL
SHAKUR). RASH KARDAM [2:32PM, 9/14/2016] Rash
Kardam: BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA daga www.hausaebooks.com.ng NA
©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-146~150. Sam Haiydar
bai ma lura da Indo, da take gefe tana sharan k’wala ba.
Sadiq ya mata horn amma Falmi taki matsawa, sai ihu
take musu kamar wacce tayi hauka. Cikin zafin rai da
qunar zuciya Haiydar ya bud’e murfin motan ya nufota,
kasancewan gidan da hasken k’oyayen wuta, yasa ta ga
Haiydar ya nufota. Sai data ga ya kusa da ita da sauri ta
mik’e taje jikin motar ta bud’e side din da Indo take, ta
soma shiga duk ta buge indo ta ture ta, tana shirin haye
kanta ta zauna ne Haiydar ya finciko ta, cak ya d’agata
tana turjewa sai da ya kaita dakinta, yasaka key ya fito.
Duk ta ya mutsa masa kayan jikinsa. Takaici goma da
ishirin ya had’u masa, zuciyar sa sai rad’ad’i take masa
tamkar zata fito waje. Ji yake ina ma da zai iya kuka,
tabbas da yaji sassaucin zafin da zuciyar sa ke masa. Da
k’yar ya janyo k’afarsa ya shiga mota, sai a lokacin ya
lura da Indo da ta had’a kai da gwiwa tana rusan kuka.
Nan yaji wani sabon bak’in ciki ya tur nukesa. Shi kenan
shikan yazu ya rasa farin cikinsa, ga auren yar aiki, ga
Falmi ta rikice masa. Bai san lokacin da yasaki wani tsaki
mai k’arfi ba. Haka aka ja motar duk da sun makara,
suka nufi gun dinner, mutane har sun soma tafiya, MC
ya fara magana da ayi a hakuri, a zauna ga ango sun iso.
Sai da abokai suka shiga, ya rage daga Ghali sai Jiddah da
Sadiq da Hasna, Su zasu shigo da Amarya da Ango.
Amarya da Ango a gaba, sai abokai a bayansu, bayanda
Ghali baiyi ba akan Haiydar ya rike hannuta fir yaki.
Harda d’an matsawa gefe, ya bar tazara a tsakaninsu.
Jidda ta jawo Ghali tace maasa” kasan me kai ka dawo
gefen Ango, ni zan dawo gefen Amarya, in munzo dai-dai
qofar shiga ka d’an ta kurasa. In hanyar yaji ya takura,
dole zai matsa ya mannu da Amaryan. Hasna kuma saita
san yanda zatayi, ta manna hannusu guri guda, nasan ba
haufi zai rike hannuta. Aiko haka akayi Jiddah ta cike gu,
wanda yasaka Indo matsawa kusa da Ango, shi ma haka
Ghali ya masa, dai-dai lokacin DJ ya sake musu kidan
Loakcin kine yayi Amarya yar *AMANA*. Kasancewar
Haiydar na son wak’ar, bai san lokacin da ya saki
lallausar murmushi, wani farin ciki ya ratsa zuciyarsa,
yasoma bin wak’ar a hankali. Hasna ko hannu Indo ta
kama ta d’aura kanna Haiydar. Take yaji wani sanyin dadi
ya ratsa zuciyarsa, sai ya samu kansa da k’ara rik’e
hannun. Ya d’an janyota jikinsa, sabida laushin fatarta da
kanshim da ke tashi a jikinta, ya mantar da shi da wa ma
yake tare. Indo ko sai niman zillewa take, don tun da
take in banda ranar da suka dawo daga gidansu Haiydar
yayi hug d’inta sai ranar walima, namiji bai taba mata
irin wanann rikon ba, sai yau. Shiko sai janyota yakeyi
cikin jikinsa. Masu k’aratu karkuga yanda suka burge,
suna sanya k’a farsu cikin Hall d’in, masu d’aukar photo
suka fara, Jiddah tace”ma Hasna bari kuga next target
d’in mu. Hasna yi sauri ki d’an zo kusa da Aisha, kin ga ta
kalminta na da tsayi, ki d’an samata k’afa kamar zata
fad’in, zai taro ta tunda kinga rabin jikinta ansa yake, ba
zai bari ta fad’i ba. Ina son ayi shooting d’insu a haka don
ya isa gun Falmi, ni kuma zan d’aukesu da IPhone d’ina.
Sai ki tutura masa a wayansa. Hasna ta d’aga ma Jiddah
hannu, ta sara mata alamar target d’in yayi. Hasna ta yi
saurin sanya ma Aisha Indo k’afa sai gata zata fad’i, da
sauri Haiydar ya tarota, ya rik’ota duk gaba d’aya ajikinsa
take, ita kuma ta rufe ido ta sadak’ar fad’uwa zatayi,
shiko kallonta yakeyi, da d’an k’aramin bakinta nan, mai
d’aukar hankali. Sam ya manta ida suke, sai ji yayi ya
samu kansa da yi mata kiss a lab’en bakinta. Haiydar sai
da ya wani lumshe ido, azuciyar shi ko cewa yake”tabbas
mata suna suka tara. Don kiss d’in da yayi ma Indo, wani
laushi yaji a leb’en bakinta, ga k’amshi gamida zaki.
Jama’an da suke hall d’in, abun ba k’aramin burgesu yayi
ba, take suka saka sowa da ihu. Masu camera kuwa suna
kan aikinsu, haka Jiddah ma ta d’aukomai harda yin
editing. Abun sai wanda ya gani, Don ko ni Rash sun
burgeni, amma ina tunani photo nan in ya isa gun Falmi
da k’aramar yaki. Haiydar cak ya d’aga Indo, bai ajiyeta
ko ina ba, sai kan kujeran da aka musu mazauni, ya
sak’aka hannusa cikin nata. Hasna da Jiddah ko sai
murna suke, don ba wanda zai gane cewa Haiydar ba
son Indo yake ba, niko Rash na tab’a k’awata Lovely
Aisha Mazoji nace”Lovely kin ga kirsan mata ko, da kirsa
da dabara Jiddah tasa Haiydar ya manta k’iyaya, ya
shagala da soyayya. Aisha Mazoji tace”taya ni gani kam,
kuma in an tab’ashi, ya iya kurin baya son bak’ar mace,
sai gulmar tsiya. “Kiga yanzu a gaban mu harda mata kiss
fa. Nace”hmm kedai bari kawai zamuga yanda wannan
drama zai k’are. *DEDICATED TO* *AISHA MUHAMMAD*
*(MAMAN ABDUL SHAKUR)* *RASH KARDAM *
[7/4/2016] Rash Kardam BABBAN KUSKEREN DANA
TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-151~155. Haka
aka gudanar da dinner kowa cike da farin ciki, Haiydar
kam tun da ya rike hannu Indo ya kasa saki. Sai da aka
gama taro suna sauk’owa Sadiq ya kasa hakuri yazo kusa
dashi, yace”ASP Aliyu Khaleed Baba. Sai da Haiydar yayi
murmushi yace”Haka sunan yake A.K Baba. Sadiq ya
cigaba da cewa “gaskiya yau naga lurv, wato wannan kiss
d’in ma duk acikin kiyayyar ne ko?. “Da tsanar bak’ar
mace. Sadiq yana wani shu’umin dariya Hasna da ke gefe
itama dariyan tafara, sai alokacin Haiydar ya dawo
hayyacinsa, ko kalon gunda Indo take baiyiba, ya tureta
wanda k’ad’an ya rage ta fad’i, Hasna ta taro ta. Ghali
yace”kaga Man d’in nan kora kunya da hauka zaka mana.
Ko sauraronsu baiyi ba ya nufi mota. Indo ko daman
atakure take don tayi hawayen har ta gaji, ba wanda ta
bari ya gane kuka take, ta b’oye har aka gama taro.
Hasna ta rikota, tazo zata sata motar da suka zo, Haiydar
ya daka mata tsawa”kee ina wasa dake ne?. “Ni sa’anki
ne?. Sadiq ya iso gunsu yace”mai kake nufi ne?. “Da wani
mota kakeso tashiga?. Cikin harzuk’a Haiydar yace”in dai
zata shiga motar nan sai dai in koma a qafa. Gannin
yanda ya yake masifa, yasa Sadiq ko magana bai
k’aramasa ba, Yace”Hasna kushiga mota in mai daku
gida. Hasna ta rik’o hannu Indo suka shiga mota sai gida.
Haiydar ko kansa ya jawo ya dawo gida. Ransu Ghali ya
baci sun bar masa motan suka tafi. Ko da ya dawo gida
dakinsa ya nufa ya kwanta, baibi ta kan Falmi ba, bare
yaja ma kansa magana. Washe gari a harabar gidansu
aka shirya crossing sword, police ne suka sha kakinsu da
mopol, sai wasu friends d’insa yan *WAI BURGET* su
kuma sun sanya kaya Green white green. Abun dai sai
wanda ya gani. Police sun cire yan Colour paty da yan
Sub gard n gard Commander. Haka yan WAI ma. Ba
abunda ke tashi a filim sai kid’an Band, har wata yar
waka suke musu, da busa mai dad’in sauraro. Amarya na
hango cikin shigar cut less mai kalar blue da baki, sai
handbag da takalmi blue da baki. Ta sha gwagwaro tayi
kyau sosai da sosai. B’ab garen Falmi ko dak’yar su
Meesha lurv da Xhara BB, su tursasata tasaka less light
pink, gata fara bai mata wani kyauba. Fir taki tsayawa
tayi make-up, duk kishi ya dameta. Ta dauro d’an kwali
suka fito, gun Haiydar suka nufa, sai wani harara take
aika masa, in ta ga Hasna ko ji take kamar ta shak’eta.
Ana ahaka akace Amarya da Ango da Uwargida su fito
za’ayi Inspection kafin a fara gabatarda bikin. Haiydar ne
yazo dai- dai inda Falmi take yariko hannuta. Sai k’ok’arin
fisgewa take, yace”kinga mutane a nan gwamma ki tsaya.
Tsaki tayi masa ta kauda kanta gefe. Ana haka sai ga
Jiddah da Hasna sun riko hannu Indo, ae take kalo ya
koma kanta, don hatta mazan da ke gun sun yaba da
tsarin kwaliyarta. Cikin nutsuwa take takawa, Haiydar tun
da ya d’aga ido ya kalleta, ya kasa d’auke kai yarasa mai
yasa duk lokacin da ya kalleta, sai yaji wani abu gameda
ita. Sam ya shagala da kallonta, sai da Falmi ta
mutsunesa ya dawo hayyacinsa. Hasna ta saka Indo a
gefen damansa, yayin da Falmi ke hagunsa. Wasu police
ne biyu da wuk’a a hannusu sai shek’i take suka mik’e,
tare da sarawa da buga k’afarsu a k’asa. Ba tare da b’ata
lokaciba masu band suka saki kid’an taken k’asarmu
*NIGERIA*. Duk wanda suke gurin saida suka mik’e
tsaye, tare da kame domin girmama qasarmu. Cikin
busa mai dadi, akayi kidan National anthem, yayi da
mutane ke bin sautin kidan har aka gama. Mutanen dake
gun suka saka tafi raf-raf. Aka zauna nan masu band
suka cigabada bugawa, ni da lovely na munsaki baki sai
kalo muke, nan wayan nan police biyun nan suka soma
paret, suka iso har gabansu Haiydar suka sara masa,
tukunan su juya tare da buga kafa, sukayi masauni a
gabansu. Anan masu kaya kalan green white green suma
suka fito, bayansu Haiydar suka tsaya . Karan kidan ya
fara tashi da k’arfi. Take suka soma zaga filin da paret, in
gun manyan Haiydar suka je, sai ya sara musu in
k’ananan sane, su sara masa. Masu camera sai d’aukarsu
sukeyi. Sai da suka zaga ko ina, kafin suka zo suka zaun.
Gard d’in police suka fara wucewa, suna parret suna
zuwa gun Haiydar da iyalansa, sai su sara masa. Sai da
police suka gama nasu kafin yan *WAI BURGET* suka
faso karkuso kuga ihu da sowa, don yanda suke gudanar
da parret d’indu, da tsarin komai abun burgewa ne.
Fatyma S.Y itace parret commoder, yayi da Farida Jigides
take yan colour patty. Gaskiya abun ya k’awatu sai
wanda suka gani. Sai da aka gama parret tukun masu
mik’a musu gifts suka taso. *DEDICATED TO* *AISHA
MUHAMMAD* *(MAMAN ABDUL SHAKUR)* *RASH LUV *
[2:32PM, 9/14/2016] Rash

Please Login or Register in order to submit comment