Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bakwai Hajiya Firdausi tace”yanzu sai
ki maye gurbi Uwarki da aikin da kike ko kuma kisan
inda dare ya miki. DEDICATED TO AISHA MUHAMMAD
(MAMAN ABDUL SHAKUR) RASH LUV [5/27/2016] Rash
Kardam BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA daga www.hausaebooks.com.ng NA
©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-41~45. Aisha Indo ba
yanda ta iya, haka taci gaba da aiki a gidan, Hajiya da
kanta ta rage mata Salary zuwa 7k, hakan yasa bazata iya
d’aukan nauyin, karatunta ba ta hak’ura. Aliyi Khaleed
Baba, tun randa yaga Falmi ya rasa nutsuwarsa,
kasancewan ya ganta irin matar da yakeso, gata fara sol,
don shi tsarinsa bai son bak’ar mace. Masu karatu
zamuso sanin, WAYE ALIYU KHALEED BABA(AK BABA).
Alhaji Khaleed Baba asalin d’an Bauchi ne shi, cikin
k’aramar hukuman Sakuwa, dake garin Misau. Yata so
cikin garun Bauchi yana aiki a kar-kashin Treasuring a
yawon aikisa yaje garin Gombe suka had’u da Hajiya
Khairat wanda take da zama a garin Gombe. A haka akayi
auresu da Alhaji Khaleed ya d’aukota suka dawo cikin
garin Bauchi, Suna da zama a State Low cost, bayan
aurensu Allah ya azurta su da d’a Aliyu, sai da Aliyi ya
girma sosai kusan shekara 12 kafin aka Haifi k’anwarsa
Hasna. Wanda yanzu itace auta. Wanan kenan bari mu
dawo labari. Haiydar yakasa hak’uri takanas yazo gidan
su Falmi, tun daga ranar suka sasanta kansu. Soyayya
mai k’arfi tashiga tsakaninsu. Kusan kulum suna tare da
juna, wata rana yazo gun Falmi tun daga nesa yaga,
Aisha zata shiga gidan sam bata lura dashiba, horn ya
mata sosai don tayi nisa cikin tunani. Sai da ya taka burki
ya fito ya fara zazaga mata masifa. Ko da Falmi tadawo ta
ga sai huci yakeyi, tace”My Haiydar mai ya faru haka?.
Nan ya fad’a mata laifin da yarinya tamasa. “Mtsss miye
na d’aga hankalunka, akan wannan yar shegen, da ba’a
san ubanta ba. “Uwarta tazo tayar mana ita. Nan taba ma
Haiydar kabarin komai harda k’arya aciki. Madadin
Haiydar ya tausaya mata sai yaji haushinta. Kwanaki sun
tafi, magabatan Haiydar sun zo ansaka ranar Aure wata
d’aya, sai shiri sukeyi, Falmi tasha gyara sosai, Falmi
kasancewar yar casu ne, event tashirya bana wasa ba,
tun daga rantalata suka fara event, har Friday idan nace
zan tsaya baku labari, events d’in bikin nan da yanda
komai ya kasance, charged d’in wayata zai d’auke, ban
gama shiba. Ranar Friday aka d’aura aure. Duk wani
abun al’ada anyishi, ranar yini da daddare abokai suka
raka ango, sai da sukayi yan barkwanci, kafin suka musu
sallama suka tafi. Haiydar ya rakasu ya dawo, Falmi tana
ganin ya dawo, tazo cikin shagwab’a tafad’a jikinsa,
azuciyar Haiydar kuwa cewa yake”wanna wata irin
Amarya ce ba kunya, amma sai ya share wata zuciya
tace”Son da take maka ne yasaka haka. Falmi bata bari
sukayi Sallah farinci da godiya ma Allah ba, ta fara aikin
sha- shafa Haiydar tare da masa wasu salo, Haiydar kasa
jurewa yayi ya d’auketa sai kan bed. Salon da ya mata, ya
rikitata ranar Falmi taji jiki, kasancewa ta kawo
budurcinta, Haiydar irin Mazan nane wanda zamu iya
cewa shi Hariji ne, a ranan sai da ya gurjeta sau uku. Da
safe sai da yayi wanka yayi Sallah kafin, yazo ya mata
wanka ya gama shiryata kena, wayarsa tayi k’ara ya
d’aga, ganin daga office ne, ya kara a kunnesa tare da
fad’in “Hello” daga d’aya b’an gare akace”Sir kazo
Commissioner ne yazo yana son ganika yanzu, akan wani
case d’in da’aka kawo. Ba yanda ya iya dole ya fita, Falmi
ko tunda taga 8:00 bai dawi ba, ga bedsheet d’in da suka
kwanta ya b’aci, ko yaye wa batayi ba. Waya ta d’auko ta
kira, Mum bayan sun gaisa tace”Mum ki turo min da
Indo zata min aiki. Mum tace”ke kina da glhankali kuwa?.
“Kice na turo miki Indo gidanki. Falmi tace”Mum Haiydar
bayanan ankirashi a gentle a gun aiki, gashi bana iya
tashi ne fa, kuma ban karya ba. Mum tana jin haka ta
gane sunyi abun garin, sai da tayi murmushi tace” gata
zuwa yanzu. Mum ta bama Indo kud’in mashine ta hau
tazo. Sai da ta mata girki ta jera mata, Falmi tace”kee jeki
d’akina ki yayi bed sheet d’in ki wanke. (Mata kira gareku,
ku kasance masu kiyaye duk wani abun da ya shafi Sirrin
Auratayyan ku, bakomai ake fad’a ba ko anuna, wanna
Sirri ne tsakaninku). Indo tunda ta gani, sai taji ba dad’i,
amma ba yanda ta iya dole sai ta wanke. Ta d’ebo ruwa
kenan ta fara wanki, sai ga Haiydar yashigo, tunda ya
hango ta, yaji ransa ya b’aci. Ko da ya ajiye mota ya fito,
dole sai yabi gefenta ya shiga gidan kasancewar qofar
main falo yana rufe, yana isowa kusa da ita, karaf idonsa
ya sauka kan bedsheet cikin kuna rai da zafin zuciya
gami da wani kara yayi kamta da gudu. Ni ko Rash ina
ganin haka na tattaro yan komatsena, nasa ka gudu dan
kar Haiydar ya had’a dani. DEDICATED TO AISHA
MUHAMMAD ( MAMAN ABDUL SHAKUR) RASH LUV
[2:31PM, 9/14/2016] Rash Kardam: BABBAN KUSKEREN
DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-46~50.
Da sauri yayi kanta, ganin haka, tasoma ja da baya,
jikinta sai bari yakeyi. Haiydar yana zuwa kutu ball yayi
da boket d’in. Yana huci tamkar wani namijin zaki, yana
jin yuwa yafito farauta. Indo ko ta mak’ure a jikin gini,
sai b’ari take, don tunda take a rayuwanta, bata tab’a
ganin fushi irin na Haiydar ba. Don in ta kali fuskansa, sai
taga kamar na zakine yazo gabanta yana huci. Kanta ya
nufo yana cewa”waya kawo ki gida na?. “Meye had’in ki
da wanke bedsheet d’in da na kwanta da matata. Indo ko
gani tsanani fushi ya had’u da tsoro, bata san lokacin da
ta sulale, kasa sumamiya ba. Haiydar ganin idonta sun
kafe, hakan ya tabbatar masa da suma tayi, wuceta yayi
ya nufi cikin gida, da fushinsa. Falmi ko tana zaune a kan
gado, takecin indimiee, wani gululun bak’in ciki ya k’ara
tokaraansa, wannan wani irin iskanci ne?. A kan gado
take cin abinci. “Mtsss yayi tsaki”. Cikin muryan
shagwab’a tace”My Haiydar ka dawo?. “Bayan tafiyanka
yunwa ta dame ni da… “Keee wa ya kawo min wannan
bak’ar mai ido kamar na mage, gida na kuma don iskaci
da rainin hankali, zanin dana kwanta da ke take
wankewa. “Mtss shikenan nikam nagama yawo,
yarinyanan zata rainani. “Ta gama sanin sirina. “Shikenan
nikam kin gama dani mtsssss. Falmi tace”to ya kakeso
nayi, ni kasan ko a gida ita, take min wanki. Hatta under
wears d’ina ita take wankewa. “Mtsss sai kiyi tayi ae. Falo
ya fito tare da bata guri, ganin zaman gun bazai masa ba,
ya nufi d’akinsa cike da kunan zuciya. Falmiko tana gama
cin abinci a gun ta bar kwanon, ta sake kwanciyarta.
Indo ko ta dad’e a sume a gun, sai da ruwan da ya zuba
ya iso jikinta, hakan yata daman farkawa. Hasken ranane
ya haska mata ido, da sauri ta mik’e, cike da tsoro,
tace”yanzu ta koma gidane ko ta shiga gidan?. Wata
zuciya tace”in kika tafi baki gama aiki ba, wani tashin
hankaline. A hankali tashiga gidan d’akin da Falmi take ta
nufa, poss d’inta ta d’auka, tafito falo da shirin ko ta
kwana. Haiydar ne ya fito, nan rake ta soma b’ari. Cikin
fushi da muryan hargowa yace”ke mai kikeyi a cikin
gidan nan da baki tafi ba?. Kasa bashi amsa tayi masifa
ya cigaba dayi, wanda hakan ya tashi Falmi ta fito.
Haiydar janyo Indo yayi yace”ki fita min a gida kar na
k’ara ganin k’afarki a gidan nan sai na karya ki. Falmi
tace”miye haka wacce zata min aiki zaka kora?. “Kasan
dai ni ban iya aiki ba ko?. “Ita zata na mana girki da
sairan aiki. Haiydar ya kulu iya kuluwa, yace”kee miye
aikin ki da baza kina aiki ba?. “Ni fa ka ganni ko agida
ruwan Lipton sai an dafa min. Cike da ta kaici yace”baki
isa ba to ni bana son girkin yar aiki. Ya wuceta fuuuu
yayai d’akinsa qofar ya bako ya kwanta yana mai takaicin
abunda ya faru, “daman haka halin Falmi yake?. Falmi
tana zuwa d’aki Mum d’inta takira, sai da ta sanar mata
da komai. Mum tace”yayi kad’an daga zuwanki zai fara
fida halinsa to bai isaba wallahi. “Yar’aiki kuma kamar ta
zauna daram, dole Indo ta dawo cikin satin da zamu
shiga, tunda baki saba aiki da kanki ba. “Ki bar min
komai a hannuna dole yayi biyayya. Falmi cike da jin
dad’i ta mata sallama, ta kashe wayar. DEDICATED TO
AISHA MUHAMMAD (MAMAN ABDUL SHAKUR) RASH LUV
[5/28/2016] Rash Karda BABBAN KUSKEREN DANA
TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-51~55. Indo
tana fita, kuka take maras sauti, tana rokon Allah ya
fitarta ya bayyana mata da danginta. Haka har ta iso
gida, tana zuwa bata huta ba ta kama wasu ayyukam, da
zatayi ma Hajiya, gashi sun k’aru sabida yan biki. Falmi
kuwa bata sake leko falo ba sai dare, da yunwa ya
dameta, wasu matsatsun kaya tasaka. Haiydar na falo
yana kalon tashar BBC WORLD ta shigo sai karairaya
rakeyi, kalo d’aya ya mata ya kasa d’auke kansa,
kasancewan bai da hak’uri. Take ma manta fushin da
yakeyi da ita, ganin taki zuwa kusa dashi, tashi yayi a
hankali yaje ya rikota, cikin rad’a yace”haba baby na
fushin ne har yanzu?. Sai da ta d’anyi farrr kafin tace”ni
yunwa nakeji fa. Hannu ta ya kamo sukaje dinning, asai
yamusu take away. Nan yaringa bata a baki tana ci sai da
ta k’oshi, ya sun kuceta sai d’akinsa, nan labarin ya canza.
Hajiya Fiddausi, sai datayi shige da fice, tasamo kan
Haiydar, ya yarda Indo ta dawo gidan da zama tana
musu aiki. Hajiya tace”ma Falmi ta bari sucika wara sai
Indo tazo, a kwai abunda takeyi ne. Falmi badan taso ba
ta amsa ma Mum d’inta. Kwanaki sun tafi yau 3weeks da
bikin Falmi, tasoma caza ma Haiydar kai, Haiydar duk
lokacin da yazo da buk’atarsa Falmi tayi burus dashi, ko
kuma in tabashi had’in kai sau d’aya, to ba zai k’ara ba.
Haiydar har ya d’an rame. Mum takira Falmi tace”to ba
zama zakiyi ki zuba masa ido ba. “Zaki fara tatsansa ne
mu had’a jari. Falmi tace”Mum to taya zan tatse sa da
yawa bacin akwai komai a gida?. “Mtss kee sai kace ba
mace ba, bakisan tanda zakiyi ki samu kud’iba. “Kina
tambayansa mana. “Ko kuma in yazo kwaciyan aure
dake, kice sai yazuba kud’i ke bazaki iya ba. Falmi tace”to
Mumcyna hakan zanyi ma kawai. Mum tace”yauwa yar
albarka. (Kira gareku mata masu irin wannan galin, idan
mazajenku sun zo muku da buk’ata, kuce sai sun baku
kud’i, wannan BABBAN KUSKURE NE, aikata hakan
haramci ne dan Allah akiyaye). Da yamma Falmi tayi
wanka tayi kyau sosai, kasancewan bata girki Haiydar ke
sayo musu tayi zaman jiransa. Haiydar ko da sallamansa
ya shigo gida, tunda ya kyalo Falmi, ya had’iye wani
yawu. Take yaji jikinsa ya mutu, dining ya wuce ya ajiye
abinci da ya sayo musu, Falmi ko bata iya cemasa sannu
da dawowa ba. Sai shine yace”ya gida fatan kin na lafiya?.
Sai da ta d’au lokaci, kafin tace”lafiya lau nake. ‘Dakinsa
yaje ya watsa ruwa ya saka 3quater da singlet ya fito, a
dining ya ganta. Shima can yaje ya zauna, ya kaleta
yace”ki d’auko plate da spoon kiyi serving d’in mu. Sai da
ta ya tsina fuska taje ta d’auko ta dawo, har ta zauna
yace”ruwa fa ko sai mun gama ci za’a d’auko?. “Mtssss ta
yi tsaki ni na gaji da yawan tashi. Sai da suka gama ci,
Falmi ta zo jikinsa ta zauna, don yau tanason ta fara
wankansa, tunda tagane shi mai yawan bukatane, wasani
tafara masa, wanda yasaka hankalinsa tashi, gashi kwana
biyu Falmi ta hanasa kanta. Shima biye mata yayi suka
dulmuya, sai da taji zai wuce ta mike zubur, cikin
dashashiyar murya yace”Falmi karki ki amincewa dani.
“pls ki taimaken una cikin yanayin bukata. Kafad’a ta ya
tsina tace”ni bazan iya ba. Cikin yanayi tausayi tafara”pls
My Falmi ki taimaken dan Allah ina buk’atarki sosai. “Duk
abunda kike buk’ata zan miki matsawan zaki bani had’in
kai. Sai da tayi wani murmushin mugunta tace”kayi
alkawari ina fad’i abunda nakeso zaka bani? Da sauri ya
amsa mata”da eh! Zan baki koma miy ne. Falmi
tace”kud’i nakeso masu yawa. “Haiydar jikinsa na b’ari ya
tashi ya duba Aljihun wandinsa ba wani kud’i masu
yawa, sai 10k ne kawai don d’azu a gun aiki, yayi sadaka
da kud’ade’en da ke jikinsa, ma masu bara, duka dubu
goma ta d’ebo yace”ga abinda suka rage min nan. Falmi
tace”nawane wannan don naga da alama basa da yawa?.
Haiydar yace”10k ne kawai bana da kud’i a jikina suna
banki. “Mtss mai dubu goma zasu min, asai baka shirya
jin dad’i ba. Haiydar kamar zaiyi kuka yace”haba Falmi ki
taimaka ma halin dana ke. Zugunawa yayi akan
gwiwansa, don bayason abunda zai b’ata mata rai. “Mtsss
to mai kake so na maka ne?. Da rauri yace”ki taimaka
min. Ummmm”zan iya barinka kayi kiss a 10k amma fa
da sharad’in bazaka wuce haka ba?. “Eh na yarda in har
zaki bari namiki d’an kiss d’in. Okay!. Da sauri Haiydar ya
taso yazo zai rungumeta, Falmi ta ja da baya, tana masa
kalon raini wayo. DEDICATED TO AISHA MUHAMMAD
(MAMAN ABDUL SHAKUR) RASH LUV [2:31PM,
9/14/2016] Rash Kardam: BABBAN KUSKEREN DANA
TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-56~60. Haiydar
ya rairaice mata, yana had’a ta da Allah, bata yarda dashi
ba sai da ta yamata Alkawarin 100k tukun ta yarda
tabashi kanta. Tun daga wannan rana Falmi tadawo galfa
Haiydar son ranta, tana sati na hud’u, Indo ta dawo
gidan da zama, duk wani aiki Indo keyi hatta gyaran
d’akin Haiydar, abincinsa da wankin kayansa duk
itatakeyi. Bayan kwana biyu, Hasna ta shirya tace”hajiya
zanje gidan Yaya indaidasu”. Hajiya tace”ki gaidasu sai
kin dawo. Mota ta d’akua sai New GRA, tana zuwa horn
tayi ma gadi ya bud’e mata. Sai da ta ajiye motarta, a
ma’ajiyin mota, tafito cikin nutsuwa tashiga cikin gidan.
“Assalamu’alaikum” Falmi da ke zaune taji sallama,
amma tsaban iskanci taki amsawa, Hasna tasake mai-
maitawa, Indo da tafito daga kitchen ta amsa, Hasna
tashigo cikin falon. Falmi tana ganin Hasna ta ganeta don
tun kafin biki sunjemata, amma dan iskanci tawani
yatsina fuska, cikin zuciyarta ko cewa take”mtss wannan
dangin miji daga gani zanyi fama daku?. “Wata d’aya da
sati biyu da biki, amma ace har sun fara sintiri wa mutu.
Hasna da murna ta k’araso gun Falmi, tace”Aunty na
sannu da gi…. Wani kalon da Falmi ta aika mata dashi,
yasata kasa k’arasa maganta. Falmi bata tanka mata ba,
sai da ta mik’e tsaban iskanci tace”daga ina haka?.
“Wacece ke naji har kina cemin Aunty. Husna ta danne
zuciyarta tace”lah! Baki ganeni bane ai k’anwar Haiydar
ne Husna. “Oh! Haka fa yana da kwanwa ko?. “Sanuki da
zuwa, Indo! Indo!”. Da sauri Indo tazo ta rusuna,
tace”gani Aunty”. Falmi tace”ga wannan yarinya, ki bata
ruwa tasha, in kin gama girki, sai ki samata”. Falmi ta
juya ta kali Hasna tace”kya iya zama anan kafin Yayanki
ya dawi. Ta wuce d’aki tana wani karairaya, Hasna baki
tasaki tana kalon ikon Allah. Indo tace”Hasna sunaki ko,
sannu da zuwa ya gida?. Hasna cikin raha ta amsa, nan
suka fara hira tana taya Indo aiki har suka gama. Hasna
taji dad’i zamansu da Indo, haka kurum takejin ta kamar
yar’uwata, duk da Indo zata ba ma hassna kamar
shekara d’aya haka. Da yamma Haiydar ya dawo, ganin
Hasna ya saki fara’a, a falo ya zauna suna hira, tukun ya
mik’e yaje yayi wanka, yafito zaici abinci, yaga Hasna da
Indo suna hira, wani mugun kalo ya sakar ma, Indo
sum-sum tamik’e tayi d’akinta. Duk abunda yakeyi Hasna
tana lura dashi, abinci yasa Hasna tayi serving d’insa yaci.
Sai can Falmi tafito cike da isa tace”kadawo shine bazaka
zo ka fad’an ka dawo ba. Haiydar yace”tayi hak’uri. Hasna
da yamma tayi musu sallama ta tafi. Ko da takoma gida,
tabama Hajiya labarin Indo da kirkinta. Ta kuma yaba da
hankalinta, Hajiya hartaji tana son ganin Indon nan.
Bayan kwanaki Haiydar yace”Falmi ki shirya zamuje
gaida Hajiya na. Da farko Falmi taki ganin Haiydar ya
dawo Aliyu na da dole ta shirya sukaje, ranan kam Hajiya
taga rashin kunya ayinin da sukayi, nan Hasna ta bata
labarin abunda ya faru, nan Hajiya tagane anyi ma Aliyi
asiri don ba haka yake ba, sam bayason raini. Hajiya tace
“Don haka dole na mik’e da addu’a. Haka su Falmi suka
dawo gida. DEDICATED TO AISHA MUHAMMAD (MAMAN
ABDUL SHAKUR) RASH LUV [5/28/2016] Rash Kardam
BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA daga www.hausaebooks.com.ng NA ©RASHEEDAH .A.KARDAM. Pg-61~65. Falmi kulum da kalan tsiyar da take
tsula ma Haiydar, Haiydar sam baida hak’uri, wani sa’in
da dambe yake kusantanta. Kuma dole sai ya biya
Haiydar ya rame sosai, har d’an bak’i yayi. Hajiya ko ta
dage da Addu’a, har masallatai ta aika ana tayata da
addu’a, Allah maji rokon bawansa. Haiydar ne zaune a
office d’insa, ga tarin takardu, amma ya kasa tab’uka
komai, a hankali yake tariyo komai na rayuwansa, duk
lokacin da yatuno Falmi, sai ya rintse ido don wani
matsanacin sha’awan dayakeji, ajiyar zuciya yayi. Surar
Falmi ne ke yawo a Indonsa, a hankali ya mik’e ya d’au
key d’in motarsa. Gida ya nufa don ji yake in bai samu
biyan buk’ata ba, komai ma zau iya faruwa. A gida ko
Falmi tayi wanka, bata aikin komai sai chatt, ga iya
taunan chewing gum kamar tsohuwar karuwa. Ita kad’ai
tana murmushi, ga k’aran shigiwan massage na
Whatsapp kamar me, duk ta cika mana kunne. Indo ko
tanata aiki, don karta makara in Haiydar, ya dawo bata
gama ba tasan sauran. Haiydar ko gudu yake sosai, don
yanda yake jinsa ba k’alau ba. Yana zuwa gida horn ya
dinga yi, kamar zai tashi sama, mai gadi ya bud’e masa
gate ya shigo, da gudu yaje yayi parking, ya fito cikin
sauri ya nufi cikin gidan, yana shiga falo ya hangota, da
sauri ya nufi inda take. Yana zuwa ya janyota jikinsa, ya
fara shin-shinata, cikin tsawa tace”Malam lafiyarka
kuwa?. “Wani irin iskanci ne haka?. “Mutum na zamansa
zaka zo kawani damesa. “Ko kamanta da dokanda na
kafa maka ne?. Sake matsowa yayi kusa da ita, ta matsa
ya biyota, nan suka fara kokawa, ganin yafi k’arfinta
tasoma dukansa, d’aukarta yayi kamar yarinya, yanufi
bedroom d’insa da ita, yana ajiye ta ta mike tace”Makam
anawa zan baka kaina?. Cike da mamaki yace”kamar
yaya?. “Bayan kud’in sadakin dana akwai wani kud’in da
zan sake biya ne?. “Oh kamanta ko?. Hanyar fita tayi, kafa
ya samata ta fad’i ya mayar da qofar ya rufe. Hmmm
ranan Falmi taji jiki dan sai da kusan magriba Haiydar ya
kyaleta, yace”kuma kisa ma ranki kulum da dadre sau
uku ko hud’u, da safe biyu kafin na fita, in nadawo uku in
ba ida zanje. “Kinga ina kyaleki ko to daga yau ba sasauci,
in kuma kinki to nasan matakin da zan d’auka. “Don
bazan saka miki ido nayita kalonki ba. Ya shiga wanka ya
fita masallaci abunsa. Ranan Falmi tayi kuka sosai, don
taji jiki, kuma ta gane maganin da suka masa yanzu baya
aiki Haiydar tun daga wannan ranan ya mayar da Falmi
kamar engine sa. Tunda tagane suka shiga wasan b’uya,
gashi ya hanata zuwa gidansu. Falmi ko tayi planning, na
5yrs, bazata haihu ba. Haiydar abun duniya ya ishesa,
yanzu kusan shekara 3yrs da aurensu, ba abunda ya
canza, a halin Falmi, ga shi ba tatab’a koda b’atan wata
ba, kuma shi ya kasance mai son yara. Ganin ba zai juri
iskancin Falmi ba ya yanke hukuncin k’ara aure. Amma
sai ya fuba mai hankali da nutsuwa tukun, ana haka aka
kawo wani case, wani mutumi sunyi fad’a da barayi har
sunjimasa ciwo, ga jini na zuna asibiti suki k’arbansa, key
motarsa ya d’auka yanufi asibiti, duk wani abunda za’ayi
yayi aka k’arb’i mutumin. Nan ya had’u da wata nurse
sunanta Amrah tana da hankali, hakan yasa ya k’arbi
number ta. Tundaga ranna soyya tashiga tsakaninsu mai
k’arfi. DEDICATED TO AISHA MUHAMMAD (MAMAN
ABDUL SHAKUR) RASH LUV [5/28/2016] Rash Karda
BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA daga www.hausaebooks.com.ng NA ©RASHEEDAH .A.
KARDAM. Pg-66~70. Haiydar ya samu Hajiya ya mata
bayani, yace”ta fad’a ma Dad, Hasna kam tafi kowa
murna. Falmi tun dataga take-taken Haiydar tasaka, aka
fara bibiyarsa nan tasamu labarin, yana neman Aure nan
hankalinta ya tashi, baran da taji ma’aikaciyar asibiti,
take ta kira Mum, tana kuka ta sanar mata. Hajiya
Fiddausi tace”karyane dole yau naje gun Malam kiyi
shiru. “Ki bar komai a hannuna. Hajiya Fiddaisi tana tashi
sai gun malamin dake mata duba, ko da ya buga k’asa
yayi wasu surkulensa. Yayi shiru can ya d’ago yace”Hajiya
sai dai hak’uri fa, dole mijin yarki zai k’ara aure, sai dai
shawaran da zan baku shine. “Zamuyi aiki a kai ku sai ku
zab’a masa mata. “Don Mahaifiyar yaron ta dage masa da
addu’a. “Aikin mu bazaiyi wani tasiri akansa ba. Hajiya
jiki ba kwari ta dawo gida nan ta sanar da Falmi kimai.
Hankalin Falmi ya tashi ta rasa mai ke mata dad’i, don
hatta indo bata barta ba bare Haiydar, kulum cikin fad’a
suke. Haiydar ya tsayar da ranan jumma’a magabatansa
zasuje, gidansu Amrah. Falmi ta fito zatayi d’akinsa taji
yana waya da Amrah ya na sai damata ran Friday,
magabatansa zasuzo, Falmi tayi kukan kura tace”kwace
wayar nan ta kamashi da fad’a, farko Haiydar ya kyaleta,
ya dawo falo tafiyosa. Nan tasha kwalansa, suna kokuwa
saiga Hasna ta iso, ganin halin da ake ciki, yasa takiya
Hajiya ta fad’a mata. Hajiya ta sanar da Abbansu Haiydar,
ta sa driver ya kawota. Zuwan Hajiya tasa Haiydar ya bar
dukan Falmi, Hajiya ta musu nasiha sosai, bud’an bakin
Falmi tace”Hajiya nifa aure ne bana so ya k’ara. “Yin
hak’uri da k’ara aure shine zaman lafiya a gidan nan. Nan
tafara rashin kunya son ranta, Haiydar ya taso zai daketa
Hajiya ta hanasa. Hajiya tace”kee Fatima aure kam ba
fashi sai anyi dole. Falmi tace”to ya auri wata ba wannan
ma’aikaciyar ba. “Ai da ya aureta gwara ya aura min Indo
a matsayin kishiya. Hasna da ke gefe tace”Hajiya ae
gwara Indo sau dubu tana da hankali. Hajiya tace”kee
wayasa ka bakinki a ciki. Hasna tace”yi hak’uri Hajiya.
Hajiya tace”ke da bakinki kikace haka ko?. “To zan gwada
miki na isa da d’ana. “Kuma ina Indon mutum ce?.
“Kuma macece?. “To zai aureta in Allah ya yarda. Cikin
sauri Haiydar yace”Hajiya ina bana son Indo gwanda ke
kini momin wata daban na tsani Indi. Hajiya
tace”hukuncin dana yanke kenan. “Fatima ta raina Indo
ne tace haka ko?. “Watarana d’an hakin da ka raina shi
zai tsole maka ido. “Aliyu! Haiydar da sauri ya d’ago don
tunda suke da Hajiya bata tab’a kiran suma ba. Hajiya
tace”in nina haifeka to ina si kamin biyya. “Indo ita na
zab’amaka kuma wataran zakayi alfahari da ita,
amatsayin mata. Hajiya tace”Fatima ina Indon take?.
Falmi cikin muryan kuka duk ra rud’e tace”bata nan na
aiketa gidan mu. “Ok! In ta dawo Hasna zata zauna
sutaho tare. Hajiya ta mik’e tace”ni na tafi kaiku ma kazo
dadaddare ina son ganinka. Hajiya tana fita Haiydar ya
mik’e sai jiri yakeji ya nufi d’aki, wannan wani irin
al’amarine?. “Naike shirin faruwa dani. Hasna abun ya
mata dad’i hawan kan kujera ta mik’e, tana jiran
dawowan Indo du tafi. Falmi ko ta d’aura hannu aka tana
cewa”shikenan naja ma kaina tabbas NA TAFKA BABBAN
KUSKURE. “Mai ya kaini furta haka ya akayi na ambaci
sunan Indo?. “Wannan shine BABBAN KUSKUREN DANA
TAFKA. “YAR AIKINA ZATA DAWO KISHIYATA. “KUMA YAR
CIKIN SHEGE. Nima Rash daga gefe nace Falmi gaskiya
kinyi KUSKURE BABBA. Bari dai muga ya wannan gurmin
zai k’are don nikam banso abarni a baya. DEDICATED TO
AISHA MUHAMMAD (MAMAN ABDUL SHAKUR) RASH LUV
[2:31PM, 9/14/2016] Rash Kardam: BABBAN KUSKEREN
DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-71~75.
Indo bata dawo ba sai daf magriba tashigo, da sallamata,
Hasna dake falo tana kalo tace”oyoyo Aunty Indo sanu
da dawowa, tun d’azu nake jiranki. Cikin sassayan
murmushi Indo tace”sannu Hasna ya kk?. Yasu Hajiya?.
Hasna tace”lafiya lau”. Indo tace”kin dad’e da zuwa ne
Hasna. Hasna tace”eh! Hajiyar ma tazo, bata dad’e da
tafiya ba. “Tace muje tare dake yanzu nan. Indo ta zaro
ido tace”lafiya dai ko Hasna?. Hasna tayi murmushi
tace”lafiya lau mudaije zakiji. Indo tace”bara na fad’a ma
Aunty aika. Hasna tace”kyaleta ki zo muje kinga Hajiya ke
kiranki. Indo tarasa mai zatace ma Hasna, can tace”karfa
ta zage ko ta maren ina tsoro. Hasna tace”Itama tasan da
Hajiya tana kiranki itama. “Karki damu yanzu zo mu tafi.
Ba musu Indi ta bita suka fito, motan Hasna suka shiga ta
su zuwa State Low cost. Cikin nutsuwa suke tafiyar har
suka iso katon katafaren gidansu, horn tayi mai gadi ya
bud’e mata, ta danna hancin motarta cikin gidan. Gurin
ajiye motoci taje ta ajiye motar suka fito tare, sannu a
hankali sushiga cikin gidan, Indo tun zuwarsu taji
gabanta na fad’uwa, addu’a tasomayi. Da sallama suka
shiga falon ba kowa, Hasna ta nuna mata kujera
tace”zauna Aunty na” Hasna taje fridge ta d’auko mata
lemu da cup ta kawo mata, saida ta siyaya sannan
tace”Aunty na barinje na kira Hajiyan. Indo murmushi
tayi wanda ya k’ara fitar mata da kyauta. Hasna ta hausa
sama zuwa d’akin Hajiya, ta tura da sallama tashiga.
Hajiya tace”Hasna kun zo tare da ita ne?. “Eh! Hajiya gata
a falo tana zaune. “To kije gunta ina zuwa yanzu. Hassana
ta sauk’o a hankali zuwa falo, kalo ta kunna musu, sai ta
mik’e ta koma d’akinta ta d’ebo ma Indo, hotunansu na
school ta kawo mata. Kusa da ita ta zauna Indo ta fara
ganin photo, Hasna tana fad’a mata sunan kwayenta. Tun
Indo na d’ari-d’ari, har ta saki jiki da Hasna, suka fara
hira sosai, a tsakaninsu nan Indo kece ma Hasna itama
tayi karatu, amma a Jss3 ta tsaya bata ci gababa. Hasna
tace”maiya hana ki ci gana Aunty n?. Nan take idon Indo
yaciko da kwalla, ta fara sharewa tace”Mamana ke biyan
min kud’in makaranta, ta rasu kuma ba mai d’aukan
nauyina. “Hakan yasa na hak’ura da karatu. “Amma ina
son nayi karatu wallahi. Hasna tace”Allah sarki Allah ya
jikanta da rahma. Indo ta amsa da amin. DEDICATED TO
AISHA MUHAMMAD (MAMAN ABDUL SHAKUR) RASH LUV
[5/28/2016] Rash Kardam BABBAN KUSKEREN DANA
TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-76~80. Hasna
hira sosai sukeyi da Indo, abun gwanin burgewa in ka
gansu ka d’auka sun dad’e da sabawa da juna. Haiydar da
kyar yashifa d’aki wani irin jiri yakeji, cikin zuciyanshi ko
cewa yake” amma Fatima ta cuceni gaskiya. “Mai ta kawo
bakinta na cewa na Auri Indo. “Ina zan kai b’akar mace?.
“Sam ni tsarina bana son b’aka. “Kuma

Please Login or Register in order to submit comment