Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yaran aunty maza masu zuwa nan gaba,hhhh
abdallah yayi dariya ita kuwa kunyane ya kamata.
Sama suke hawa wanda palo 2 ne a saman,dama da hagu,na dama shine na manosh
komai *milk colour ne* na hagu kuwa na maryam ne komai *peach colour ne*.
Woooo!😘zanso ace kunga gidannan,kowannesu da daining nashi colourn zanso ace kunga gidannan,kowannesu da daining nashi colourn
palonshi,sannan a palourn maryam akwai wani ki hine da store komai light blue ne
sedai bayi da girma kamar kichin d'in k'asa. Agefen maryam akwai d'akinta da
toilet a ciki,daga gefe kuma d'akin bbynsu mace ce mai ziwa bayan sunyi aure
ba'asa komaiba dai amma wall peper pink ne. Se kuma d'akin baki da toilet a
ciki.

A palon manosh kuwa dainingne se kuma d'akinsa da toilet. Gaskya tsarin gidan ya
burgeni mu samman idan ka haura sama, palour 2ne a gefenka ga peach ga kuma
cream.
Manosh ya nuna musu ko ina tare da musu bayani. Abdallah ya dad'e yana addu'a a
cikin gidan sannan ya yabawa manosh da irin k'okarin dayayi a wannan gidan
nashi,dan base na fad'a.
Drinks masu sanyi ya d'auko musu daga frdje,mamaki sukayi lokacin daya bud'e
fridje d'in a cike yake da drinks da kuma faro water. Maryam dai taki shan
komai,abdallah ne yasha abinshi shida manosh,yace nifa banga d'aki naba,manosh
yace d'akinka uana daga gefen flour ata waje,yace yawwa bari naje na duba,manosh
yace to muma gamu fitowa.

Shuru maryam tayi gashi palourn yad'au sanyi,dan tun shigowarsu ya kunna AC.
Tashi yayi daga inda yake zaune ya dawo inda take yace tashi muje ki zauna a
palo na kafin mu tafi dan nacewa su marwan sekin fara zama akan kujerun kafin su
zauna. Ba musu ta mik'e suka k'arasa a 3seta ya zauna,ita kuwa a 2,yace tashi ki
dawo nan,sam tak'i tace a'a nanma na zauna ai,yace pls apple kizo zan mana pic
ne anan,amma sam kunya ya hanata tashi,haka ya yashi yace inda take ya zauna
batare da jikinsu ya had'uba ya musu pic. Thankyou yace da ita tare da nuna mata
pic d'in,murmushi tayi tare da karb'an wayan dan sunyi kyau sosai,yace amma fa
kin fini kyau dan haka zanyi deleting,tace a hakan pls ka barshi wlh kama fini
kyau,yace to shikenan tare da mik'ewansu a tare. Kallon juna suka tsayayi,take
ta kawar da kanta gefe tace gida yayi kyau sosai Allah yasa mu shigo a sa'a
Allah kuma ya k'ara arziki ya karemu daga dukkan....hannunsa taji acikin nata
yasa ta kasa k'arasawa,shi kuwa yace ameen aunt. Hannunta take k'ok'arin gwacewa
daya lura da hakan seya sake mata hannun yace sorry apple haka kawai naji cewa
in rik'e hannunki,kanta ta d'ago suna kallon juna atsarge tace muje,murmushi
yayi tare da cewa to muje,gaba tayi yana biye da ita a baya,sedaya kashe komai
sannan ya fito harta fita waje.
Sunanta ya kira aunt,juyowa tayi tare da kallonshi,yace zo muje gida flower
naki,da murna taje suka bi gefe sam takasa b'oue farincikinta sebin flower d'in

takeyi da fararen hannunta hakwaranta tas a waje shikuwa se pic yake mata batare
data saniba. Can kuma ta hango wani guri mai kama da swiming pool,amma kuma
taganshi a rufe da wani glass kana iya ganin cikinsa,sosai taji dad'i tare da
kallonshi tana murmushi,gwalo yayi mata da harshensa tare da dannan gefen pool
d'in seya bud'u. Sam ta kasa boye murnanta tace thankyou so much peach,mirmishi
yakeyi tare dajin dadin yadda yaga tana farinci seyaji dad'i sosai har cikin
zuciyarshi yace Always my jealousy😜. Yake ta b'ata rai tare da mik'ewa tayi
hanyan komawa gun mota,da sauri harda gudunshi yasha gabanta tare da had'a
hannayenshi gu d'aya yace👏🏻 _pardon me apple_, k'itayi zata wuce ta gefenshi se _pardon me apple_, k'itayi zata wuce ta gefenshi se
yayi saurin rik'o yatsan hannunta guda 2 yace inyi tsallen kwad'o? D'aga kanta
tayi alaman eh,aiba b'ata lokaci ya saki yatsunta yahau yin tsallen kwad'on se
dariya takeyi sannan tace ya isa haka shikenan har a yanzu dariyan takeyi,shi
kuwa se kallonta yakeyi yana mirmushi. Daidai nan abdallah yazo yace gaskya
d'akina yayi kyau sosai nagode,manosh yace bakomai d'an aunty kafi haka aguna.
Abdalla yace naga swiming pool amma na ganshi a rufe kuma na kasa bud'ewa,manosh
yace na rufene saboda bana so kowa ya fara shiga se auntynka,amma muje in bud'e
maka tunda ta tab'a ruwa,murmushi abdallah yayi suka tafi acan manosh yayi ta
mishi pic sannan sukayi tare,maryam taga shuru yasa ta lek'asu taga se selfi
sukeyi,abdallah yace auntyna kizo muyi tare,amma sam tak'i,dole abdallah yasa
taje manosh yanata d'aukansu sannan suka kama hanyan komawa girei bayan sayayyan
da sukayi a shop. Godiya sosai abdallah yayi dan kayayyaki masu tsada manosh ya
sake saya mishi.

Maryam ma ta tayashi godiyan sannan sukayi sallama ya tafi ita kuwa taje tanata
baiwa maman lbrn gidan manosh. Dad'i sosai mamaji tare dayin addu'a.
Washe gari alhamis su miher harsun fara shirye shiryen biki lubna ce mai
tayata. Su rash sukace sam su dole ayi biki amma maryam tace babu abunda zatayi.
Bayan isha abdallah yazo sunata hira da maryam yace wlh aunty kaina ciwo yake
min kid'an kamamin mana,nan ta kama mishi kan da addu'a har mama tana cewa toga
paracetamol d'an aunty ka daure kasha,yace a'a kamun da aunty taminma naji dad'i
seda safe,aunty tace to Allah ya sauwaka yace ameen.

Da asuba yau jumma'a bayan an idar da sallan asuba,abdallah yayita karatun
qur'ani mai girma da daddad'an muryansa mai k'arawa mai sauraro imani. Yakai 1hr
yanayi sannan akayi wa'azi aka watse,gidansu maryam ya shigo suka gaisa tace
kaji karatunka na yanzu a wayata nayi recording,mirmushi yayi yace kai aunty
keda ma naki yafi nawa shine kiketa tara muryana a wayarki,tace eh har gobe
kiran sallanka yana cikin wayan manosh,dariya yayi yace Allah yabarmin ke
auntyna,tace ameen nima Allah yabar min kai,babane ya shigo yace abdallah ya
jikin dai,yace ai naji sauk'i baba,baba yace Allah ya kara lfy,yace ameen.
Seyace aunty naji su aunty rashida sunce zasuyi biki sosai ina fata dai banda ke
ko? Tace eh bandanikam walima kawai su captain zasuyi,yace kin kyauta aunty irin
wannan karatun zanyi a wannan ranan Allah ya kaimu lokacin kawai aunty,tace
ameen sannan ya fita.

8:40am mama tazo d'akin maryam tana cewa maryam yau kuma kece mai baccin
safe,toki tashi maryam *innalillahi wa'inna ilaihirraji'un* da sauri ta farka
tace mama lfy,mama tace maryam yau kuma munyi rashin ABDALLAH seta fashe da kuka
tare da rik'e maryam gam. Maganan kamar a mafarki tajishi,amma yadda taga
mamanta ta riketa ta kuka tasan cewa ba mafarkibane gaskyane, *innalillahi
wainna ilaihirraji'un*itama take furtawa tare da kallon mamanta tace wani
abdallan kenan mama kina nufin abdallah nah? Da sauri ta mik'e bata jira amsar
mamaba ta zurma himar nata tayi waje.
Jama'an data gani a wajene tun daga bakin masallaci har k'ofar gidansu abdallah
yasa ta k'ara fashewa da kuka tana wuce mutane batare datasan cewa wandon

sleeping dress bane a jikinta,harta k'araso k'ofar gidan dakyar ta samu hanya ta
shige ciki. Kukan rash ta fara jiyowa dana mamansu,rash ta mik'e ta rungumeta
tana cewa shikenan abdalla yatafi yabarmu maryam innalillahi wa'inna
ilaihirraji'un....
[7:12am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: 🍭🎈AUNTY'N YARA🍧🎁AUNTY'N YARA🍧🎁

Written by sad-nas

*dedicated to mmn adnan* (babby)❤)*❤)*❤)*

51-52 zama sukayi sunta kuka sosai,hiransu na d'azu kawai taketa tunowa a
zuciyarta da kuma dariya yayita sasu ita da manosh lokacin da sukaje ganin
gida,nan ta sake fashewa da kuka tana cewa ashe daman bankwana muketayi dakai
d'an aunty,innalillahi wa'inna ilaihirraji'un suketa nanatawa tare da cewa Allah
ya jik'anka abdallah yasa ka huta.
Yah ibrahim ne da friends nashi seke fitowa da gawan abdallah bayan sun gama
mishi sutura. Koda suka fito daga d'akin ya ibrahim kuka sosai jama'a keyi,da
sauri maryam ta d'ago da kanta ai kuwa setaga gawan a hannunsu suna zuwa gun
mama dashi,tunda yah ibrahim ya had'a ido da aunty seyaji hawaye yazo mishi ido
amma ya daure ita kuwa kuka sosai sukeyi ita da rash.
Mama ta matso tayita mishi addu'a,rasha da maryam ma suka matso se kuma baban
maryam d'in tunda shine matsayin ubansu dukkansu. Haka aka d'auki gawan aka fita
dashi yayinda jama'a suketa kuka akai mishi sallah,batare da b'ata lokaciba aka
kaishi gidansa na gaskya hardasu manosh wato "the 5 emms" dan yah ibrahim ya
tura musu texs d'in rasuwan k'aninshi abdallah kuma d'an autansu. Yah ibrahim
ya kasa barin kabarin se hawaye yakeyi akan kabarin,friends nashine taredasu
marwan suka d'agashi jiki sanyaye suka dawo gida inda aka zauna kab'ar gaisuwa.

Hmmm!rayuwa kenan,yau kaine gobe bakaibane. Kuduba dai kuga irin mutuwar da
abdallah yayi,ran friday,kuma koda yabar gidansu maryam ya wuce gida hira sosai
sukeyi da mama da yah ibrahim rash kam tuni ta koma bacci dan ko wani sallama
basuyiba,in banda gaisuwa daya mata na safiya tace ya jikin,yace wlh na samu
lfy. Koda suka gama hira dasu yah ibrahim alwala yayi yayi sallah sannan yace
mama tea zansha,ta had'a mishi yasha ya ajiye cup d'in yaci gaba da addu'oinshi
bayan nan seya kwanta akan sallayan a d'akin yah ibrahim dama tare suke
kwana,tofa kwanciyan kenan dabai tashiba. Yah ibrahim kuwa yana gum mama suna
hira,bayan sun gamane ya dawo d'akin yace abdallah a k'asa kuma,tashi ka kwanta
akan kafifar mana,shuru bai tashiba,kuma kowa yasan abdallah sam bayida nauyin
bacci,hakan yasa ibrahim tab'ashi amma seyaji baya numfashi. Salati ya kamayi
tare da girgiza abdallah amma babu abdallah ayau ya rigamu zuwa gidan da duk
wani musulmi seyaje dazanar lokacinmu yayi.
Allahu akbar,Allah yasa muyi irin rasuwan abdallah ameen.

Ana zaune agun makoki kowa juki yayi sanyi,idan aka tuna da karatunshi na asuba
cikin suratul muh'd. Kai jama'a duniya ba komai bace wlh,Allah ya gafarta mana
kurakurenmu ameen. Manosh se kallon hotunanshi yakeyi a wayanshi yana tsaye
tagun pool ya d'aga yatsan hannunshi d'aya wato ALLAH WAHID. kwalla manosh yaji
a idonshi amma sam yaqi zubar dasu,dan bayaso azabtar da abdallah,domin shi kuka

ga mamaci azabace ake k'arawa mamacin. Jama'a sosai abdallah ya samu kowa
alkhairai kawai kakeji abakinsa akan abdallah,hakan yasa yah ibrahim farinciki
sosai,domin shaidar duniya itace zata bika har lahiranka.
11:00am su manosh suka shiga cikin gidansu rash,inda suke zaune a rana suka
shigo da yah ibrahim sukayiwa mama gaisuwa dakuma rash harma da maryam,dan dole
agaida maryam saboda indai kasan abdallah tofa dole kasan maryam dan kowa
shaidane akan k'aunar da take tsakaninsu. Rash da maryam basu iya amsa
gaisuwanba banda kuka da sukeyi har'yanzu,haka suka fice tare dayiwa baban
maryam gaisuwa sannan suka tafi.
Haka dai akayita zuwa gaisuwa mutane ma'a magana.
Yau monday yaune uku dan haka su manosh da iyayensu sukazo hardasu dad,akayi
addu'an sannan sukayi musu gaisuwa suka wuce. Da hantsi su mum d'in manosh
danasu marwan harda miher da lubna sukazo gaisuwa. Kukan da rash takeyi yasa
duksuma suketayi. Miher tace ina yah ibrahim muyi mishi gaisuwa,samira ce ta
kirashi yazo suka gaisa harda lubna,tausayinshi ya kamata setaji sabon
k'aunarshi yana shiganta a hankali saboda wannan shine ranar farko da suka fara
ganin junaeye to eye,dukda dai dama tayi mishi gaisuwa a waya kuma tagayamishi
cewa zasuzo ranan uku. Yace mun gode sosai Allah ya bada lada,sukace ameen
sannan ya gaida mum nasu ya fita waje.

Rayiwa kenan yau wenesday bikin su maryam saura 2dys kawai. Manosh ya kira
maryam a waya haryau kuka takeyi,yace pls apple kiyi hakuri kibar kukan,batace
mishi komaiba se dan Allah ina neman alfarma a d'aga bikinmu se zuwa wani lokaci
pls? Shuru yayi yace ok apple zanyiwa baba magana kinji,tace nagode sannan ta
katse wayar. Manosh ya sami mahaifinshi da zance amma se mahaifinshi yace munyi
maganan da iyayensu amma sunce baza'a d'agaba tunda an sanar,sannan mamacin
bazai dawoba sedai idan akwai wani biki da zakuyi to duk kuyi canceling nashi
saboda rasuwan. Manosh yace to dad mungode sannan ya tafi tare da sake kiran
apple ya gaya mata,aise fashe da kuka sosai wanda ya d'aga mishi hankali da
sauri ya katse wayan cike da damuwa ya kira marwan suna magana,marwan yace eh
wlh ibrahim ma cewa yayi kawai ayi bikin baza'a d'agaba kuma wlh nima naso a
d'aga. Manosh yace to yaushe zamuje girei,marwan yace anjuma ba,manosh yace dama
ba'yi musu jeren kichineba kud'in nake son bawa apple ta sayi kayan kichine
sannan suje suyi jere amma yanzu komai ya tsaya kenan,marwan yace sedai muba su
mum kawai su k'arasa mana dan kaga ba time yanzu gaskya.
Haka kuwa akayi a ranan mum da 'yan'uwansu sukayi sayayyan kayan kichine abin
se wanda ya gani aka shirya komai tas zuwa 8:pm suka gama komai aka rufe gidan.

Ran alhamis da safe bayan an gama yiwa miher lalle tasa driver yakai mai zanen
lallen har girei dan ayiwasu maryam rash da samira. Dayake tana sauri nan danan
ta musu ta gama zuwa azahar ta gama musu,maryam tace nawane kud'inki,mai lallen
tace an riga da'an biyani zan koma,nan driver ya maidata gidansu miher aka
biyata kud'ade masu yawa aka kaita gun zahida da amina ma ta musu.
Bayan la'sar angwaye sukazo harda yusuf angon amina. Amare suka fito amma sam
babu wata walwala a fiskarsu,angwayen basu damuba dan sunso a d'aga auren amma
sam ank'i. Bayan sun gaisane kowanne yaja fefe da matarsa suna magana,yayinda
majid da muhsin da yusuf suke gu d'aya da yah ibrahim suna magana. Manosh yace
apple,shiru tayi dan sam setaji bata son auren. Yace babu wani abu da kike
buk'ata,tace babu komai tare da kwalla a idanunta,ledan hannunsa ya mik'a mata
dan dole ta karb'a yace kije gida zamu tafi muma amma pls kibar wannan
kukan,batace komaiba ta wuce gida batare data musu sallama ba. Manosh jikinsa a
sanyaye yace wlh ibrahim aurennan da d'agashi akayi se nan da 2month,gabad'ansu
baso sukeyiba wlh mutuwar abdallah kamar yau akayi suke jinta a jikinsu,muma
kuma haka wlh,muhsin yace wlh kuwa. Ibrahim yace haka Allah yayi karku damu
Allah yayi mishi rahama,suka amsa da ameen sannan suka tafi.

Bayan isha manosh ya kira apple,tace kayi hakuri pls da abinda nake maka ba
laifina bane,yace don't worry apple am okay with everything kinji,wlh naso abar
auren amma hakan baiyuba,tace hakane nagode,yace kidena min godiya apple am
sorry for d lost of our abdallah,shuru tayi hakan ya tabbatar mishi da cewa kuka
takeyi,yace apple are you okey? Tace "yeah am fine" cikin muryan kuka tace peach
gobene fa abdallah zaiyi karatu a walima,ashe fad'a kawai yakeyi...manosh yace
pls stop it apple,babu abinda zai canja zauyi walimar kuma karatun abdallah zamu
saurara agun insha Allah. Tace thankyou so much peach,yace "anything for apple"
_i love you so much_,tace me too. Dad'i yaji yace ki huta kinji gud nyt,tace
thankyou.

Lubce agun doctor da safiyar friday taje ayi mata gwajin jini ko tana d'auke da
H I V. Amma sam babu komai Allah ya kareta,murna sosai tayi tare dayiwa Allah
godiya,bayan ta kira yah ibrahim ta gaya mishi komaine,seta kira maryam ma.
Murna sosai maryam tayi tace shikenan barka lubna,tace nagode maryam bazan manta
dakeba sannan ina tayaki murnan zama matar bro manosh,maryam cikin hawaye tace
nagode.
Bayan sallan juma'a aka d'aura auren masoya 6 a babban masallacin jumma'a dake
jimeta,inda angwaye sukasa jallabiya ash da lullub'i irin na larabawa,sunyi kyau
sosai kuma suna cikin wani ni'ima mara misaltuwa amma dukda haka manosh da
marwan akwai damuwan rashin abdallah sossi a fiskansu,bare kuma da suka san
halin da matansu suke ciki a yanzu haka kuka sosai sukeyi an kasa rarashinsu dan
ansanma bajin rarrashin zasuyiba dan haka akabarsu suyi mai isarsu....
[7:12am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: 🍭🎈AUNTY'N YARA🍧🎁AUNTY'N YARA🍧🎁

Written by sad-nas
&
Hama gee muhd

*dedicated 2 iman muh'd alee*❤💕
❤)*

53-54 Hankalin manosh ya kasa kwanciya seya sake kiran maryam,daidai lokacin da
yapendo ladi tayita mata nasiha har tayi shuru sannan ta barta. Wayan ta d'auka
tare dayi sallama,yace aunt ina fata kin dena yin kukan,tace eh,yace gud pls
kiyi hak'uri komai ya wuce da akwai yadda zanyi inganki yanzu dana zo,tace
bakomai,yace inatayamu kasancewa miji da mata yau,murmushi tayi tace nima
haka,dad'i sosai yaji yace gaskya an cika sosai dayake kuma jumma'a mun samu
jama'a harda wanda ba'a gayyacesuba,mirmushi tayi tace to Alhamdulillah ina
gaida angwaye,yace apple,tace na'am,yace i luv u apple,wani iri taji yadda yayi
maganan tace me too.
Yace semunzo anjuma ko akwai abinda kike bukata,tace eh akwai yace menene,tace
flower,murmushi yayi yace zan kawo miki anjuma idan nazo d'aukan matata,tace da
kanka,yace yes ba matatabace,tace eh amma ai da manya zamu,zauna a motan,yace
a'a nidai dagani seke,dariya tayi tace a'a nidai manya nafiso,ok bakya son
inkaiki ko,toshikenan nibazan zobama nayi fushi. Tace haba fushi kuma dani,yace
yes se anjuma bari mu gaisa da friends na dad,tace ok pls karka manta da

flowernah,yace indai bazan manta dakeba to hakama flowern,murmushi tayi shima
haka sannan sukayi sallama.
Nasiha sosai akayiwa amare harma da angwaye musamman manosh ance dole yabar
maryam taci gaba da karatunta,yace dukya amince harda sa hannu kuma ya rubuta
cewa maryam itace matarsa ta farko kuma ta karshe babu k'arin aure tare dasa
hannunsa dana mahaifinsa akabawa babanta takardan da kuma malamanta se kuma
iyayen manosh d'in.

Da dare bayan sallan isha aka had'a walima ta maza agu d'aya, inda akasa karatun
abdallah ne kawai yake tashi agun ga malamai da angwaye da abokai dadai jama'a
sosai,masu kuka sunata kukansu,harda su maryam dan angwayen sun kirasu a waya
donsu saurari walimar. Karatun abdallah yakai awa daya sannan malam balalau yayi
musu wa'azi sosai tare dayiwa abdalla addu'oi akaci abinci maiji da lfy aka sha
aka k'oshi sannan aka rufe taro da addu'a.
Bayan an d'an watsene aka fara shirin zuwa d'aukan amare. Nidai bazan iya irga
motocin da sukazo d'aukan maryam rashida da kuma samiraba,dan tun daga titin
daya shigo unguwansu maryam wata *holmare*acike yace tun daga k'arshen layinsu
har kan titi,wasu motocinmma emty suka koma. Ko wacce amarya da manya aka
had'ata wanda yapendo ladi itace k'anwar mama maryam,se kuma goggo hafsatu itace
k'anwar baban maryam,dayake maryam mai jama'ace hakaaka wuce da kowace amaryam
katafaren gidanta tare da jama'anta.
Masha Allah kawai kakeji kota ina ana yaba gidajen amaren,tare da wanke ido suna
kallo. Abokin manosh ne yayi musu jagora har sama inda d'akin maryam yake,shi
kuwa manosh ango yana tajin farinciki sosai a ranshi yau ya mallaki maryam apple
nashi se godiya yakeyiwa Allah. Maryam tana zaune a gadonta na alfarma ita kanta
tana cikin farinciki sesai akwai damuwan rashin abdallah wanda har a yanzu kuka
takeyi data tuna zuwansu gidan tare. Bayan anga gida anyi san barka masu cire
kauyanci sunyita fama se dariya akeyi masu d'aukan pic sun d'auki ko ina a
gidan,gefen manosh ne kawai basuje dan a rufe yakema. Haka aka sake maidasu
girei se mutane kad'anne kawai a gidan amaren,sayayya angwaye sukayiwa amare da
kuma wanda suka rakosu nan aka kawo musu,inda abokin manosh yace wannan wai na
amaryarmuce,wata ta karb'a tare dayin murmushi tace to amarya tagode sannan ya
tafi ita kuwa taje ta kaiwa maryam a d'akinta.
Koda maryam ta bud'e amincine a take away ga kuma nama mai zafi da drinks,dama
yunwa takeji dan haka ta taci sosai tayi hamdala gashi naman yayi mata dad'i.
11:00pm manosh ya kira number maryam ta d'auka lokacin su yapendo sunyi bacci
dukkansu a d'aya d'akin bak'in da kuma palonta,ita kad'ai ce a d'akinta se
friends nata 2 koma ince 'yan'uwanta yaran yapendonta da kuma goggonta sune
mazaunin k'awayenta. Ta d'auka tare da cewa hello,yace apple kinyi bacci ne,tace
zanyi dai,yace su goggo fa,tace duk sunyi bacci,yace ke kad'aice idonki biyu? Ta
juya ta kalli nafisa da hadiza da suke kwance a k'asan kafet suna waya da
mashinshinansu,tace eh sedai kawayena biyu sune idonsu biyu,yace ok ina son
ganinki pls,tace to kana ina,yace ina d'akina na k'asa,tace to ina zuwa tare da
katse wayar. Nafisa da hadiza sukace wato bazai iya hakura mu tafiba gobe
ko,kunnuwansu maryam taja tace kawai danyace inje shine har kuke fassara wani
abu,to Allah ya shiryeku ta wuce a hankali dan kar su yapendo suji,su hadiza
kuwa se dariya suke mata suna binta da kallon tsokana.

Da sallama ta shiga,ya amsa yana zaune akan gadonsa da kayan ball masu dogon
hannu. Tana tsaye tace gani,kallonta yakeyi tun daga k'asa har sama,dan rigan
baccine a jikinta riga da wando dogo kuma himar nata har k'asa ya sauka sedai
yana iya hango kayan jikin. Kunya taji sosai kanta na agefe,yace bazaki
k'arasobane,ahankali tace daga bakin gadon ta zauna tare da cewa gani,yace
fruits nakeso ki yankamin pls aunt,murmushi tayi tace to ina suke,yace nakai
miki kichine,tace ok tare da mik'ewa ta ta fita cikin jin kunya shi kuwa yanata

binta da kallo. Kichine ya burgeta sosai,da irin abubuwan dake ciki,tirai
k'arami ta d'auko ta goge da karamin towel data gani an jerasu dewa sannan ta
d'auki wuk'a ta yanka mishisu kamar yadda ta saba sedai yau batayi zanen
fiskanshi dasuba ta wanke hannu takai mishi tare da sallama. Lokacin yana gyara
gashin kansa seya juyo tare da k'arasawa gunta ya karb'eta yana kallon friuts
d'in ba amar yadda ta saba mishi,kallon juna sukayi a tare suna rik'e da tirai
d'in,kunya taji se tayi saurin kawar da kanta gefe tana murmushi,yace rik'e
kayanki nibazan shaba tunda bakyaso inshane,rik'e tirai d'in tayi tace kayi
hakuri bawai hakabane,yace banci abincibafa friuys d'in kawai nafibuk'a kumani
wannan yamin kad'an,murmushi tayi tare da juyawa ta fice,shima murmushin yakeyi
yana kallonta.
Bayan 2minit ta dawo ta ajiye mishi akan stul d'in mirrow shi tana kallon
fiskanshi,se murmushi yakeyi dan kuwa tayi zanen fiskanshi da friuts d'in abin
yana birgeshi sosai. Kallonta yayi tana tsaye bata zaunaba,hannunta ya kamo yace
bazaki zaunabane,tace eh zan komane,yace ina kenan? Tace d'aki,yace bazakije ko
inaba anan zaki kwana,k'irjinta ya buga tace a'a nidai zan tafi sakeni dan
Allah,ai kuwa seya janyota ta fad'o jikinsa kan cinyarsa,hannayenta tasa ta rufe
fiskanta dan kunya dataji,murmushi yakeyi tare dashan fruits nashi baice da ita
komaiba. Kunya sosai taji,gashi ta kasa tashi kuma tak'i bud'e fiskanta tana
zaune kan ciyarsa,setaji yasa hannunshi akanta ya manna kanta da k'irjinsa yace
idan bacci kikeji tokiyi baccinki ajikina kinji,tmaryam kamar ta nitsi dan kunya
aranta tace qato dama manosh ya iya soyayya haka,tace wlh inaso in koma
d'akine,bana so su yapendo susan nafito,yace saboda me,aiko sun sanima bazasuce
miki komaiba sunsan na zama mijinki yanzu. Tace dan Allah ka barni in tafi,yace
tosekin bud'e fiskarki,ba musu ta cire hannayenta amma tak'i su had'a ido,shidai
friut kawai yaketasha bayama kallonta sam,hakan ya bata daman satan
kallonshi,murmushi yakeyi da sauri ta sunkuyar da kanta,yace aibase kinyi satan
kallonaba kiyita kallona bakomai na zama naki yanzu,kunya taji tace pls ina so
in tafi kayi hakuri,yace zaki tafi amma sena gama shan friut,shuru tayi tare da
juyawa tana kallon friut d'in wanda ko rabi baiyiba,kanta ta d'ago tana
kallonshi tana ganin yadda friut d'in yake wucewa a mak'ogoronshi,dariya yayi
tare da sunkuyo da kanshi suna kallon juna,tayi saurin kawar da kanta shikuwa
yace meyasa kike son kallonane apple nifa banso wlh,ita dai batasan meyasa
bayaso tadinga kallonshiba,tace to kabarni in tafi bacci nakejifa,yace ainagaya
miki sena gama kozaki kwanta akan gadon inna gama se'in rakaki,tace a'a dan
tanajin dad'in turarenshi sosai kuma bataso ta kwanta kar bacci ya d'auketa.
Manosh yaci gaba dashan friut tana satan kallonshi a hankali,fiskanta taji ya
rik'o batayi zatoba yace banace miki banason kina kallonaba, tace bazan
sakeba,yace b'ude bakinki in baki kankana,tace nakoshi,yace idan baki shaba anan
zaki kwanafa,ido ta d'ago tana kallonshi,yace yes am serious apple,ba musu ya
d'auko yankakken apple yasa a bakinshi sannan ya rik'o fiskanta suna kallon
juna,kunya taji kuma babu yadda zatayi wani irin kallo mai kashe jiki yake mata
hakan yasa ta nutsu,ya kawo bakinsa mai d'auke da apple d'in daidai saitin
bakinta wanda ita kanta basan lokacin data bud'e bakinta d'an kad'an yasa mata
apple d'in yana gutsuransa ahankali ita kuwa rufe idanunta tayi tana jinshi
saura kad'an abakinta seya cire bakinshi yana kallonta idanunta a rufe dan kunya
da wani yanayi da takeji,idanunta ya tsunbata tare da kwantar da kanta a
k'irjinsa yayi magana cikin wani irin murya yace kici sauran kinji,ba musu ta
faraci idonta a rufe,sedata cinye tace" zan tafi" cikin wani murya mai shigan
jiki,yace bazaki tafiba sena gama kiyi hakuri kinji,shiru tayi bata sake d'ago
da kantaba tana kwance a k'irjinsa harya gama,seyace nagama to muje in rakaki?
Kanta kawai ta d'aga alamun eh,yace to d'ago fiskanki,sam ta kasa,hannunsa yasa
ya d'agota yana kallon fiskanta tare da tambayarta meyafaru apple,tace bakomai
kamar zatayi kuka,kwantar da ita yayi akan gadon tare da mik'ewa ya kashe wutan
d'akin,ya dawo gunta tare da kwanciya akanta ya rungumeta sosai,kuka ta fara
tace dan Allah ka barni in tafi,yace apple ki dena kuka bazan miki komaiba
kibarni a hakan "for some minit pls" apple ya k'arasa maganar akunnenta. Shuru
tayi amma k'irjinta se bugawa yakeyi gashi yayi mata nauyi kafad'arsa take
bugawa ahankali tana cewa peach pls cikin muryan shagwab'a,bakinsa kawai taji
acikin nata yana kissing nata,ahankali itama ta fara kissing nashi se k'ara
matseta yakeyi wanda shi kanshi yakejin tausayin. Jikinta taji ya jik'e yayinda
take jin yadda abu yake fitowa daga jikin manosh,tsoro taji sosai,se bayan

2minit ya saki bakinta tare da barin jikinta ya kwanta a gefe yana sauke
numfashi,da sauri maryam ta mik'e zata gudu yayi k'ok'arin kamo hannunta amma
hartakai gun kofa,mik'ewa yayi ya cafkota tare da rungumeta sosai yace "thankyou
apple" kiyi hakuri kinji,batace komaiba,seyayi peacking kunnenta yace i luv u
apple,tace i luvu too,sake matseta yayi sosai sannan ya saketa tareda bud'e
kofan yana rik'e da hannunta hargun steps sannan yace mata gud nyt,kai tad'aga
mishi sannan ta hau sama dasauri yana binta da kallon sannan shima ya wuce
d'aki ya shiga toilet yin wanka.
Maryam taga harsu nafisa sunyi bacci,dan haka ta wuce toilet ta gama komai
sannan ta fito ta mayar da kayan data ciren don karsu nafisa su mata tsiya da
safe,sannan ta kwanta tana tuna abinda ya faru tsakaninta da manosh tace wato
yanzu harya gamsu kenan a hakan tunda dai gashi yafitar da maniyi? Hmmm se kuma
taji dad'i aranta tace wato dai ya iya soyayya amma shine kamar ba
ruwanshi,murmushi tayi aranta tace i love you so much peach,da haka bacci ya
d'auketa.............
[7:12am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: 🍭🎈AUNTY'N YARA🍧🎁AUNTY'N YARA🍧🎁

Written by sad-nas
&
Hama gee muh'd

*dedicated to aunty binta* _matar bro_❤)*❤)*❤)*

55-56 Washe gari da asuba maryam ta tashi tayi wanka tare dayin alwala tazo tayi
sallah sannan ta zauna shafa mai ta shirya tsap

Please Login or Register in order to submit comment