Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tak'i d'aunkan call
d'n nashi har sau 3.

Bayan azahar ya sake kiranta seta d'auka hello,yace apple ina kiga shiga
haka,tace sorry bacci nakeyi dan kaina da yake ciwo,ya kake yasu mama,yace eyyah
sorry apple ya jikin naki,tace da sauki sosai,yace zanzo da yamma kinji,tace to
nagode sekazo.

Dab la'asar manosh yazo abdallah yana kiran sallah,alwala yayi yayi sallah
sannan suka zauna hira da abdallah inda yake tambayarshi ina marwan,makosh yace
yana gun aiki,nan dai sukai ta hiransu manosh se dariya yakeyi seda aka watse
sannan maryam ta fito babu ko fara'a a fiskanta.
Ta k'arasa da sallama,suka amsa sannan abdallah yace auntyn yara yanaganki haka
babu ko murmushi, tace bakomai abdallah banajin dad'ine,yace sannu Allah ya baki
lfy,tace ameen sannan ya kalli manosh yace toni zan tafi seka sake zuwa,manosh
yace to bari na baka sako,yace to,sannan manosh ya bud'e motarshi ya fito da
leda da gani kayayyaki ne a ciki yan kanti ya mik'awa abdallah. Abdallah ya
karb'a yace wazan kaiwa?manosh yace nakane na baka kyauta,godiya sosai abdallah
yayi yace auntyn yara ki tayani godiya,mirmushi tayi tace mungode Allah ya saka
da alkhairi suka amsa da ameen sannan abdallah ya tafi.
Maryam tace ko zamu shiga cikin gidane,yace yau kuma,tace eh ko kuma muje zaure
in shinfid'a maka taburma wlh bana jin dad'ine,manosh yace amma kinje hospital
ne,tace banjeba dan ko su mama basu saniba,yace tomeyasa,tace babu
komai,kallonta yakeyi tun daga sama har k'asa sannan ya d'auki wayarsa ya kira
muh'd ya gaya masa cewa inda hali yazo girei ya duba apple nashi sannan ya katse
wayar tare da cewa to muje zauren karki fad'i min anan,murmushi tayi sannan ta
wuce gaba shi kuwa ya fito da sayayyan fruits daya mata da sauran abubuwan
kwad'ayi yabi bayanta lokacin taje d'auko taburma da karamin carpet ta shinfid'a
mishi carpet din ita kuwa ta zauna a taburman.

Sam tak'i kallon manosh dukda dai tana son ganinsa dan yau red top ne a jikinsa
da black jeans se kamshi yakeyi. Shi kuwa kallonta yakeyi sosai,can dai tace
meyasa ka kira muh'd ai naaha magani,shuru yayi kamar baijitaba yana ci gaba da
kallonta,da taga yayi shuru seta d'ago da kai tana kallonshi suna kallon
juna,murmushi tayi tace nika dena min irin wannan kallon bana so,yace tobase ki
hananiba,mik'ewa tayi taje ta yanko mishi kankanan daya kawo mata dasu apple ga
greves dadai sauransu tayi jerensu a tirai kamar fiskan manosh sannan taje ta
ajiye mishi ta yadda zai gane fiskanshi tayi drawing. Mamaki sosai yayi yanata
kallon drawing d'in danya burgeshi sosai harya bashi sha'awan ci,amma kuma
bayaso ya b'ata drawing d'in,kawai setaga ya d'ako wayanshi yanata d'aukan pic
din friut d'in.
Bayan ya gamane yace fiskan waye kenan wannan,tace na wanda zaisha,dariya yayi
wanda ya k'ara mata sonshi azuciyarta,yace haka fiskana yake kenan? Tace eh amma
dai fiskanka yafi wannan kyawun gani. Dad'i sosai yaji amma baice mata
komaiba,wayansane ya fara ringing ya d'auka ok bari na fito. Kallonta yayi yace
bari muh'd ya shigo kuma ki tabbata kin gayamishi abinda yake damunki kinji ko,
mamaki sosai tayi har mh'd yazo kenan,tace to sanna ya fita suka shigo tare.
Muh'd yayi sallama ta amsa sannan suka zauna tace ina wuni,yace lfy lau aunty ya
jiki ashe bakiji dad'i ba,tace eh amma da sauki,manosh yace ba wani sauki wlh
dairewa kawai takeyi danko a gida basu saniba. Muh'd yace haba aunty pls kidena
wasa da rashin lfyanki karki sawa kanki ciwo kinji,mirmushi tayi tace kainane fa
dama kuma nasha paracetamol,manosh yace towayace kisha? Murmushi tayi tare da
kallonshi cikin zolaya sannan ta taahi ta wuce gida. Manosh yanata binta da
kallo,muh'd yace haba prince irin wannan kallo haka,manosh yace wlh bata da lfy
daga ganinta daurewa kawai takeyi pls ka gwadata sosai. Muh'd yace "calm down
dude" zata samu lfy insha Allah. Faro mai sanyi ta kawo musu sannan ta
zauna,muh'd yace mungode amma wannan fiskan yamin kyau kamar fiskana. Dariya
sukayi dukkansu,manosh yace a'a kaje can samira ta maka naka wannan fiskan
nawane kuma bazaka ciba,dariya mh'd yayi tare da d'aukan inibi d'aya yasa a
bakinsa yace shikenan zanen ya b'aci. Manosh yace gaskya baka kyautaba,memakon
ka jira in fara sha kafin kasha,mikewa maryam tayi ta sake d'auko inibi tazo ta
mayar inda mh'd ya cire sannan tace shikenan magana ya k'are.
Dariya sukayi sannan manosh ya far sha cikin nutsuwa take satar kallonshi,dan
bai tab'a cin wani abu suna tareba se yau.

Muh'd yace nagode aunty gaskya abin ya burgeni nima zance samira ta dinga min.
Manosh yace copy copy,murmushi sukayi sanna muh'd yace aunty meke damunki ne?
Tace wlh ciwon kaine kawai,k'irjinta yana mata ciwo amma sam tana jin kunyan
cewa harda k'irjinta. Muh'd yayita tambayoyinta tana bashi amsa sannan yace ok
ina zuwa bari inje inzo,manosh yace akwai wani damuwane,yace no bakomai sena
dawo sannan ya tafi.
"Manosh yace kin tabbata abinda kike ji kenan?"
"Tace eh kanta na kallon wani gefen"
"Manosh yace apple bana so ki b'oyemin komai imma kina jin kunyan muh'd toki
gayamin tunda baya nan"
Maryam taga bazata iya b'oyewaba dan yadda take jin k'irjinta,setace da k'irjina
yana min ciwo sosai.
"Kallonta yakeyi cikin damuwa,dan yana lura da yanayinta yasan tana jin ciwo
tadai k'i fad'ane kawai.
"Sunanta ya kira a hankali yace apple?
Kanta ta d'ago ta kalleshi har idonta yayi jah tace na'am tare da sunkuyar da

kanta,yace se kuma inane yake miki ciwon? Tace shikenan....bata gama k'arasawaba
taji cikinta ya kame kamar an soka mata wani abu,innalillahi wa'inna
ilaihirraji'un taketa nanatawa a zuciyarta.
Manosh yace ya kikayi shuru,tace bakomai ina zuwa,bata jira mezaiceba ta mik'e
ta wuce gida yana binta da kallo. Koda ta k'arasa gun mamanta ta wuce a d'aki ta
cire doguwar himar nata ta fad'a kan gado tana cewa mama cikina ya kameni sosai
yana min ciwo. Hankalin maman ya taahi sosai tayi kanta tana mata sannu tare da
tofa mata addu'oi,tace bak'on ya tafine? Cikin jin ciwo take magana tare da kame
cikinta tace basu tafiba suna zaure.
Mama ta rasa yadda zatayi seta d'auki wayanta ta kira baban maryam ta gaya mishi
komai,shima hankalinsa a tashe ya kira number yah ibrahim yace lallai yaje gida.

Bada b'ata lokaciba yah ibrahim yazo a zaure sukaci karo da manosh. Su gaisa
sannan yace ina maryam d'in? Manosh dabaisan komaiba yace ta shiga ciki,yah
ibrahim yace kasan bata da lfy,yace eh na sani harma abokina ya dubata yanzu.
Kan yah ibrahim ya d'aure seyace bari in shiga ciki dai dan yanzu babanta ya
kirani yake cemin bata da lfy sosai cikinta na ciwo,a razane manosh ya mik'e
yace ciki kuma,tacewa yanzu kenan ko,ibrahim yace eh sannan ya wuce ciki akabar
manosh cikin damuwa sosai.

Maryam se juyi takeyi tana addu'oi,har ya ibrahim yayi sallama,mama ta fito tace
bari na fito da ita sannan ta koma tasawa maryam himar,shi kuwa yah ibrahim da
sauri ya kira rash a waya yace tazo yanzunnan kuma cikin shiri.

Bada b'ata lokaciba sega muhammad yazo sakamakon wayan da manosh yayi mishi. A
tare sukazo da rash ta gaishesu sannan ta wuce ciki,maryam ta fara hangowa babu
yadda take mama tana rik'e da ita ita maeyam bata iya ko mik'ewa tana sunkuye
kuma rik'e da cikinta.
Da sauri rash ta k'arasa ta riketa sosai tana mata sannu. Hankali mama a tashe
tace gaskya zan biku muje asibitin nan dan hankalina zaifi kwanciya,waya tama
baban maryam,sannan ibrahim yaje ya sanar dasu manosh komai,se manosh yaba
ibrahim keyn motanshi yace ya d'auki su mama a ciki shi kuma zasu tafi da muh'd.
Haka kuwa akayi su manosh suka tafi shida muh'd sannan ibrahim ya bud'e musu
motar, da sauri abdallah yazo dan yadda yaga mama da rashida suna rik'e da
auntyn yara,baice komaiba ya karasa yace lfy mama,tace wlh maryam ce ba lfy
zamuje asibiti. Subhanallah nima zan biku, ibrahim yace shiga baga to,abdallah
ya shige gaba su mama kuwa suna baya suka kama hanyan jimeta.

Asibitin da muh'd yake aiki sukaje, aka wuce da ita kai tsaye. Ae a lokacinne
manosh da muh'd suka gaida mama sannan muh'd ya wuce duba maryam.
"Yana shiga rashida ta fito ta wuce gunsu mama,shi kuwa manosh kunya sosai ya
kamashi gaahi k'ananan kayane a jikinshi,nan ya kira su majid cikin k'ank'anin
lokaci suka zo dukkansu ukun.
Marwan majid da muhsin sukaje suka gaida mama sannan suka gaisa da ibrahim.
Rashida tana gefe ita da abdallah sannan marwan ya k'araso suka gaisa ranta a
b'ace,amma seya d'auka kodan rashin lfyan maryam ne.

Muh'd ya fito su manosh suka k'arasa da sauri donjin meke damunta harda yah
ibrahim d'in da abdallah. Mama da rash kuwa suna tsaye a gefe guda.

Muh'd yace *ulcer* kawai babu wani abu, kuma dole zata zauna a asibiti dan se'an
k'ara mata ruwa har leda biyar. Sannan yayi mata allura yanzu dan har tayi bacci
ma, ibrahim yace to mun gode kayi duk wani abunda ya dace pls yanzu medame ake
buk'ata? Muh'd yace haba aiba komai wlh already nasa mata ruwan karka damu babu
wani abu da ake buk'ata kudai tayamu da addu'a kawai. Godiya sosai ibrahim yayi
sannan yace bari naje na sanar da mama dan hankalinta a tashe yake,muh'd yace
muje inyi mata bayani.
Bayani sosai muh'd yayiwa mama tare da cewa ta kwantar da hankalinta maryam zata
samu lfy insha Allah. Godiya mama tayitayi sannan ya tafi gunsu manosh.
Manosh yace zan iya ganinta,majid yace jeka ka kanga inba hakaba ai bazamu gane
hankalinkaba ad'an lokaci kad'an kashi harka fita hayyacinka kamar ba sojaba,
dariya sukayi baima kulasuba ya wuce d'akin tana kwance babu himar a jikinta se
atamfa d'inkin doguwar riga daga sama ya bada shape amma k'asan a bud'e yake.
Karon farko kenan da manosh yaga maryam babu himar ajikinta,mara ce sosai gata
'yar karama bata da jiki sam,amma k'irjinta a cike suke. Bai k'arasaba ya janyo
k'ofar ya koma gunsu majid yace muje ko,dan muma mamanta damar shiga, haka
sukayi musu sallama suka wuce yacewa ibrahim ya rik'e key din motarsa dan zirga
zirga,amma sam ibrahim yak'i seda ya bashi key din,shi kuwa manosh ya karb'a
suka tafi.

Auna tfya mama da rash suka wuce d'akin da maryam take harda ibrahim da
abdallah.
Tausayin maryam ya kama rsah sosai tayi dana sanin gaya mata kallomin jiyan
dukda dai tasan bashine silan rashin lfyanba amma tana k'aunar maryam a ranta
sosai.
Manosh kuwa ya gayawa mum nashi da kuma miher,sannan yacewa dad nashi yana so ya
bashi kyautar mota guda d'aya dan zaibawa su maryam ne dan abinda ya faru yau,da
baijeba kenan se sunyita neman motan hawa. Dad d'in manosh business man ne sosai
kuma yanda gidan saida motocin,sannan yana k'aunar manosh sosai,dan haka yace
manosh yaje ya d'auki duk motar da yake buk'ata. Godiya sosai manosh yayi dama
suna hira da abdallah sosai kuma abdallah ya gaya mishi motar da maryam take so
saosai a ranta shine *307 red* dan haka ya wuce yaje ya d'auko mata red d'in
kuwa guda d'ayan kenan ya rage aka rubuta sunan maryam akan takardun da komai
sannan yazo dashi gida ya nunawa mum da miher sukaita murna tare da addu'oi yace
bari ya watsa ruwa sesu tafi shida miher...
[7:10am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: 🍭🎈AUNTY'N YARA🍧🎁AUNTY'N YARA🍧🎁

Written by sad-nas
&
Hama gee muh'd

*dedicated to seemby luv &

leemcy*😘😘

31-32 miher tayi shiga na alfarma,daidai nan lubna ta kirata a waya tana

tambayanta ya maganan zuwa tambayane nasu bro manosh,nan miher take gaya mata
cewa ai maryam bata da lfy tana hospital d'in su bro muh'd yanzu hakama ina
jiran prince ya fitone mu tafi.
Lubna tace eyyah Allah ya bata lfy,a ranta kuwa tace Allah yasama ta mutu.
Koda wasa lubna bata gayawa miher cewa tasan maryam ba,kuma bata yiwa miher
tambayoyi akan maryam d'in sam,dan gudun zargi.

Manosh ya fito
mik'awa mihaer
yau bro manosh
*307*din apple

cikin shigar indians da blue sari na maza yayi kyau sosai,ya
key d'in *benz* nashi yace taje zai bita a baya. Mirna sosai tayi
yabarta tayi driving da kanta. Tana gaba yana binta a baya da
nashi.

*Atiku abubakar mall* suka nufa inda manosh ya kashe kud'i sosai harta flaks
seda suka saya mata da cups su plate dukdai wani abu da zasu buk'ata a hospital
haka mihar tayi ta d'auka, se kallonsu akeyi don yadda sukayi kyau shi kuwa
captain ko dariya bayayi se amsa waya da yakeyi. Mihar tana biye dashi bayan sun
biya kud'ine suka tafi tana gaba yana binta a baya har,suka isa hospital d'in.
Lokacin yah ibrahim da abdallah sun koma girei domin suyiwa maman rashida bayani
kuma tayi abinci dasu. Manosh yacewa miher ta shiga idan maman maryam bata
d'akin tozai shigo,ai kuwa seta shiga da sallama da kuma kayayyaki sosai a
hannunta har rashida ta tayata da wasu,sannan ta sake komawa ta kwaso sauran
nanma seda rash ta tayata sannan suka gaisa maryam tana bacci har yanzu,mihar
tace yamai jiki,rash tace da sauki wlh,tace Allah ya sauwaka mama fa? Tace mama
sun fita da baba amma inaga sun kusa dawowa.
Da sauri mihar ta fita taje ta sanar da bro manosh,kafin su shigo maryam ta
farka tana cewa mama zansha ruwa,dama yah ibrahim yad'an sayo abin tab'awa
kad'an dan haka rash ta mik'a mata ruwan tasha sosai sannan ta koma ta kwanta
rash tana mata sannu da jiki,tace yawwa.

Manosh da mihar suka shigo da sallama,kunya sosai maryam taji tace rash mik'amin
himar d'ina,da sauri tad'an rataye matashi a k'irjinta sannan suka k'araso.
Rash suka gaisa da manosh yace ya mai jikin,tace da sauki yace to Allah ya bata
lfy tace ameen sannan rash tace mihar mud'an basu guri ko,tare suka tashi suka
fita sannan yazo ya zauna akan kujeran da yake kusa da gadonta yana kallonta.
Kunya sosai taji ta dai daure ta tashi ta zauna tare da gyara rufe jikinta tace
ina wuni,kallonta kakeyi tare dajin k'aunarta yana ratsashi yace lfy apple ya
jiki,tace da sauk'i.
Yace wato dama kina jin jiki shine kika cemin kaine yake miki ciwo ko,mirmushi
tayi tace amma ai da sauki yanzu. Yace drip d'in harya k'are ne? Tace eh yace se
bayan isha za'a samin wani,yace ok Allah ya baki lfy apple,tace ameen tare dajin
kunyanshi sosai danba himar a jikinta dukda dai ta rufe jikinta amma yana iya
hango kananan kitson dake kanta gata da bak'in gashi.

Ya maida kallonsa kan wayanshi yace ina wayanki,nan ta mik'a mishi ya karb'a ba
tare daya kalletaba ya shiga galary, pic d'in da rashida tayi mata da kayan daya
saya matane ya gani pic d'in sun mishi kyau sosai atake ya turasu zuwa wayanshi
sannan yasa mata credit na 3k seya mik'a mata yace kimin kyau a hotonnan ya nuna
mata wayanshi.
Murmushi tayi tace nagode meyasa ka tura baka sanar daniba,yace tokiyi hakuri
bazan sakeba. Batace komaiba se kuma tace nagodefa da d'awainiya Allah ya saka
da alkhairi,shuru yayi kamar baiji metaceba yana ta dannan wayanshi.

Ita kuwa se kallonshi takeyi dan yadda yayi kyau sosai. Batate daya kalletaba
yace apple nifa bana so ayita kallona,kinya sosai taji dan tasan bai
kalletaba,tace nifa ban kallekaba,yace kin kalleni mana aina ganki,tace ta ina
kenan yace ta idona mana, dariya tayi tana ci gaba da kallonshi se wayanshi yayi
k'ara ya d'auka yadai miher,tace bro mum da dad nata sun dawo dayake sunsan kana
ciki se basu shigoba,yace ok tnx sannan ya katse wayar tate da mik'ewa tsaye
yana kallonta. Itama shi take kallo tace ina zakaje,yace zan tafi in barki ki
huta mana,kawai jin bakinta tayi tace mishi pls karka tafi yanzu,yace meyasa
bakya so in tafi,tace haka kawai,ka zauna kamin hira.
Ba musu ya koma ya zauna yaci gaba da danna wayanshi yana magana batare daya
kalleta yace su mama sun dawone kuma suna waje shiyasa nake so in tafi dama ina
son inga baba. Tace to ai bakomai suma bazasu shigoba inhar sunsan kana
ciki,yace eh hakanne yasa zan tafi ai. Yanayin manosh yana burgeta sosai da wasu
irin abubuwansa,sam seyaso kallonta kafin ya kalletan,sannan kamar bakoda yaushe
yake son magana ba. Shuru tayi tanata kallonshi sosai tana yaba kyansa a
ranta,seyace tunanin me kikeyi apple,shuru tayi,yace pls ki dinga cin abinci
sosai sannan ki dena cin yaji dan abdallah yacemin kina cin yaji sosai. Mamaki
tayi sosai,tace yaushe kukayi hira dashi haka,yace ina ruwanki,tayi murmushi
tace to zan dena insha Allah tunda yana nemar yimin illa. Manosh ya mik'e yace
apple am goying amma zanyi missing naki wlh yau bazamuyi hiraba kenan tunda mama
tananan bazan iya kiran wayankiba amma zan dawo safe kinji, tace to nagode
sosai. Yace Allah ya baki lfy tace ameen sannan ya nufi kofar fita,harzai bud'e
kofa tace eeem....tsayawa yayi cak tare da juyowa yace yes akwai wani abu
ne,mirmushi ta mishi tace bakomai seda safe,shima murmushin ya mata tare da cewa
idan akwai ki gayamin,tace akwai abinda nake so amma zanyi maka texsn,yace ok
ina jira sannan ya fita.

Manosh ya gaida mama cikin girmamawa sannan ya gaida da baba tare da cewa dama
yana son magana dashi,daidai nan yah ibrahim yazo da abinci sosai a kwando suka
gaisa sannan ya wuce.
Miher da rash suka shiga da mama sega yah ibrahim,miher ta gaishesa sannan ya
ajiye abincin tare da cewa aunty ya jikin dai,tace da sauki sosai,yace to Allah
ya baki lfy tace ameen sannan ya fita gunsu baba inda suke magana da manosh.
Godiya sosai baba ya dingayi tare da cewa ibrahim kagafa mota ya kawowa maryam
wannan kyauta yayi girma dewa wlh dukda dai kace mahaifinkane yayi mana mun gode
sosai,nanma ibrahim yayi godiya sosai,sannan yaje ya kira mama itama baba ya
gaya mata godiya,sosai sukayi wanda baizai misaltuba,manosh yaji dad'i sosai a
ranshi sannan ibrahim ya rakashi hargun motarshi sukayi sallama,sannan ya kira
miher a waya,nan ta musu sallama tace zasu da mum nata da safe,rash ce ta rakata
har wajen mota sannan suka tafi.

Koda baba ya gayawa maryam kyautar da manosh yayi mata da taimakon babanshi
mamaki sosai tayi,babanta ya nuna mata takardun motan dukda sunanta a jiki,dan
kunya bata iya cewa komaiba anata tayata murna sannan baba yace zasu tafi shida
ibrahim seya tuk'a motar maryam d'in shi kuwa baba yahau nashi suka tafi ibrahim
yanata mamaki.

Manosh yayiwa maryam texs kamar haka
_am still waiting my apple_
_akan abunda kike so_
Koda maryam ta karanta setaji a yanzu kam bazata iya cewa komai se tace

_Allah ya saka da alkhairi_
_wannan kyauta yayi girma dewa my peach banajin zan iya sake tambayar wani abu_
Bayan manosh ya karantane seya ce
_pls apple kigayamin indai kina so inyi farin ciki dan ina k'aunarki sosai apple
nd i can do anything just for you sweetheart_
dad'i sosai maryam taji sannan ta sake tura mishi
_ba wani abu bane illa flower_ _i love you nd i love flowers so verry much
peach_

Koda ya gama karantawa murmushi yayi yace indai wannan ne sekin gaji dashi dan
lambunsa guda zanyi a gidanmu my apple,da haka yayi bacci.
Washe gari da safe ya shirya seda ya tambayi maryam tace su baba sunzo sun
koma,ita da mama da rash ne,yace ok ganinan zuwa tace to sekazo.

Koda manosh yazo cikin kakin sojojinshi yake se kallonshi yakeyi,office muh'd ya
wuce yace yadai abokina ya wifey nane da jiki,muh'd uace tofa tu ba'a baka
ba,kar dai harka shirya kenan se tafya,manosh yace wlh kuwa driver yana waje
daga nan airport zamu wuce,muh'd yace ok jeka ka fito se in rakaka,manosh ya
wuce d'akin da sallama dama mama ta fita tunda maryam tace manosh yazo taje can
d'aya d'akin gun wasu matan da y'arsu ba lfy suma.
Manosh ya shigo kenan rash ta mik'e tare da gaisheshi sannan ta fita,ita kuwa
maryam flowers d'in kawai take bi da kallo da kuma yadda yayi kyau a kakin
sojojin. Akan kujeran ya zauna suka gaisa seya ajiye mata flowern a gefenta,da
sauri ta d'auka tana murmushi tare da shinshinawa taji wani k'amshi mai dad'i
wanda yasa ta limshe idanunta tace _thankyou so much captain_,murmishi yayi yana
kallonta yadda take ta murna da ganin flowers d'in,itama shi take kallo yare da
d'auko *ring*mai kyau na maza ta mik'a mishi batare datace komaiba. Hannun yasa
ya karb'a tare da cewa thankyou apple naji dad'i sosai,yasa a yatsan hannunshi
tare da pecking d'in yatsan nashi yana mata murmushi tare da cewa ya jikin,tace
naji sauk'i sosai wlh,manosh yace alhamdulillah zuwa gobe za'a sallameku insha
Allah nizanyi tfy kuma zankai 1week kafin in dawo su dad zasuje gun baba dan asa
mana rana kinji?
Sam maryam bataso tfyan manosh ba haka kurun tad'an canja fiska,shi kanshi ya
lura da hakan seya sauya muryanshi yace "apple r u aokey?" Tace yes am fine ina
zakaje? Yace zanje kaduna ne,karki damu kinji zan dawo insha Allah addu'arki
nake buk'ata apple,kallonshi takeyi tare da tausayin kanta tace Allah ya kare
min kai,yace ameen suna kallon junansu ciki so sannan tayi saurin kawar da kanta
gefe tana kallon flower daya kawo mata,manosh bazai iya jurewaba dan haka ya
mik'e tare da cewa nizan tafi apple ga wannan,ya ajiye mata kud'i a gefen
gadonta sannan ya nufi kofar fita. Har yakai gun k'ofan kanta na kallon
flowern,seya juyo yana kallonta sam taqi kallonsa har ya gama kallonta sannan
yaja k'ofa ya fita harzai kulle kenan seta d'aga kanta suka had'a ido cikin
tausayin junansu yace _i love you so much apple_
_tace i love you too manosh_
Harda d'an kwalla a idonta sannan yaja kofar da sauri ya rufe,ita kuwa hawayene
suka zubo mata kona menen oho....
[7:10am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: 🍭🎈AUNTY'N YARA🍧🎁AUNTY'N YARA🍧🎁

Written by sad-nas
&
Hama gee muh'd

*dedicated to mom sudais* *(awans❤)*)*

35-36 Hankalin maman maryam ya kasa kwanciya,seta kira baban maryam a waya tana
tambayanshi ko maryam ta iso? Baba yace a'a bata isoba,hankalinta ya sake tashi
tace malam yaci ace ta iso ai,shi kanshi hankalinsa ba'a kwance yakeba,amma
seyayita kwantar mata da hankali da daddad'an kalamai yana cewa kinsan fa maryam
da taimako da kuma tausayi,zaiyu wani abinne ya tsaida ita a hanya amma bari
nabi sawunta.
Mahaifin maryam ya rufe shop nashi yabi hanya ai ko seyaga almajirai sunata
d'iban abinci a k'asa kuma ya tabbatar da cewa wannan kulan abincinshine.
Wayansa ya d'auka ya kira matarshi ya tambayeta cewa me kika dafa minne yau,tace
shinkafa da miyace mai had'e da wake,katse wayan yayi ya kama fad'in
*innalillahi wa'inna ilaihirraji'un* tare da duduba guraren kozai hango maryam
amma sam se *rivom* nata daya hango wanda shida kanshi ya sayo matashi.
Hankalinshi ya tashi sosai,ya kira number'n maryam yanata ringing amma ba'a
d'aukaba har kusan sau biyar. Haka ya wuce gida a rud'e inda ya had'u da yah
ibrahim da abokanshi suka gaisheshi ya amsa amma suna ganinshi sunan akwai
abinda ke faruwa,ibrahim yace baba lfy kuwa,yace lfy lau ka biyoni gida.

Haka suka juya abokanshi suna tsaye daga waje su kuwa suka wuce gida. Mama tana
jin sallama ta fito tare da cewa malam lfy,nan ibrahim ya gaisheta sannan baba
ya gaya musu duk abinda ya gani a hanya sannan yayita kiran number'n maryam
shuru. Addu'a suketayi dukkansu tare da tunanin to ina maryam take?
Ibrahim ya kira rashida da sameera a waya suka ce mishi sam maryam bata zoba,ya
sake kiran zahida da amina suma sukace bata zoba,nan ya wuce gidan hajiya iya
nanma batanan,koda hajiya iya taji lbrn hankalinta a tashe harda kukanta dan
yadda take son maryam a ranta.

Nan tayi lullub'i ta wuce gidansu maryam inda mahaifiyarta taketa addu'a tare da
kwalla a idonta. Duk wanda yaji yasan ba lfy bane domin maryam bata tab'a yin
hakaba,ga kuma rivom da mahaifinta ya gani agun yasan lallai akwai matsala
sosai.
Bayan anyi sallan azahar ne mahaifin maryam yayi bayani a masallahi akan a
tayasu da addu'a. Duk wanda yaji seyayi addu'a dan base na gaya muku daliliba.
Cikin k'ank'anin lokaci magana ya baza ko ina a garin girei. Ibrahim ya
kira manosh a waya amma yanata ringing bai d'agaba,hakan yasa ya kira number'n
marwan bugu d'aya ya d'auka bayan sun gaisane yake ce mishi manosh fa,domin
yayita kiranshi amma bai d'aukaba,marwan yace wlh ni ina office ne maybe baya

kusane. Ibrahim yace ok dama wlh maryam ce aketa nema tun d'azu taje kaiwa
mahaifinta abinci har yanzu shuru babu ita babu lbr,ahanya akaga kulan abincin a
zubar a k'asa sannan an tsinci rivom d'inta har haryanzu babu wani lbr.
*innalillahi wa'inna ilaihirraji'un* marwan yaketa nanatawa tare da mik'ewa
yayi gun manajer'nsu bayan sunyi magana marwan ya d'auki motarsa se gida.

Miher ya gani a tsakar gida zata fita,nan dai suka gaisa yace ina prince,tace
yana bacci bayajin dad'i kanshi yana ciwo. Marwan yace ok sannan ya wuce d'akin
miher tanata binshi da kallo dayya taganshi tasan ba lfy,haka kawai taji ta fasa
tfyan dan tana so taji menene da sauri tabi bayan marwan ta lab'e daga bakin
kofa inda taji marwan yana cewa "dude" "dude" ahankali manosh ya bud'e ido yana
mamakin ganin marwan a wannan lokacin. Marwan yace sorry na tashe ya jikin,yace
alhamdulillah lfy? Marwan yace ka kashe wayar kane,manosh yace no a silent nasa
dan ind'anyi bacci wlh ya akayi,marwan yace "dude" akwai matsala baga'a apple ba
tun 11:40am yanzu gashi har 3:20pm,kuma duk inda ake tunanin tana zuwa anje bata
nan sannan........da sauri manosh ya mik'e tare da d'aukan wayanshi yaga miss
call din baban maryam dana ibrahim dadai wasu daban,number'n apple ya kira
yanata ringing amma sam bata d'agawa. Kamar zaiyi kuka ya sake kiran wayan
yanata cewa "pls apple pick d call okey" where are you apple,wurgi yayi da wayan
seda screen d'inshi ya pashe ya shige toilet da wuri,shi kuwa marwan ya d'auko
wayan amma ina ba'a ganin komai taci screen.
Manosh ya fito ya shirya suka fita ko mum nashi bai sallamaba,daya ga miher yace
miher maryam ta kiraki?miher da jikinta yayi,sanyi tace a'a,yace kiyita kiran
numbern ta sannan ki gayawa mum cewa ba'aga maryamba nina fita.

Hawaye miher ta fara dan yadda taga bro nata ya hargitse a lokaci d'aya.
Basu wuce ko inaba se girei,inda suka isa har parlon mahaifinta yana zaune da
mutanen unguwa,sukayi sallama tare da gaisuwa sannan manosh ya farayiwa baba
tambayoyi kamar ba surukinsaba,shi kanshi baba yasan manosh a rikice yake,manosh
yana gama jin komai ya musu sallama suka wuce gurin yayita dube dube amma baiga
komaima. Abokinsa *faruq* ya kira wanda yake aiki a *mtn office* yace faruq
matar

Please Login or Register in order to submit comment