Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

maryam lokacin da aka kusayin aurensu,nasa
akayi nesa da ita yayinda nake samun duk wata lbr agun miher wanda ita kanta
basan inada hannuba,tun daga numan nasan aka sakeyin nesa da ita mum zuwa jejin
yankari dake jihar bauchi,amma dayake Allah ba azzalumin bawansa bane dukda cewa
ita maryam tasan cewa nine nasa ayi mata hakan amma sam tak'i gayawa ko iyayenta
da suka haifeta ta b'oye zancen cikin ranta domin bataso asamu matsala tsakanin
familynmu da kuma familyn su bro manosh saboda tasan irin shak'uwa da soyayya
dake tsakanin bro marwan da kuma bro manosh hakan yasa tayi shuru tabar komai
aranta mum.
Marwan yana tsaye abakin k'ofa ya kasa shigowa yana sauraron lbrn da lubna
take baiwa mum nasu,wanda mamakine sosai abaiyane a fiskarsa.
Lubna taci gaba da cewa mum bayan maryam ta dawo gidane,shi wanda na basu aikin
yace inje muyi magana domin maryam tasan komai kuma k'ila zata tauna musu
asiri,tsoron kar sunana ya fito dan yadda nake tsoro bro marwan yasa ranan na
fita naje can inda saddam yake ya bayan GG..kuka lubna ta fashe dashi tace mum
koda naje juice ya siyaya mana nidashi,ban kawo komai a rainaba saboda k'ishin
danakeji a wannan lokacin kawai sena canye wannan juice d'in,shikenan ban sake
sanin inda nakeba kodana farka senaji jikina wani iri mum saddam ya cuceni yamin
fyad'e....
Mum ta kama salati tare da kwalla a idanunta itama lubna haka tace naso na
kira miher amma senayi tunanin bazata rufamin asiriba dole za'a sani,shine na
kira maryam ban b'oye mata komaiba na gaya mata komai,kinsan me mum hankalin
maryam ya tashi sosai take tazo inda nake mum ta taimakamin ta kimtsa kaina
hawayene cike a idanunta tare da tausayawa,muna tare da ita su bro manosh sukazo
gun nida maryam muna ciki d'akin ab'oye a toilet munata addu'a saboda maryam
tayiwa bro manosh k'aryan cewa tana cikin kasuwa suna sayayya se kuma gashi yazo

inda muke a d'akin saddam,hankalin maryam ya tashi sosai badan komaiba sedan
jinin dake kan katifar saddam kuma gashi ni babu yadda nake alokacin jikina rawa
kawai yakeyi. Cikin ikon Allah mukaji suna cewa saddam ya gudu kenan tunda gashi
harda kwad'o ajikin kofan,kuma wlh mum babu wanda ya kullemu ta waje,seda suka
tafi muma muka fito da sauri shine maryam ta kawoni har gida tayi miki k'aryan
cewa bigeni akayi da mota naji ciwo a k'afa,kuma mum maryam itace ta had'ani da
ibrahim wanda yake matsayin yayanta,bata b'oye mishi komai akan batun fyad'en da
aka minba ta gaya mishi komai,tare da neman amincewarsa akan ya aureni,k'aunar
da ibrahim yakeyiwa maryam ne yasa ya aureni badon yana sonaba,kuma wlh mum koda
na rana d'aya ibrahim bai tab'a nuna kyamarsa akainaba se kauna da kulawa na
musamman kuma har gobe babu wanda yasan da wannan zance fyad'e dagani se maryam
da ibrahim duk maryam tayi hakanne don ta rufamin asiri mum da kuma k'aunar da
take min,gaskya mum maryam macece wanda ba'a samun irinsu a zamanin yanzu,ina
ganin k'aunarta aduk lokacin da muka had'a ido da ita.
Dan haka zan iya yiwa maryam komai koda hakan zaisa in rasa rayuwatane to lallai
zanbawa maryam k'odata guda d'aya watak'il zan iya biyanta da alkhairan datamin
arayuwa......

Ba mum kad'aiba harta marwan dake tsaye a waje ya shigo rai a b'ace,take lubna
ta gudu bayan mum dan yadda ta ganshi tasan sarai yaji komai dan haka ta fara
kuka sosai tana cewa waiyo mum dan Allah karki bari ya dakeni wlh ina da ciki
mum,bro marwan dan Allah kayi hakuri.
Mum tace karka tab'ata marwan nace ka kyaleta! Cak marwan ya tsaya yana kaima
lubna sakon harara yace baga irintananba mum,daga taimako gashi ta b'ata mana
suna tayi abin kunya,ke bari kiji ingaya miki dabadan cikin dake jikinkiba wlh
yau dase na kusan karyaki wawiya mara hankali dole kibar mana gidanmu dan dama
ke 'yar tsuntuwace ni kad'ai iyayena suka haifeni tsintattiyar mage kawai ya
fita rai a b'ace ya fisgi mota.
Daga lubna har mum kuka sukeyi lubna tana bin mum da kallo mai d'auke da tambaya
tace mum menaji bro marwan yake cewa? Wainiba 'yarku bace? Tsuntoni kukayi
hakane mum? Mum da kuka yaci karfinta tace hakane lubna keba 'yarmu bace.
Lubna ta tsaya da kukanta tace tosu waye iyayena mum,a ina kuka samoni
mum,meyasa kuka b'oyemin mum? Mum cikin kuka ta rik'o hannun lubna tace shi
kanshi dad naku baisan iyayenkiba lubna domin ce mishi nayi na tsuntokine,lubna
keba 'yar kowa bace se 'yar Alhaji muh'd atta. Zaro ido lubna tayi tace wanne
kenan mum? Mum ta rungumeta tace wanda dai kika sani mahaifin maryam *auntyn
yara* ku 'yan biyune lubna maryam itace babba sannan ke uwarku d'aya ubanku
d'aya da ita lubna ki gafarceni dan Allah,cikin mamaki lubna ta janye jikinta
tace taya hakan ya faru kenan mum? Kina nufin kowa yasan hakan kenan? Mum tace
babu wanda ya sani dagani se hajiya iya kakarki lubna. Kuka sosai lubna takeyi
tare da barin palon da gudu......
[7:14am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: 🍭🎈AUNTY'N YARA🍧🎁AUNTY'N YARA🍧🎁

Written by sad-nas
&
Hama gee muh'd

*dedicated to sis fatima tahir*❤🌺
❤)*

71-72 Da sauri auntyn yara ta waigo donjin me lubna take cewa,kai se sukayi
gwaru akansu atare sukakai hannu goshinsu don sunji zafi dukkansu.
Maryam ta karb'i wayan hannunta tare da cewa sannu lubna ita lubna sannu take
mata suna masu kallon junansu cike da murmushi,maryam tabar d'akin da sauri ta
koma d'akinta tare dasa wayan a kunnenta tace cikin zumud'i tace *hello peach*,
muryan manosh yace apple ya kike yasu abdallah,lfyanmu lau peach nah ina ka
shiga ka barmu da tashin hankali da kewa,yace kiyi hakuri apple yanzuma na
kirakine dan in gaya miki cewa ki mance dani a rayuwarki kwatakwata kamar baki
tab'a had'uwa daniba domin bazan sake dawowa garekuba apple ki cireni a
zuciyarki su abdallah kuwa ki gaya musu cewa na mutu kuma mamaci baya dawowa ta
yadda zasu manceni daga k'arshe kuma ki samu miji wanda kike ganin zai rik'e min
su alfiya ki aura koda d'aya daga cikin abokainane wannan shine dalilin dayasa
na kiraki kinji apple,ya k'arashe maganan cikin murya maiban tausayi.
Ita kuwa maryam tunda taji abinda ya fara fad'a taketa zubda hawaye harya
k'arasa. Jin tayi shurune ya sake kiran sunanta apple pls am sorry,na zab'i
hakanne dan in cetoki daga sharrin shukrah bawai don wani abuba...bai k'arasa
maganaba naryam ta katseshi da cewa ya isheni haka peach bana son sakejin komai
daga gareka indai akan wannan magananne mubarta kawai,yanzu ka gayamin ya yake a
ina kake me kuma shukrah tayi maka haka peach? Yadda manosh yaji muryan apple
bashi yasan tana cikin tashin hankali,yace karki damu da sanin halin da nake
ciki apple dama abinda na kira in gaya miki kenan ina miki bankwana ta karshe.
Da sauri da kuma ihu tace pls peach karka katse wayannan ka saurari abinda
zance maka,ina cikin wani hali sosai peach na rashin lfy,k'odata gabad'aya sun
b'aci dole se an min dashe,yanzu haka ana shirye shiryen fita dani india ne dan
haka ka saurareni wata k'ila maganata dakai na k'arshe kenan zaiyu idan najema
bazan dawoba dan haka inaso ka yafemin dukkan wasu abubuwa dana maka na rashin
sani,sannan ina so ka sani har inbar duniya babu wani d'a na miji dazan iya zama
dashi bayan kai kuma har inbar duniya bazan dena yin addu'a Allah ya d'auraka
akan shukrah daduk wani abu mai cutarwa ameen,inaji ajikina cewa zaka dawo
garemu peach,sedai bana tunanin zaka sameni sedai iyayenka da kuma yaranmu peach
dan Allah ka kula min dasu domin kune farin cikina daga k'arshe ina k'aunarka
k'auna ta hak'ik'a wanda baya k'arewa _i love you so much peach_, alfarma d'aya
zan nema agunka shine inji kalmar soyayyata abakinka pls...?
Kwalla sosai manosh yakeyi idanunshi kamar attarugu,amma ina bazai iya gaya
mata kalmar so ko d'ayaba,dan haka yace ina miki fatan alkhairi apple se
anjuma......
Kuka sosai maryam ta fashe dashi tana cewa peach dan Allah karka barni ka tsaya
ka gayamin cewa kana sona dan Allah my captain,kuka sosai takeyi tana kallon
wayan. Mama da lubna da suke tsaye akanta tun ihunta na farko sune suka rik'eta
sunta rarrashi dan sunji dukkan hiran maryam da manosh d'in.
Yah ibrahim da babane suka shigo dajin muryan kukan maryam suna tambaya ko
lfya? Nan lubna ta gaya musu komai,inda mamaki ya kamasu sosai. Yah ibrahim
yayita kiran numbern amma sam baya shiga,maryam dai se kuka takeyi tana ta
surutai kamar wanda ta zare tana cewa baba manosh yace in samu miji inyi aure
yana nufin ya sakeni kenan baba,menayi mishi dazai min haka baba,nagaya mishi
halin da nake ciki amma koya kula baba,innalillahi wa'inna ilaihirraji'un. Lubna
tana rungume da yarta itama kuka takeyi sosai,sam bata son ganin naryam cikin
damuwa musamman ma datasan cewa yartace uwarsu d'aya. Hakadai ranan lubna bata
koma gidantaba shi ibrahim d'inne ya koma saboda mahaifiyarsa ita kad'aice se
mai musu girki. Daga baba har mama abin ya basu mamaki ganin yadda lubna
takeyida maryam,bayan iyayenta sun rarrashetane se suka barsu a d'aki ita da
lubna.

Yah ibrahim kuwa tunani iri iri yakeyi a zuciyarshi,ga kuma damuwan halin dayaga

maryam aciki yau ya tausaya mata sosai harma yake tunanin inama dashine ya
aureta da shikenan maryam bata da damuwa sam,amma ina haka Allah yake tsarawa
kowa rayauwarsa. Wayarsa ce tayi k'ara number manish ne,mamaki yayi sosai tare
da d'auka da sauri yace slm,wslm yaji muryan manosh,basu gaisaba manosh yace na
kirane don inji cewa dagaskene za'a fitar da aunt india? Ibrahim yace eh
hakane,manosh yace to shikenan idan kun dawo ka sama mata miji ka aurar da ita
dan nikam bazan dawo garekuba na zab'i in zauna anan domin ceton apple zan iya
jure komai ibrahim shiyasa nafiso ace kaika auri aunt ba waniba pls ka auri aunt
nasan zaka kula da ita kamarni. Ibrahim yace mekake fad'ane captain insha Allah
zaka dawo kuma kadena sa ran cewa wani abu zai same aunty babu abinda zai sameta
da yardan Allah zaka dawo kushi gaba da zamanku munata addu'a kuma shukrah
setasha wahala wlh muguwa...tsawa maikyau ibrahim yaji akunnensa ana cewa wlh
k'arya kake ibrahim wahala kam sedai auntyn yara amma badai niba,kuma zanga
yadda zaku karb'o my manosh daga hannuna dama kai kad'aine mai taka min birki
kuma ina so kasan cewa my manosh yabarku kenan har abada bazaku sake
ganinshiba,sannan ka gayawa mahaifin maryam ya kiyayeni wlh su dena b'ata
lokacinsu waisu suna so suga bayana to wlh idan bai dena shiga gonataba sena
tozarta maryam d'in da kuke ji da ita. Hhhhh ibrahim yayi dariya yace dama ashe
kece shukrah,kece kika ari muryan captain kike so ki b'ata tsakaninsu da
aunty,to Allah ya tona asirinki muguwa,ina so kisan cewa aunty tafi k'arfinki
shiyasa har yanzu kika kasa mata komai shine kika b'ullo mata tasan muryan
mijinta koh,tota Allah ba takiba wannan kad'ai bai isheki shukrah,komai kikayi
seya warware hakan yana nufin bazaki tab'a samun nasara akanmu bane kuma
mahaifintama yafi k'arfinki hatta shi captain yafi karfinki wlh kawai dai
jarabawace Allah ya sauko mishi dashi kuma insha Allah zamuci wannana jarabawan
muzuba dake shukrah *QUR'AN* yana sama da komai acikin duniyan kuma dashi zamu
karb'o captain agurinki idan kuma kin isa toki hanamu d'aukoshi daga gareki
kawai lokaci muke jira kekanki kisan duk duniya babu wanda captain zai bud'ewa
zuciyarshi ta shiga ta zauna se *aunty* . Haushi da takaici yasa shukrah katse
wayar
Yah ibrahim ya tsinci kanshi dayin murmushin tare dajin dad'in sanin cewa ba
manosh bane yayi magana da aunty shukrah ce. Take ya kira baba a waya ya gaya
mashi komai,baba baiyi mamakiba dan yasan babu abinda aljanu basayi, take yaje
ya sanar dasu maryam dan hankalinta ya kwanta.
Ai kuwa dad'i sosai taji tare dayin add'ua Allah ya kare mata mijinta ya kuma
dawo dashi garesu.

Marwan kuwa yana kwance ne kawai amma yakasa bacci dan irin abubuwan dayaji yau
da kuma gani. Tun bayan barin su lubna gidan yaketa tambayar hajiya iya kakarsa
meke faruwane danshi kansa yasan akwai wani abu dayasa lubna tayi mata hakan
amma sam hajiya iya tak'i cemishi komai se kukan nadama da taketayi babu
sassaushi. Haka marwan ya gaji ya tafi gida gun mum nasu,koda ya gayawa mum nasu
abinda lubna tayiwa hajiya iya sam mum batayi mamakiba,shima marwan d'in ya lura
da yanayin mum d'in nashi wanda yasashi tambayar mum nasu yace wai meke faruwane
mum nakasa fahimtar komai tabbas akwai wani abu dayake faruwa mum dan Allah ki
gayamin.
Marwan ya kamota suka zauna yana share mata kwalla.
Mum ta dubi marwan tace zan gaya maka marwan amma sekamin alk'awarin bazaka bari
mahaifinka ya d'auki mummunan mataki akainaba, cikin rashin fahimta marwan yace
banganeba mum?
Mum tace marwan dad naka yana k'aunarka fiye da komai a duniya,idan yasan abinda
na'aikata tonasan zamana dashi yazo k'arshe, kaine zaka iya hanashi rabuwa dani
d'ana saboda k'aunarka da yakeyi.
Marwan ya sauke ajiyar zuciya yace namiki alk'awari mum har abada bazan bari
ku rabu da dad ba. Mum tace nagode marwan, sannan ta fara bawa marwan lbr kamar
haka...

[7:14am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: 🍭🎈AUNTY'N YARA🍧🎁AUNRY'N YARA🍧🎁

Written by sad-nas

*dedicated to AUNTY SIS*

_nagaba yayi gaba na baya se lbr our sweet aunty, kece ta farko kuma kece ta
karshe,babu wata bayan ke *aunty sis*,muna alfahari dake akoda yaushe...

75-76 marwan ya rasa mema zaicewa mum nashi,dan tsabar yadda jijinshi yayi sanyi
kamar k'ank'ara. Cikin sanyi murya yace mum danasan abinda kika aikata kenan
daban miki alk'awarin dana d'auka mikiba,amma koba komai ke mahaifiyata babu
abinda zan iyayi ko kuma ince miki,sedai kiyi hakuri amma sam abinda kukayi
baidaceba sam wlh mum abin babu dad'i ji. Matsowa yayi kusa da ita yana kwalla
kamar yadda takeyi yace mum kidena kuka inaso kimance da cewa kin bani wannan
lbrn,ki d'auka cewa har yanzu sirrine kamar yadda kuka rufeshi keda hajiya
iya,dan gaskya mum nibansan ne nake cikiba a yanzu haka. Komin dad'ewa gaskya
zai fito wanda bansan yazan tsinci kainaba a wannan lokacin da kowa zaisan me
mahaifiyata da kakata suka aikata.
Jiki babu kwari ya mik'i zai fita tayi saurin kamoshi tace dan Allah kaban
mafita ya d'ana. Mum wlh babu wata mafita danasan zan baki akan wannan lamarin
domin baki bani wani ilimi akan hakanba lokacin da kuka bani tarbiya keda dad.
Mum tace nasan ban kyautaba shiyasa nake neman nafita marwan? Marwan yace mafita
shine kisami dad ki gaya mishi komai tun kafin lubna tatona muku asiri mum.
Bayan fitan marwan ne mum taketa kukan dana sanin akan abinda suka aikata.
Shikuwa marwan gida ya koma da zazzab'i mai k'arfi daya rufeshi,seda rashida ta
kira dr muh'd a waya yazo gida yayi masa allura da kuma magunguna inda suke
mishi sannu. Sam marwan ya kasa had'a ido da abokan nashi saboda tun a yanzu
kunyansu yakeji bare kuma ace gaskya ta bayya kowa yaji.
"Lubna ce kwance tana bacci ad'akin maryam hankalinta kwance,ita kuwa maryam
se mamakin kulawar da lubna tayi da ita takeyi acikin zuciyarta tare dajin sonta
a ranta. Wayan lubna ce yake k'ara koda maryam ta duba setaga yah ibrahim
ne,daidai nan lubna ta farka tare dasa wayan a kunne tace hello,yace kin tashi
lfy yasu aunty,tace lfyansu lau ya mama,yace tana lfy ina hanyan zuwa d'aukanki
da fatan kin shirya? Ta murza ido tare da kallon maryam tace wlh yanzu na tashi
ko wanka banyiba kabari se anjuma kad'an pls...? Yace ok naji amma ki tabbata
kin shirya dan zamubi gidan marwan mu gaisheshi bayida lfy tun jiya zazzab'i mai
k'arfine ta rufeshi wlh. Subhanallah!tobari kawai na shirya nan da 1hr sekazo.
Maryam ta kalli lubna tace lfy? Lubna tace bro marwan ne ba lfy zazzb'i
sosai,maryam tunda nake ban tab'aganin rashin lfyanshiba bro marwan yana sona
sosai har cikin ranshi dukda zafinshi amma akan gaskya yake komai nashi i
respect him so much aunty,maryam tace eyyah nima barina shirya muje tare inyaso
zanbi gunsu miher zuwa yamma sena dawo.

Maryam ta gama shiri tsaf,ita kuwa lubna tana zaune tana k'are mata kallo,maryam
tace naga kina zaune,lubna tace eh bazan maida kayan jikinabane shiyasa dan
sunyi datti. Maryam ta gane me take nufi hakan yasa ta d'auko mata zanin da
manosh ya saya mata tunda ta d'inka bata tab'a sawaba ta batashi tace ga wannan
kisa,godiya sosai tayi ai kuwa nan danan ta mik'e tasa sun mata kyau sosai
ajikinta ta juyo tace aunty nagode kayan sun amshi jikinki sosai wlh harda
rungume maryam,azuciyarta tace nagode sosai 'yar'uwata jinin jikina.
Mama ta shigo tace todai sekunci abinci kafin ku tafi,bamusu sukaci amma
maryam kad'an taci dan dama tunda aka nemi manosh aka rasa tadena cin abinci.
Ita kanta mama lubna tana burgeta kome dalili oho,ita kuwa lubna sakewa sosai
tayi dasu ko'ajikinta dukda ta lura da cewa suna mamakin yadda ta sake dasu
tazama kamar 'yargida.
Gun motan yah ibrahim suka nufa bayan sun gaisa suka shige maryam ce a baya
suna tfy ta hango manosh daga nesa. Peach ta kira sunanshi cikin mamaki wanda
yasa yah ibrahim tsaida mota da sauri suka had'a baki tare da cewa ina yake?
Tayi musu nuni da hannu zuwa inda yake tsaye ajikin wata black car. Mamaki sosai
sukayi dan tabbas shine tsaye sanye da kakin sojojinsa ya hard'e hannaye yana
duba agogon hannunsa bisaga dukkan alamu wani yake jira...
[7:14am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: 🍭🎈AUNTY'N YARA🍧🎁AUNTY'N YARA🍧🎁

Written by sad-nas
*dedicated to ummi hambali*🌺🌺🌺

_Assalam fans nagode sosai da kulawarku,lfyata lau kawai sungullane yake min
yawa a'yan kwanakinnan shiyasa bakwajina_. 🌺

_sannan masu min tambaya akan konice marubuciyar *lalata*, no! Banibace *sadnaf ce* dafatan kun gane_😊

73-74 Marwan auren so da k'auna mukayi da dad naka kuma shi shi d'an wan
mahaifinane auren dangi aka mana nida dad naka.
Tun ina 'yan'mata Allah ya d'oramin son yara musamman mata,kowa yasan da haka
a dangi. Bayan munyi aure da mahaifinka ne kusan 2yrs kafin na samu
cikinka,bazan iya gaya maka burin da muka d'auka akan wannan cikinba,dan muna ta
fatan Allah yasa mace zan haifa,amma se yazama kaine marwan na haifa,hakan baisa
na fidda ran haifan maceba.
"Marawan har kakai 12yrs ban sake sake samun cikiba,babu irin damuwa da tashin
hankali da bamu shigaba harta dangi,dayake ansan yadda nake son mace,gashi dangi
kam kowa namiji yake haifa ba mace ko d'aya. Hajiya iya mahaifiyar dad naka tana
sona sona tamkar 'yar cikinta sam bata son ta ganni cikin damuwa,har zamuje
gidan marayu d'aukan yarinya,amma se mahaifin dad naka wato wan mahaifina yace
a'a bai aminceba,hakan yasa muka hakura har wata rana naje girei gun hajiya iya
yini...

"Muna zaune se aka zo da sallama wai wata mata tana nak'uda kuma ta galabaita
sosai gashi duk mak'otan sunce bazasu iyaba sedai a nemo tsofi,sakamakon mijinta
baya kusa,kuma yana fama da kansa ana tunanin idan an kaita asibitima kud'i za'a
nema lokacin kuwa kowama yana fama da abinda zaicine. Hakan yasa nida hajiya iya
mukaje gun wannan mata mai nak'udan wanda batama san inda takeba ta zama abin
tausayi bata cikin haiyacinta sam.
Munfi awa muna kanta cikin ikon Allah ta haifi bby girl kyakkyawa,kwalla ne ya
zubo a idona dan ji nayi kamar in gudu da jaririyar,muna cikin murnan kenan sega
wani kai ya fito ashe dai 'yan biyune dukkansu mata,murna sosai mukayi nida
hajiya iya muna cewa ashe 'yan biyune shiyasa ta wahala haka.
Tofa shine hajiya iya tace dama mijin natan baida hali kuma gashi har yara
biyu,dan haka tace in tafi da d'aya tunda babu kowa a waje,duk wanda suke jiran
haihuwan harsun gaji sun tafi saboda sunga bata haihuba. Ni kuwa banyi tunanin
komaiba saboda yadda nake son mace,a d'ankwalina na nad'e jaririyan nasata cikin
himar na koma gidan hajiya iya,acan na mata wanka da komai na koma gun hajiya na
d'auki kayan jaririya d'aya dayake sund'an sayi kayan kad'an,na koma na sama
mata.
Ita kuwa hajiya iya tayiwa jariya da uwar wanka ta kimtsasu saf,amma har'a
lokacin uwar jaririyan bata farfad'owa harse bayan awa biyu,koda taga abinda ta
haifa murna sosai tayitayi tare dayiwa hajiya iya godiya.
"Bayan hajiya iya ta dawo gidane,tace maza in tafi da jaririyar gida kar
asirinmu ya tonu,tsoro ya kamani nace tome zan gayawa dad naka? Tace zata mishi
bayanin cewa an sami jaririyar ne a hanya aka ajiyeta kuma kowa na tsoron d'auka
saboda yadda duniya ta canja,shine ita ta d'auka mana tunda tasan muna son 'ya
mace. Dayake lokacinma dad naka yana umrah shine komai yazo da sauk'i kuma haka
muka gayawa kowa na dangi da kuma abokan arziki harda kuma....
Hajiya khadija ta tsaya anan da lbrnta tana kuka,marwan kuwa jikinsa yayi
sanyi yama rasa me zaice mata saboda shidai asaninsa wannan abunda mum nashi da
kakarsa sukayi sata kenan satan jaririya. Mum ta lura da yanayin marwa tayi
saurin rik'o hannunsa cikin muryan kuka tace marwan karka manta kamin alk'awarin
zaka taimakeni amma tun yanzu naga rashin jin dad'i afiskanka,marwan karkace
komai ka saurari ci gaban lbrn..
Haka na rik'e jaririyannan na samata sunan hajiya iya muna kiranta da *LUBNA*
gata sosai ta samu agun mahaifinka,kuma dukkanmu muna sonta tsakani da
Allah..marwan ya katse mum nashi da cewa naji mum kuma na fahimta,yanzu lubna
'yar gidan wayene,su wanene iyayenta a ina suke? Mum tana kuka sosai tace marwan
iyayen lubna sunan a raye kuma acikin girei sannan 'yartama tana raye dan lubnan
itace k'arama. Marwan ya mik'e tsaye yace mum baku kyauta ko kad'an wlh,wannan
abinda kuka aikata bansan me zance akaiba kun kyauce sosai wlh kun raba yarinya
da iyayenta da 'yar'uwanta yanzu idan maganannan ya fito waje duniya sukaji mum
ya kike so inyi da raina,sunanefa zai b'aci mum ace mahaifiyata ta aikata hakan
mum,da wani ido zan dubi jama'a musamman abokaina mum? Kwallane yake zuba daga
idanun marwan yace a ina suke? Mum ta mik'e ta kasa dena kuka tace marwan se
yanzu nake nadaman abunda na aika busa son zuciyata.
Marwan yace no mum,dukda tarbiyan da kuba lubna kiga dai abinda ta aikatawa
*aunty* yanzu da asirinta ya tonu a lokacin da dawani ido zan kalli princ
mum,kinsan yadda nake son manosh kinfi kowa sanin shak'uwarmu dashi da kauna
dake tsakaninnu ashe ankama lubna ce tayiwa aubty haka daya zanyi,kumafa kiga
ita *auanty* ne ta had'a lubna da miji nagari irin ibrahim,mum kinsan yadda
ibrahim yake son aunty,wlh daya san lubna ce tayiwa aunty haka wlh bazai tab'a
bariba,amma kuma duk wannan bai isaba kika yaudaremu dukkanmu dangi akan
tsintota kukayi alhali bahaka maganan takeba haba mum... yanzu waye mahaifin
lubna ki gayamin mum?
Cikin nuryan kuka sosai tace bakowa bane *illa mahaifin maryam aunty'n yara*
marwan aunty itace twin sister'n lubna ita ta fara zuwa duniya kafin lubna,ta

k'are maganan tana zama a k'asa kamar kayan wanki. What! Marwan ya tambaya da
k'arfi da fiskan mamaki tare da juyawa yana kallon mum nashi kamar yaga dodo
yana fad'in *innalillahi wa'inna ilaihir raji'un*,ita kuwa mum kuka kawai takeyi
tana rik'e da hannun d'an nata...
[7:14am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: 🍭🎈AUNTY'N YARA🍧🎁AUNTY'N YARA🍧🎁

Written by sad-nas

*dedicated to ayusher muh'd*😘❤😘

77-78 da sauri yah ibrahim ya tsaida motarsa suka fito dukkansu suka nufi gun da
*manosh* yake tsaye,cikin mama maryam ta rik'o hannushi tace peach? Ahankali ya
juyo yana kallonta kamar wawa,yah ibrahim yace aunty sakeshi...ai bai k'arasa
maganaba seka wata kyakkyawar budurwa ta fito daga wani shago kawai ta d'auke
maryam da mari tana cewa ke wace irin shashashace dazaki rik'emin miji?
Ai kafin yah ibrahim yayi magana lubna ma tayi saurin d'auke budurwan da mari
tace ai shashashun suna dewa wawiya jaka ke har kinkai a tab'a mijinki,yah
ibrahim ne ya shiga tsakaninsu yanayiwa lubna fad'a,ita kuwa maryam sam bataji
marinba tamaida hankalinta gun manosh da yake tsaye yanata kallonta baya ko
kyafta idonsa. Ahankali ta sake dawowa gefensa tana mai zubda kwalla tace
*peach* jikina yana bani cewa kaine dan Allah kacemin wani abu. Kawai setaji
yace baiwar Allah banine wanda kike tunaniba,sunana *muawiya* sannan wannan
matatace. Kuka mai k'arfi maryam ta fashe dashi tare dabarin gurin aguje zata
koma mota nan sukayi kicimus da majid,kallon juna sukeyi har cikin ido tanata
hawaye tace majid dan Allah ka k'are mishi kallo wancan ba captain bane duba
kakinsafa dan Allah kazo muje nasan zaka iya ganeshi tunda tare kuka taso.
Da sauri majid ya karasa lokacin fad'a sosai akeyi tsakanin lubna da wannan
budurwan tace cewa kisa maganata a ranki cewa senayi maganinki,lubna tace ta
Allah ba takiba banza mara hankali da kyar yah ibrahim ya janyo lubna ya kaita
mota gun maryam se faman kuka takeyi lubna ta zauna a gefenta tana rarrashinta.
Majid yaje dabda manosh ya tsaya yana k'are masa kallo tun daga k'asa har
sama,shima manosh d'in kallonsa yakeyi kamar dai yadda yayiwa maryam,majid yace
*dude kaine*? Budurwan tace yau naga ikon Allah waiku wasu irin mutanene
haka,kawai kunzo kun damemu kunat....tsawa mai kyau majid ya daka mata kimin
shuru badake nakeyiba! Take ran budurwan ya b'aci idanunta sukayi jah jazur
kamar attarugu tayi saurin rik'e hannun manosh tace kadaiga yadda akacimin
mutunci amma ka kasa sewa komaiko,shikenan mutafi dan idan nacigaba da zama anan
to lallai mutanen dake yankinnan kam zasu shiga cikin matsala. Yah ibrahim da
majid suka kalli juna sukace matsala kuma? Daidai nan maryam ta fito daga mota
da gudu tana cewa yah ibrahim wlh peach d'inane shine gashi yana min bye bye.
Koda yah ibrahim da majid suka maida kallonsu ga manosh da budurwan se sukaga
wayam,babu su kuma babu motarsu.
Mutanen dake gurin kowa kafa menaci ban bakaba kusan rabi duk sun gudu,su kansu
yah ibrahim sun tsorata sosai,majid yace ina suka shiga? Maryam cikin muryan
kuka tace wlh manosh ne yah ibrahim wannan duk aikin shukrah ce wlh sune lokacin
da take magana kaida majid kuna kallon junanku se manosh ya juyo yana kallon
inda seting motarmu take shine ya d'aga min hannu yanamin bye daga nan kuma suka
b'ace yah ibrahim dan Allah kace tadawo min da mijina inda manosh ya tsaya nan
maryam taje ta zauna agun daya ajiye kafafunsa tanata kuka,lubna da yah ibrahim
ne suka d'agota dakyar suka kaita mota shima majid ya shiga nashi suka koma
girei gidansu maryam.

Koda baban maryam ya samu lbrn abin shuru kawai yayi danya rasa mezaice,mama
kuwa tanata rarrashin maryam tare da cewa lubna kekuwa meyasa kika rama mata
marin?yanzu gashi kin mari aljana idan kuma

Please Login or Register in order to submit comment