Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

d'aya ya bata ta karb'a tare dayin
godiya,yace bakomai ki koma inda kike dan nasan sun kusa dawowa zanyi iya
k'okarina dan in taimakeki ki dena damuwa kinji? To nagode sannan ta koma taje
ta zauna tare da bud'e malt d'in da biskits tana sha.
Wayarta ta bud'e sega texs d'in manosh dana miher,na miher ta fara bud'ewa inda
taga hoton manosh sanye da maroon jaket,ita kanta maryam tasan manosh ya shiga
wani hali daga ganin hoton nashi,sannan ta karanta texs nata kamar haka
_slm 2u my aunt_
_bansan mezance mikiba aunt,amma ina cikin damuwa sosai musamman yadda naga bro
manosh ya zama kamar bashiba dan rashinki_. _Aunt munanan munata addu'a Allah ya
d'auraki akansu,kinga dai yadda bro nah ya zama wlh tun jiya baici komaiba har
yabar gida yanzu_. _ina sonki wifeynmu,pls koda empty rexs ne ki aiko min dan
inji sanyi a raina_. Yours miher....

Koda maryam ta karanta setaji kwalla ya zuba mata,nan ta tura mata da
_thankyou so much sis,nagode sosai da kulawarki,kuma nayi farin cikin ganin

pic d'in peach,dan yasani farinciki sosai wlh_. *nagode*

Koda taga texs d'in manosh batayi reply ba se kawai ta kirashi. Katsewa yayi ya
kirata ta d'auka tare da cewa *captain*, sanyi yaji har cikin ranshi yace yes
apple a wani hali kike yanzu? Karka damu ina halin lfy,sedai nayi fushi
dakai,meyasa mena miki apple? Saboda kabar cikinka da yunwa rabonka da abinci
tun breakfast d'in safe meyasa hakan peach? Am sorry apple amma kema ai bakici
komaiba,eh amma yanzu haka ina shan malt da biskits,naga pic naka yanzu miher ta
turo min peach a jiya kawai amma ka canja. Yadda yaji muryanta kamar zatayi kuka
yacewa sojan da yake driving tsaya anan ka karb'o min malt da biskits,sannan
yace "apple am goying to eat now okey" pls banaso kisa damuwa aranki muna hanyan
bauchi kinji? Murmushi tayi tace "thankyou peach" cikin sanyin murya. Sunanta ya
kira a hankali *aunt*, cikin muryan kuka tace uhmm,yace pls stop it apple i will
soon come to u okey? Har yanzu kukan takeyi "tace okey i have to peach byee...
Bayan ta katse wayanne ya had'iye tausayinta a wuyanshi daidai lokacin aka kawo
malt da biskit d'in ya bud'e ya fara sha,bayan ya gamane ya karb'i driving d'in
gudu yakeyi kamar zai tashi sama..

Can kuwa koda maryam ta ajiye wayan da sairi ta kashe ta mayar pant d'inta dan
taji zuwan mota.
Saddam ne tare da sauran abokanshi 3 suka dawo,wannan d'ayan da suka bari yana
kwance ya mik'e yare da cewa ya kuka dad'e ne haka? Saddam yace wlh bari
kawai,ta tashi kuwa,eh ta tashi tayi sallah,saddam yace gaskyafa ni a matse nake
wlh dan haka kawai zan sauke gajiyata akanta wlh,d'ayan yace haba saddam karkayi
haka pls da safiyannan idanma hakane ai gara ka bari se dare kai kanka zakafi
jin nishani idan duhu yayi. Saddam yace hakanefa,to gaskya dole na koma cikin
gari in nemo wata dan wlh a matse sosai nake kasan abunka da sabo,yana kaiwa nan
yaje ya duba maryam tana rakub'e a gefe tana kuka. Dariya sosai saddam yayi yace
garama ki dena wannan kukan domin anjuma zakiyi wanda ya fishi sauti hhhhhhhh

Hankalin maryam ya sake tashi domin taji hiransu. Abinci wani ya kawo mata ya e
gashi kici ko fine girl,ko kallonshi batayiba ya ajiue ya k'ara gaba.
Tana jin motarsu ya tashi ya tafi ta lek'o taga duk sun tafi seshi wannan bawan
Allah. Wayarta ta kunna ta nemi layin manosh amma sam baya shiga,ta tabbatar da
suna hanyane dan haka taje tayi alwala tare dayin sallan walaha tayi addu'oi
sosai sannan ta sake gwada numbern manosh har yanzu dai shuru yak'i shiga,haka
ta koma gefe tana zaune tanata karatun qur'an a cikin zuciyanta har azahar tayi.

Maryam tanayin alwala yazo yace amma ki gayamin sunan k'awayenki mana,tace lfy?
Yace lfy lau,nan dai ta dinga kiransu harta gama yace babu wasu da kike tunanin
sun tsaneki? Tace gaskya babu,yace to shikenan jeki kiyi sallah.
Bayan ta idarne seta bud'e wayanta cikin ikon Allah call d'in manosh ya
shigo,da sauri ta d'auka tace hello,yace peach kina dai lfy ko? Tace lfy lau
manosh kuna ina,pls kazo da sauri domin suna da niyan aikata wani abu a kaina
pls..karki damu apple inanan a inda kike yanzu zanzo gareki,mik'ewa tayi da
sauri tare da jujjuyawa tana kallon jejin tace ina kake peach?...
Wayan hannunta ya karb'a tare da kashe wayar gabad'aya yana binta tana komawa da
baya tana cewa dan Allah kayi hakuri. Ran saddam a b'ace yace wato dama da waya
a hannunki ko,to wlh bazaki b'ata min aikiba sedai in kasheki in kashe banza.
Bindiga ya d'au zai harb'eta d'aya mutumin yace haba saddam kar kayi haka mana
mace zaka kashe kuma k'aramar yarinya,kawai muyi gaggawan barin nan d'in shine

mafita,domin yarinyar data saka aikin itace take baiwa masu binciken address
d'in inda muke dan a kamaka ka fita daga rayuwarta for good. Kan saddam ya
d'aure sosai yace kana nufin *LUBNA AHMAD* tana min wasa da hankali ,yace kwarai
kuwa.

Mamaki ya cika maryam ta nanata sunan a cikin ranta *lubna ahmad*? Kawai seta
d'iba da gudu ta barsu atunaninta ai su manosh sun iso inda take. Bindiga saddam
ya d'aga tare da harbinta ai kuwa seya sameta a saman hannunta kusa da
kafad'arta,ihu sosai maryam ta saka tareda fad'uwa k'asa tana kuka. Saddam zai
kara mata se d'ayan ya bige bindigan yace meyasa hakane saddam wai kasheta
zakayine? Sauran ukun ne sukazo da mota sukace kuzo mu sampe sojoji sunji k'aran
bindiga zasuzo kuma,d'ayan yace bari in d'auko yarinyar dan bazamu barta a
hakaba ai. Da gudu saddam yahau mottafi suka tafi suka barshi,gashi sam baiga
maryam a inda ta fad'iba kamar wanda ta b'ace. Yanata tsaidasu saddam amma sam
sunk'i tsayawa sema harbinsa dasukayi a k'afa ta yadda bazai iya guduba. Ai kuwa
segasu manosh da gudu ya k'araso yana cewa apple, apple na iso ina kike? Kan
mutumin ya nufa tare da d'agoshi yace ina maryam! Take mutumin ya fara b'ari dan
yasan shikenan kashinsa ya bushe tunda ya shiga hannun *sojoji*, yace *sir* wlh
ban saniba acan ta fad'i nima ita nake nema...
[7:12am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: 🍭🎈AUNTY'N YARA🍧🎁AUNTY'N YARA🍧🎁

Written by sad-nas
&
Hama gee muh'd

*dedicated 2 Adon gari group*❤)*❤)*❤)*

41-42 Hajiya khadija ce zaune agidansu maryam tanata kuka,maman maryam se
hak'uri take bata,tace yanzu fisabilillahi me maryam tayi haka dahar za'a
d'auketa a rabata da iyayenta,se kuma ta sake fashewa da kuka mamace taketa bata
hak'uri.

Auntyn yara ta dubi tsohon dade rik'e da hannunta yana tab'a inda aka harb'etan
da hannayensa,cikin ikon Allah sam bataji zafiba. Se alokacin da take kallon
tsohonne seta tuna cewa wannan shine wannana tsoho mai farfad'iyan data tab'a
taimakawa lokacin daya fad'i akan titi rananne farkon had'uwanta da *peach*
shiyasa bata bance fiskanshiba sam. Murmushi tayi tace baba,yace na'an maryam
kin ganeni ashe,tace sosaima kuwa meya kawoka nan bab ya jikinka? Murmushi yayi
yace jiki da sauk'i maryam tun bayan rabuwana dake na taimakawa mutane hud'u
yanzu kece ta biyar,tace eyyah baba Allah ya saka da alkhairi,dama a nan jihar
bauchi kakene? A'a a jihar adamawa nake ca *hong* ayyah baba a hong kake dama
toya akayi kazo nan? Maryam saboda ke nazo danaga kina cikin damuwa kuma dama
nace kece mutum ta biyar dazan taimakawa shiyasa nazo. Har zatayi magana ya
katseta da cewa maryam ki saurari abinda zan gayamiki da kyau,tace to baba ina
jinka amma akwai wanda ya kamata mu had'u dashi nasan kuma sun iso yanzu gashi
sun karb'e wayana nasan zaiyita nemana baba. Yaga dai ta damu sosai seyace karki
damu zan kaiki har inda suke kiban hankalinki anan maryam,tace to baba ina jinka
yare da kallon hannunta daya d'aure mata bayan wasu abubuwa dayayi wanda basan
meneneba.

Baba ya kalli maryam yace nasan zaki gayawa mutane cewa *lubna ce* tasa akayi
miki haka ko? Tace eh baba,yace to karki gayawa kowa maryam,cikin mamaki tace
meyasa amma dolene in gayawa iyayena ai,baba yace harta iyayennaki kada ki gaya
musu komai kuma bana so ki tabbayeni dalili indai har kin yadda dani kinsan
bazan cutar dakeba to rashin gayawa kowa shine afi akhairi a gareki maryam.
Mamaki sosai ya baiyana a fiskar maryam tace to baba idan ban fad'a an d'auki
matakiba ai zata sake bin wata hanyan,yace bazata sakeba maryam maganar gaskya
niba mutum bane kamar ke maryam ni alja....bai k'arasaba maryam ta tsorata sosai
tare da mik'ewa tana komawa dabaya dukda dai tasan batasan kota inda zatabiba.
Baba ya mik'e yace maryam karkiji tsorona ki d'aukeni kamar kina tare da
mahaifinkine,dan Allah karki sanar da kowa cewa lubna ce ta miki haka kigayawa
kowa cewa su saddam ne,sannan yanzu haka bawan Allah can yana can hannu sojojin
zasu gana kece zaki iya dakatar dasu tawajen gayamusu cewa shi bayida hannu
taimakonki yake da niyanyi shine suka miki rauni kinji maryam? Cikin rawan jiki
dama tunda taji shiba mutum bane taketa add'ua,setace to baba dan Allah inaso in
koma gida,yace ba gidaba maryam karki rud'e ki nitsu kinji,kibi wannan hanyan
gabanki zaki samesu nina tafi.
Yana kaiwa nan ya b'ace,gudu maryam tasa tare da kiran sunan manosh...!
Kamar daga sama manosh yaji muryanta ta gefensu da sauri ya juya ya nufin gun da
gudu yana apple, "where are you?" Can ya hangota tanata gudu tana juya bayanta
har suka iso gun juna.

Kallon juna suka tsayayi yayinda take ta waige waige,manosh ya lura da cewa bata
cikin hayyacinta sam. Sunanta ya kira aunt? Da sauri ta juyo se'a sannan ne ta
dawo hayyacinta nan ta tsaya kallonshi cikin so da kuma tausayin yadda taga ya
zama. Sunanshi ta kira tare da murmushi tace manosh,shima murmushin yayi tare da
k'are mata kallo da wuri yakai hannunshi gurin hannunta da aka harbeta sannan ya
juya yana kallonta cikin tuhuma. Ita kanta tasan dalilin kallon nan tace wani
bawan allah na hango shine yayi saurin d'aukeni ya kuma taimakamin sosai shinema
ya d'aure min hannun. Manosh yace yarone ko tsoho? Har cikin ido take kallonshi
ta kuma gane me yakenufi wato yana kishi wani ya tab'a jikinta kenan. Tace
tsohone manosh kamar mahaifina yake kuma wlh ba wani tab'a jikina sosai yayiba
abun nashi daban al'ajabi kuma sam bana jin wani ciwo yanzu,murmushi yayi mata
dan yasan sam maryam bazata mishi k'aryaba ya yadda da ita har cikin zuciyarshi.
Matsowa yayi kusa da ita gab kad'anne a tsakaninsu kunya sosai taji sannan ya
mata kwarjini sosai ta yadda bazata iya had'a ido dashiba. Hannunshi ya mik'a
mata mana'a tazo su tafi,amma sam tak'i bada hannunta tanata jan himar nata da
d'ayan hannun. Murmushi yayi yace Alhamdulillah "i'm so happy to see you apple"
kanta a sunkuye tace "me too" sannan ya d'auki wayanshi ya kira babanta yace
baba mun sameta lfyanta k'alau gatanan yanzu zau taho,maryam ta karb'i wayan
tana kallonshi tare dayin dariya tasa a kunnenta tace hello baba,yace
alhamdulillah 'yar baba Allah ya amsa addu'armu barka 'yata,mirmushi tayi wanda
yaji dad'i sosai tace baba ina mama,nan mama ta karb'i wayan tace maryam
Alhamdulillah bari naje kichin na dafa miki abinci 'yar albarka,dariya tayi tace
ina sonki mamat semun dawo na kuma gode sosai da addu'oinku.

Bayan ta gamane ya kira miher da mum nashi nanma suka gaisa sannan ya kira su
marwan suka sakegaisawa daidai lokacin suka iso gun otansu manosh d'in.
Maryam ta hango bawan Allah yana ta zubar da jini a k'afanshi yayinda wani yake
gyara mishi k'afa. Da sauri tace peach me kuka mishi haka,wlh sam bayi da laifi
kokad'an dan shinema wadda yake kiran baba a waya,sannan taimakona yakeyi sam
bayida hannu a ciki dan Allah ku rabu dashi,manosh yace apple pls karkisa baki a
ciki,tace pls manosh ka saurareni wlh..ya isa apple,yana da hannu mana tunda ya

biyosu kuma ai shima yasan da zance sacekin inhar da gaske yakeyi meyasa bai
sanar da 'yan sandaba. Shiru maryam tayi dan yadda taga ran manosh ya b'aci
cikin k'ank'anin lokaci da sauri tabar gun ta koma jikin motarsu tana zubda
kwallah.

Manosh yabi bayanta tare da bud'e mata gaban motan yace shiga mu tafi,ba musu ta
shiga ta zauna daga tsakiya tana ci gaba da kukanta wanda babu sauti hawaye awai
kake hangowa yana zuba. Hankalinsa ya tashi nan ya shigo gaban shima yana zaune
tagun k'ofa driver a ya shiga maryam tana tsakiyansu sannan sauran suka tattaro
tarkacen su saddam da wannan mutumin a bayan motan suka kama hanyan.
Maryam ta share kwallanta kanta a sunkuye dan gabad'aya a takure take. Manosh
yace da driver idan kaga wani shop ka tsaya agun,yace ok sir.
Maryam ya kalla yace apple me zakici,tace ni banason komai,yasan cewa fushi tayi
yace dolene kici wani abu dan kina jin yunwa sosai,tace ni banajin yunwa muje
kawai,nan driver ya tsaya suka fita shida manosh nad'an wasu lokuta sannan suka
dawo amma drivern bai shigo motaba.
"Anosh yace apple karb'a kici,tayi kamar bata jishiba,ya sake cewa bana so mu
fara haka dake pls apple ki barni inyi aikina inyaso zan barshi daga baya amma
ba yanzuba kinji? Ko kallonshi batayiba tace amma nace maka babu hannunshi
fa,yace yes aunt i know bincike kawai zanyi akan wanda yasasu kuma shi yasan
kowanene,tace nima na sani ai saddam sunanshi kafin kuzo suka gudu,yace eh
saddam dinma akwai wanda ya sashi ai,tace pls peach indai kana sona to kawai
kabar maganan tunda Allah yasa nadawo nina yafe wlh,murmushi yayi yace ok apple
eat first okey,tace nifa bazanci komaiba seka janye,yace tona janye karb'i apple
d'in kici pls,karb'a tayi yana mata murmushi sannan shima ya fara cin nashi ita
kuwa sam ta kasa ci tana rike dashi. Ta lura da cewa yana kallonta dan haka tace
nifa bazan iya cin komai ayanzuba senaje gida,bakinshi ya matso dashi daidai
kunnenta yace "kinaso inyi fushi dake koh?" Kunya taji tace wlh bazan iya cin
komaiba kayi hakuri,shuru yayi bai sake ce mata komaiba sunata tfy har suka iso
*yola*.
Dad'i sosai maryam taji suka wuce da bawan Allah can barac nasu inda ya mik'awa
manosh wayan maryam yave lokacin da take wayane ya karb'e wayan,bayan ya ajiye
wayan shine na d'auke. Manosh ya karb'a sannan yazo suka wuce girei itadai
maryam tanata tausayawa mutumin can dasuka kama,ahanyane manosh ya bata
wayanta,tanata godiya tace a ina ka samo dan ai wayan tana hannun saddam ne,nan
yagaya mata komai daidai lokacin suka iso k'ofar gidansu maryam a girei...
[7:12am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: 🍭🎈AUNTY'N YARA🍧🎁AUNTY'N YARA🍧🎁

Written by sad-nas
&
Hama gee muh'd

*dedicated 2 matan kwarai grp*💐🌹

43-44 k'ofan gidansu maryam a cike yake da jama'a kowa yana jiran dawowar auntyn
yara,koda akaga motan sojoji ya tsaya da sauri aka nufo motar anata hamdalah da
mata murna sosai,musamman abdallah hannu ya d'aga sama yanayiwa Allah godiya.

Su manosh suna tsaye daga waje yanaganawa da jama'a,ita kuwa ta wuce gida dasu
rash da sameera daidai sauran jama'a. Maryam ta rungume mahaifiyarta tana
murmushi bayan nan ta zauna bada lbrn abinda ya faru amma sam tace batasan
bayasa a mata hakanba,nan dai kowa yayita tofa albarkacin bakinsa. Can akajiyo
hayani a waje nan take kowa ya fito,yarane da almajirai suketa tsalle da wak'a.
_Alhamdulillah auntyn yara ta dawo,ta bayya,Allah mungode maka daka dawo mana da
auntyn mu lfy lau_.
Hahahah sunatayi manosh ya nufin gurin se zuba musu kud'i yaketayi yara se k'ara
murya sukeyi suna d'iban kud'i yah ibrahim ne yazo ya koresu yace toya isa haka
mungode kowa ya wuce gida,nan suka watse suna murna. Dariya manosh da ibrahim
sukayi sanan suka wuce gunsu baba suna magana,maryam ta wuce band'aki tayi wanka
tare da d'auro alwala tazo tayi sallolinta sannan taci abinci sosai dan dama
tana jin yunwa.
Bayan ta koshine tace mama da sauran wani abincinne zan zubawa manosh a kula
ne,mama tace eh akwai,nan taje ta had'o a kula ta kawowa maryam tace
gashi,godiya tayi tare da mik'ewa taje palon babanta tare da sallama suna zaune
da yah ibrahim da kuma abokinsa soja wato yusuf maryam ta ajiye musu abinci
sannan ta koma ta d'auko plate da kuwa ruwan sanyi tare da exotic d'in da hajiya
khadija ta kawo musu.

Bayan ta fitane yah ibrahim ya zuba musu ba laifi kuwa sunci sosai sannan sukace
zasu tafi. Maman maryam tazo suka gaisa sannan ta musu godiya,manosh ya kira
maryam ya sanar da ita cewa zasu tafi ta kwanta ta huta,godiya sosai ta mishi
yare da jajdada mishi cewa karya cutar da bawan Alla can,murmushi yace yace "yes
my princess"tambayoyi kawai zai amsamin nayi miki alk'awarin bazan cutar dashiba
matuk'ar zai amsamin tambayoyin da nake buk'ata agunshi. Dad'i taji sosai tace
yaushe zaka sake zuwa? Yace se jibi akwai wani abune,tace yes ina son *flower*
murmushi yayi yace angama aunt gobe mum da miher zasuzo zan aikota dame kuma
kike so? Tace da *peach d'inah*,dariya yayi itama haka sannan suka tafi. Yah
ibrahim ya shigo gida sunata hira dasu rash daga k'arshe suka tafi.....

Washe gari da safesartuday ne,dan haka su marwan suka da safe sukayiwa maryam
barka sannan suka d'anyi hira suka tafi. Da misalin 11:00am mum d'in manosh da
miher sukazo nanma dai suka zauna kad'an,miher dasu maryam sunata hira a
d'akinsu yayinda ta mik'a mata flowern da bro nata ya bayar akawowa marya,dad'i
sosai taji tare da lumshe ido su miher da rash se dariya sukeyi mata suna
zolayarta. Awa d'aya su miher sukayi sannan suka tafi sesu zahida da amina
sukazo,bak'idai sosai suketa zuwa da abin arziki babu wanda yake zuwa empty.
Hajiya iya ce zaune a gaban maryam tanata kuka tana rungume da maryam,maryam
da mamanta duk kansu ya
d'aure da irin kukan hajiya iya. Amma se suka d'auka kodon k'aunarda takeyiwa
maryam ne.

Saddam ne zaune a d'akinsa ya kira lubna a waya yace kina ina,tace ina gida me
nakeji wai maryam ta koma gida? Yace kizo mu had'u dan muyi magana,tace ok amma
bazan fito da motaba zanzo yanzu semu had'u,yace ok.
Babu wani b'ata lokaci lubna ta shirya cikin after dress black tahau nape se
daidai gate d'in gg ta kira saddam a waya tace ina daidai gg,yace wlh motata
tayi pashi bamma bar gida ko zaki k'arasone semu fito tare,bata soba dai amma
dan bataso asirinta ya taunu setace to gashi kayiwa mai napen kwatance. Nan suka
d'auki hanya har inda saddam ya kwatanta musu,se kuwa gashi ya fito daga

d'akinsu yazo yabiya mata kud'in dan ita batada canji.
Bayan mai nape ya tafine saddam yace ki shigo mana kar wani wanda ya sanki ya
ganki anan kinga se'a ganki kamar mutumiyar banza,haka tabishi a baya suka shiga
sannan ya kulle k'ofan ta key,lubna data zauna aiseta mik'e tare da cewa ya kuma
ka rufe kofan saddam? Take ya canja ido yace ashe ki muguwace munafuka ban
saniba,kece kike gayawa maryam inda muke kaita dan azo a kamani in fita daga
rayuwarki ko lubna,hakazakimin,wlh to bazan barki hakaba sena lalata miki
rayuwarki kafin in bada kaina. Kuka lubna ta farayi tace haba saddam wlh bansan
komai akan abinda kake fad'aba taya za'ayi in kira lubna kuma,dan Allah karkamin
haka saddam wlh karyane duk wanda ya gayamaka karya yakeyi wlh,nan dai lubna ta
rikice ta fara kuka. Shuru sadda yayi yace kiyi hakuri lubna na d'auka koda
gaskene wlh,bakomai share hawayenki mu tafi domin yanzu ni suke nema abokina ya
yaudareni wlh amma zanyi maganinshi baisan wayenibane shiyasa,juice ya zuba mata
da sauri ta karb'a tasha batare dayin wani tunaniba ta shanye tas dama datajin
k'ishi. Shi kuwa saddam wayo ya mata dan kartayi kuka ta tona mishi asiri dan
haka ya juba magani a ciki ai kuwa take lubna ta fara fita hayyacinta,saddam
kuwa ya tashi ya fara cire kayan jikinshi tas tana iya ganinsa bakomai a
jikin,nan hankalinta ya tashi tana k'okarin tashi amma ina seta fad'a kan
katifarshi kamar macacciya,da sauri ya rabata da kayan jikinta tas se lashe baki
yakeyi kamar tsohon maye,yahau shafeta tare da wani irin gigicewa da ganin
kyakkyawar suranta. Cikin k'ank'anin lokaci ya rabata da budurcinta gashi ya
kwashi romo sosai danshi a tunaninshi an dad'e da sanin lubna saboda irin shigan
dayaga takeyi. Bayan ya gamsune yayi saurin watsa ruwa ya shirya tare da kwashe
kud'ad'en dake jakarta ya d'auki akwatinsa ya gudu da motarshi.

Koda lubna ta dawo hayyacinta kuka sosai takeyi tare da tsinewa saddam albarka
tana tuna yanzu shikenan ya gama b'ata mata rayuwa ya zatayi kenan? Miher ce
kawai ta fad'o mata arai harta d'auki wayarta zata kirata kuma seta tuna cewa
koda yaushe miher suna tare da majid kuma tasan dole miher zata fad'a wanda idan
bro marwan yaji shikenan nata ya k'are. Kuka sosai lubna takeyi gashi jikinta
duk jini haka ta rasa yadda zatayi kawai se maryam ta fad'o mata a rai data tuna
da abinda wani tsoho ya gaya mata akan maryam,ai kawai seta kira maryam.
Lokacin su maryam sun shigo jimeta dasu yah ibrahim dasu sameera,mamaki tayi
sosai da ganin kiran lubna,seta d'auka hello,lubna cikin miryan kuka take magana
hello maryam dan Allah ki gafarce akan abinda na miki nasan kinsan komai amma
dan Allah ki rufamin asiri dan yanzu hakama Allah ya saka miki akan abinda na
miki maryam sadda ya cuceni yamin fyad'e bazan iya kiran kowaba seke,saboda
abunda wani tsoho ya gayamin dan Allah maryam ki taimaka kizo saddam ya gudu
yanzu haka ina d'akinsane a bayan gg idan aka sani za'a kasheni a gida musamman
bro marwan maryam dan Allah ki rufamin asiri. Shuru maryam tayi ta kasa cewa
komai,kuma batasan ya za'yi tabar su rash taje ita kad'aiba. Nan tace ok inazuwa
tare da kashe wayar, tace yah ibrahim dan Allah ku saukeni anan ku shiga kasuwan
rash idan naje na gama zan gaya muku inda nake sumu tafi,yah ibrahim yace to
shikenan sannan ta sauka tahau nape se bayan gg,nan dai ta kira lubna tayi musu
kwatance suka k'arasa har gun sannan ta sallameshi ya tafi,ta sake kiran lubna
nan taji k'aran wayan a kofar gabanta,da sallama ta shiga taga lubna a kwance
cikin jini,tsorata sosai tayi tare da dasa key a kofan tana ta addu'a,ta k'arasa
ta taimaka mata ta mik'e ta rakata toilet dake kicin d'akin sannan ta tsaya daga
bakin kofa tana mamakin abinda ya faru.
Wayartace tayi k'ara ta d'auka hellow peach,yace apple nah kina ina,k'irjinta ya
buga tace ina jimeta munzo sayayyane dasu yah ibrahim idan muka gama zan sake
kiranka muna cikin kasuwane,yace ok badamuwa,tace ina kake? Yace muna kan aiki
yanzu zamuje inda saddam yake zaune ne mu kamashi,tace a ina kuka sameshi
peach,yace wai yana bayan gg yanzu haka muna hanyane,tsoro ya kama maryam tace
to shikenan sena kiraka,yace ok byee. Maryam tace lubna fito su manosh suna
hanyan zuwa nan domin sun samu lbrn cewa saddam yana nan karsuzo su tarar damu
anan gashi na mishi karyam idan ya samemu anan tofa ina cikin tahin
hankali,lubna take zawo ya kamata haka tayitayi a toilet d'in tana kuka,ita kuwa
maryam se kallon windo takeyi tare da k'ara rufe ko ina a d'akin,daidai lubna ta

fito tasa kayanta da sauri jikinta se b'ari yakeyi tausayinta ya kama maryam har
seda tayi kwalla,seta d'aga zanin gadon taje ta wanke da ruwa tazo ta bazashi
akan gadon sannan maryam ta kwashe mata wayanta da sauran kayan makeup nata tasa
a bag na lubnan suka yunk'uro zasu fita kenan sega motar su manosh,aida sauri
suka wuce toilet sunata addu'a ita kuka lubna zawone ya sake kamata haka
tayitayi tana hawaye sosai dan yadda take tsoron bro marwan barema kuma aji cewa
an mata fyad'e ne hmmmm...
[7:12am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: 🍭🎈AUNTY'N YARA🍧🎁AUNTY'N YARA🍧🎁

Writren by sad-nas
&
Hama gee muh'd

*dedicated 2 khafeelat abdulhafis*❤)*

45-46 tsayawar mutar sukaji,ba lubna kad'aiba ba harta maryam a tsorace
take,gashi tayiwa manosh karyan cewa tana kasuwa kuma yanzu idan ya ganta a
d'akin saddam kimarta zai ragu a idonsa addu'anma dakyar take iyayi,ita kuwa
lubna idan ka gantama dole kayi kwalla dan tausayinta. Muryan manosh sukajiyo
yana cewa ya kuma naga padlock a k'ofan,hakan yana nufin saddam ya sake tserewa
kenan?yusuf yace ai mu b'alla kofan kawai k'ila sawa yayi a rufeshi ta baya dan
muyi tunanin bayanan.
Maryam da lubna aise suka tsure suna *innalillahi wa inna ilaihirraji'un*
jikinsu se rawa yakeyi. Bawan Allah ne yace duk yadda akayi saddam guduwa yayi
baya ciki domin banga motarshiba lallai yasan za'azo nemanshi shiyasa ya
gudu,manosh yace ina kenan kake tunanin zai tafi?yace numan zai koma inda yakai
maryam,wanine yazo wucewa manosh yace kai ina wanda yake zama anan?mutumin yace
d'azu ya fita da kayansa dewa ya zuba a mota da gudu yabar nan. Manosh yace muje
yusuf,nan danan sukabi bayan saddam gudu sosai manosh yakeyi da mota.

Basu maryam kad'aiba,harta ni *sad-nas* seda nace *alhamdulillah* wani irin
ajiyar zuciya maryam ta sauke tare da k'arayin godiya wa ALLAH sannan suka fito.
Lubna tace kwad'o fa naji sunce ansa ajikin k'ofan to taya za'ayi mufita
kenan,maryam ma abun ya bata mamaki tace towaya mana kwad'o kenan?
Gwada bud'e kofar tayi cikin mamaki taga kofan ya bud'u,kallon juna
sukatsayiyi ita da lubna dukkansu mamakine ya bayya a fuskarsu,maryam tace
shikenan gaskya muyi hanzarin barin nan,dan nima su yah ibrahim suna jirana.
Lubna ta rik'o hannunta tace kije maryam niki barni anan dan bazan koma gidaba
wlh bro marwan zai kasheni. Maryam tace ki dena fad'a haka lubna aiba a son
ranki bane fyad'e aka miki kawai ki fad'a musu gaskya,lubana tace wlh na
gwammace insha wani abun in mutu amma sam nikam bazan iya komawa gidaba maryam
bazaki ganebane,ba'asan ina da alak'a da saddamba,idan kuma aka sani to za'amin
kallon mutumiyar banza za'ace dama mun saba iskanci dashine baza'a tab'a uarda
fyad'e yaminba wlh nan ta fashe da kuka sosai..

Tausayinta ya kama maryam tace toke meya had'aki dashi lubna?

Lubna tace wlh kawai yaketa bibiyata waishi yana sona,ni kuma danaga 'yan shaye
shayene se tsoro ya kamani dan kar sumin wani abu shiyasa na tsaya muka dai
gaisa duk dan mu rabu lfy,so dewa idan maza suna takuramin saddam shine mai
taimakona dayake anganshi ana tsoronshi dan ansan zai iyayin kissa ma indai a
kainane,kuma babu wanda yasanshi a gidanmu hakan ya bani daman sakewa dashi dan
taimakona da yakeyi,nima ina mishi kyautan kud'i sosai amma

Please Login or Register in order to submit comment