Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mai kidin ne sosai dan haka maryam take morewa
agunta.
[7:10am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: 🍭🎈AUNTY'N YARA🍧🎁AUNTY'N YARA🍧🎁

Written by sad-nas
&
Hama gee muh'd

15-16 Lubna ce kwance a gida tana chartn setaga numbern maryam akan list nata.
Nan take ta kirata suka gaisa sosai sannan maryam ta mata godiya.
Samira ta dawo daga mubi dan haka sukazo gun maryam ita da rashida sunata hira
se wayan maryam ya fara ringing,tana dubawa taga zahida ce,tasa a handfree suka

gaisa,se take gaya mata cewa majid marwan muhsin da kuma muh'd sunzo su
gaisheta,maryam batayi mamakiba dan dama manosh ya tambayeta unguwansu. Maryam
tace eyyah sun kyauta Allah ya biyasu su,tace ameen gaskya k'awata sun
had'u,dariya su samira sukasa tare da cewa kai zahida kodai...zahida tace wlh
kuwa muhsin ya kyasa yanzuma muka gama waya dashi,dariya suka sakeyi se maryam
tace shikenan abu yayi kyau to Allah ya tabbatar da alkhairi,zahida tace ameen
nagode sosai.
Koda maryam ta ajiye wayan dariya sukayi tare da shewa sukace lallaifa abu
yayi kawaye da abokai hahahah. Maryam tace ya isa mana duk randa mukayi waya da
manosh seyace in gaisheku,sukace to amaryan captain muna amsawa,kallonsu takeyi
tana murmushi tare da cewa amarya tun bamuje ko inaba,rashida tace ai
zakuje,dariya sukayi sannan ta d'auki kiran manosh tasa a hands free slm,yace
wslm aunt kin tashi lfy,lfy lau ya aiki,yace kai kibari akwai akwai gajiya ban
samu na kiraki da safeba wlh ban zauna bane hope kina lfy,tace lfy lau,yace yasu
mama,tace duk k'alau suke,yace bakije gun baba a shop bane,tace eh se zuwa
anjuma,yace ok,tace yanzu zahida take gaya min cewa su majid sunje sun dubata
mungode fa,yace bakomai wlh muhsin wai yana ciki,dariya tayi tace to Allah ya
tabbatar musu da alkhairi,yace ameen,ina samira da rashida da amina,tace muta
tate dasu amma banda amina,yace to banisu mu gaisa,tace to sannan ta mikawa
samira sukasha hida yanata mata raha,tace ab'asan soja da dariyaba amma kai
gashi kanada far'a,yace kika sani kodan ina son k'awarkine,tace no bahaka
bane,yace toya akayi kika sani,tace kowa ya shaidi soja baya wasa kuma ba
dariya,manosh yayi murmushi yace to ai ni k'aramin sojane,manya ne suke hakan
kuma sud'inma ba dukka bane. Sameera tace ina fata dai zaka rik'e mana friend
namu da kyau,yace base kin fad'a samira "because i luv her over" dariya tayi
tace to Allah ya barku tare musha biki,yace ameen nagode sosai,tace yawwa ga
rashida. Rasha tace captain zance nece kodai prince manosh dan sunan naka na
larabawane,dariya yayi sosai yace duk wanda kika kira,tace captain d'in dai ina
wuni,yace lfy ya kuke ya apple d'ina,tace lfyanta k'alau ya aiki,yace
alhamdulillah,tace to Allah ya sanya alkhairi adai rik'e mana ita amana dan
kaine mutum na farko data amshi soyayyarshi,yace insha Allah rash bazaku samu
wata matsala daga gareniba dan nima itace mace ta farko data fara shiga
jinina,rash tace jini gabad'aya, yace "yes ina ji da ita sosai pls ku kula min
da ita sosai" rash tace to gaskya munji dad'i Allah ya barku tare,yace ameen
nagode da addu'arku,tace bakomai gata nan.
Maryam tana murmushi tace hello,yace eeeeh aunt ya akayine,tace babu,yace friend
naki suna da kirki sosai wlh kun burgeni gaskya saura zahida da amina ki turo
min number'nsu dukkansu kinji,tace ok mungode,yace banace miki bana son godiya
ba,tace ai ya zama dole,yace nidai banaso,tace to shikenan byee yace byee.

Yaune manosh ya dawo daga abuja,nan kuma dad nashi ya dawo daga tfy. Manosh yaje
har palo ya gaida dad d'insa sannan ya gaya masa ra'ayinshi akan maryam,dad yace
a ina take,yace a girei ne,k'irjin dad nashi ya buga amma seya ce to badamuwa
zanyiwa iyayen abokanka magana semuje,manosh yace yace to dad nagode,dad yace
Allah ya sanya alkhairi yace ameen sannan ya wuce d'aki ya shirya da sauri cikin
kananan kaya yasha turare sannan ya d'auki kits d'in tsaraban maryam yayiwa mum
sallama yace zanje girei ne,tace to Allah ya kare,yace amin ya fita. Miher ta
bishi har waje tace bro gun yarinyar ne,yace ke sunanta maryam ba yarinyaba,
tace to ka gaisheta,yace yawwa k'anwata barima in baki numbernta ki dinga
kiranta kuna gaisawa kinji, mihar tana son bro manosh sosai dan yana sonta kuma
yana kulawa da ita sosai sam bayaso yaga an b'ata mata rai,dan haka itama taga
ya dace taso abinda yake kauna dukda dai ita tasoshi da k'awarta lubna amma
hakan baiyuba.

Shida muhsin da marwan da muh'd suka tafi danshi muhsin yana gun zahida,hakama
majid yana gun miher. Wayanta ya kira yace aunt gani a waje,tace yaushe ka dawo
daga abujan,yace d'azu,mamaki sosai tayi dan bai sanar da itaba,tace to ina
zuwa.

Munbern rashida da samira ta kira tace pls kuzo yanzu,ba jimawa sukazo ta d'aya
kofar bayan,duk himarne a jikinsu suka fita.
Salam,suka amsa wslm,bayan sun gaisa ne manosh yace dama bakisan marwan ba
toshine wannan,tace eyyah sannu,yace yawwa maryam ya kike ya hakuri damu,tace
bakomai,yace to idan yayi badaidaiba ki sanar dani zan hukuntashi,dariya sukayi
sosai,muh'd yace zamu hukuntashi dai,maryam ta gabatar da rashida da kuma
samira, sannan suka fara hira,manosh yace aunt yane,tace bakomai,yace muje daga
can kinji su marwan zasu damemu,muh'd yace gara dai kam,tana dariya suka d'an
matsa gefe.
Hannunsa a aljihu yace baba yana gidane,tace eh,yace yasan munzo,tace eh
nagayawa mama kuma nasan ta gaya mishi,yace ok kinsan bana so kiyi
laifi,murmushi tayi tace ya k'anwarka,yace miher lfyanta k'alau tamace in
gaisheki,sannan na bata numbernki,tace eyyah ina amsawa,yace tun bata gankiba
amma tana sonki sosai. Maryam tayi dariya tace nagode ina majid da muhsin,yace
suna hira gun zahida majid kuma na barshi a gida gun miher,tace tofa,yayi dariya
yace kinga marwan da muh'd ma sun biyonine dan su fahimci juna dasu samera kinga
in Allah yayi se ayi bikinmu rana d'ara d'aya,dama akwai wani abokina YUSUF
AHMAD shima sojane ya tab'ayin aure matarsa ta rasu agun haihuwa ita da bbyn
dukka se bai sakeyin aureba,shine na had'ashi da amina. Maryam tace eyyah Allah
ya jikansu,yace ameen kinga shikenan za'ayi bikin abokai da kuma k'awaye ko?
Murmishi tayi tace to Allah ya tabbatar,yace ameen meyasa bakya son yin magane,
tace bakomai,yace kinaso nima inyi shuru ne,tace a'a se wayansa ya fara
ringing,bak'uwar numbern ce ya d'auka tare da cewa hello,muryar mace ce tace yah
manosh lubna ce, yace ok lubna ya kike ya gida,tace lfy lau ka dawo lfy,yace lfy
lau wlh yasu mama,tace lfyansu lau dama na kirane in maka sannu da dawowa,yace
to nagode sosai numbern ki kenen,tace eh shine,yace ok thankyou,tace ok seda
safe sannan ya katse wayar tare da saving d'in numbern a wayanshi maryam tanata
satankallonshi da yake hasken wayan yana haska fiskanshi.
Gaskya manosh ya had'u take fad'a a ranta,seya katseta da cewa kina satan
kallona ko,kunya taji sosai dan batasan ya gantaba,tayi mirmushi tace a'a,yace
eh mana aina ganki,meyasa zakiyi sata bayan ni nakine,dariya tayi wanda ya
baiyana fararen hakwaranta,yace nima bari na haskaki to,wayanshi ya haska
fiskarta tayi saurin juya kanta,seyace to shikenan na dena,sannan ta juyo yace
inga wayarki,ba musu ta mik'a mishi,yanata danne danne ashe numbernshi yake
dailing dan yaga wani suna tasa mishi, ita kuwa tanata kallonshi tana k'ara jin
sonshi a ranta. Yace "PEACH & CREAM" gaskya sunan yamin dad'i sosai apple
thankyou,murmushi tayi tare dajin kunya tace wato dama sunan dana samishi ya
duba, wayan ya mik'a mata ta karb'a tare dajin kunya se wayanta ya fara
ringing,dubawa tayi taga UNCLE IBRAHIM,d'auka tayi tace slm uncle ibrahim ina
wuni,yace lfy lau aunty ya gida ya fama da yara,tace lfy lau ya aiki,yace
alhamdulillah muna kai,tace Allah ya taimaka yace ameen yasu mama da baba,tace
lfyansu lau wlh, yace dama na kira mu gaisane,tace nagode sosai tana mirmushi
shi kuwa manosh se kallonta yakeyi.
"Bayan ta gamane manosh yace kar inyi laifi amma waye wannan? Tace brothern
rashida ne brothernmu dukkanmu, tun muna primary yake mana lesson a gida har
secondary, da shine yake koyar damu a gida tare da sauran yara,bayan tfyan shi
NYSC ne yace indinga koyar da sauran yaran,kuma duk yan unguwan uncle ibrahim
muke kiranshi.
Manosh yace ok,amma akwai wani abu kuma bayan wannan? Tace a'a meyasa ka
tambaya,yace to ai naga ya kirakine kuma da dare,murmushi tayi a zuciyarta kuwa
tace wato dai kishi kake, tace ai duk muna waya dashi hardasu sameera bawai ni
kad'ai bane,kuma ya zama kamar d'an gida dan hargun mama yana shiga su gaisa
sannan ya tafi. Manosh yayi magana a zuciyarshi yace gaskya akwai atsala,afili
kuma yace ok tobakomai apple zamu wuce kar'in rik'eki dewa, tace to mungode
Allah ya kiyaye hanya ka gaida miher,yace zataji insha Allah sannan suka k'arasa
gunsu marwan.

Manosh yace to muje guys,muh'd yace amma baka kyautaba danka gama hiranka sekace
muje,yace to ai ahikenan nima ba gamawa nayiba kawai dai hakura nayi dan haka
kuma ku hakura,marwan yace to rashida nagide sannan yace aunty maryam mun gode
sosai semun sake zuwa dan yanzu kam ni kad'ai zan dinga zuwa prince yana takura
mana,dariya sukayi lokacin manoah ya fito da k'aramar kits a mota yace to
shikenan nima hakan yafimin kowa yayi zuwanshi,manosh ya mik'awa maryam kits
d'in batare dayace komaiba tasa hannu ta karb'a tare dayin godiya sannan ya
mikawa samira wani leda yace ga tsarabanku,godiya sukayi sosai sannan sukayi
sallama suka tafi.

Ahanyane manosh yake ce musu akwai matsala gaskya dole su dad suzo da wuri ayi
tambaya dan ban yarda da uncle ibrahim d'innan da apple ta gayaminba. Dariya su
muh'd sukasa tare da cewa soja da tsoro,yace a'a kunsan fa bana zama sosai,shi
kuwa yanzu idan ya dawo daga NYSC ai suna tare kenan 24 gaskya da sake. Marwan
yace tobase ke hakuraba tunda ya zama sirikina zan nema maka wata ai,duka manosh
yakaiwa marwan yace d'an iska wlh zanyi maganinku bazaku sake biyoniba,hakadai
suketa hira da hara har suka isa gida lokacin muhsin ya dawo dagun zahida nan
dai sukaita tsokanan manosh wai gaskya seka dage tunda ku biyu masoyanta. Nima
dai sad-nas nad'an tayasu kad'an😜
[7:10am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: 🍭🎈AUNTY'N YARA🍧🎁AUNTY'N YARA🍧🎁

Writeen by sad-nas
&
Hama gee muh'd

17-18 Washe gari miher ta kira maryam a waya suka gaisa sosai take ce mata iher
ce k'anwar captain manosh,murmushi maryam tayi sannan suka sake gaisawa,miher
tace dan Allah ki rik'e min bro na da kyau dan ina sonshi sosai banaso ya shiga
cikin damuwa ta dalilinki pls auntyna,maryam tace insha Allah hakan bazai faru
ki kwantar da hankalinki,dad'i sosai miher taji sukaita hira sannan sukayi
sallama.

Mahaifin manosh kuwa tunda yaji cewa a girei d'ansa yake neman aure se
hankalinsa ya tashi,amma dai dukda haka ya gayawa aminansa sunce,zasuje nemawa
manosh aure dan yana son ayi biki da wuri,amma se iyayen,sukace abari tunda
AZUMI yazo se bayan sallah se suje tunda su marwanma sun sami nasu matan,dan
haka aka yanke shawara za'aje bayan sallah.

Soyayyan abokai da k'awaye dai yana tafiya yadda ya kamata abin gwanin ban
sha'awa. Sannan abinda zaifi burgeka a soyayyarsu shine soyayya mai tsafta
sukeyi,bakamar irin soyayyar da akeyi a zamanin yanzuba,seka budurwa da saurayi
suna kissing d'in junansu wasuma har huging kai wasuma har tab'a jikinsu suke
bari namiji su aganinsu hakan shine wayewa ko kuma iya soyayya amma fa ku sani
bakomai bane se sab'on Allah da kuma ragewa kanki mutunci a idon saurayin.
Wlh mafi yawancin maza suna son tab'a jikin mace,wasu sunayi yin hakan dan nasu
manufarne wasu kuma sunayin hakanne dan su gwada macen,idan kika yarda yaci gaba
da tab'aki to wlh wani daga ranan bazaki sake ganin ya dawoba dan zai d'auka duk

samarinki haka suke miki tunda yasan halin mazan. Amma idan kika taka mishi
birki dole ne zaiyi respecting naki sosai kuma bazai tab'a rabuwa dakeba sedai
in dama ba aurenki yake sonyiba.
"Amma zamanin da muke ciki yanzu sedai addu'a" se kaga budurwa ta nemi yaro
k'arami kona makotanta ta goyashi sunce hospital wai tanaso tayi planing dan ta
bada tazara,su kuwa doctor ko nurse ba tare dasunyi bincikeba sesu sama duk
kalan planing d'in da take buk'ata shikenan budurwa ta maida yaro taje ta samu
saurayinta wanda dama shine ya bata wannan shawaran waidan ya kai sadakinta
gidansu yana ga ai yanzu kam shikenan kin zamat tashi,shiyasa taje tayi planing
domin su shek'e ayarsu kafin suyi aure ya santa tun a waje,kuma bazai tab'a
aurenkiba tunda ya samu abunda yake so,koda kuwa ya aureki tofa bazai dinga
ganinki da mitunciba kuma wulak'anci kala kala zai dinga miki bayan zunibin da
kika kwasa wa kanki. Hmmm 'yan uwana mu kula mu dinga yiwa kanmu fad'a mu kare
addininmu da kuma martabarmu ALLAH YASA MU DACE MUFI K'ARFIN ZUCIYANMU AMEEN.

Addininmu ya koyar damu addu'oi iri iri,zamanin yanzu seda addu'a. Ina masu
yara,ko k'anne ko jikoki dadai sauransu mu tsaya tsayin daka dan nemowa yaranmu
ilimin addini kafin mujega na zamani,kuyi k'ok'ari kusa yaranku a ISLAMIYYA. Mu
kasance masu yiwa yaranmu addu'oi da fad'in alkhairi akansu idan sun b'ata mana
rai bawai muyi musu bakiba. Wannan addu'a tana kore komai,tana kare komai a
fad'in duniyannan dan haka mudinga yiwa yaranmu safe da yamma. Fiyayyen halitta
ANNABI MUHAMMAD (S A W) yace koda sabon gida mutum yayi tofa wannan addu'a ita
kad'ai zakayi batare dakayi sauk'an QUR'AN ba ko kuma yanka, addu'a ce mai kyau
sosai.

AUZU BI KALIMATILLAHI TAMMAT,MINSHARRI MA FALAK3× sannan shine yace adinga yiwa
yara sau 2 a rana ma'ana safe da yamma so uku2. Allah ya gafarta mana
kurakurenmu ameen.

Lokacin musabak'a yayi. Kuma auntyn yara itace aka d'auka a girei local gov,
inda aka shiryashine a mubi local gov. Duk wani malamin sunna ya halarci wannan
musabak'an amma banda manosh sakamakon yanayin aikinsu,amma friends nashi
duksun halarci gurin inda maryam muh'd Attah kokuma ince aunty'n yara zata
karanta SURATUL BAK'ARA.
K'ira'a kakeji yana tashi masu imani se zubar da kwalla sukeyi,dole abin ya
birgeka mai sauraro da kuma mai kallo. Koda akazo kan maryam ana kiran sunanta
jama'a suka d'au kabbara ALLAHU AKBAR kaje ji yana tashi a wannan gurin, himar
d'inta milk colour har k'asa mai hannu sannan tafiya takeyi cikin nutsuwa harta
k'arasa ta k'arb'i abin karatu ta fara da korar shaid'an sannan ta fara karatu
😓 ☺. Ba iyayen maryam kad'aiba,harda wandama basu santaba seda suka zubda
kwalla da murya da Allah ya bata mai dad'i sauraro,su majid masuji dad'i
muryantaba se a yau da take karatu,kowa da abinda yake fad'a a ranshi akan
maryam. Miher kuka takeyi sosai dajin karatun maryam tana mai jin haushin kanta
data fifita karatun boko sama dana addininta.
Har aka tsaida maryam sannan ta tsaya suma kansu malaman badan sunsoba sedan
lokaci yayi nata kamma harya wuce. Kabbara kawai akeyi da k'arfin gaske su
muhsinma da muryansu sosai suke kabbara yayinda manosh yake jiyowa daga wayansa
da miher ta kirashi yanata sauraro,wani k'aunartane na susamman yake shigansa
wanda shi kansa bazai iya baiyyanawa. ALLAHU AKBAR, dan Allah FANS kuma kuce
ALLAHU AKBAR!nasan ku kanku maryam ta burgeku,k'ilama baza'a rasa masu zubda
kwallaba danjin haushin kansu na rashin neman ilimin addini,tofa ku sani lokaci
mai k'ure mukuba ba'a tsufa da neman ilimi Allah ya bamu ilimi bar albarka damu
da 'ya'yanmu ameen.
[7:10am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: 🍭🎈AUNTY'N YARA🍧🎁AUNTY'N YARA🍧🎁

Writeen by sad-nas
&
Hama gee muh'd

19-20 Bayan an kammalane ake kiran wanda sukazo na d'aya, a suratul bak'ara
maryam itace tazo na d'aya. Koda aka kirata kuka takeyi harta isa inda *sheik
malam balalau* ya bata kyautarta masu sayawa tanata hawayae ta k'arb'a harda
key'n mota, jama'a suna ta kabbara.
Hakadai aka gama taron miher ta k'ara gurinta ta rungumeta tana tayata murna
tare da murmushi sosai a fiskarta. Itama maryam d'in rungumeta tayi sannan
k'awayenta su su 4 d'in suka rungumeta kowa yana tayata murna su muhsin suka
k'araso gunta suna tayata murna dad'i taji sosai ga abokan arziki dukdai se zuwa
akeyi ana tayata murna. Bayan tad'an nutsu ne se miher ta mik'o mata waya tace
bro na zaiyi magana dakai, karb'a tayi tare da komawa gefe tace slm.
"Wslm my appale congratulatoins" tace "thankyou"ya aiki,yace ki bari kawai kawai
wannan aikin namu baiyiba gadkya dayasa nayi missing taro kamar wannan,am verry
sorry my apple,tave bakomai wlh wa'yanda ka turoma yayi wlh naji dad'i sosai
Allah yabar k'auna,yace ameen apple gaskya bansan mezan ceba wlh dan lokacin da
nakejin karatunki ni kaina bansan yanayin da nakeji ba,murmushi tayi tace dama
kaji,yace yes miher ta kirani naji tun daga farko har k'arshe. Tace eyyah nagode
zamuyi waya anjuma kaji,yace ok wait,tace to menene,yace *I LUV U* murmushi tayi
tace *minfu mi yid'ima* sannan ta kashe wayar yanata dariya tare dajin dad'i a
ransansa da samu mace kamar maryam.

Duk kyautan ta rabar da wasu,mota *honda civic ce* ash ta samu dan haka ta
mallakawa mahaifinta shi kyauta.
Ranan auntyn yara tana tafiya zataje kaiwa mahaifinta abinci seta ga wani mutum
jikinsa duk jini yana buk'atan taimako,da sauri ta k'arasa tace subhanalillah
lfy bawan Allah,yace wlh wanine ya bugeni da mota ko tsayawa baiyiba,kwalla ne
kawai maryam ta fara dan yadda yaji rauni tace amma mutane sam babu imani a
wannan zamanin, nan ta tsaida wani mai mashin tace dan Allah ka taimaka mishi,ba
musu ya taimaka zai kaishi asibi,tace Allah ya kare Allah ya baka lfy,yace ameen
'yan mata nagode gaskya kina da hali mai kyau,murmushi tayi tace bakomai
d'an'uwa amma a maimakon godiyan da zakamin,inaso idan kasamu dama kataimaki
mutane uku a rayuwarka,suma kuma kace su taimakawa wasu ukun,yace insha
Allah,sannan mai mashi yace yaja suka tafi.
Maryam tana tafya tana tuanin mahaifin su rashida k'awarta,shima wanine ya
bugeshi da mota amma sam yak'i tsayawa wanda hakan shine sanadiyan rasuwanshi
dayake uazo da k'aran kwana.

Hajiya iya tana zaune a palonta tanata zubda hawaye ita kad'ai,tana cewa yah
Allah ka yafemin da irin wannan zalinci da son zuciya irin nawa,Allah ka bani
mafita akan wannan abi dana aikata tun kafin inbar duniya.

Lokaci yata ta tafiya yau azimi saira sati, bayin Allah sunata raba abinci wa

talakawa, manosh da abokansa suka had'a kayan abinci sosai buhu sugar shinkafa
gero gyad'a da dai sairansu suka raba a jimeta da gidan marayu sannan suka aika
da sauran wa gidajen surikansu.
Su kuwa 'yan matan sayayya na musamman suka musu na kayan azumi.
Azumi saura 3days uncle ibrahim ya dawo, murna agun yara ba'a magana, shima yayi
kewarsu sosai nan dai akaita ihun da tsalen dawowansa. Ibrahim mutum ne mai
kirki ga hankali da nutsuwa bafulatanine baida hanke sosai amma kyakkyawane.
Suna kama sak da albdallah,rashine kawai tayi kama da mamansu amma sukama
babansu marigayi suka d'auko.
Lokacin maryam tana gidansu rashida ita da samira,dan haka suka fito sukaje
gunshi suna mishi sannanu da dawowa. Kallonsu yakeyi cike da kewarsu ya e
sannunku na sameku lfy,sukace lfy lau sannan suka k'arb'i kayansa suka wuce
mishi dashi gida.

Bayan isha ibrahim yazo gidan su maryam kamar yadda ya saba. A tsakar gida
maryam ta shinfid'a masa taburma,bayan sun gaisa da mamane yana zaune suka gaisa
da maryam suna ta hira dai daga nan mama ta wuce d'aki.
Ibrahim yace ya bayan rabuwa,tace alhamdulillah gaskya munyi kewarka sosai ,yace
to ai nima haka kuma alhamdulillah yanzu kam na kammala se muka aiki ayita
tayamu da addu'a. Maryam tace to Allah ya baka mai albarka yace ameen result
naku shuru ko,tace eh wlh har yanzu,yace naji ana cewa soon zai fita,tace to
Allah yasa muga alkhairi,yace ameen ya fama da yara,tace bakomai aina saba yanzu
suma kullum sesun tambayi yaushe zaka dawo,yace eyyah ai sunce tunda na dawo
yanzu to auntyn yara seta huta ka karb'eta,murmushi maryam tayi tace hakadai
suke fad'a tun kafin ka dawo. Yace hakan za'ayi ai dan kina k'ok'ari abubuwan
suna miki yawa aunty,tace wlh bakomai har yanzu ni aunty ce,yace eh mana har
gobema,dariya tayi shima haka sunata hira har isha suna jiyo miryan abdallah mai
dad'i yana kiran sallah,se yace bari na tafi seda safe ki gayawa mama na
tafi,yace to a huta gajiya,yace tonagode sannan ya tafi.

Lubna kuwa abun duniya ya dameta taji ance bayan sallah za'aje tambayan aurensu
manosh,gashi tasan maryam ce yarinyar da manosh yake so. Hankalinta a tashe tuni
ta dena kiran maryam bayan zagi kala kala da takeyiwa maryam, harta hakura ta
dena dan sam maryam bata kulata.
Wasu 'yan iskan maza y'an iska ta nemo y'an shaye shaye tace tanaso su sace
maryam sannan su watsa mata *acid* a fiskanta ta biyasu kud'i sosai tare da basu
address d'in maryam da kuma nuna musu hotonta,amma tace su bari se bayan azumi
ma'a dai bayan sallah da kamar sati d'ati d'aya sesu d'auketa.

Yau aka d'aiki azimi maryam tana gun hajiya iya suna hira, hajiya tace maryam
kiyita sani a addu'a kinji,maryam tace insha Allah hajiya.
Azumi yanata tfy,maryam sunayin abincin masallaci ita da mahaifiyarta sannan
wasu sukan shiga dan su tayasu aiki dab magrib se'a fita dashi kofar masallaci
ayita rabawa bayin Allah irin qanda gwamnati take rarraba a unguwannin nan.
[7:10am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: 🍭🎈AUNTY'N YARA🍧🎁AUNTY'N YARA🍧🎁

Written by sad-nas
&

Hama gee muh'd

21-22 Azumi yanata tafiya,abdallah se samun kayan sallah yakeyi agun jama'a. Dan
shine mai kiran sallah a masallaci gashi da shiga rai. Ranan manosh manosh da
marwan sunje girei se marwan yace aboki abdallah zoka gaisa da abokina wanda zai
auri auntyn yara.
Abdallah yazo suka gaisa cikin fara'a yace dama kaine kake neman auntynah,manosh
yace eh nine,abdallah yace to Allah ka rik'eta da amana karka cutar da ita dan
Allah dan ance soja suna dukan matansu. Dariya sosai su manosh sukayi sannanya
rik'o hannun abdallah yace har abada abdallah,karka sa ranni zan wulak'anta
maryam domin ina k'aunarta fiye da yadda nake k'aunar kaika kuma wlh bacika baki
nake makaba kaji? Abdallah yace alhamdulillah naji dad'i sosai Allah ya tabbatar
muku da alkhairi,sukace ameen,sannan yace auntyn yara ta aikeni bari aje aje na
dawo,sukace to seka dawo sannan ya tafi.
Abdallah yaje gunda uncle ibrahim yake da friends nashi yamusu slm tare da
gaisuwa sannan yace yah ibrahim gurinka nazo an aikoni,ibrahim yace to ina
jinka,se kuma abdallan yayi shuru,ganin shurunne ibrahim ya mik'e yace to muje
gefe ka kaya mun.

Bayan sun koma gefene abdallah yace yah ibrahim auntyn yara ce ta aikoni
gunka,dad'i sosai ibrahim yaji da akace auntyn yara yana sonji menene aikan.
Abdallah yace tace wai tayita kiran number'nka amma yak'i tafiya,wai inzo ince
maka tayi bak'i kuma tana so gu gaisa dasu. Ibrahim yace bak'i wani iri maza ko
mata?abdallah yace maza wanda yake nemanta da kuma aunty rashida. K'irjin
ibrahim ya buga sosai yace abdallah dama zance danaji da gaskene kenan akan
auntyn yara? Abdallah yace eh yaya hakane tare da sunkuyar da kansa k'asa yana
tusayin yayan nashi don shi kad'ai yasan irin k'aunar auntyn yara da yakeyi amma
dayake bai gama karatunshiba shiyasama baiyiwa mahaifinta magana akaiba yafiso
seya gama komai na karatunshi. Ibrahim yace kaje ina zuwa,sannan abdallah ya
tafi jikinshi a sanyaye.

Ibrahim ya kunna wayanshi ya kira number'n maryam ringing d'aya ta d'aunka tare
da salma,wani irin dad'i yaji har cikin ranshi dajin daddad'ar muryanta. Yace
aunty wai kina nemana,murmushi tayi tace eh na kira wayanka ban samuba,yace wlh
na kashene saka makon damuna da akayi,tace eyyah,yace ganinan ina zuwa ki basu
hakuri kinji,tace laa bakomai wlh sunanan a waje dama gurinka kawai sukazo. Yace
tonagode da mutuntani da kikayi aunty se anjuma,tace bakomai aikafi haka a guna
uncle ibrahima nima nagode.

Koda ya ajiye wayan shi kad'ai yasan meyakeji a cikin ranshi game da maryam.
Ya k'arasa gumsu da sallama suka gaisa sosai kuma cikin fara'a dama shi ibrahim
na kowane kamar dai maryam d'in. Hira sukayi sosai kamar sun dad'e da sanin
juna,yayi musu tambayoyi suka bashi amsan gaskya domin wani abunba manosh
b'oyewa yakeyi,sam bayaso asan mahaifinshi mai arzikine. Haka sukaitayidai har
suka gama sannan suka sallama ibrahim ya wuce gida,se manosh ya kira maryam a
waya yace aunt pls ki fito in ganki zamu wuce,tace har gun gaisa kenan zaku
tafi,yace eh wlh ibrahim yana da kirki sosai wlh gaskya naji dad'in had'uwa
dashi,dad'i taji da aka yabi ibrahim tace nagode nidai bazan fitoba aiba gurina
kazoba,ya marairaice murya yace pls aunt kinga marwan yanata min dariya ai gara
shi tunda rashi bata nan hankalinsa a kwance "pls come aou aunt"kodon fita kunya

a idon marwan don wlh yau idan muka koma shimenan ya samu abun tsokana harsu
majid sesunji. Dariya tayi tare da katse wayar d'inkin atamface a jikinta na
fitet gaun seta sa himar iya gwinwanta ta fito.
Tunda ya hangota yake murmushi tare da k'are mata kallo harta iso gunsu tana
murmushi,marwan yace ai wlh banso ki fito har addu'a nakeyi a raina amma se
gashi kin fito meyasa aunt,mirmushi tayi tace saboda banaso ku mishi
dariya,manosh yace "thankyou aunt"tare da kaiwa marwan bugu a bayansa yayi
saurin shigewa mota gurin tuk'i ya rufe kofar maryam tanata dariya. Manosh ya
dawo da kallonshi kan maryam yace wato har kin fara min yanga ko,tace aiba yana
bane dama gun uncle ibrahim kukazo ba gunmuba,yace eh amma dai ai kinsan zanso
in gaki ko,tace to ai gashi ka ganni kuma ni zan wuce gida,yace nidai ban
sallamekiba tukunna,tace to sallameni,murmushi yayi wanda ya k'ara mishi kyau
tana kallonshi shi kuwa wani gurin yake kallo daban. Tace wlh ka dingayin
mirmushi yana k'ara maka kyau,dad'i yaji sosai yace wauace ki kalleni,mirmushi
tayi tace ni ban kallekaba kawai dai na fad'a makane,yace kin kalleni mana kuma
ai ke kika sani na fara murmushi sosai wlh,tace ahakan,yace "yes" ki tambayi
miher zata gaya miki ni gaskya bancikayin fara'aba, yace hmmm to gaskya nidai ka
dinga yi kaji,yace ai inayi kuma danke.
Tace to shikenan zan wuce,yace meyasa kikemin hakane aunt kodon kinga ina sonki
sosaine shiyasa kike min haka,tace a'a wlh aiba guna kazoba kuma ai min
gaisa,yace to shikenan mun tafi,tace kayi fushi kenan,yace a'a banyiba kawai dai
zamu tafine,kallonshi takeyi amma sam yak'i kallonta kuma yana tsaye yana
fiskantarta,tace toshikenan Allah ya kiyaye hanya,yace ameen sannan ta juya ta
shiga gida,mota ya bud'e yashiga marwan yaja suka tafi.

Manosh ya saba idan suka bar girei seya kira maryam a hanya,amma yau sam sebai
kirataba abun yad'an dameta tace to kodai fushi yayine? Har bayan 2hrs bai
kiraba,kuma a wannan lokacin tasan suna gida,marwan ne ya kirata yace aunt mun
iso gida lfy,tace alhamdulillah tona gode sosai,yace bakomai wlh mune da godiya
sannan sukayi sallama.

Har bayan isha manosh bai kira maryam se taji taba kyauta mishiba dan tasan
fushi yayi dukda dai basu tab'a

Please Login or Register in order to submit comment