Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

samun matsalaba se yau. Har 9:00pm seta d'auki
wayanta ta kirashi yanata ringing harya d'auke,zata sake kira kenan setaga call
d'inshi,ta d'auka cikin sanyin murya tace hello
Shuru yayi baice komaiba
Ta sake cewa hello
Nanma shuru yak'i yayi magana, tace hello manosh,
Karon farko data kira sunanshi kenan,seyaji dad'i har cikin ranshi amma baice
komaiba,ta sake cewa "manosh pls talk 2me" yace me kike so nace miki aunt? Tace
wai fushi kakeyi danine, shuru yayi uanajin daddad'ar muryanta,ta sake cewa
"manosh am talking to you" yace inace ni kike kora agaban marwan ko? Wani iri
taji a ranta dan yadda yayi maganan batasan lokacin datace "am so sorry manosh i
din't main to hurt you pls?" Nanma shuru yayi,ta sake cewa manosh wai bazaka min
magana bane kuma kanajina? Yace "yes" take jikinta yayi sanyi tace manosh am
sorry pls,nanma shuru yayi seta katse wayan. Hankalinta ya tashi sosai tayi dana
sanin yimasa hakan.

Har 10pm manosh bai sake kirantaba,seta tsinci kanta cikin damuwa sosai sam ta
kasa sakewa,dan tana son manosh sosai acikin ranta. K'arar shigowar texs tayi a
wayanta da sauri ta d'auka ta bud'e taga

_Am sorry too apple_
_I love you so much_
_Nd i will call you leta_
_Am talking with my dad now okey,manosh loves you so verry much apple_.

Maryam tana gama karanta texs d'in taji dad'i sosai a ranta tayi murmushi tana
mai k'ara jin sonshi na ratsa jikinta,tace i love you too peach tare da rufe
idanunta tana murmushi.....
[7:10am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: 😔🎈AUNTY'N YARA🍧🎁AUNTY'N YARA🍧🎁

Written by sad-nas
&
Hama gee muh'd

*Dedicated 2 sarah katagum*💋

23-24 Seda manosh suka gama magana da dad nashi,sannan ya koma d'aki ya kira
maryam har gurin 11:00pm. Maryam har tayi bacci,ta jiyo wayanta na k'ara da
d'auka tare da sawa a kunnenta amma idonta a rufe yake tace hello,cikin muryan
bacci, yace "apple am sorry for waking you up"tace "don worry manosh am
fine"muryanta ya kashe mishi jiki gabad'aya atake yaji inama tana kusa dashine.
Sakeyin k'asa da muryanshi yayi yace "are you sure" tace "yeah am fine"ai manosh
aiseya fara juyi akan gadonshi yace "no apple you have to sleep"zan kiraki da
asuba kinji,tace "okey good night" yace sweet dreams apple,murmushi kawai ta
mishi tare da katse wayar. Manosh ya sauke ajiyar zuciya yace "ooh my
apple"Allah ya nunamin ranar da zan mallakeki a matsayin matata,da wannan
tunanin bacci ya kwasheshi.

Wannan karon manosh baiyi tfy ba,har akayi nisa da azumi sannan suka kaiwa 'yan
matansu kayan sallah a d'inke kuma masu tsada,da kuma redimate ga fashions ga
takalma da jaka da turare komai dai suka had'o musu kowa da irin nashi,sannan
sukayiwa iyayensu,harta abdallah seda manosh da marwan suka mishi kayan sallah.

Almajirai sam basa so azumi ya k'are,gashi indai a girene to kusan rabinsu
sunsan maryam. Daidai da sabulun wanki ko omo haka zatayita raba musu 1/1 tace
suyi wanki dashi,dan haka suna sonta sosai.

Azumi
gashi
wanke
wanke

ya k'are yau gobe sallah se murna akeyi su maryam ansha kitso gata da
amma sam ita tafi so tayi kitso akan tabar kanta haka,su rashida kuwa
kai kawai sukayi amma zahida kitso tayi da ameena babale,su samirane yan
kai,gashi suna lalle gayu dai sosai sukayi.

Manosh bai samu zuwa rananba dan haka maryam tayi *cake* mai dad'i kuma
had'ad'd'e dama duk sallah tanayi. Mhaifinta kuwa drinks ya sayo kala kala dan
yasan 'yar tashi da jama'a bugu da k'ari suna son maryam sona hak'ik'a zai iya
kashe duk dukiyarsa dan farin cikin maryam,shiyasa ma idan ka shiga d'akin
maryam wlh bazaka tab'a zatan cewa a cikin gidansu d'akinta yakeba dan yadda
mahaifinta ya gyara mata shi,gurin zuba littattafaima na musammanne,ga computer
komai dai se wanda ya gani.

Yau take sallah kowa se murna su maryam suka shirya shirya tafiya *idi* anko
suka sha ita da rashida da samira da himar nasu neavy blue toyobo dogaye har
k'asa masu hannu sunyi ado sosai se k'amshi sukeyi. Mama tazo tace to maryam
kinyi bak'o a waje,tace bako kima mama,tace eh,da sauri ta mik'e ta fita kawai
setaga drivern manosh ne da *406* ash wai yazo ya kaisu masallaci. Mamaki ya
kama maryam tace wlh kaje kawai masallacin fa babu nisa da k'afa zamu tafi,yace
a'a madam idan na koma fad'a zaimin kiyi hakuri. Shuru tayi tace to ina zuwa,nan
ta koma ta sanar da mamanta,mamanta tace to maryam kuje kawai tunda haryazo,
haka suka fito abdallah ne a gaban motan su kuwa ukun suna baya sunata salati
zikiri har suka isa, sannan yayi pakin a gefe shima yaje akayi sallah.
*Allahu Akbar Allah ka k'ara dauwamar damu a musulunci ameen*
Bayan an idarne sukaita hotuna a wayansu,ai se suka hango uncle ibrahim da
friends nashi nan suka wuce aka gaisa sannan sukayi pictures da uncle ibrahim da
kuma friends nashi yana tsaye kusa da maryam hotunan sunyi kyau sosai,shima
driver se d'aukansu yakeyi a tap batare da sun saniba,amma sam bai d'auki su
ibrahim ba.
Bayan sun gama ne sukayi sallama sannan suka zo gun drivern ya maidasu gida.
*cake din* maryam ta zuba mishi a kula tare da soyayyen naman kaza da kuma ruwan
faro mai sanyi ta bashi,karb'a yayi tare da godiya ya tafi.
Bayan tfyanshine ta kira manosh tace mun godefa,yace bamun b'ataba meyasa kika
kirani,tace godiya na kira in maka sannan kuma....yace sannan kuma me, tace
inaso ka kawo min *miher* anjuma mu yini,yace coman kike bani kenan,tace *no
captain* alfarma nake nema,yace nak'i bazan kawotaba,tace haba mana pls ka
kawota,yace nak'i d'in,tace to shikenan ni zanzo gurinta anjuma,murmushi yayi
yace zan turo azo a d'aukeki sannan ya katse wayar ya sake kiranta.
Ta d'auka tace bana bukata dama zamuje gun zahidane se mu wuce gurin ameena.
Yace wa kika tambaya babu inda zakije,tace saboda da me,yace ra'ayinane
hakan,shuru tayi tace to shikenan ka kawomin miher dan tace seka yadda kafin
take fita wani girin pls ka barta,yace sekin ce *am sorry peach* dariya tayi
tace menayi to,yace nidai na gaya miki,tace ok am sorry peach,murmushi yayi yace
tosekin fad'a da muryana,tace ni mace kai miji ai muryanmu dabanbanci bazan iya
ba,yace to bazata zoba,tace pls mana captain,yace wlh sekinyi muryana, nan dai
ta gyara muryanta wai a dole zatayi irin nashi,ai tun bata k'arasaba take dariya
shima haka take ta katse wayar tanata dariya shima hakanne muhsin yace ku
kamashi muje gun malam mahmud yayi mishi ruk'iyya inaga yad'an samu matsala
ne,daroya sosai manosh yakeyi harya shiga gida,mum da miher se binshi da kallo
sukeyi,miher tace the prince lfya kuwa,yace wlh maryam ce take haukatani uama
manta mum nashi tana palon,ai take ya seta kanshi yace mum dama kina nan
ne,yad'an sosa k'eya,tace nidai inaso akawomin maryam d'innan inga mai sunana
kuma sirikata,miher tace dama yau nake so inje in bro ya yadda zuwa jibi kuma se
inje mu taho tare.
Manosh yace a'a ki bari dai jibin se driver ya kaiki ku taho tare,miher bata so
hakanba amma tasan manosh magana d'aya yakeyi dan haka ta sanar da maryam cewa
baza samu zuwaba se jibi,maryam bataji dad'iba dan batayi zaton manosh zaik'iba.

Da yamma su manosh sukaje gaisuwa gun surukansu tun daga gun mahaifin ameena
suka fara har na zahida sannan suka wuce gire mota 3 masu zafi.
Kyakkyawan k'arb'a aka musu dama ansan da zuwansu. Koda sukaje gidansu
rashida da samira sannan suka wuce batare dasunyi hira da 'yan matanba.
Bayan sun komane ya kira maryam se fushi takeyi waidan ya hana miher zuwa. Babu
irin rarrashin dabai mataba amma tak'i tanata fushi. Yace am sorry apple zan
kawota jibi da kaina kinji,tace banso indai kai zaka kawota bazaniko inaba,yace
to shikenan bazan zoba zan kiraki anjuma pls zan d'auki wani kiran kinji,tabace
komaiba ta katse wayan shi kuwa ya d'auki wayan oganshi.

Kamar yadda manosh yace yau miher ta shirya driver ya kaita gun maryam,mirna
sosai maryam tayi bayan sun gaisa da mamane se suka wuce d'akinta,ita kanta
miher d'akin ya burgeta dukda dai ita 'yar masu akwai ne. Hira sukayi kad'an
maryam ta cikawa miher ciki da abin mak'ulashe sannan tace bari in yiwa mama
sallama semu tafi dan in dawo da wuri koh,tare suka mik'e sukai mata sallama
tace a gaishesu sannan suka tafi.

After dress ce red a jikin maryam tayi kyau sosai taga sun tsaya a wani
katafaren gida. Koda aka bud'e gate se taga ashe cikin yafi wajen had'uwa,bayan
sun k'arasane taketa ganin flawers kala kala masu kyau sosai. Miher tana rik'e
da hannunta se gaisheta gards din sukeyi har suka k'arasa palo, me zata
gani...hoton miher da manosh ne da kuma iyayensu,jikinta yayi sanyi tanata
fad'in *innalillahi wa'inna ilaihirraji'un* tabbas maryam bazata tab'a mance
fiskan wannan mutumin da take tunanin shine mahaifin manosh ba,acikin ranta kuwa
tace wlh bazan tab'a b'oyewaba koda hakan zaisa in rabu da manosh peach d'inaba.
Miher tace yanaga kina ta kallon hotonmu da iyayenmu nadai fi bro manosh
kyau,murmushin kawai tayi tace nidai bance komaiba,miher ta kaita d'aya palon
sannan ta zauna tace ina zuwa bari na kira mum sannan ta wuce wani kofa,ita kuwa
tana zaune kanta a sunkuye tana tunani.
[7:10am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: 🍭🎈AUNTY'N YARA🍧🎁AUNTY'N YARA🍧🎁

Written by sad-nas
&
Hama gee muh'd

Dedicated 2 FIDDY G MUH'D
💋😘😘

25-26 Mum da miher sun fito a tare kan maryam a sunkuye, tayi saurin durqusawa
qasa ta gaishe da mum din manosh cikin fara'a da sakewa sosae mum ta amsa mata
gaisuwa tare da tambayanta ya mutanen gidan, sun dae gaisa sosae amma kan maryam
a sunkuye yake. Mum tace ki saki jikinki fa , nan kaman gida ne haka dae sukaci
gaba da hira mum ta kama hanya ta tafi ta barsu ita da miher. Miher ta kawo mata
kayan maqolashe kala kala, maryam bata iya cin komai ba in banda ruwa da tasha.

Suka dan yi hira kadan daedae lokacin dad din manosh ya shigo yana kiran miher
da sauri tace naam dad, sannan ta fita taje wurin dad dinta, yace ke da wa kuka
shigo?? Tace nida wanda bro manosh zae aura ne. Tazo gaida mom ne nan dae tace
dad bari tazo ta gaishe ka, tayi sauri ta koma taje ta kira mrym da sauri ta
fito kanta a sunkuye ta durqusa har qasa ta gaishe da dad shima ba laifi cikin
fara'a ya amsa. Koda suka gaisa ya wuce dakinshi ita kuwa maryam tana kallonsa a
nitse ta sake tabbatarwa wannan shine mutumin da nan da bazata taba mantawa
dashi ba a rayuwarta.

Jiki sanyaye ta koma falo suka zauna dae, ita kanta miher ta lura da sauyi daga
gareta amma bata ce mata komai ba. Maryam ta dan zauna na kusan 30 mins tace to
gaskiya zata tafi saboda batason dare yayi miher tace bazaki tafi ynxu ba dole
se bro manosh ya dawo dan shine zai maida ke gida maryam tace aa ni bamuyi haka
dashi ba dan allah ki tashi ni zan koma gida. Miher taga dae da gaske takeyi dan
haka ta kira bro manosh a waya ta sanar dashi bada jimawa ba yazo daedae
lokacinda suka fito tayi sallama wa mum zata tafi, mum ta hada mata goma ta
arziki ta rako ta har kofar falo sannan ta juya , shi ko dad daman ya riga da
ya fice. Ko da ta iso wurin mota tana tsaye shi ko manosh ya danno shi da marwan
kallonta yakeyi tun daga sama har qasa saboda kayan ya bala'in mata kyau
murmushi kawae takeyi tare da gaishe da marwan bayan sun gaisa ne manosh ya
matso kusa da ita yace wato bazaki gaishe ni ba kenan?? Shuru tayi batace mishi
komai ba tace nidae ka kaini gida yace ae ba ni na kawo ki ba wanda ta kawo ki
saeta maida ke,maryam ta maida kallonta gun marwan tace marwan kaji abinda yace
ko,marwan yace rabu dashi muje in maidake,duka manosh ya kaiwa marwan tare da
cewa ina ruwanka acikin hidimata,marwan yace da ruwana mana aunt muje in kaiki
gida kinji tare da dannan keyn mota ya bud'e mata gaba ta shiga ta zauna sannan
manosh ya karb'e keyn a hannun marwan yace zaka zauna a baya kenan,marwan yace
eh ba matsala,maryam tayi mirmushi yayinda miher tasa mata goma na arzikin da
mum ta had'ota dashi sukai sallama manosh yaja mota suka tafi.

Tunda suka fara tfy manosh da marwan ne suketa hira itakam tayi shuru tana ta
tunani a ranta. Manosh ya lura cewa akwai sauyi tattare da ita,yace kira sunanta
a hankali apple,juyowa tayi suka had'a ido sannan ta mayar da kanta gefe,shuru
yari bai sake cewa komaiba har suka iso girei,marwan yace jirani abokina bari
naje gun rash a tsatstsaye yanzu zan dawo.
Bayan marwan ya tafine su kuwa suna zaune a cikin mota manosh yace apple meyake
damunki? Murmushi tayi tace bakomai,yace no apple karmu fara haka dake pls ki
gayamin dan nasan akwai wani abu,tace gaskya naji dad'in yadda aka karb'eni a
gidanku mum naka tana sona sosai nagode sosai tana murmushi tare da kallon
kyawawan idanunsa,shima idanun nata yake kallon yayi da yakejin shaid'an yana
zugashi da cewa kayi kissing nata manosh,maryam taga kallon da yake mata ya fara
wuce gona da iri dan haka tayi saurin kawar da kanta tare da cewa zan shiga
gida. Manosh ya dawo hayyacinsa yace bakomai apple kin cancanci a k'aunaceki
domin kina da halayya na gari masu kyau daban sha'awa,dad'i taji tace ai kaima
haka,dan azamanin yanzu da kyar asamu namijin da baya iya tab'a koda hannun
budurwansa shiyasa kullum nake k'ara sonka manosh nasan cewa kana min so na
gaskyane kuma mai tsafta. Jikinshi yayi sanyi dajin kalaman maryam,yayi hamdala
a cikin zuciyarsa yace Allah nagode maka danafi k'arfin shaid'an a wannan
lokacin Allah ka k'ara kareni akan sha'awar da nakeyiwa maryam ameen. Ta
katseshi da cewa ya naga kayi shuru,yace bakomai kawai bana so ki tafine harse
marwan ya dawo,murmushi tayi tace toshikenan kamin hira,yace kedai zaki min,tace
ni nawa sun k'are ai,yace to mata biyu nake sofa in aura dake da kuma wata kin
amince? Murmushi tayi tace eh na amince mana ai halal ne kana iya yin
hud'uma,dariya sosai manosh yakeyi,wanda yake burge maryam dan manosh ya had'u
wlh sedai sam bai fiye yin dariyaba wanda ta lura hakanma dan itace yakeyi se
kuma dasu marwan ko miher. Manosh ya tsargu da irin kallonsa da maryam takeyi
yayi sauri tsayawa da dariyan nashi yace "apple why are looking at me like

that?" Kunya sosai taji dan batama san ya akai taketa kallonshi hakaba,kuma aduk
lokacin take kallonshi sha'awarta tane kawai yake kamashi. Maryam tace ina son
ganinka aduk lokacin da kake dariya dan kanamin kyau sosai manosh,jiyayi kamar
ya rungumeta dan yadda yake ji,amma seya daure yayi d'an murmushi tare da
d'aukan wayarsa ya kira marwan yace ganinan zuwa mutafi sannan ya katse wayar
maryam tana kallonshi,shi kuwa bai sake kallontaba hannayenshi suna kan siterin
mota yace apple am goying,mamaki taji amma setace tonagode Allah ya kiyaye hanya
yare da bud'e kofar mota ta fita se nanne shima ya fito tare da d'aukan abubuwan
da mum ta bata yake mata har zauren gidansu ya ajiye.
Tace nagode tana murmushi,kallonta yayi batare dayayi murmushi yace *minfu
miyatti* sannan ya wuce motarshi ya shiga yaja yana mata bye,ita kuwa murmushi
kawai take mishi daga k'arshe ta d'aga masa hannu sannan ta wuce gida.

Maman maryam tayi farin ciki sosai dajin yadda aka k'arb'i maryam hannu
bibbiyu,ga kuma zannuwa da less masu tsada ga sarka da turare da mum din manosh
ta bata.
Maryam ta koma d'aki tana kwance se kuma ta tashi ta bid'e kit nata ta d'auko
memori tasa a wayarta ta sake tabbatar da cewa lallai wannan shine mahaifin
manosh,hawayene suka fara zuba a idanunta se taji wayanta na k'ara,koda ta duba
*peach &cream* ne seta d'auka tare da share hawayenta tace hello,manosh yace
apple mun tafi,tace to Allah kare nagode,yace ameen *i luv u* murmushi tayi tare
da cewa *she luvs u 2* dad'i yaji yace thankyou apple,tace always *peach* wayyo
Allah manosh kamar zaiyi hauka yana mirmushi ya katse wayar yatana lumshe
ido,marwan yace bari in karb'eka dan naga kamar ka gaji,dariya sukayi dukkansu
sannan manosh ya fizgi motar kamar zasu fire sama,marwan yace a'a mudaije a
hankali kaga dukkanmu tuzuraire hhhhhh

Maryam kuwa wasu zazzafan hawayene suke zub'o mata tinda ta ajiye wayar. Tace
inason sosai manosh,yanzu ya zanyi kenan? Wayarta ta d'auka ta kira uncle
ibrahim bayan sun gaisa tace dam inaso miyi magane in baka cikin mutane,yace ok
bari na kiraki.
Bayan ya katsene ya sake kiranta yace yes aunty ina jinki,tace ka tuna da wannan
vedion dana tura maka a wayarka,yace ai devio d'aya kika tab'a turamin na wanda
ya buge mahaifina ko? Hawaye ya sake zubowa a fiskarta tace eh shi,yace eh har
yanzu yana wayana ai,tace bakowa bane wannan mutumin illa mahaifin manosh yah
ibrahim. What! Mahaifin manosh kikace,tace eh shine na tabbatar da hakanne yau
danaje gaida mahaifiyarshi yah ibrahim bazan iya b'oye makaba dannima mahaifinka
mahaifinane sannan mun dad'e muna nemanshi se gashi kuma ashe shine mahaifin
manosh,kukane yaci karfin maryam take ta katse wayar. Hankalin ibrahim ya tashi
sosai ya rasa meyake mishi dad'i musamman dayaji maryam tana kuka,don ya dad'e
dasa son maryam a ranshi tun mahaifinshi yana raye ya sanar dashi,amma se
mahaifinshi yace karka damu ibrahim ka gama karatunka tukunnan maryam 'yace
aguna nima zafin samun kwarin gwuiwa idan ka gama karatu ka samu aiki se inyiwa
mahaifinta magana tunda amininane. Hakan yasa ibrahim ya hakura yabar abin a
ranshi amma kash *muna namu Allah yana nashi* hankalin ibrahim atashe ya wuce
gidansu maryam.....
[7:10am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: 🍭🎈AUNTY'N YARA🍧🎁AUNTY'N YARA🍧🎁

Written by sad-nas
&
Hama gee muh'd

Dedicated 2 *ANEELURV*🌹

27-28 Uncle ibrahim yana isa yayi sallama,maryam ta fito tare da amsa
sallamar,tunda ganin fiskarta ya tabbatar tayi kuka. Kallonta yakeyi mai cike da
kauna,yace ina mama,miryarta k'asa ba tare data kalleshiba tace tana d'aki.
Ibrahim yace aunty meyasaki kuka,shuru tati ta kasa cewa komai,ya sake cewa
aunty pls banaso in sake ganin hawaye a fiskarki wlh na yafewa mahaifin camtain
amma saboda kece kawai wlh dabadan keba danayi k'aransa,aunty kin wuce duk yadda
kike tunani aguna sannan babanki ya rik'emu kamar uba tun bayan rasuwan
mahifinmu dan haka ki wantar da hankalinki kinji wlh komai ya wuce zan samu baba
anjuma muyi maganan.
"Maryam ta d'ago da kanta tana kallonshi tace nagode sosai yah ibrahim,basan
dame zan biyakaba a duniyannan Allah yabar zumunci. Murmushi yayi mata tare da
cewa ameen aunty pls kicire komai a ranki karki nunawa captain wani canji sannan
karki sanar dashi kinji,to tace dashi yace to ai seki murmushi dan fishi bai
kamacekiba,dariya takeyi wanda yake kara mishi kaunarta a ranshi nan sauyin
kallon da yake mata ya canja,wanda ita ita da kanta ta lura da hakan,take
jikinta yayi sanyi,shi kuwa juyawa yayi ya tafi batare daya sake cewa komaiba.

Tunani sosai maryam ta shiga akan yanayin yah ibrahim tace kodai sona yakeyi to?
Kai a'a da sona yakeyi aida ya dad'e da fad'a kawai dan kila dan kokarinane yasa
yake sona haka amma kuma meyasa yakemin wannan kallon da manosh yake min sannan
ya tafi babu sallama?
Wayanta ta d'auka ta kirashi bugu d'aua ya kayse ya kirata ta d'auka da sanyin
murya tace yah ibrahim katafi babu ko sallama? Yace am sorry aunty bazan iya
tsayawa inaci gaba da kallonki bane,tace todai ai semuyi sallama koh kamar dai
yadda muka saba. Murmushi yayi yace tokiyi hakuri aunty nayi laifi,murmushin ta
mayar mashi tace ba komai ya wuce dama shiyasa na sake kiranka. Yace tona gode
aunty ina so in miki wata tambaya pls ki gayamin karkiji kunyana,tace to inaji,
"you love camtain right?" Shuru tayi dan bata tab'a tunanin jin wannan tambayan
daga garesaba,yace aunty kinyi shuru,tace yah ibrahim yana da wani haline mara
kyau kodai kasan wani abu mara kyaune game dashi? Yace "aunty" namiki tambaya
kimin tambaya,cikin sanyin murya tace yah ibrahim bazan iya b'oye maka komai a
duniyannan ba "yes ina sonshi" amma wlh idan yana da wani aibu kagayamun ko kuma
baba,tunda dama ai nace kayi bin ike akanshi. Ibrahim yace hakane aunty wlh bayi
da wani aibu ko hali mara kyau kawai dai na tambayekine,tace tomeyasa kamin
tambayan? Yace yanzu nayi laifi kenan,yace bakayiba nima ina so ka gayamin me
dadilin tambayan? Yace idan muka sake had'uwa zan gayamiki yayinda nake kallon
fiskarki kinji,tace toshikenan nagode,yace ok bye sannan ya katse.

Maryam dai da tunanin maganansu ta kwana a rai kuma daahi ta tashi.
Rashida ce taje gun maryam,lokacin tana zaune a gaban *computer* tana sanye da
blue jeans da kuma jan top mai dogon hannu ta nad'e kanta da *light brown* gyale
k'arami,rashida tace kai amma kinyi kyau a kayannan bari in miki *picture* ai
kuwa maryam tayi dariya fararen hakwaranta suka bayyana rash ta dauka tare da
cewa gaskya ki turawa captain wannan pic din dan yayi kyau sosai wlh. Murmushi
maryam tayi tare da kab'ar wayan rash tana ganin pic din, nan suka koma kan
k'aramin gadonta tana shirya books nata rashida se d'aukata takeyi,maryam tace
ke ya isama mana.

Dariya rash tayi sannan suka fara hira nanne maryam take gaya mata cewa mahaifin
manosh ne ya buge mahaifinta kumata gayawa yah ibrahim,hankalin rashida ya tashi
sosai ta mik'e tsaye tace mahaifin manosh fa kikace,maryam tace eh wlh wlh shine
kinsan jiya naje gaida mum nashi acan naganshi. Rashida tace wlh bazai yuba,ya
rabani da mahaifina shikenan aahe manosh bai sami mahaifi nagari wlh tunda har
zai iya yin kissa sannan kuma ya gudu mugu mara imani wlh Allah ya isa mana.
Maryam tace dan kiyi hakuri rash kidena fad'a haka,rash tace ai wlh ba mutumin
kirki bane tunda haka yake Allah yasa camtain karya d'auko halinsa dan wlh indai
halinsu d'aya to ina tausaya miki maryam. Maryam tanata bata hakuri amma ina
rash se kuka takeyi harta fara cewa to yanzu kinsan hakan tome kuke ciki da
captaim maryam? Maryam tace kamar ya rash? Rash tace har yanzu kina son captain,
maryam tace rash wani irin magane haka kuma pls kiyi hakuri ki nitsu pls,rash
tace in nutsu,hakan ya nuna har yanzu kina tare da captain kenan maryam
mahaifina fa mahaifinkine,kuma har zaki iya ci gaba da soyayya da d'ansa,lallai
nagode danke mahaifin na raye shiyasa keto marwan d'inma daga yau bani bashi
tunda shi abokin manosh ne koma ince amininsa dan haka kema daga yau *bani bake
maryam* tana kaiwa nan ta ta fice tanata kuka sosai.
Mamakine sosai ya kama maryam dajin kalaman rash,dan tunda suka taso ko musu bai
tab'a shiga tsakaninsuba kowa ya sansu kuma yasan shak'uwarsu sannan maryam tana
son rash sosai fiye da sauran k'awayenta dan haka se abin ya dameta sosai, dama
mamanta ta tafi angiwa dan haka ta rufe gida tabi bayan rash.
Kuka sosai rash takeyi itama mamanta bata gida dan yare suka fita da maman rash
d'in sunje barkan haihuwa. Maryam tace haba rash yau har zaki iya furta cewa
*bake bani* akan manosh,rash nasan ina son manosh amma wlh soyayyar da nake miki
yafi wanda nakeyiwa manosh,domin shi zan iya rabuwa dashi amma ke na d'aukeki
tamkar k'anwatace da muke ciki d'aya meyasa zakice haka dan Allah? idan rash
jajur dan kuka tace wlh karyane maryam dakam nasan kina sona amma banda yanzu
dan haka ki fita kibar mana gidanmu ki fita bana bukatan in sake ganinki dake da
kowa nakima ki fita anan da k'arfi ta hank'e maryam har waje se jinta tayi ta
mannu da mutum ta bayanta. Da sauri ta goge hawayen idonta tare da juyowa se
sukayi ido hud'u da yah ibrahim take hawaye yaci gaba da gangarowa a fiskanta ta
juya tana kallon rashida da tsoro ya gama kamata dan ganin yah ibrahim datayi.
Wucewa maryam zatayi da kukanta se yah ibrahim yayi saurin rik'o hannunta yace
auntyn kiyi hakuri meya had'aku? Karon farko kenan danamiji ya rike hannu maryam
bata iya cewa komaiba se kokarin fisgan hannunta takeyi agun yah ibrahim tace
dan Allah ka sakeni yah ibrahim zan tafi gida,yace no aunty dan Allah ki tsaya
yana rike da hannunta ya juya rai a b'ace yana kallon k'anwarshi rash yace ke
meya faru,jiki na rawa ta gaya mishi,ya e shine yau da hannunki harkin iya
hankad'e maryam rash? Ina ruwanki azan,yana rik'e da hannun maryam harya isa gun
rash *belt* d'in jikinshi ya zaro rash ta fara kuka tare da cewa dan Allah yah
ibrahim kayi hakuri wlh bazan sakeba.

Rash ta tsorata sosai dan tasan halinshi sarai, kukda dai bai tab'a dukantaba
tunda take. Maryam tayi saurin shiga tsakaninsu tana hawaye tace dan Allah ya
ibrahim karka dake pls,tsawa ibrahim ya dakawa maryam wanda dukkansu seda suka
tsorata yace aunty ki matsa! Rash ta rike maryam sosai tana bashi hakuri. Maryam
tace kayi hakuri yah ibrahim amma sedai ka dakemu dukkanmu tana kuka sosai.
Jikinshi yayi sanyi dan yadda yaga maryam take kuka haka ya sake *belt* din a
k'asa rash kuwa da gudu ta fita ta wuce d'akin mamanta ta kulle da key. Maryam
ma tazo zata wuce amma seya tareta,kuka takeyi tace yah ibrahim zan tafi
gida,yace *aunty am sorry pls akan abinda rash tamiki*,maryam batace komaiba
tace pls kaban hanya in wuce,yace sekin share hawayenki,bai jira me zataceba
yasa hannunsa yana share mata,tayi saurin kawar da kanta gefe tare da buge
hannunsa daga kan fiskanta,amma ina seya sake mayarwa tare da rik'e hannunta
yace pls aunty ki dena kuka wlh har cikin raina nake jin kukanki sabo da yadda
nake *k'aunarki tunda dad'ewa*. Da sauri maryam ta d'ago da kanta suna kallon
junansu sosai har cikin ido,hakan ya sake rikitar da ibrahim sosai aise ya

tsinci kanshi da fara matso da fiskarshi dedai nata da niyan kissing nata.
Idanunta ta zaro tare da bigeshi gefe tayi saurin barin d'akin da gudu ta wuce
gida,shi kuwa wani ajiyar zuciya ya sauke huuuuuh! tare da nadaman abinda yake
son aikatawa...
[7:10am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: 🍭🎈AUNTY'N YARA🍧🎁AUNTY'N YARA🍧🎁

Written by sad-nas
&
Hama gee muh'd

Dedicated 2 *billy tabacco*🌹

29-30 Maryam tana komawa gida ta wuce d'akinta dama mamanta bata dawoba,ta
kwanta tana kuka sakamakon tunawa da kalmomin rash agare. Dan bata tab'a zaton
cewa wani abu zai shiga tsakaninsuba.
Wayartace ta fara ringing kodata duba se taga manosh ne,haka

Please Login or Register in order to submit comment