Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

satin samira da amina suka haihu,manosh yana gari akayi
suna. Hmmm abundai ba sauk'i.
Bayan dawowan manosh ne yapendo ta koma amma nafisa tana nan daga gidan take
zuwa makaranta,dan manosh ya rok'a abar nafisa tad'an zauna kafin twins suyi
kwari. Ita dai nafisa bata soba,dan haka maryam taketa mata dariya tana
tsokanarta, nafisa tace seki barni da yara kije kuyi soyewa da mijinkiko wlh na
kusa tafiya. Hhhhhhhh maryam tayi dariya tace tome aikinki babu inda zakije se
lokacin aurenki yayi kuma wlh ki tabbata kina kula mana da yaranmu idanma
biyanki kikeso muyi to zamuyi amma kar in sake ji kina kirana idan peach nah

yana gida saboda kina takura mana wlh. Harara nafisa takewa maryam tare da
d'aukan teadyn alfiyya ta jefi maryam dashi, da sauri ta fita da gudu inda
sukaci karo da manosh yayi saurin rungumeta tace peach kaga nafisa ko,d'aukanta
yayi cak se d'aki yace muje karma ki sake komawa sedai in twins suna buk'atan
nono. Kiss ta manna mishi tare da cewa yawwa angon maryam shiyasa nake k'ara
sonka,daga nan kuma suka wuce duniyartasu.

Ayau ake auren yah ibrahim da lubna,programs sosai lubna tayi su maryam sune
k'awaye su manosh kuwa abokai kuma yayyu.
Zanso kuga bikin abin sha'awa da birgewa babu wasu k'awaye iya zallah sune
kawai,sedai shi yah ibrahim yanada friends sosai. Mahaifin lubna shiya gina musu
gida mai kyau acikin jimeta,inda akayi harda d'akin mamansa daga gefe.
Dukda dai yah ibrahim yasan halinda lubna take ciki,amma dukda haka a had'e
yajita sosai saboda gyara datasha sosai,kuma da taimakon Allah tunda fyad'e ne
bawai dasonta bane, zaman lfya sosai sukeyi hankali kwance,zumunci mai k'arfi
yashiga tsakaninsu kamar 'yan'uwa.

*****
3years
Lokaci babu wuya yanzu su abdallah sunada shekara uku,ga wayo shiyasama akasa a
skul dukkansu.
Yau sartuday sukaje girei gun kakarsu zasu kwana d'aya sunbar manosh shi kad'ai
agida.
Alfiyya ita dai se shigan turawa kawai take so adinga mata,shi kuwa manosh cewa
yayi abarta tunda k'aramace idan ta fara girma se'a dena sayowa,maryam batasoba
amma haka ta hakura. Farin rigane a jikin alfiyya tare da wani dogon takalmi se
kuma hula inda gashinta ya rufe mata fiska dan tsawo,dan tafi maryam gashi
gashin manosh suka d'auko,sunaji da yaran sosai akama mutane suna son yaran
musamman alfiyya. Haka ta ishe maryam waisam tayi mata hoto dan idan baban
maryam angonta ya dawo zata nuna mishi,dariya maryam da mmnta sukayi sannan ta
d'auketa........
[7:14am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: 🍭🎈AUNTY'N YARA🍧🎁AUNTY'N YARA🍧🎁

Written by sad-nas

NOTE
*sorry fans,kunjini shuru ne saboda rashin lfy danayi 2days,sannan cikin
satinnan muna da bikine dan haka kuyi hakuri da rashin post nawa da zakudinga
gani*
*masoyana kuwa ku sani cewa kuna raina akoda yaushe,najin dad'in ganin
sak'onninku na nuna kulawarku agareni,kuyiwa amaren da za'a aurar daga gidan
addu'an Allah ya basu zaman lfy,Allah kuma ya dauwamar dasu a d'akin mazajensu
ameen*

*yan matan da zawarawan da basuyi aureba kuma to Allah ya
nagari ameeen sad-nas luvs u so verry much*❤)*❤)* ❤💐

zab'a muku mazaje

65-66 Ayau akayi hutun first term,inda manosh ya kashi su alfiyaya kaisu gun mum
sunyi 2weeks,daga can kuma sesu wuce gun maman maryam a girei.
Gida daga maryam se manosh,tana zaune a d'akin alfiya tanata k'arewa d'akin
kallo duk kewarsu ya kamata gashi manosh bai dawo da ruwaba yau har 9:30pm
sannan taji shigowar motarshi, da sauri ta fito tana sanye da gajeren wandon
manosh da kuma wani shets nashi fari dama ya kasa mishi dan haka tasa ya mata
kyau sosai ta tsaya ajikin k'ofan shigowa daga gefe,yana shogowa da sallama tace
kamashi nan! Tsorata sosai yayi ita kuwa kayayyakin hannunsa ta karb'a ta wuce
da gudu tana mishi dariya tare da cewa soja dajin tsoro,gaskya kaba dani wlh
peach tanata dariya tare dayi mishi gwalo ta wuce sama.
Ahankali ya k'arasa saman yana mana kallon,zaki gane kuranki. Bayan ta ajiye
komaine,tazo da gudu ta haye bayanshi tana cewa
_aga aga_ _aga tsoja dajin tsoro aganshi hhhhh_
Ai kuwa daya cirota yayi daga bayanshi bai ajiyeta ko inba se d'akinshi yana
cewa nine matsoracinko,tace sosaima kuwa ka cika babban matsoraci,ta fad'a tare
da mishi galo,shi kuwa kallonta kawai yakeyi yace wayace miki kisa min
kayana,tace ai yanzu kam sun zama nawa tunda sun kasa maka,bakaga yadda suka min
kyau fiyema dakaiba. Shi kanshi yasan sunyi mata kyau sosai amma seyace sam basu
miki kyauba kuma ki cire min kaya dan bance na bakiba,ta marairaice tace haba
bby nah,yace waye bby'n?ta nunashi da yatsan hannunta batare datayi
maganaba,manosh yayi murmushi yace wlh na wuce bby tunda har na samo abdallahda
alfiya,hhhhhh maryam tayi dariya tace to babban mutum naji,amfa ka sani bakai
kad'ai ka samosubayace ni kad'aine mana saboda lokacin dana samosu ai bakya
cikin hayyacinki kuka kawai kike kinsan me kike cewa? Ta girgiza kai sunayiwa
juna murmushi,yace cewa kike _pls peach kayi hakuri wlh dazafifa,baka
tausayinane kanaji ina maka magana,dan Allah ka tausayamin peach kasanfa ni
k'aramace_
Dariya sosai maryam takeyi shi kuwa yana kallonta yace wlh kuwa haka kika dinga
cewa,ita kuwa maryam yanayin yadda yayi maganane waishi adole yana kwaikwayon
muryanta shiyabata dariya.
Janyota yayi tare da cire mata kayan jikinta itama ta tub'e masa nashi suka wuce
toilet sunata cud'ar junansu sannan suka fito tana manne a jikinsa.
Bayan sunyi shirin baccine se suka wuce daining sukaci abinci yasha fruit yana
cewa wlh nayi missing d'in honeys d'ina sosai fa,maryam tayi murmushi tace to ai
hakuri zamuyi kamar gobene sekaga har hutun ya k'are. Yace ina kullum zanje
inyita ganinsu mana hira,tace nifa,yace zan kiraki a waya se'in had'aku.
Haka dai sukaita hira har suka kammala sannan suka wuce d'aki,kwanciya yayi akan
gadon sannan ya janyota tare da kashe wutar.

Wato idan manosh da maryam suna luv seka d'auka yau ne farkon amarcinsu saboda
wata ni'ima na musamman da Allah yayiwa maryam,sam ita bata shan wani maganin
mata koma wani irine daya wuce fruit,shima bawai dan yayi mata maganiba sedan
kawai ita tana son fruit,kuma se Allah ya had'ata da wanda yafita son fruits.

Akullum satin manosh akanta dabanne,bayan sun samu gamsuwa sosaine yake ce mata
gaskya aunty Allah yayi miki wata baiwa ko kuma ince halitta wanda bakowace mace
bace take dashiba,yace wlh apple aduk lokacin dana kusanceki banda irin ni'imar
dani kad'ai nasan dad'inki to wlh koda yaushe senaji wani farinciki mara
misaltuwa a tare dani,sannan zazzafar k'aunarkice take shiga jikina tun daga
tafin kafata har tsakiyar kaina pls apple gayamin sirrin.
Dad'i sosai taji wanda bazata iya b'oyewaba tace wlh bakomai sedai ince
Alhadulillah kuma zanci gaba dayiwa Allah gofiya yasa in d'aure haka har
abada,dan banida wata buri irin inga koda yaushe kana samu gamsuwa dani 1000%
peach,yace kin wuce 1000% apple aguna babu wata adadin dazan iya dangantaki
dashi sedai incigaba dayiwa Allah godiya daya bani wannan kyautar apple d'in
nawa 'yar baiwa. Sanyi taji har cikin ranta tare da sake shigewa jikinsa tana
juyi irinna sake taso da shawa'a, ai kuwa sannu a hankali manosh ya rikid'e
yashiga sarrafa yar bbynsa son ranshi gata 'yar k'arama mara nauyi,dama kuma
kunsan ance siraran mata daban suke😘.
Idan manosh yana tare da maryam tofa nuna mata yake shekarunsu dai-daine,shiya
ita kanta maryam take gamsuwan da koda yaushe tana buk'atan su kasance a tare.
Kai soyayya tayi a rayuwa.

Washe gari maryam ta hana manosh fita kwata-kwata,babu yadda baiyi da itaba
danya rarrasheta ta hak'ura amma sam taqi wai ita dai dole seya zauna suyini
suna luv ko Allah zai karb'i addu'ansu ta sake samun wani ciki.
Haka ya zauna da apple a gida tare da sanar da kowa cewa bayajin dad'ine,ai kuwa
gaisu aketa zuwa gida,wannan na fita wannan zai shigo,manosh dai dariya kawai
yakeyiwa maryam. Tace to wlh babu wanda zai sake ganinka duk kace musu kayi
bacci batajira mezaiceba ta shagwab'e tare da fara kai hannunta cikin
wandonshi,ai tuni suka haura sama anata abu d'aya,seda suka gaji sosai dukkansu
sannan suka kwanta bacci har azahar.
Byan sun idar da sallah ne sukaci abinci sannan suka koma bacci suna farkawa
ya janyota jikinshi akadai suketa abu d'aya,sannan sukayi wanka da sallan
la'asar se tace zauna in baka lbr,ba musu ya zauna tana kwanshe a jikinsa tana
mishi hiran zamanin annabawa,kawai setaji yana cewa apple tashi kinji,tace
meyasa,yace pls apple,da sauri ta tashi aisetaga idonshi sunyi jah sosai,tace
lfy peach meya shiga maka idon haka mugani,bakinta takai zata hura mishi
idon,setaji yace aisekiyi kuwa nidai yanzu muna miki bankwana.........
Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un3× maryam taketa maimaitawa tare da tab'a
inna manosh yake kwance amma sam bata ganin komai agun se pillow, addu'a maryam
ta farayi tana kuka amma sam har yanzu bata ganin manosh a d'akin daga ita se
gado da pillow.
Kukata farayi tana cewa peach,ina kake pls peach kadena me kuma haka,waje ta
fito ta nufi d'akinta amma bayanan,ta duba ko'ina dai acikin gidan kozata
ganshi,dukda dai ita tasan suna tare dashi a d'akinshi batare daya sauka daga
gadonba tanemeshi ta rasa.
Ai take maryam ta rikice tare da tsorata ta d'auki wayanta ta kira yah ibrahim
tace hello yah ibrahim akwai matsala babba wannan karon na nemi manosh sama da
k'asa na rasashi kuma yanzu muna tare dashi anan wlh b'acewa yayi.. yah ibrahim
kansa ya d'aure sosai yace aunty b'acewa kuma kamar yaya,tace wlh duk yadda
akayi SHUKRAH CE itace ta d'aukemin mijina yah ibrahim wlh itace..ai se yanzu
ibrahim ya gano abinda maryam take nufi,yace kiyi hakuri aunty ganinan zuwa
sannan ya katse wayan ya kira mahaifin maryam ya gaya mishi abinda maryam ta
gaya mishi,dukdai wanda yaji se kanshi ya d'aure,dukda dai su yah ibrahim kam
sunsan komai,amma kuma mamakinsu shine yaza'ayi shukrah ta d'auke manosh lokaci
d'aya kuma ace b'acewa,ibrahim yace lallai akwai aiki sosai tausayin aunty kawai
yafarayi tunma baigantaba a halin yanzu,tana zaune a inda suke itada manosh tana
cewa peach dan Allah ka fito ganinan ina jiranka pls peach.

Wayanta ta d'auka ta kiran mum d'in manosh tana kuka ta gaya mata komai,rikicewa
mum tayi tare da fad'in alhaji karma ka fita akwai matsala,yanzu maryam ta
kirani wai manosh ya b'ace yanzu a d'aki batare daya tashi yaje wani guba
b'acewa kawai yayi yau ni maryam wannan wani irin abune kuma.

Cikin 1hr gidan manosh ya cika da iyaye da kuma abokai. Kuka kawai maryam taketa
rusawa,tun daga gate ake fara tambayan mai gadi koyaga fitar manosh,yace ai oga
yana cikin gida yau sam bai fito ko tsak'ar gidaba.
Haka suka karasa ciki,maryam taje ta rungume mamanta tana cewa mama manosh wlh
banganshi. Su marwan da ibrahim da kansu suka wuce ko ina agidan suka duba amma
sam babu manosh,gashi maryam ta tabbatar musu da cewa tana zaune ajikin kalmarsa
na karshe yanata cewa apple tashi,ganin jan da idonshi yayine tace barita hura
masa dan ita atunaninta abune ya shiga mishi ido,takai baki kenan setaji yace
aise kiyi.
Tunda lbr ya sami dad d'in manosh ya samo malamin sunna ya gaya mishi komai tun
daga farko har karshe,yah ibrahim yace ina wayanshi aunty,tace duk a d'aki yake
amma babu yanzu,majid yayi saurin kiran wayan ai kuwa se waya ta fara ringing,a
hands free yasa ta yadda kowa zaiji.
Muryan mace tanata dariyan mugunta wanda kowa hankalinsa ya koma gun wayan,majid
yace hello abokina,tace hhhh abokinka kuma,wannan matar abokinkace ai. Ibrahim
ya karb'e yace wace matar kenan,dariya tayi sosai tare da cewa ohh yah ibrahim
barkanmu da sake ganawa ka manta abinda na gaya maka,nace zan dawo kuma gashi na
dawo ai auntyn ta gama more rayuwarta dashi kuma na hakura na barsu,dan haka
nima yabzu lokacina kabawa aunty hakuri sannan karku b'atawa kanku lokaci dan
wlh manosh bazai dawoba domin shi nawane yanzu! Ta k'arasa maganar cikin tsawa.
Ibrahim yace amma shukra ke acikin aljanunma kafira ce wawiya,kiyi
gaggawan dawo da manosh idan ba hakaba mukuma zamu klarb'o manosh da ikon Allah.
Dariyan nugunta tayi tace wlh kana burgeni sosai yah ibrahim da karfin halinka
da kuma jarumtarka,lokacin dana d'auke manosh wlh kai kawai na fara tunowa,da
ace kai zuciyata takeso ta tuni na d'aukeka. Yace karya kikeyi wlh yanzu ina
kika kai manosh,tace yananan kacewa maryam garama ta kwantar da hankalinta dan
duk k'aunarshi da takeyi tofa a bayan nawa yake,sannan ta dena wannan kukan
kasan dama lfy bata ishetaba,kukaita manyan hospital zasu saboda akwai babban
ciwo da yake amunta,karkuyi wasa har ciwon yayi nisa *k'odarta guda d'aya yana
da matsala* idan baka yaddaba kuma kuje ayi mata gwaji,ba kuma nina samata
ba,nadai gaya mukune dan ku d'auki mataki da wuri sannan ku sama mata wani mijin
tayi aure dan wlh manosh bazai dawoba,daga k'arshe ina baku hakuri iyayen manosh
kaunarsa nakeyi sosai shiyasa na muku haka kuma babau abinda zai sameshi,yah
ibrahim seka sake jina dan kai kad'ai kawai zanyi magana dashi ma'assalam!
Koda aka sake kiran wayan se akajita a rufe,duk wanda ke parlour jikinshi a mace
anma rasa me za'ayi akai. Malam yace ku kwantar da hankalinku tabbas zata dawo
dashi da yardan Allah muyita addu'a zansan yadda zamuyi,domin hakan na faruwa
sosai ta wasu k'asashen,maganar k'arshe itace lallai aje ayiwa maryam gwaji
domin zai iya yuwa maganar shukran gaskyane, dama bata da lfya ne? Mahaifin
maryam yace eh tun bayan haihuwanta take fama kuma ance mana dai babu komai,dad
d'in marwan yace to ai se'a shirya zuwa kano muji,baban maryam yace badamuwa
zamu je,dan wani lokacin aljanu suna iya fad'in daidai,sannan karku damu insha
Allah muh'd zai dawo domin na tab'a had'uwa da wasu wanda abin ya faru irin
haka,kuma matar tadawo sedai ta d'auki kusan watan shidda kafin suka dawo da ita
da kuma lfy lau.
Haka dai baban maryam da wan malamin da dad d'in manosh ya kira sukaita
kwantarwa mutane da hankali hardai suka samu sukuni a ransu,sannan akace maryam
ta shirya su tafi gida da iyayenta,zuwa gobe za'a musu komai suwuce kano,yah
ibrahim yace nima zanje,haka aka watse kowa dai jiki sanyaye, maryam kuwa
batasanma me take cikiba sam tak'i yarda tace babu inda zataje manosh zaidawo

d'aki bazai sametaba,tausayinta ya kamasu mum d'in manosh ta rungumeta tanata
rarrashinta itama kukan takeyi har suka k'arasa gun mota dakyar ta shiga motan
mamanta tana cewa kiyi hakuri maryam jarabawace kuma insha Allah zakici wannan
wannan jarabawan ki daure kiyita addu'a. Dama yah ibrahim ne yaje ya d'aukosu
baban maryam,dan haka shiya d'aukesu ya mayar dasu mama da maryam sun zaune a
baya, hmmmm akwai aiki........
[7:14am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: 🍭🎈AUNTY'N YARA🍧🎁AUNTY'N YARA🍧🎁

Written by sad-nas

*dedicated to sad-nas fans*❤)*❤)*❤)*

69-70 Hajiya khadija tana tsaye a palo se faman rusa kuka takeyi tana kiran
lubna,amma ina lubna ta d'auki bag da gyalenta ta fito da sauri tana hawaye ta
nufi gun mota,inda hajiya khadija taketa faman kiranta amma ina aguje ta figi
mota se girei.
Hajiya khajida ta kira hajiya iya ta gaya mata komai,hankalin hajiya iya ya
tashi sosai dama kuma ranan batajin dad'in jikinta sam. Sallamar maryam ce yasa
hajiya iya tayi saurin katse wayan tace maryam yanzu seda kikazo dubani dukda
irin halin da kike ciki? Maryam tayi murmushin k'arfin hali tace haba hajiya ai
rashin lfy ya wuce komai ya jikin naki? Tace da sauk'i yasu hajiyan,maryam tace
lfy lau sannan ta marairaice murya tace hajiya kusan *sati uku* fa kenan babu
lbrn manosh d'ina gaskya banajin zan iya ci gaba da rayuwa indai har na rasashi
har abada,tacigaba da cewa hajiya ina son manosh fiye da tunaninku ko a wani
hali yake ciki se Allah😰
Hajiya tayita rarrashinta da kalamai masu sanyaya zuciya dukda dai ita maryam ji
take kamar ana sake sata kukane hakan yasa ta mik'e ta wuce cikin d'akin hajiya
ta shige toilet domin wanke fiskanta,ita kuwa hajiya sebinta da kallo takeyi
cike da tausayawa da kuma laifin datayiwa maryam da iyayenta wanda a yanzu
taketa d'an dana sani da kuma tunanin abinda zai biyo baya yanzu da hajiya
khadija tace luvna tasan komai gashi ta fita tana kuka ba'asan ina ta nufaba.
Kamar daga sama hajiya iya taga lubna ta shigo rai a b'ace ko sallama babu
ta fara zagin hajiya iya zagi marasa dad'in ji. Hakan yasan maryam ta fito da
sauri har tana tuntub'e,tsakanin lubna da hajiya iya ta shiga tana cewa lfyanki
kuwa lubna,wani irin rashin hankaline wannan me kuma ya kawoki nan dahar zakizo
kina mata irin wannan rashin mutunci? Lubna batama san waya shiga tsakaninsu da
hajiya iyaba saboda yadda ranta ya b'aci cewa take kinji kunya wlh tsufanki bai
amfaneki da komaiba se tsuta dacin amana wlh kunya nakeji wai ace ke
kakatace...lubna bata kai ayaba taji wawan mari da maryam ta sake mata a fiska
tace baki da hankaline wai lubna kin santane? Kuma meta miki haka dazaki mata
wannan cin fiska sekace wanda bata da tarbiya?
Se a wannan lokacin lubna ta lura da cewa ashe hasanantace maryam jininta,hawaye
masu zafi suke kwaranyowa daga fiskanta cikin sanyi murya tace maryam lfy lau
kuma nasan me nakeyi hajiya iya ta cuceni ta cuci rayuwata kuma wlh har abada
bazan tab'a yafe mataba tir da mai hali irin naki wlh kinji kunya kuma ki sani
randa kowa zaiji wannan abun rananne kowa zai d'aukeki a matsayin tsohuwar banza
kokuma ince tsoffin banza wlh kunji kunya kun cuci mahaifina sannan kin cuci
d'an cikinki tunda shima baisan komai akaiba muguwar tsohuwa... mari maryam ta
sake bata tace lubna ki fita kibar gidannan dan bazaiyu in barki kiyita hauka ba
da alamun tab'in hankali a tattare dake,waya ta d'auka ta kira yah ibrahim take
gaya mishi irin cin fiskan da lubna takeyiwa hajiya wanda har a wannan lokacin

zagin takeyi shi kansa yah ibrahim yana jiyo muryarta da munanan kalaman da take
gayawa hajiya iya. Ita kuwa hajiya iya kuka sosai takeyi tare da kasa had'a ido
da dukkanninsu saboda tasan bata da gaskya,ita kuwa maryam rungume hajiya iya
tayi tana rarrashinta tare da cewa lubna kibar gidannan baki san cewa bata da
lfy bane? Lubna tace ai dole tayi rashin lfy,sakayya ne ta fara gani tun a
duniya akan abinda ta aikata natabbata idan kika san abinda wannan tsohuwar
banzan tayi wlh sekin tsaneta har abada,maryam wannan tsohuwar basonki takeyiba
domin ita ta rusa miki farincikinki muguwace ta k'arshe shiyasa take kyautata
miki sosai dan abinda ta aikata miki amma kinji kunya wlh tsohuwar banz....mari
mai kyau marwan ya d'auke lubna dashi wanda har yah ibrahim seda ya tausaya mata
bare kuma maryam da hajiya iya.
Yah ibrahim yace haba marwan irin wannan marin,yayi saurin kamo matarshi ya
rungume ita kuwa lubna dukda tsoron marwan da takeyi amma sam a wannan lokacin
seta nemi tsoron ta rasa bare kuma yanzu da tasan shiba yayanta bane,tace ko
kasheni zakayi wlh bazan dena zagin tsohuwar banzan nanba maciya amana wlh kinji
kunya,sannan kuma karka sake marina dan baka da wani iko akaina ina fatan ka
gane me nake nufi,tunda kakarkace sekaje gareta amma dole maryam zata bar
gidannan,da gudu taje ta janyo maryam daga jikin hajiya kaka tace zomu tafi
*aunty* ki rabu da tsohuwarnan datasan bata da gaskya ai gashi tayi shuru bata
cewa komai se kukan nadama da takeyi wlh kin cucemu kuma nikam bazan tab'a
yafewaba.
Mamakine ya kama marwan sosai shidai yasan lubna tana tsoronshi sannan bata
da rashin kunya amma yadda yaga ta dage tana kuka tana magana hakan yasa
jikinshi yayi sanyi yaje gun kakanshi hajiya iya yanata rarrashinta,maryam da
yah ibrahim ma mamaki abun ya basu,maryam ta fisge hannunta tace koma me hajiya
iya tamiki bata cancanci haka daga garekiba lubna tafa haifi mahaifinki tunta
naji kince kakarkuce,lubna tace kakar bro marwan dai amma banda ni kizo mutafi
*aunty* bazaki gane komaiba a yanzu kuma banaso ki gane komai saboda bayida
amfani a yanzu muje my luv kakyi k'ok'ari asamu a fitar da *aunty* waje ayimata
aiki wannan shine burina na farko na biyu kuma Allah ya bayyana mana
captain,tsantsan farin ciki maryam ta rungume lubna tana hawaye saboda an sosa
mata inda yake mata k'aik'ayi. Wani irin dad'i sosai lubna taji lokacin da suka
rungume juna da jinin jikinta,tana maganan zuci tana cewa ancuceni da aka rabani
dake 'yar'uwata bazan iya gaya miki komai ayanzuba saboda damuwan da kike
ciki,sannan dukka cewa hajiya khadija ba mahaifiyata bace ina sonta sosai har
cikin raina saboda k'auna data nunamin wanda ko d'an cikinta bro marwan
albarka,sun nunamin gata na k'arshe hakan yasa bazan gaya miki komai yanzuba dan
naji tace ko daddy nama baisan da zancenba to amma yaya hakan ya faru kenan ya
za'ace daddy baisan cewa niba 'yarsa bace? Yah ibrahim ne ya katse lubba da
zancen zuci da takeyi idanunta rufe tana kance a kafad'ar maryam.
Afirgice ta d'ago da kanta tana kallon maryam,mamakine ya kama maryam d'in
daduk wanda yake tsaye agun. Lubna ta wayance tace muje na rakaki gida *aunty*
dan kema baki da lfy muje ki kwanta ki huta my luv muje,yah ibrahim yace kaka
dan Allah kiyi hak'uri bari na kaisu gida zan dawo,maryam zatayiwa kaka magana
kenan se lubna ta janyota da k'arfi tace muje nikam dan idan ina gidannan tofa
abin bazai mana kyauba nan gaba,haka maryam ta bita a baya kamar wata wawiya se
cikin motan yah ibrahim.
Yah ibrahim yace meyake damunkine my luv,mum naku ta kirani tana tambayana
kokinzo gida nace mata a'a,munyita kiran numbernki bakya d'auka kuma mum tace
mana rai a b'ace kika bar gida kina kuka shine tasa marwan yaje ko ina ya nemo
mata ke hankalinta ya tashi sosai wlh waime yake faruwane my luv,kuma menene
hajiya iya tayi miki haka? lubna dake zaune a baya itada maryam seta rushe da
kuka tace wlh an cuceni my luv kuma bazan tab'a yafewaba,gara cutan da saddam
yamin so dubu akan wannan cutan da akamin wlh, kuka sosai takeyi kamar ranta zai
fita wanda yasa hankalin yah ibrahim da maryam tashi sosai tare da mamakin jin
kalaman lubna. Maryam ta janyota jikinta tanata rarrashi har suka iso gidansu
maryam,dukkansu suka wuce cikin gidan inda yah ibrahim ya wuce palon baba su
kuwa suka wuce d'akin maryam,wani sanyi da ni'ima lubna ta tsinci kanta a
ciki,maryam tace barina dubo mama ina zuwa,lubna tace to.

Fitan maryam kenan wayanta ya fara ringing,lubna tana dubawa taga *PEACH &
CREAM* ai da gudu ta fito ta nufi d'akin mamansu tana cewa hello,ai kawai setaji
muryan manosh yace apple, da gudu da murna take kiran aunty ga bro manosh...,
[7:14am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: 🍭🎈AUNTY'N YARA🍧🎁AUNTY'N YARA🍧🎁

Written by sad-nas

*dedicated to sweet sis maryam tahir (hajja)*🎁🌺

67-68 koda suka isa gida maryam kuka kawai takeyi,su abdallah kuwa suna gidansu
mum dan ba'ama zo dasuba.
Iyayen maryam sun tausaya mata sosai,musamman yah ibrahim,ahankali aka fara
shirye shiryen tfyansu kano domin aduba lfyar maryam kamar yadda shukrah tagaya
musu,mama da yah ibrahim da kuma muh'd ne suka tafi kano inda dad d'in manosh
yabiya musu kud'in jirgi se aminu kano.
Kamar da wasa doctor ahmad babban dr ne wanda kowa yasani, ya iya aikinsa
sosai batare da b'ata lokaciba cikin 2days akayiwa maryam duk wani gwajegwaje
daya dace,maganan shukrah dai ya tabbata domin k'odan maryam kusan dukma sun
samu matsala wanda dolene se'an mata sabon dashe,ma'ana se'an sa mata wani
k'odan.
Hankalin mama ya tashi sosai,tanata hawaye,yah ibrahim da muh'd ne suke
rarrashinta tare da kwantar mata da hankali,kwanansu biyar suka koma yola.
Mamaki sosai akayi dajin matsalar maryam,mahaifinta yace zai fitar da ita
zuwa *india* domin ayi mata aiki,amma sam maryam tak'i tace ita babu inda zataje
se manosh ya dawo.
Su marwan sunyi iyakan k'ok'arinsu zuwa masallatai da kuma malaman sunna akan
abinda ya sami amininsu manosh,sun raba kud'ad'e sosai kota ina zuwaga marasa
k'arfi domin atayasu da addu'a Allah ya baiyana manosh.

Addu'oi sosai aketayi ba dare ba rana, kusan kullum ake kiran number manosh amma
sam baya shiga yau kusan sati kenan.
Abdallah da alfiya kuwa tunda akace musu daddynsu yayi tafiyane shikenan suka
yadda tunda dama yanayin tfya yayi 2to3month ma baidawoba,dan haka sam basu
damuba.
Ahankali mahaifin manosh yake shirye shiryen tfyansu maryam india batare da
sanin mahaifin maryam ba.
Idan kaga maryam da miher dole ka tausaya musu sun rame sunyi wani iri,barema
maryam da damuwan yayi mata yawa kuma dama kunsan batada auki.
Miher tana son bro nata wanda kowa yasan da hakan,shiyasa majid yake iya
k'ok'arinsa domin kwantar mata da hankali,hakama maryam kullum nasiha iyayenta
suke mata da kuma yah ibrahim dasam baya son ganinta cikin damuwa,hakan yasa
zaibada k'odanshi guda d'aya asawa maryam,amma sam koda aka gwada baiyi

daidaiba.
K'awayen maryam gabad'aya sun zama abin tausayi domin ganin irin halin da maryam
take ciki,rashida tace da marwan ita aje a gwadata idan har a'a iya sawa maryam
k'odanta to wlh ta bayar da guda d'aya tunda zasu iya rayuwa da d'ad'd'aya,
marwan yace karki dau luv zamu samo mafita amma ina tausayin aunty sosai
wlh,friend na manoh dukkansu basa iya kocin abinci saboda rashin abokinsu,kowa
yasan irin shak'uwar da take tsakaninsu.

Mahaifiyar manosh kuwa ta zama Allah sarki domin sun d'auki son duniya sun
d'aurawa manosh dayake shine d'ansu na fari.
Kuma duk wanda yasan manosh ko kuma wata alak'a dake tsak'aninsu tofa dole ya
shiga damuwa. Cikin sati biyu lbrn manosh ya baza ko ina dayake sojane mai kwazo
ga kuma taimakon marasa k'arfi,sam bayida kyama kamar dai matarsa wato *auntyn
yara*.
Lubna ce kwance a gidansu tana cewa mum nata gaskya mum lokaci yayi daya
kamata in taimakawa maryam akan taimako da rufin asirin data min,mum zanje inba
maryam k'odata guda d'aya,bazan iya bari anemo k'odan wani dabamu saninshiba
asawa maryam.
Hajiya khadija tace lubna lfyarki kuwa bana so ki sake sa bakinki cikin
maganannan,kuma wace irin taimako maryam tayi miki haka? Lubna cikin muryan kuka
tace mum kinsan me,ada bani da wata mak'iya irin maryam saboda yadda nake
k'aunar bro manosh araina,babu wanda yasan hakan dagani se miher naso in sanar
dashi amma dayake shiba mijina bane senaji cewa ya samu mata a girei,nayi bak'in
cikin hakan sosai tunma bansan wacece yake nemaba,ranan muka had'u da maryam da
kuma friends nata a yakubu shopping plaza na yarda keyn motata batare dana
saniba ta biyoni ta bani anan ne muka san juna da maryam harna karb'i numbernta.
Mum daga bayane na san cewa maryam itace yarinyar da bro manosh yake so,tun daga
lokacin tsanarta ya shiga zuciyata nayi niyan d'aukan mataki sosai dan in raba
maryam da bro manosh. Lubna tayi shuru tana kuka sosai cikin tausayawa tace mum
kinsan me? Nice nasa akayi kidnaping

Please Login or Register in order to submit comment