Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta gaida Abba , amsawa Abba yayi da fara'a ɗauke kan fuskarsa yace " Allah yayi muku albarka insha Allah auranku har mutuwa alfarmar shugaban Halitta , Ameena dake gefe tana zaro ido dan yanzu gani take tata ta ƙare Abba ne yace " ki wuce mota kafin inzo babu musu ta fice cikin sauri ta zauna gidan gaba dan yau bazata zauna gata gashi ba tasan bata kyauta ba amma inta tuno burin zuciyarta na saita raba Kamill da farinciki shike ƙara mata ƙaimi gurin aikata tsiyarta san ranta, zufa babu inda baya keto mata dan tsa tsauran ra'ayin Abba tasan zuwan da dawowar.
Abba ne yaci gaba da cewa insha Allah wata mai kamawa zaku ziyarci ƙasa mai tarki Diyana batasan lokacin da murmishi ya kufce mata ba Kamill godiya yayi itama haka , ya kamata ka siya mata mota son inma driver ne sai a samo , to Abba Kamill yace " cikin fara'a , ajiye diyana bandir ɗin ƴan dubu dubu yayi a gefenta cikin jin kunya Diyana tace "Abba mun gode Allah ya ƙara lafiya , daga haka Abba ya miƙe tare da gyara malun malun ɗinsa yayi musu sallama , yana ficewa ya nufi mota back side ya shige batare da ya kalli Ameena ba driver yaja suka wuce masaukinsu.
koda suka isa kowa gurin kwanciya ya nema Amena bata bi takan Abba ba kasancewarsa mai sauƙin kai dakuma bijirewa , washe gari Diyana tana ta haɗa Kamill da Allah akan yakaita gidan su , da zarar tayi magana sai yace " yafison tace " da ciki suganta tayi nauyi , cuno baki tayi tare da kai masa dukan wasa , suyita zagaye palo suna guje guje , da yamma Kamill na zaune yana kallo Diyana na kitchen taje duba girki , wani uban ihu yaji da ya sashi tashi da gudu ya haura sama yana kiran sunanta , wayo my blood na ƙone da mai wayo Allah na , jiyayi kamar zafin ya koma jikinsa abinka da masoya ƙunar ma ba wata mai yawa bace amma duk sunbi sun ruɗe , komawa gefe tayi ya ƙarasa aikin tana gaya masa abinda zaiyi, suna gamawa aka nufi dining aka jere komai , Kamill yace " yazu saura wanka ya rage mana , rufe ido Diyana tayi dan kunyarsa takeji sosai , kamo hanunta yayi suka haura zuwa ɗakinsa ya cire mata kaya shima ya cire nasa , idanuta arufe gam haka suka shige toilet shiko ogan hankalinshi ya tashi da ganin kyan diri irinna Diyana , tabbas yayi sa'ar mata daya bari dayaga samu yaga rashi , a gurin wanka ma sai da akayi drama duk da idonta a rufe yake taƙi yarda ya taɓata rabi wanka rabi tsokana duk inda ya taɓa sai ta zille tana dariya , naɗota yai a towl ya shimfiɗeta a kan bed , rufa mata baya yai tare da ja musu blanket , tunda Diyana taga haka tasan daƙyar yau idan mai afkuwa bata afku ba ga shegen tsoro , ganin Kamill yayi kamar mai bacci yasata miƙewa a hankali , batagai ga sauka daga kan gadon ba taji ya cafko mata hannu tare da matseta a jikinsa , tsam ta matse jikinta dan yau jikinma rawa yakeyi to meye dalili ? batada mai bata amsa yasa tabar abin a cikin zuciyarta ,jin salon komai ya sauya yasa Diyana runtse ido tare da adu'ar Allah ya bata ikon farantawa mijinta Allah kar ya bata ikon wulaƙantashi ko nuna gajiyawa , babu ta inda baya aika mata da message na jikinta cikin sa'a ko ina na amsar saƙon , ada yana taraiyya yana ywan harka da mata amma duk abinda ya keyi bai taɓa sanin kowacce macce ba gashi ma tunda yai aure komai ya lafa , dama ance aure ni'ima ne tabbas kuma ya yarda , jin ya cire towel ɗin da ya naɗeta yayi mata rumfa da ƙirjinsa ya sata runtse ido tana ambato sunayen Allah adu'ar saduwa da iyali yayi sabda gudun sheɗan kana yafara neman hanya , cikin salo daƙwarewa yake aikinsa yayin da yake adu'oi kala kala a cikin zuciyarsa, tun Diyana na daurewa har ta kai ga haɗashi da Allah da ya barta amma ina Kamil yayi nisa , bashi ya sarara mata ba sai da ya tabbatar da ya mai data cikakkiyar mace sannan ya mirgina gefe yana mai da nunfashi , kana daga palo kana jin surutunsa yana cewa " Allah yayi miki albarka my Diya haƙiƙa nayi sa'ar mata mai tarbiya ilimi dakuma hankali kin biyani my Diyana ya rungumeta tsam a jikinsa yana shin shinar gashin kanta tare da raɗa mata i love you cikin sa ssanyar muryasa mai ratsa jijiya , idanunta a lumshe ga hawaye dake zarya tausayi ta basa amma da yake shiɗin shine , yace" tunda baza kiyi shiru ba bari in samo mana baby ai ɗazu inata hangosu sunata cewa " dady ina momy dariya Diyana tasa tare da rufe ido cikin jin kunya.
[29/06, 8:27 pm] Mom Islam Ce💃: 37 & 38

Ƙara langwaɓewa tayi a jikinsa tana yi masa kukan shagwaɓa , shiko sai ƙara lallaɓata yake kamar ƙwai , tashi muje muyi wanka , uhm ni bazani ba kace kai ƙadai pls , Diyana ta faɗa cike da shagwaɓa , Kamill dake dariya yace " nikuma dole sai da ke kitashi kawai kokuma in tasheki , maƙe kafaɗa tayi tana shirin sanya masa kuka , to barin ƙara Kamill ya faɗa tare da haɗe rai , babu shiri ta miƙe ta yayibo towel ɗin zata ɗaura ya ƙwace tare da ciciɓarta zuwa toilet , yana direta taji wani azababben zafi na shigarta wayo momy ta fara kira tana tsale ga sabon hawaye yana yimata sintiri a fuska , sorry my Diya Kamill ya faɗa fuskarsa da alamun damuwa , tara mata ruwan zafi yayi a bahon wanka kana ya ɗiga detol ya ɗago ta ya sanya ciki , ihu tasa tare da riƙeshi gam tana cewa wlh da zafi ruwan ka cireni dan Allah , bai kulata ba sai ma ƙare ma halittarta kalo da ya keyi ita kam tsabar wuya tama mance tsirara take , jin tayi shuru tayi luf yasa Kamill tabbatar da ruwan ya ratsa ta , buɗe gurin tafiyar ruwan yayi wanan ya tafi yakuma tara mata wani , sai da yayi hakan har sau uku kana ya temaka mata tayi wanka shima yayi idonta a rufe dan muraran kunyar ganin halittarsa takeyi bare shi kansa , a haka suka gama ya naɗeta kamar jaririya shikuma ya ɗaure ƙugunsa da wani ƙaramin towel a hanunsa ya ɗaurawa Diyana a kanta suka fice , kayana na ɗaki na fa zani in ɗauko , no bazakije ba yau sabuwa kike dole sai sabon kaya , shagwaɓe fuska tayi tana turo baki , dariya Kamill yasa yana ƙare mata kallo kamar yau ya taɓa ganinta , my Diya .
Kamill ya kira sunata cikin sanyin murya , na 'am tace " tare da mai da hankalinta gareshi , kina sona ? zaro ido tayi dan bata taɓa tunanin zata tsinkayo irin maganar nan a gurinsa ba anya shine kuwa ? katse mata tunani tayi dan duk maganar da takeyi a cikin zuciyarta take " My Diya kina sona , Kamill ya faɗa a karo na biyu , kallon ƙwayar idonsa tayi sai kuma ta sunkuyar ƙasa tana wasa da zoben hanunta , miƙewa yayi tare da nufar gaban mirror ya nemi stool ya zauna yana ƙarewa kansa kallo , tabbas ba yabon kai ba ni kyakyawa ne nasani to meye yasa Diyana bazata bani amsar tambayata ba ? kodai dagaske bata fara sona ba ? duk kansa yake yiwa wanan tambayar , kawar da tunanin yayi ya ɗauki lotion ɗinsa mai ƙamshi ya shafa tare da turaruka masu sanyi ya yiwa kansa gyara tare da shafa mayukan daya saba ya miƙe zuwa drower , kayansa ya ciro sabbi wanda bai taɓa sawa ba kasancewar yakanyi ɗinki duk ƙarshen wata yakanyi kusan kala goma banda ƙana nan kaya da yake siya , shadda ce gezna brown tasha aiki ba ƙarya , hula ya ciro kakar shaddar sai agogo daya ɗauka a glass ɗin da suke a jere kamar shago kana ya ɗauki takalminsa ya juyo ko kallon inda Diyana take baiyi ba ya fice palo ,jin ana kiran sallahar magrib yasa shi miƙewa ya nufi masallacin dake gidan yai sallah , yana idarwa ya dawo gida ya nufi dining bai sauka ba sai da ya tabbatar da ya cika cikinsa tab sanan ya dawo kan doguwar kujera 3siter ya kwanta tare da zubawa kwaliyar sama ido , tunani iri iri gashi ya fara ɗawainiyar son Diyana gashi kuma tana nema taƙi karɓar soyayyarsa.
Gajiya da zama Diyana tayi cikin lokaci ƙalilan zazzaɓi mai zafi ya rufeta wanda ko buɗe ido bata iya yi ga azabar ciwon kai , daƙyar ta samu ta janyo pilo ta kwanta ga wani sanyi dake addabarta , bata lura da blanket a kusa da ita ba hakan yasa kana nesa kana jin ƙarar kaɗawar haƙoranta, kamar an tsikare shi ya miƙe ya nufi ɗakinsa , yaje da niyar ko kulata bazai yi ba yaci karo da ita tana ta rawar sanyi , da sauri ya ƙarasa tare da cewa " ya illahi my Diya maiya sameki kodai nine in ni na ɓata miki rai pls kiyi haƙuri bada son raina bane am srry mgna yake kamar wani zautacce amma Diyana ta kasa koda ɗaga yatsanta banda hawaye babu abinda ke fita daga fuskarta , matsowa yayi ya rungumeta yana jin ɗumin jikinta sosai ,jin ana kiran sallahar isha'i yasa shi shimfiɗa darduma ya tada sallah yana idarwa ya nufi inda Diyana take shafa fuskarta yayi idanunsa cike da hawaye ya fice ya nufi bedroom ɗinta , hankalinshi a tashe ledar kayan da Abba ya basa jiya ya dubo mata doguwar riga baƙa mai adon golden stone dakuma ɗankwalinta , ya buɗe drower ya ciro mata pant da under ya fito , yana shiga ya samu ta ɗan miƙe tana cewa " zan sha ruwa cikin azama ya nufi fridge ya ɗauko swan water marar sanyi ya buɗe ya bata tasha , babu batun shafa mai ya sanya mata kayan ya fito da ita palo ya kwantar , ɗauko keys ɗin ƙofar palon yayi kana ya goyata a baya ya fito ya kulle ƙofar ya nufi mota , drivers abin ya basu mamaki ganin Kamill zai yi driving da kansa , ganin abinda ya goyo yasa kowannen su tashin hankali masu kula da shi duk babu wanda yayi gigin zuwa tambayarsa , kasancewar sun sani inhar yana cikin ɓacin rai basa tunkarar shi , kai tsaye ana buɗe masa get ya fice da uban gudu ya ɗauki hanya Rahama hospital ya kaita asibitin kuɗi , kasancewar shine mafi kusa dasu , suna isa ma'aikatan hospital ɗin suka fito domin taryar su Kamill , zasu ɗauki Diyana ya dakar dasu da kansa ya ɗauketa ya shiga da ita , suna shiga aka fara bata temakon gaggawa hankalin Kamill a matuƙar tashe sai zaga libraryn asibitin yake zama ma ya ga gareshi , kira yaji a wayarsa hakan yasa shi saurin ɗagawa kasancewar yaba wa doctors number sa , kazo ina office abinda yaji ance kenan aka katse wayar , da sauri ya nufi office ɗin babban likitan , samunsa yayi zauns a kujera da farin glass manne a fuskarsa yana ƴan rubuce rubuce , kaine mijin mara lafiyar da aka kawo ɗazu ? eh eh Kamill yace " dan burinshi yaji meke damun Diya ɗinsa , akwai abinda yai matuƙar tsorata ta har yake barazana da zuciyarta so a kula kar adinga tursasa ta abinda bataso kuma tana buƙatar bacci sosai sai zuwa gobe zamu sallameku , ajiyar zuciya Kamil yayi kana yace " babu damuwa nagode , ya tashi zai fita ya dawo am zan iya ganinta ? eh doctor yace , ok Kamill ya nufi ɗakin da shigarsa ya sameta kwance iya ciwon rana ɗaya ta rame abinka da marar ƙiba takuma sirancewa sai dogon hanci da dara daran idanuwa , lumshe ido tayi tare da miƙowa Kamill hannu , da sauri ya ƙarasa ya zauna a kujerar dake kusa da gadonta ya haɗe hanunsa cikin nata , sannu my Diya Allah ya baki lafiya , lumshe ido tayi kana tace " my blood naji sauƙi fa karka damu wlh, dole in damu farinciki na babu lafiya daga ke sai Abba kune farinciki na , hawaye yaga na bin kumatunta cikin sauri ya share mata yana cewa " wanan maganar ce ta saki kuka am sorry karki ƙara nima nayi shiru , ina mahaifiyarka .......sauran suka maƙale mata a bakinta , dama yana jiran wanan ranar , danginsu ƴan uwansa babu mai bibiyar gidansu babu mai tambayar mahaifiyarsa sai yau ko Abba ma baya maganar ta iya kaci yaji ance ta mutu tun yana ƙarami anya kuwa mutuwar tayi ? ya fara waswasi a cikin zuciyarsa bai kai ga bata amsa ba takuma jefo masa tambaya , wanan matar itace ta raineka ko ? eh Diya amma mai yasa bakida lafiya zaki tadawa kanki da hankali pls kidena kibari kiji sauƙi zanyi miki bayanin komai.
[30/06, 4:32 pm] Mom Islam Ce💃: 39 & 40

Uhm Diyana tace " tana shafo sajen fuskarshi dake matuƙar burgeta, tashi ɗaya tunanin mahaifiyarsa ya dawo masa da baya tunanin ta da yanzu kan hankalinsa yayi matuƙar tashi yana son yasan ta mutu ne kokuma akwai wani abun da ake ɓoye masa , juyawa yayi yaga bacci ya ɗauketa , ajiyar zuciya ya sauke tare da duba agogon dake manne a tsintsiyar hanunsa , ƙarfe biyar na yamma , fitowa harabar hospital ɗin yayi yana dube dube wani katafaren shago ya hango da alamu baza'a rasa abin sawa a bakin salati ba , yana zuwa ya karɓi malte da viju milk dakuma donute ya biya kuɗin kana ya nufi hospital ɗin , idon ta a buɗe da yake baccin ba mai nauyi bane , ina kaje ? Diyana ta jefo masa tambaya da sa sanyar muryarta , naje nemo miki abinci ne , uhm bana jin yunwa fa , janyo ledar Kamill yayi ya ɗaauko maltina zai bata ta kawar da kai tare da ce masa babu mai madara ne , dariya taso bashi ya kwai kwayi yanayin maganarta yana dariya , haɗe rai Diyana tayi tace " nafasa sha ma sorry kar kiyi fushi pls my Diya , murmishi tayi masa wanda har dimple ɗinta ya loɓa , a baki ya diga bata viju ɗin har sai da tayi rabi ta kawar da kai , ƙin cin donut ɗin tayi shiko bawa cikinsa yake duk da yana cikin damuwa , my blood ka kira momy ka faɗa mata banida lafiya , cewar Diyana , no baza'a tada musu hankali ba nima ko Abba ban faɗawa ba karki damu insha Allah kinma samu lafiya gobe za'a sallamemu , barin kira securitys ɗina su siyo miki kayan da zaki canxa zuwa anjima , tom Diyana tace " dan batason yi masa musu , fita yayi ya nufi masallaci dan magrib tayi , bashi ya dawo ba har sai da akayi isha'i sanan ya fito ya kira aka siyo mata kaya ya karɓo dan bai bari sun shigo ba kasancewar Allah ya zuba masa kishi sosai , doguwar riga ce dakuma hijab ya shigo room ɗin da aka kwantar da ita , samunta yayi a zaune a kan gadon tana ta rarraba ido da sallama ya shiga ya sami kujera ya zauna , dubanta yai yace " gafa kayan nan , karɓa tayi tare da godiya ta ajiyesu a gefe , ta kallesa tace " zanyi sallah , tana shirin miƙewa doctors suka shigo su biyu mace da namiji ya yanayin jikin ? suka tambayeta tare da tambayar ko akwai abinda yake damunta , babu komai Diyana tace " suka gama abinda zasuyi suka fice. temaka mata yayi tayi alwalah ya fita zuwa mota ya ɗauko sallah yana shigowa ya shimfiɗa mata ta sanya hijab ta tada sallah , neman gurin zama yayi yana ƙare mata kallo , tana idarwa tayi adu'oi ta shafa ta ninke sallayar ta dawo bakin gado ta zauna Alhmdulilh Kamil yace ya sakar mata murmishi , itama maida masa tayi da haka dare yayi sosai , dan a lokacin ƙarfe takwas , gadon kusa da Diyana Kamill ya hau yaja sabon blanket ɗin dake ajiye a ko wane gado , itama kwanciyar tayi , kasancewar zirga zirga da yasha yana kwanciya bacci yayi awon gaba dashi , itama baccin ne ya kwasheta sbda allurori da tasha , washe gari da asbha kowanensu ya tashi bayan sunyi sallah ta shiga toilet ta haɗa ruwan wanka wata likita ce ta shigo da sabon soso da sabulu ta miƙawa Diyana , Kamill ne yace " my Diya ko inzo inyi miki wankan ne ? da sauri ta shige tare da turo ƙofar da ƙarfi tana dariya , tana gama wanka ta leƙo ta huduwar ƙofar tace " my blood miƙomin kayana , yana ji yaƙi kulata , sai da ta sake magana a karo na biyu ya miƙa mata yana mamakin kunya irin ta Diyana kamar ba wayayya ba taɓɓ , tana gama sanya kayan ta fito kasancewar bbu mai wani kallo da Kamill ke binta dashi ne yasa ta hura masa iska a ido tare da cewa " kamar an sauya ni ? murmishi yayi yace " sauyi kuma waye ? kaine kaine ta faɗa tana nunasa , tama bashi dariya sosai sai da ya dara, suna haka aka kawo takardar sallama , tare da cikon kuɗi 40k haka ya biya suka nufi gida.
yau su Abba suka koma Kano har yanzu tsakaninsa da Ameena sai dai haɗuwa ta mota ko kulata beyi itama bata bi ta kansa ba tasan inhar ta matsa sai tayi nadama , suna sauka a mota kowa yai part ɗinsa , waya naga ta ciro ko zama batayi ba tahau kiran wata number da babu suna , ji nayi ance Hajiya barka dai yawwa bos ina maganar matar da kazo ka tafi da ita shekara talatin da suka wuce ? wacce kenan ? bos ɗin ya tambaya , ko ka mance Hajiya ameena ok ok na tuna ,ai a hanyar Lagos na yar da ita kwanaki naga an nunota a tv na tsorata kar asirinmu ya tonu zaro ido Hajiya Ameena tayi tare da cewa " nshiga uku Allah ya auna mana arziƙi taɓ , daga haka ya katse wayar bai sake bi takan maganar ba , zufa ce ke karyo mata ta ko ina, magana ta fara kamar wata taɓaɓɓiya , nasa boka ya rufe bakin kowa gashi asiri na yana neman tonuwa , inhar hankalin Alhaji dana ɗansa suka dawo to babu makawa nariga na mutu wlh gashi rabona da boka tun lokacin da yaimin aikinnan , jimami da fargaba suka taru a zuciyar Amina , koda wane lokaci gani take za'a iya hasko fuskar mahaifiyar Kamill shiyasa ma kwana biyunnan ta ƙauracewa tv kwata kwata.
Hajiya ce riƙe da hanun Tinene tana yimata mita akan tanaso yau ma sai sun shirya Alhaji yace baza su ba to bazata lamunta ba babu mai zuwa dubota , haka dai ta cika gidan da masifa shigowar Alhaji yaci karo dasu harda Afreeda a jikin mota , ina zuwa kuma Hajiya ? ko kallonsa batayi ba bare yasa ran da zata amsa masa , sadda kai ƙasa yayi tare da cewa "Allah ya baki haƙuri Hajiya , yana tafiya sai da ta tabbatar ya ƙule cikin gidan ta kira driver tace " ya kaisu gidan su zabiya , cikin sauri suka shige driver ya tada mota suka ɗauki hanya , sun ɗanyi tafiya sanan suka iso anguwar , horn drivern yayi mai gadi ya buɗe masa suka shige , yana parking suka fito Afreeda da gudu ta shige ciki ta fara ƙwanƙwasa ƙofa , jitayi Kamill yace " waye zaro ido tayi ta ƙame a gurin dole ta jira Hajiya ta iso , ai basu buɗe bane ? suka barki a tsaye kamar bishiya ? eh Afreeda tace " tana dariya , masifa Hajiya ta fara tana cewa " zaku buɗe ko sai mun rotsa gilahin da taɓarya , jin muryar Hajiya yasa Diyana miƙewa tace " my blood granny ce tazo , cikin fara' a yace " barkansu barin je in sako kaya ya miƙe da sauri ya haura sama, buɗe musu ƙofar tayi tare da rungumo Afreeda suka shigo ciki , halan mu ba mutane bane da zaki ƙyalemu ko ? cewar Hajiya , laa yi haƙuri granny barkanku , taɓe baki Hajiya tayi tahau waige tana cewa " ina shugaban naji maganarsa ina ya ɓuya , ya shiga ciki Diyana tace " tana kallon Afreeda da ta ƙara girma tayi ƙiba , sis bakida lafiya ne ? Afreeda ta tambayeta , eh sis cewar Diyana , Hajiya ce ta kalli Diyana tace " an gamu kenan sai a kiyaye shan magani mai ɗaci ku yaran zamani da sanabe , yanzu gashi ashe rabo ne ke kiranki , sunkuyar da kai Diyana tayi sbda taji takun takalmin Kamill yana tahowa , ga kunya da ta kamata , Hajiya ce tace " to abamu ruwa musha tunda sai mun roƙa , sis pls tashi ki ɗibo ruwa , ajiye mayafinta Afreeda tayi ta nufi fridge ta kwaso su drinks da ruwa ta ka wowa hajiya , tare da neman gurin zama , Hango Kamill Hajiya tayi daga nesa taga kamar balarabe , to shikuma wancan waye ? dan naga ba kalar fatarmu ce da shi ba , dariya ce taso kubcewa Diyana tace " bature ne nima a gidan na gansa.
[30/06, 6:40 pm] Mom Islam Ce💃: 41 & 42

Kamill dake sauko wa cikin takunsa na ƙasaita ya durƙusa har ƙasa ya gaida Hajiya kana ya dubi Afreeda kallon inda Diyana take yayi sai yaga kamar ƴan biyu dariya Diyana tasa dan ta lura da kallon da yake yi musu sunkuyar da kai Afreeda tayi tare da cewa " barka da rana ywwa barka yasu momy cewar Kamill , suna lafiya Afreeda tace " komawa ciki Kamill yayi naga ya ciro wayarsa ya danna lambar Diyana , bata ɗaga ba dan tasan mai kiran yasa ta miƙewa tayi bedroom ɗinta dan taga kamar nan ya shiga , oh ni ƴa su yaran zamani babu kunya ta tafi ta shanyamu yayi har ana hanani zuwa ina masifa , tana shiga Kamill ya rufo ƙofa tare da rungumota yace " my Diya kin yi baƙi kin mance dani ko ? to ya jikin naki ? da sauƙi tace " tare da lumshe ido , ciro kuɗi yayi zasukai 20k ya bata yace " tabawa su Hajiya shi zai je Abuja yau ɗinnan amma bazai dawo yau ba , rau rau tayi da ido kamar mai shirin kuka tace " to muje tare man nikam bazan iya zama ni kaɗai ba , kiyi haƙuri zamuje amma ba yau ba jirgi zan hau kinga yanzu ƙarfe biyu , da ƙyar ya rarrashe ta ta amince zasuje sati na gaba , Allah ya tsare tayi masa ta ɗauki kuɗin ta dawo palo , wani mugun kallo Hajiya ta wurga mata tare da cewa dusa kika shuka ke daɗi miji ko kin tafi kin barmu ko wai waya babu , Diyana dai batayi magana ba ta dire wa Hajiya kuɗi a jikinta , zaro ido hajiya tayi zatayi magana Diyana tace " kiyi masa godiya , Kamill da ya fito hanunsa riƙe da wayoyi hajiya tace " to mai gida an gode fa , babu komai Kamill yace " a gaida momy ya fice , Diyana sai kallonsa take fuskarta da alamun damuwa ta dawo kujera ta zauna , to duk Allah ya tsaren da kikayi masa beyi ba sai kin ɓata ranki a banza to wlh

Please Login or Register in order to submit comment