Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a dai dai wanan time ɗin yakeda buƙatar mace " a duk lokacin da gari yai sanyi to baya cikin kwanciyar hankali ,ga gararsa kwanciyar tayi ya dawo palo ya kwanta yana rawar sanyi , haƙoransa babu inda baya rawa ga wani wahalalen nunfashi dayake sauƙarwa .
Kamar an tsikari Diyana ta miƙe tare da buɗe ƙofa ta fito palo ko me take nema oho , jiyo sautin sauƙar wahalalen nunfashi ya sata ƙarasawa da gudu domin taga waye , Kamill ne kwance jikinsa nata ɓari , abinka da mace mai tausayi sai ta tallafo kansa ta gyara masa kwanciya tare da miƙewa ta nufi ɗakinta ta haɗo masa shayi mai zafi ta kawo masa , tashi kasha , jiki na rawa Kamill ya fara shan shayin cikin ikon Allah zufa ta fara keto masa ta ko ina yadena jin sanyin , tunda Diyana ta tabbatar ya dawo hayyacin sa ta janyeshi tare da cewa " kaci darajar tausayin da Allah yasa min amma badan haka ba babu dalilin da zai sa in temakeka taja tsaki.
Kamill dai jiki babu ƙwari dan haka bai kulata ba ya maida kansa ya kwanta ,
Zuwa ƙarfe goma da rabi yaji sauƙi sai ciwon mara dake ɗan damunsa , haka dai ya haura zuwa ɗakinsa yai wanka ya sauya kaya sai ƙamshi yake zubawa dole duk macen da ta gansa sai ta yi sha'awar ya kasance mijinta , fararen kayane a jikinsa ta baƙar hula mai adon farin zare ga tsadaden agogon sa da takalminsa fari , sakowa yakeyi a hankali kamar ba shine mai rashin lafiya ba , direct ɗakin Diyana ya dosa ya murɗa handle ɗin ƙofar cikin sa'a ta buɗe , zaune ya sameta tana makeup itama fa tayi kyau sosai ta haɗe cikin baƙin leshi mai adon jan flawoyi tagama shafa powder tana shafa pink ɗin janbaki ɗakin ya game da ƙamshi , tsayawa Kamill yayi yana ƙare mata kallo cikin zuciyarsa yana cewa " gaskiya da auran soyayya mukayi da na more wanan mai zan so a jikinta mtsw ya kauda tunanin da ɓacin rai ,
Baiyi magana ba ya fice itako tun shigowar sa tana kallonsa ta mirorr bata kulasa ba , ɗage kafaɗa tayi irin ko a jikina ɗinnan .
Ba'a jima ba taji ƙarar tsayawar motarsa tasan shine ya dawo , kuloli ne masu kyau a hanunsa guda biyu ya nufi dining dasu ya jere su tare da ɗauko su fanta da 5alive da sauransu ya ajiye , kuma komawa ɗakin Diyana yayi wanan karon harda sallama , amsawa tayi cikin siririyar muryarta , zama yai a gefen bed tare da cewa am sorry mata ta kiyi haƙuri da dukkan laifukan da nayi miki nasan ban kyauta ba , nan danan zuciyar Diyana ta karaya kasancewar ta mai saurin fushi dakuma tausayi uwa uba ga son a risina mata, bakice komai ba my Diya? sharesa tayi tana ƙoƙarin miƙewa , janyota yayi ta faɗa jikinsa suna jin ninfashin juna ya kai fuskarsa kan tata tare da cewa nayi miki magana tare da bada haƙuri kinƙi kulani ko kinason Allah yayi fushi dake ? tuno nasihar su momy da dady tayi cikin karayar zuciya tace " na haƙura wata irin runguma ya kai mata tare da manna mata kiss a kumatunta , munada baƙi fa , waro ido Diyana tayi tare da cewa " mai za'a dafa musu ? no nasiyo kawai inason ki zama cikin shiri , oky Diyana ta faɗa da murmishi ɗauke a fuskarta.
[23/06, 9:45 pm] Mom Islam Ce💃: 25 & 26

Yana shirin fita wayarsa tayi ring number abokinsa ke yawo a screen ɗin wayar , amsawa yayi tare da sallama yace "Nasir kun iso ne ? daga can ɓangaren naji ance gamu nan shigowa muna bakin get , ok Kamill yace " ya ajiye wayar .
ɗauko turare yayi ya feshe Diyana tare da cewa " yakamata kiyi wanan murmishin mai kyau lumshe ido Diyana tayi tana ƙarewa bakinsa da yake mata magana kallo .
Suna haka sukaci ana ƙwan ƙwasa ƙofa , da sauri Kamill ya fita ya taro su yana yimusu sannu da zuwa kasancewar su biyu ne shida matarsa Fadila , iso yayi musu zuwa inda zasu zauna , Nasir na zama yace " aboki ina amarya ne nifa kasan akwai surutu , dariya Kamill yasa yace " karka damu amarya na ciki tana fitowa inaga ko kunya ce ta hanata amma barinje ina zuwa , daga haka Kamill ya miƙe ya nufi bedroom ɗin Diyana samunta yayi da waya a hanun ta tanata ɗaukar kanta a photo , eyee Kamill yace " tare da zama ya rungumeta yafara yimusu salfe , oya tashi suna son ganinki , kukan shagwaɓa Diyana ta fara tana cewa " nikam kunyarsu nakeji , sorry my Diya kawai ya sunkuceta ya goya kamar baby ya kawo ta palo ya zaunar da ita kan kujera yana cewa " to munzo Nasir ga amarya ta iso , dariya Fadila da Nasir suka sa Fadila tace " mu ba baƙi bane Diyana , tun Diyana na noƙewa har ta sake suka gaisa suka fara hira , miƙewa Diyana tayi tafara jido musu kayan abinci tana jere musu , masha Allah sunci babu laifi sukayi godiya , Fadila ce ta kamo hanun Diyana tace " zomuje Nasir da baki baya shiru yace " mata iyayen gulma zaki koya mata halin naki ko ? suka kwashe da Dariya , suna cikin tafiya Fadila tace " inane bedroom ɗinki ? gashi nan Diyana tace " cikin jin kunya.
Shigewa sukayi Fadila ta rufo ƙofar tare da zama a gefen gadon Diyana .
sunana Fadila wanan mijina ne wato yaya Nasir Allah bai bamu aihuwa ba kuma har yanzu bamu fidda rai ba , muna zaune a garin kano nima ƴar Kano ce .Allah sarki Diyana tace " Allah ya baku masu albarka , Fadila ce ta amsa da amen , janyo hand bag ɗinta tayi kana tace " bamu sami damar yimuku tsaraba ba amma ke nayi miki , tunda naji sunanki Diyana sunan sis ɗita ne , murmishi Diyana tayi .
Fadila ce ta miƙawa Diyana wata ƙaramar jaka mai ɗauke da tsadadun humra da magunguna , duk da batasan ko maganin meye ba tace " nagode , Fadila ce tayi dariya kana tace " tun banyi miki bayani ba ? kinga wanan turaren a fuska ake shafawa inhar kinsan Kamill na gida karki sake ki shafa in zaki fita , to Diyana tace "ɗago wani turaren tayi a ƴar wata kwalba tace " kinga wanan turaren a ƙasan mararki in zakije gurin oga , rufe fuska Diyana tayi alamar jin kunya , akwai millk? eh Diyana tace " Fadila ce tace " ɗauko guda ɗaya , kasancewar ta kwaso kayan tea ɗin ɗakinta yasa ta miƙowa Fadila da cup ɗin da ta buƙata , ta koma ta zauna tana kallon Fadila ta fasa madara ta juye tare da garin maganin nan dakuma wani haɗin dabino ta cewa " Diyana ungo ki shanye , no bazan shaba Diyana tace " idanunta sunyi rau , pls kisha bazan kawo miki abinda zai cutar dake ba wanan haɗin da kike gani ba a siyar dashi a nan kasancewar kayan suna yiwa masu magani wuya daga Nigar yake , nifa anty kiyi hakuri dan kona sha ma ....ta mance da wa take magana ta rufe fuska tare da juyawa , dariya Fadila takuma yi a karo na biyu tace " a taƙaice dai kice Kamill bai karɓi haƙƙinsa ba ? eh Diyana tace " sai kuma tayi shiru , to yanzu meye matsalar kece ko shine ? shine Diyana tayi saurin faɗa , maiya haɗaku ? ba auran soyayya kukayi ba ? a ' a gaskiya baya sona nima bana sonsa , innalilahi Fadila ta faɗa cikin mamaki , ga yanayin ku yana nuni kamar kuna son junanku ? uhm Diyana tace " dan maganar m ta isheta , to kwantar da hankalinki nayi miki alƙawarin sai Kamill yazo yana baki haƙuri amma tunda nariga na haɗa maganin nan kisha ƙila yau ya nemi haƙƙinsa , nifa ba so nakeyi ba , Diyana tace " tana cuno baki , ke bakisan maza sai da lallami ba ko ? Fadila ta faɗa tana kallon Diyana daƙyar ta samu Diyana ta shanye wanan magani tass , Fadila ce ta jiyo ring ɗin wayarta tana duba mai sunan my lovely ne ya sata miƙewa tare da cewa " bani number ki , gaya mata Diyana tayi kana Fadila ta fice tabar Diyana , juyi Diyana takeyi a ɗakin tarasa mai zata bawa Fadila dan jininsu ya haɗu , ɗauko wani ƙaton turare na kwali tayi a akwatinta mai tsadar gaske tasa cikin leda ta yafo gyale ta fito dashi , samunsu tayi a tsaye suna shirin tafiya , Nasir ne yace " amarya bakya lefi kokin kashe ɗan masu gida , dariya Fadila tasa tace " bata kashe ba dai da anyi mata hukunci , Diyana dai tana riƙe da leda a hannu sai da taji suna cewa " to mun barku lafiya Nasir ya ajiye kuɗi masu yawa a kan kujera yace " abawa amarya , godiya sukayi masa kana duka suka fice , cikin sanyin jiki Diyana tabi bayansu dan ji takeyi kamar sun daɗe da Fadila , su Fadila na shiga mota ta ɗora mata ledar a cinyarta ta juya idanunta cike da hawaye , tana shiga bata tsaya ba ta wuce bedroom ɗinta ta faɗa bed tare da sakin kuka mai ban tausayi Allah yasa rayuwar auranta ta ɗore cikin farinciki tabbas inhar Kamill da gaske yakeyi to ta zubar da makaman yaƙinta zata farantawa iyayenta.
bacci mai nauyi ne yai masarar ɗaukarta ba ita ta farka ba sai misalin ƙarfe biyar na yamma ta jita a jiƙe kamar tayi fitsari , tuno maganar Fadila da tace " mata zataji hakan yasata miƙewa ta nufi toilet takumayin wanka ta zauya kaya , iya mai kawai ta shafa sai turare mai ƙamsi ta fito palo , bata sami kowa ba tunani ta fara kodai Kamill bai shigo bane tun fitarsa ta ɗazu ? batada mai bata amsa ya sata yin shiru ta nufi kitchen taliya jollof ta ɗora wacce taji kifi da kayan ƙamshi nan da nan gidan ya game da ƙamshin abincin Diyana , ta iya girki amma batayi a gidansu kasancewar abinci ba ya cikin lissafinta wanan ɗin ma dan ta farantawa Kamill tayishi, sai da ta gama ta wanke komai kana ta fito dasu ta dawo palo ta zauna tana mayarda nunfashi , yanzu kuma mamaki takeyi wai itace take wanan hidimar taɓ wanda da a gida ne ko nawa za'a bata bazatayi shi ba , kawar da zancen tayi ta miƙe ta nufi bedroom ɗinta , shiru shiru Kamill bai dawo ba har akayi magrib ,sai bayan isha'i sanan taji nocking cikin sauri ta miƙe tana rawar jiki ta iso palon , oyoyo my blood ka dawo lafiya ? haɗe rai Kamill yayi kamar an aiko masa da ranar mutuwarsa kana yace " dallah bani guri , mamaki ne ya cika Diyana a tunaninta ya bata haƙuri ai yanzu zama zasuyi na soyayya duk da iya kyanshi ke birgeta.
Tsayawa tayi sororo tana kallonsa da mamaki kusan tureta yayi ya wuce kamar zai tashi sama , mayarda ƙofar tayi tasa key kana ta nufi bedroom ɗinta ta kwanta ta kifa kanta tana kuka , mai yasa na damu dashi ? mai yasa nake yawan tunaninsa ? a iya sanina auran bana soyayya mukayi ba yakamata na fita harkarshi kar ya raina ni lol , duk ita kaɗai take wanan surutun
[24/06, 9:52 pm] Mom Islam Ce💃: 27 & 28

Mamaki da tuno lallaɓar da yayi mata tayi oh dama ashe haka maza suke ? ta tambayi kanta tana shirin miƙewa , jin ring ɗin wayarta ya sata dawo da baya dan ganin mai kiran , number Fadila ne da tayi seven da anty Fadila , ɗauka tayi tare da cewa " barka anty kun isa gida lafiya ? barka my lil sis wlh muna nan Abuja gidan ƙanin dadyn shi so ya oga , share hawayen da suka zubo mata tayi tace " tunda ya fita ban sashi a ido na ba sai yanzu nayi masa sannu da zuwa harda girki ko saurara ta baiyi ba , kusan tureni ma yayi , a 'a 'a anty Farida tace " tare da riƙe baki kamar suna tare , Diyana
Fadila ta kira sunanta , na'an anty , Fadila ce tace " yanzu yana ɗakinsa ne ? eh Diyana tace " tana jiran abinda Fadila zata faɗa mata , ki tashi kiyi wanka ki shafe jikinki da wanan humarar dana kawo miki ,ki shafa wanan turaren a fuskarki , to Diyana tace " cigaba Fadila tayi da cewa " kisami Sleeping dress mai kyau wanda zai bayana komai na jikinki kisa shima ki feshe shi da turare , kije gurinsa cikin murya mai sanyi kiyi masa kalami mai daɗi tare da ɗan shigewa jikinsa , taɓɓ Diyana tace " to bazai saurareni ba kinaso in dawo da tabo kenan bazan iya ba anty , no ƙanwata zaki iya inkinsa kanki karkiji komai inda kukayi ki kirani ki gayamin , to kawai Diyana ta iya cewa dan a halin yanzu bazata kuma yarda da shirya warsu ba , daganan sukayi sallama Diyana ta ajiye wayar tana ta tunanin maganar anty Fadila ,ta shafe lokuta a zaune a gurin har dare yayi nisa ta miƙe ta dannawa ƙofar key tare da yin adu'ar bacci ta kwanta , washe gari da safe bayan ta gyara gadonta tayi wanka ta sanya gajeran wandon jeans da riga ves mai siririn hannu rigar iya cibiyarta ta kifa cikinta a gado tana tuno rayuwarta ta gida , cikin farinciki , tunowa tayi Kamill yayiwa momy alƙawari zasuzo tun jiya amma bai kuma magana ba ,
Fitowa tayi tana shirin hawa up step sai kuma ta fasa tana ganin kamar zai wulaƙanta ta kuma tanson zuwa ganin momynta , wata zuciyar ce ta ingiza ta , cikin takunta a hankali ta haye zuwa ɗakin nasa da sallama ta tura door ɗin bataga kowa ba hakan ya bata damar shiga kai tsaye , kasancewar babu kowa a palo yasa ta shiga bedroom ɗinsa batare da jin tsoro ba , samun sa tayi a kwance yayi rup da ciki yana juyi idanunsa sun sauya launi , murmishi tayi kuma ta ƙudiri aniyar yau ɗinnan sai ta gigitashi amma bazata bari ya fiddata daga matsayinta na budurwa ba har sai lokacin da soyayyar su ta ɗore sosai , my blood Diyana ta faɗa da cold voice ɗinta hakan kuwa yakuma sa Kamill cikin yanayi , yafara kiranta a wahalce my Diya pls help me dan Allah zan mutu ki temakawa rayuwata , yau kam Kamill bai bata tausayi ba tunda bai san mai ake kira da hakan ba , kai tsaye taje gareshi tare da yi masa rumfa da ƙirjinta ɗago hanunsa tayi taji ya sakesa sharab hakan yasa ta tabbatar da bashida wani power a jikinsa good Diyana ta faɗa a cikin ranta , mirginoshi tayi kamar ƙaramin yaro ta haɗe bakinsu guri ɗaya , wani ƙamshi da ya ziyarci bakinta mai kamada na flevor yasata lumshe ido , Kamill abin nema ya samu yafara wasa da komai na jikinta yana fitarda nunfashi ƙasa ƙasa, itama wani yanayi ne ya ziyarce ta wanda ita kanta batayi tsammani ba , jin yana yimata wasu abubuwa wanda yake neman tarwatsa ƙudirinta yasata yin azama ta fizge da sauri tayi hanyar fita , pls my Diya ki temakeni karki tafi ki barni dan Allah , duk wanan surutan nasa basuyi tasiri a zuciyar Diyana ba sai ma dawowa ɗakinta da tayi tana maida nunfashi gashi jikinta duk ya yi sanyi ga ɓata jikinta da tayi , toilet ta shige ta haɗa ruwan wanka mai ɗan tsafi ta daɗe tana wankan zuciyarta cike da tunani iri iri , shin wai itace tayi wanan aika aikan ? anya idan Kamill ya fito bazai hukunta ta ba ? gashi yanada extra key na ɗakinta nashiga uku ni Diyana ko a mafarki ban taɓa tunanin zan iya haka ba .
Duk ita kaɗai ke wanan lissafin haka ta kwanta bata sa komai a cikinta ba , washe gari bataji motsin Kamil ya fito ba , tunani tafara kodai bashida lafiya ne oho ta bawa kanta amsa , karma inje in tarowa kaina masifa , ta shige kitchen tare da ɗora ruwan zafi ta soya ƙwai da bredi ta juyo a plet gakuma ruwan zafin a cup , jin kamar motsin mutum ya sata juyawa , ganinshi tayi yana mirginowa duk yabi ya rame kamar wanda yayi sati yana ciwo , ba shiri ta mayar da plet ɗin da cup ɗin nata ta dawo gurinsa ta tsuguna tare da cewa " bakada lafiya ne ? girgiza mata kai yayi alamar eh, to barin kira driver a wahalce Kamill, yace " ban saki ba waro ido Diyana tayi tana mamaki irin wulaƙanci na Kamill da har za'a temaka masa yake hanawa , haɗomin ruwan zafi da lipton kisa lemon tsami , sai da tayi kamar bazata je ba sai kuma ta tafi ta haɗo masa ta kawo tare da temaka masa ya zauna yana riƙe da mara , miƙa masa cup ɗin tayi tare da barin gurin takoma kitchen ta kwaso plet ɗin da ta mayar da cup tayi ɗakinta , Kamill na kallonta ta wuce , mayarda hankali yayi gurin shan shayin nasa cikin ikon Allah ya haɗa zufa ciwon marar ya lafa masa , a hankali ya miƙe ya sauka ƙasa a daddafe ya dawo palo ya kwanta akan 3siter .
Diyana na ɗaki sai da ta cika cikinta sanan ta janyo fillo ta kwanta .

Zaune momy da dady dakuma Hajiya da Tinene suke a palo Afreeda na zaune a gefe tana game a wayarta , Hajiya ce ta dubi dady tace " Alhaji zamuje dubo wanan zabiyar gobe , dady ne ya katse Hajiya da cewa " Hajiya kubari sai an kwana biyu man , faɗa Hajiya ta kamayi wai dady zai hanata zumunci , bayan sun gama momy ta dubi Hajiya tace " Hajiya mijin yace " suna nan zuwa , riƙe baki Hajiya tayi tare da jinjina kai kana tace " uhm wato yau naga surukar zamani to ko yanzu zasu zo sai naje garama ku ƙyaleni , zan tafi da Tinene ta dinga yimata wanke wanke , buɗe baki dady yayi suna haɗa ido da momy tayi masa alama da yayi shiru , momy tasan Diyana ba yarda zatayi ba shiyasa bata kula zancen ba.
Afreeda kam duk wanda yai magana take kallonsa dan kwana biyunnan ji takeyi kamar sis tanta na cikin wani hali , gudun karta fuskanci ɓacin rai a gurin Dady ya sa bata tambayeshi zuwa gidan ba , amma tunda Hajiya zataje itama zata bisu su tafi insha Allah .

Zuwa azhar jikin nasa yayi masa sauƙi kiran escort ɗinsa yayi a waya , jinayi yace " kayi min take away na farfesun kaza pls , angma oga , kana ya kashe wayar , bayan wasu mintuna ƙalilan sai aka fara nocking come in Kamill yace " har yanzu yana kan kujerar a zaune , shigowa akayi da wata leda mai kyau mutumin ya miƙa masa , karɓa yayi tare da bashi 5k yace " ga kuɗin mutumin ne yace " oga 2k ne no ka riƙe kawai , godiya yayi masa kana ya fice ,
Shiri Hajiya takeyi na zuwa gidan Diyana , Afreeda kam harta kammala kasancewar simple makeup tayi ta sanya doguwar riga fara mai adon black stone tayi kyau sosai , fitowa palo tayi da takalmin ta hill da pos ɗinta kalar takalmin baƙi da mayafinta a hannu , dakuma cake ɗin da momy ta bata ta kaiwa Diyana dan sun san bazata dinga cin abinci ta ƙoshi ba.
[25/06, 6:56 pm] Mom Islam Ce💃: 29 & 30

Kamill na gama abinda zai yi ya koma ɗakinsa dan har yanzu bai fara zuwa aiki ba , bayan Diyana ta tashi tayi sallahar azhar ta fito palo fridge ta nufa ko zata sami abu mai ɗan sanyi , cikin sa'a ta sami exotic buɗewa tayi tafara sha sai da ta tabbatar da ta cika cikinta tsaf sanan ta dawo kujera ta zauna tare da kunna tv wani film suka hasko a tasha tauraruwa hankalinta ya tafi a gurin kallon , bata ankara ba taji an ɗauketa cak gashi bataga wanda ya ɗauketa ba , ganin ɗakinta aka shige da ita ya sata shan jinin jikinta da cewa ba kowa bane sai Kamill , yana direta ta ɗago kai tana kallonsa , ita dai sajensa da ƙaramin lip ɗinsa suna birgeta , baiyi mata magana ba sai ma hararar ta daya soma yi , karki sake kiyi tunanin ina sonki ne auran fansa nayi a yayin da zan tada miki da GUGUWAR ZALUNCI na a lokacin zaki tabbatar da koni waye , mtsw Diyana taja tsaki , kana tace " haka kake faɗa kullum ai bansan ka cika mai ZALUNCI ba har sai kasa na dena nunfashi , kuma nima ɗin banda biyayya mai zai kaini auran ka baka cikin kalar.....wani mahaukacin mari Kamill ya sakar mata tare da cewa ki adana kalamanki kar su gudu su barki na faɗa banasonki wawuya jaka , ya fice cikin zafin rai , kifa kanta tayi tana kuka tare da tunanin inhar ta ɗore Kamill na samun lagon dukanta to wataran zai yumata illa gara ta nemi mafita tun yanzu , wayarta ta janyo ta dubo lambar mom Khady wato aminiyar momynta , mom Khady ce ta amsa da my daughter nayi miki lefi ko ? rabona da gidanki tun biki , uhm kawai Diyana tace " sai kuma kuka daya kubce mata baji babu gani , innalilahi mom Khady tace " maiya sameki ne my daughter kodai babu lafiya ne ? cikin sha sheƙar kuka Diyana tace " momy banason aurannan wlh banaso , ya ilahi momyn Khadi tace " tana shirin janyo jakarta dake gefe dama yanzu ta dawo daga anguwa, ta miƙe da waya a hanunta come dwn daughter gani nan zuwa yanzu , duk wanan maganar da akeyi a kunnen Kamill dake ɗan duniya ne sai ya shigo ɗakin da fara'arsa yana cewa my Diya zoki tayani wanka tare da kashe mata ido , wani mugun kallo ta wurga masa duk da haka bai bi ta kanta ba ya janyota suka faɗa bed yayi mata rumfa da yalwataccen ƙirjinsa , haɗe bakinsu yayi guri ɗaya yana aika mata da saƙonni na musamman kasa hanashi tayi dan tanajin daɗin inda yake sarrafa harshen sa a cikin bakinta , jin yana lalubar breast ɗinta ya sata saita nutsuwarta tana shirin ƙwacewa , shiko Kamill gaba ɗaya ya fita hayyacinsa sai sauke nunfashi yake , suna cikin haka sukaji an turo ƙofa , a razane Diyana tayi namijin ƙoƙari ta fizge daga riƙon da Kamill yayi mata , tabi bayan momyn Khady da ta shigo ta koma palo ta zauna , tana zuwa ta faɗa cinyarta tare da sakin kuka , murmishi momyn Khady tayi tare da ɗago Diyana ta zaunar gefenta .
Wanka Kamill ya shiga a ɗakin Diyana kana ya buɗe wata ƴar drower dake cike da sabbin kayansa ya ɗauko boyel fari mai tsadar gaske ya sanya bai tsaya shafa mai ba ya ɗauko takalmi da wayoyinsa ya fito , kai tsaye palo ya nufo inda ya tarar dasu a zaune Diyana na kuka tana wurga masa harar shiko yana sakar mata murmishin gefen baki , duk abinda sukeyi a idon momyn Khady tana karantar su , durƙusawa Kamil yayi tare da cewa ina yini , cikin sakin fuska momyn ta amsa tace " masa ya aiki anyi taro lafiya , miƙewa Kamill yayi tare da cewa alhmdulilh ya nufi fridge kayan sha ya direwa momyn a kan table ya kawo mata cup , yce " Diyana kizo , ya

Please Login or Register in order to submit comment