Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

juya zuwa ɗakinsa kallonta momy tayi tace " tashi kije man ni banga wata matsala a zamanku ba wlh kin tayarmin da hankali ko tambayar dadyn Khady banyi ba na fito , momy bazaki gane bane wlh ...shiittt cewar momyn tashi kije mijinki na kiranki ni zan tafi zan aiko Khady zuwa gobe kuma anjima zamuyi waya , hawaye na zuba a fuskar Diyana tace " momy yanzu bazaki zauna kiji dalilin kukana ba ?" no dalili shine kisani aure ibada ne kowa da haka ya saba kinaso Allah yayi fushi dake ko ? ganin kukan Diyanan ya tsananta yasa momy fita tana cewa sai munyi waya kije mijinki na nemanki, juyowa tayi hankalinta a tashe shin kowa ya kasa fahimtar zaman da takeyi a gidan auranta ne wanan wace irin jarabawa ce ? my Diya tajiyo kiran daga sama batayi ƙoƙarin amsawa ba ta wuce izuwa ɗakin kamill ɗin , ko sallama batayi ba ta tura ƙofar ganinsa tayi zaune da waya a hanunsa yana murmishi , yana jin ta shigo ya ɗago fuskarsa tare da waso mata mugun kallo yace " waye yabaki izinin shigomin ɗaki maza ki fita banason ƙazamin jikinki a ɗakinnan , kai ka kirani cewar Diyana kifita nace ....cikin tsawa yake yimata maganar mamaki da al ajabi sun hana Diyana matsawa mutum kamar aljan yanzu ya gama kiranta da muryarsa mai daɗi harda yimata murmishi amma yanzu tazo yana wulaƙantata , bazaki fita ba ko nan ɗakinki ne ? ok zonan na gane sai kice min kina buƙatata ne kin kawo kanki , har yanzu dai Diyana na tsaye batace " komai ba sbda lamarin yafara bata tsoro anya bashida aljanu ? ta tambayi kanta ashe maganar ta fito fili , ba aljanu ba a bishiyar kuka nake kwana Kamill ya bata amsa tare da rausayar da kansa gefe kamar mace , lunshe ido Diyana tayi ta juya zuwa ɗakinta , tana shiga taci gaba da kukanta tunaninta shine shin mutane basa ganin halin da nake ciki ne ya Allah ka kawomin ɗauki , ɗaga kanta tayi cikin mamaki ta kalli agogon dake manne a jikin bango tace " har biyar tayi ko sallah banyi ba ? miƙewa tayi ta shiga toilet ta watso ruwa tare da ɗauro alwalah ta shimfiɗa darduma ta tada sallah , tana idarwa taji yunwa tayi mata sallama , kasancewar tanada ruwan zafi da kayan shayi yasata ɗauko cup ta tsiyayi ruwan zafin ta haɗa tea mai kauri ta janyo kwanon cake ɗinta tafara aikawa cikinta , sai da taji tayi nak sanan ta ajiye cup ɗin ta janyo wayarta , number sister Afreeda ta dannawa kira cikin sa'a tana ring sau ɗaya Afreeda ta ɗauka tare da cewa " oyoyo my sis kwana biyu ? turo baki Diyana tayi tace " bawani ko nemana bakuyi kun mance dani kwata kwata , dan Allah kiyi haƙuri da yau zamuzo da Hajiya sai dady ya tsayar damu wai mubari sai end of this month , zaro ido Diyana tayi tace " to ai yanzu saura kwana goma wata ya ƙare har sai lokacin zakuzo taɓɓ , kiyi haƙuri barin kaiwa momy wayar ku gaisa , no zan kirata barshi kawai, ko sallama Diyana bata yiwa Afreeda ba ta katse wayar , momy ta kira suka gaisa take tambayarta yaushe zata zo , dariya momy tasa tce " banda abinki daughter waya bani zuwa gidanki yanzu ? kidai ƙara haƙuri zanzo amma ba yanzu ba kici gaba da yiwa mijinki biyayya pls dan Allah ki kula da tsaftar jikinki da gidanki , to momy Diyana ta faɗa tanajin kamar tayi tsuntsuwa ta ganta a jikin momynta amma babu hali , zan aiko driver ya kawo miki saƙo kinji ? tom Diyana tace " tare da cewa ki gaida dady nakira wayarsa akashe , daganan sukayi sallama .
Yau kwanan diyana goma sha ɗaya tunda tazo bata taɓa leƙa wjen gidan ba , sanya hijab har ƙasa tayi ta fito tana zagayawa ashe gidan yanada ɗan girma babu laifi , ga swimming pool gwanin sha'awa jitayi tana sha'awar sanya ƙafafunta a ciki , zama tayi a kujerar dake maƙale a gefen gurin ta zura ƙafafunta tana tuno rayuwa idanunta a lumshe kamar mai bacci , tuno zamanta na ƙauye tayi abin sai ya fara bata dariya idanunta a rufe amma sai ƙyal ƙyala dariya takeyi kamar tana magana da wasu.
[27/06, 3:48 pm] Mom Islam Ce💃: 31 & 32

Jitayi ance waye ya baki izinin fitowa waje ? sanin mai muryar ya sata juyo da kanta gareshi tace " waye mai bani izini ? zaki tashi ki wuce kokuma kinaso ranki ya ɓaci ? tuno nasihar momy ya sata miƙewa ta nufi ciki ranta a ɓace kamar zatayi kuka , bata tsaya a palo ba ta wuce bedroom ɗinta tana mita tare da sawa ƙofar key.
Shirin fita yayi batare da ya waiwayi Diyana ba , motar da ya dawo da ita ya shiga tare da ficewa da gudu yahau titi , direct gidan abokinsa ya nufa da rabonsu da haɗuwa tun bikinsa sai dai suna haɗuwa a waya , yayi tafiya mai nisa ya iso anguwar mai suna gadon ƙaya , wani ƙerarren gida naga ya nufa tare da yin horn , cikin sa'a driver ya buɗe get ɗin tare da ɗagawa Kamill hannu yana cewa " barka da zuwa Alhaji , cikin isa Kamill ke amsa gaisuwar tare da ƙarasawa ciki yana parkin abokin nasa ya fito mai suna Abubakar oyoyo my ango na amarya suka kwashe da dariya , riƙe masa hanunsa Abubakar yayi suka nufi cikin gidan , wani rantsatsen palo naga sun shiga bazan ce yafi na Kamill haɗuwa ba amma shima wanan ƙarshe ne gurin kyau , kujera Abubakar ya nuna wa Kamill tare da cewa " barin kirawo amarya ku gaisa , mirmishi Kamill yayi tare da maida hankalinsa kan waya , ɗago kan da zaiyi yaga Abubakar tare da amaryarsa Safeena tana ɗauke da ciki , hakan ba ƙaramin birgeshi sukayi ba sai yaji inama ace Diyana ce da cikinnan da yafi kowa jin daɗi , kawar da kansa yayi ba tare da ya bari sun gano komai ba ,Kamill ga amarya fa , dariya Kamill yasa kana yace " amarya munkusa zuwa shan suna Allah ya ƙara lafiya , kan Safeena a sunkuye ta gaida Kamill ta tambayi matarsa cikin sakin fuska yace " lafiyanta lau tace " a gaisheki , ina amsawa Safeena tace " tare da miƙewa ta janyo table tafara jerawa Kamill kayan motsa baki , taje fridge ɗauko drinks har kala hudu Abubakar ya miƙe da gudu ya rungumota tare da raɗa mata a kunne karfa ki wahalar min da baby dan zanyi miki hukunci my honey kashe masa ido tayi ta raɗa masa a hankali abokinka na kalonka ko bakajin kunyarsa ?" juyawa Abubakar yayi bayan ya karɓi kayan hanun Safeena ya isa gurin Kamill da duk abinda sukeyi yana kan idon sa , ango ayi mana haƙuri fa , dariya Kamill yakuma sawa kana yace" kuyi dai ku gama baby na kallonku , suka tuntsure da dariya , komawa ɗaki Safeena tayi ta bar musu gurin sbda tsaro , abokina naji daɗin ganin zamanku cikin kwanciyar hankali , Kamill ya faɗa tare da dafa Abubakar , kana yakuma yi shiru .
Kallonsa Abubakar yayi cikin fahimta da karantar yanda walwalar fuskarsa ta sauya lokaci guda , matsowa Abubakar yayi kana yace "karka ɓoye min komai game da zamanku da matarka dan yanayin ka ya nuna baka cikin farinciki , gashi maimakon da kayi aure kayi ƙiba kayi kyau kawai sai naga akasin hakan ko lafiya ? Abubakar ya tambayi Kamil ,hmm Kamill yace " wato Abbak sunan da Kamill ke kiransa kenan tun suna yara kasancewar iyayensu ƙawaye ne haka iyayensu maza ma abokai ne , Kamill yace " tunda muke da Diyana ban taɓa sanin daɗin aure ba , haka bama zaman lafiya ko kaɗan bugu da ƙari banama kulata , buɗe baki Abubakar yayi cikin mamaki yace " yau watanku ɗaya da kwana biyu amma haka kuke zaman doya da manja ? dana sani da haka bata faru ba tun farko gaskiya dan lefin yana gurinka inda ka tafi da ita haka zaku zauna so inason kasan a rayuwa babu abinda yafi aure daɗi da sanya kwanciyar hankali , ba auran soyayya kukayi ba ? Abubakar ya tambayi Kamill . cewa" Kamill yayi gaskiya ba auran soyayya mukayi ba sbda wani lefi da tayimin shi ya sanya na aureta dan na rama ta gane kurenta , amma badan haka ba ni banida larabar yin aure yanzu , innalilahi Abubakar yace " tare da tafa hannu yanzu abokina har kayi hankalin da zaka wulaƙanta mace gaskiya da sake , inhar kanaso kaji daɗin aure dole ka koya mata soyayya zallah ,kwashe labarin gurin bikin da suka haɗu da Diyana yayi ya gayawa Abubakar tare da cewa nifa banison raini wlh badan bazan iya riƙe mata biyu ba da aure zanyi ni bazan iya ɗaukar raini ba kamata ace ina bin mace taɓɓ , murmishi Abubakar yayi kana yace " ai dole mubi mata tunda sune iyayenmu kuma abin jan raini da kake faɗa yanzu ai zamanku ma zai sa ta koyi rashin kunya sosai ma , tunda baka jata a jikinka ba dole sai ka sauke girman kannan inhar kanason farinciki , kuma maganar fansa ka ajiyeta a gefe ka rungumi matarka kuyi zaman lafiya Kamill.
Jinjina kai Kamill yayi yanajin abin kamar tatsuniya Abubakar ya fahimci duk mganar dayayi batayi tasiri a kansa ba dan haka yace " kadai bi a hankali wlh kar daga baya kazo kana dana sani , babu wani dana sani da zanyi abokina kadai tayani da adu'a Allah ya saka min auran mata biyu wanan ba ajina bace ksancewar babanta ma talaka ne , zaro ido Abubakar yayi yana mamakin raina talaka da sukeyi amma ba abin mamaki bane dan Kamill baisan menene talauci ba tun tashinsa bare yanzu da inyaga dama yakan leƙa ofisoshin mahaifinsa amma baya aikin komai iyakaci yadinga jin alart ta waya koda wane lokaci , Kamill har yanzu baka ma fahimci me nake cewa " ba shi so kokuma zaman soyayya anayi da almajira ma sai tafi wata ƴar mai kuɗin iya kula da miji bare matarka mahaifinta nada arziki dai dai gwargwado , dariya Kamill yasa kana yace " to ni mema zance menene soyayyar caɓ akwai aiki gaskiya.
Babu wani aiki sai dai inhar kai ka maida abin aiki amma inkabi shawara ta to zaka zauna lafiya kuma zaka gode min , shafa sajensa Kamill yayi tare da cewa " zan gwada barin wuce kasa amarya ta gudu ɗaki , dariya Abubakar yayi kana yace " ok muje in rakaka mota suka fice sunata hirar maganar gidan Kamill .
Kamill na shiga mota Abubakar ya koma gida shikuma aka buɗe masa get ya fita , gidansu ya zarce sbda ya kira mahaifinsa yana nan , da shigarsa ya samu anata rabon abinci kasancewar al'adar gidan ne hakan in wata yayi nisa , kowa sai gaisuwa yake miƙo masa daya gaji da amsawa ya ƙyalesu a gurin , palon mahaifin nasa ya ƙule inda ya samesa kishingiɗe a kan gado da jarida a hanunsa, da sallama ya shiga ya nemi kujera mai zaman mutum ɗaya ya zauna tare da ɗan rusunawa yace " barka da yamma Abba ya jama'a , lafiya lau Abban yace " tare da kai dubansa ga fuskar Kamill my son , Abba yace " har yanzu bai dena kallonsa ba . na'am Abba , yanaga kabi ka rame menene matsalar dafatan dai gidanka babu damuwa dan na tabbatar da yarinyar tanada hankali dakuma tarbiya , babu komai Abba Kamill ya faɗa tare da ƙaƙalo fara'a a fuskarsa , to amma wane tunani kakeyi da ya sanyaka rama ? wlh Abba ba komai badan Abban ya yarda ba ya ƙyakeshi , kaje ka gaida mamanka kuwa , haɗe fuska yayi kana yace " tana ciki ne ? eh Abban yace " ka gaisheta kazo ina son ganinka jiya dana dawo na taho muku da tsaraba kai da matarka , tom Abba Kamill yace " ya nufi cikin gidan , samunta yayi a babban palo tana riƙe da remote a hanunta gefe kuma Apple ne take ci kamar mara lafiya a yanayin taunar da take yimasa , sallama yayi kana ya nemi kujera ya zauna bai jira amsawarta ba yace " barka da yamma ya jama'a lafiya Ameena tace " tare da yanƙare baki gefe , miƙewa Kamill.
[28/06, 3:39 pm] Mom Islam Ce💃: 33 & 34

Miƙewa yayi tare da barin gurin ya koma palon Abba inda sabo ya saba hakan sam baya damunsa tunda haka ya taso tun yana ƙarami Abbansa kawai ya sani mai yi masa gata gashi ya taso cikin nera amma babu wulaƙancin da bai sha a gurin Ameena ba , hasali ma yana zarginta da kisan mahaifiyarsa , dare ɗaya ta kwanta ciwo a ranar kafin hakan bazai taɓa mantawa ba dan duk da yana yaro bai hanashi mugun wayo ba wata kalma da ta tsaya masa a rai itace " lokacin yana ƙarami yazo wucewa ta saitin ƙofar Ameena zashi ɗakin mahaifiyarsa yaji suna hira ita da ƙawayenta suna cewa ki sanya mata abinda boka ya baki man , mamansa na mutuwa ya laƙawa Ameena amma har yau bai bari kowa yaji ba , tayu ƙoƙari rabashi da ubansa Allah baiyi ba haka ta haƙura da cutar baƙin cikinta , koda Kamill ya koma ɗakin Abbansa kaya ya gani zube a kan gado ƙarasowa yayi kana yace " Abba wanan kayan fa ? nakune yaron kirki kai da matarka , indian fation ne masu kyau dakuma parkistan riga da wando harya hango irin kyan da Diyana zatayi a cikin wanan kayan , ya kayi shiru my son ? Abba ya jefo masa tambayar kunya ce ta kamasa dan kayan Diyana ne a hanunsa yanata jujuyawa , mungode Abba Allah ya ƙara lafiya da nisan kwana , zan koma Abba , murmishin su na manya Abba yayi tare da cewa to a gaida ƴar tawa insha Allah Abba Kamill yace " kana ya fice ya nufi motarsa kasancewar kwana biyunnan kan yayi zafi ba'a batun dreba ma .

Bashi ya isa gida ba sai da ya tsaya a masallaci yayi sallahar isha'i kana ya wuce gida yana parkin ya shige babu kowa a palo sai tashin ƙamshi yakeyi , kai tsaye ɗakinta ya nufa tana zaune a bakin gado da waya a hanunta tayi wanka ta haɗe cikin shadda blue taji ɗinki mai kyau ga wata sarƙa mai walwali da ta sanya a wuyanta , aslamu alaikum , yi tayi kamar bazata amsa ba sanin darajar amsa sallama ya sata amsawa ko kallon inda yake batayi ba , bare yasa ran zatayi masa magana , sannu da hutaww Kamill yace " da sa, sanyar muryarsa yawwa sannu , daga haka ta miƙe tabi lafiyar gado , wata zuciyar ce tace " ka bita kawai gashi ta nuna maka abinda take so , wata zuciyar kuma tace " karfa ka jawa kanka raini dan inbaka man taba ƴan mata nawa ne a waje suke sonka ƴaƴan manya baka sauraresu ba , tuno nasihar Abubakar yayi da yace " dole ka bita ahankali dakuma nuna soyayya , toshi kam yarasa ma menene soyayyar kasancewar shi ba ma'abocin shirme bane dan ya ɗauki soyayya ahirme shikam amma wai gashi yau shine yake yiwa mace magana take ƙin kulasa taɓɓ akwa aiki , ɗaga waya yayi ya kira mai gadi tare da cewa ya buɗe bayan motarsa ya ɗibo masa kaya angama mai gadi yace " ya ruga da gudu zuwa inda aka aikeshi shikuma ya kashe wayar , bubuga ƙofar da yaji ne ya sashi miƙewa ya karɓo kayan ya dawo ya zauna yana cigaba da kallon Diyana da tayi kamar mai jin bacci , yakai waje 30 mins a haka ganin babu sarki sai Allah ya sashi barin ledar a gurin ya fice daga ɗakin ya nufi nasa , kwanciya yayi a kan bed yana mamakin kansa wai shine yabi mace , tab gaskiya Abbak yana neman badasa a gurin wanan yarinyar wai kuma a cewarsa ta haka ne bazata rainasa ba , to gashi tun yau an fara shikam yanajin bazai iya cigaba da binta ba gaskiya , gara ko ciwon mararshi ce ta motsa yasha magani uban me ma zai samu a gunta banda yarinta lol sai surutansa yake kamar zautacce , bayan ya gama ya cire kayan jikinsa ya shige toilet ya watsa ruwa , yana shirin kwanciya yaji yunwa ta taso masa babu shiri ya miƙe ya nufi palonsa ya buɗe fridge ya ɗauki malte yasha kana ya dawo bedroom ya kwanta da tunani iri iri bacci ya kwashesa .
Itama Diyana wanan kwanciyar da tayi batasan lokacin da bacci yayi gaba da ita ba sai farkawa tayi taga agogo ƙarfe huɗu , miƙewa tayi tare da ɗauro alwalah ta tada sallah , nafiloli tayi tana cikin yi taji ankira asbha bayan ta idar ta tada sallahar farilla tana idarwa tabi gado ta kwanta tanajin kewar momynta , wani lokacin d share hawaye gashi Kamill yaƙi kaita gidan batasan da wace irin murya zata yi masa magana ya amsa mata ba.
Washe gari da safe misalin 7:am ya shirya cikin pink ɗin yadi mai laushi kana mai tsadar gaske bayan ya gama shafa mayukansa masu ƙamshi ya sanya hula a kansa ya feshe jikinsa da turaruka masu ƙamshi ya kwashi wayoyinsa da keys ya fito , kai tsaye bedroom ɗin Diyana ya nufa yana shirin buɗe door yaji wayarsa na ring dawowa yayi da baya ya amsa wayar , jinayi yace " Abbak ya gida ya kuma mom twins ?lapiya naji Abubakar yace " can kuma ya jefowa Kamill tambaya , an dace kuwa ? ko ɗaya Kamill yace " nifa nakasa shawo kanta pls i need your help , ka temaka yanzu dai abinda nakeso da kai shine karka gajiya dan dole zakasha wuya kafin aci nasara abokina , sallama sukayi Kamill ya shige bedroom ɗin , samunta yayi da cup a hannu tanata juya cokali da ruwan shayi a ciki ko madara babu gashi fuskarta ta jiƙe da hawaye , innalilahi Kamill yace " a fili tare da ƙarasawa gurin da take zaune dama inhar tana bedroom gurin zamanta baya wuce bakin bed , zama yayi kusa da ita kana ya rungumota yafara shafa kanta a hankali alamar rarrashi , am sorry my baby insha Allah wani abu bazai ƙara faruwa ba a tsakaninmu dan Allah ki tausaya min yanayi yana shafa gashin kanta da yayi luf ya kusan rufe mata fuska , batayi ƙoƙarin hanashi ba sai ma wani marayan kuka da ta saki sbda tuno kwanaki da zaiyi baƙi yayi mata wayo dan karsu gano meke faruwa tsakaninsu, ya salam Kamil yace " lokacin daya ɗauketa cak ya ɗora kan jinyarsa , baki haƙura ba kenan? wlh kinji na rantse bazan ƙara wulaƙantaki ba na gano kuskurena mu gyara zaman auranmu pls my Diya , lumshe ido Diyana tayi, kana tace " ka daɗe kana wanan kalamin halan yau ma baƙi za'ayi shine ake lallami na , murmishin yaƙe Kamil yayi kana yace " yau babu wanda zai zo kawai inason gina farinciki ne a jikin gidana , rungumeshi tayi tana kuka mai ban tausayi shima ƙara matseta yayi a jikinsa yana jin sonta tana bin kowacce gaɓa ta jikinsa , gyara mata zama yayi tare da kashe mata ido yace " my Diya me zaki samomin insa a cikina dan yau da wuri nakejin yunwa , lumshe ido tayi kamar mai jin bacci tace " mai kake so muje mu dafa dan yau dole ka shiga kitchen , kamo hanunta yayi suka fito zuwa kitchen fuskokinsu cike da farinciki, doya ta ɗauko ta miƙa masa da wuƙa tace " ga naka aikin babu musu ya karɓa suka fara aikace ai kace , yam balls sukayi dakuma wainar kwai tare da yin zobo wanda yaji cocumber da flevor da abarba , kichen ɗin sai ƙamshi yake zubawa , suna gamawa Diyana tayi wanke wanke shikuma Kamill ya goge gurin , ɗaukar abincin sukayi tare da nufar dining Kamill da jug a hanunsa ita kuma Diyana hanunta ɗauke da foodflaks suna shirin kaiwa dining sukaji sallama , da ganin mai sallamar Kamill ya ɗauke kai , Diyana batasan ko waye ba hakan yasa ta amsa sallamar tare da yimata umarni da nuna gurin zama.
[29/06, 4:45 pm] Mom Islam Ce💃: 35 & 36

Yatsina fuska tayi ta zauna tare da ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya shidai Kamill bai kalli inda take ba sai ma kawar da kai dayayi yace " ina yini , Hajiya Ameena na karkaɗa ƙafa tace " lafiya amma kaji kunya haka ka koma ?ina isar taka da rashin kunya yanzu mace ce mai juyaka koda yake babu mamaki haka uwarka tayiwa mahaifinka , yanzu Diyana tafara gano ko wacece Hajiya Ameena , cikin zafin nama ya isa gabanta da shirin wanketa da mari Diyana ta riƙe masa hannu tare da durƙusawa tana hawaye tace " inba ban faɗa dai dai ba wanan ɗin uwa ce a gurinka kome zatace karka fara yimata rashin biyayya , zuciyar Kamill tafasa take dan wanan matar ta kaishi maƙura tabbas wataran zai illata ta tunda ta tako har gidansa take zagin mahaifiyarsa da take kwnce a kabari , barshi ya mareni indai rashin tarbiya ne ai ya saba wlh kinyi kuskure da kika auri ɗan wahala , mai maitawa Diyana tayi cikin zuciyarta ɗan wahala kuma ? wucewa ɗaki tayi da gudu dan kuka yaci ƙarfinta , tana zuwa ta faɗa gado tare da sakin sabon kuka shin wanan matar tazo tarwatsa mata aure ne kokuma so takeyi ta kaita ta baro inko haka ne kota ƙara zuwa bazataje gaisheta ba , hankalin Kamill a tashe ya nuawa Hajiya Ameena ƙofa tare da cewa " kifita tunda ba gidanki bane , kutumar uba Hajiya ameena tace" tana haki kamar mai shirin dambe , bazan fita ba kasa a fitar dani banza marar tarbiya kawai , ganin batada alamar fita yasa Kamill danna lambar Abba ring ɗaya Abba ya ɗaga amma Kamill bai bari tasan kira yayi ba , cigaba yayi da cewa zansa a fitar dake , kalmar da Abba yaji ne yasashi cewa kai da waye Kamill , Kamill baiyi magana ba maganar da Abba yaji itace " kayi asara da ka ɗauki halin tsiya agun uwarka , idanun Kamill cike da hawaye yace " Abba wanan Ameena ce fa har gidana tazo take zagin mahaifiyata a gaban mata ta , innalilahi Abba yace " ku jirani dukkan ku ganinan zuwa dama jiya mukazo Abuja nida Ameenan yau ta cemin zata gidan ƙawarta ashe nan zatazo , Abba ne yasa drivern sa ya juyo da mota zuwa anguwarsu Kamill , drivern na yin horn aka buɗe get ya shige ajiye motar yayi a parking spice drivern na shirin buɗewa Abba mota cikin azama Abba harya buɗe ya fito , Ameena dake ruwan bala'i tana cewa aure ka keso ka kashemin to wlh ta Allah ba taka ba , karaf a kunnen Abba yace " ai naji komai ya ƙarasa shigowa yana yimata kallon banza, tsabar masifarki kin biyo ɗana har gidan sa kina ci masa mutunci a gaban matarsa to wlh bazai yuwu ba kuma bazan lamunta ba naji duk wani abu da kike faɗi Kamill , Abba ya kira sunansa , kiramin matarka da sauri Kamill ya nufi bedroom ɗinta yana tura ƙofa ya sameta zaune kan stool ta kifa kai da guwaiwa tana gursheƙen kuka , rungumota Kamill yayi tare da share mata hawayen yace " taso muje Abba ya zo yanzu kuma yana son ganinki , miƙewa tayi ta zura hijab har ƙasa tabi bayan Kamill daya rigata wucewa , samun Abba tayi zaune kan kujera samun guri tayi a ƙasa kan kafet ta zauna tare da sunkuyar da kai kasa

Please Login or Register in order to submit comment