Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tanata zaro ido cikin fuskar nan jin fitsari yana ɗiga ta gefe yasa Diyana cewa , shine aka jiƙa mana ƴaƴanmu to tun wuri ki kwashe shi kokuma yanzu mu tafi dake ƙasarmu , Hajiya na kuka tana tsane fitsari da zaninta sbda akwai sikel ɗin ciki a jikinta , tagumi ta zuba tana magana , duk inda naje sai kun biyoni?" a 'garin namu ma baku barni ba ,haka anan ma bazaku barni ba ?" .
Hajiya tasa kuka tace " wlh kakanmu ya cucemu da yabar mana gadon aljanu wayoo mun higa uku , nanfa Diyana da Afreeda suka fara kwasar rawa suna takawa kai kace aljanun gaske ,
Jiyo tari sukayi ta gefen Tinene , Afreeda ce ta ƙarasa gurin tace " idan baki tashi ba saimun maidaki akuya , ai da gudu ta miƙe jiki na rawa kan kace me ji kake ɓirrr tana shirin sake musu kashi ,
Waro ido Diyana tayi tace " kifito kizo yanzu birnin mu zamu kaiku ,
Cikin azama Hajiya ta sakko ta durƙusa gaban Afreeda kasancewar tafijin tsoron teddyn hanunta , tace " kuyi haƙuri yarinya ce batasan komai ba kuyi mata aikin gafara dan Allah , nasanku kunfimu haƙuri to ku ƙara , Afreeda ce ta kece da dariya marar sauti sosai ta dubi Hajiya da ta jiƙe da zufa dakuma hawaye , jitayi tausayinta ya shigeta ta dubi Diyana tafara yimata wani irin yare , gani nayi Diyana ta girgiza kai alamar a'a .
Matsowa Diyana tayi tace " nan ɗakin na uban ubanmu ne yatafi misira kuma yabamu ajiyarsa to kufice kokuwa musa a ɗagaku sama ,
Tinene da taƙi fitowa daga bayi , Afreeda ta ƙwanƙwasa ƙofar tace " kigama muna jiranki, ku bakwa ganin mutane a gefenku a kwance zaku shigo mana ɗaki koku bar wanan ɗakin ko gidan gaba ɗaya kokuma mu ɓatar daku daga duniyar .....! kafin su ƙarasa magana Hajiya ta buɗe bayi ta janyo Tinene dake tsaye babu ko wando kasancewar in zatayi kashi saita cire wando , suka nufi palo babu ko magana,
Tafawa sukayi Afreeda tace " zamu gudu , raɓawa sukayi ta gefe suka wuce batare da kowa ya gansu ba , dama momy na can sama sukuma suna ƙasa ,
Suna shiga bedroom ɗinsu suka fara tsalle sunata dariya ,
Duba wayarta Diyana tayi lokacin ƙarfe biyu da rabi na dare, kowacce ta nemi gurin kwanciya asuba ta gari.
Washe gari da safe kowa na gidan na bacci kasancewar weekend ne sai shaɗaya 11am suke breakfast,
Tun shida Hajiya ta tashi taje ɗakin Nana mai aiki ta tasota ,
Sata ɗora ruwa tayi da abinci , babu shiri tafara kiciniyar abinda Hajiya ta sakata ,
Da farko dai ruwan wanka aka miƙowa Hajiya cikin sauri ta karɓa tana sakawa Nana albarka , tashin Tinene tayi tazo tayi wanka yau a garinsu zasu kwana , Tinene dake bacci mai daɗi cikin bacci , tace "Kaka ni kibarni nayi bacci kina ganin jiya gudawa tasani gaba , tsabar haushi da ya cika Hajiya tace " uban gudawa , dan uwaki ni zaki gayawa kinyi gudawa to tun wuri kitashi muje kiyi wanka , dan yau sai Shafa ƙauyenmu , a zabure Tinene ta miƙe ta riƙe ƙugu tace " wlh babu inda zani ,
Kaji kaka dai da wani zance , muna hyan hyayi da burodi kice mutafi to yasin ko dafani akeyi nan naga gurin zaman dan haka kima canza tunani ,
Riƙe baki Hajiya tayi tana tunanin kodai Tinene ta mance halin da suka shiga jiya take batun zama, to bara inje inyi wankan in fito wlh saikin bini bazakisa ubanki ya tambayeni ina kikaje ba ,
Wucewa Hajiya tayi ta nufi ɗakinsu da ya zame mata abin tsoro tashiga da adu'a tana cewa " wa innahu sulaimanu wa innahu bismillahir rahmanir rahim, tashige ta surka ruwan ,
Bayan tayi wanka ta fito ta , tattara kayanta a buhu ta shafa manta da farin kwali ta sanya kaya ta fito palo.
Baccin kuwa ta koma hankali kwance da mamaki inna ta hamɓareta tace " wlh kitahi kokuwa insa masu gadi su ɗaukeki , da sauri ta tashi tayi ɗakinsu , tana shiga aljanun jiya suka faɗo mata ihu tafara kurmawa tana ƙarawa , a na biyun ne ya tashi mutanen gidan dukansu da sauri momy ta fito tana tambayar lpy kuwa? Hajiya da yanzu take shirin shiga ɗakin dan tsoro ya hanata tace " leƙa kigani faɗimatu ko aljanu ne , aljanu kuma ? momy ta mai maita ,
Eh leƙata , Hajiya ta kasa taɓuka komai sai cewa leƙata, shiga momy tayi ta leƙa bedroom ɗin ganin tinene na wanka tana tsala ihu yasa momy shiga tafara tambayar anya lpy kuwa Tinene ? , nan ma hankalin Hajiya yakuma tashi taƙara tattaro kaya tana cewa wlh aljanu sun samu a gaba a gidannan , inna zuwa ƙauyenmu bazan sauka ko ina ba sai gidan malam fari ,dan wlh dole ya yimin istahara akan aljanun gidan Alhaji ,
Duk da nima na gidana basu barni ba dole naɗau mataki , momy dai jin hajiya takeyi dan ba abokiyar yinta bane ,
Amma su da basu taɓa jin hayaniyar komai ba amma ace wai gidansu da aljanu , kodai rikicin tsufanne ya motsa , to Allah ya daɗa karewa momy tace " ta fice , Diyan da Afreeda suna zaune a palo kowacce ranta fess Hajiya zatabar gida , amma basu nuna a fuskarsu ba ,
Ganinsu a palo yasa momy cewa " ku bakusan abinda ke faruwa bane ?" yamutsa fuska Diyana tayi tace " good morning momy , bata amsa ba sai ƙara jero musu tambayar taƙarayi ,
langwaɓar da kai Afreeda tayi kana tace " momy munji ihu ne mafa ya tashemu wlh "mai ya faru ne , kuje ku tambayi Hajiya , daganan momy tayi gaba ,
suna ganin momy ta wuce suka tafa suka miƙe kowacce ta koma gado ,
Ɓangaren Hajiya tagama shiri tsaf Tinene take jira , itama Tinenen tunda Hajiya tace mata inhar bata zo sun tafi ba to babu ruwanta ,
Ko ta mance da takarar da aljanun jiya sukayi na cewa zasu ɓatar damu , aikwa babu shiri Tinene jiki na tsuma tace " zan biki yasin bazan zauna ba ,
Amma fa zamuyi kewar ruwan hyayi mai madara ,
Ke dalla can marar tunani lafiyar mu tafi hyayi dan haka mutafi kawai , basa bibiyar ƴan gidan sai baƙi to dole na nemowa Alhaji magani wataran mutan gidan zasu nema ,
Nafito ina zaure kisameni a can , Tinene dake ɗaura zani tace " ganinan .

Kamill ne zaune a wata ƙayatacciyar kujera ita kanta kujerar abin kallo ce bare wanda ya zauna akan kujerar , dogo ne fari ,
yanada manyan idanu inka ganshi kamar balarabe ,
Gashin kannan nasa luf luf kamar wanda ake shafashi ga baƙin sajen da ya ɗan kewaye bakinsa yana ɗauke da pink lips ,
Yanayin jikinsa kaɗai ya ishi mai kallonsa yasan cewar kuɗi yazauna bai taɓa neman abu ya rasa ba ,
idan kuɗi yakasa samar masa yakan sa basira ,
Idan basira ma bata samo masa ba yakansa ƙarfinsa domin ya mallaki abinda zuciyarsa takeso ,
iyayensa suna zaune a kano unguwa uku , gidansu ya fita daban da shauran gine gine amma shi ba mazauni bane, haka mahaifinsa Alhaji Safiyan gidan kuɗi baya rayuwa a Nigeria , kasancewar sa hamshaƙi , bare uban gayya wato Kamill .
Ɗai ɗai garin da bai mallaki gida ba saboda hutawa aure baya gabansa hakan yasa iyayensa zuba masa ido yakeyin abinda ranshi yakeso,
Juyi yayi a kujerar ya kalli bodyguard ɗin dake zagaye dashi yace " kun gano min gidan su wanan yarinyar ?" yes oga mun ganshi mahaifinta shine Alhaji Sani alherin Allah , buga ƙasa Kamill yayi tare da furzar da isa daga bakinsa ya katse mai maganar da cewa " wato ubanta bama kowa bane amma ta takani , to wlh bazan barta ba saina tozarta ta dole tayi hankali koda a gaba akace ta yiwa wani haka bazatayi ba ,
Miƙewa yayi ya nufi ciki daga bakin ƙofar flowers ne suketa haska ko ina , shiga yayi yana takunsa na ƙasaita ya zauna a kan wata fitinanniyar kujera ,wanan ɗaki na Kamill faɗar kyansa bazai rubutu ba,
Kasancewar ya tsaru shi kansa palon kai kace ɗakin mai mata ne , ga wani ƙamshi dake tasowa ta jikin wasu flawoyi dake manne a bango, ɗaukar apple ya ɗauka yakai bakinsa , kaɗan ya gutsura ya ajiye tare da cewa , natsaneki!!!!.
Ya riƙe kansa dake yimasa wani irin ciwo kasancewar sa inhar yasa damuwa a ransa to sai yayi zazzaɓi ,
wanan karon ma hakan ce zata faru ,
tashi ɗaya jikinsa yai zafi , babu inda ya iya bare ya kira bodyguard ɗin nasa su temaka masa sbda ya hanasu shiga part ɗinsa muddin ba shine ya turosu ba ,
Baccin wahala ne ya ɗaukesa sai wajen ƙarfe uku na rana ya farka ,
Jikin yayi masa sauƙi sosai miƙewa yayi ya zauna kan bed tare da janyo bed side ya ciro maganinsa ya ɗauki ruwa a fridge yasha ,
Jin wayarsa na ring ya dawo kan kujera ya ɗauki wayar , cikin muryar tasa da duk wanda yasansa yasan babu lafiya , yace " Aslamu Alaikum Abba .
Wa'alaikumussalam ɗan albarka ya kake , Kamill ne yace " lpy lou Abba yaushe zaka dawo ?" gobe insha Allah mai kakeso ?" dariya Kamill yasa kana yace " Abba akwai kyakyawan albishir wlh Allah dai ya dawo dakai lafiya , kodai mafarkina na ne zai tabbata zan sami suruka , dariya kamill yayi yace " saidai kazo ɗin sukayi sallama ya kashe wayar.

Hoton fuskar Diyana ne keyi masa yawo da wata shu'umar dariya yayi ya miƙe toilet ya nufa ya ɗauro alwala yafito domin zuwa masallaci.
Da wani buhu Tinene ta fito da alamu buhun kayansu ne , Nana tazo wucewa Hajiya ta kirata , durƙusawa tayi tace " gani hajiya ,
Hajiya dake mamular goro tace " ina abincin namu ?" da sauri Nana ta miƙe tanufi kitchen ta fito da shinkafa , da cokula guda biyu dakuma faranti ,
Bajeshi Hajiya tayi, suka fara ci jin abincin yayi daɗi Tinene ta turo baki tafara shura ƙafa tana cewa" gaskiya kaka inhar na yarda na biki to yasin nayi asara ,
Innalilahi bina hine asara?"
Ƙara kai lomar shinkafa Tinene tayi tana cewa wanan ai hine kaga samu kaga rahi any zan iya bin Kaka kuwa ,
11am momy da iyalanta sun hallara a dining yau kam sun gaishe da Hajiya , breakfast momy da Afreeda sukeyi banda Diyana da ruwan lifton takesha sai juya cokali takeyi a ciki alamar akwai abinda ke damunta, babu wanda ya kulata ,
Wayar momy ce tafara ring ganin sunan dady yasata ɗagawa tare da gaisuwa ,
Ganinan shigowa ma ina bakin get , masha Allah momy tace " Allah ya shigo dakai lafiya ,
Hajiya da ɗan ƙullin buhunta da Tinene suna zaune ,
Sukaji sallamar Alhaji ,
Washe baki Hajiya tayi tace " hannu dai Alhaji ,
ywwa Hajiya munsame ku lafiya ?
Lpy lou Hajiya tace " tana daɗa gyara ɗaurin bakin buhunta ,
Hajiya mekuma muka samu ?"
Diyana da Afreeda ne suka karɓe zancen da cewa barka da dawowa dady , kafin ya amsa Hajiya tace " gida zan wuce bazan ƙara kwana a gidanka ba kaji na gaya maka ,
Sunkuyar da kai momy tayi dan wanan al amarin yafi ƙarfinta da tana ganin abin kamar wasa yanzu ya wuce tunaninta , gara taja bakinta tayi shiru inyaso insun gama ta tofa nata ,
Gyara zama dady yayi yace " Hajiya kina nufin wai ƙauye zaki koma ?" eh Hajiya tace "
maiya faru da zaki ɗago tafiya haka yanzu da bayau zan dawo ba sai dai inji ta tafi kenan , Hajiya ce ta nuna momy tace" laifin matarka ni babu ruwana ehe tafiya zanyi gidanka duk aljanu hatta ɗakin da muke ma saida suka jamana kunne ,
Miƙewa tayi tare da janyo hanun Tinene tace " tahi karmuyi dare, momy da sai yanzu tayi magana tace " kayi haƙuri dan Allah ,
Da' na ɗauka ba tafiyar zatayi ba , shiyasa ban gaya maka ba .
Hanyar fita Hajiya take shirin yi dady yasha gabanta tare da durƙusawa yace " Hajiya dan girman Allah kiyi haƙuri ki zauna babu komai a gidannan ,
Zan kira ayiwa gidan sauka yau ɗinnan dan Allah karki tafi ,
Tausayi ɗa da uwa Hajiya ta juyo ta zauna kan kujera tana cewa " to wlh tun wuri ka kira malamin dan jiya a rumfa muka kwana ,
Dady baiji daɗi ba sam amma baice komai ba ,
Sama ya haura zuciyarsa babu daɗi ,
Bin bayansa momy tayi tana jiran abinda zai biyi baya ,
Salama tayi ta samesa yana cire maɓallin rigarsa ,
Ciki ciki dady ya amsa bai ko kalleta ba ,
Zama momy tayi a gabansa tare da janyo hannayensa ta zaunar dashi ,
haba mijina mai nayi da zakayi fushi dani ?"
Inhar maganar Hajiya ne to kayi haƙuri naɗauki lefin dan girman Allah ,
duk da haka bai kulata ba saima shirin shiga toilet ɗin ɗakinsa daya fara yi ,
Da sauri momy taje ta tara masa ruwan wanka ta tsaya a toilet ɗin tana jiran shigowarsa , tasan mulki da isa irin tasa ,
Har ace gadon wa Diyana tayi hmm , momy taji shiru bai shigo ba ,
tana fitowa ta samesa a zaune yayi shiru yana bubuga ƙafa,
ɗumin hawayen da yaji ne yasa shi ɗago fuska a razane yace " Faty maiya faru , cikin kukan kissa momy tace " nabaka haƙuri kaƙi saurarata kasan bana jurar ɓacin ranka ,
Janyota yayi jikinsa yafara shafa gashin kanta alamar tayi shiru , bakya girma ,
Dady yace " yana murmishi , itama murmishin tayi tace " to kaima ɗin haka ne ,
miƙewa dady yai yace " zoki taimaka min inyi wanka idan na kintsa inason muyi magana dake ,
Miƙewa momy tayi daga kan cinyar dady ta riƙo masa hannu suka nufi toilet ,
Diyana da Afreeda ne a ɗaki kowacce na baƙin cikin dawowar Hajiya gidan , gaskiya dama Allah bai dawo dady yau ba da sunji daɗi ,
Diyana da abin duniya yataru yayi mata yawa tace " kiji ɗazu wai laifin momy take cewa ?" Afreeda ce ta cire tagumin fuskarta tace " ai wlh tadinga haɗa momy da dady faɗa kenan tunda bakinta bashida zip .
Haka dai suka dinga jajantawa gashi sun rasa mafita da zasu ɓullowa lamarin.

Yau Alhaji Safiyan ya sauka a Nigeria bai sanarwa kowa ya sauka ba sai drivern sa , kai tsaye daga airport unguwa uku aka wuce dashi wato gidansa ,
tun daga bakin get bodyguard keyi masa barka har yakai ga shiga cikin gidan ,
Hajiya Amina dake zaune a kujera wata dattijuwar mata tana mammatsa mata ƙafa ta miƙe , tana murmishi tare da cewa " barka Alhaji dawowa babu sanarwa ,
Alhaji ne yace " banda abinki Meena wanan karon nefa ban sanar miki ba to ayi haƙuri , sukasa dariya dukkansu ,
Tunda ma'aikatan gidan sukaga shigowar Alhaji kowacce tashe kitchen mai girki nayi mai haɗa lemo nayi mai farfesu kifi nayi mai farfesun kaji nayi abinci dai kala kala kowacce ta kama dama ƙa'idar gidan kenen ,
Amina ce tace " Alhaji tashi muje kayi wanka sai kaci abinci ,
Babu musu ya miƙe amma a zahiri burinsa yaga Kamill ,
Bayan yayi wanka yai shigar alfarma ya fito shida Ameena suka nufi dining da masu aiki suka cikashi da kayan ciye ciye dakuma abinci masu lafiya ,
jollof ɗin shinkafa Ameena ta nunawa Alhaji tana dariya tana cewa " alhaji ga abinda kakeso yaji kayan lambu ,
Alhaji dake daddana waya yace " zubamin kisamin farfesun kifi a gefe,
Bayan dady yaga cin abinci ya tambayi Kamill ,
yamutsa Fuska Ameena tayi tace " rabona da insashi a ido 3 weeks kenan ,
Jinjina kai Alhaji yayi batare da yace " komai ba ya miƙe ya fice direct ɗakinsa ya nufa ya kwaso wayoyinsa ,ya danna lambar Kamill , ring ɗaya ya ɗauka tare da sallama , Alhaji na amsawa yace " kazo gida ina nemanka ,
Tom Abba harka iso ne ?"
Eh Abban yace " ya kashe waya .
bubuga ƙafa Kamill yashiga yi kamar ƙaramin yaro yana cewa " natsani zuwa gidannan wlh amma babu inda na iya dole na naje ,
wanka ya shiga ransa a ɓace ya fito ya zura jallabiya baƙa mai hula ,
ko shafa mai baiyi ba yafito riƙe da key a hanunsa ,bodyguard ɗinsa ne suka fara jero masa barka ,
Babu wanda ya kula driver ne ya fito da sauri yace " Alhaji wacce motar za'a ɗauko ,
wani mugun kallo kamill ya watsawa driver ,
Babu shiri driver yayi ta kansa , ma'aikatan gidanne suka fara gulma akan yanayin da uban gidansu ya tashi Allah yasa lafiya ,
Jin faɗuwar gaba ta tsanta masa yasa shi ambato innalilahi a rayuwarsa yatsani Amina shiyasa ko gidan baya son zuwa , Allah yasa ba wani bom ɗin ta haɗa masa ba a gurin Abba ,
Shiga wata mota yayi fara kyakyawa ya harba titi , tafiya yakeyi yana tunani yarasa dalilin faɗuwar gabansa ,
wani mahaukacin horn yayi sanin ko waye yasa masu gadi da kowa na gidan saita nutsuwarsa ,
Mai gadi na buɗewa Kamill ya shiga , daga bakin get ɗin yayi parking ya nufi ciki , duk yawan mutanen da suke miƙo masa gaisuwa bai kula kowa ba, ko sallama baiyi ba ya shiga palon , Ameena na zaune tana kallo a tv ta ɗago kai ta kalesa ta mayar da hankali ga tv .
Abba na ciki ?" Kamill yace " kana ya kawar da kansa gefe yayi ,
Ganin bazai sami amsa ba ya wuce ta bai ko ƙara kallon inda take ba ,tofa maiya haɗa Ameena da ɗanta ..
Yana shiga ya sami Abba zaune da laptop a hanunsa yana sanye da farin glass a fuskarsa ,
Cikin fara'a Abba ya ɗago kai yace " oyoyo my son ,
Barka dai Abba Kamill yace " yana neman gurin zama ,
Bayan sun gaisa da Abba shiru ya biyo baya na ƴan wasu mintuna , Kamill ne yafara dana sanin sanarwa da Abba , alƙawarin da yayi ,
Jin shiru yayi yawa Abba yace " to Kamill Abbanka ya dawo cike da farincikin son jin albishir ɗin da zakayi masa ,
Wata mumunar faɗuwar gaba ce takuma ziyartar Kamill zufa na keto masa ,
Cikin ransa yace " zan cuci kaina mai ya kaini gayawa Abba kuma inya faɗi magana baya sauyi , shafa sumar kansa yayi yace " am Abba dama dama...
Abba ne ya fahimci maganar tayiwa ɗan nasa nauyi ya murmusa yace"karka damu koma menene gayamin bakada matsala ko kaɗan ,
Kamill ne yace " Abba yarinya nagani ...
Ragowar maganar ta maƙale masa a maƙoshi , masha Allah Abba yace " yana faɗaɗa fara'arsa , Kamill ko sai yanzu yakeyin asalin dana sani sosai .
Ƴar gidan waye ?" Abba ya tambayi Kamill ,
Ƴar gidan Alhaji Sani alherin Allah ce , Abba ne ya ƙara murmusawa yace " haƙiƙa wanan rana nake jira naji daɗi sosai nayi farinciki , ai mutumuna ne shiɗin babu damuwa komai zai dai daita kaidai kaci gaba da nemanta insha Allah auranku zai zamo alkairi ,
Kan Kamill a sunkuye baice komai ba yanata nazarin maganar da ya yiwa Abba , nasiha Abba yashiga yimasa akan halin rayuwa , daga ƙarshe Abba yace" ka kiramin Amina ,
ɓata rai Kamill yayi yace " tafice daga gidan zan shigo naga tahau mota driver ya jata, what..! Abba yace " yaushe ta tambayeni dahar zata fita , oky jeka idan mukayi magana da uban yarinyar zan kiraka , tom Abba Kamill ya fice ranshi ta wani fannin fess wanan makirar zatasha faɗa , ya fice daga gidan ,
Yana shiga mota maganar da ya gayawa Abba dakuma farincikin da Abba yayi akan maganar auran ba ƙaramin ɗaga masa hankali yayi ba ,
Tabbas Diyana bata cikin jerin matan da yakeso , sbda ita ɗin batada kunya ga rashin sanin darajar mutane ,
" Gaskiya nayiwa kaina da zuciyata rashin adalci Kamill yaketa nana tawa kamar bitar karatu ,
ikon Allah ne ya kaisa gidansa , yana zuwa yayi horn ba'a ɗauki lokaci ba mai gadi ya buɗe get ɗin da gudu tare da durƙusawa yana miƙa gaisuwa , ɗabi'ar Kamill ne in ana gaishesa ƙin daraja mai gaishesa , basajin daɗin abinda uban gidan nasu yake yimusu , amma babu inda suka iya shiyasa suke taka tsan tsan da duk wani abu dazai haɗasu dashi .

bodyguard ɗinsa kuwa kowanne ya shiga tai tayinsa kasancewar oga baya wargi ,
Gashi yafita da ɓacin rai kuma ya dawo dashi .
Fitowa palo Alhaji Safiyan yayi , ganin Ameena na zaune tana danna waya , yasashi neman guri ya zauna , kana yace " meena yaushe zaki dena fita batare da izinina ba ?" waro ido Ameena tayi tace " ina zanje Alhaji ?"
Yanzu na aiko aka cemin kinfita a mota , buɗe baki tayi tasan babu mai yimata wannan sharin sai Kamill ,
Tarasa mai tayi masa ya ɗauki karan tsana ya ɗora mata ,
Hawaye ne suka fara zarya a fuskarta cikin she sheƙar kuka tace " Alhaji sai yaushe ne zaka dena kama maganar wanan yaron ,
Ina nake zuwa ?
Alhaji da ya ƙurawa fuskar Ameena ido yace " naji ya wuce amma kisanj Kamill ba yaro bane yakai time ɗin da zandinga shawara dashi so kin fahimta?"
Kawar da kanta gefe tayi dan intaci gaba da biye masa zasuyi babu daɗi '
Ita kuma batason musayar yawu da mijinta.
Bayan dady ya fito daga wanka momy ta temaka masa ya shafa mai ya sanya kaya , janyota yayi kusada shi suka zauna akan kujera ya kalleta yace " Faty mgnar da nakeson yi dake shine inason mahaifiyata ta zauna tare dani ,
Banison tayi nisa dani duk da akwai mai kula da ita a can ɗin ,nima inason samun nawa ladan , shafo kansa momy tayi kana tace " Habiby nima inason zaman Hajiya a gidannan ,
Ita da kanta ta matsa wai saita koma ƙauye tace " da aljanu a gidanan , nidai a iya sanina bansan dasu ba , amma bansan ko akwai ba .
Gyra zama dady yayi yace " ina tunanin harda rikicin tsufa .
Daganan suka miƙe tare momy ta kashewa dady ido tare da cewa , ga shayinka fa na shigo dashi , okay dady yace " ina zuwa yanzu zan dawo ya fice .
ƙasa ya sauƙo yana tunanin tafiyar mahaifiyarshi , samunsu yayi a palo zaune suna kallo ,
Zama dady yayi kana yace " barka da hutawa Hajiya ,
Ywwa barka Alhaji ya aikin naku ?"
Lpy lou dady yace " yana kallon Tinene da keta baza ido a tv " ke baki iya gaisuwa bane ?" sosa kai ta shigayi tana washe haƙora tace " hannu dai ina uni lpy dady yace " yana murmishi , ring ɗin wayarsa ce ta katse masa maganar da yakeson yi .
Ganin sunan mai kiran nasa yasa shi miƙewa da sauri ya haura steps zuwa ɗakinsa lokacin momy na toilet ɗinsa tana wankewa kasancewar bata yarda da ƴan aiki sudinga taɓa mata abinda ya shafi mijinta ba .
Zama yayi a bakin gado tare da amsa kiran ,
Sadda kai ƙasa yayi da alama da wani babban yake waya ,
dady ne yace " Allah ya temaki mai gida kuma Allah yaƙara maka lpy , daga can ɓangaren mutumin yace " wata muhimmiyar magana ce ta taso amma dole sai mun haɗu .
Cikin rawar jiki dady yace " to ko inzo me kawai ace kamarka ka shigo layinnan ,
NO. mutumin yace " karka damu dole nine zanzo buƙatar hakan ce ta taso karka damu.
Cikin rawar jiki dady yace " to da ƙarfe nawa zaka iso , mutuminne yace " bayan sallahar isha'i yayi ko ?" dady da fara'arsa yace " yayi Allah ya kawoka lpy ,
Sukayi sallama.
bayan dady ya ajiye wayar ne yafara tunanin mai zai kawo Alhaji....gidannan kodai yayi laifi ne , wata zuciyar tace "

Please Login or Register in order to submit comment