Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta katse wayar.
Iya ƙolokuwar ɓacin rai Kamill yayi wani uban ƙara yasa wanda yaja hankalin masu tsaronsa dakuma masu yimasa hidima , suka shigo da saur, lpy oga ? suka tambaya a tsorace , idanunsa sun kaɗa sunyi jawur ya kallesu kana yace " karku damu kowa ya koma gurin aikin sa zan nemeku anjima,
Haka suka fice jiki babu ƙwari dan kwana biyunnan basajin daɗin ganin shugaban nasu haka .
Yanzu burinsa kawai yaga ankawo masa Diyana a matsayin mata Allah ne kaɗai yasan hukuncin da zaiyi mata , Ya miƙe tare da zagaye ko ina na ɗakin ranshi a ɓace .
Biki ya ƙarato shiri akeyi na musamman fanin momy da dady dakuma fanin iyayen ango ,
satin Diyana ɗaya a gidan momyn Khady yau ta dawo gida , kowa ya ganta sai yai sha'awarta .
Momy ce ta jata zuwa ɗaki , Diyana . momy ta kira sunanta
Na 'am Diyana tace " momy ce tace " shi mijin naki ya taɓa kiranki kuwa ?" a'a momy .
Diyana tace " kanta a sunkuye , momy tace " bare har akai ga maganar kuɗin anko taɓɓ , Diyana dai batace komai ba taci gaba da wasa da gezar rigarta , fashewa da kuka momy tayi tana salati , wanan aure shine ake kira da auran dole.
shigowar dady ne yasa momy saurin share hawayenta ta ƙaƙalo murmishin ɗole , tace " barka da dawowa Alhaji , ywwa dady yace " ya nemi guri ya zauna ,
Kalon diyana yayi tare da cewa kibamu guri daughter.
Dama abinda takeson ji kenan dan zaman ɗakin ya isheta kasancewarta ba mai son yawan surutu ba ,
Tana shiga bedroom ɗinsu taga Afreeda a zaune tanata kuka ƙara tashi hankalinta yayi ,
Da sauri ta iso kusada ƙa nwar tata tayi ta rungumeta , meya faru ne my sis ? wani kukan Afreeda takuma saki tana cewa " sis yanzu kin yarda ki auri wanan mutumin sis tafiya zakiyi ki barni , hawaye masu zafi ne suka zubo daga fuskar Diyana ,
Takuma rungume Afreeda sunata kuka .

BAYAN KWANA BIYAR.

Zaune yake kan ƴayataccen bed ɗinsa da yaji tsadden zanin gado , idan nayiwa yarinyar nan haka banyi mata adalci ba koda yake ta wula ƙanta ni , amma duk da haka kamata yayi nayi ruwa biyu , sai tashigo in tada mata da GUGUWAR ZALUNCI na shi kaɗai yaketa zancen zuci , yaci gaba da cewa" iyayenta zasu fahimci wani abun fa...
janyo wayarsa yayi ya danna lambarta da yai seven da no. ring ɗaya ta ɗauka cikin sanyin murya , kwanciya yayi tare da cewa " barka da wanan lokacin ƴan mata , ywwa dawa nake magana , ƙara duba number tayi tanajin kamar ta gane mai muryar amma tarasa inda tasanshi , fatan masoyinki ne mijin da zaki aura , zatayi magana ya katseta da cewa " ayimin haƙuri nasan nayi laifi dahar saida lokacin bikinmu ya ƙarato nafara kira ,
Diyana da taji wani sanyi ya mamaye zuciyarta tace " babu komai karka damu ta lunshe ido kamar yana ganinta , janyo fillo Kamill yayi tare da rungumewa ya daɗa kashe murya , yace " ya shirye shiryen bikinmu ni yanzu burina inganki kusa dani saboda in nuna miki zallar soyayya dakuma farinciki , Diyana da tayi nisa cikin love ta gyara kwanciyarta dama a kujerar palo take kwance , batasan Hajiya na gefe a tsaye ba tun ɗazu .
Gaskiya nayi sa'a nima ina fatan hakan amma meye na zumuɗi , dole nayi sbda muryarki nasani bansan kyawunki ba koda yake inada tabbacin kyanki shima ƙarshe ne, dariya tasa marar sauti sosai tace " kaima hakan ai , to yanzu dai nawa kikeda buƙata sbda a halin yanzu zanbar ƙasar sai ana gobe ɗaurin aure zan dawo , cewar Kamill .
Lumshe ido Diyana tayi kana tace "duk abinda ka bada yayi .
Kamill ne yace " 3 hundred thousand yayi ? eh tace " cikin farin ciki .
sallama sukayi kana ta miƙe waigowar da zatayi sukayi ido biyu da Hajiya , ko kallon inda Hajiya take Diyana batayi ba , jiyo maganar Hajiya tayi tana cewa " gulma da ance ba'aso yanzu kuma anzo ana kwarkwasa , wucewa Diyana tayi zuwa bedroom ɗinsu batare da ta kula Hajiya ba jin son lovely ɗinta takeyi kamar zai fasa zuciyarta , shigowar Afreeda yasa Diyana faɗaɗa fara'a tace " sis yanzu my husband ya kiranj , murmishi Afreeda tayi cikin zuciyarta tace " hmm ƴar uwata har yanzu bakisan wa zaki aura ba ina tausaya miki dakinsan Kamill zaki aura nasan da kina nan kina rusa ihu inma ba'a kaiki asibiti ba da sauƙi , sis sis me kike tunani a firgice Afreeda ta waigo idanunta cike da hawaye tace " banason rabuwar mu my sis , Diyana dariya tasa tana cewa inajin kamar nafi kowa sa'a a duniya sbda mijin da Allah yai min zaɓi, hmm Afreeda tace " tare da kwanciya a gefen Diyana .
Kamill ya turo wa Diyana kuɗi , bayan ta ciro a p o s kasancewar yanzu bata cika zuwa bank ba , dama sunsi komai karɓar kuɗin momy tayi tabata 50k ta riƙe a hanunta , ƙanwar momy data zo daga kano ta tsarawa Diyana haɗaɗen lalle baƙi da ja , ga gyaran gashi da sukaje jiya , ɗinkuna akalla tayi sunkai kala ashirin kuma duba babu marar tsada .
a ƴan kwanakin nan tayi ƙiba saboda kulawar da take samu daga gurin Kamill , suna tsaka da waya yace " amma baxa'ayi wani event ba ko dan har yanzu ban dawo nigeria ba , my lovely babu abinda za'ayi karka damu cewar Diyana killer smile Kamill yayi yasan yafara sata a layi kafin ya goce ta .

*RANAR ƊAURIN AURE*
Da safe misalin ƙarfe bakwai ƴan uwan momy suka sata gaba wai gashi biki na ƴar fari amma babu wani wasa da akayi , momy da ta jiyosu tace " ku ƙyaleta karku damu Allah dai yabasu zaman haƙuri kowa ya amsa da amen .
Zuwa ƙarfe goma angama tsarawa Diyana kwaliya ta haɗe cikin material less mai tsada anyi mata ɗinkin riga da sikel ba ƙaramin kyau tayi ba ,
wasu magunguna aka dinga ɗura mata da turaruka momy da momyn Khady suka faɗa mata inda zatayi dasu ,
Zuwa sha ɗaya Kamill ya kirata ya sauka a garin kano , wani irin farinciki takeji na daban , iskar ma da take kaɗata ta ranar ta daban ce ,
[

A yau dubban mutane suka sheda ɗaurin auran Kamill Safiyan da amaryarsa Diyana Sani , ɗaurin auran da yasami halartar manyan mutane ta kowane ɓangare musamman ma ɓangaren mahaifin Kamill , kowa ya sanyawa auran Albarka , Kamill kam bai sanarwa yawancin abokansa ba a cewarsa wanan auren nasa auran hukunci ne sbda yanason tada GUGUWAR ZALUNCIN sa bayan amarya tazo , mahaifinsa duk bai fahimci hakan ba , kayan lefen da aka kawo gidansu Diyana ya girgiza mutane tabbas nera tayi kuka duk cikin kayan babu na 50k momy ma tasha mamaki amma ba'a mamaki da ikon Allah yasata jan bakinta tayi shiru .
Hajiya da tinene sunsha ɗinkin atamfa riga da zani suma ba ƙaramin kyau sukayi ba amma Tinene na gefen Hajiya bata bari tayi nisa da ita .
Bayan sallahar magrib Diyana da Afreeda na hango manne da juna sunata kuka kowacce idanunta fal da hawaye , momy da ta shigo kiran Diyana ta gansu a haka , itama kawar da kanta gefe tayi tana share hawayen daya zubo mata daughter kizo dadynku na nemanki , daga haka momy ta fice , sakin juna sukayi Diyana ta tafi kiran dady .
Da sallama ta shiga palon dady kanta a sunkuye , kallon tausayi dady yayi mata yasan tayi masa biyayya kuma shima yana son ya kwatanta kyautata mata ,
Dady gani , ywwa daughter abinda nakeso kisani aure ibada ne yinayi bari na bari karki maida gidan auranki gurin cin kasuwa kokuma filin faɗa da miji karkiga dan bai baki kulawa kina waje kice inkin shiga ciki bazaki bashi kulawa ba , kizamo mai tausasa murya ga mijinki kizamo mai tausayinsa kizamo mai faranta masa kamar inda kika yimin biyayya Allah yabaki ƴaƴa masu albarka masu biyayya , cikin muryar kuka Diyana tace " dady ka yafe min.
Dagani kasan ƙarfin halin magana yakeyi yace " na yafe miki Diyana .
yayi mata umarni da ta tafi , tana tafiya tana kuka wata yayar momy ta jata zuwa part ɗin momy , nan ma nasiha suka yimata mai ratsa zuciya kowa tausayinta yakeji kasancewar labarin auran da akayi mata ,
9:pm motar ɗaukar amarya ta ƙaraso tayi wanka ankuma shiryata jikinnan kamar anyi ɓarin turare , duk inda ta zauna ƙamshi ke tashi sai ta barmusu tsaraba ,
rabuwa da momy ba ƙaramin kuka tayi ba sbda sabo turken wawa , Afreeda gata ga amarya suna riƙe da hanun juna , Hajiya cewa tayi bazataje ba sai daga baya zataje taga gida a nutse ,
sunyi tafiya mai nisa sosai sanan suka shigo anguwar da dadyn Kamill ya siya masa gida , tun daga nesa suka hango gidan shi kaɗai , gashi ba wani ƙato sosai ba amma nera tayi kuka , horn drivern nasu yayi aka buɗe masa get ya shige dasu , yana parking wata ƙanwar momy tace " fito da ƙafar dama kiyi bismillah , tana fitowa itama ganin tsaruwa da kyan gidan yasata sunkuyar da kai gefen zuciyarta tanajin tayi sa'ar miji , mai kula da ita ,
rungumeta sukayi kai tsaye suka kutsa cikin gidan gaskiya inhar nace zan tsaya misalta kyan gidannan bansan irin misalin da zanyi muku ba ku ƙaddara gidannan kamar irin ginin turai bedrom aka shige da ita aka zaunar da ita akan gado , cigaba sukayi dayi mata nasiha sanan suka sata tayi wanka ta sauya kaya , suka feshe mata jiki da turare sukabi ko ina na ɗakin da turare mai sanyin ƙamshi ,
Sallama sukayi mata , a lokacin ta gane lallai aure ya wuce tunanin mai tunani , Afreeda da ta kwanta jikinta taba kowa tausayi janta sukayi tare da cewa " yanzu ba'a kwanan gidan amarya kiyi haƙuri kizo muje kiyimata adu'ar zaman lafiya kawai , haka aka janye Afreeda tana kuka suka fice daga ɗakin , kasancewar batada wasu ƙawaye .
Bata gama tsorata ba sai dataga mutane sun watse ita kaɗaice a gidan hankalinta ya fara tashi , miƙewa tayi ta murɗa handle ɗin ƙofar toilet , alwala ta ɗauro sbda batayi magriba da isha ba , tana fitowa ta shimfiɗa dar duma ta tada sallah , bayan ta idar ta kwararo adu'oi ta shafa , lumshe idonta tayi tana mai godiya ga Allah ta ninke dardumar ta koma kan gado ta kwanta kamar wata baby , jin shiru har ƙarfe 10: yasata janyo wayarta ta lalubo lamar Kamill da tayi seven da my blood danna kira tayi , jin tana ring ba'a ɗaga ba tafara tunanin ko lafiya tunda bai saba yimata haka ba .
Ƙara danna kira tayi a karo na biyu nanma shiru ba'a ɗaga ba , ajiye wayar tayi tare da fashewa da kuka dama idanunta sun kuɓbura daƙyar take buɗesu , shiru shiru har ƙarfe sha biyu na dare , lokacin ma bacci mai nauyi yayi gaba da ita sbda gajiyar biki.
Zaune yake a guest hause ɗinsa dake kano , tofa masu karatu ango baya Abuja yana ma kano .
bacinsa yake shara hankalinsa a kwance kamar ba ango ba bashi ya farka ba sai wajen asbha lokacin anata kiraye kirayen sallah daga ma ban bantan masallatai , kasancewar akwai masallaci a gidan yasashi nufar masallacin .
Har akayi sallahar asbah Diyana na bacci ba ita ta tashi ba sai ƙarfe bakwai na safe , a firgice ta sako daga gado tare da nufar toilet tayi brush ta ɗauro alwalah tafara sallah tana idarwa ta koma ta kwanta inka ganta abin tausayi .
Kogin tunani ta shiga to ina my blood tamayar da take yiwa zuciyarta kenan , babu mai bata amsa yasata janyo filo ta rungume tare da share ƴar kwallar data zubo mata.
Wayar ta ce tafara ruri cikin sauri ta janyo wayar ta ɗauka Kamill ne mai kiran hakan yasata gyaran murya , tana duba fuskar wayar taga my sis cikin ƙarfin hali ta kara a kunne tare da cewa" ƴar uwata yakike ? ya momy da dady , Afreeda dake dariya tace " kowa lafiya dafatan dai amarya na cikin ƙoshin lafiya , normal sis ina lafiya yaushe zaki zo ? zaro ido Afreeda tayi kana tace " kema kinsan ba barina fita za'ayi ba amma karki damu inanan zanzo cikin satinnan , daga haka sukayi sallama .
tashi tayi tafara zagaya ko ina na palon babu laifi nera tayi kuka kuma ko ina ƙamshi ke tashi ga kayan kallo nagani na faɗa , haurawa step tayi tana mai ƙarewa fentin kallo kai kace ƴar ƙauye , ɗakuna uku ne a saman,
Na farkon tafara buɗewa wani fitinannen ƙamshi ne ya daki hancin ta batasan lokacin data kutsa kai ciki ba ,
Hoton da tagani ne yasata faɗi jugub cikin firgici da tashin hankali tafara nuna hoton da yatsanta tana cewa " kardai shine , wayo nashiga uku na lalace badai shine mijina ba dady bakuyimin adalci ba inhar shine baku sanar dani ba , kuka takeyi tana matse kanta lokaci ɗaya ciwon kai yayi mata sallama , amma har yanzu bata dena kallon hoton Kamill ba .
ƙara nuna hoton tayi a karo na biyu tare da cewa " natsaneka na tsaneka bana sonka bana ƙaunarka takuma fashewa da kuka mai ban tausayi , jan ƙafafunta tayi da suke neman ƙin ɗaukarta ta nufi ƙasa nata riƙe da kai , bata sami damar ganin sauran ɗakunan ba tayi gamo da ɓacin rai, gado ta faɗa zuciyarta fal baƙinciki inta tuno maƙiyinta shine mijinta lallai akwai aiki tasan auran hukunci yayi bawai na tsakani da Allah ba , tabbas shine mai kirana a waya tabbas shine , magana takeyi kamar zararriya tana riƙe da kanta har yanzu .
Bayan tagama juye juyenta bacci mai nauyi yai nasarar ɗaukarta , baccinta takeyi cike da mafarkai iri iri duk na Kamill dakuma yanayin zamansu .
sai ƙarfe ɗaya ta farka tana tashi yunwa tayi mata sallama , kitchen ta nufa cikin sanyi jiki ta buɗe handle ɗin ƙofar ,komai akwai a kitchen ɗin babu abinda babu , in baku manta ba dama ba gwanar cin abinci bace , fridge ta buɗe shima cike yake da lemu kala kala , nutrimilk ta ɗauka mai sanyi ta koma kitchen ta ɗauko cake ta ɗora kan plet ta dawo palo tafara ci , bawani daɗi yake yimata ba amma saboda yunwar data addabeta yasata maida hankali ga ci .

Zaune momy suke a dining kowa da sakwara a gabansa da miyar egusi da naman kaza gefen kowanen su shayi ne mai kauri gakuma bredi da wainar ƙwai .
Hajiya dake kan kafet a zaune ita da Tinene ta dubi dady tace " Alhaji gobe in Allah ya yarda zanje gidan wanan zabiyar in dubota , to Hajiya dady yace " yaƙara da cewa " Allah ya tsare hanya driver zai kaiki , dady nima zani cewar Afreeda Allah ya tsare dady yace " musu momy kam tunda ta tashi takejin jikinta babu daɗi tanajin kamar akwai abinda ke faruwa da Diyana kasancewar ta mai zurfin ciki yasata yin shiru batare da ta gayawa dady ba .
Haka dai suka gama breakfast ɗinsu kowa ya watse .

yau kwanansu biyu da aure ko leƙowa bai yi ba ,a iya kwana biyu Diyana ta rame sosai fuskarta babu wani farinciki kana ganinta zaka gane .
Sallamar su Hajiya ne yasata amsawa cikin fara'a niko nace aure mai gyara hmm .
Guri Hajiya da Tinene da Afreeda suka nema tare da kallon Diyana dake zaune da remote a hanunta , bayan sun gaisa Hajiya tace " ƴarnan mai yaja miki rama haka ? kinfara nuna masa halinki na ragwanta da raki ko ?" sunkuyar da kai Diyana tayi dan bazata iya sanar da wanan tsohuwar damuwarta ba , miƙewa Afreeda tayi ta koma kusa da ita suka rungume juna , tashi ki kawo musu wani abin akwai drinks a fridge ɗauko musu kiduba kitchen akwai cin cin.
Riƙe baki Hajiya tayi tare da cewa kinci gidanku ta watsawa Diyana daƙuwa , waye yace "miki yanajin yunwa kokuma kawo ko bazanci ba sai naci ehe ,Diyana ba surutun Hajiya ne a gabanta ba hakan yasa ta gyara kwanciya a doguwar kujerar da take zaune tayi matashi da cinyar Afreeda .
Riƙe baki Hajiya tayi bata ƙara cewa komai ba , ta miƙe tare da juye abinda Afreeda ta ɗebo a gaban hijab ɗin Tinene ,to kitaso mu tafi inkuma kinzo zaman ɗaki ne sai muji , Hajiya tace tana shirin ficewa , miƙewa Afreeda tayi idanunta sun ciko da hawaye tace " my sis sai munyi waya .
Kasa magana Diyana tayi saboda kukan da ya ƙwace mata , tanaji tana gani suka tafi suka barta a gidan da shida kurkuku duk ɗaya.
Yau kwaanta uku a gidan bayan tayi sallahar Azhar ta jingina kanta da gado tun tana wani tunani daban har bacci yai nasarar ɗaukarta , jin an watsa mata ruwa mai kamada na ƙanƙara yasata saurin buɗe ido ta miƙe cikin tsoro , Kamill ne tsaye yana sanye da shadda fara tasha aiki kannan yasha hula sajens luf luf ba ƙaramin kyau yayi ba , wayabaki lokacin bacci a gidana ? cikin tsiwa Diyana ta taɓe baki kana tace " inbanyi bacci ba mai kakeso nayi ? ke karki kuskura kiyimin rashin kunya dan ni da kike ganina ina hukunta marasa kunya so ki kiyaye kisan ko da wa kike magana , taɓe baki takuma yi a karo na biyu tace " mtsw har ya ɗaga hannu zai kai mata mari ko mai ya tuna oho sai ya fasa ya fice daga ɗakin
Part ɗinsa ya wuce ya watsa ruwa kana ya fito ya shafa mayukansa masu ƙamshi ya nufi drower ya ciro gajeren wando da farar singlet ya sanya , ɗaukar wayoyinsa yayi kana ya sauka ƙasa , yana sauka yaji wani ƙamshi mai daɗu ya bugi hancin sa , leƙe ya shiga yi ta ina ne jin ko ta ko ina ƙamshin ke fitowa yasa shi nufar ɗakin Diyana cikin ƙasaita ,
samunta yayi a kwance kan gado hawaye sun bushe a fuskarta keee...! tashi ki dafamin indomie Diyana da takejin maganar kamar a mafarki ta kuma juyawa tana gyara kwanciya , fincikota yayi tare da cewa " gidanku babu manya ne ? karki manta yazu daga ni sai ke a gidannan so kuma kinsan matsayina a gurinki ko kin mance my blood ɗinne yau ? kuka Diyana ta fara mai sauti tana cewa "wlh ka cuceni Allah sai ya sakamin danasan kai ne zaɓin da iyayena sukayi min wlh bazan amince ba , zama gefe gado yayi tare da janyota yana riƙe da bakin maganar yace " sai kuma gashi kin yarda kuma inyi abinda nakeso dake , runtse ido tayi tana tuno irin tsanar da tayi masa tabbas bazata taɓa son sa ba koda nan gaba.
Ƙara matsowa yayi kusa da ita suna jin nunfashin juna yace " baby tashi ki dafamin indomie kuma wlh nabaki 3mins zaro ido Diyana tayi dan wanan lokacin yayi kaɗan , tunowa tayi to inma bata dafa ba uban me ya isa yayi mata , yana ficewa ta koma ta kwanta,kamar daga sama taji saukar bulala mai tsafi , innalilahi ta ambata cikin muryar kuka .
Mai nayi maka ? jaka aka kawo maka? to wlh ka kuma dukana ka gani, duk wanan maganar da Diyana takeyi idanunta a rufe , janyota Kamil yayi haɗi da cigaba da janta har hanyar kitchen , haka tadinga jin zafin janta da yayi a step ga kurjewa da tayi bugu da ƙari ƙarfinsu ma ba ɗaya ba , tayi iya yinta gurin ganin ta ƙwace amma abin ya citura , babu tausayi ko imani ya wurgata kitchen yana mayarda nunfashi tare da gurnani kamar zaki , oya ki wuce ki dafamin ko inyi miki abinda yafi haka , babu shiri Diyana ta miƙe bakinta da guwai war hanunta duk ya ƙuje ta kuna gas kana ta ɗora ruwa yana tafasa tasa komai tare da mangyaɗa da sauransu , sai da ta juye a plet ganin baya kallonta ta zabga gishiri a ciki ta miƙa masa , banza kalmar da ta fito daga bakinsa kenan , sai da Diyana ta ruga da gudu tace " ai ba'a banza ɗaya sai dai biyu ta shige bedroom tana cigaba da kuka tare da murɗa key ɗin ƙofar.
Ƙwafa yayi dan yasan bakinta ba mutuwa zai yi ba , dining ya nufa ya zauna tare da ɗaukar cokali ya fara juya indomien lomar farko yaji ɗan karen gishiri kamar iya shine a abincin , Diyana ....bazaki fito ba wlh yau sai kin gane bakida wayo uban wa yace miki haka ake girki ? shiru batare da ta amsa ba ya sashi ƙara tunzura yana huci ya haura up step , kai tsaye ɗakinsa ya nufa ya faɗa gado zuciyarsa nayi masa saƙe saƙe , ring ɗin wayarsa ne yasa shi ɗago kai ya nuba mai kiran nasa Abba ne , Kamill yace " tare da ɗaukar kiran ya kara a kunne , Aslamu alaikum Abba barka , cikin farinciki Abba yace " dafatan kuna lafiya ya ɗiyata ? tana lafiya Kamill yace " to masha Allah ka nutsu my son yanzu kayi aure fa .
To insha Allah Kamill yace " daga nan sukayi sallama .
Kwanciya yayi kansa na kallon sama yana tuno kalar muguntar da zai sake yiwa Diyana a karo na biyu , daga haka bacci mai nauyi yayi nasarar saceshi , jinshi shiru yasa ta buɗe ƙofa ta fito saɗaf saɗaf tayi kitchen flaks ɗin ruwan zafi ta ɗauka kasancewar tunda masu kawota suka cikashi da tafasashen ruwa batayi amfani dashi ba , ɗibo kayan haɗa tea tayi da duk wani abinda zata buƙata harda ragowar cake ɗinta da butter duk ta kawosu ɗakinta ta jeresu kan bedsite ɗinta kana takuma dannawa ƙofar key , haɗa shayinta tayi mai kauri tanasha tana gutsirar cake , da haka har ta ƙoshi sosai , ajiye cup ɗin tayi tare da gyatsa ta lumshe idanunta , tunowa tayi rabonta da waya da momyn ta tun safe dan haka ta ɗauki wayarta ta danna number my mom , ring ɗaya momy ta ɗauka cikin farinciki tace " my daughter dafatan kina nan lafiya ? eh ina lafiya momy ya Afreeda dakuma wanan tsohuwar ? dariya momy tayi tace " duk suna nan lafiya amma babu wata matsala ko ? naji muryarki babu daɗi ? uhm babu komai Diyana tace " akwai fa naji muryarki ta sauya ni mahaifiyarki bazaki sanar dani ba ko to wa zaki gayawa ? kuka Diyana ta fashe dashi dan zuciyarta ta tsinke da kalamin momy.
Bankaɗo ƙofar da taji anyi ne ya hanata gayawa momy halin da take ciki , bata ankara ba taji an fizge wayar daga hanunta , Aslamu alaikum momy ya gida ya aiki yakuma lil sis , dagajin muryar tasan mijin Diyana ne , washe baki momy tayi tace " lafiya lao ya ƙoƙari Allah yayi muku albarka Allah ya albarkaci rayuwarku , amen Kamill yace " tare da cewa mun gode momy muna nan zuwa gobe insha Allah, momy ta mance da maganar su da Diyana cikin farinciki sukayi sallama da Kamill .
wurgo mata wayar yayi Allah ya temaka bata faɗi ƙasa ba , tare da cewa " wlh duk ranar da naji kin gayawa wani yanayin zaman mu sai na illata ki , lumshe ido tayi batare da ta kalli inda yake ba , sai da ya gama surutansa sanan ya fice .
Washe gari bayan sallahar ashba garin ya tashi da sanyi mai shiga jiki kwance Diyana take a bed ta ƙudun dune da blanket sai kwasar baccinta takeyi .
Tunda Kamill ya dawo daga masallaci yake jinsa cikin wani yanayi , ɗakinsa ya wuce yana rawar sanyi , idanunsa sun kaɗa sunyi jawur dama

Please Login or Register in order to submit comment