Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ɗauka bayan ta karɓi chanjin ta suka wuce gida .
Hajiya na tsaye a bakin ƙofa tayi zugum tana jiran shigowar Diyana tsoronta ɗaya kar ƴar mutane tabi wani ƙauyen ,
Jin sallamarta yasa Hajiya washe baki tace " ina kika higa ne ƴar albarka ?" Diyana ce ta taɓe baki kana tace " naje siyo ruwa ne ,yaron yana ajiyewa ya fita .
Salati Hajiya tahau rafkawa tare da cewa"au yanzu duk tsaftatacen ruwan dake tuluncan be i'heki ba saikin siyo ruwan bature ? dont worry Diyana tacewa Hajiya ,
A' lallai kuwa wlh Alhaji ya ɗauko hanya marar ɓulewa amma zai kuma dawowa wlh bazata saɓu ba ,
Ita dai Diyana tama wuce abinta ta ɗauki ruwan alwalah tana idarwa ta tada sallah janyo jakarta tayi ta ɗauki cake ɗin da momy tayi mata tafara ci da nutrimilk , ƙara duba wayarta tayi chaji saura 20% gashi tunda tazo bata sami lambar momynta ba sunfara waya da Afreeda network ya ɗauke , dafe kanta tayi tana tunanin anya zamanta zai yi a ƙauyen nan,
Bayan sallahar isha'i Hajiya ta zubowa Diyana tuwo miyar kuka da man shanu tunda Hajiya ta shigoda tuwon tafara jin tashin zuciya da sauri ta kawar da kwanon tana toshe hanci , wata uwar harara Hajiya ta wurga wa Diyana dan yau ta ƙureta ,
Hajiya ce ta kama ƙugu tace " ke ƴarnan banison kinibibi wlh inbaki fita idona ba zan dakaki ,
dariya ma tabawa Diyana aikuwa tahau ƙyaƙyatawa dukda ita ɗin ba mai son yawan dariya bace , aikuwa Hajiya ta ƙara ƙuluwa ta kuma girgiza ƙugu niko nace kamar muciya lol Diyana kam zanyo blanket ɗinta tayi ta shimfiɗa a palo ta yi filo da jakar kayanta , tsabar bakinciki da ya isheta ma waƙa ta kunna ta toshe kunenta ,
mita Hajiya taci gaba dayi kamar zata ari baki oh ni Hafsu naga ta kaina indai birni ne wlh Allah wadai nikam tayi uwar ɗaki tana kakaɓe zaninta ,
tana zama tayi bakin gado tana lilo da ƙafarta ,kasancewar gado mai rumfa ,
juyawar da zatayi taji cizo innalilahi to mai ya sameni ?" hango cinnaka tayi yana tafiya ta gefenta sai yanzu ma tafara jin cizon , abinka da jikin tsohuwa yaji jiki tafara susa lalubar ƙarƙashin filo tayi koda zataga man zafi gurin harya kwaile tsabar susa tana ganin man tahau sharɓawa aikuwa tasha zafi ƙaramin hauka ne batayi ba, Diyana tana jiyo surutunta tayi shiru tana bin waƙar Hamisu breaker mai taken Jarumar mata anan gurin ma Hajiya tana jiyo saurin muryarta dan taƙi jinin tayi magana ayi kunnen uwar shegu da ita ,tofa da alamu dai Hajiya bazasu jitu da Diyana ba ..
Diyana kuwa cikin ranta cewa takeyi ai tunda kince sa ido ne aikinki to wlh nafiki bari dare yayi sosai zaki gane .
Bayan wasu mintuna bacci ya ɗauki Diyana bata samu tayiwa Hajiya hukunci ba .
Washe gari da asbha Hajiya ce tafara tashi sai da ta idar da nafil filinta tazo ta tashi Diyana ganin taƙi tashi yasa Hajiya fara sana'ar tata wato mita komawa tayi ta kwanta tunda ta tasheta taƙi tashi ,
Saida gari yayi haske misalin ƙarfe bakwai Diyana ta motsa lokacin Hajiya ta kuma tashi tana gaban murhu ɗumama tuwo ,
Sannu Diyana tacewa Hajiya kanta a ƙasa ,
Yawwa ƴar albarka Hajiya tace " shigewa banɗakin da ya zame mata dole tayi bayan ta fito ne ta sunkuya zatayi alwalah taji Hajiya na masifa Diyana ce tace " shidai mutum kullum cikin masifa yake ,
ashe Hajiya ta ji, aikuwa takuma ɗorawa tana cewa yanzu ban isa nayi ajiya ba sai anyimin sata ankwahe nama ankwahe abinnan da akeyi da fulawa to yau zanci uwar ɓarawon nan bari Tinene ta shigo ƴar kan uba datanada gaskiya da asubar fari zaka jiyo sallaɓarta tazo cin ɗumamen tuwo .
Diyana dai bata sake magana ba tana gamawa taje ta fara sallah tana idarwa tayi adu'oin ta, ɗibi ruwa a randa badan ranta yaso ba ta koma ɗakin ta ɗauki soso da sabulu tashiga wanka , ta daɗe tana wanka kasancewar jiya bata samu tayi wankan dare ba ,
Tsaye Hajiya take tana jiran shigowar Tinene ganin ta shafe mintuna bata shigo ba yasa Hajiya komawa ɗaki tafara cin tuwonta ,
sai da rana tayi sosai har anyi azhar Tinene ta kwaɗo sallama , gyan gyaɗi Hajiya takeyi a kan kujera amma dake tasa abin a ranta a zabure ta miƙe tanajin Tinene ta shigo ta cakumo ta tare da cewa yanzu kin kyauta kenan? " Tinene ce tahau borin ƙarya tana cewa wlh kaka kidena ƙalamin sata nice kaɗai a ɗakin ? Hajiya ce takai dubanta ga Diyana dake tsara kwaliya tana shirin sa kaya tace " to wazan ƙalawa inba keba waccan mai kamada zabiyoyin ba komai takeci ba bare nace ita to wlh zan haɗaki da Talatu dan bazan yarda ba, haka dai Tinene tasamu ta zulle dama ba yau suka fara ba .
Kwanci tashi asarar mai rai yau kwanan Diyana shida a ƙauyen SHAFA babu abinda ya sauya na daga ɗabi'unta sai dai takanci abinci intaga yayi mata .
Diyana ta gyara kayanta sbda basuyi datti ba ta ninkesu ta saka a jaka a ƴan kwanakinnan suna ɗan magana da Hajiya ,
Gobe takesa ran driver zai zo ɗaukarta wayoyinta babu caji duka sbda garin babu gurin caji tun tana baƙincikin hakan har tazo ta haƙura ,
A daren yau ne Diyana ta shirya yiwa Hajiya mugunta .
7:pm na dare bayan Talatu tazo sunɗan taɓa hira da Hajiya har Diyana ta gaishe ta ,ta jima a gidan sanan ta tafi yau dai tunda Tinene ta tafi gida bata shigo ba gashi dare yayi sosai lokacin ƙarfe tara da rabi , Diyana ce ta ɗauko bredin da Hajiya ta bada aka siyo mata da madara kasancewar yanzu dai ƙyan ƙyamin ba kamar da ba amma fa akwai ,
yanzu damuwarta ɗaya Allah yasa kar ace za'a tafi da Hajiya dan tanada yaƙinin zata dinga haɗasu faɗa da dadynsu amma daga yau zata fara tsorara ta ta ,
Hajiya tagama gyan gyaɗin da tasaba akan kujera ta miƙe tacewa "Diyana ƴar albarka sai da safe, Allah ya tashemu lpy Diyana tace " yaukam bacci babushi a idanunta duk akan za'ayiwa Hajiya hukunci .
Ƙarfe goma da rabi kamar an tsikari Diyana ta miƙe ta juya ta ciro wani farin hijab nata mai niƙab dogo har ƙasa da ' alama na sallah ne ,
Shiga cikin uwar ɗakin tayi tana ƙarewa jeren ɗakin kallo taɓ wasu ɗakuna ma sai ƙauye wai yazuma anan gidan a dol gidan masu kuɗi kenen ko uhm ,
Tunowa tayi da abinda ya kawota , tsinken tsintsiya tasamu tafara shafo fuskar Hajiya dashi kana ta ɗauko kujera ta zauna tanata bin fuskar da tsinken tsintsiya , jin anyo ta wajen kunnen Hajiya yasata farkawa a zabure tana cewa yauma shazumamun ne suka kuma shigowa bayan na rannan dana kwashe ,
Bata lura da Diyana dake gefe ba sauya murya Diyana tayi tace " nazo tayaki kwana ne nice yarinyar Aljani ɗan kutub wata uwar durowa Hajiya tayi ganin farin abu, babu fuska kamar likafani...!

Dan Allah kuyi haƙuri kuji tausayin bil adama wata uwar dariya Diyana ta saki badan tasan tanada babbar murya haka ba, tsumar jikin da Hajiya takeyi ne ga ɓurma mmen baki gaskiya comedy.com taci dariya ita da bata dariya sosai ,
Girgiza kai Diyana ta fara yi da farin hijab ɗin da ya rufe mata fuska , itako Hajiya ta haɗe hannuwa biyu tana cewa kuyi haƙuri nidai bansan laifin danayi muku ba tunda kwana biyu ba higa jejin nakeyi ba bare kuce naje na yimuku wani abin ,
Wata uwar ƙara da Diyana ta saki ne yasa Hajiya zabura zatayi palo dosota Diyana tafarayi kana tace " kwanta kuma da safe mukaji kinyi maganar mu sai mun juya miki baki gefe maza ki kwanta Allah sarki Hajiya an maidata kamar baby .
Ta koma ta kwanta tare da runtse ido Diyana ko yin alamun kamar mai fita tayi ta shigo a hankali ta kwanta .
Washe gari Hajiya a makare ta tashi lokacin ma anyi sallar asbha tunda ta tashi yau ko mita babu juyawa tayi taga inda Diyana ke kwance taje kusa da ita tace " ke ƴar albarka tashi gari ya waye , tom kawai Diyana tace "jiki a sanyaye Hajiya taje ta haɗa wuta ta je yin alawalh kafin taje sallah wutar ta kama ta ɗora ruwan kunu ta je sallah tana idarwa ta koma uwar ɗaki ta riƙe baki tana mamakin abinda ya faru da ita jiya gashi ance karta gayawa kowa , girgiza kai tayi tana nazarin inhar Alhaji yazo yau to bazata zauna a garinnan ba sbda tunda aka fara yimata haka to gaba ranta za'a nema ta miƙe tayi waje ,
Diyana na lura da yanayin Hajiya jitayi kuma taɗan bata tausayi wata zuciyar tace " ai da bakiyi mata haka ba da tana nan tana mitar da tasaba .
Tinene ce ta shigo tana kiran kaka ! kaka ! jin Hajiya taƙi kulata yasata ƙarasowa tace " kaka lafiya kuwa ? Hajiya ta sako tuwo a kwano zatakai ɗaki tace " ke ni kauce kibani gu , kaucewa Tinene tayi ganin yau babu masifa kuma babu alamun wasa .
ƙarfe goma na safe driver ya iso ƙauye lokacin Diyana ta shirya shi kawai take jira ai tanajin horn ɗin mota ta miƙe tana cewa to Hajiya a yafemu ,
Hajiya dake ɗaki tanayi walha sallamar ta kenan ko adu'a batayi ba ta taso tana mita ,
"Saikace ina cizonki ai kyabari in fito ke ga ganɗoki ko kokuma mun gundureki ne ?".
Lumshe ido Diyana tayi batace komai ba , hakadai Hajiya tayi ta gama tayi shiru .
Driver ne ya fito daga mota ya shigo gidan Hajiya durƙusawa yayi har ƙasa ya gaisheta cikin fara'a ta amsa tana tambayarsa yasu Alhaji da Faɗimatu ?".,
duk suna lpy suna gaidaki driver yace " ya miƙe tare da kallon Diyana ya gaisheta a yangace ta amsa dama ɗabi'arta kenan,
Kana yace " inkin shirya hajiya sai mu tafi ai kafin yakai ga ƙarasa magana Diyana tace " nafa shirya dama kai nake jira Hajiya dai taga ikon Allah wata ƙatuwar leda tabawa driver ya bawa momy zasu fita kenan sai ga Talatu ta shigo ,
Ina kwana Diyana tace "da fara'a Talatu ta amsa da lpy yaune tafiyar ne ? eh Diyana tace suka ɗunguma sukayi waje ,
back side ta shiga suka kuma yin sallama Diyana ce ta kalli Hajiya kana ta ɗan yamutsa fuska tace " ina wanan yarinyar ? washe baki Talatu takuma yi tace " ai na aiketa hyagon Haliru 1k Diyana ta bawa Talatu ta ajiyewa Tinene aikuwa sun sanya mata albarka .
Motar na shirin tashi Hajiya tace "to ƴar albarka sai Allah yayi zuwanmu killer small Diyana tayi kana tace " saikin zo driver yafara tafiya .
Shunyi tafiya mai nisan gaske kana suka ɗauki hanyar Abuja Diyana takan tuna rayuwarta ta ƙauye jifa jifa tayita murmushi musamman farin hijab ɗunnan data sawa Hajiya yana matuƙar sata nishaɗi ,
Jin horn da driver yakeyi ne yasata ɗago kai Alhmdulilh tace cikin ranta ,mai gadi na wangale get ta
Hango momy da Afreeda suna tahowa da murmishi a fuskar su hawaye ne suka zubo mata tarasa na miye ,
Mai gadi ne ya buɗe mata murfin mota ta fito da gudu ta faɗa jikin momy ta saki kuka ,
Afreeda ganin kukan sistan ta yasata fara kuka ,
Momy ce ta hausu da faɗa tana cewa " meye kuma na kuka bayan Allah ya dawo dake lafiya ,
Diyana batayi magana ba suka ɗunguma zuwa palo zama sukayi a kujera momy sai kallon ɗiyar tata takeyi ga wata muguwar ramar da tayi kuma jikinta ta gefen fuskarta ga cizon sauro nan, jinina kai momy tayi batare da tace komai ba ,
Tunani ta fara batada ikon hana Alhaji tafiya da Diyana ƙauye .
Jin hirarsu ce ta dawo da ita daga duniyar tunani Diyana tace " momy mai kuka dafa ne ? Afreeda ce tace " tuwon shinkafa miyar shuwaka ,
Yamutsa fuska tayi kana ta ƙara da shagwaɓe fuska kamar zatayi kuka tace " acan ma mutum baiji daɗi ba , anan ma bazanji ba ?" momy dai batace komai ba sbda rigimar Diyana tafi ta ɗan yaye wani time ɗin ,
Diyana ce ta miƙe tana fushi ta nufi fridge hango fanta tayi mai sanyi hakan ya sata ɗaukowa ta ciro ragowar cake ɗinta a hanbag tafara ci kamar an aikota ,
Niko nace su Diyana an daɗe ba'a haɗu ba .
Saida ta shanye babbar kwalba kana tayi gyatsa ta maida kanta ga kujera ta jingina ,
Momy da Afreeda banda kallonta babu abinda sukeyi ,
Afreeda ce ta ƙunshe dariya tace " sis yaushe rabon da kisha fanta ?".
Shigowar dady ne ya hana Diyana bawa Afreeda amsa .
Momy ce ta miƙe tayi masa barka da dawowa tare da karɓo wata takarda dake riƙe a hanunsa ,
Diyana da Afreeda ma sannu da dawowa sukayi masa ,
Cikin farinciki ya amsa yace " daughter ansha ƙauye ina kika baro Hajiya ?" Diyana ce tace " ai tana gaishe ka wai sai tazo ,
Madallah dady yace " ai takusa zuwa ma nanda two weeks insha Allah ,
sunkuyar da kai momy tayi dan batada ta cewa a wanan gaɓar haka dai suka dinga hira da dady .
Afreeda ce suka haɗa ido da Diyana tayi mata alamun ta, taso akwai labari da sauri sukayi ciki suka bar momy da dady a palo suma tashin sukayi kowa ya watse akabar palon shi kaɗai .
bayan sunyi sallahr magrib Afreeda ta gyara zama ta dawo kusa da Diyana tace " my sis kinsan me ? nayi sabon saurayi a bikin Hindu da naje shekaran jiya ,
Diyana ce ta dubi Afreeda kana tace " sis karfa ace soyayya zaki fara a ƙarancin shekarunki yanzu fa kina 18 years ne amma kike maganar soyayya .
Ɓata rai Afreeda tayi tace " haba sis mai yasa aduk lokacin da na kawo miki shawara sai kin nemi hanani yin abu ,
Afreeda tafara kuka. gyara zama Diyana tayi ta rungumo Afreeda tace " my little sis ina sonki banison ta sanadiyar soyayya karatunki da brain ɗinki su shiga wani hali , so yanzu dai kibari zuwa tomorrow zamuyi magana karki damu .
Haka dai suka bar zancen sai zuwa gobe amma ran Afreeda ya ɓaci bata bari sistern ta ' ta fahimta ba kasancewarta mace mai fushi sosai.
Kawar da ɓacin ran tayi ta hanyar cewa " sis ya kikayi da zaman village ? naga kin rame sosai kuma kinyi baƙi .
Hmm kedai bari wlh nasha wuya ko a mafarki bana burin sake zuwa wanan ƙauyen sbda wlh ni nasan halin da na shiga ga tsohuwar nan masifa tayi mata yawa , Diyana ce ta kwashe labarin bidirin da tayiwa Hajiya aikuwa suka dinga dariya .
Afreeda ce ta riƙe haɓa tace " sis ashe wanan tsohuwar zata dawo gidannan ? gaskiya tana dawowa mun shiga uku .
"hmm ai bakisan wani abu ba wlh inhar tadawo saita gwammace dan wlh momy zata dinga sawa ido , muma dai ba barinmu zatayi ba aikuwa zata gwammace kiɗa da karatu dan wlh duk dare sai na horata dariya suka sa kana ko wacce taje toilet tayi wanka Afreeda saida ta fita sbda cikinta baya jurar yunwa ,tasami abinda zatasa a bakin ta suna ƙarasa salolinsu kowa ya kwanta .
9am kow yayi sallahr asbha ya koma bacci kasancewar yau weekend sai 11:am suke breakfast ,
Ƴar aikin su na kitchen tana ta haɗa musu abinci ,
Afreeda ce ta fara motsawa brush ta shiga toilet tayi kana ta nufi kitchen dan cikinta baya yimata uzuri ,
Diyana kam anata sharar bacci anji katifa mai laushi lol,
Ƙarfe sha ɗaya kowa ya hallara a palo kan dining momy dady Diyana dakuma Afreeda kowa yai wnka da shiga ta alfarma a jikinsa , bayan sun gaisa ne kowa ya maida hankali ga cin bincinsa saɓanin Diyana da takecin soyayyen dankali da shayi ,
Dady ne ya kalli momy yace " Hajiya fa gobe zata zo Fatima , momy ce tace "Allah yasa muga goben lfiya Alhaji amen dady yace " Diyana da Afreeda suka haɗa ido kowacce ta buɗe baki basu bari dady ya gansu ba kowacce ta maida hankali ga plet ɗin gabanta , suna gamawa dady ya miƙe ya shige ciki binsa momy tayi kasancewar tun jiya ya gaya mata sunada meeting a office .
Diyana ce tace " wlh dady yasa wanan tsohuwar a rai bai san inhar ya kawota aiki zata basa ba hmm , haka dai suka dinga hira wacce duk ta Hajiya ce dakuma abubuwan da zau shirya mata .
gari na wayewa dady ya fara ƙwalawa driver kira da azama ya ƙaraso ya durƙusa gaban dady,
Dady ne yace "inason ka ɗauko Hajiya ne amma karka bari ta kwaso komai iya kayanta kawai,
Angama Alhaji driver yace " kana ya miƙe .
Lokacin da ya ɗauki hanya ƙarfe tara na safe sai dai muyi masa fatan isa lafiya ,
Da isarsa yai sallama Hajiya na girka daddawa gidan ya gurme da wari ya durƙusa ya gaisheta amsawa tayi tana cewa" lalle lale da ƴan binni barka da zuwa ,yawwa driver ya amsa Hajiya .
Wanke hannu tayi tace " to shiga ɗakin man, da shigarshi Hajiya ta miƙo masa kwanon fura da nono aikuwa driver yayi murna sosai dama yana abota da fura da nono ita kuma Hajiya bata rabo dashi , sai da ya cika cikinsa dam sanan ya dubi Hajiya dake zaune hankalinta na kan kalwarta yace " Alhaji ne yace " inzo in taho dake , hajiya ce tace " har satin ya zagayo ne dahar zai turoka , driver ne yace " to yadai ce inzo in tafi dake , jinjina kai Hajiya tayi tace " leƙa ƙwar gida ka kiramin yaro
to driver yace " ya miƙe yana fita yayi sa'ar ganin wata yayarinya tana doso gidan ,
ina wuni tace masa 'amsawa dtiver yayi da lafiya lao ,
Nan gidan zaki shiga?
Eh yarinyar tace " okay suka shiga a tare , tun daga tsakar gida Tinene tafara wankawa Hajiya kira ,kaka kizo Talatu ta aikoni wai ki hammata gihiri ,
Hajiya na mita ta fito tana cewa Tinene kiyi maza ki hirya yau binni zamu kwana ki gayawa Talatu ta haɗo miki kayanki ,
Driver dai komawa mota yayi yabarsu a gurin.
Wani uban tsalle Tinene ta doka harda taka rawa tace "hikenan zamu zamo ƴan binni tafara tafiya tana yarfe hannu tasa dariya , takuma canza tafiya wai zatayi kalar tafiyar Diyana .
Hajiya dai tashige gurin shirya kayanta ,
Kamar wacce aka zabura tayi waje da gudu driver dake mota ya hangota dariya yasa yace " ƴan matan ƙauye hhh.
Tinene na isa gida tafara wankawa Talatu kira fitowa tayi tafara yimata faɗa akan wanan kiraye kirayen da takeyi tun daga ƙofar gida , to albishir zan yimiki yau kaka zata binni ,
Da sauri Talatu ta ajiye ledar gyaɗar da take ɓarewa tace " kai dan Allah ?" wlh kuwa to zomu tafi gidan Tinene ce tace " a'a nidai kayana zan tsaya shiryawa Talatu bata jira ta saurari Tinene ba tayi waje , a ƙofar gida ta ƙarasa sa mayafin.
Tana shiga tasami Hajiya a tsakar gida ta fito da buhu , cikin azama ta ƙarasa tace " inna wai yau zaku tafi binni ? gashi kuma kina gani , ina tace tana ciciɓar buhun ,
Talatu ce tace inna yanzu tafiya zakiyi ki barni ?" kuka Hajiya tasa tana cewa " zan dinga zuwa karki damu nima ba ason raina zanyi tafiyar nan yau ba ,ina Tinene tazo ta kawo buhun nata in haɗa da nawa Talatu ce ta share hawayen da suka kwaranyo mata tace "inna inkika tafi wazai dinga bani wani abin idan na nema , Hajiya ce ta kunce ɗaurin zaninta kana ta ciro kuɗi a lalitarta, sunkai dubu goma ta miƙawa Talatu da keta share idanunta da mayafi ,
Cikin farinciki ta karɓa tana godiya .
Hajiya tasan wuyar da Talatu kesha a gidan mijinta wata rana baya bada kuɗin cefane kokuma yace" ta auni masara ta kai niƙa babu kuɗin girkawa hakan yasa Hajiya take matuƙar tausaya mata amma bata cika nuna mata a fili ba sbda gudun wata rana ,
Hasali ma shine yasa takeson ɗaukar Tinene duk da ta zamo budurwa dan a ƙalla zatayi shekara goma sha huɗu ,
Hajiya nada tabbacin kakar baɗi ubanta zai ce aure zaiyi mata kuma gidansu haɗin zumunci sukeyi .
Hajiya ce ta ƙara kai kallonta ga Talatu tace " inada buhun masara a ɗaki dana wake kuma ga shinkafa nan rabin buhu akwai mangyaɗa , duk ranar da bakida kayan awo ga mukulli nan kizo ki buɗe ,
Wani sabon kukan Talatu ta ƙara fashewa dashi tana tunanin kowa ya rasa mahaifiya yayi kuka tabbasmahaifiya itace abin alfahari ga kowane ɗa kuma itace take sanin ɗanta yaci ko bai ciba dazarar taga bai ciba zata fasa cin nata ta miƙa masa ,
haka dai sukayi sallama jikinsu duk a mace Tinene kam murna ta cika zuciyarta burinta taje birni ta waye tadinga kalar tafiyar Diyana dan komai na Diyana birgeta yakeyi .
Hajiya na kulle ƙofar ta miƙawa Talatu mukulli takuma ce mata akwai dambun nama a kwallah ki ɗauka mukan mun fito.
To Inna Allah ya saukeku lafiya cewar Talatu , Hajiya ma dauriya takeyi haka dai akasa abubuwan da takeso suka shiga mota ,
Tinene ta ƙwalawa Talatu kira , tana matsowa tace " Talatu dan Allah ki gayawa Bashiru nayi tafiya , maketa Talatu tayi kana tace " bakida kunya ne kifa kintsu Tinene rayuwar binni ba irin tamu bace ki nitsu ina gaya miki , sallama suka kuma yi motarsu ta tashi zuwa garin shugaban ƙasa wato Abuja ,
Basuyi wata tafiya mai nisa ba dan basu fita a kano ba Hajiya ta tsayar da driver tana cewa" kai baka tsayawa mutane suyi fitsari ne ? ko kuma so kakeyi yarinya tayi a wando ,
Ayi haƙuri Hajiya driver yace yana parking ɗin motarsa a gefen titi fita sukayi tare da wani galan da suka ɗuro ruwa a cikinsa,
Hajiya ma fitsarin tayi suka dawo mota .
Fitarsu Kano keda wuya Tinene ta hango mai gasa masara shirin kuka tahau yi tana cewa Hajiya itafa yunwa takeji ,
Shidai driver badan uwar mai gidanshi ya ɗauko ba babu abinda zai hana baiyi musu magana ba ,
Hajiya ce tace " kai tsaya a siya mata wani abun tasa a bakin salati ,
Driver ne yace " Hajiya nan basu siyar da komai fa , Tinene ce ta karɓe da cewa ga mai masara can wlh ko ita nasamu ai ƴaƴan cikina sa barni na huta ,
Hajiya ce ta ciro nera ɗari tace " driver ya siyo musu ƴan uku hamsin ,
driver yasan babu hakan yasa ya ciro kuɗi a aljihunsa ya miƙawa mai masara dan yasan inhar yakoma bai siyo ba Hajiya zata iya tsigaleshi , yana miƙa musu ,ya tada mota .
Sunyi tafiya mai nisa sbda sun wuce garuruwa da dama , jin motar tayi shiru yasa shi leƙa wa ta mudubi , hamdallah driver yayi ganin mai damun mutane tayi bacci , cikin ikon Allah sai gasu a Abuja har sunkusa layin su , Hajiya ba taɓa zuwa tayi ba shiyasa tayi gum da bakinta ,
Horn ya shiga yi , mai gadi ne ya wangale get ɗin yana ɗaga musu hannu ,
Hajiya ƙarewa gidan kallo takeyi badan ta ɗan yarda da drivern nan ba da zata iya cewa gidan ƴan yankan kai ya kawota amma bari ta zuba masa ido tagani ,
Yana parking ya fito tare da buɗewa su Hajiya ,
Tinene tayi bacci Hajiya ce ta ɗaka mata duka a razane ta tashi takalli Hajiya sanan ta kalli ina suke , mutsuke ido tayi tace " alkur'ani da gaske ne nayi mafarkin gani a wata sabuwar duniyar Hajiya ce ta sharara mata mari kana tace " zaki fito ko zaki zauna ni gaba zanyi dan inama tunanin kamar ba gidan Alhajin ya kawomu ba sbda babu ko wulƙawar mutane sai tsintsaye , Tinene ce ta fito tana shafa kumatunta

Please Login or Register in order to submit comment