Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ki kula , ko bi ta kanta Diyana batayi ba tace " sis zomu shiga kitchen , miƙewa Afreeda tayi suna shirin tafiya Hajiya tace " Tinene rakasu tunda sun wareki Diyana bataso ba amma Afreeda tace " tazo suje , da shigarsu aka fara tunanin abinda za'a girka muyi faten doya mai kifi pls sis cewar Afreeda ok bakida matsala , sis ɗauko mu fere no cewar Diyana miƙawa wanan yarinyar ta fere ɗauko kaza a fridge a soya , haka suka dinga aiki baji ba gani ga faten doya ga soyayyar kaza ga lemon abarba da yaji kayan ƙamshi suna gamawa aka fara jerawa a dining Hajiya na zaune hankalinta ya tafi gurin kallo, gyara kitchen ɗin sukayi kana suka dawo palo aka zubawa kowa a plet ƙa'idar Hajiya ita da jikarta basa zama a kan kujera hakan yasa aka zuba musu a faranti babba aka zubo kazar a plet shikuma juice ɗin a jug hira sukeyi tsakanin Diyana da Afreeda wani sa'in kaji Hajiya tace " ƙarya ne lokacin da suka gama cin abinci ƙarfe biyar na yama suka fara shirin tafiya , Hajiya ce tace " zan bar miki Tinene ta tayaki zaman kaɗaici , no ki tafi da ita kawai Diyana ta faɗa tana yamutsa fuska , kan uba Hajiya tace " to karki ɗauketan Allah yasa ina sonta masu mugun hali kawai kedai wanan ƴa bansan inda kika kwaso mummunan hali ba ke zomu tafi , ta nuna Afreeda Diyana ce tace " gobe driver zai kawota ƙundun uba wlh baku isa ba , kinƙi riƙe Tinene shine kikeson ki bar ƙanwarki to ƙafata ƙafarta , haɗa ido Diyana sukayi da Afreeda Diyana tace " pls dont follow her my sis , iye yo ko Alhaji ne ya zageni da turanci na barshi bare ku marasa kunya maza fito mu tafi , Guduwa Afreeda tayi har mgrib bata fito ba ga Diyana anyi juyin duniya taƙi magana da Hajiya taga uwar bari dole ta riƙe hanun Tinene suka bar palon tana masifa kamar zata ari baki, suna zuwa driver ya taso da gudu da har zai tambayi Afreeda jin faɗan da Hajiya ke surfawa yasa shi jan baki yayi shiru , haka dai suka shiga mota bata dena masifa ba sai da sukayi nisa ta fara gyan gyaɗi Tinene kam ranta ya ɓaci ashe dama haka ƴan binni ke ƙyamatar ƴan ƙauye take magana cikin zuciyarta , suna isowa Tinene ta tashi Hajiya , ana buɗe musu mota suka fice , da shigar su palon suka sami momy da dady suna cin abinci , zama sukayi a kan kujera Hajiya tace " faɗima kinga mun dawo babu wanan yarinyar ko , to nayi nayi dasu ina kunen ƙashi garesu nace tazo mu tafi taƙi wlh haka na barta , ita wace na tafi da ita ta tayata aiki, wanan mai kamada zabiyar taƙi ƙarɓarta oh ni naga duniya , dady ne yace " to ai shikenan momy tace " amma Diyana batada kirki ko kaɗan kai da ɗan uwanka , ita kuma Afreedan mijin nata na nan shine tazauna musu ko , ina driver yazo ya ɗauko ta , barin kirata a waya dady yace " yana ɗauko wayarsa a aljihu , lambar Diyana ya danna cikin sa'a ta shiga , ina Afreeda ? tambayar da dady ya wurgowa Diyana kenan , Afreeda gata nan ina yini dady lafiya dady yace " yaci gaba da magana mijin naki na nan shine dan bakuda hankali kika barta anan ko ? lahh dady bayanan wlh ɗazu ya tafi Abuja gidan su , oky dady yace " tare da katse wayar , ajiyar zuciya Diyana da Afreeda sukayi sunata tsalle , Hajiya dake jin abinda ake faɗe tace " ƙarya suke ko kafin mu fito yana gida yama fita aiki ne , momy dai batada bakin magana dady ma ci gaba yayi da cin abincin sa dan rigimar Hajiya ta musamman ce , miƙewa tayi ta nufi ɗakinsu dan yin sallah , momy ce ta kalli Tinene tace " kije kiyi sallah kizo kici abinci to Tinene tace " ta miƙe .
Kamill na isa kai tsaye gidansu ya wuce part ɗin Abbansa , cikin sa'a ya sameshi yana zaune da wani akwati a hanunsa , oyoyo my son Abba ya faɗa cikin farinciki , zama kusa da Abba Kamill yayi tare da risinawa ya gaishesa , bayan Abba ya amsa ne yake tambayar Diyana lafiya lau Kamill yace " jiya ma aka sallamo mu daga hospital , a firgice Abba yace " mai ya sameta ? wlh zazzaɓi shiru Abba yayi dan ya fara ƙisima wani abu a ransa , to Allah ya bata lafiya Abba yace yana cigaba da duba akwatin dake gabansa, hankalin Kamill ne ya koma kan akwatin ya zubawa kayan akwatin ido , cikin azama Kamill ya ɗauko wani photo yana gogewa yace " Abba munyi kama da wanan matar kodai itace " umma na ? shiru Abba yayi hawaye nabin kuncin sa , Abba meya faru dan Allah bata mutu bane ko ta mutu ? ina zan sani my son Abba ya faɗa da muryar kuka to ina take saceta akayi , tagumi Abba ya zuba dan wanan amsar kalma ɗaya zai iya gayawa Kamill itace " mun nemeta mun rasa kaf dangina da danginku babu mai ambatarta bare su tambayeka , ya ilahi koni mancewa nayi da ita tun daga lokacin da ta ɓata, miƙewa Kamill yayi idanunsa sunyi jawur da alamun damuwa a ransa kimanin shekaru talatin da ƙyar ma idan tana raye , jikin bango yaje ya zame yana kuka mai ban tausayi ya taso cikin gata da soyayya a guri ubansa amma bai san daɗin mahaifiya ba tabbas dole ya nemo mahaifiyarsa ko labarinta koda hakan zaiyi sanadin rayuwarsa , kuka yake mai sauti yayin da Abba ya kasa rarrashin sa , shima kukan yake babu mai bawa wani haƙuri.
Muje masallaci muyi isha'i inyaso sai muyi magana anjima in mun dawo , haka suka fita fuskarsu babu walwalh masallacin gidan suka nufa inda sukayi alwalah Kamill ya daɗe yana adu'ar Allah ya baiyana mahaifiyarsa haka ma ɓangaren Abba suna idarwa suka dawo babban palon Abban , abinci masu aiki suka jere musu , Abba ne yace " kaci abinci tukun sai muyi magana.
[01/07, 6:16 pm] Mom Islam Ce💃: 43 & 44

Cikin sauri ya dinga tura abincin badan komai ba sai dan yana jin yunwa banda haka abincin ma ba daɗi yake yimasa ba , koda ya gama dawowa yayi gurin wanan akwatin ya buɗesa , hotunansa ya gani lokacin yana ƙarami gakuma matar da Abba yace mahaifiyarsa na tungume dashi sunyi kama sosai , Abba ina jin mu bada cigiya gidan redio da gidajen tv dakuma zaridu duk dai kafafen sada zumunta , em my son Abba yace " zamuje amma sai zuwa gobe yanzu kam dare yayi , haka suka zauna su saƙa wanan su kunce wanan , misalin ƙarfe tara na dare Kamil ya miƙe tare da nufar part ɗinsa duk da yayi aure ɗakin bai sauya a mazaunin nasa ba , yana shiga yayi wa ƙofar key kana ya cire kayan jikinsa yasa na bacci , tunowa yayi da Diyana tabbas baiyi adlci ba tunda yaga photon mahaifiyarsa ya kashe waya ,number ta ya shiga gwada a cikin rashin sa'a yaji switch of abu goma da ashirin shikam wace jarabawa ce take neman sa , da haka bacci ya ɗaukesa cike da mafarkin Diyana tana ta kuka , washe gari tunda yai sallah ya kasa komawa bacci ƙara gwada lamar yayi jin a kunne yasa shi sakin murmishi , aslm my blood haɗe fuska Kamill yayi kamar tana ganinsa yace " nayi fushi ai, dariya Diyana tasa kana tace " wato ka iya wayo ni banyi fushi ba sai kai ? to afuwan mijina yau ɗin zaka taho , jim Kamill yayi kana yace " my Diya wata ƴar matsala ce ta taso dan Allah ki kwantar da hankalinki zuwa gobe da wuri zan dawo ,bu buha ƙafa Diyana ta shiga yi tana cewa " to mai ke faruwa naga mood ɗinka duk ya sauya ina ji a jikina babu lafiya fa , murmishin yaƙe yayi dan ya kwantar mata da hankali sanin sharuɗan da likita ya bada yasa shi cewa " kawai muna zuwa duba company ɗinmu ne shi yasa , uhm Diyana tace " ina Abba kace ina gai she shi , zai ji kina shan magani kuwa ? eh Diyana tace " gama Afreeda tare muka kwana , Kamill ne yace " bata wayar , miƙa mata wayar Diyana tayi cikin jin kunya Afreeda tace " barka da safiya yaya , yawwa barka ƙanwarmu dafatan kin tashi lafiya ? lafiya lau Afreeda tace " yasu Abba , Abba yana lafiya cewar Kamill , me zan siyo miki ?" amma sai zuwa gobe zaki tafi ko ? cewar Kamill , a'a anjima driver zai zo , dariya Kamill yasa yace " aiko babu inda zaki kibari zuwa gobe zan taho miki da tsaraba kinji cikin jin kunya Afreeda tace " Allah ya kaimu ta miƙawa Diyana wayar, my Diya Kamill ya faɗa cikin sanyin murya kinsan me ? a'a Diyana tace " nayi mafarki kin haifi twins cikin dakiya yake maganar dakuma ƙoƙarin ganin ya sanyata farinciki , dariya tasa tana cewa " to wazai tayani raino ? ni da ke man my Diya sai zuwa anjima ya katse zancen , ok ka kulamin da kanka mijina ta manna wawayar kiss , katse wayar yayi tare da furzar da isaka mai huci ya fito tare da sanya takalminsa ya nufi part ɗin Abba , samun Abba yayi yana breakfast , cikin ladabi ya durƙusa ya gai dashi , shafa kansa Abba yayi tare da sanya masa albarka , neman guri Kamill yayi ya ƙurawa Abba ido , ƴan kwanakin nan ya rame matuƙa , tausayin kansa ne ya kamashi ashe ko gawar mahaifiyarsa babu labari taɓɓ innalilahi shikam yaga tasku , lura da duniyar da ya tafi ne yasa Abba cewa " my son ka rage tunani fa , to Abba Kamill yace " badan yanajin zai iya ba , ƙara dubansa Abba yayi a karo na biyu yace " son zo kayi breakfast yanzu zamu fita , cofee kawai zan sha Abba bazan iya cin abinci ba , kallon tausayi Abba yayi masa bai ce komai ba , Abba ne ya haɗa masa cofee ɗin tare da bashi a baki kai kace " ƙaramin yaro , yana gama sha Abba ya tattaro wayoyinsa da abubuwan da zai buƙata suka fito shida Kamill , ko ɗakin Ameena basu nema ba sukayi ficewar su ,driver na ganinsu ya tada mota tare da buɗe musu back side suka shige , kai tsaye gidan redio suka nufa tare da bada cigiya , suna fitowa Abba yaje gidan jarida zasu nan ma suka bada cigiya harda gidan tv sanan suka dawo gida , kafin su dawo suna hanyar tahowa sukaji ana cigiyar mahaifiyar Kamill , jikin Kamill ne yai sanyi yace " Abba kaji har an fara sanarwa , eh Abba yace " batare da ya ƙara magana ba , gida suka wuce lokacin ƙarfe uku na rana , a gajiya suka zarce bedromm ɗin Abba , wash Kamill yace " dubansa Abba yayi kana yace " ka kira yatinyar nan kaji ya jikin nata , wlh na mance Abba amma ɗazu da safe munyi waya , ok Abba yace " Kamill ne yace " Abba mai zai hana mu kira malamai ayi abin sadaka dakuma saukar alqur'ani mai girma akan Allah ya baiyano da mamana , idanun Abba ne suka ciciko da hawaye sbda kar ya karayar wa da Kamill zuciya yasa bai bari ya gane ba , za'ayi Kamill insha Allah kuma zansa a tayamu da adu'a yanzu ma barin kira malam Usman cewar Abba , ciro wayarsa yayi tare da danna number , cikin sa'a ta shiga yana ɗauka suka gaisa , Abba yayi masa bayanin komai , malam Usman ne yace " wato wanan al'amarin akwai rikitarwa an yiwa matarka abinda bazaku sake haɗuwa ba kuma bazata sake wai wayar ƴan uwanta ba , tana nan a raye insha Allah zamu ƙoƙarta da adu'a kuma za'a ganta , farinciki fal zuciyar Kamill , washe gari yau kwanan Kamill biyu yau yake shirin tafiya gida gashi yanason su ƙara bincike , zaune suke a Familly palo wanda inhar kana zaune zakaga kowa mai shige da fice koma wanene kasacewar ƙifofin glass ne , labarin da aka hasko ne a tv yaja hankalinsu sosai , jin an saki cup a ƙasa sukayi an gurfana da guwaiwa , juyawar da za suyi Ameena ce take uban kuka tana cewa na shiga uku , anga wanan matar a garin Kaduna a gindin gadar bakin dogo tana bara , a gigice Abba ya miƙe bai tsaya saurarar Ameena ba ya fice da gudu yana ƙwalawa drivers kira , cikin sauri suka iso tare da durƙusawa , maza kuje offic ɗin police na kaduna ga adrees ga number waya kuna isa ku kira anga Maimunatu , masha Allah suke faɗi kasancewar duk sun santa , suka ɗibi mota Abba yace" zan dinga kiranku inajin yanayin tafiyar taku , Allah ya tsare Abba yayi musu tare da komowa ciki ya sami Kamil yana ta kaiwa Amenna naushi baji ba gani, A'a meye haka son ? idanun Kamill sunkaɗa sunyi jazur kamar garwashi yace " Abba itace itace ,itace me ? Abba ya tambaya zata gaya maka koma menene , Kamill na saketa tahau cewa " nice na koreta gashi boka ya mutu na rabata da kowa nata na korata gari mai nisa gashi an ganta sai na kasheta sai na kashe ta , ran Abba ne ya ɓaci ya danna number mahaifiyar Ameena tare da cewa " zan sakota a mota a kawota gida zata gai sheku daga haka yayi mata sallama ya nufi bedroom ɗinsa ya fali takarda ya rubuta mata saki uku , ya dawo palo ya wurga mata , akwati ɗaya Abba ya wurgo mata tare da kiran ragowar drivern da ya rage yace " ya kaita bauchi , ihu ta sanya tare da ɗurawa Abba zagi ga dukka halamu sai dai muce inzaka gina ramin mugunta ka gina dai dai kai gudun kar wata rana ya rifta da mai haƙin ramin , tana kuka haka suka shiga mota ga takardar sakinta a hanunta tana ta surutai.
10:pm shiru shiru babu labarin Kamill gashi tana ta gwada waya taƙi shiga , a kira na shida ne ya ɗaga tare da cewa " dan Allah kiyi haƙuri anga Ummana shine ya hanani dawowa , tsalle Diyana ta doka tare da miƙa godiya ga Allah tace " kodai muzo gobe ne ? kibari zuwa jibi kafin nan ta warware sai kizo kiyi1 week cikin farinciki Diyana ta ce a gaisheta sukayi sallama ,Afreeda dake kallo bacci na shirin ɗaukarta tace " sis dafa bakison mijin amma naga yanzu kamar zaku haɗiye juna ? dariya Diyana tasa tace " to ƴar sa ido zomuje mu kwanta jibi zamu wuce kano zaki ko ? zaro ido Afreeda tayi kana tace " ina tsoron dady sai dai in shi yayan ne zai kira ya faɗa , karki damu insha Allah tare ma zamu tafi ki kwantar da hankalinki suka wuce bedroom suka kwanta sai muce asha ta gari.
sai 11:pm drivers suka shigo inda gidan ya turare da ƙamshi iri iri Abba yasa ayi girki girke masu rai da lafiya , shigo da umman Kamill sukayi duk tayi tsufan wuya dama shekaru sun ja , wanka ta shiga a ɗakin da yake nata a da tana fitowa Abba ya shafa mata mai ya sanya mata powder ya ɗauko doguwar riga ƴar kanti fara da ɗankwalinta ya shirya umma tsaf ya fito da ita hanunta riƙe da nashi suka fito palo inda Kamill ke zaune yana hawayen farinciki , ganin umma da Abbansa ba ƙaramin daɗi yaji ba har yana musu photo Abba ne yace " son baka girma ko , ita dai Umma sai raba ido take hankalinta na dawowa jikinta a hankali amma batasan ko waye Kamill ba ,cikin ladabi ya durƙusa yace " umma ina yini , lafiya tace " tana ƙare masa kallo da mai kamada tanason gano wani abu , Abba ne ya katse mata tunani ta hanyar cewa "ɗanki ne Kamill fa , nan da nan hawaye suka zubo a fuskarta tace " Kamilu ashe Allah zai haɗamu ? shima Kamill ɗin kuka yake yaje ya rungumeta .
Diyana ce ta kira dady take sanar masa abinda ke faruwa a gidansu Kamill na ganin mahaifiyarsa da akayi sun tayashi farinciki dady yace " goben idan kun shirya kubiyo ta nan sai mu je mu dubo ta ,
washe gari Diyana da Afreeda sun gama shiri suka fito Diyana ce ta miƙowa Afreeda bag ɗin kayansu kasancewar duk yanayin jikinsu ɗaya kuma Afreeda bata ɗauko kaya ba , suka nufi mota , driver na tada mota suka ce anguwar su za'a kaisu babu musu cikin lokaci ƙalilan sai gasu yai horn aka buɗe suka shige , da gudu Diyana ta shige tana kiran momy , momy dake tsaye da gyale a hanunta batasan lokacin da ta rungume Diyana ba tana murna , Hajiya ce ta fito sanye da hijab a karkace tana cewa in kun gama rashin kunyar kufito muje kar muyi dare , bayan sun gaisa da kowa suka nufi tasu motar da ban Diyana ma tasu daban suka ɗauki hanya zuwa Kano ,sunyi tafiya mai nisan gaske kana suka iso garin kano sai da suja kuma yin wata tafiyar sai gasu a bakin wani tangamemen get wato gidasu Kamill , ana buɗe get suka shige akayi parking kowa ya fito dama Diyana ta gayawa Kamill zasuzo suna shiga da sallama suka sami Abba da umma zaune a kujera ɗaya Kamill na gefe yana dadanna waya , durƙusawa yai ya gaida su dady tare da Hajiya da momy , zama sukayi tare da yi musu murna na ganin umma Abba ne ya dubi Umma yace surukanki ne fa murmishi Uma tayi aka sake sabuwar gaisuwa , tashi ɗaya aka cika musu gabansu da kayan motsa baki, Kamill ne ya fice tare da kashe wa Diyana ido , umma ta lura da komai murmishi kawai tayi , Diyana na ganin Kamill ya fita ta fara shirin kiran wayar ƙarya itama ta fice kaf cikin ɗakin sun gano su amma babu wanda yai magana , Afreeda na ganin basuda kunya, kai tsaye harabar gidan ta fito ta rasa ina zata dosa ya sadata da ɗakinsa , ji tayi an ɗagata sama ana tafiya da ita dariya tashiga yi tana cewa my blood baka ganin masu aiki ne , bai kulata basai da ya sauketa a tsararren ɗakinsa mai sanyin ƙamshi , direta yayi a tangamemen bed ɗinsa tare da raɗa mata nayi missing ɗinki fa , rufe fuska tayi adu'arta Allah yasa kar ya taɓa mata lafiyar jiki , zoki shirya min kaya anjima zamu wuce , no ni bazan tafi ba gurin umma zan zauna , dariya Kamil yasa yace " umma taga Abba sai kuma yai shiru , daga haka suka shiga hirar yadda sukayi kewar junansu .
dady da momy dakuma hajiya ne suka fito da niyar tafiya aikuwa Abba yasa an haɗa musu hidima sosai , umma tayi murna , ganin babu Diyana babu alamarta yasa su wucewa batare da sun nemeta ba.

*After nine months*
Diyana na hango da ƙaton cikinta aihuwa yau ko gobe wata ranar laraba tana zaune taji azabar ciwon baya da mara , hajiya dake zaune a gidan tunda cikinta ya tsufa ta lura da naƙuda take hakan ya sata yi mata adu'a ta bata tasha cikin ikon Allah mai sosai ya fara sai gashi ta santalo yarinyarta mace , fara kyakyawa , gyara baby Hajiya tayi kana ta gyara gurin dakuma mai jego , sai da Diyana tayi wanka Hajiya taga tana cikin ƙoshin lafiya aka kira su momy aka sanar musu dasu Abba da Kamill dake Kano farinciki ba'a magana ranar suna yarinya taci sunan umma gata kam Diyana ta ganshi , motsi kaɗan tayi za'a tambayeta meye , farinciki a famillyn abin sai san barka.
Ansa bikin Afreeda inda ta sami wani ma'aikaci shima yanada kuɗi sosai cikin wata uku akayi biki lokacin yarinyar Diyana ta fara wayo da suke yimata laƙabi da Umaima , ga dariya , biki akayi na manya kasancewar gagarumar gudun mawar da Abban Kamill dakuma shi Kamill ɗin ya bada ranar ɗaurin aure anyi event sosai bikin ya birge kowa ankai amarya cikin Abuja A. Y. A anguwa ce ta manyan mutane gidanta ita ɗaya , sai dai muyi mata fatan Allah ya kawo ƙazantar ɗaki , anan na kawo ƙarshen wanan littafi kurakuren dake ciki Allah ka yafe mana Allah kasa ya faɗakar kana yakuma amfani al'umma bissalam .

Domin neman ƙarin bayani 08141799224.

MOM ISLAM

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment