Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta ya kasance tayi gagawar iya turanci KO test baza'ayi mata ba dan ya fadi gaskiya bata iya komai ba .

Cikin minti talatin ta gama shiryawa ta daure gashin kanta da kyar ta saka hijabin Wanda yake da tsayi sosai domin har ya fi rigar tsayi ta juyo cikin nutsuwa ta fito wajen Hajiya Hawau da ta gama mata abin kari da kuma zuba mata wani a kwano ta saka mata a jakar da kudin abinci idan ta cinye wanan abincin , tana fitowa ta gaisar da Hajiya

Hajiya ta ce" kai kayan nan sun karbeki Ramatutu wly sunyi miki kyau nasan duka sai kinfi yaran kyau


Yar Mahaukaciya tayi murmushi ta ce" Hajiyata kings hijabin harda wajen fitar da hanu


Hajiya ta ce " kema kya fada zamani , tashi mu je muyi jiransa kar ya tafi ya barki ga abincinki komai da komai harda kayan hada shayi idan kinje ki zauna ki karya sanan ki shiga ajin kinji KO?

Ta ce " toh suka fito kofa wajen mai gadi suka zauna suna jiran fitowar Idriss Wanda KO daga baci bai farka ba

Sai karfe bakwai da rabi ya fito shima dan kar aje bata shirya ba suyi lati ranar zuwanta ta farko bai dace ba , yana fitowa ya hangosu Hajiya a zaune a yar tayani tsegumi ita kuwa a tsugune a gefenta ai besan sanda dariya ta kufce masa ba ya ce " aiki ga mai kare ka

Haka ta Mike ta shiga ya tayar suka haura titi suna tafe yana yi mata bayanin yanda zata yi dan karta sha wahala sosai, ya ciro wani kati mai walwali ya Mika mata ya ce" wanan katin cin abincin ki ne na biya na shekarar gaba daya sanan na zabi na biya idan kinje kinada damar duk lokacin da kika ji yunwa ki shiga restaurant ne part VIP ki shiga can ki zabi kalar abinda kike sha'awar ci a kawo miki ki ci ki dan huta kiyi sallah sai ki huce wajen karatun ki , karkiyi wasa da karatun nan naki domin kafin ki fahimci lesson sai kin sha fama tunda baki iya rubutawa da karantawa ba aman da yardar Allah zaki iya harma ki koya min , ya karasa yana murmushi '

Tayi murmushin itama ta miko hanu ta karba tana godiya ta ce" ai kuwa kaga Hajiya har ta zuba min kayan abincina a jaka

Ya kwalalo ido ya ce" to kaji yo ai baza'a barki ki shiga da wani abinci ba gudun karki zo da abinda zai bata miki ciki kuma a tsayar da karatun KO wani ya ci ya bata masa ciki a samu matsala , makarantar nan akoy shegen tsaro dan haka ki kiyaye ki dena zuwa da komai wanan din ma ki juye shi a nan idan kin shiga kya karya , hakan kuwa akayi ta juye komai ya rakata har kofar shiga daidai nan aka tsayar da shi ita kuwa aka caje Jakarta aka rage litatafan aka ware na ranar abinda zasu yi sai wani litafin aka saka mata dan saboda karatun da zata ringa dauka da wasu malaman bayan aji .


[15/10 19:17] Official_Amnoor: [20/9 10:16] Sajida: 🇳🇪Belles écrivaines du Niger



*'YAR 👧🏻*

*MAHAUKACIYA👹*

*_Na SAJIDA_*





20

Haka Yar Mahaukaciya ta shiga cikin makarantar ta nufi office din da aka nuna mata taje ta ja ta tsaya ta shiga rapka salama ta kai wajen minti biyar a nan a tsaye sai da wani dalibi ya zo ya dana wani jan abu sai taga kofar ta bude ya shige ta kwalalo ido tana nan tsaye ya fito yayi tafiyarsa ta lumshe ido tayi bismillah hanunta na karkarwa ta dana jan abun kofar ta ce wani guiui ta bude ai uwa an hankadata ta fada sai zazare ido take tana kifkif da ido


Mutumin dake zaune ya hakimce da shigar manyan kaya a jikinsa gefensa kuwa da wasu mutane sai dadana computer suke gaba kadan da shi kuma jerin wasu mutanen ne suna observing dalibai a computer ita dai tayi tsai tana kalon su yayi gyaran murya ya mika mata hanu da nufin ta bashi takardarta Wace idan tazo zata gabatar a kaita aji a nuna mata komai

Ai gaba daya takardun hanun nata da litatafen da jakar ta ajiye masa saman table din nasa na glass ta ce" wly sun caje ni kosan ma yaya ya juya da shi KO karyawa banyi ba


Nan da nan suka shiga kalon juna , banban na zaune Wanda ke hakimce ya ce" ur name?


Yar Mahaukaciya tayi Kifkif da ido tana kalonsa fuskarta bayane da tsoro kafin tayi magana téléphone din saman table din yayi ringin ya Mika hanu ya daga


Daga dayan bangaren ya ce " tazo KO?

Abdallah mai kula da makarantar ya ce" aa dalibai dai suna ta shigowa har yanzu bamu ga mai sunanta ba aman ga wata tsaye inajin bata iya turanci ba ma


Mubasshir ya ce" what? Na fada maka yar gidana ce kuma akoy abinda ya tsayar da ita ba'a kula da karatunta ba kayi mata hausa idan tazo shine zakana cewa baka sani ba ? Look idan kaga bazaku kula kan karatunta ba na tura a dauko mini ita , karatu KO a Wace kasa take so sai na kaita kuma KO wani kalar malami sai na sama mata ya koyar da ita



Abdallah ya ce " kayi hakuri abin du bai kai nan ba yaya sunanta ne?


Mubasshir ya zaro ido yayi Saurin rufe kan wayar ya kali idriss da ya saka shi a gaba kan a kula kar su banzatar da ita ya ce" kai sunanta fa?


Idriss ya dane dariyarsa ya ce" *RAHAMA IDRISS*



Mubasshir ya yatsina fuska ya kara a kunan sa ya ce" Rahama idriss


Abdallah ya tambayi Yar Mahaukaciya dake tsaye da hausa ya ce" kece Rahama Idriss?


Da Sauri ta gyada kanta ta ce " eh Nice


Abdallah ya ce" sir itace a kara hakuri zata samu kyakyawar kulawa


Mubasshir ya ce " ohk thx ya datse Kiran


Abdallah da kansa ya mike ya raka Yar Mahaukaciya aji Sanan yayiwa malamin bayanin idan ya gama ya nuna mata office din hajiya Amina , ya juya ita kuma ta samu waje ta zauna ta shiga kalon Malan yana ta gwaranci toh gwaranci mana domin ita dai ba abinda take ganewa a cikin abubuwan da yake fada tana dai kalonsa har ya gama ya kaita wajen Hajiya Amina inda ta kwashe awa uku tana koya mata A B C D ......Z, sanan taje wajen cin abinci inda ta sha mamaki kamar ba a cikin makarantar yake ba kuma gaba daya sai daukan ido wajen yake nan taga manya manyan yan mata da samari kowa yana harkokinsa wasu suna ta selfi wasu suna buga gem , wasu suna ta labari, wasu suna zance, wasu kuwa suna jiran abincin su kai wajen ba dai tsaruwa ba ,


Cikin tsoro ta nufi wani table mai shegen kyau Wanda taga ba kowa samansa sanan harda wani rubutu a farar takarda ta nemi waje tayi zamanta da bismillah tana dan yarfe hanunta domin ba komai a hanun ta mugun gaji ne da rubuta A B C din nan , tana zama bata ma gama hutawa ba taji muryar wata cikin turanci na fadin tayi ta tashi ga princess nan zuwa table dinta ne ,


Abinka da Wanda bata san mai take cewa ba kawai sai ta dan sakin mata murmushi ta waiga dan taga inda zata kai katin ta a zuba mata abinci ta ci ta koma masalaci ,

Bata Ankara ba sai ji tayi an daki table din ta dago kanta da sauri tana kalon wace ta buga table din , wangalau tayi da idanuwanta tana kalonta batada KO dan kwali a kanta ta sha kananan kitso na atash sun mugun yi mata kyau , ta kara girar ido sunyi zako zako ta sha lips dinta mai sheki gwanin kyau gata fara kar ta budi baki cikin turanci ta ce " ke yar gidan uban waye harda zaki zo ki dora tsumakaran duwaiwanki a saman kujerarr da ni nake zama?


Yar Mahaukaciya bata kauce idanuwanta daga kalonta da take ba ita mamaki take Kenan ana zuwa makarantar babu hijabi KO dan kwali?


Ita kuwa ganin kalon da take yi mata da idanuwanta kamar na mage kuma ta ki yi mata magana yasa cikin zafin rai ta saka hanu ta ja hijabin Yar Mahaukaciya tana fadin shegiya mai acuci bari na tona miki asirin abinda kike boyewa a hijabin yanzu haka wani kurji ne da ke daidai lokacin gaba daya daliban wajen sunyi ca suna kalonta dan kowa yasanta da rashin mutunci yar gidan embasader ce table dinta ba mai zama mutun daya take shayi shi kuwa yayi kwana uku bai zo makarantar ba shi yasa take taka rawarta yanda take so a makarantar, kuma taga bakuwar fuskar nan tana kokarin kawo mata raini dole tayi maganinta

Da karfi ta idasa Jan hijabin Yar Mahaukaciya harda ribom din da ta daure kanta da shi ya biyo hijabin gaba daya gashinta ya barbazu har gadon bayanta cikin gigita ta Mike tsaye ai kaf wajen suka kwashi waouh domin sai da ta Mike dirinta ya fito ita kuwa baiwar Allah kokarin ganin ta kame kanta take suna tsaka da wanan rigimar chef din cafetariar ta fito itama ta sha ado da masarar Riga a daure a tsatsonta ta fito cikin turanci tana tambayar mai yake faruwa?


Princess da gaba daya jikinta yayi sanyi domin sai da ta raina kanta duk irin tarin adon nan da ta sha kuwa sai taga tamkar wata banza a Yar Mahaukaciya ga kalar gashinta kalar blonde kuma gashinta ne ba atash bane ga tsahi da gareshi ga shegen santsi ga yanayin jikinta da ka ganta ka san daga gidan hutu ta fito ,


Wani daga cikin daliban ya ce" aunty wanan mai kyau ce ta zauna a table din princesses shine princesses take fada

Aunty ta kali Yar Mahaukaciya ta ce" ina katin ki yarinya ?


Yar Mahaukaciya jin an ce kati ta gane na cin abincinta ake tambaya ta juya nan kasa inda ya fadi ta dauko ta mikawa Auntyn ,

Aunty ta zaro ido ta ce" kai princesses kin san da wa kike magana kuwa? Kinsan du wanan gyaran da muke tunda safe na tarbanta ne ? Kinsan KO yar gidan wacece?


Gaba daya suka bada hankalinsu wajenta har Yar Mahaukaciya domin yanzun da Hausa tayi magana don kuwa ta tsorata kar wanan yar masefar princesses din ta ja musu asara dan an hau shegen table dinta , ita kuwa yar mahaukaciya tambayar kanta take to ita kuwa Yar gidan waye harda za'a yiwa yar gidan ambasader fada dan ta taka ta ???




Nima ina son sanin amsar wanan tambayar???????????????????????????????????
[22/9 09:23] Sajida: 🇳🇪Belles écrivaines du Niger



*'YAR 👧🏻*

*MAHAUKACIYA👹*

*_Na SAJIDA_*






21

Princesses cikin karaji ta ce" aunty tell me nace Yar gidan waye ita?


Aunty cikin hausa taci gaba da bayaninta domin an gargadeta tafi son hausa a yaririkan da ta iya ( zuki ) ta ce " Kanwar *MUBASSHIR AA* ce


Gaba daya suka kuma fadin waouh 😳 yar hayaniya ta kaure a wajen wasu suce she is nice , wasu suce daman su , wasu su ce ai da ganin yanayinta yar manya ce

Cikin karaji Princesses ta ce" chut up, i said shut'up , ya ishe ku haka , duk kyanta da takamarta da isarta mai take bamu? Kuma ai ita kanwarsa ce ba yarsa ba , sanan da kuke wani daman ku so what? Ni ni da kaina nake takama kuma takamar wata bata birgeni tunda ba abinda take bani


Aunty ta ce" ni tana bani princesses domin KO wajen nan da ba dan oga AA ba da ban sameshi ba kuma a kan abincin yarinyarnan kadai kika san miliyan nawa ya zuba? Har ta gama karatunta idan kulun zatana cinye duk abinda zamu dafa a nan bazata karar da kudinta ba don haka idan bazaku girmama juna ba kowa ta ja da class dinta ta kama hanun Yar Mahaukaciyya suka nufi wani guri na musaman mai manyan kujeru da kapet da flawer da kaga wajen kasan na manya ne ta zaunar da ita ta ce " to hajiya mai za'a kawo miki?


Yar Mahaukaciya da har yanzu ta kasa gaskata wanan dangorma da aka sha da wanan balarabiyar sunan da tayiwa princesses Kenan tana mamakin wai ita Yar Mahaukaciya itace kanwar Mubasshir kuma tana mamakin irin yanda ake jinjina cewar ita kanwarsa ce , sanan ga wajen da aka tanadar mata dan kawai ta huta , ta lumshe ido a ranta ta ce" Allah na gode maka da wanan ni'ima da ka yi min Allah ka kara rufa min asiri duniya da kiyama sanan ka bayanar min da Mahaifiyata , jin Aunty ta dage tana ta bata hakuri ita tsoro take kar aje tayi fushi ta fadawa AA ya fasa duk abin arzikin da suke da shi


Yar Mahaukaciya tayi murmushi ta ce" ba komai, sanan komai ma ina iya ci aman bana son mai yayi yawa a abinci da kuma yaji


Aunty ta ce " an gama Hajiya aman dan Allah kiyi hakuri kar kiyi fushi ki manta da komai ba saï kin sanar da AA ba


Yar Mahaukaciya ta ce" aa manta ba komai wly


Aunty ta mike tana murna sanan tana mamakin halayar kanwar AA sam bata da girman kai , wani sashi na zuciyarta ya ce ai dan Kudin ba tsinta tayi ba a ciki ta tashi ta ganta shi yasa bai dadata da kasa ba



Cikin ikon Allah Yar Mahaukaciya ta fara sabawa da yanayin makarantar sanan sosai take kara maida hankalinta kan karatunta duk da princesses sai da ta bi didigi ta gane ajin da take ita da kawayenta sukayi tayi mata dariya aman ita KO a ranta bata taba nuna musu tasan suna yi ba hakan na kuna musu rai kuma bata taba fadawa koda Hajiya Hawau ne balatana Idriss

Bayan an dawo daga hutun sallah ne Yar Mahaukaciya tayi kawa mai suna Fati yar adamawa , sosai Fati ke kaunar Yar Mahaukaciya kuma tana kara koyar da ita yanayin rayuwa da irin yanda su yan mata masu tashe masu shekara 17-18 a duniya suke taka rawar su balatana ita da Allah yayi mata baiwar kyau duk da har yanzu boye abinta take aman daga girarta kadai zaka gane ta hadu

Shirye shiryen shiga hutu har na wata guda suke inda sai da suka zana jarabawar karshen shekara fitowarsu Kenan daga aji Yar Mahaukaciya ta zauna tana jiran fitowar Fati , sai can bayan minti ashirin sai gata ta fito ta nufo wajen da Yar Mahaukaciyar ke zaune suka mike suka nufi cafetariat dan su ci abinci sai kuma kowa ya kama gabansa sai bayan hutu

Suna shigowa wata Mariam ta ce" Rams beby please ki dan bamu pass na shiga wajen diner Auren AA manan mu je mu ba idonmu kalaci


Yar Mahaukaciya ta kaleta tayi murmushi bata ce komai ba domin su ita da yar kakarta suna gefe mai suka sani kan harkar auren sa? Ita da rabonta da ta saka shi a ido har ta manta cos kulun tana makaranta idan kuwa ta dawo tuni dare yayi sai karatun isalamiya bata da lokacin kanta ma bale ta san abinda ake yi ashe har diner za'a yi ta dan daga kafada irin kayi zancen zucin nan ka basar

Tina ta ce" na fada miki fa ba zaki samu ba dan kuwa wajen na manyan manya ne aman ni nayi mamaki ma da zai auri wanan yarinyar kinga ita fa ba wata yar masu kudi bace , sanan eh lale ta hadu aman bata da wani jiki motarta ma fa tun wada dad dinta ya saya mata ce ni din nan ma sau nawa ina canja mota yayanta dai docter ne kuma ya hadu ba karya aman shima bashida jiki

Fati ta ce" ke kuwa du a ina kika san wanan labarin?


Tina ta ce" hum irin yanda Nadia Yar gidan gomna ke son bawon Allahn nan ai ita take da labarin komai ai ance asiri ne ma suka yi masa


Fati ta girgiza kai ta ce" koma dai menene tunda maganar aure ta ratsa ai Allah ya saka albarka a ciki dan haka mu munyi nan ta ja hanun Yar Mahaukaciya uwa makaho da dan jagora
Suna zama ta ce" besty tell me


Yar Mahaukaciya ta ce" mai zan fada miki?

Fati ta ce" ana aure a gidan ku shine zaki boye mini ? KO don ni nawa uban bai kai matsayin da za'a dama da ni bâ? Nasan daman ban isa na samu shiga ko cikin gidan ku ba aman ai ki fada min ma ai naga mutuntawa ne KO?


Yar mahaukaciya ta ce" haba besty kinsan kin fi haka a wajena kuma ni da ake cewa wata kanwar sa ce aa ko daya

Fati ta ce" mai kike nufi

Yar Mahaukaciya ta ce" zancen da tsayi aman karki damu nayi miki alkawarin idan lokacin ki sani yayi zan sanar da ke

Fati ta ce" ohk domin ita irin mutanen nan ne da basa son takurawa mutun idan baiyi ba niyar abu hakan yasa ta ja bakinta ta tsuke ta ciro wasu glass biyu farare kar masu shegen kyau kwaya biyu , kalar glass din KO da dare ne saka shi ake KO da rana gashi yana idon mutun aman bai hana a ga yanayin yanda idonka yake domin farin ne ta dauko har kara hasken kwayar ido yake ta mikawa Yar Mahaukaciya ta ce " kingan su wly tsada ne da su kuma so nake idan zamu dawo makaranta da shi zamu ringa zuwa cos yanzu mun zama manyan beby ta karasa tana daga gira tana dariya


Yar Mahaulaciya ta yi dariyar itama ta ce" ai kuwa sai dai idan na saka wanan abin to na saka likaf domin ina mugun jin kunyar fitowa a haka da wanan

Fati ta hade rai 😡 ta ce" malama idan rabuwar fada kike so muyi sai muyi bani kayana ma ki gani

Da Sauri Yar Mahaukaciya ta zuge Jakarta tana fadin " bai kai nan ba hajaju ayi hakuri , su duka sukayi dariya haka suka tayin hirar su har Aunty ta leko ta ce" Hajiya dreba ya zo inji Oga ki taso a kaiki gida


Yar Mahaukaciya ta Mike suka yi salama da Aunty kan Allah ya sake hada fuskokinsu suka fito ita da kawarta mai daukar nata har cikin makarantar ya shigo ta shiga sai kara bye suke yiwa juna du taji ba dadi a ranta aman ya ta iya hakane daman sabo tirken wawa


Suna isowa ta sauko daga cikin motar ta nufi wajen su tun a tsakar gida ta cire hijabin ta shanya shi domin du ji take hana kanshi tiraran Mariam din nan da ta rungume ta , kuma ita bata son tirare mai karfi

A nitse ta nufi falon su tana fadin Hajiyata an bamu hutu Hajiyata shikenan kin denan wuni ke kadai , maganar ta tsaya mata a makogwaro lokacin da ta hango Idriss zaune ya dawo daga tafiyar da yayi wajen wata guda Kenan , bata san lokacin da ta yarda jakar hanun nata ba ta tafi da gudu kamar karamar yarinya tana oyoyo yayana oyoyo yayana

Shi kuwa gaba daya da bakin da hancin ya saki yana kalonta har ta zauna saman kujerar da yake zaune tana ta kyakyata dariyar ganinsa abinda bata taba yi ba Kenan a tsawon zaman da suka yi Kenan ita ma tayi missing dinsa kamar yanda ya kasa zama ya karasa aikinsa dan dokin ya dawo ya ganta


Hajiya da take tsaye tana dariyar itama kuma tana mikawa Mubasshir kwaryar furarsa Wanda shima ya shagalta da mamakin to du murnar nan da take yi ta mainene? Daman haka dariya ke yi mata kyau ?

Muryar Hajiya ta dawo da ita inda ta ce" yau dai mita ta kare kulun ki sakani a gaba da rigima wai nesa ne ka tafi? Ita nayi mata kwatance ta je ta kawo ka

Gaba daya suka kwashe da dariya banda Mubasshir Wanda lokaci daya yaji gabansa na dukan uku uku

Ita kuwa Yar Mahaukaciya sai a lokacin ta ganshi zaune itama gabanta ya fadi dan gani tayi ya kara wani girma hanayansa du da tsintsiyarsu kawai ake gani aman jijiyoyin dake konce a jiki suna Nuna alamar kakarfen namiji ne , sanan farin sa har wani yelow yelow yake yi KO don ya saka shada ruwan duhu ce ga sagen nan nasa masha Allah baki sidik , ai nan da nan ta dan kwashi karkarwar da bata san KO ta meye ba , ta shiga kame kame ta ce" am am yaya ina zuwa bara na canja uniform dina ,
Ta mike tayi ciki da sauri har kafafuwanta na hardewa


Hayiya ta ce" Yata kenan sarkin kunya zumudi ya sha'afar da ita ta manta ba hijabin sai yanzu ta Tina

Idriss ya ce" Hajaju Yar taki ta girma fa masha Allah


Hajiya ta turo dan Kwali gaba ta ce" eh hakane kana gani matar gidan gwomna sak tafi karfin docter


Idriss ya zaro ido ya ce" ai kuwa Na shiga siyasa daga yau , abokina zaka jefa min kuri'a KO?

Mubasshir yayi wani malalacin murmushi bai ce komai ba ya kurbi furar da iyakarta makogoransa domin kwakwaluwar tasa ta tafi duniyar tunani bata baiwa makogwaronsa damar isar da furar cikin cikinsa ba , tambayar kansa yake" wacece ita? Wai wacece ita?






I don't know *Honorable*
[23/9 09:04] Sajida: 🇳🇪Belles écrivaines du Niger



*'YAR 👧🏻*

*MAHAUKACIYA👹*

*_Na SAJIDA_*




22

Taba kafadarsa da Idriss yayi shi ya dawo da shi daga tinanin sa kuma har karar hadiyar furar da ya kurba wani kwadak,


Idriss ya ce" kai namiji yaya dai , wly kasa harkar auren nan sosai a ranka na fada maka komai zai zo cikin sauki ka yarda da ni ,


Mubasshir ya ce" kai ina hajiya yana waigawa dan bai ma ji lokacin da tace bara ta nunawa Yar Mahaukaciya dinkunanta na auren Mubasshir , Wanda idriss na dawowa sai da ya karbo a wajen tela sanan ya karaso gida ,


Idriss ya bushe da dariya ya ce ta shiga wajen Zuciya


Mubashirr ya gala masa harara ya ce" Malan da Allah ka dan rufe min baki haka na samu na ci abincina cikin nutsuwa baka ganin du na rame ?


Idriss ya ce " ka rame fa, haba dai ai masu irin jikin ku basa ramewa , kirar samudawan? Ai ku kulun kara ku ake

Mubasshir yayi murmushi yana kurbar furarsa



Cikin daki Hajiya ce da Yar Mahaukaciya idan ta gwada wanan ta cire ta gwada wancen dan gadaranci shada ma harda ta wajen angwaye ya dinka mata, ga na wajen yan matan amrya masu ji da kansu , ga na diner Wanda kudinsa kadai abin kama kai ne , kuma dukansu anyi mata dinkuna masu kyan gaske , ta warware doguwar bakar rigar da yan matan zasu saka da dare wajen diner rigar ita kadai dubu hamsin ake siyar da ita a kwari harda Jakarta da kuma takalminta , wanan rigar kaf cikin kayan tafi kowace shiga ran Yar Mahaukaciya , dagata take tana karawa banda murna ba abinda take tana fadin Alhamdulilah , Hajiya kuwa tafita murnar domin har dan asusu ta shiga yi dan ganin ta samu KO na safe ta dinkawa yarta itama , sai gashi Allah yayi gaba daya ankon kala tara an kawo mata harda Karin na wajen maza ,

Hajiya ta jayo akwatin

Please Login or Register in order to submit comment