Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kasance Doguwwar mace fara ga shegen kyau masHa Allah ga iya Jan aji ga yanga kai Sahla da ba dan halayenta ba sai nace goma ce cifffffff sai dai kashhh irin wanan gata da ta samu ya saka bata ganin kan kowa da gashi , baba KO karami zata takaka san ranta domin tasan abinda ta taka


Abinda ke hadasu fada da Hajiya Hawau irin yanayin shigarta da kuma sangartar ta idan fa hanya ta hado su sai dai ita ta rakube ta fice sanan ita ta fice hakan yasa sam basa jituwa suke yar tsama , hakan nayiwa Hajiya Marhaba dadi domin taki jinin sirikar tata abu ya hana tayi maganin ta Elahj domin yana matukar kaunar jangom lakabin da take kiranta da shi Kenan ( ya Allah ka tsare mu amin )

Abu daya yake saka Sahla dan sadakawa soyayar Mubasshir da ta wayi gari ta tsinci kanta a ciki tsundum hakan yasa take dan rage wasu abubuwan a cikin halayenta domin shi bazai lamunci rashin mutuncinta ba idan kuwa ta rasa shi tasan ta tafka asara ( tofah )




Ci gaban Labari


A hankali ya aje furar domin sai ya deba da niyar kaiwa bakinsa sai ya mayar da ludayin yana matukar son ya sha furar nan kyankyaminsa ya hana shi ya sauke ajiyar zuciya ya mike yana saita agogon hanunsa ya dan dubi Sahla kasa kasa ya ce " ki kaiwa hajaju furar nan ki fada mata na koshi , sai tomorrow ya juya ya saka kansa gaba yana tafiya cike da isa tamkar dan Sarki


A hankali tana kalonsa har ya fice daga harabar gidan ta sauke nanauyar ajiyar zuciya ta lumshe idanuwanta ta ce " i love you My man i really love u ta kuma lumshe idanuwanta ta ce " zaka soni ne a hankali domin nasan dan ni kadai aka yi ka , ta Mike ta saka kafa ta shure furar harda hararan kwaryar tayi waje ta nufi motarta dan tasan a yanzu ya bar unguwar tana iya fita









😌😌😌😌😌😌😌😌😌
[9/9 20:15] Sajida: 🇳🇪Belles écrivaines du Niger



*'YAR 👧🏻*

*MAHAUKACIYA👹*

*_Na SAJIDA_*









12


Karar tashin motar Mubasshir ya saka Hajiya ta fito , tana fitowa tayi arba da furar a kife a kasa ludayin a yashe , ran Hajiya ya gama baci domin ita irin mutanen nan ne masu baiwar ji , idan dai kayi magana tana kusa da izinin Allah zata ji abinda ka fada ta duka ta shiga tatare kwaryar furar sai ga Yar Mahaukaciya da Idriss sun fito


Idriss ya ce " toh ikon Allah iyancy wa ya barar da furar dan Gatan naki?


Hajiya Hawau ta watsa masa harara ta ce " zan kifeka a wajen nan idan ka kuma kirana da iyancy tunda ni ba yare bace , kuma da kake maganar Wanda ya zubar min da fura ai yar gwal ce ta zubar , aman ba komai hatsi ta wulakanta shi kuwa Allah ya hane mû da wulakanta abinci Allah ya shiryeta


Idriss yayi sanyi ya duka ya karbi kwaryar da ludayin ya nufi gidansu da Sauri har yana harde kafa , ita kuwa Yar Mahaukaciya ta kama Hajiya Hawau ta zaunar saman kujerar da Dan Aljannah ya tashi ita kuwa ta dauko wani kwanon da koshiya ta tsuguna ta debe sama saman furar ta gyara Wanda bazai kwasu ba ta dawo ta zauna ta shiga shan abinta , Hajiya Hawau tayi murmushi a ranta tana fadin duk inda yarinyar nan ta fito yar girma ce ,,,,,



Cikin bacin rai ya nufi cikin gidan daidai Sahla zata fito da motarta ya yayi Saurin shan gabanta wani irin kiiiii kake ji karar taka birki ya saka hanu ya bude murfin motar kafin ta fito ya shako kwalar rigarta ya cirota daga cikin motar ya daga hanu ya kifa mata mari sanan ya daga kwaryar furar da abin furar a ko'ina ya juye a saman kanta yayi mata tamkar hula ,


Wani irin ihu da kuka da ta saki shi ya janyo hankalin Hajiya Marhaba dake hakimce tana kalo , kafin ta fito Sahla ta fado dakin da gudu tana ihun ta mutu ta lalace


Hajiya Marhaba ta riketa cikin tashin hankali tana tambayarta lafiya? Mai ya sameta ? Faduwa tayi ne? Jin karnin nono yasa ta lakato abin furar ta zaro ido ta ce ubanwa ya zuba miki fura a jiki bayan yasan kin tsani nono a rayuwarki? Fada min uban wanene ya aikatawa yata haka?



Idriss ya shigo ya harde hanu ya ce' ni ne nan momy ni na kifewa wanan yar furar nan


Hajiya Marhaba ta zaro ido ta ce" son kana hauka ne? Mai sisternka tayi maka ? So kake ka kashemin ita ne? Why zaka dauki irin wanan matakin a kanta?



Idriss ya ce"" Momy please Ki dena daurewa rashin mutuncin yarki gindi ki dena bata Goyon baya , yanzu dan tsabar rashin tarbiya ta dauki furar da Iya ta dama ta zubar? Sa'arta ce ita?


Ran Hajiya Marhaba ya gama baci jin wai dan an zubar da furar wancen jangom din ne aka taba mata lafiyar ya cikin kunan rai ta ce " dan Uwar ubanka ta zubar din , KO ita Hawaun ta zubar sai mai? Son ka kiyayi rashin mutuncina ka kiyayi bacin raina ,kan beby ina iya aikata komai ka guji bacin rana son, kuma ita din sai nayi mata abinda tunda tazo duniya ba'a taba yi mata ba shirmen banza shirmen wofi dan taga ina daga mata kafa shine zatana kokarin hada min maseefa tsakanin yayana? To ni da ita shege ka fasa hauka kawai ta ja hanun Marhaba suka haura sama dan ta wanke mata furar da Idriss ya kifa mata a jiki sanan ta dauri aniyar ganin bayan Hajiya Hawau ta dau alwashin cikin su biyu sai dai daya ta kai labari ( toh Fa wai uwar mijin ce haka , ta Haïfa ta yaye ta tarbiyantar ta nemawa yaron ilimin ya girma ya zama wani ya auroki kuma wai ki mayar da uwar banza , ya ilahi , Allah ka raba mu da sirinkan banza amin)



Idriss yaja dogon nunfashi ya lumshe idanuwansa a ransa ya ce " ya Allah ka shirya min mahaifiyata , Allah karka dauki ranta a cikin wanan hali nata , ya ubangiji ka shirya min ita , ya juya ya nufi dakinsa dan ya shirya ya fito yaje su gama shawarar su shi da Ramatu ( Yar Mahaukaciya )




Karfe hudu na yama bayan sun gama girkin su suna zaune suna taba hira Idriss yayi salama yaje ya zauna kusa da Hajiya Hawau ta kashe mata ido daya yace yaya dai madame naga kinci goron baki goge bakin bafa ,


Hajiya Hawau tayi dariya itadai tana son jikan nan nata ta ce " yo ai nafi kyau a haka kaga idan naci goro bai zubo ba har dan kantsa wani nake na dan zuzubo shi yafi kyau



Idriss yayi dariya dan baya so su bata da ya fadi sunan nata wato Iya yanzu zasu hau sama su fado ,

Ya ce " kakus ni kuwa ina son kara sanin yarnan taki fa


Hajiya hawau ta kali Yar Mahaukaciya ta ce " o Ramatutu yayanki na magana


Yar Mahaukaciya ta kale shi ta ce " na'am?

Idriss ya ce " nace a karatu daidai ina kika tsaya? Karatun islamiya, da kuma na boko?


Yar Mahaukaciya tayi fiki fiki da ido tana kalon sa ,

Idriss ya kuma maimaita tambayar sa yana kalonta , ta sada kanta kasa ta shiga wasa da yar yatsarta karama


Carab Hajiya Hawau ta ce " ai kuwa yaron nan inajin yar tawa bata da KO daya ,


Idriss ya kaleta fuskarsa cike da mamaki ya ce " aa fa a wanan zamanin da ilimi ya yawaita ya zagaya KO ina ace mace kamar wanan duk da da alama bata fi shekara 17 ba aman ai bai dace ace kamar ita batayi karatu ba , ai KO ba na bokon akoy na arabi KO?


Yar Mahaukaciya dai kanta a kasa bata ce komai ba


Idriss ya sauke nunfashi ya ce kina da shekara nawa akayi miki aure?


Yar Mahaukaciya ta dago kanta cikin sanyin muryarta da mugun sanyin jiki domin sam bata son karyar da zata yiwa mutanen da suka sakata a inuwar su aman ya zatayi , tana gudun su koreta domin a yanzu tana mugun tsoron waje da gida ,

Cikin mutuwar jiki tace" iyayena sun mutu tun ina karama na hadu da mahaifin yarona aka daura mana aure a bola shima talaka ne bashi da komai hakan yasa muka shigo nan garin dan mu samu na abincin mu , tayi tsai dan ta kara Tino wani abin taci gaba da fadin , muna zaman mu lafiya ya fara rashin lafiya har Allah ya amshi ransa , daman cikin gidan haya ne muke zaune shine suka koremu na fito ina neman hanyar da zata maidani bola aka bige min yarona ta fashe da kuka ,

Hajiya Hawau ta jayota jikinta tana share mata hawayenta ta ce " bana hanaki kukan nan ba? Na fada miki Nice mamanki KO? Maza dena kukan KO ni ma nayi


Yar mahaukaciya ta kontar da kanta saman cinyar Hajiya tana ajiyar zuciya , Idriss ya lumshe idanuwansa ya ce " toh aman da mai kike sallah?


Yar Mahaukaciya ta ce " yanda kuke yi ni ma haka nake yi


Idriss ya ce ina nufin mai kike karantawa idan kina sallah


Yar Mahaukaciya ta gyara zama ta fara sisisusus da dan bakinta ,


Idriss ya zaro ido ya ce " meye sisisisiisis


Ta ce " ai haka su saratu suke yi idan naje yi musu wankau

Idriss ya girgiza kai ya ce " am kakus idan na fita zan yiwa Malan yunusa magana ya zo ya fara yi mata karatun islamiyar , salarta da komai kafin nan zan samo mai lesson shima ya fara yi mata kafin na gyara takardunta sai muga yanda za'ayi


Hajiya hawau ta washe hakora ta ce" kai Allah yayi maka albarka dan nan Allah ya biyaka da jannatul firdauss


Yar Mahaukaciya ma ta dago kanta da murmushi konce a fuskarta sai da gabansa ya fadi domin ba karamin kyau murmushin yayi mata ba ta ce " na gode yayana Allah ya biya


Idriss ya mike yana fadin ki saka hijab ki zauna cikin shiri da KO wani lokaci zai iya zuwa ya fice daga gidan









I'm back😁
[9/9 20:15] Sajida: 🇳🇪Belles écrivaines du Niger



*'YAR 👧🏻*

*MAHAUKACIYA👹*

*_Na SAJIDA_*









13

Karfe biyar da rabi Mai gadi yayi salama ya gaida Hajiya Hawau ya sheda mata ga Mutumin da Idriss yace a bari ya shigo idan ya zo ,


Hajiya hawau ta amsa masa ya juya inda aka yiwa Malan yunus shinfida a banban falon dakin Hajiya Hawau a nan za su ringa yin karatun kulun har ita hajiyar ,



Cikin ikon Allah kulun sai Malan Yunus Ya zo da yama sunyi karatun arabi da Yar Mahaukaciya yau har sati uku Kenan sosai take fahimtar hukunce hukunce na musulunci gaba daya , domin kowace rana akoy abinda zasu karanta sanan a kulun sai yayi mata wa'azi sosai sosai , sai yanzu ta san cewar itama mutun ce mai daraja domin an haliceta a jinsin bil'adama , idan yana bata tarihin manzanin mu da irin yanda suka sha gwogwormaya dan yada adinin musulunci sai taji wani irin shaukin adininta taji wata irin soyayar adininta taji haushin shekarun da ta shafe a bola bata zuwa ta saurari karatu koda yaran na tsokanar ta ,


Bangaren Malan Yunus yana matukar jin dadin karatu da Yar Mahaukaciya domin idan yana koya mata karatu tana bada hankalinta gaba daya ga saukin daukan harda domin akoy tambayoyi sosai kan du abinda ya koyar da ita


Yau ta kama alhamis tun da safe Yar Mahaukaciya tayi aikace aikacenta ta gama ta dora girkin su karfe biyu ta sauke komai har jus jus dinsu da suke hadawa ta gama ta saka a frij Hajiya Hawau sai aikin sanu take jera mata , sai da ta gama taje tayi wanka ta fito ta daura zaninta ta zira rigarta na atampa ta fito ta nufi falo wajen hajiya Hawau


Tana shiga ta zauna kasa , saman kapet wanan na daya daga cikin al'adunta sam bazaka ganta saman kujera idan baban mutun na sama ita sai dai tayi zamanta a kasa koda kuwa ka tashi tana matukar jin kunyar hawa wajen da ka tashi



Hajiya Hawau ta dago kanta daga kalon da take tace : taso maza yau na kunce miki kitson nan da na yi miki uwa mai takaba


Yar Mahaukaciya tayi murmushi ta matsa kusan Hajiya Hawau ta kunce daurin dan kwalin kanta Hajiya Hawau ta kama tsifa

Suna tsaka da tsifar Docter Idriss yayi salama ya shigo cikin falon da Sauri Yar Mahaukaciya ta shiga kiciniyar kwace kanta don ta rufe domin KO hijab babu a jikinta gashi rigarma ba zumbuleliya bace


Hajiya Hawau ta kama baki ta ce " ke zauna min kaji min yarinya to dan wanan dan neman ya shigo shine zakina kokarin ganin kin kwacen kanki? To ba yayanki bane shi din?


Idriss ya zauna ya ajiye jakarsa baka da alama daga office yake , ya dago kansa ya ce " Iyancy mitar mai kike yi ne?


Hajiya Hawau ta turo daurin dan kwalinta gaba ta kankance idanuwa ta nuna masa yatsarta ta ce " Kai wanan yaro ka kiyayeni , ka FITA a idona na rufe aradu zan kai kararka wajen ubanka dan ni din nan da kake gani daidai nake da kai



Idriss ya bushe da dariya har yana rike ciki ya ce " haba Madame haba madame mai yayi zafi kiyi hakuri kin sani sarai ke din ta kudin ce KO?



Ta kuma turo bakinta , Yar Mahaukaciya tayi murmushin diramar Hajiya da jikanta ta dan juyo fuskarta ta ce " Yaya ina yini ya aiki


Idriss da sai yanzu ya lura da ita domin da ya shigo ya ji dai hajiya Hawau na mita aman bai san mitar mai take yi ba , ya amsa salamarta idanuwansa a saman tarin gashin kanta da ake kuncewa

Ya ce " Hajiya wai atach ne yar taki tayi?


Hajiya Hawau ta ce " Allah ya kiyashemu da Karin gashi, ai gashinta ne ba wani atach


Idriss ya zaro ido ya ce " Aman ya naga uwa na nasaru wanan kalar gashin ai ba na hausawa bane kinga fa ja ne ga tsayi aman kina yi masa shampo KO ?



Yar Mahaukaciya ta dago kanta idanuwanta yana mage ta saukesu a fusfar idriss ta ce " YAYANA kuma mainene shampo?



Idriss ya hadiyi wani yau da ya tsaye masa a makogoronsa a ransa ya kara yarda tabas Ramat ba bahaushiya bace to aman wai ita wace yare ce?


Ya ce " hajaju ki bar kan nata mana na kaita saloon a wanke mata idan mun dawo sai ki dadaure mata


Hajiya hawau da daman hanayenta sun gaji sosai ta ce " to dan Albarka Ramatutu tashi ki dauko hijabinki ku tafi a wanke miki da abin wankewa kinji ?



Yar Mahaukaciya ta mike tana dan jan rigarta dan ta rufe mata jikinta aman ina da Sauri Idriss ya kawar da kansa daga dubanta yana fadin a'uzubilah yana kawar da kansa ,



Ta dauko zumbulelen hijabinta ta zira Idriss ya bar jakar Ma'aikatan NASA a nan suka shiga mota


Daidai zasu FITA daga harabar gidan sai ga Sahla da kawarta Alisha sun shigo suna shan kidan su ran Sahla ya gama baci domin wanan ai zubar mata da mutunci ne Idriss yayi niyar yi ya zai dauko wanan bagidajiyar a motarsa kuma gashi kawarta Alisha ta gani ga irin yanda Alishan ke maseefar son Idriss din



Alisha ta waigo ranta a bace ta ce """"""""""












Love u



[15/9 14:03] AMNOOR😍: [11/9 13:10] Sajida: 🇳🇪Belles écrivaines du Niger



*'YAR 👧🏻*

*MAHAUKACIYA👹*

*_Na SAJIDA_*








14

Alisha ta waigo ranta a bace ta ce " masoyiyar mai idanuwana suke gane min ? Wacece wanan kuma? Mai dinsa ce?



Daidai Sahla na kokarin yin parking tace" no karki kula wanan shirmen kinsan brother da tausayi , kuma wanan mai aikin wancen tsohuwar ce nasan ita zata ce sai ya kaita ta sayo mata wani abin ,



Alisha ta ce " kuma sai su layu a waje daya da ita kamar wata sa'ar sa?



Sahla ta ce " kinga karki batawa kanki rai a banza idan ta koma baya ya zama direbanta Kenan fa ? Dan haka manta ni zanyi maganin su



Alisha tayi murmushi ta ce " shi yasa nake sonki kawata




Sahla itama tayi murmushin ta ce " muje ki tayani shiryawar kinsan da kowani lokaci yana iya shigowa shan furar wanan jangom din , kinga kuwa mun dade bamu haduba ya dace ya gani tamkar sabuwar Amarya , sukayi shewa suka tapa suka nufi cikin gidan su Docter Idriss





Sun danyi tafiya mai dan nisa domin yafi son ya kaita wajen wata kawarsa da suka fara karatu tare kawai ta dena taje ta karanto saloon ba abinda bata iya ba , sosai ta kware a fanin gyaran kai kafa hanu make up da dai sauransu ,


Suna isa ya daga wayarsa ya shaida mata cewar gashi yazo da kanwar sa za'a yi mata gyaran kai ,cikin murna ta ce " ku shigo mana





Suka bude suka shiga , tunda suka shiga Yar Mahaukaciya ta saki baki da hanci tana kalon ikon Allah gaba daya ta sha'afa , a ranta fadi take kai duniyar nan bazata dena firgitani ba , wani abin idan ka gani uwa ba dan Adam bane ta saka shi ,



Idriss suka gaisa da Amina cikin raha , yayi mata nuni da Yar Mahaukaciya yace " itace



Amina tayi masa kalon tuhuma a ranta tana fadin wanan ce kanwar tasa, to yaushe momynsa ta haifeta, aman sam bata kama da yan gidansu Allah yasa dai ba budurwarsa bace cosss nafi kowa sonsa a duniya ( to kaji )




Tunda ta bude kan Yar Mahaukaciya mamakinta ya karu haka ta dage ta kunce sauran kitson sanan ta raba shi gida shida ta shiga shafa princess a jiki sai da yaci gida biyu ta gama ta barshi ya kama , shi dai Idriss yana ta dadana wayarsa , ya kai minti ashirin sanan ta saka roba ta wanke mata shi tas ta dauko abin cask ta dadaura mata manyan sanan ta Sakata a cikin cask din , da farko Yar Mahaukaciya har gyara zama take taji sanyi sanyi na ratsata daga baya sai wata iska mai shegen zapi ta ce bismillah haka ta cije kebenta ta daure har ya bushe , Amina ta kashe ta saka banban macaji tana caje mata kan



Ta kali Idriss ta ce " wani kala za'ayi mata?



Yar Mahaukaciya da take jin dadin kanta domin iska ta ko'ina ratsata take ta ce " kitso za'ayi mini manya




Amina ta zaro ido ta ce " ai wanan gashin ba kalar kitso bane kalar ayi paking da shi ne ya sha gyara aman kitso ai ba NASA bane



Idriss ya ce " kawai daure mata shi yanda ya dace , am wa'incan dogayan rigunan bakake naki ne?




Amina ta ce" eh nawane ta shiga daukowa bayan ta daurewa Yar Mahaukaciya kanta da ribom , Idrisss ya daukarwa Yar Mahaukaciya kala biyar ba ta kasa da dubu ashirin a ciki kuma gaba daya masu shegen kyau ya biya suka juya gida








Suna isa gida Direct gidan kakus ya shige da motarsa suka kwashi ledojin sukayi ciki da su , suna shiga Hajiya Hawau tayi musu oyoyo suka shige falonta inda ta shiga bubude kayan da Idrisss ya siyowa Yar Mahaukaciya ta dago kanta ta kaleshi ta ce" kai aman kayan nan sunyi kyau masha Allah sai dai duka bakake ne dan nan



Idriss ya ce " ai ana dorasu saman kaya ne sai a nada mayayi a saman kai sosai suke yiwa mutun kyau



Hajiya hawau ta ce " Yar albarka tashi ki saka daya na gani dan karmu tashi fita na rasa yanda ake sakawa shi kuwa aje bayana tana fada tana mikawa Yar Mahaukaciya daya a cikin rigunan , ta Mika hanu biyu ta karba ta nufi dakinta da ita



Tana shiga sai da ta dan kara watsa ruwa domin bata son rigar tayi dauda KO kadan sai dai ribom din nata ya kunce gaba daya gashin ya bazu a bayanta , tayi tayi ta daure aman ta kasa dan bata iya yanda akayi mata a saloon din ba , a hankali ta ware rigar tana bismillah ta saka pant ta zira rigar da bismillah domin bata gama hadace adu'ar saka sabin kaya ba , ta kama yar igiyar jiki ta daure ta dauko dan kwalin kawai tayi masa uwa ganmo a kanta ta juya a hankali ta nufi falon wajen su Hajiya Hawau





Tunda ta karaso kusan falon ta hangi keyar mutun lupluplup da kashi konce ita a tunaninta ma mace ce , sai Hajiya da ta hanga sai washe hakora take , kunayenta suka tsinto mata Hajiyar na fadin" Kai Dan Aljannah gaskiya kun jima a tafiyar nan fa ai kunyi wata KO




Cikin muryar tasa mai cike da yanga ya ce " aa kwanan mu 23 kadai bamu jima ba



Idriss ya ce " ai kuwa garin ya karbeka mutumi na




Hajiya tayi carab ta ce " i ka rigani a fili dan nan na rigaka a zuci



Idriss ya girgiea kai ya ce " kakus Kenan shi kuwa Mubasshir murmushi kawai yayi ,



A hankali ta juya zata koma dakinta ta sako hijab Hajiya Hawau ta ganta ta ce " Yar Albarka zo mana naga rigar




A hankali kamar Wace Kwaï ya fashewa a ciki ta juyo ta nufo cikin falon , cikin siririyar muryarta tayi salama daidai Sahla ta dano kai da yar SALAMARTA cikiciki ta bangaje Yar Mahaukaciya da haushin ta shiga motar yayanta , Dan kwalin Yar Mahaukaciya ya fadi kasa gaba daya gashin kan nata ya gama fitowa sai sheki yake ga kanshin mayukan kai a tare suka dago suna kalonta kafin ta kai kasa Idriss ya tarota a jikinsa



Gaban Mubasshirrrr yayi Mugun faduwa a hankali ya sauke idanuwansa kas yana kalon Babar yatsar kafarsa



Ran tsohuwa yayi kololuwar baci ta nuna Sahla da yatsa ta ce """"""









💋
[11/9 13:12] Sajida: 🇳🇪Belles écrivaines du Niger



*'YAR 👧🏻*

*MAHAUKACIYA👹*

*_Na SAJIDA_*










15


hajiya hawau cikin bacin rai ta nuna Sahla da hanu ta ce " ke yarinyar nan kin fiya neman magana , shin yaushe zaki fara mutuntani ne? Ki tuna ni fa na haufi mahaifinki aman kashinki yafini daraja , ta girgiza tana kama hanun Yar Mahaukaciya ta juya ta ce " Idrissu karka ce mata komai ka barta duniya ce , ta kuma juyawa wajen Mubasshir da ita ya kurawa ido bai taba ganinta a irin wanan halin ba tabas KO wacece wanan tanada baban mukami a wajen Hajiya ,


Hajiya ta hade hanayenta biyu tana kalon sa tace" Yarona dan Allah karka hukuntata dan ta batamin ka barta ta hukunta kanta da kanta , ka BArTA ta gane cewar mutun yafi kudin nan nasu daraja , ta ja hanun Yar Mahaukaciya suka nufi kicin



Gaba daya jikin Sahla yayi sanyi

Please Login or Register in order to submit comment