Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tare da yin bismillah ya fara shan yaourt din da Sahla ta kawo masa yana tunanin yanzu koda gubar ce haka zata didika masa ya sha,

Har ya kusan shanyewa sai ya gumtse à bakinsa ya tare da hannunsa ya cire kofin ya jawota jikinsa ya hade bakinsa tamkar zaiyi kissing dinta

Idannuwanta ta zaro Jin ya zuba mata yaourt din da nufin itama ta sha,
Da sauri ta janye kanta tayi bayi da gudu tana kokarin amai domin har ta hadiye wani,

Murmushi ya saki ya Mike a nitse ya bi bayanta ya jingina kansa da jikin bayin sai da ta gama amanta sannan ta juyo,

Gabanta ne ya fadi ganninsa à tsaye yana kalonta

Mubasshir yayi yannayin damuwa ya ce" Sahla Lafiya ? Kyankyamina ne kike ?


Da sauri Sahla ta zaro ido ta ce" kyankyaminka fa ? No wly KO daya


Mubasshir ya tsareta da ido ya ce" to ya akayi kike kakari haka ? KO dai kin hadiye wani Abu à ciki ne ? KO da wani abin à ciki ?


Sahla ta kuma zaro idannuwanta tamkar mujiya ta ce" wani irin da wani abin à ciki ? Kana nufin zan saka maka wani Abu da zai cutar da kai ne ? ( abinka da marar gaskiya)


Mubasshir ya yatsina fuska ya matso kusanta, sai da ta dan ja da baya domin duk ta tsargu da kanta, hakan ya sa ya wayance ya kamota gaban miror din bayin ya dora kansa saman wuyanta da wata murya ciki ciki yana shafa mararta ya ce" relax, relax, nifa du ba can nayi va, Ina dai mamakin yanda à Yau kike guduna, Ina mamakin daga na zuba miki abin bakina Kin zabura Kin tofar, dole tsoro ya shige ni kar aje KO kin rage sona ne, KO kuwa bakina yake wari ban Sani ba ?



Sahla da wata irin kasala ta gama rufeta har lumshe idannuwanta take ta ce" bana son shiga hakin Yar uwata ne, husband ita ce da kai, bana son ka tashi da shanyayen jiki gobe kiyama


Mubasshir ya lumshe Idannuwansa yana sauraron tatsuniyar munafukar matarsa, à hankali ya ce" are u prégnant ?


Da sauri ta bude idannuwanta domin tamkar ya buga mata guduma ne, Yau du wani iri take ganinsa tamkar ya san abinda ta aikata sai faman kawo mata sirin da daga ita sai mahaifiyarta suka Sani, cikin wani irin yanayi ta janye jikinta sannan ta kakaro murmushi ta ce" bafa zan biye maka ba, mu shiga hakin baiwar ALLAH, dan haka mu tafi Nayi maka rakiya kar lokaci ya kure


Mubasshir shima ya mayar mata da murmushin ya ce" ban taba gani KO Jin labarin matar da aka yiwa kishiya take zumudin raka mijinta dakin amaryar tamkar Wanda take fatan ta rabu da su ? My baby kiyi kokari ki samo cikin bebyna Nayi miki alkawarin gaba daya dukiyata da na malaka ta nan Lagos da sunan ki, kafin yarona ya Zo sai na dawo da dukiyata ta makah nan


Sahla ta zaro ido ta ce" Da gaske ?? Sai kuma ta wayance ta ce" ai yanzu ni bazan yarda ayi haka ba Tunda mu biyu ne, dan haka muje Nayi maka rakiya, sannan Ina son raka angona ne dan na samu rabauta sannan na kafa tarihi



Mubasshir yayi murmushin yake ya taba kuncinta ya ce" Tabas kin kafa tarihi, sannan ya shige Sahla na biye da shi tana ta yauki



suna shiga bangeren Yar mahaukaciya sai da gaban Sahla ya fadi, domin fadin tsaruwar falon ma Bata baki ne,

Mubasshir ya mika hannunsa ya kamo na Sahla domin sai wani dari dari take, haka suka ratsa falon na farko suka nufi dakunnan, daki na uku ne nata ya saka hannunsa à hankali ya bude kofar


abin mamaki maimakun su tardo amarya à lulube cikin rufa na amare, à tare suka wangame baki Wanda ya saka nima na waiga wayan nawa ya kufce ya fadi kasa da sauri na rarumo wayar don na dauko muku dalilin firgitarmu


Fadimatul Islam ce tsaye tana dadage tana faman sai ta dauko wani Abu à saman werdrob dinta , ta sha damamen bakin wando sidik mai santsi sai daukar ido yake, da Riga mai kamar jikin mage gashishikan jikin rigar sai kyali suke, gashin kanta à sake yake har gadan bayanta sai kyali yake ya sha gyaran Amare, du burar da zata yi sai mazaunanta sun motsa tamkar an cika balanbalan da ruwa ana girgizawa, haka na shanunta idan ta bura dai sunyi sama domin ba abinda ta saka daga ciki, ai tana Jin sun shigo din nan bisa hudubar auntynta wato Hajiya Rafi'at tayi wata irin juyowa ta nufo su tana buga kafa aman abin mamakin tamkar Bata ga da Sahla à wajen ba,

tana isowa ta shiga dire kafafuwanta tamkar Yar baby karama tana juya idannuwanta nan nata tamkar na mage tana dan kikifta su haka sai yarfe hanu guda take ta mika hannunta ta kamo hannun Mubasshir da ya zama tamkar gunki nunfashi kawai yake fitarwa aman komai na jikinsa ya tsaya ya daina anfani, kalonta yake kwakwaluwarsa ta tafi caji domin Tunda yake da ita bai taba ganinta da shigar kakanan kaya ba, KO ranar da ya bareta à Léa a duhu komai ya wakana , du ganin da zai yi mata da doguwar rigarta KO zani da atamfa aman koda atamfa bai taba ganinta ba,


Yan hannunsa da Yar mahaukaciya tayi ne ya fargar da shi cikin shagwaba ta ce"nurulkalbi plz kazo ka dauko min CD na Gaza daukowa, yayi min nisa gashi Ina son Nayi kalo



Sahla dake tsaye Bata san sanda ta ce" tap, tun karfinta ba


à tare suka juyo suka kaleta, Islam ta ce" Lah auntyna yaushe kika shigo ? Kinga Ina ta my one ban lura da ke ba i'm SO sorry yayi mantuwar tasa ne kafin ya fito KO ???



Sahla ji tayi uwa ta make bakin Yar mahaukaciya dan Haushi , ita zata nunawa bariki ? Aman zata fada, ta danyi murmushi ta ce" ikon ALLAH, amaryar nan anya kuwa ? Kai kanwata ba KO irin kukan za'a rabu da su mama din nan du da ba'a jima da haduwa da su ba, ba'a wani shaku ba, aman ai amarya koda zawara ce ranar tarewarta ya dace à bude mata lulubinta ba ta bude ba



Yar mahaukaciya tayi dariya harda dan rike cikinta ta ce" Lah yanzu aunty à tinaninki yaune tarewar ? Ai an dade da sanin wannan hanyar yauma Nayi niyar na dawo kusa da mijina ne dan na ringa dama masa dakan hanu na fura cike da ada'ar soyaya


Sahla ta juya da sauri ta kali AA dake tsaye yana kalon ikon ALLAH, irin yanda islam ke mayar da du bakar maganar da Sahla ta yaba mata, maganganun da take Ramawa haussa ne cikin haussa, Sahla ta ce cikin bacin rai" Daman ka dade da tarawa da ita ? Toh à matsayin matarka KO dadiro ?


Yar mahaukaciya ta ce " matarsa ai dadiron sa ce, sai dai mata suna suka tara sanan akoy dadiron mijinta bayan Aure kuma akoy dadiro kafin Aure da kuma bayan Aure, ta juya wajen wata akwati Karama mai shegen kyau ta ce" Aunty kinga kyautar budurcina Wanda yayi min ni tawa kirar Dubaï ce harda dan gwal à ciki, taki ma irin haka ya baki ????????



Sahla tayi tsit ta kasa Bata amsa kawai sai ta juya da gudu ta fita daga dakin inda suka rakata da ido, Islam ta dan saki murmushi ta juya tana kokarin saka Baban hijabinta dan ta kwonta baci



AA yayi tsam yana kalonta ya juyo yana tambayar kansa mai kenan ? Mai hakan ke nufi ? Wai shin duka wannan abin da Islam tayi wasan kwakwayo ne ????????? No bazai yiwu ba ba zai yiwu ba








zai yiwu kai AA 😄😄😄😄😄😄😄😄😄😄😄😄😄😄😄🙄🙄🙄🙄🙄🙄🙄🙄🙄🙄🙄🙄🙄🙄🙄🙄🙄🙄🙄🙄🙄🙄
[21/1 08:11] Sajida: 🇳🇪Belles écrivaines du Niger



*'YAR 👧🏻*

*MAHAUKACIYA👹*



*Na*
*Sajida*






77




*Manzan Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata agareshi yace: duk wanda yai min salati a rana sau dubu {1000} to bazai mutu ba har sai nai masa bishara da Aljanna. Wanda ya yada wannan hadisin to hakika yana sona, wanda kuma ya boye to hakika yayi nadama*








Kalonta yake cike da al'ajabinta, wai daman tana magana haka ? Toh Wa ya koya mata irin hakan ? Au yanzu fa wuta ce ta kuna masa KO ? Yayi murmushi ya zauna bakin bed din yana kalon yanda take kiriniyar daure gashin kanta

À hankali ya ce " baki ci nasara ba, domin fushin bai dameni ba


Yar mahaukaciya ta waigo ta dan kale shi ta juya ta ci gaba da shirin bacinta,

Shima kyaletan yayi yana nan zaune har ta gama ta juyo tana kalonsa, domin à saman bed din yake ya tankwashe kafafuwansa


Juyawa tayi tana kalon tsakar dakin nata sai lalausan kafet à shinfide, ta nufe shi da niyar konci


Mubasshir ya ce" Islam

Cak ta tsaya Bata waigo ba, ya lumshe Idannuwansa ya ce "ki dawo saman bed dinki ni zan kwana à kasan, yana gama fadar haka ya buda jerin kayansa da aka zuba à dakinta ya dauko tawol ya nufi bayi

Yana shiga ta juya harda dan gudunta ta haye bed dinta ta ja lalausan bargonta ta rufa ta tofe jikinta da ada'o'i ta lumshe idannuwanta sai barci


Can cikin dare ta farka dan gyara konciyarta ta jita à jikin mutun, hakan ya matukar firgitata ta mika hanu à hankali ta kuna fitilar jikin bed din mai dan duhu

Fuskar Mubasshir ta tsurawa ido da kontacen sajensa Idannuwansa a rufe sai bacinsa yake hankali konce, à nutse ta tsurawa kirjinsa ido yanda gashin ya konkonta alamun nutsuwa à tare da shi,


"idan kin gama kalon ki kashe fitilar my islam, haka kawai kalo da tsakar daren nan ?

Muryar Mubasshir ta tsinta Idannuwansa a rufen nan aman yana fadin haka, da sauri ta shiga zare ido tana kokarin tashi daga kirjinsa ta ce" ni, ni ba wani kalo da nake nini


Kara jawota yayi sannan cikin muryar mai baci ya ce" shiiiiiiiiiit, Ina bukatar ki à jikina SO kiyi min hakurin hakan, ya kara rumgumeta da kyau à jikinsa


Luf tayi cike da kunya tana kara sine kanta à kirjin nasa nan da nan kuwa baci yayi awon gaba da su



Karan wayarsa ta tayar da su à tare ya mike à hankali ya lalubo wayar, sunan umina ya gani à jikin screen wato Hajiya Fadimatu cikin Bari ya daga ya kara à kunansa ya ce" Maman islam Lafiya ?


Ajiyar zuciya ta sauke ta ce" Dan Fadimatu Ina yarinyata ? Hop lafiyarta lau ?


Mubasshir yayi murmushi ya juya yana kalon Yar mahaukaciya da tayi tsuru cike da tsoron Jin ba'asin Kiran domin karfe biyar ma Bata cika ba, ya ce" ga yarinyarki zaune ta tankwashe kafa tana zare idon tsoron Jin kiranki à karfe Hudu maman Mubasshir,


Hajiya Fadimatu ta kali hajiya hafsat dake ta murmushi ta ce" bani yarinyata kaji ko


Mubasshir ya mikawa Yar mahaukaciya wayar sannan ya tsareta da ido,

Tana amsa tayi salama

Hajiya Fadimatu ta ce " my Daughter lafiyanki lau ? Ba abinda yayi miki ?


Islam kunya ta cika ta, kawai sai ta kasa magana ta shiga sisine kai, ganin haka ya karbi wayar ya ce" Maman Mubasshir ki kontar da hankalinki plz, y'arki tana cikin koshin Lafiya, kunya ta hanata baki amsa,


Hajiya Fadimatu tayi murmushi ta ce" na kasa baci ne, du da Elhaj Muhammad ya fada min yanda kuka yi, aman sai nake jina bana tare da nutsuwata, plz karka cutar min da yarinya


Mubasshir ya ce" Maman Mubasshir kin san wani Abu ?


Hajiya Fadimatu ta ce " aa

ya ce" Maman Mubasshir Ina tsananin son Y'arki,


Hajiya Fadimatu ta zaro ido, hajiya hafsat ma ta zaro ido ai ba shiri ta datse Kiran, Hajiya hafsat kuwa ta bushe da dariya domin yanda hajiya Fadimatu take dan zazaro ido abin à daran ne, hajiya hafsat ta ce " aunty plz ki konta ki huta ni kam kinga Nayi nan, ta shige bargo tana ta dariyar Mubasshir da islam da mamansu


Mubasshir ya saki murmushi Jin ta datse Kiran, ya juya ya kali islam yanda ta dukunkune à cikin bargo ya san kunyar abinda ya fada ne ya saka tayi hakan, ya matso à hankali yayi mata kis à kuncinta sanan ya ce" kinsan mamanki tana tsoron kar à maimaita abinda ya faru ne kar à jima yarta ciwo


Yar mahaukaciya ta zaro ido ta kara matsowa can karshen bed din à ranta tana tunanin daman haka yake Sam kunya Bata ishe shi ba,


Ya Mike yana murmushi ya nufi bayi ya dauro alwallah ya shiga nafilfili


Karfe takwas na safe wayar hajiya Marhaba ta tayar da Sahla daga baci,


Hajiya Marhaba ta ce " baby Ki tashi haka mana da barcin nan naki kiyi ki leka ki ga yanda suke ciki



Sahla ta diro daga bed dinta ta ce" bara na wanke idannuwana na leka kinga abin nan na jiya ya kona min rai zinariyar nan ba karamin kudi aka kashe mata ba, abinda ni bai ban ba ita ya Bata, aman su suka ja ma kansu, nasan yanzu ta dade da mutuwa Bara na hanzarta na kwashe su zinariyar kafin yan sanda su zo




Hajiya Marhaba ta ce " yawa Yar Gari maza hanzarta



Sahla idannuwanta kadai ta wanke ba KO tunanin Wanka KO alwallah dan rama sallar asuba haka ta hanzarta wanke fuskarta ta bude bangarenta ta nufi na Yar mahaukaciya har tana harde kafafuwa wajen sauri


tana isowa Bata yi tunanin yin salama ko wani abin ba kawai ta tura kofar Baban falon ta shige

Gabanta ne yayi mugun faduwa inda kafafuwanta suka Gaza daukarta ta zube nan tana kare musu kalo su Mubasshir da islam sun sha wata farar Shadda bugagiya ta sha aiki kala daya, saï Aunty Rafi'at da fati suna zaune saman table suna cin abinci sai anuri ke fita daga fuskarsu


wani ihu ta saki ta ce..............................,,,,,,,,,,,,,.............
[21/1 08:12] Sajida: 🇳🇪Belles écrivaines du Niger



*'YAR 👧🏻*

*MAHAUKACIYA👹*



*Na*
*Sajida*






78


*Yaya Hayat Admin na hayat haussa novel, haussa novel nd fashion cool novel..... Patati nd patata sako zuwa gareka, kayiwa girman ALLAH ka barmin novel dina yanda ka ganshi cos nawa ne ba naka ba, haba taya zakana hada document da novel dina da numbobin wayarka da sunayen Grup dinka kuma ba tare da izinina ba ? Ka manta y'ar mutan Niger da na nemi alfarmar ka saka ni à grup Ina bin novel din auntyna matan Ali ka bukaci kudin shiga ni da nake Niger Ina zan ga naira hakan yasa kaki sakani sai yanzu zaka yi anfani da naya novel din ? Kai walahi idan ka kuma anfani da novel dina dan kayi document da shi ban yafe ba ka barshi yanda yake idan na gama abina zan hada abina à document na gode*

Wani ihu ta saki da ya saka suka Mike a tatare, da hanayenta ta daga tana nuna su tana kokarin yin magana da gudu ta Mike ta fice ta nufi dakinta tana zuwa ta danna Kiran mahaifiyarta,

Hajiya Marhaba na daga wayar Sahla ta rushe da matsanancin kuka


Hajiya Marhaba ta ce " ke pretending kike KO kukan gaske ne ?


Sahla ta ce "mama lafiyansu lau, suna zaune suna karyawa cikin annuri, KO dan ta saba da shine ya sa Bata gaji da shi ba, ya sa bai halakata ba, mama mai yake faruwa da ni ne ? Daga wannan sai wannan, KO duba fa ki gani tun kafin ta tare yake like mata kenan yafi sonta da ni KO ?



Hajiya Marhaba cikin tashin hankali ta ce" wani irin mutun ne kika aura Sahla ? Shi asiri baya cinsa ne ? Bara Nayi Kiran tsinanan bokan nan Naci kutumar..... Don kuwa bazai yiwu na barshi ya cinye min kudi kuma aiki bai ci ba, KO kontar da hankalinki kiyi musu basaja tamkar ta kirki, ni na fisu zama hatsabibiya, zasu ga abin mamaki, da ni suke zancen


Sahla ta saki ajiyar zuciya ta ce" à da Ina tunanin sasauta masa aman à yanzu na tsane shi mama, dalili kontawa da yayi da wannan yarinyar har ta kare min kalo ta gwada min abinda ya siya mata,


Hajiya Marhaba ta ce "barni da su, Tunda kika gane hakan ai da kyau


Suna katse wayar hajiya Marhaba cikin bacin rai ta danawa bokanta kira

Cikin magagin baci na mutumin da bai tashi ba har karfe tara boka ya daga wayar hajiya Marhaba,

Rufe shi tayi da fada tana fadin ita zaya yaudara aikinta yaki ci

Wata uwar ashar ya dura mata sannan cikin yannayin mashaya ya ce" ke kika Bata aikinki Yar akuya, dan haka li jirayi sakamakonki na zagin aljannu da kika yi, dif ya kashe Kiran

Hajiya Marhaba ta bi wayar da kalo ta Mike tayi Kiran kawarta azumi,
Tana dagawa ta shiga zayane mata abinda ya faru, ta dora da fadin" kinga kuwa shine yayi min aikin Elhaj na daga bayan nan da ya fara warwarewa, yanzu haka yanzu zanyi Kiran uwar tasa Ina kuka idan ta taho ta tsalako shikenan hauka har kabarinta, sai sauran tsinanun, To aman na fara kokonto


Ji tayi an warce wayar daga hannunta ta dago da kanta da sauri idannuwanta suka sauka à fuskar mijinta da lokaci daya kamaninsa na tsare gida tun suna samartaka ya dawo masa, daga bakin kofa kuwa Baban danta ne ya dora hannu biyu à kai yana rusa wani matsanancin kuka, fitowa yayi ya jawo dansa suka zauna suna Jiran isowar su Sahla domin su hajiya Fadimatu har sun karaso inda yayi Kiran Mubasshir ya bashi umarnin KO à daure ne ya kawo Sahla wace ya yana shiga ya tsorata ta ta hanyar fadin mamarta ba Lafiya

Ai da Gudu ta fito suka kama hanyar gidan mahaifinta gaba dayansu banda fati


Suna karasawa ta fita da gudu tayi falon umanta, tana zuwa ta tarar da jama'a à falon inda suka taru kowa yayi jigum, shi kuwa Idriss sai rusar kuka yake

Ihu ta saki ta dora hannayenta biyu à kanta ta nufi Idriss tana tambayar ta mutu ne ? Mai ya sameta ? Wani ne ya kashe min uwa ? Ina maman a.....

Dim kake ji ta hadiye sauran maganar à bakinta, sanadiyar wani wawan mari da abanta ya zabga mata, kafin ta dago ta kali mai marin nan nata ya kwasheta ji kake kush karar faduwarta à kasa, kafin ta gama dandace abinda ke faruwa da ita ya bita kasa ya shiga nausarta


da gudu suka ririke shi suna fadin haba Elhaj, idan rai ya baci ai hankali baya gushewa,

Sahla dake zubar da jini ta goshinta ta kasa daga hanunta da alama ya karye fuskarta kuwa har ta canza kala, ta ja jiki ta rike kafar Idriss tama kasa kukan du irin azabar dake tsigarta, idannuwanta ta dago har jini ya dan konta ta zuba masa su ta ce" mai ke faruwa Yaya Idriss ?


Idriss shima ido cikin ido ya ce" Sahla asirinku ne ya tonu,


Sahla ta zaro ido ta ce" wani asirin mu ? Ni da Wa ?


Idriss ya ce" asirinku na shirin ku na halaka rayuwar bayin ALLAH da suka yi muku rana dan ku malake abinda ba naku ba, ke harta asirin da mama ke yiwa dady na ta juya shi yanda ta ga dama ya karye Sahla, yanzu haka ta bine wani à kofar dakin dad Bata tsoron yayi dawowar bazata dan kawai ta tsoratar da Hajiya (hawau) cewar dad ya mutu yana dakinsa idan ta tsalaka ta haukace à cewar bokanku, Allah ya taimaka muna shigowa dakinta muka nufa dad cike da mamakin za'ayiwa mama sherin bin bokaye sai gashi yaga haza domin shaida ta kirarin mutun da kansa KO ta Zina ta shaidu,


Sahla zuwa wannan lokacin ta gama tsurewa, tsoro da fargaba da tashin hankali da kunya suka mugun lulubeta, cikin nauyin harshe ta ce" Wa ya fada muku ?


Abanta cikin wata irin murya mai cike da kunci ya ce" Wanda ya boye mana dan ya kare mu, Wanda ya zuba muku ido dan yaga imanin ku, Wanda à cikin ruwan sanyi ya dago ku à fili *ALLAH* kenan, Wanda baya baci,


Sahla ta waigo ta zubawa fuskar Mubasshir ido a ranta tana tunanin ashe ya ji komai shi yasa yayi tayi mata tambayoyin nan ?


Idriss ya Mike ya nufi kofar dakin mahaifiyarsa ya bude dakin, tana jingine da kofar tana sauraron komai, ta dora hannunta à kai tana tunanin yanda aka yi hakan ta faru ai kuwa Bara ta kirayi boka ta fada masa ta bashi hakuri ya kuma shirya mata wani sihirin ( oh wai Kin manta rana dubu ta barawo, rana daya ta mai kaya ?)

Budewar da yayi tana tsaye, ya zuba mata ido itama shi take kalo, ai kuwa ta shiga zaro ido hango mutanen falon, ta fito tana inda inda ta ce" aa fa, aa fa, wannan duka karya ne, ni ban aikata ba, aban Sahla karka yarda à hadani da kai, kai kasan à yanda
Nake kula da hajiya bazan iya cutar da ita ba, kai kafi kowa sanin hakan KO ? Ta juya wajen Idriss ta ce" Docter kaima ai shaida ne matso nan ka furta mahaifiyarka ba abinda tayi kowa ya tashi ya fice gidansa,


Sahla ta ce" mama.

Hajiya Marhaba ta juyo gabanta ne yayi wani irin faduwa, fuskar Sahla ta Haye tayi sindim, jini ya shigar mata ido ga hannunta ta kasa daga shi

Hajiya Marhaba ta ce " ubanwa ya taba lafiyar jikinki ? Fada min ubanwa ya dake ki ?


Mahaifin Sahla ya ce" ni ne, ni na daki y'ar da nake tir da...... Da sauri Elhaj Muhammad ya ce" kul na haneka da yin mumunan furuci Wa y'arka, SO kake ta shiryu KO ta baude ? Rashin tunani dana sani, kaucewa hanya ya tabata ga iyayen da zasu aibata y'ayansu dan sun kaucewa hanya, To mai zaka yi kenan ? Mala'iku suna gagawar amsar adu'ar iyaye Wa y'ayansu da amin KO wace kala ce dan haka ka kiyaye kar danasani yayi yawa rayuwarka


Hajiya Marhaba ta karewa Elhaj Muhammad kalo cikin kunan rai ta ce" ai dole ka fadi haka, kai ka kilace taka sakaryar y'ar zaka yi mana bariki à nan, toh wly baka Isa ba


Mahaifin Idriss ya juya dan yiwa Idriss magana sai dai abin mamaki bai ganshi à inda yake tsaye ba

Kiriniyar bude dakinsa yake domin idan za'a bude dakinsa sai an sha fama da kofar

Da sauri suka nufe shi aman kafin su Isa har ya bude kofar da gudu hajiya Marhaba ta rike shi aman da yake karfin ba daya ba zai kufce mata Mubasshir ya damko shi, kokowa suka shiga suna kokarin turo shi, garin ta tura shi karya shiga dakin da ta bine abinda zata haukata hajiya hawau da shi, ita kafafuwanta suka shiga, abin ikon ALLAH kawai sai ji suka yi ta kwashe da wata muguwar dariya


À tare suka furta inalilahi Wa'ina ilaihi raj'une, hanayensu à saman kansu

Mubasshir ya saki Idriss Wanda ya juyo jiri na kwasarsa ya zube à nan sumame


Ita kuwa sai dariya take babakawa, haukan dariya hauka mai wuyar warkewa, haka suka yi jigum jigum inda suna waigowa itama Sahla ta suma ( to fa wanzam baka SO à jikinka)


To fans tambayana à nan shin Sahla zata ci gaba da zama à matsayin

Please Login or Register in order to submit comment