Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ransa KO yana Sauri ya je wani wajen ne hakan yasa ya kasa control din kansa"


Hajiya Fadimatu ta shafa fuskarsa ta ce" Ya jima yana barcin ne?"



Docter ya ce" eh toh sai da muka daidaita komai ya samu kamar awa uku muna ta neman yanda zamu sanar muku, zuwa yanzu yaci ace ya farka ma sai dai da alama yana jin dadin bacin, Muje ma'am na baku takardun da ake bukatar a cike da kuma na maganin sa"




Hajiya Fadimatu ta kali Yar Mahaukaciya dake tsaye itama tana sauraron bayanan likitan ta ce" Yata bara na dawo" ta juya ta bi bayan doctern




Da tafiyarsu Yar Mahaukaciya tayi tsai tana kalonsa sai bacinsa yake gashin idon nan nasa yayi zagar zagar a konce baki yayi lufluf da shi , bakin nan nasa tamkar ya shafa man lebe sai sheki yake namiji da shekin lebe, a hankali ta jawo kujera ta zauna daf da shi ta dago hanayenta ta dora saman cinyoyinta ta tokare habarta ta zuba masa ido tana kare masa kalo a ranta tana matukar mamakin mumurdewar hanunsa shi kuwa ba karfe yake ci ba a saninta bata taba ganinsa yana irin daga karfen nan aman hanunsa yana yan dambe da ake nunowa a tashar TL9 ,


Tana haka har wani irin baci ya kama idanuwanta ta karewa dakin kalo ba wajen konciya hakan yasa ta dan dora kanta daga bakibakin gadon baci yayi awon gaba da ita ( toh fa ke da aka barwa marar lafiya?)




Cikin nutsuwa ta turo kofar ta shiga da salamar ta , murmushi ne ya subuce mata ganin Mubasshir ya farka yana kalon Yar Mahaukaciya dake baci duk da bai ga fuskarta ba yana son sanin KO wacece ke konce kusan sa ,


Shima Murmushin ya sakar mata ya dago hanunsa irin ta karaso


Hajiya Fadimatu ta karasa suka gaisa da gudan jininta ta ce" Dan Fadimatu yaya saukin jikin?



Mubasshir yayi murmushi cikin muryar maran lafiya ya ce" maman Mubasshir i'm sorry"



Ta girgiza kai ta dora yatsarta a saman lebensa ta ce" no dan gidan Fadimatu dena bani hakuri yarona, Allah ya baka lafiya "


Yayi murmushi yana kalon hanunta magunguna ne ya dan yatsina fuska a ransa ya ce " tap gaskiya ni bazan sha maganin nan ba"



Bayan ta ajiye ledar maganin ta zo a nitse ta tana murmushi ta ce" oh Yar Fadimatu nasan bacin nan na jiya daman bai wani isheta ba , baiwar Allah gashi yanzu mun kado KO abinci bata ci ba




Gaban mubasshir ya fadi ya lumshe idanuwansa yana kalon mahaifiyarsa na kokarin cirewa Yar Mahaukaciya hijabinta dan ya shake mata wuya , yayi gagawar kawar da kansa yana kara rintse idanuwansa a ransa yana ta adu'o'i kan Allah ya kare masa idanuwansa da kalon banban muradin sa



Idanuwanta ta bude suka yi ido hudu da Hajiya Fadimatu tayi murmushi ta ce" Mama kin dawo? Baci ne ke damuna



Hajiya Fadimatu ta ce" ai Dole yar Fadimatu, Konta ki hutawarki , ai likitan yace zai mabu salama aman sai dai mu tafi gida da yayanki dan nayi Kiran number matarsa ta yiwa mahaifiyarta rakiya bata nan shi kuwa baya son shan magani sai dai mu tafiyarmu gida da shi



Yar Mahaukaciya ta gyada kanta tana leken fuskarsa ta ce" Allah ya kara afuwa



Hajiya Fadimatu ta ce" Amin , sanan taci gaba da hada masa yan magungunan da likita ya ce ya sha idan ya farka sai a basu salama su je gida ya ci gaba da sha




Cikin ikon Allah likita ya salame su suka nufi gida da magungunan su, aman tunda ya farka bai yarda sun hada ido da Yar Mahaulaciya ba , koda tayi masa sanu da jiki hanunsa kawai ya daga mata a hakan har suka isa gida , inda Hajiya Fadimatu ta rasa décision din da zata dauka domin shi dai ba lafiya ne da shi ba, bazata yarda ya kwana a dakunan kasa ba , kuma dakin nasa shine Yar Mahaukaciya ta zauna, sanan tana ganin lokacin ta fada musu gaskiya yayi KO dan su dan saba da juna









😳😳😳😳😳😳🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻😳😳😳😳😳😳😳😳
[17/11 16:30] Sajida: 🇳🇪Belles écrivaines du Niger



*'YAR 👧🏻*

*MAHAUKACIYA👹*

*_Na SAJIDA_*







54

Tana zaunen nan falon tana waya da Hajiya Hawau Yar Mahaukaciya ta fito da kwaryar fura a hanunta ta sha damu sai kanshin kayan daka da cikwui take, cikin nutsuwa ta dan zauna har Hajiya fadimatu ta gama wayar



Ganinta ta karaso ya saka Hajiya Fadimatu fadin "toh Hajiya sai kin zo zuwa yamar, sanan kar fa ki daga hankalinki da sauki jikin"


Tana gamawa ta juyo da murmushin nan nata mai tsada ta kali Yar Mahaukaciya


Yar Mahaukaciya ta taso ta nufota ta ce" Mamana ga furar yayan nan na dama nasan zai sha"


Hajiya Fadimatu ta ce" Sanu da kokari Yar Fadimatu, aman tafi ki kai masa furar yana dakina"


Yar Mahaukaciya ta juya ba dan taso hakan ba dan kuwa tunda yayi hatsarin nan tamkar ya wani tsaneta ne KO baya ji idan tayi magana dan kuwa sai dai kawai ta ga yana hararanta



Cikin nutsuwa da faduwar gaban da bata san KO ta maicece ba ta tura dakin bakinta dauke da salama ,



Idanuwa ta zaro ganin AA Mubasshir jingine da bed ya dafe zuciyarsa ya mike kafafuwansa yana kalon kasa sanan ga wani hawaye na bin fuskarsa , bata san lokacin da ta yar da kwaryar furar ta nufe shi har tana harde kafa


Tana isa ta dire gwuiwoyinta a kasa ta saka yatsarta ta lakato hawayen kuncinsa dan tabatarwa kanta kuka yake, cikin sarkakiyar murya ta ce" Yaya Mubasshir jikin ne? Ina ke yi maka ciwo? Ka sha maganinka? Dan Allah ka dena kuka, bara na kirawo Mamana"


Ta mike da niyar FITA ta kirawo Hajiya Fadimatu sai taji an riko mata hanunta riko ba na wasa ba , riko na keta da zafi sanan aka fisgota


Dabash ta zauna domin sauran kadan ta kifo a kansa Allah ya sota, ta shiga zazare ido tana tsoron abinda ya saka ya rike mata hanu haka sanan irin yanda ya hada fuska ka rantse cewar ba AA bane , gaba daya ya zama wani abin tsoro





Nunfashi ya ja ya sauke ya zuba mata ido yana ayana abubuwa da dama a ransa sannan ya bude bakinsa yayi iya kokarinsa wajen furtawa mai raya tinaninsa mugayen kalamai inda ya ce" *I hate you*



Da Sauri Yar Mahaukaciya ta dago idanuwanta wa'inda suka fara canza launi sai hasken mai kama da na magen da ya fara fitowa ta zuba masa su



Hakan ba karamin karayar da shi yayi ba aman sam baya jin zai iya lamuncewa zuciyarsa abinda take so ya ci gaba da fadin" *Yes i hate you, na tsani na hadu da ke, na tsani na zauna tinaninki sanan rashin lafiyata ta dalilinki ne, ke ke din nan dai ke ba zawara ba aman kinfi zawara sanin hanunki dan har kin iya yanda zakiyi ki rikitar da maza, Abdul na sonki, Abdallah na sonki, jama'a da yawa na harin cewar suna sonki , Ni....ya ja nunfashi yaci gaba karyarki ta sha karya a kaina, Ni nafi karfin nace wai ina sonki abin ba dadin ji dan haka ina mai umartar ki da kiyi gagawar tsayar da daya a cikinsu wa'inda suka zubar da girman nasu na aura miki ki kara gaba dan kuwa bana son na ringa cin karo da ke a cikin gidan nan*




Yar Mahaukaciya dake kalonsa cikin matsanancin faduwar gaba da tarin hawayen dake zuba daga idanuwanta ta ce" *Mai yasa ka tsaneni? Shin wani laifi na aikata?* "



Mubasshir ya kawar da kansa dan kuwa hawayen nan nata ji yake tamkar ya jawota jikinsa ya saka harshen sa ya lashe su sanan ya rukunkumeta dan kar Wanda ya kalan masa ita, yayi gagawar watsar da tinanin ya ce" *kwarai kuwa kina da laifi, kin fi kowa laifi ke laifinki yafi karfin na kawar da kaina kansa dan haka ki kiyayi abinda na fada mini* "



Yar Mahaukaciya ta Mike da kyar ta juya tana tafiya , har ta kusa fita ta juyo ta dawo inda duk takun tafiyarta bugawar zuciyar Mubasshir ne,


Tana dawowa ta tsuguna kanta a kasa ta ce" *shin tsanar da kayi min ta yan'uwantakar ce KO mai?*


Kwarai tambayar ta zo masa a bazata kuma sai a sanan y'a gane ilimi ne da ita , ya kawar da kansa cikin kame kame ya ce" *ai musulmi baya tsanar musumi banza haka, ina yi miki son yan'uwantaka wanda koda Maman Mubasshir bata yarda da ke ba dalilinki na musulma zan taimaka miki aman banda wanan son ba wani* "


Yar Mahaukaciya ta kuma cewa " *Son soyaya ne na aure baka yi min?* "




Mubasshir ya gyada kansa da alamar gajiyawa da tambayoyinta



Da mamakinsa sai gani yayi ta saki murmushi ta ce" *Har ka bani tsoro yaya, daman ni? Wacece ni? Ilimin me gare ni? Mahaifiyata Mahaukaciya ni yar bola har nayi tsamanin soyaya daga kamarka? Ta yi dariya irin da mamaki ta ci gaba" ai dan gata sai Yar Gata, i'a zan fadawa Abdallah idan da gaske yake ya fito inji yayana* "

Tana gama fadar haka ta mike tayi waje da gudu da alamar jin kunyar nan ,


Mubashir yayi gagawar rike daidai zuciyarsa yana sakin wata irin ajiyar zuciya tamkar yayi tsere, ya silale nan ya konta yana kalmar shahada domin a yanda zuciyarsa ke bugawa shi yasan kawai lokacinsa ne yayi, yasan kawai shi tashi ta kare domin bai san ciwon *So* ba, ta kafa masa wuka ta barshi da tsiyayar jini a kahon zuciya,







Toh fa AA ai gwara karka bige plz ku tayani da adu'ar kar ya tafi🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻
[18/11 19:08] Sajida: 🇳🇪Belles écrivaines du Niger



*'YAR 👧🏻*

*MAHAUKACIYA👹*

*_Na SAJIDA_*







55

Tana fita dakinta ta fada ta ja ta rufe ta silale jikin kofar tana maida nunfashi, a hankali ta furta" *Ya Allah , kai kayi talaka kayi mai kudi, kai kayi mai gata da marar gata, ALLAH da kai na dogara domin kaine gatana, Allah kayi min zabi ba zabina ba, ALLAH ka zaba mini abinda yafi zama alkhairi a rayuwata, Ya Allah* " ta rintse idanuwanta hoton Bakin AA na furta mata kalmar *I HATE YOU* tayi Saurin bude idanuwanta ta mike tana fadin A'uzubilahi mina shaidanin'rajim ta fada bayi ta sakarwa kanta ruwa




Bayan sallar Magarib Yar Mahaukaciya ta sauko amsa Kiran Hajiya Fadimatu a falo ta sha Riga da Zani na atamfa ta zaya mayafi ja tayi kyau tamkar Yar Tsana duk da ba wata kwaliya ta zana ba , tana isowa ta tsuguna ta gaishe da Hajiya Fadimatu



Hajiya Fadimatu ta amsa cikin sakin fuska sanan ta ce" Yar Fadimatu ana salama da ke ina jin Abdallah ne



Yar Mahaukaciya ta sine kai ta mike ba tare da ta amsawa Hajiya Fadimatu ba dan wani irin nauyinta da take ji, ta nufi kofa


Tana FITA Hajiya Fadimatu ta sauke ajiyar zuciya a fili ta ce" astaghfrullah ya Allah ka yafe min wanan abin da nayi , Allah ka san abinda ke zuciyata Allah ka shige min gaba, sanan ta kama hanyar dakinta


Tana shiga dakinta ta tarar da Mubasshir yana zaune saman darduma yana Jan carbi , a nitse ta nufi windown dakin ta bude madubin tana lekawa



Mubasshir dake zaune yana hailala yana neman sauki wajen Ubangijin sa yayi fatiya ya juyo yana kalon Mahaifiyarsa ya ce "Maman Mubasshir ina yini? "


Hajiya Fadimatu ta juyo da murmushinta ta ce " Lafiya lau Dan Fadimatu, kaga Mamarka da tsegumi KO? Ina kalon yata ne "



Mubasshir ya ce "Yarki?"


Hajiya Fadimatu ta ce" yes zance ake kaga yanda ta ja gefe tamkar Wanda take tsoron saurayin"



Mubasshir ya zaro ido bai san sanda ya ce" What? Zance ? Kuma ita da wa?



Hajiya Fadimatu tayi masa kalon lafiyarka? Domin tambayoyin nasa a jere sanan ya mike lokaci guda har mazari jikinsa yake ,


Da Sauri ya juya ya fada bayi yana tari ya kuna pampo ya sha ruwa da kyar tarin ya sake shi ya juyo ya fito, yana fitowa ya tarar da Hajiya Fadimatu tsaye hankalinta tashe ta ce" Son jikin ne?"



AA ya girgiza kansa da yake Sara masa ya nufi bed ya konta yana rinrintse ido



Hajiya Fadimatu ta bi bayansa ta dafa shi ta ce" KO mu tafi asibitin ne? "



Mubasshir ya girgiza kai sanan da kyar ya ce" maman Mubasshir ba komai karki damu"



Zata yi magana taji ana konkwasa dakin ta taso ta bude a tinaninta Yar Mahaukaciya ce sai ta ga Hajiya Hawau



Murmushi ta saki tana fadin" Hajiya barka da warhaka , sanan ta bata guri ta shige cikin dakin


Hajiya Hawau ta kali Hajiya Fadimatu ta ce" Hajiya da wa yar tawa ke zance ? KO dai shine sirikin namu?



Hajiya Fadimatu ta ce" shine kina gani sai wani kawar da kai take," ta karashe tana kokarin kawar da fuskarta gefe dan kar ya dagota



Hajiya Hawau ta ce" ai kuwa idan ya shirya ai sai ya fito kawai ayi da shi"



Mubasshir dake sauraron zancen su a ransa ya ce" tazo ganina ne KO tazo ta karasa ni, ? A fili kuwa da kyar ya samu ya tashi ya juyo yana kalon su ya ce" Barka da zuwa Hajaju"



Hajiya Hawau ta karasa tayi tamkar yanzu ta Ganshi ta ce" Dan Aljannah ya jikin?



Mubasshir ya ce" Jiki yayi sauki Alhamdulilah, daman ina son zuwa wajen ki sai gaki kin zo"



Hajiya Hawau ta gyara zama ta ce" toh bani na sha"



Ya dan furzar da iskar bakinsa cikin kawar da kai ya ce" *Abdul ya sameni kan zancen nazo na sameki ki fadan inda Rahma take yana son aurenta , plz ki taimaka ki fada masa na yarda da son da yake mata* "



Hajiya Hawau ta kali Hajiya Fadimatu itama ta kale ta irin kalon aikin banza din nan sanan ta ce" *Ai yata anyi mata miji sai dai kuyi hakuri* "



Irin kwaruwar ta dazu ya kuma yi wanan Karin yama kasa tashi balatana ya shiga bayin ya samu sasaucin kwaruwar da yayi ta hanyar shan ruwa,


Wasa wasa tari ya tirnike shi tun yana rike daidai zuciyarsa har ya saka yana kokarin faduwa,


Da gudu Hajiya Hawau tayi bayi ta dibo ruwa inda Hajiya Fadimatu ta zauna tana rike da shi suka bashi ruwan ya sha, suka kuma bashi ya sha yana ta ajiyar zuciya



Hajiya Fadimatu ta dora kansa saman cinyarta tana shafa bayansa a hankali ta kali Hajiya Hawau da ido tayi mata maganar da su kadai suka gane abinda suke nufi sanan cikin muryar nutsuwa da kontarwa mai sauraro hankali ta ce" *Ya zakayi kokarin boyewa Wanda ta dauki cikinka ta raine ka ta shayar da kai ta juri rigimarka ta ga girman ka damuwarka? Ya zakayi kokarin yin gardama da abinda na hango a kwayar idanuwanka? Shin ka manta alkawarin mu na bazaka boye min sirinka ba?* "



Mubasshir cikin Mutuwar jiki ya dago da kansa daga cinyar Hajiya Fadimatu gabansa na ci gaba da faduwa a ransa ya ce" Kardai Maman Mubasshir ta rigayi Mubasshir sanin abinda ke zuciyarsa? Kar dai Maman Mubasshir ta gane cewar Mubasshir ya kamu da son Yar Gidan Fadimatu? Son da yake kokarin zautar da shi? Kaunar da tayi masa shigar bazata?


Hajiya Fadimatu tayi murmushi ta kawar da kanta ta ce" *Idanuwanka sun nuna tsantsar tsoro da fargabar abinda na karanta a tare da kai* "


Ta Juyo ta kama kafadunsa ta ce " *YA KAKE KOKARIN KASHE KANKA KAN HALALIN KA , IYALINKA, MATARKA? SHE IS UR WIFE MUBASSHIR* "


wani irin dum dum dum maganar ke yiwa Mubasshir a kunansa , wasu tambayoyi ya juyo yayi min Wanda nima nace AO🤷🏻‍♀







Tambaya yake shin Maman Mubasshir ta kuwa san sunan wa ta kama tace matarsa? Shin ta gane KO wanene a gabanta? Idan ta gane yaushe aka aura masa ita? Yaya zai yi da Abdul amininsa? Yaya zaiyi da ita kanta Rahmar?????????????????????????????????muje zuwa 😲
[24/11 20:05] Sajida: 🇳🇪Belles écrivaines du Niger



*'YAR 👧🏻*

*MAHAUKACIYA👹*

*_Na SAJIDA_*







56
adu'ar samun sasaucin kunci da tashin hankali

*ALLAHUMA, LA SAHLA ILLAMA JA'ALTAHU SAHLAN, WA'ANTA TAJ'ANUL HAZNA, IZA SHI'ITA SAHLA*

Hajiya Hawau ya tsurawa ido yaga itama shi take kalo, ya juyo ya kali mahaifiyarsa a fuskarta ya karanci sam ba wasa a cikin bayanin ta,


Wani lalatacen murmushi ya saka yana dan juya kai cikin muryar tausayi ya ce" Eyah maman Mubasshir ba fa ni nake nufi ba, ina nufin *ABDUL* yayan Sahla ne ke son Rahma fa, "



Hajiya Fadimatu ta ce" look son, Rahma matarka ce, taya zakana hada ta da wani kuma? "



Cikin wani yanayi ya juyo ya kale su ya ce" *ku yiwa Allah ku dena hada maganar nan cos ni kunuwana suna jiyo mini wani abin daban, Wanda kuma yake impossible, Rahma dake kofa tsaye tana zance da wani saurayin, gardi, Rahamar da aminina abokina yake matukar so, sai kuma kunuwana su rinka jiyo mini cewar matata ce? Ni ?* "


Hajiya Fadimatu ta mike cikin kakausar murya ta ce" *akoy wasa tsakanin uwa d'a da , sannan akoy zancen gaskiya, Ni Mahaifiyarka ni na samu alwalinka a matsayina na mahaifiyarka da kuma Hajiya Wace ta zamto sheda kuma ta bada amanarta muka yanke wanan hukuncin, ranar juma'a ya daura aurenka da shaidu a gidansa na nan, idan kana musu kayi Kiran sa, idan kuma baka yarda da hukuncina ba to ka watsa min kasa a ido* " ta karasa cikin yanayin bacin rai, dan a ganinta Mubasshir yama raina ta ne yana so yana basarwa



Mubasshir jikinsa yayi sanyi jin furucin mahaifiyarsa da yanayin bacin rai a tatare da ita duk dan shi, da Sauri ya karasa ya tsugunna kasa gabansa na faduwa ya kama kafafuwanta ya ce" Maman Mubasshir kiyi hakuri please, ba ina nufin ban yarda da maganarki bane, KO ban yarda da zabinki ba, no abin ne ya zo min a bazata, Dan Allah kiyi hakuri"

Hajiya Fadimatu ta sauke ajiyar zuciya ta kali Hajiya Hawau dake murmushin jin dadi, a nitse ta kamo shi ta dago shi suka koma bakin gadon , cikin nutsuwa ta ce" Dan Fadimatu, zaka yi min biyaya ka rike min yata tsakaninka da Allah?? "



A ransa ya ce tamkar yanda zan rike raina da mahinmanci , a fili kuwa yayi murmushi ya ce" Maman Mubasshir koda aljana ce kika aura min dole nayi biyaya ba zancen musu " ( ehem ) ya ce GABA da fadin " damuwata biyu ce Maman Mubasshir, Abokina da kuma ita yar taki"



Hajiya Hawau ta dafa kafadarsa ta ce" abokinka ba yanda ya iya domin matar mutun kabarinsa, sanan inada kwakwaran dalili na yin hakan, dan haka kayi fatan alkhairi kawai, "


Hajiya Fadimatu ta dora da " to aman mai yasa kace da y'a ta?"



Mubasshir ya dan kawar da kai yayi kokarin kauda kishinsa sanan ya ce" kinga hanzu ma fa da igiyar aurena tana zance Maman Mubasshir , kuma kina kalo kika barta "



Hajiya Fadimatu da murmushi ta ce " Gidan ku , ta je tayi zancen"


Hajiya Hawau ta ce" aa Hajiya baza'ayi haka ba , an soke zancen"



Mubasshir ya sauke ajiyar zuciya a nitse ya Mike ya nufi bayi ya kuna ruwa ya wanke fuskarsa ya dago kansa yana kalon miror, wani murmushi ya subuce masa a saman lebensa a hankali ya furta " *Matata ce* , ya lumshe ido yana kalon kasa , sanan ya kashe pampo ya fito a ransa yana fadin "wly idan bata shigo ba zan je na dawo da ita dan kuwa ba zai yiwu ba "




Yana fitowa ya tarar basa dakin, ya sauke ajiyar zuciya sai a lokacin ya samu ya nufi window ya bude yana ta hangawa, ajiyar zuciya ya sauke ganin basa nan, ya juyo a nitse ya tada Salah saman salaya dan ya kara godewa ubangijin sa da wanan kyautar da yayi masa ba tare da wayon sa KO tashin hankalin sa ba,





Tana shigowa ta tarar da su Hajiya Hawau zaune , direct jikin Hajiya Hawaun ta je ta lafe tana dora kanta a saman cinyarta


Hajiya Fadimatu ta ce" Yar Fadimatu bakon ya tafi?"



Yar Mahaukaciya ta dan sine kanta irin jin kunyar nan bata ce komai ba ,


Hajiya Hawau ta shafa kanta cikin nutsuwa ta ce" Yar Gidana muna son yin magana da ke" ,


Yar Mahaukaciya ta dago gabanta na faduwa , badan komai ba sai dan tsoron kar ace ta koma gidan su Abdul, don kuwa KO da anyiwa Sahla aure mahaifiyarta na nan shi ma Abdul din yanzu tsoronsa take .............




Hajiya Fadimatu ta gyara zama ta ce""""""""",,,,,,,,,,,,,"""""""""""











Sourou
[26/11 19:16] Sajida: 🇳🇪Belles écrivaines du Niger



*'YAR 👧🏻*

*MAHAUKACIYA👹*

*_Na SAJIDA_*







57



Hajiya Fadimatu ta gyara zama tayi gyaran murya ta ce" Yar Fadimatu shin na isa na sakaki abu kiyi , KO na hana ki ki guji yinsa?"



Yar Magaukaciya ta yi gaggawar daga kanta jikinta na rawa dan haka kawai ta tsinci faduwar gaba a tatare da ita ,



Hajiya Fadimatu ta kawar da kanta domin sai yanzu wani nauyin tunkarar Rahma da zancen nan ya darsu a zuciyarta , ta kuma juyowa daidai Lokacin da Mubasshir ke saukowa ya canza kayan jikinsa sai zuba kanshi yake ya fesa tiraren Hajiya Fadimatu , ja yayi ya dakata yana kalon su , shi kansa a yanzu gabansa faduwa yake bai san dalili ba ( zaka sani )



Hajiya Hawau ta ci gaba da fadin " shin kin dauke mu a matsayin iyaye? Wa'inda suka isa da ke , wa'inda zasu iya yanke hukunci dan inganta rayuwar ki? Wa'inda zasu guji ganin kin halaka sai inda karfin su ya kare? Shin a yau idan muka zo miki da wani hukunci da muka yanke a kanki zaki yarda da shi? "



Zuwa wanan lokacin Yar Mahaukaciya ta gama jika da gumi, domin KO ba komai ta san wanan zancen mai matukar mahinmanci ne, tabas wanan zancen mai mahinmanci ne tana rokon Allah ya sa alkhairi ne, idanuwanta ta dago wa'inda suka kara girma na tashin hankalin da ta shiga ta sauke su a fuskokin su hajiya , wani irin kwarjinin su ya daki kwayar idanuwanta da Sauri ta sada kanta kasa cikin gargadar murya ta ce" Mamana, hajiyata, iyayena, kun yanke hukunci a kaina shine kuma kuke yi min shawara? Wacece ni? No a duniya banda mahaifiyata sai ku gareni , kun isa da ni , Ko mai kuka yanke a kaina ni na san alkhairi na ne dan haka bani da musu KO ja da maganar ku"



Wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyoyin su, kaunarta da Karin ganin darajarta da kunyarta suka darsu a zuciyoyin nan uku,


Hajiya Fadimatu ta sauke ajiyar zuciya da ido ta yiwa Hajiya Hawau nuni da ta fadawa Yar Mahaukaciya abinda suka yi ,



Hajiya Hawau ta kara gyara zama ta ce" *Daman ranar juma'ar can da ta shige aka daura miki aure ke da Dan Aljannah* "


Bugawar zuciyar Yar Mahaukaciya daidai da kiftawar idanuwanta, domin kwatakwata idanuwan ta kasa tsayar da su sai kikifta su take, jikinta gaba daya rawa yake, kafafuwanta dake tankwashe ta samu ta hau saman su ta yi tamkar zaman rakumi a hankali cikin rawar jiki ta dauko hanunta guda ta tokare habarta , hawaye wani na bin wani



Jikin Hajiya Fadimatu yayi sanyi, ta taso a nitse ta kamo Yar Mahaukaciya ta dora kanta a saman cinyar ta tana shafawa tana gyara mata gashin kanta da shi kansa ya jike wajen hudodin, har a lokacin jikinta rawa yake sanan bata furta komai ba,



Ta kai minti

Please Login or Register in order to submit comment