Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dake aje gefe ta ce" wanan ranar litinin da ta huce ina zaune ina dinke takalmin nan naki mai igiya ina mitar sai na saya miki wani kafin ku shiga hutu , sai ga dan Aljannah ya tambayeni mai yake faruwa meye nake dinkewa , ni kuwa na fada masa gaskiya nace takalmin yar gidana ne ya tsinke daman sai da na fada mata bazai yi karko ba to kyanlin ya birge ki kika dauko shine nake gyara miki shi dan kar ki tashi tafiya anguwa kuma babu ,

Shine ya ce na kawo su ya amsa ya fita bai jima sosai ba ya dawo min da wanan rungujejiyar akwatin nayi nayi na buda na kasa na rasa meye a ciki sai kin samu hutu daman nace sai mu kai a bude mana


Yar Mahaukaciya ta ce" kinga kuwa akwatin ba karama ba , tana bin rubutun jikin tana ta karantawa sai taga an rubuta o daman hakane a jikin , O, C, K, sai 1,1,2.....0 a hankali ta Dana saman O din , ba Hajiya ba Yar Mahaukaciya kanta sai da ta tsorata a tare suka furta Ya salam

Yar Mahaukaciya ta rufe akwati ruf domin shake take da takalma harda silifas kamar lefen yayan masu kudi, ta kali Hajiya da ta fara washe hakora ta ce" Hajiya wanan na matarsa ne ya kawo miki ajiya kika ajiye a nan


Hajiya lokaci daya murnarta ta koma ciki ta ce" kinji dan nema je ki kirawo min shi 😡


Yar Mahaukaciya ta 😳 ta nuna kanta ta ce " ni??


Hajiya ta ce" to yo kema idan ba yar neman kike son zama ba ramatutu nawa ce a dakin nan , haba zaburi ki je wajen Dan Aljannah ki kirawo min shi nan dakin ni hajiya 😡


Yar Mahaukaciya ta ja hijabinta ta juya uwa Wace Kwaï ya fashewa a ciki🙁 lebenta sai karkarwa yake bata hango idriss ba ya shiga gida ya fito momynsa tayi kiransa , a hankali take tahowa gabanta na faduwa haka kawai take matukar jin tsoronsa ,

Jin shiru ya sa Hajiya fitowa ta ce" la'ila a nan kike ?

Mubasshir ya dago kansa yana kalon su

Hajiya ta karaso ta zauna face dinsa ta ce" Malan Dan Aljannah ka rasa Wanda zaka baiwa ajiyar takalman figagiya sai ni ?😏


Mubasshir yayi sororo shi dai yasan Sahla take kira da Figagiya , to aman wasu takalman?

Ya ce" Madame wasu takalman?


Hajiya ta ce " na cikin wanan akwatin mana 😣


Sai da ya kurba ya hadiye kayansa cikin konciyar hankali ya ce " ba fa na Sahla bane na Yar gidan ki ne , bana son kakata tana shan wahala wajen dinke dinken takalma , tunda Allah yayi tafiyar ba tsari har ana tsinka takalma shi yasa na kawo wanan kafin a gama mata na saudiya wa'inda sosai suke da kwari KO kafar doki ce bazaiyi gagawar tsinkewa ba

Nan da nan hajiya ta shiga murna tana dariya tana godiya ta kali Yar Mahaukaciya ta ce" zo kiyi masa godiya mana yarnan


Yar Mahaukaciya da ta rasa to maganganun da aka dandakara mata kuwa na menene? Ai ita kuwa bata tafiya da Sauri ma balatana ace haka KO don shi ya saya sai ya fada miki ba dadi ta cuno bakinta ta karaso ta ce" an gode , Allah ya kara budi , ya sa ka fi haka


Shi dai bai ce mata komai ba kuma yana kalon yanda take maganar bakin a cune har sai ta dane lebenta take maganar , sai mamakin adu'ar da tayi masa da Sauri ya kuma kawar da kansa a ransa ya ce" amin


Bayan wani dan lokaci Idriss ya dawo sai zuba kanshi yake Hajiya da Mubasshir dai binsa suke da kalo ya zauna shima aka shiga labari da shi , sai tambayoyi yake yiwa Yar Mahaukaciya kan karatunta da kuma kawa nawa tayi , ai ana tabo zancen kawa ta juya ta gyara zama tana bashi labarin diyar fulani da Saurin fushinta ,sai dariya suke gaba dayansu banda Mubasshir da ya san komai kawai ji yake kamar maimaita masa ne ake don komai da take ciki a makarantar sai an kiraye shi an sanar masa shi kuwa ya bada umarnin da ya dace


Hajiya ta waigo ta ce" Yanzu dan Aljannah daga anyi auren zaka dena zuwar min KO?


Ya zaro ido ya ce" kai ikon Allah hajiya nine fa namijin ita matar , itace zaman gida ya kama fa

Idriss ya bushe da dariya ya ce" kaima ya kamaka Malan dan kuwa ni du randa ya angonce sai munyi wata ba inda muka je


Hajiya ta ce " to dan nema sai ka nemi matar ai ,😏

Idriss ya ce" please hajaju ki dena fadar min da gaba kin ji

Tayi murmushi , haka dai cikin raha sukayi ta zantawa Har Yar Mahaukaciya tayi musu sai da safe ta ficewarta dakin Hajiya , tana tafiya Mubasshir ya Mike yayi musu salama suka fito tare da Idriss suna kara tataunawa kan diner DAyar da za'ayi a cikin gidansa Wanda ya gina gari guda a ciki za'a gudanar da diner da zata halara manya manyan baki har na kasar saudiya da chtadi....... ....................


















Asuba ta gari angon Sahla
[15/10 19:18] Official_Amnoor: [13/10 14:37] Sajida: 🇳🇪Belles écrivaines du Niger



*'YAR 👧🏻*

*MAHAUKACIYA👹*

*_Na SAJIDA_*




23
Tunda garin Allah ya waye jama'a ke kai kawo manya manyan mata masu ji da kansu kawayen Hajiya Marhaba , tayi wanan gayar ne dan kawai a tsayar da shagulgulan da za'ayi mawakan da za'a dauko har na wajen diner , da sauransu


Sahla ce ta fito daga dakinta tana waya , Hajiya Marhaba ta ce" beby ina kuma zaki je haka?


Sahla ta juyo ta ce" mom zan je na zabo kalar Wanda zan dora , tayi kirana ta ce ta kawo su jiya


Hajiya Marhaba ta ce " Ohk karfa ki yarda ki jima, sanan ki san da kinyi lulubi saboda kin san ya hane ki fita so ki kula


Sahla ta amsa mata tayi gaba abinta




Idriss ya dago kansa ya kali mahaifinsa ya ce" ina yaro ban taba ganin mutun mai biyayar iyaye kamar ka ba abanah, aman tunda na kawo shekara goma sha uku a duniya sai naga ka fara janyewa da Hajiya , Abanah karka manta Hajiya kai kadai gareta danginku duk babu, Abanah yar uwarta daya ba mai aure a nan bace bata da labarinta ma , shin Abanah idan ka samu dan lokaci na ka zauna kadan da kakata bazaka je ka gaisheta ba ? Tana matukar nisa rashinka a cikin zuciyarta kuma nasan bata barci Haba Babana karka manta fadar Allah ce mu maza mu bi iyayenmu matayenmu kuwa su bimu dan samun tsira a gobe kiyama, a kulun idan muka zauna da ita sai na bata hakuri sai tayi murmushi ta ce ba komai , ya hade hanayensa ya ce" kayi min rai Abanah ka gyara koma meye tsakaninka da Hajiya ka koyar da mu kulawa da tamu mahaifiyar 😌


Mahaifin Idriss , Ilyas ya kare masa kalo gaba daya jikinsa ba kwari ya ce " Idriss please tashi ka bani guri ina bukatar tinani


Idriss ya mike yana adu'ar Allah ya sa mahaifin sa ya gane

Bayan fitar Idriss Elhaj Ilyas ya mike ya har wani juwa yake yana mamakin kansa, mai yake sha'afar da shi da mahaifiyarsa? Yaushe rabonsa da ya kai mata abinci ya zauna ya bata ta ci yana yi mata hira? Mai ke damunsa? Cikin Sauri ya juya daga office dinsa ya shiga motarsa ya nufi gida , yana zuwa ya bar motar a kofar gida gudun kar Marhaba ta Ganshi ya dawo yanzu


Cikin Sauri ya fada bangaren Mahaifiyar sa , sai da ya lumshe ido domin Hajiya ba dai kanshi ba , kulun cikin zambada tiraren huta take na hayaki kalakala , ga tsakar gidanta sai ka yarda Abu ka dauka ka cinye, kai ba dai tsafta ba Allah ya bata abinta ,

Cikin faduwar gaba yake takawa a hankali yana dosar dakin bugun zuciyarsa na tsananta , kuma wani bangare na zuciyarsa na korarsa ya rasa meye wanan, aman a yau kaunar ya ga Hajiya ta rinjayi kin ya ganta,
Sautin dariyarta ya tsinkaya tana fadin" kai aman akoy aiki kwabin fulawa wajen yan mata kadai ta isa ta saka bawa ciwon ciki dan dariya


Yar Mahaukaciya da ta takarkare zaune a saman tabarma ta saka Roba baba tana kwaba fulawar da zasu yi fanke na mutanen hajiya tunda Hajiya ta zuba mata kilo biyu ta kasa kwabeta sai nishi take ita kuwa Hajiya ta ce ai kuwa sai ta koya

Salama yayi inda cikin zabura Hajiya ta dago kanta ta zubawa fuskar gudan jininta ido , kasa amsa salamar tasa tayi dan tsananin mamaki ,
Suna yin ido hudu ya dauki sauki ya je da Sauri ya tsuguna ya dora kansa saman ciyoyinta ya rike kafafuwanta daga kasa ya saki kuka kamar karamin yaro


Yar Mahaukaciya dake zaune ta waigo ta zaro ido , tunda tazo gidan nan yau kadai Allah ya taba hadata da mahaifin Idriss daga kamar ta gane cewar mahaifinsa ne , da Sauri ta Mike ta basu waje

Ya kusan minti goma yana ta kuka a saman cinyar Hajiya Hawau , Wanda kukan ke ratsa duk wata gaba ta jikinta , ta rasa ya zata yi sai ta daga hanunta zata shafa kansa sai ta kasa , ji tayi an daga hanunta an dora saman kan Elhaj Ilyas ta dago kanta tayi ido hudu da *Mubasshir* ya sakar mata wani lalausan murmushi sanan yayi mata nuni da ta kula baban, baiyi magana ba gudun kar ya ganshi a haka ya shige a hankali dakin Hajiyar .

Cikin nutsuwa Hajiya ta ce" mai yake damunka Dan gidan Hajiya?

Da sauri ya dago kansa ya kuma rushewa da kuka yana fadin dan Allah ki yafe min , wly ban san abinda yake damuna ba , na rasa nutsuwata na rasa abinda ke damuna , na rasa farin cikina Hajiya ki yafe min


Hajiya Hawau ta share hawayenta ta ce" kulun cikin yi maka adu'a nake Dan gidan Hajiya , ka sani Allah yana tare da mai gaskiya kuma ka kara riko da adininka Allah ya baka lafiya

Elhaj Ilyas ya ce" Amin na gode Allah ya kara tsawon kwana da lafiya , nan fa tsakani uwa da Da suka shiga hirar su




Mubasshir na shiga ya tarda Yar Mahaukaciya zaune saman wata kujera mai tsayi tana kalon madubi da macaji ( masarci) a ganunta tana caje gashin kanta da kyar sai nishi take dan kuwa daga ta caje sai ya koma ya nanade kansa haushi ya kamata ta wurgar da macajin tana fadin wly sai na askeka gaba daya ma na huta , haka kawai



Mubasshir dake tsaye yana kalonta yau dai yayi niyar sai ya san wai atach ne take sakawa KO kuwa haka kalar gashinta yake ,


Yayi gyaran murya ,

Da Sauri Yar Mahaukaciya ta kale shi , sam bata ji karar shigowarsa ba , kuma tirarensa da ya zama KO da yaushe yana gidan sai ya kasance kanshin tiraren KO yaushema jinsa take a hancinta hakan yasa KO yanzun da tana caje kanta ta dan ji kanshin bata wani kula ba , tana ganinsa ta shiga neman hijabinta da a tinaninta saman bed din Hajiya ta ajiye shi , da Sauri ta bude akwatinta ta dauko na makarantarta ta zumbula Sanan ta shiga kikifta ido,



Mubasshir shi abin nata dariya ma ya bashi wai kariya bayan bugu , aman sam bai daran ba ya ce" menene kike kokarin rufewa tamkar naki bayan kin loda gashin doki KO na matacen mutun a kanki ?


Yar Mahaukaciya jin an ambaci ta loda gashin matacen mutun a kanta ya saka ta kwalalo ido waje ta ce" karde aje gashin nan na matacen mutun din ne?


Mubasshir ya kaleta a ransa ya ce zata raina min hankali , a fili ya ce" ya zanyi miki tambaya kiyi min ni ma?


Yar Mahaukaciya tayi kalar tausayi ta ce" wly kaga gashin mutane duk baki ne, gashin Fati ma baki ne, haka na princess da su Tina su Mariam duka baki ne, kaga kuma ance idan mutun ya mutu gashinsa fari yake zama, kuma ni tun ina yarinya yara idan suna bina sai suna cewa Yar Mahaukaciya mai farin gashi matata, ...... Maganar ta tsaye mata a makogwaro lokacin da ta ambaci sunanta a gaban Dan Aljannah da Sauri ta rufe bakinta ta tura bayi tayi shigewarta

Mubasshir dake tsaye yana sauraronta gaba daya zancen ya shige masa duhu mai take nufi da yara na kiranta da *Yar Mahaukaciya*? Mai hakan ke nufi?


Sahla dake labe tana sauraron su ta jiyo gaba daya abinda suke fada ranta ya gama baci ya mijin da zata aura ya zo yana magana da wanan banzar? Kuma taji Ashe ma ita din *Yar Mahaukaciya ce*, ai kuwa zata fadawa momy tun wuri ayi maganin wanan abin tun kafin a jaza mata bala'i








Wayo Yar Mahaukaciyata
[13/10 14:37] Sajida: 🇳🇪Belles écrivaines du Niger



*'YAR 👧🏻*

*MAHAUKACIYA👹*

*_Na SAJIDA_*









25

Mubasshir ya zubawa mahaifiyarsa ido yana nazarin karyar da zai tafka mata domin gaba daya ya daburce baima san abinda yake fada ba har ya furta haka , to wai shi mai ma ya dameshi da lamarinta ? Da gani tanada tabuwar hankali dan kuwa abinda take furtawar nan ba na masu hankali bane ,

Tabashin da mahaifiyarsa tayi ne yasa ya dawo daga tinanin da ya kuma fadawa ya kaleta ya dan yatsina fuska ya ce" mamana Sahla ce ta fiya rigima , kinsan bana son harkar kade kaden nan yayi yawa ita kuwa ta kuke wai aurenta tana son kowa ya sani


Mahaifiyarsa ta zuba masa ido na wajen seken talatin tayi murmushi ta shafa fuskarsa ta ce " Yarona sadauki ne irin haka bazai taba tayar masa da hankali ba , sanan karka manta yaro bazai iya yiwa mahaifiyarsa wayo ba sai dai ta kawar da kai ta nuna cewar bata gane ba , ina mai baiwa yaron Fadimatu shawarar ko ma mai yake damunsa ya kama Allah shi ne mai komai mai kowa ,

Ta mike a nutse ta kontar da kansa dan kuwa duk da hakan ba na farko bane aman a kulun yana mamakin yanda akayi Mahaifiyarsa take karantar zuciyarsa , ya san bayan ita ba wanda ya isa ya gane yanayinsa , cikin nitsuwa ta ja masa bargo ta mike ta daidaita masa ac din dakin ta sauka wajen bakinta




Tunda Sahla ta jewa mahaifiyarta da labarin tana kokonton Idriss na son Wanan yarinyar da mahaifiyarta mahaukaciya ce Hajiya Marhaba tayi masa inkiya da zuwa wajenta duk da ba kirikiri ta hana shin ba aman fir daga ta aike shi nan sai ta aike shi nan


A bangaren Yar Mahaukaciya suma nasu shirin suke ita da kakarta Hajiya Hawau sam babu abinda ke damun su domin suna da komai na aikin su ,

Ana jibi daurin auren Mubasshir da Sahla da dare Hajiya Hawau ta kwaba kunshi na hausa ta kunsa a kafarta sanan Yar mahaukaciya ma ta daidaita ledarta ta kunsa mata har a hanunta daya suka yi konciyarsu

Kiran salar farko ya tashe su suka cire kunshinsu suka gabatar da sallah

Bayan sun gama Yar Mahaukaciya ta tsuguna ta gaishe da Hajiya Hawau

Kamar yanda ta saba tayi mata nasihohinta sanan ta dora da cewa " rabonsa da gidan nan tun ranar da Dan Gidan Hajiya ya zo


Yar Mahaukaciya ta kaleta ta ce" wa fa?


Hajiya ta ce" Dan Aljannah mana jiya har mafarkinsa nayi


Yar Mahaukaciya ta mike tana murmushi ta ce" kai soyayar Hajiya da Dan Aljannah, To Allah ya sa lafiya


Hajiya ta ce" bawan Allah nasan zulumin zai auri tashin hankali ne ya hana shi fitowa Allah dai ya fida shi lafiya


Yar Lahaukaciya tayi Murmushi ta ce" Amin ta FITA ta shiga harhada kayan aikace aikacenta sanan ta ciro furar tasa ta shanye tana fadin kar aje ta lalace



Karfe Uku na yama Fati Yar Adamawa tayiwa gidan su Idriss dirar mikiya , zo ka ga murna wajen Yar Mahaukaciya ta rasa ina zata saka kanta haka itama Hajiya Hawau ita da kanta ta kara gyara musu dakin Yar Mahaukaciya dan su sauka a nan suyi zaman su dan su sake


Fati tana zaune tana kalon Yar Mahaukaciya dake ta zuba ta ce" wai na tambayeki ina shirye shiryen taron bikin?


Yar Mahaukaciya ta nuna mata kunshin kafarta ya na tsohuwa ta ce " gashi kuwa


Fati ta bushe da dariya tana nuna Kafar Yar Mahaukaciya ta ce" Aman wly ke dai ina kawai dan kakus tayi kunshi kema sai ki wani tashi ki dadabka abu a kafa? Malama tashi maza mu goge shi , ta ciro wani abu a Jakarta ta gogogawa Yar Mahaukaciya a kafa da hanu nan da nan suka fara zapi , a nan suka shige bayi ta wanke mata suna fitowa Fati ta zazage jakarta sai ga lale ya fado da ja da baki , ta dauka ta shiga kwabawa cikin ledar ruwan sanyi ,ita dai yar Mahaukaciya kalonta kawai take dan kuwa bata san ta iya zana kunshi ba


Fati ta ce" To malama kalon fa? Dan Allah ki canza kayan nan kar mu bata su dan kuwa sunyi Haske da yawa


Yar Mahaukaciya ta juya ta dauko wata doguwar rigarta ta atamfa mai duhu sosai ta saka sanan ta saka hularta baka abinka da farar fata , ita ba wani ado tayi ba aman ta hadu ta dawo ta zauna tana kalon Fati


Cikin nutsuwa da kwarewa Fati ta kama hanunta ta zana mata kunshi dan ubansu , Yar Mahaukaciya sai murmuqhi take dan kuwa ya mugun birge ta har yan yatsunta sai da ta zana musu mai kyan gaske , sanan ta kama kafar sai labarinsu suke suna kyakyata dariya



Wata lalausar fata da wanan mahaukacin kanshin dake saka bawa nutsuwa taji gak da ita sanan wani abu mai sulbi ya taba hanunta
Cikin sauri ta dago kanta idanuwanta suka sauka saman fuskar Dan Aljannah wato *Mubasshir* Ya tsuguna ya kama tsintsiyar hanunta inda ba kunshin yana kalo tamkar Wanda yaga wani sabon abin da bai taba gani ba ,

Ya sha wata dakakiyar shada kalar marun sai kyalkyali take kai kace yaune daurin auren , ya dago kansa ya kali Fati da tayi mutuwar zaune tana kalon tsararen halitar nan ba idonta kadai ba daidai da bakinta tayi masa wangalau uwa kofar na isa tana kalonsa yau gata ga Mubassir AA a fili ba a TV ba


Mubasshir da har a lokacin hanunsa rike da tsintsiyar hanun Yar Mahaukaciya Wace take jin uwa fitsari zai kufce mata dan Sakata ya ce """""""""""""""""""""""".................."""""""""""""
[13/10 14:37] Sajida: 🇳🇪Belles écrivaines du Niger



*'YAR 👧🏻*

*MAHAUKACIYA👹*

*_Na SAJIDA_*




24
Sahla na fita ta ficewarta ta nufi cikin gidan su, tana zuwa ta shige dakin mahaifiyarta tana haki,

Hajiya Marhaba na ganin yanayin yar Tata ta Mike ta nufi dakinta tana fadin tana zuwa, tana shiga ta tarar da Sahla tana ta haki ta ce" Beby lafiya?


Sahla na ganin mamarta ta fashe da kuka har tana buga hanayenta jikin bed tun karfi

Hajiya Marhaba ta je da gudu ta rike hanunta tana fadin Beby wa ya taba miki zuciya haka? Fada min uban wa ya taba min ke? Idriss ne KO?


Sahla ta shiga sauke ajiyar zuciya ta ce" mom ni fa kawai a kori yarinyar nan daga gidan mu , gaskiya ta fara fice Gona da iri ,


Marhaba ta ce" wace yarinyar?

Sahla ta ce " wanan mai kalar fatar zabaya mana,


Hajiya Marhaba ta ce" toh mai tayi ?


Sahla ta dago kanta ta ce" kinga irin yanda Yaya Idriss ke kashe mata kudi kuwa? Sanan yarinyar uwarta Mahaukaciya ce , tana nan tana hauka kina son samun sirika Yar Mahaukaciya ne? Kuma duk da Mubasshir ya tsaneta hakan baya hana shi zama inda take, kinga tun wuri kiyi maganinsu dan kuwa yau naga dad a wajen Hajiya .



Hajiya Marhaba ta zabura tana dafe kirji ta ce" what? Dadyn naki ne ya tafi wajen Hajiya? To mai yasa bai fada min ba? Mai yaje yi wajenta ? KO dai asirin nawa ya karye? Kam akoy matsala ,

Ta juya ta dauko wayarta ta dana kira tayi ciki ta bar Sahla zaune tana dariyar cin galaba , sanan tayi kwafa tace" da naso na barki ki dan gana da danki aman tunda kika fifita wata bare a kaina ni da ke sai dai sheri ba dai khairi ba ( Allah ya shirya mana yayanmu )


Mubasshir ya jima tsaye bata fito ba kuma yaji tafiyar Aban Sahla hakan yasa ya juyo ya fito ya yiwa Hajiya salama ya nufi gidansu zuciyarsa cunkushe da abubuwa kala daban daban,


Yana shiga yaji sautin wakar larabawa hakan yasa cikin farin ciki ya dan kara Sauri ya isa baban falon mahaifiyarsa , ai kamar jira ake yana saka kafa yaji gaba daya an shiga watsa masa tirare , ta ko'ina wasu na fesawa sai hamdallah suke , daga gefe kuwa Ashe mawakiyar ce suka zo da ita takanas sai yi take tana juyin nan na larabawa,

Mubasshir ya sada kansa kasa da kyar yake iya cira kafarsa yana dana sanin zuwansa a wanan lokacin gashi suna kokarin rikita masa lisafi ,


Hajiya Fareedah ce ta taso ta kama hanunsa ta karaso da shi kusa da mahaifiyarsa ta ce" yarona an girma, Alhamdulilah yau har zan wankeka , Allah mai kyauta da kari ,Mubasshir ya zama ango


Mahaifiyar Mubasshir tayi murmushi da taga sai kawar da kai take , tasan baya son kida yayi yawa , baya son yawon hayaniya, inda ya sha banban da ita domin ita tana mugun son mutane tana son KO wani motsi zata yi ta jita kusa da mutane ,
Ta ce" nurul'ayne mai yake damunka?


Hajiya fareeda tayi caraf ta ce" ku shiga daga ciki mana sai ya fada miki aman a nan bazai yiwu ba tunda kinga akoy mutane da yawa


Mubasshir na jin an bashi damar tashi ya Mike yayi sama , ya nufi dakin mahaifiyarsa ya konta ya lumshe idanuwansa yana fadin wacece ita? ( wai mai ya shafeka malan 😏 )


Cikin nutsuwa ta turo kofar ta shiga da salama aman bai ma san ta shigo ba , ya lula duniyar tinani ,

A nitse ta ISO ta tsaya a kansa tana mamakin abinda yake saka Mubasshir cikin tashin hankali haka tana mamakin abinda ke saka shi tinani haka , KO yana tina mahaifinsa ne? KO taron nan da yayi yawa ne yake damunsa?

Ta kai minti ashirin a tsayen nan bai san tana wajen ba hakan yasa ta matsa ta zauna kusan sa ta dago kansa ta dora saman cinyarta ta ce" mai yake damun Mubasshir da har ya kasa fadawa mama?



Mubasshir ya dago kansa ya ce" maman Mubasshir al'amuranta na mugun daure min kai


Mahaifiyarsa ta ce" Al'amiran wa fa?


Sai a sanan ya Ankara da abinda yake fada ya dago idanuwansa da suka rine ya ce"""""""",,,,,,,,,,,""""""""""












🙋🏿
[13/10 14:37] Sajida: 🇳🇪Belles écrivaines du Niger



*'YAR 👧🏻*

*MAHAUKACIYA👹*

*_Na SAJIDA_*




26

Cikin nutsuwa ya ce " wanan abin da kuke zanawa fa na aljanu ne


Yar Mahaukaciya sarkin tsoro ta zaro ido tana kalonsa , Fati kuwa ina bakinsa kawai take kalo da

Please Login or Register in order to submit comment