Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tana Yi maka karya ka yarda har kana zubar da hawayenka, da ganin zagar idanuwan yarinyar nan ka San Yar bariki ce ba karama ba Aman har a iya sauraron ta harma a aurawa mijina ita bayan ba a San asalinta ba?

wani irin kalo ya watsa mata Wanda ya sa yata hadiye sauran maganar ta, yana Al'ajabin daman haka take? Bata da kunya har ya dauketa tamkar Yar sa ya Cikin sa yake kyautata mata? Daidai da rigimar mota da ta Dora mahaifiyarta ta kawo Karar MahaifinTa ya ki saya mata da yayi masa magana ya nuna bashi da Hali hakan ya saka aka kawo mata ashe bata da kunya? Ransa ya Kai kololuwar baci ya buda baki ya ce"""""""""""""""""""""""""""::::::::::::::::::::::::::::::::::::""""""""""""""
[13/1 07:25] Official_Amnoor: [6/1 08:26] Sajida: 🇳🇪Belles écrivaines du Niger



*'YAR 👧🏻*

*MAHAUKACIYA👹*



*Na*
*Sajida*







*66*
Sahla cikin kuka har tana kokarin shidewa ta ce" sun cuce ni, sun wulakanta ni, ashe dama Mubasshir macuci ne ? Azalumi ne ? Allah ya isar min, sanan sai na halaka su daya bayan daya


Idriss ya zuba mata ido yana rike da ita, cikin muryar tausayi ya ce" mai yayi miki ne ? Sahla ki dena irin maganganun nan ba kyau, ki dena please, ki tashi na wanke miki jinnin nan, ki nutsu sai muyi maganar


Sahla ta kara fashewa da kuka ta ce" Yaya Idriss zaman dadiro fa yake yi da ita, karuwar sa ce ashe, shi yasa ya nacewa zuwa wajen hajiya da nufin shan fura ashe da abinda suke kulawa ?


Daidai wanan lokacin gaban Idriss sai dukan tara tara yake, da sauri ya matse hannunta ya dagota cikin kakausar murya ya ce" ki dena, ki dena kokarin kayar min da gaba, ki dena kokarin ganin bugun zuciyata ya tsananta, ki fito ki fada min inda zancen ki ya nufa, shin Wa kike nufi ? Da Wa Mubasshir ke cin amanar ki ?


Sahla ta dago idannuwanta ta kali yayanta ganin yanda yake Bari, ta ce" eh wannan mai kama da aljannun, da ita nake, ita na kama da Mubasshir à dakin sa a saman bed dinsa

Da sauri ya ja baya yana girgiza kai ya ce" no, no Sahla, Rahama *Tawa ce* ni kadai, abinda nayi mata bazai saka tayi fushi da ni ba har ta kula wani na, sanan kudin sa KO kyan sa bazai saka ta juya min baya ba domin ni din nan ni zan fadi irin halayar Rahama na, bazata taba yin taraya da wani namijin da ba muharaminta ba, yana dai lalabarta ta yafe min ne na aureta muyi rayuwar mu cikin SO da kaunar juna, baki gani da kyau ba, ya karashe yana langwabar da kansa irin ta bashi karin haske à abinda ta gani,



Sahla ta Mike tsaye ta dafa hannun yayanta ta ce" idannuwana basu yi karya ba, tabas kusancin da na tarar yafi karfin aminta, ka Sani indai da boka KO malan sai inda karfina ya kare, na haramtawa wannan yar mahaukaciyar mijina, ta juya ta banko kofar




Idriss ya zauna dabas yana fadin "no Mubasshir ba mazinaci bane, haka Rahama, to mai Sahla ke nufi ? Ganin yana kokarin fadawa wani tunanin ya saka shi mikewa yana kokarin kamala aikin da ya fara sai ya je gidan su Mubasshir din ya ji yanda suka kaya ta amince ta aure shin KO aa ? (🤔 eyah Idriss)


Karfe hudu da rabi sun gama cin abinci, Hajiya Hafsat ta kali yar mahaukaciya ta ce" Yar aunty tashi ki leko min yayanki KO ya farka ?


Da sauri yar mahaukaciya ta dago kanta gabanta ya yanke ya fadi, tsoro ya shiga zuciyar ta,

Hajiya hafsat ta kawar da kanta dan ta karanci tsoro à fuskar y'ar Tata,

Yar Mahaukaciya ta Mike gwuiwa à sace ta nufi sama , tana zuwa kofar dakin da ya zama malakinta bugun zuciyarta ya tsananta, rintse idannuwanta tayi tana karanto duk abinda ya Zo mata bakinta,

Cikin ikon ALLAH ta samu kwarin gwuiwa, ta tura dakin ta shiga kanta à kasa tana harde kafafuwa,


Mubasshir da fitowarsa kenan daga Wanka dalilin ruwan sanyi da elhaj Muhammad ya saka shi anfani da shi da kuma sanyin AC ga daman mutumin ba dama, hakan ya hadasa masa shiga wani yanayi marar musaltuwa, wannan shigarsa Wanka na uku ne yana sakarwa kansa ruwa aman sai kara mumurdewa yake,

Kalonta yake tamkar sabuwar halita, ganin ita Bata karaso ba, sanan ita Bata juya ba ya saka shi yin gyaran murya,


À hankali ta dago kanta, idannuwanta suka sauka à kan Mubasshir dake tsaye daure da tawul, ido ta zaro tana dafa kirjinta tayi saurin tsugunnawa kasa ta rufe idannuwanta ta dora hannayenta biyu saman kanta ta ce" na shiga uku,


Mubasshir ya zaro ido yana kalonta, tamkar wace ta ga wani dodo, à hankali yake takowa sai da ya ISO Daidai ita ya ce" malama kin Zo karbar hakinki ne ? Mai yasa baki da hakuri ne islam ?


yar Mahaukaciya ta dago kanta da haushi haushi ta mike da niyar ramawa wata kunyar ta kuma darsun mata bazata iya jure kalonsa à haka ba, ta juya da sauri zata bar dakin

Mubasshir yayi taku biyu ya riko hannunta ya juyota da karfi ta fado kirjinsa, gaba daya gashin kanta ya rufu à kirjinsa, ya saka hannunsa na dama ya dago habarta idannuwanta à rufe ruf, bugun zuciyarta na bugawa tun karfi tamkar nasa, à hankali ya saki murmushi ya ce" *u love me yarinya*


yar mahaukaciya ta bude idannuwanta da suka tara kWallah à cikin su ta zubawa fuskar Mubasshir ido, gabanta ya kuma faduwa ta rintse idannuwanta ta kuma budewa tana Jin wani abu na ratsa sasar jikinta tun daga kanta har kafarta, cikin karfin hali ta ce" *No, bana sonka AA*

Kafin ta rufe bakinta ya hade bakinta da nasa ya shiga kissing, kis din da bai san ya iya shi haka ba, kis din da bai san haka ake ji ba, yayi haka ne da niyar ya hukunta bakinta da ya furta abinda baya cikin zuciyarta, yayi haka ne dan kar ta kuma furta abinda zai iya halakashi sai dai kash ya kasa control din kansa, ya kasa hana kansa dena kissing din Islam, ya kasa raba jikinsa da nata, gaba daya jikinsa Bari yake ya dagata yayi saman bed da ita, cikin rawar jiki ya kama rigarta ya................... 😳😳😳😳😳😳😳😳😳😳😳😳😳😳😳😳😳😳😳😳😳😳😳😳😳😳😳😳😳😳😳😳😳😳😳😳😳😳😳😳😳😳😳😳😳





*Dan Allah ku gafarceni na jinkirina, abin ne yayi yawa, insha ALLAH na kusan gama shi, sanan Wa'inda suka tambayeni farkon sa KO karshen sa kuyi hakuri zan nemo muku cos na canza wayar ne nima banda shi, rashin sanin amsar da zan baku ya saka banyi muku replay ba, Ina kara godiya masoya ALLAH ya sa ku yi min uzuri, love u all* *SAJIDA*
[6/1 08:26] Sajida: 🇳🇪Belles écrivaines du Niger



*'YAR 👧🏻*

*MAHAUKACIYA👹*



*Na*
*Sajida*




67

*My Aïcha, aishata, tawa Ina mugun yin ki, irin da yawa din nan, wannan page naki ne gabaki dayansa lv u*





Kokarin sabule mata rigar yake gaba daya hankalinsa ya fara barin jikinsa, jikinsa sai bari yake, gashi bakinta à nasa yana ta kissing bai Bari ba,

Yar mahaukaciya sai kicikicin din kwace kanta take domin wannan lamarin ya girmi tunanin ta, yafi karfin kwakwaluwarta da gangar jikinta, sai zare ido take jikinta na Bari,
Dagewa tayi, tayi wani motsi hade da nishi nishi domin ta kasa ihu sadaniyar rike mata bakin da yayi,

Idannuwansa ya dago Wa'inda suka rine suka yi jajawur da su ya sauke à cikin kwayar idanuwan yar mahaukaciya wace nata sun cika da kwalah, sai jujuya su take tana kokarin isar da sakonta ta hakan,

Cikin yanayin bukatuwa ya cika mata bakin ta, ai kuwa ta fashe da kuka tun karfinta tana shasheka


Mubasshir ya tsareta da ido yana kalonta, karfa ta raina Masa hankali, ai bazata ce kuka rashin sabo ne ba dan kuwa koda jama'a zasu taru à kansa bazai yarda cewar Bata saba da wannan ba, KO du wannan kukan na Bata son sa ne ? Shi bai ce baya sonta ba sai itace zata yi irin haka ?

Cikin kukan ta ce" ni karka kuma taba min jikina ni ba yar 🙊 , ta hadiye maganar ta sakamakon tunawa da tayi da Wa take magana,
Kokarin saukowa take daga bed din ya jawo hannunta ta fado saman kirjinsa ya dagota ya ce" baki gama yi min kashen ba kuma zaki tafi ?


Yar mahaukaciya ta sada kanta bugun zuciyarta na tsananta, ta kasa magana


Yaci gaba da fadin" mace bata gindaya min sharuda, nine namijin ni zaki bi komai matsayinki dole ki duka min, dole ki gaishe ni, dole ki bi umarni na, sanan wannan yayi Nuni da jikinta y'ace" gonata ne, à koda yaushe, à KO wani irin yannayi inada iikon shigarsa na fita à shi ba tare da wani KO shi kansa sun yi min iyaka ba, da ke da jikinki malaka ta ne, ki guji juya min baya KO kokarin tsayar da ni idan na bukace shi, i'm i clear ?


Yar mahaukaciya ranta ya gama baci wannan shine à dakeka à hanaka kuka, Taya zai mayar da ita tamkar wata propriété 🤷🏻‍♀, ta rintse idonta cikin wata irin murya mai Shegen dadi ta ce" ni na san zan zamto ne tamkar baiwa à wajenka Yaya AA, har yanzu ni ba kowa bace face mai neman kanta, Ina neman kaina sosai, karka damu KO don gudun kar na kuma tsintar kaina à wacen rayuwar zanyi kokarin kaucewa bacin ranka,

Gaba daya jikinsa yayi wani irin sanyi ya rasa mai zaiyi kawai sai ya jawota jikinsa ya rungume ta tsam à jikinsa yana Jin yanda sonta yake bin sasar jikinta yana ratsa KO'ina na jikinsa,


Wayar sa dake ajiye à saman bed din ta kwashi tsuwa tun karfi tana shaida Idriss ne ke Kira,


à tare gabansu ya fadi tayi saurin mikewa shima ya mika hannu ya dauko yana wani kawar da kai uwa yana gabansa,
Da kyar ya samu ya daga wayar ya kara à kunnansa



Idriss ya ce" mutumina ya garin ? wai kana inane Ina ta nemanka ✌🏻 days ?


Mubasshir dake kalon Islam ta juya baya tana tafiya bayanta sai juyawa yake har ta bar dakin ya saki ajiyar zuciya


Idriss ya ce" llafiya nake Jin muryarka wata iri ?


Mubasshir ya ce" Lafiya lau likita


Idriss ya sauke ajiyar zuciya ya ce" gani fa kusan gidan zan biyo naji yanda kuka yi da kakus ta fada maka inda princess take ?


Mubasshir ya Hadiyi wani yawu kafin yayi magana Idriss ya katse wayar,

Da sauri ya mike yabi jikinsa da kalo ya kali kofar dakin ya kuma kalon wayarsa à hankali ya furta chuiiiiiiiiiiiiiiiiiit ya zanyi ?









Na sani👵🏽👵🏽👵🏽👵🏽👵🏽👵🏽👵🏽👵🏽👵🏽👵🏽👵🏽👵🏽👵🏽👵🏽👵🏽👵🏽👵🏽👵🏽👵🏽👵🏽👵🏽👵🏽👵🏽👵🏽👵🏽👵🏽👵🏽👵🏽👵🏽👵🏽👵🏽👵🏽👵🏽👵🏽👵🏽
[6/1 08:26] Sajida: 🇳🇪Belles écrivaines du Niger



*'YAR 👧🏻*

*MAHAUKACIYA👹*



*Na*
*Sajida*






68

Tafe take tana adu'ar ALLAH ya sa kar à gane AA ya taba mata jikinta, tana saukowa ta tarar basa nan sai auntyn ta, cikin sauri ta nufi kofa dan gudun kar ta gane abinda ya faru da ita,



Tana kokarin bude kofar Idriss ya turo ya shigo, ido ta zaro tare da wata faduwar gaba

Shi kansa saï da gabansa yayi wani mugun faduwa Wanda bai san Dalili ba,
Hakoransa ya washe da alamun murna à fuskarsa ya nuna Yar mahaukaciya ya ce" Princesse, ke ce ? daman kina nan ? daman abokina ya taimakeni ya kilace min ke ?



Yar mahaukaciya ta fara ja da baya cike da tsoron sa da kuma tinanin lokacin da ta kamo rigarsa tana kukan ya taimaketa kar à kore ta daga gidan su ya bige mata hannun sannan ya tunkuda ta, raurau take da idannuwanta tana girgiza kai


Gaban Idriss ya ci gaba da Faduwa tsoro da fargaba suka darsu à zuciyarsa, cikin kalar tausayi ya ce " haba Rahama ta, karki ji tsoro na KO ki guje ni, kar abinda nayi à rashin sani ya saka ki guji zuciyar da ta ginu da kaunar ki, kiyi hakuri ki saurare ni dan Allah, ya mika hannun sa da niyar ya riko nata hannun domin yakan rike hannunta ba tare da wani tunani ba


Yar mahaukaciya ta rintse ido ta ce" don't tuch me Idriss, karka yarda ka taba min hannuna


Daidai lokacin hajiya hafsat ta taso don ganin wannan ikon ALLAH, shi kuwa wannan wanene ? Mai kalamansa ke nufi da baby ?

Tana isowa ta ce" malan Lafiya ? Wanene kai ? Mai kake SO ?


Idriss ya juyo yana kalonta, gabansa ya fadi haka kawai, ya kaleta tsananin kamarta da Rahama har ya baci, ya juya yana yi musu kalon kurilah, Daidai nan Hajiya Rafi'at suka fito ita da elhaj Muhammad tana rike da banban plat da kwanoni à sama, shi kuwa yana rike da assietoci da cokula da dan kondon fruits sai murmushi take zuba masa shi kuwa yana ta labari


À tare suka juya suka zuba musu ido, inda suma à lokacin suka lura da mutanen dakin,

Cikin nutsuwa Hajiya Rafi'at ta ajiye abincin, ta karbi na hannun mijinta ta ajiye , daidai nan Idriss ya kara matsowa kusan su hajiya Rafi'at dan ganewa idanuwansa wata mai kama da yar mahaukaciyarsa kuma,


Yana karasowa sai ya ga ai wannan elhaj ne uban gidan mahaifinsa, Wanda Tunda abansu ya hadu da shi hanyar arzikinsa ta budu , shi ya bada goyon bayan karatun sa ma da kuma aljihunsa har ya samu ya cimma burinsa na zama Baban Docter,

Cikin yanayin rudu ya ce" aba, kaine à nan ?


Elhaj Muhammad da har yanzu gaisuwarsa sai ya dan rungume mutun banda mata ya matso yayi masa irin gaisuwar larabawa ya ce" son daga Ina haka ?



Idriss ya juya yana kalon kwayar Idon yar mahaukaciya ganin iri daya da na elhaj ya ce" Aba Ina cikin rudu, naga Rahama na kama da Wa'inan, yayi nuni da su hajiya Rafi'at, ya ci gaba'
Sanan saï naga hasken fatar ta da idannuwanta


Elhaj Muhammad ya karasa fadin" da yatsunta, da hancinta, da tsayinta, da yannayin maganarta duka nawa ne, son kaga *Kanwarka*, *Y'a ta daya da na malaka à nan gidan duniya*


Idriss ya zaro ido ya juyo yana kalon yar mahaukaciya da alamun tambaya à bakinsa


Daidai zata yi magana Mubasshir da saukowansa kenan kuma ya fahimci yannayin Idriss ya ce" *Freind* sunanta *Fadimatul islam* sannan yaron da ya rasu à asibitin ka kaninta ne, ga mahaifiyarta, ga kanwar mahaifiyarta ga mahaifinta sannan ita ba zawara bace ,


Idriss ya ce" Freind please ka kuma wayar min da kai, nasan baka taba yi min karya ba, sannan aba bazai yi min karya ba, ya juya ya kali Yar mahaukaciya da tayi tsuru ya ce" sannan ban ga dalilin da Princess zata yi min karyar rayuwarta ba



Mubasshir ya rintse ido, wai wani Princess, ya kawar da kansa,

Hajiya fadimatu ta ce"mu zauna na fayace maka komai game da y'a ta,


Haka suka dugunzuma suka zauna inda hajiya fadimatu ta gyara zamanta tana yiwa Idriss bayanin duk abinda aka fada mata yan awani da suka shude, Wa'inda Idriss kawai ya kurawa yar Mahaukaciya ido cike da tausayin rayuwar ta, ashe ita mai mugun gata ce haka ?


Tinaninsa ya tsaya daidai lokacin da kunuwansa suka jiyo masa mugun labari mai rikitarwa mai tsoratarwa Wanda yayi imanin kawai sakarkarun kunuwansa ne suke jiyo abinda ba'a fada musu ba, toh inba hakan ba à labarin Princess dinsa mai ya kawo cewar an daura mata Aure da amininsa AA Mubasshir ?



Cikin wani irin yannayi ya juyo da kalonsa wajen Mubasshir yana wani dan murmushi ya ce" Freind wai kaji kunena saï gizo yake yi min KO ?


Mubasshir ya kawar da kansa yana kalon Yar Mahaukaciya, cikin kakausar murya ya ce" Islam ki je daki ki saka hijab saï ki sauko


Yar Mahaukaciya ta kale shi, à maganar sa babu alamun wasa à cikin ta, hakan yasa ta Mike a nitse ta nufi matatakalar benen don aiwatar da umarnin AA,


Idriss ya zaro ido ya Mike tsaye yana binsu da kalo ya ce" Mama kina nufin an daurawa Rahama Aure da Mubasshir ?


Hajiya Fadimatu ta zuba masa ido tana kalon sa,

Elhaj Muhammad ya ce" son What's happen ?


Idriss ya ce" Aba dan Allah kar ku yi min haka, wly ni nake son ta, dan Allah karku huce abinda Nayi mata ta haka, wly wly à rashin sani na aikata haka, aman ni Nafi kowa son zama da ita, ban san ya akayi na kasa sauraronta ba ku yi min rai karku rabani da ita,


Ya juya wajen Mubasshir dake kalonsa yayi saurin rike hannunsa ya ce" broth kafi kowa sannin Ina sonta dan Allah ka ce ka barmin ita


Mubasshir ya kawar da kansa zuciyarsa na bugawa, tabas da ace ba'a rigayi daura masa Aure da Islam ba da ya hakura ya barwa Idriss koda hakan zaiyi sannadiyar rasa farin cikinsa KO rasa nunfashinsa gaba daya, domin Idriss dan uwa ne à wajen sa


Dafa kafadarsa aka yi ya juyo ya sauke Idannuwansa à fuskar wace ta dafa shi, ba Wanda ya san da ta shigo domin hankalin su du ya tashi, dan kuwa Idriss d'à ne,


Hajiya hawau kenan tsohuwa mai ran karfe, Tunda aka gama rikicin iyayen Fadimatul islam hajiya fadimatu tayi kiranta kan tazo ta ga abin mamaki

Tun lokacin da hajiya fadimatu ta fara bada labarin yar mahaukaciya ta shigo falon domin a bude Idriss ya barshi yana dokin ganin yar mahaukaciya

Cikin nutsuwa ta ja hannunsa suka zauna

Ya jima jikinsa na Bari kansa à saman cinyarta tana tofa masa adu'a har ya daidaita numfashin sa,

Hajiya hawau ta ce" alhamdulilah, alhamdulilah, Idriss ka dawo cikin hayacin ka Tunda har ka tina ta,

Idriss Kasan cewar wani baya auren matar wani sannan wani baya haifan d'an wani, tabas mun hada auren nan dan gujewa Islam rigimar mahaifiyarka aman ka Sani kafin mu hada shi sai da muka yi listahara mun saka anyi mana tsakanin ka da ita, da kuma tsakaninta da Dan Aljannah, cikin ikon ALLAH ALLAH ya dora mu kanta da dan aljannah domin shi muka barwa zabi ,shi ya san abinda ke boye

Ka dauki wannan abin à zuwan kadarar ubangiji Idriss, karka manta wani ransa ya rasa, wani ya rasa mahaifiyarsa KO mahaifinsa KO matarsa KO dansa aman yayi hakuri, Idriss Tunda kuwa Bawa yana iya jure rashin mutun dungugun à gidan duniya lale zai iya rasa komai ya dangana da ikon ALLAH saï ALLAH ya jikansa ya jagoranci lamuransa,
*Ya kai jikana Ina yi maka gargadi da kawar da kai daga hukuncin ALLAH saï kaga ka gama da duniya lafiya*


Ba Idriss ba elhaj Muhammad kansa saï da zuciyarsa ta karaya da wannan gargadi na wannan tsohuwa mai hangen nesa da yarda da adinninta wato *Musulunci*


Idriss ya share hawayen sa ya dago rinanun idanuwansa ya ce" na gode hajiyata, Allah ya kara Lafiya, insha ALLAH daga yanzu na dena wannan maganar, Allah ya bani Wanda zata maye mini gurbinta


Gaba daya suka amsa da ameen, inda ya mike suka gaisa da Mubasshir ya ce" hei freind ka kula min da kanwata, kar Inji kar in gani abinda zai saka ta hawaye cos da Sahla da Islam Ina jinsu à jinnin jikina


Mubasshir ya jawo shi suka rungume juna suna dan bubuga bayan juna (Maza kenan da manyan ne da anga kuka lol)


Bayan ya dawo daga rakiyar Idriss ya tarar suna cin abinci su duka sai dariya suke, suna labari harda hajiya hawau, ya nemi waje zai zauna Hajiya Fadimatu ta ce" kai, tashi ka sauko min yarinya ta ci abinci mana


Mubasshir ya Mike ya haura sama, yana Isa ya tura dakin ya shiga,

Hangota yayi zaune ta hade kanta da gwuiwarta tana rusa kuka, gabansa ya yanke ya fadi à ransa ya ce" na shiga uku, kardai kukan rabata da Idriss ne take, tana nufin tana sonsa kenan ? Idan ba haka ba Tunda ta hayo take kukan nan ? Bazai yuwu ba, cikin bacin rai ya nufeta..............................................................................................................................







wai Ina Sahla ne ? Fadimatul islam Wa take SO ne ? 🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀ mai kuka Dauka darasi à wannan novel ? Daga taku yar mutan Niger
[6/1 08:26] Sajida: 🇳🇪Belles écrivaines du Niger



*'YAR 👧🏻*

*MAHAUKACIYA👹*



*Na*
*Sajida*




69
Cikin kakausar murya ya ce" ke, kukan me kuma kike ?


Da sauri yar mahaukaciya ta dago kanta tana kalonsa, à ranta ta ce" oh ni *Yar Mahaukaciya* an hadani da bahagumen mutun, shi bashida aiki sai fada, hum dan baya sona ne da yana SO na da ya tatale ni,


Mubasshir ya ce" kalon fa ?


Cikin sauri ta ziro kafarta tana goge hawayenta tayi tsaye kanta à kasa

Ya lumshe Idannuwansa ita kam akoy Kira, à fili ya ce " mu je ki ci abinci KO ?


Ya juya yayi gaba, yar mahaukaciya ta biyo bayansa



Hajiya Rafi'at ta ce" aunty yaushe ne y'ar taki zata tare ne ?


Hajiya fadimatu ta ce" da Nayi niyar karshen satin nan, To da kika Zo da uzurin nan à yanzu kam ban Sani ba


Elhaj Muhammad ya ce" ni wannan sha'ani naku na mata ban san kansa ba, please ku bani matata muyi tafiyar mu tare chainar nan dan ganin wannan matar yanda zanyi da ita, sai ku shirya y'ar ku, madame a shirye take, ya karashe zancen yana kalon hajiya hafsat,

Tayi saurin sada kanta kasa, ita dai bata san yanda zata yi da elhaj ya dena saka ta kunya ba


Hajiya fadimatu tayi dariya ta ce" to Yaya kika gani kanwata hakan yayi ?



Hajiya hafsat ta kara sine kai ta ce" ni fa ku dena tambayana na please du yanda kuka tsara hakan za'ayi


Gaba dayansu suka kwashe da dariya domin yanda take maganar uwa ta zura da gudu, Hajiya Hafsat kenan sarkin kunya

Karshe dai sai tsakanin hajiya fadimatu da hajiya Rafi'at aka yanke shawarar inda fafur hajiya Fadimatu ta kafe à kan Hajiya Rafi'at ta zauna à gidan ta saboda ba kowa à gidan su dan su elhaj Muhammad da hajiya Hafsat tafiya zasu yi kasar chaina wajen hajiya Falmata,



Washe gari Mubasshir ya tashi ya tafi gidan sa bisa umarnin mahaifiyarsa KO dan yayi nisa da Fadimatul Islam su samu su tsumata da kyau domin tun daga sokoto suka dauko aunty Habibu M Shehu ta gyara Fadimatul islam inda ta dage ka'in da na'in tun daga kanta har tafin kafarta gyara suke sha kala daban daban,
Yau à dama wannan à Bata ta sha, in an jima ta shiga cikin ruwan tirare, Idan ta fito ta tsuguna à na tsuguno, da kanta take shafe mata jikinta da mayukan da ta hada masu kara santsin fata, da laushi, da kyali, harda rami aka yi daidai da jikinta Wanda Aunty habiba take rufeta da bargo ta

Please Login or Register in order to submit comment