Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

irin
siffar jikinsa,ko wanka Darusi zaiyi saiya barsu a
cikin kogon dutsen ya nausa can cikin dajin yayi
tafiya mai nisa yaje cikin wata korama wacce ko
kudi aka baiwa mutum akace ya shigeta ba zai
yarda ya shiga ba saboda tana tsakiyar wadansu
dogayen tsaunika ne guda bitu kuma wurin akwai
duhu sosai.Kai da gani kasan cewa baza a rasa
samun mugayen halittun cikin ruwa ba a wajen ko
kuma mugayen bakaken aljanu,amma shi gogan
naka kai tsaye yake shiga cikin koramar yayi
wankansa hankalinsa a kwance dogaronsa kawai
shine ALLAH.Kullum Jarumi Darusi ke fita daji ya
farauto musu abincin da zasu ci wani lokacin
saidai suga ya kaso gada ko barewa,wata rana
kuma suga ya harbo katon tsuntus haka zaizo ya
fige tsuntsun ya gasa shi sannan ya raba naman
kaso hudu daidai ya baiwa kowa rabonsa,sau tari
rabon nasa ma ko rabinsa baya cinyewa sai ya
kara a kan na Sarila.A ranar kwana na bakwai ne
da sassafe lokacin da Jarumi Darusi ya tafi farauta
a daji domin ya samo musu abinda zasu ci sai
Sarila taji karfin jikinta yazo har ma ta iya mikewa
zaune,Yazirina da Mujahid kuwa kowannensu
dama tun kwanaki biyu sukaji karayar dake jikinsu
ta fara warkewa domin suna iya yin komai da
kansu,Yazirina na iya dingisa karyayyar kafar tata
shi kuma Mujahid na iya motsa hannunsa.Koda
Mujahid Da Yazirina suka ga Sarila ta sami damar
iya mikewa zaune da kanta sai suka kamu da
tsananin mamaki,cikin murna Mujahid ya dubeta
yace,tabbas Darusi dan baiwa ne gashi da karfin
damtse na gaban kwantance,kuma gashi da ilmin
likitanci,hakika yake Sarila baki da abinda zaki iya
saka masa a cikin wannan duniya.Koda jin wannan
batu sai Sarila tayi murmushin mugunta tace ai
kuwa nice nake da abinda zan saka masa dashi.Ba
da komai zan saka masa ba face BUTULCI kuma
tukuicin taimakon da yayi mini shine na kashe shi
a lokacin daya gama aikinsa ya kaimu Kogon
Taskar Ajali.Koda jin wannan batu sai mamaki ya
kama Mujahid yace ke Sarila waishin har yanzu
kina nan akan wannan batu naki duk da ganin
yadda Darusi ya ceci rayukanmu har sau biyu?
Sa'adda Sarila taji wannan tambaya sai ta bushe
da dariyar mugunta a karo na biyu tace niga ba'a
raineni cikin samin menene halacci ba,basan wani
abu waishi tausayi ba ko jin kai,abinda na sani
kawai shine SARA da SUKAn sassan jikin
bil'adama ko Aljan
Wannan shine makarantata.Daukan rai kuwa shine
babban darasin da nafi kwarewa a kansa.Babu
abinda nake so a cikin duniya sama da kudi da
mulki,Burina kawai shine na ga ina sarrafa komai
da kowa a kan tafin hannuna kamar yadda ake
sarrafa waina akan kaskon tukunya.Koda jin
wannan batu sai Yazirina ta jinjina kai tace ai kuwa
indai haka ne nima cin amanata zakiyi kuma ki
yaudareni kaci amanata yayin da muka isa kogon
taskar ajali.Sarila tayi dan guntun murmushi tace
shin kin manta ne cewa na rantse da darajar
iyayena bazan biki a kan wannan dukiya?Yazirina
tace hmm ai wanda duk baigwa mutuncin iyayen
wani ba to bazai ga nasa ba ma.Ta yaya zakiyi
rantsuwa da iyayenki wadanda baki sansu ba,baki
ma taba ganinsu ba kiyi zaton cewa zan yarda da
rantsuwar taki?Aini kawai yanzu lokaci nake jira
domin naga karshen tika tiki.Har Salira ta budi
baki zata ce wani abu sai Mujahid ya tari
numfashinta ya dubeta cikin alamun karayar zuciya
gami da nadama yace ki gafarce ni yake Yazirina
kiyi sani cewa nayi miki wani laifi guda daya.Koda
jin haka sai Yazirina ta dubeshi cikin alamun
matukar mamaki tace wane irin laifi kayi mini?
Mujahid yace a baya nayi miki karya guda daya
nace nine dan baiwar da zai kare ki daga dukkan
abin cutarwa.To lallai bani bane wannan dan
baiwar Jarumi Darusi ne tunda gashi har sau biyi
ko ince sau uku rayuwarki na shiga cikin mugun
hali amma na kasa tserar dake sai Darusi ne ya
kubutar dake.Dajin haka sai Yazirina tayi
murmushi tace aini ma naga Zahiri da idanuna
kuma na gamsu cewa Jarumi Darusi ne dan baiwar
da zai kubutar da rayuwar gaba dayan jama'ar
dake wannan nahiya tamu bawai rayuwata ba ni
kadai.Koda jin haka sai Sarila ta dakawa Yazirina
tsawa tace kina nufin kenan zaki mika wuya a
gareshi ki karbi addininsa?Kafin Yazirina tace wani
abu saiga Jarumi Darusi ya shigo cikin kogon
dutsen dauke da wata katuwar barewa a
kafadarsa.Kawai sai ya dubesu yace ku gafarce ni
yau na dan jima a cikin daji ban dawo da wuri ba
gashi na barku a cikin yunwa.Caraf sai Mujahid
yace haba yakai JARUMIN JARUMAI ai mune ya
kamata mu nemi gafararka tunda mun barka da
wahalar jinyarmu a cikin kogon dutse har tsawon
kwanaki bakwai.Darusi yayi murmushi yace bari
nayi sauri na gyara mana naman barewar nan muyi
kalaci domin mu tashi mu kimtsa tunda yau ne
ranar ci gaba da tafiyarmu kamar yadda muka
tsara.Nan take Darusi ya fede barewar nan ya
gyara komai a jikinta sannan ya hada wuta ya fara
gasawa.Adaidai wannan lokaci ne ya dubi Sarila
yayi mata sannu sannan yace ina tayaki murna
bisa samun saukin jikin da kikayi a yau,gashi har
kin iya tashi zaune.Maimakon Sarila ta dubeshi
cikin fara'a tayi masa godiya sai kawai ta murtuke
fuska kuma ta daka masa harara ta kau da kai ba
tare da tace uffan ba.Al'amarin dayayi matukar
bakantawa Mujahid Rai kenan yaji kamar ya tashi
yaje ya rufe Sarila da duka domin ji yayi kamar shi
ta wulakanta amma saiya basar,shi kuwa Darusi
sai yayi murmushi kawai ya kau da kansa ya
cigaba da aikin gashon barewar.A cikin abinda
baifi sa'a guda ba su Jarumi Darusi sun kammala
buda baki nan take suka harhada kayan su suka
gama shiri tsaf aka dora Yazirina da Sarila akan
dokin Darusi,Mujahid da Darusi kuwa sai suka
wuce gaba a kasa.Darusi na ruke da linzamin
dokin suka nausa cikin daji.Saida suka shafe
kwana tara suna ratsawa ta cikin dazuzzuka su
kwana nan su tashi can ba tare da sun hadu da
wani mugun abu ba,duk tsawon wannan lokaci
kome su Sarila suke bukata sai an tsaya anyi
musu kuma duk tsawon tafiyar da za'ayi Darusi bai
taba cewa ya gaji ba ko kuma yace a tsaya ayi
wata Bukata.Komai wahalar abu kuma koda babu
shi a kusa sai Darusi ya bazama yaje ya nemo,duk
dawainiyar da Darusi ya saba yiwa Sarila bai fasa
ba duk da cewa wani lokacin ma tana kyararsa
tana yi masa wulakanci iri iri.A ranar kwana na
tara ne suka yada zango a wani dogon daji mai
yawan surkuki a wannan lokaci rana ta fadi
magriba ta doso,kai kuma a sannan Sarila taji
karfin jikinta sosai,da kanta ma ta sauko daga kan
dokin kawai sai gani akayi ta zare takobi ta kama
tsalle tsalle tana kaiwa iska SARA da SUKA wato ta
rinka baiwa kanta horon yaki.Nanfa Mujahid da
Yazirina suka kura mata idanu cikin matukar
mamaki,shi kuwa Darusi sai ya sauke jakar
guzurinsa daga bayansa ya fiddo tanti ya fara aikin
kafashi.Cikin sauri Mujahid yazo ya taya Darusi
aikin inda ya dubeshi yace yakai Abokina menene
dalilin da yasa ka yanke hukuncin mu yada zango
anan?Koda jin wannan tambaya sai Darusi yayi
ajiyar zuciya kuma ya bude baki cikin karamar
murya yadda su Yazirina ba zasuji maganarsu ba
yace dajin dake gabanmu kadan mugun daji
ne,akwai wata babbar runduna ta yanfashi a
cikinsa,kuma sun dana mana mugayen tarkuna na
kama mutane yadda komai yawan AYARI basu isa
su iya tsallakewa ba.Adadin yan fashin yakai DUBU
ARBA'IN kuma zakwakuran mayaka ne na
kwatance,idan muka kuskura muka shiga cikin
sansaninsu da wannan duhu zasu iya cutar damu.
TASKAR AJALI
Littafi Na Shida (6)
Part B
Zasu iya cutar damu.Saukin tama nasan duk irin
tarkunan da suke danawa kuma nasan sirrin
dajin.Kada ka gayawa su Sarila wannan batu
saboda nafi son sai tura takai bango sun gane
muhimmancina da amfani na da kuma
gaskiyata.Sarila tafi kowa kina a cikinku kuma
nasan idan har na kaiku har can kogon Taskar
Ajali sai tayi yunkurin kashe ni.Koda jin wannan
batu sai mamaki ya turnuke Mujahid yace ya akayi
kasan wannan al'amari?Tabbas abinda ka fada
shine a cikin zuciyar Sarila har ma furuci tayi akan
zata aikata hakan.Darusi yace ubangijina ya kan
sanar dani abubuwa da dama a cikin mafarkina
walau na tsiya kona arziki,hatta fafatawar da nayi
da sarki Damnash a can kofar kogon dutsen nan
saida aka nuna mini duk abinda zai faru amma
saboda nayi imani da ubangijin nawa dari bisa dari
ban fasa yin komai ba kuma hatta mutuwa bana
tsoronta akan wannan tafarki da nake kai bare wani
bil'adama tunda na san cewa akan gaskiya
nake.Ka daina damuwa akan duk irin wulakancin
da Sarila zatayi mini gami da wulakanta ni,ina mai
tabbatar maka da cewa sai tayi nadamar duk
abubuwan da takeyi mini a anan gaba kuma akwai
wani babban dalili da yasa kome zatayi mini bazan
damu ba.Koda jin haka sai mamaki ya sake
turnuke Mujahid yace menene wannan babban
dalili kuwa?Darusi yace kayi hakuri zaka ga komai
da idanunka,ka sani cewa da zarar mun gama da
rundunar yan fashin dake gabanmu tafiyar sa'a
kacal zamuyi mu riski wani babban gari waishi
Birnin Zamras.Koda jin wannan batu sai Mujahid
ya kamu da tsananin mamaki ya ka ya dubi Darusi
cikin alamun kaduwa da rashin yarda yace ai kuwa
yadda na sami labarin shine daga can birninmu
zuwa wannan birni da kake fada tafiya ce ta a
kallah kwanaki casa'in,ta yaya zaka ce muna daf da
riska alhalin gaba daya yau kwananmu goma sha
shida kacal da baro gida?Sa'adda Jarumi Darusi
yaji wannan batu sai yayi murmushi yace ai abinda
baka sani ba shine ina rokon ubangijina ne yana
gajarce mana tafiyar wata uku a cikin sati biyu
saboda haka da izinin ubangijin nawa inasa ran
cewa zamu isa kogon Taskar Ajali a cikin sati
shida maimakon watanni bakwai zuwa tara.Kada ka
gayawa su Sarila wannan sirri,wannan amana ce a
tsakaninmu.Koda jin wannan batu sai Mujahid ya
gyada kai yace lallai kuwa zaka sameni mai ruke
amanarka.Bayan su Jarumi Darusi sun gama kafa
tantin sai suka yiwa Sarila da Yazirina shimfidarsu
a ciki su kuma suka fito wajen tantin suka kunna
wuta suka zauna suna jin dumi suna hira amma
sai bayan Darusi ya gabatar da sallarsa ta
magriba.Yazirina da Sarila kuwa kowaccensu na
zaune akan shimfidarta tana cin ragowar
gasasshen naman barewar da sukayi guzuri.A
wannan lokaci ne Yazirina ta dubi Sarila tace nifa
Gaskiya sanyi nakeji sosai saboda haka waje zan
fita na zauna tare dasu Mujahid nasha dumin
wutar da suka kunna.Koda jin hakan sai Sarila ta
murtuke fuskarta tace indai sanyi kikeji ai ba sai
kinji dumin wuta ba a waje zaki yi
maganinsa,kawai ki kwanta ki lulluba da bargonki
mana,kedai kawai kice kina son kije kiyi ta kallon
fuskar Mujahid.Yazirina tayi murmushi tace amma
dai bakiyi mini adalci ba idan kika fadi haka tunda
nidai banga wani kuskure ba don zuciyar wani ta
kamu da AZABAR SOn wani.To waishin ma me
yasa kikeyin kishi dani akan Mujahid?Amsar itace
kema kin kamu da sonsa kuma hujjata itace kin
samu damar kashe shi a baya har sau biyu amma
sai kika ki kashe shi a lokacin da kike nemana
ruwa a jallo domin ki kashe ni ki rabani da
Taswirar dake hannuna.Caraf sai Sarila ta tari
numfashin Yazirina tace ke mu ajiye batun soyayya
yanzu saboda ita soyayya bata samun kafuwa
sosai face ana cikin nishadi da kwanciyar
hankali,ki tashi kije kiyi duk abinda kikeson yi daga
yau bazan sake sa miki ido ba.Koda gama fadin
hakan sai Sarila ta kwanta akan shimfidarta taja
bargonta ta lullube jikinta.Koda ganin haka sai jikin
Yazirina yayi sanyi ta kasa mikewa ta fita waje don
haka itama saita kwanta taja bargo.Kashe gari da
sassafe suka tashi duk su hudun sukayi shiri suka
nausa cikin daji.Ana fara yin tafiyar ne Mujahid ya
tsaya daf da Darusi suka rinka tafiya kafada bai
yarda ya gusa daga kusa dashi ba.Koda ganin
haka sai Sarila ta dubi Yazirina wacce ke gabanta
akan doki guda da suke zaune tare tayi mata rada
a kunne tace yake yar uwata ina mai tabbatar miki
da cewa lallai akwai wani mugun abu a kan
wannan hanya da muka biyo amma Mujahid yasan
da hakan bai sanar damu ba.Cikin mamaki
Yazirina tace yaya akayi kika san da hakan ko
kuwa a cikin madubin tsafinki kika gani?Sarila ta
numfasa tace ai tun daga ranar danayi gumurzu da
Jarumi Darusi sai komai na tsafina yayi rauni,shin
baki lura da yadda Mujahid ya kasance ba ne
tunda muka baro kogon duntsen nan ba?Ko
yaushe yana daf da Jarumi Darusi yaki yarda ya
nisanta dashi,duk yadda akayi ya gaya masa sirrin
dajin da muka dosa.Abinda na fuskanta shine
zuciyar Mujahid ta fara karkata izuwa yin imani da
addinin Darusi shima Darusi ya fahimci haka shi
yasa yake kokarin kula dashi gami da bashi
kariya,mu kuwa ya barmu da halinmu da dabarmu
da kuma abin dogaranmu.Koda jin wannan batu
sai hankalin Yazirina ya DUGUNZUMA ainun domin
ta fahimci cewa babu wanda yasan irin iyakar
wahalar da zasu sha a cikin wannan tafiya,abinda
zai hanasu shan wuyar kuwa abu daya ne kuma ba
komai bane face karbar addinin Jarumi Darusi.Ita
dai Yazirina zuciyarta rawa takeyi kan hakan a duk
sa'adda ta tuno da irin wahalar da mahaifinta
yasha kafin ya hada wannan sihiri na taskar ajali
da yadda ya shafe shekaru masu yawa yana tara
dukiyar sai taga cewa lallai ba zata iya hakura ba da
mallakarta don cika burin
mahaifin nata,a can wani bangaren daban na
zuciyarta ta kuwa ta fara gamsuwa da cewar
addinin Darusi shine ADDININ GASKIYA tunda
gashi yayi abubuwan al'ajabin da babu wani jarumi
ko matsafi daya taba yin kamarsu,abu na uku data
barshi a can karkashin ranta shine duk yadda zata
yi saita tabbatar da cewar ita kadaice zata mori
wannan dukiya ta mahaifinta saboda tafi kowa
cancanta da hakan.Duk lokacin data kalli fuskar
Sarila sai taga kamar bakin kumurcin maciji ta
kalla mai shirin kawo karshen rayuwarta.Koda aka
kara nutsuwa cikin wannan daji sai Sarila da
Yazirina suka dora hannayensu akan kufen
takubbansu kuma suka rinka kallon samansu da
kasansu da kuma gaba da bayansu.Koda ganin
haka sai Darusi ya dubi Mujahid a fusace cikin
karamar murya yace shin ka baiyana sirrin wannan
daji ne gasu Sarila?Mujahid ya gyada kai da sauri
yace na rantse da girman iyayena ban gaya musu
komai ba saidai kawai idan jikinsu ne ya basu ko
kuma suna zargi.Darusi ya jinjina kai yace tabbas
jikinsu ne ya basu cewar munzo waje mai
hadari,abinda nakeso dakai shine lallai ka cigaba
da nanikata karka bari a sami nazara a tsakaninmu
da kai wacce takai taku uku.Koda jin haka sai
Mujahid ya gyada kai yace zan lura da
hakan.tafiyar rabin sa'a na cika sai gasu Jarumi
Darusi sun iso wani katon fili mai tsananin tsawo
da fadin gaske wanda za'a iya kiransa da suna
'KARE GUDUNKA.Babu ko bishiya guda daya a
wajen kuma babu wani katon dutse ko tsauni sai
kananan duwatsun wuta wadanda aka shimfidasu a
kas tamkar dama ado akayi dasu a wajen,iya
hangen mutum bazai gano karshen wannan daji
ba.Kwatsam sai su Jarumi Darusi sukaga wadansu
gungun yan fashi suna fitowa ta gabas da
yamma,kudu da arewa su da yawa ba adadi
tamkar gaba dayan mutanen duniyar ne suka
fito.Su dai wadannan yan fashi sun kasance arnan
daji,babu komai a jikinsu face walkin
fata,kafafuwansu babu takalmi amma kowannensu
na dauke da mugayen MAKAMAN YAKI a jikinsa
irin wanda idanu basu saba gani ba,sun kasance
girda girda wato manya manya,ga tsawo kuma ga
kauri kuma duk jikinsu a murde yake cike da
kwanji da tarin jijiyoyi,kai da ganinsu kasan cewa
lallai sun sami horon yaki.Kafin cikar wadansu
dakiku tuni wadannan Arnan Daji sun yiwa su
Jarumi Darusi KAWANYA.Koda ganin wadannan
yan fashi sai Yazirina da Mujahid suka firgita ainun
ita kuwa Sarila ko gezau batayi ba,Jarumi Darusi
kuwa sai ya cigaba da tafiya abinsa ya durfafi cikin
yanfashin ba tare da shakkar komai ba.Mujahid na
biye dashi daf da daf,koda ya iso daf da yanfashin
sai suka dare suka basu hanya ba tare da dayansu
yayi wani yunkuri ba na kawo musu hari.Koda
ganin haka sai Yazirina ta tsikari bayan Sarila
tacemaza mana kibi bayansu Darusi domin mu
sami albarkacinsa kada su yakemu.Koda jin haka
sai Sarila ta waigo ta dakawa Yazirina harara tace
da ita ai idan muka bishi a baya da sauri mun
muna cewa munyi imani da addininsa kenan kuma
mun tsorata.Kada yawan wadannan arnan daji su
tsoratar dake shin kin manta ne da irin tsananin
jarumtaka ta da kuma karfin sihirin tsafina?Ai
wadannan ba komai bane zan iya dasu.Cikin
tsananin fishi Yazirina ta daga murya tace ina
jarumtakar taki da karfin tsafinki a lokacin da
mukayi gumurzu da Aljana Marwisa?Me yasa kika
kasa kwatar kanki a hannunta?Inbadon Jarumi
Darusi ba da tuni kin dade da shekawa
Barzahu,kiyi sani cewa ni nasan Darusi bazai bari a
kashe mu ba anan amma abinda banso shine
wahala,ki tuna da yarjejeniyar da mukayi a baya ta
yan kwanaki mun sha wahala sosai shin yanzu ma
so kike musha wata wahalar?Adaidai wannan lokaci
ne Darusi da Mujahid suka gama ficewa daga cikin
arnan dajin ya zamana cewa banda kallon kallo
babu abinda ya wakana tsakaninsu.Koda Mujahid
da Darusi suka koma gefe daya sai suka tsaya cak
suka zuba idanu suga yadda su Sarila zasu zo su
wuce ta tsakiyar yanfashin kamar yadda suma suka
wuce.Nanfa Sarila da Yazirina sukaga wani abin
mamaki domin shugaban yan fashin ne yazo
gaban Jarumi Darusi ya risina ya kwash gaisuwa
sannan sukayi maganganu,suna gama tattaunawa
sai shugaban yanfashin ya dawo cikin yan uwansa
sannan ya fuskanci su Sarila wadanda ke bisa doki
a lokacin da sauran yaran nasa suka toshe hanyar
dasu Mujahid suka ratsa suka wuce kawai sai
Sarila ta dubi Yazirina tace baki da wani zabi
wanda yafi ki tayani yakar wadannan yan fashi
domin mu kutsa ta cikinsuda karfin tsiya mu isa
inda su Darusi ke tsaye,ina mai tabbatar miki da
cewa ba zamu iya karar da wadannan mutane ba
don haka kawai mu tsayar da hankalinmu wajen
kutsawa ta tsakiyar su da karfin tsiya har mu
wuce.Koda gama fadin hakan sai Sarila ta zare
takobinta ta kwarara uban ihu,hatta shugaban
yanfashin wanda babu kamarsa a girma,kwarjini da
kirar sadauki saida hantar cikinsa ta kada
sakamakon jin wannan mugun ihu na Sarila.Itama
Yazirina saita zare tata takobin a lokacin da Sarila
ta sakarwa dokin linzami ta nufi tsakiyar yan
fashin.Ai kuwa sai shugaban yanfashin da dukanin
yaran nasa suka rugo da gudu izuwa kansu kai
kace beraye ne guda biyu aka ajiye a gaban
miliyoyin maguna.Bama Sarila da Yazirina ba hatta
dokin nasu idan wadannan yanfashi suka dasa
masa wawa fiye da kaso tara cikin gomansu ba
zasu sami koda tsoka guda ba.Koda ya rage saura
baifi taku biyar ba ayi mugun gamo tsakanin
yanfashin dasu Sarila sai shugaban yan fashin ya
dako tsalle sama yana ruke da wano dogon mashi
ya kawowa Sarila suka a kirji.Cikin bakin zafin
nama Sarila ta kade mashin da takobin hannunta
ita ma ta daka tsalle sama daga kan dokin ta doki
kirjin shugaban yanfashin da kafarta gudaDa kafarta guda yayi baya taga taga
har taku uku
ya tsaya kyam!A lokacin da Sarila tayi
wata irin
fanka a sama tamkar an murza
katantanwa ta tare
hare haren da dakarunsa suke kawo
mata na sara
da suka kuma ta maida martani.Ita
ma Yazirina
dake zaune a bayan dokin haka ta
shiga kare hare
haren yanfashin tana maida
martani.Nanfa wuri ya
yamutse aka ruguntsume da
masifaffen yaki,hatta
jarumi Darusi sunyi matukar burge su
bisa
jarumtakar da suka nuna yanzu domin
basu taba
zaton cewa zasu iyayin hakan ba
amma inda
tambayar take shine zasu jure wannan
bakin
artabun har zuwa wani dogon lokaci
kuwa?Abin
fatan shine Allah yasa kada suy
karkon kifi.Ana fara
wannan gumurzu sai Sarila ta rinka
kutsawa ta
cikin Arnan dajin da dokin nasu da
karfin tsiya ta
banke su suna karawa gaba saidai
kaga maza na
zubewa kasa tamkar ana sassabe a
gona,amma
abin haushin kuma abin tashin
hankali shine sara
da sukan da Sarila da Yazirina ke yiwa
arnan dajin
baya tasiri a jikinsu.Duk sa'adda
takubbansu ya
hadu da jikin arnan dajin saidai kaji
kara na tashi
tamkar haduwar karfe da karfe fa
zarar sun banke
yanfashin da doki koda karfin naushi
sun zube
kasa sai su ga sun mike tsaye zumbur
sun cigaba
da artabun ba tare da alamar sun
jigata ba.Da
zarar dokinsu Sarila yakai tsakiyar
yanfashin sai
kuma akaga an dawo dashi baya can
farko da
karfin tsiya,saida akayi haka har sau
uku ba tare
da sun sami nasarar koda kashe
mutum daya ba
jal daga cikin yanfashin kuma suma
yanfashin ko
lakutar jikinsu dayansu basu samu
ba.Al'amarin
dayayi matukar dugunzuma hankalin
Sarila da
Yazirina kenan saboda sun san cewa
jiki da jini sai
a hankali.Dole ne su gaji idan aka
cigaba da
wannan gumurzu ahaka izuwa tsawon
lokaci,shi
kuwa shugaban yanfashin koda ya
cewa wankin
hula zai kaisu dare sai ya fusata ainun
ya
shammaci Sarila ya soke dokin nasu
da mashin
hannunsa a ciki take dokin yayi tutsu
dasu yana
haniniya suka rikito kasa daga kansa a
lokacin da
dokin ya baje kasa matacce.Maimako
n Sarila da
Yazirina su karaya sai suka kara kaimi
suka cigaba
da yaki maimakon su cigaba dakai
Sara da Suka
sai suka fara kai NAUSHI da
BUGU.Gashi dai
yanfashin suna jin naushin suna
faduwa kasa
amma sai kaga suna mikewa tsaye
zumbur suna
cigaba da gumurzun.Koda aka shafe
rabin sa'a ana
wannan artabun sai labari yasha
bamban domin a
sannan ne Sarila da Yazirina suka dan
fara gajiya
har yanfashin suka fara samun damar
gabzar musu
naushi a fuskokinsu da sassan
jikinsu.Nan da nan
kuwa aka fara hada musu JINI da
MAJINA amma
saboda bakin naci gami da tsananin
juriya irin ta
JARUMAN KWARAI sai kuma suka
cigaba da maida
martani.Babu yadda Sarila da Yazirina
basuyi akan
su kutsa ta cikin yanfashin da karfin
tsiya su fice
amma sai suka kasa,abin ma daya
daure musu kai
shine lokaci guda yanfashin suka
daina kai musu
hari da makamansu sai naushi da
bugu da hannu
da kafa,aikuwa koda aka sake shafe
wata rabin
sa'ar sai Sarila da Yazirina suka jigata
ainun
saboda sarkin yawa yafi sarkin karfi
ya zamana
cewa basa iya kai hari sai kare
kai.Sannau a
hankalo kare kan ma ya gagaresu,a
sannan ne fa
akayi musu laga laga da tsabar naushi
da bugu
suka zube kasa wanwar jini na yoyo
ta cikin
hancinsu da bakinsu kuma suna
numfashi sama
sama kamar ransu zai fita.Bisa
mamaki sai sukaga
yanfashin sunki kashe su sun ja da
baya cikin yi
musu KAWANYA kuma sun bude
hanya saiga
Jarumi Darusi da Mujahid tare da
shugaban
yanfashin kafada da kafada sun taho
gare su,wasu
yaran yaran yanfashin na janye da
dawakai guda
hudu.Koda suka zo daf dasu sai Darusi
ya dubi
Sarila cikin murmushi yace ga
dawakai nan ku
tashi ku hau mu cigaba da tafiya
domin isa birnin
Zamras.Koda jin wannan batu sai
Sarila ta yunkura
cikin matukar karfin hali ta mike tsaye
sannan ta
baiwa Yazirina hannunta ta kama ta
tashi
tsayen.Sarila da dubi Darusi cikin
alamun tsananin
fishi da kiyayya tace ya zaka raina
mana
hankalinmu,zuwa birnin Zamras
tafiya ce ta kwana
casa'in daidai?Kuma me yasa ka
barmu muka sha
wannan bakar wahala haka alhalin
kana da ikon
wucewa damu lafiya.Koda jin tambaya
sai jarumi
Darusi yayi murmushi yace dama so
nake kiyi mini
wannan tambaya da bakinki saboda
komai da
lokacinsa.Tabba s daga birnin Zamras
tafiyar sa'a
daya ce kacal abinda yasa na barku
kuka sha
wannan wahala a hannun wadannan
yanfashi shine
har yanzu bakuyi imani da ubangijina
ba amma ko
yanzu kuka karbi addinina ba zaku
kara fuskantar
wata matsala ba da izininsa.Idan
kuwa kuka karbi
addinin nawa har sai mun isa kogon
taskar ajali
kamar yadda kukayi alkawari to duk
masifar da
muka hadu da ita zan barku da ita ne
in yaso
karfinku da tsafinku ya ceceku,bazan
taba
taimakonku ba face naga zaku hallaka
muraran
kamar yadda nayi alkawari da
farko.Koda gama
fadin hakan sai Jarumi Darusi ya juya
ya karbi doki
guda daga dawakan hudu ya haye
shima Mujahid
sai yayi sauri ya karbi guda ba tare da
yin wata
gardama ba sai Sarila da Yazirina ma
suka karbi
dawakan suka hau,faruwar hakan keda
wuya sai
shugaban yanfashin yazo gaban
jarumi Darusi ya
sake risina a karo na biyu cikin
girmamawa yace
ya batun alkawarin da kayi mana
cewa zaka koyar
damu yadda ake bautar Allah a cikin
wannan
addini naka mai daraja.Ka sani cewa
tuni a halin
yanzu mun daina fashi kuma duk
abubuwan da
kuka umarcemu munayi bamu ajiye
daya ba.Koda
jin haka sai farin ciki ya lullube
jarumi Darusi yace
da zarar na dawo daga kogon Taskar
Ajali zanzo
na cika wannan alkawari a
gareku,yanzu abokan
tafiyata da suka jarraba jarumtakarsu
a akan taku
sun jigata ainun kuma kun san irin-
bala'in dake cikin birnin Zamras don
haka ba zamu
iya shiga dasu a haka ba,saboda haka
ina neman
alfarma na shiga dasu cikin birninku
domin a sami
likitan da zai duba lafiyarsu kuma ya
basu maganin
da zasuji karfin jikinsu.Koda jin haka
sai farin ciki
ya turnuke shugaban yanfashin tare
da sauran
gaba dayan jama'arsa,ya dubi Jarumi
Darusi yace
munfi kowa murna da karbarka a
matsayin
bakonmu idan da hali ma muna
neman alfarmar
kuyi kwana uku a cikin birninmu kafin
ku wuce
izuwa birnin Zamras.Darusi yayi
murmushi tace
zan duba na gani idan da halin
yiyuwar hakan sai
ayi.Nan take shugaban yanfashin tare
da sauran
jama'arsa suka yiwa su jarumi Darusi
jagora suka
nufi birnin nasu yar guntuwar tafiya
sukayi ta cikin
wata duhuwa suka hango bukkokin
birnin na arnan
daji masu tsananin yawan da mutum
zai iya shafe
kwana biyu yana kirga su ba tare da
ya gama
ba.Tun daga nesa su Sarila suka jiyo
bugun
tambura na tashi anayi musu lale
marhaban,ashe
tuni labari ya riske mutanen garin
cewa ga jarumi
Darusi can ya dawo.Kafin su isa kofar
garin kuwa
gaba dayan mutanen birnin mazansu
da
matansu,yara da manya sun fito sun
jeru a kofar
birnin sunyi sahu sahu suna ta shewa
da farin ciki
dauke da kyaututtuka iri iri,al'amarin
da yayi
matukar daurewa Mujahid,Sarila da
Yazirina kai
kenan suka cika da tsananin mamakin
dalilin da
yasa gaba dayan mutanen wannan
birni suke
matukar kaunar jarumi Darusi haka
kuma suke
girmamashi gami da murnar
ganinsa.Nanfa maza
da matan suka tashi rike da
kyaututtukan saboda
yawansu.Gaba daya matan wannan
gari suna
sanye ne a cikin suturar data rufe
jikinsu tsaf kuma
da yawansu sun kasance KYAWAWAn
gaske
ababan kwatance.Duk da irin tsananin
kyau irin na
Sarila da Yazirina saida kyawun matan
arnan dajin
ya burge su saboda yanayin kalar
jikinsu wankan
tarwada ne kuma fatarsu tana sheki
sosai kuma ga
laushi,sun kasance dogaye masu
madaidaicin
kaurin jiki,suna da kira mai kyau irin
wacce
kowane 'da namiji ke dimaucewa idan
ya
gani,sannan gashin kansu dogo ne ya
zuba har
kasan mazaunansu ga tsananin baki
da kyalli
tamkar madubi.Kai tsaye Sarkin Arnan
dajin ya
wuce dasu jarumi Darusi izuwa
gidansa.A gaba
dayan birnin babu wani gida da aka
kera shi yayi
kyau kamar na sarkin domin shi da
tubali akayi
shi kuma yana da girma sosai,a
tsakiyar birnin
yake kusa da tsohon dakin bautarsu
amma a halin
yanzu ma an rushe dakin bautar tun a
ranar da
jarumi Darusi yazo birnin.Cikin wani
katon daki aka
shigo da Jarumi Darusi tare da
Miujahid,Sarila da
Yazirina kuwa sai aka shigar dasu can
cikin gidan
wajen matan sarki aka kaisu wata
babbar turaka
wacce ta kawatu ainun aka kwantar
dasu aka
shimfide,saida wata likita tazo ta duba
su ta basu
wani magani suka sha sannan suka ji
jikinsu ya
daina tsami tamkar basu sha lugudan
duka
ba.Take sukaji kwarin jikinsu.Nan take
aka kawo
musu abinci da abin sha suka ci
sukayi hani'an
sannan aka nuna musu kewaye sukaje
sukayi
wanka suna fitowa daga wanka sai
kuyangi suka
shafe musu jikinsu da wani irin mai
mai kamshi da
taushi sannan aka kawo suturu irin na
mutanen
garin aka basu suka sanya.Acan
turakar da aka
sauke jarumi Darusi da Mujahid kuwa
ana kaisu
sai aka barsu su biyu jal!A cikin dakin
har izuwa
tsawon dan lokaci tamkar an manta
dasu daba
daya.Kwatsam!Sa i ga wata
santalelitar kyakkyawar
budurwa ta gaban kwatance wacce a
gaba daya
matan dake garin babu mai kyanta ta
shigo cikin
dakin dauke da farantin
abinci.Fuskarta cike take
da annuri tanayin murmushin farin
ciki tamkar
wacce aka yiwa bushara an bata
duniyar gaba
daya.Koda Mujahid yayi arba da
wannan
kyakkyawar budurwa saiya dimauce
ya fita daga
haiyacinsa ya aiyana a ransa yace ina
ma ace
Yazirina ce wannan kyakyawar
budurwa da nafi
kowa dacewa

Please Login or Register in order to submit comment