Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dajin amma shiru bata ga su
Mujahid ba ko alamar su bata gani ba.Haka tayi
gabas da yamma,kudu da arewa ta karkade ko ina a
cikin dajin bata ga ko wane abu dazai nuna
alamunsu ba.Kawai sai Sarila ta tsuguna a kasa ta
daga kanta sama tana mai wangame bakinta ta
kwarara uban ihu wanda ya cika dajin gaba daya da
amsa kuwa,sautin ihun saida yakai har cikin ko ina
a birnin na Yamein,kuma ya firgita duk wani abu mai
rai tamkar zaki ne yayi ruri a tsakiyar kasuwa.Ba
komai ne yasa Sarila tayi wannan mugun ihu ba face
tsananin bakin ciki bisa ganin cewa su Mujahid sun
bace mata da gani kuma bata san a inda zataje ta
same su ba.Kawai sai Sarila ta fashe da kukan
takaici kuma ta shiga tunanin abinda ya kamata tayi.
*Al'amarin Mujahid kuwa lokacin daya shigo cikin
wannan sarkakiya goye da Yazirina a guje yana
waigen bayansa cikin tsananin tsoro sai kawai yaji
kafarsa ta zurma cikin wani rami take ramin ya
karawa kansa fadi suka fada cikinsa shi da Yazirina
tamkar an je fasu a cikin RIJIYA mai zurfin kamu
DUBU don haka bai san sa'adda ya kurma uban ihu
ba saboda tsananin razanar da yayi kuma yadda yaji
suna ta cigaba da fadawa cikin karkashin kasa.Ashe
suna fadawa cikin wannan ramin sai ramin ya cike
da kansa daga sama,ciyawa mai huduwa tayi tofo a
daidai inda ramin yake,Sarila tazo ta wuce ta kansa
da gudu bata ma san cewa rami bane a
wajen.Kwatsam sai Mujahid yaga sun fado tsakiyar
wata kasaitacciyar fada amma babu kowa a cikin
fadar face wata mace yar kimanin shekaru talatin da
shida zaune bisa KARAGAR MULKI fuskarta cike da
ANNURI.Kallo daya mutum zai yiwa matar ya san
cewa ta cika hatsabibiyar bokanya,matar ta dubi
Mujahid cikin murmushi a lokacin da yake tsaye
bisa kafadunsa goye da Yazirina wacce har a sannan
bata farfado ba daga dogon suman da tayi kuma jini
bai daina diga ba daga jikin raunin kanta dana
kirjinta,tace,Lale marhaban da sarkin barayin wannan
zamani kuma yaro DAN BAIWA Mujahid Ibin
Assudusi,kayi sani cewa rayuwar abokiyar tafiyarka
na cikin mugun hadari sakamakon raunika biyun da
Sarila tayi mata amma zan iya ceto rayuwarta a
yanzu idan ka amince da sharadina.Cikin rawar jiki
da rawar murya Mujahid yace ni bama sainaji
sharadinki ba na amince kawai ki hanzarta ceto
rayuwarta.Koda jin haka sai matsafiyar ta bushe da
dariyar murna nan take ta tafa hannnunta sai ga
wadansu kuyangi guda hudu sun shigo cikin
fadar.Da zuwansu sai suka kama Yazirina suka
sauketa daga bayan Mujahid suka yunkura zasu tafi
da ita izuwa cikin daki amma sai Mujahid ya tsaida
su yace dole a tafi tare dani duk inda za akai
Yazirina.Koda jin haka sai Matsafiyar tace shin ka
manta ne cewa Yazirina bata son wani da namiji ya
taba jikinta bare yaga tsiraicinta.Dole ne a cire gaba
daya rigar dake jikin Yazirina kafin a iya yi mata
magani.Mujahid ya numfasa yace zancen yaushe
kuma tunda na goyata ma a bayana tsawon lokaci
ina gudu da ita bata ma san a halin da take ba,idan
har kin matsa baza aje dani daki da za ayi mata
magani ba to ina son na cire jakarta ta guzuri daga
jikinta na ajiye mata har izuwa lokacin da zata dawo
cikin haiyacinta.Koda jin wannan batu sai matsafiyar
ta tuntsire da dariya a karo na biyu sannan ta nutsu
tace ai babu abinda zanyi da taswirori biyun da take
cikin jakar Yazirina tunda kamar ka bani tuwo ne
babu miya.Duk wanda ya mallaki wadannan
taswirorin guda biyu ba tare daya mallaki ta ukun ba
wacce aka zana akan gadon bayan Jaruma Sarila
tamkar an bashi kyautar mutumin mutumi da bazai
iya yi masa aikin komai ba.Toofah!!!Wata sabuwa su
Yazirina sun fada hannun wata Matsafiya.Nima dai
mamakin yadda wannan matsafiya ta gina fada a
karkashin har ta ceci su Yazirina ta kubutar dasu
daga Zaluncin Sarila yasa nace bari idan tsaya anan
saboda al'ajabi.Bazai iya yi masa aikin komai
ba.Samun wannan
Taswirar dake bayan Sarila yafi komai
wahalar samu
a wannan duniya a yanzu,zamuyi
maganai mai
muhimmanci nan gaba bayan Yazirina
ta dawo cikin
haiyacinta kuma zaka iya daukar jakar
guzurin daga
jikin Yazirina.Take Mujahid ya dauki
jakar ya rataya
ta a kafadarsa su kuwa wadannan
kuyangi hudu sai
suka tafi da Yazirina suka shigar da ita
cikin wani
daki suka kwantar da ita akan gado
sannan suka
shiga aikin gyara raunikan jikin nata
saida aka dinke
raunikan duka biyun sannan aka shafa
mata magani
a kansu.Bayan nan sai kuyangin suka
mayar da
rigar Yazirina izuwa jikinta suka
suturceta suka fice
daga cikin dakin suka barta ita
kadai.Da ma Mujahid
na zaune a fadar tare da matsafiyar an
kawo masa
abinci da abin sha na alfarma yana ci
kuma suna
hira.Koda yaga wadannan kuyangi
hudu sun fito
daga cikin dakin da suka kai Yazirina
sai ya dubesu
yace shin zata rayu kuwa?Shugabar
kuyangin da
dubi Mujahid cikin murmushi tace ka
kwantar da
hankalinka mun tsayar da jinin dake
zuba a jikinta
kuma mun shafa mata magani,nan da
cikar kamar
sa'a biyu zata fardado.Koda jin haka
sai murna ta
kama Mujahid ya koma kan kujerar da
yake zaune
ya dubi matsafiyar yayi mata godiya
sannan yace
wai shin menene sunanki kuma
menene dalilin da
yasa kika gina fadarki anan cikin
karkashin kasa?
Tabbas na gamsu cewa kin cika
hatsabibiyar
bokanya tunda har Sarila ta kasa gano
nan din,da
ace ta gano da tuni yanzu ta shigo ta
gama damu
gaba daya ta karbi abinda take farauta
a wajen
Yazirina.Koda Mujahid yazo nan a
zancensa sai
matsafiyar ta kyalkyale da dariya
sannan tace da
farko sunana Muznaira bin
Salmara.Nima 'yace a
wajen marigayi Boka Salmara mahaifin
Jaruma
Yazirina.Koda jin wannan batu sai
Mujahid ya mike
tsaye zumbur cikin tsananin mamaki ya
dubeta yace
ya akayi kika zama yar boka Salmara
alhalin ance
bai taba aure ba kuma bai taba
haihuwa ba,ita kanta
Yazirina har ya bar duniya bai san da
cikinta
ba.Koda jin wannan tambaya sai
Hawaye ya zubowa
Muznaira tace tabbas abinda ka fada
gaskiya ne
amma ka sani cewa kafin Boka Salmara
ya fara
neman Basma mahaifiyar Yazirina
saida ya nemi
mahaifiyata da tazarar shekaru ashirin
tun sa'adda
ma yake matashin saurayi babu yadda
mahaifiyata
batayi ba akan Salmara ya aureta
amma sai
yaki.Karshen ma da duka da wulakanci
irin na
rayuwar bariki suka rabu a takamaimai
ma saida
yayi mata dukan KAWO WUKA ya
farfasa mata jiki ya
barta a kwance jina jina yayi
tafiyarsa.A zatonsa ma
tuni ta dade da shekawa
Barzahu.Saboda bakin cikin
wannan abu da Boka Salmara yayi
matane yasa
bayan ta kwana talatin da uku a
kwance tana jinya
tayi hijira daga garin ta koma wata
nahiya dabam,shi
kuwa Boka Salmara daya daina jin
duriyarta sai yayi
zaton cewa ta mutu an rufe bakinta.A
can nahiyar
birnin Hindu mahaifiyata ta sauka a
gidan wani
attajiri ta kama yi masa aikin
bauta,dama attajirin ya
taba haduwa da zaluncin Boka Salmara
ya kwaci
dukiya mai yawa a hannunsa sa'adda
sukayi wani
kasuwanci bisa wannan dalili ne
attajirin ya
tausayawa mahaifiyata kuma ya cigaba
da kyautata
mata.Bayan sati biyu ne mahaifiyata ta
gane cewa
tana dauke da juna biyu na Boka
Salmara,Al'amar in
daya jefata cikin tsananin bakin ciki
kenan ta fashe
da matsanancin kuka.Koda Attajirin ya
dawo gida
yaga halin da take ciki na bakin ciki
sai ya
tambayeta dalili,ba tare da boye komai
ba ta sanar
dashi cewa ta gane tana dauke da juna
biyun boka
Salmara kuma lallai sai ta lalata
wannan juna
biyu.Koda jin wannan batu sai Attajirin
ya bushe da
dariyar farin ciki.Lokaci guda kuma ya
nutsu ya dubi
mahaifiyata yace ai ba zaki zubar da
wannan ciki ba
saboda shine kadai makamin da zaki
iya yakar Boka
Salmara dashi ki DAUKI FANSAR
abinda yayi
miki,nima nayi RAMUWAR GAIYA,kiyi
sani cewa
binciken danayi akan Boka Salmara
duk matar daya
sadu da iya indai ta sami juna biyu
dashi sai ta
sami duk irin sirrikan tsafin dake
jikinsa haka ma
abinda zata haifa zaizo duniya ne a
tsume cikin irin
TSUMIN TSAFInsa.Lallai zamu reni
abinda zaki haifa
har izuwa lokacin da za kwashe gaba
daya dukiyar
da Boka Salmara ya tara wacce a halin
yanzu babu
wani attajiri da yake da kamarta a
cikin gaba daya
fadin wannan duniya,idan har muka
sami nasarar
hakan tofa sai bakin ciki ya kashe Boka
Salmara.Da
ransa yana ji yana gani zai dawo
matsiyaci kuma
yalaka fitl wanda bashi da abinda zai
ci sai yayi
bara.Yayin da Attajirin yazo nan a
jawabinsa sai farin
ciki ya lullube mahaifiyata har ta kaisu
ga yin aure a
cikin kwanaki kadan.Don haka lokacin
da cikin
mahaifiyata ya tsufa aka haife ni sai
jama'a suka
dauka cewa ni 'yar wannan attajiri
ce.Tun banfi
shekara shida ba a duniya gaba dayan
mutanen
birnin hindu suka tsorata da al'amarina
bisa gani
irin abubuwan al'ajabi da nakeyi na
tsafi,sai dakai
cewa hatta sarkin Hindu na wannan
lokaci wato
mahaifin Sarauniya Iklaira bin Aslam
ta yanzu yana
matukar tsorona yana y mini biyayya
kuma yana
aiko mini da dukiya mai yawa a
karshen kowane
wata guda.Attajiri da mahaifiyata kuwa
kullum suna
dorani a kan TAFARKIn kassara Boka
Salmara suna
nuna mini cewa bani da makiyin daya
fishi a doron
kasa.Bisa binciken danayi a hallarar
tsafina ne na
gano cewa bazan taba iya sace dukiyar
Boka
Salmara ba har sai bayan mutuwarsa
kuma sai yar
uwata Yazirina ta baiyana mun hada
kai NI da ITA
mun kashe Jaruma Sarila mun kwafe
taswirar dake
bayanta mun hada da ragowar
taswirorin dake wajen
Yazirina.Koda Bokanya Muznaira tazo
nan a
jawabinta sai Mujahid ya sake kamu da
tsananin
mamaki gami da fargaba ya dubi
™Abubakar Haleefah Physicist™
Muznaira cikin alamun firgice yace ta
yaya kike zaton
cewa Yazirina zata yarda da duk
wannan labari da
kika bani yanzu kuma ta yaya zata
amince ku hada
kai domin ku mallaki wannan dukiya
tare?Ashe
kenan RABA DAIDAI zakuyi tunda dai
kinason sace
dukiyar ne domin ki dauki fansa akan
Boka Salmara
saidai ki hakura tunda babu sauran
DAUKAR FANSA
akan matacce.Koda Mujahid yazo nan
a jawabinsa
sai Muznaira taja dogon numfashi
gami da ajiyar
zuciya sannan tace banda batun daukar
fansa wadda
ke gabana akwai batun tunanin ceto
rayukan
miliyoyin jama'a.Idan na bar Yazirina
ta mallai
wannan dukiya dake can TASKAR
AJALI ita kadai
zatayi irin zaluncin da sauran sarakuna
da sauran
matsafi keson yi ya kasance su kadai
ne da
makusantansu kejin dadi a cikin
wannan duniya.Ni
burina shine jin 'KAI,TAUSAYI da
TAIMAKO kamar
yadda kai ma zuciyarka ta kansace mai
imani,inai
mai tabbatar maka da cewa Yazirina
bata da wani
wabi wanda yafi ta hada kai dani
domin inda da abu
na biyu wanda take nemansa ruwa a
jallo.Koda jin
haka sai Mujahid ya sake kamuwa da
mamaki yace
ke kuwa menene wannan abu?
Muznaira tayi
murmushi tace bazan fada kome nene
basai a gaban
Yazirina dake kwance domin bana son
ta farka bata
ga jakar guzurinta ba a kusa da ita don
zata iya yi
min hauka a cikin fadata idan bata
ganta ba.Koda jin
haka sai Mujahid yayi murmushi ya
mike tsaye ya
nufi cikin dakin.Da shigar Mujahid
cikin dakin sai ya
duro kofar dakin ta kulle sannan ya
zauna akan wata
kujera dake daf da Yazirina ya kura
mata idanu.Nan
take yaji ya kamu da tsananin sonta
saboda
dimaucewa dayayi da ganin kyawun da
Allah ya
bata.Abinda ya daure masa kai kenan
shi kansa
domin a rayuwarsa bai taba gani wata
'ya mace da
yaji yana son taba sai ita.Saida
Mujahid ya dauki
lokaci mai tsawo yana ta kallon
Yazirina har ya tafi
duniyar tunani inda ya tsinci kansa a
cikin wani
kasaitaccen lambu tare da Yazirina a
zaune suna
hirar soyayya cikin nishadi.Kwatsam
sai yaji tarin
Yazirina ta farka a firgice a razane tana
mai mikewa
zaune.Koda ta bude idanunta tayi arba
da jakar
guzurinta a kafadar Mujahid sai yai
wuf ta suri jakar
ta bude ta leka cikinta,kawai sai tayi
ajiyar zuciya
cikin alamun samun nutsuwa sannan ta
dubi gabas
da yamma kudu da arewa ta dubi
Mujahid kuma ta
shafa raunin kanta taji an dinke shi ta
shafa raunin
kirjinta shima taji an dinke shi kawai
tace ina ne nan
kuma ya akayi muka zo?Kafin Mujahid
ya budi baki
yace wani abu sai sukaga an turo kofar
dakin an
shigo,ba wani bane ya shigo ba face
bokanya
Muznaira.Koda ta hada idanu da
Yazirina sai
Yazirina ta mike tsaye zumbur ta kura
mata idanu
cikin mamaki ba don komai ba sai
saboda ganin
yadda suke matukar kama da
junansu.Nan take
Muznaira ta gabatar da kanta a wajen
Yazirina ta
kwashe labarinta kaf ta zaiyane mata
sannan ta
kwaye hannun rigarta saiga kambun
tsafin Boka
Kaisu Bin Alkama,Muznaira ta dubi
Yazirina tace
yake yar uwata na sani cewa kina
neman wannan
kambun tsafi na boka Kaisu ruwa a
jallo saboda shi
ne kadai abinda zai kare ki daga
sharrin jaruma
Sarila to nafi wata biyu da sato shi a
can fadar Boka
Kaisu,ina mai tabbatar miki da cewa ni
kadai ce zan
hada karfina da naki mu sami nasarar
kashe Sarila
mu kwafi wannan taswirar dake kan
gadon bayanta
sannan mu tafi izuwa TASKAR AJALI
mi debo
dukiyar ubanmu Boka Salmara.Idan
har kin amince
zaki hada kai dani bisa aminci da
alkawari lallai
burinmu zai cika,koda jin wannan batu
sai idanun
Yazirina suka zazzaro suka kama kallon
juna ita da
Mujahid ta rasa abinda zatace.
SHIN YAZIRINA ZATA AMINCE TA
HADA KAI DA
MUZNAIRA SU TAFI ZUWA TASKAR
AJALI TARE...?
WACE IRIN MUMMUNAR BARNA
SARILA ZATA
CIGABA DAYI A KOKARIN NEMAN
YAZIRINA?
WANE IRIN MATAKI SAURAN BOKAYE
DA MANYAN
SARAKUNAN DUNIYA ZASU DAUKA
AKAN SARILA DA
YAZIRINA?
WAISHIN MUJAHID NE BAKON
SAURAYI DAN BAIWA
DA ZAI IYA TAIMAKON YAZIRINA KO
KUWA WANI NE
DABAM WANDA BAI BAIYANA BA?
YAUSHE NE ZA'A TAFI IZUWA KOGON
TASKAR AJALI
KUMA WADANNEN IRIN MASIFU DA
BALA'I NE AKAN
HANYAR?
SHIN MUJAHID ZAI NUNAWA
YAZIRINA
SOYAYYARSA A GARETA?
IDAN YA NUNA MATAN ZATA
KARBESHI KUWA?
Mu hadu A Taskar Ajali Littafi na Uku
don jin
cigaban wannan labari.Amma mene
hasashen ku?
Nima da wannan nake ce muku sai
mun hadu a
Littafi Na Uku.TASKAR AJALI
Littafi na biyu 2
Na Abdulaziz sani M gini
Ebook creat by Shuraih Usman
Ebook publish by www.hausaebooks.cf
Ebook din nan yazo maku ne daga shafin www.hausaebooks.cf
Kuna ziyarci shafinmu don samun sababbin littatafai
Ga duk wanda ke bukatar ebooks nashi ya samu shiga cikin wepsite namu sai ya turo mana da littafin ta Email namu hausaebooks@gmail.com
TASKAR AJALI 3
Littafi na Uku 3
Na Abdulaziz sani M gini
Ebook creat by Shuraih Usman
Ebook publish by www.hausaebooks.cf
Ebook din nan yazo maku ne daga shafin www.hausaebooks.cf
Kuna ziyarci shafinmu don samun sababbin littatafai
Ga duk wanda ke bukatar ebooks nashi ya samu shiga cikin wepsite namu sai ya turo mana da littafin ta Email namu hausaebooks@gmail.com


Lokacin da Yazirina ta kama raba idanu tsakanin
Bokanya Muznaira da Mujahid ta rasa abinda zata ce
bisa hadin kanta da Muznaita.Koda Muznaira taga
haka sai ta kyalkyale da dariya a lokaci guda kuma
ta murtuke fuskarta ta dubeta cikin nutsuwa tace
yake yar uwata kiyi sani cewa baki da wani cikakken
lokaci nayin dogon tunani bisa wannan al'amari
kuma baki da wata mafita a cikin wannan matsala
face ki bani hadin kai tunda a halin yanzu rayuwarki
na cikin mummunan hadari,ki tuna cewa Sarila na
farautarki haka kuma manyan bokaye da manyan
sarakunan duniya suna farautarki ruwa a jallo.Ba
karamar sa'a kikayi ba da kuka fado hannuna ba
amma da tuni taku ta kare,na baki tsawon kwanaki
uku kiyi tunani da shawara keda abokin tafiyar
taki,da gama fadin hakan sai Muznaira ta juya ta fice
daga cikin dakin tana mai jan kofa ta rufeta.Faruwar
hakan keda wuya sai Yazirina ta dubi Mujahid tace
me ka gani don game da al'amarin wannan matar?
shin ka amince mu hada kai da ita?ka sani cewa ni
a halin yanzu duk fadin duniyar nan mutum daya ne
jal zan iya bashi yardata.Koda jin wannan batu sai
Mujahid ya dubi Yazirina cikin mamaki yace wanene
wannan mutum wanda zaki iya bashi yardarki?
Sa'adda Yazirina taji wannan tambaya sai tayi dan
gutun murmushi ga Mujahid tace shine wanda ya
ceci rayuwata daga hannun Sarila a yau din nan,in
ba don shi ba da tuni yanzu na zama tarihi.Koda jin
wannan batu sai Mujahid yayi murmushi yace a'a ba
ni bane na ceci rayuwarki yar uwarki ce Muznaira ta
cece mu gaba daya ta zukomu izuwa nan cikin gidan
da karfin sihirin tsafinta.Yazirina tace amma ai ni ba
don ka goya ni ba a bayanka kayi wannan
azababben gudu ba na ban al'ajabi da ita ma bata
sami nasarar cetonmu ba yakai abokin tafiyata kuma
amintaccena,kayi sani cewa duk da Muznaira ta
kasance yar uwata zuciyata bata aminta da ita ba
domin ina ganin cewa a karkashin zuciyarta akwai
wata muguwar nufin wadda tasa lallai take son
mallakar wannan dukiya ta mahaifinmu shi yasa take
neman hadin kaina,ni yanzu babban tashin hankali
na shine bansan iyakar adadin rayukan da Sarila
zata salwantar ba a kokarinta na farautata,kaga
kenan buyana a wani wuri dominta bazai haifar da
komai ba face karin asarar rayuka da dimbin
dukiya,ya kamata lallai musan hanyar da zamubi mu
fuskanceta domin muga karshenta mu kwafe wannan
taswirar dake zane a kan gadon bayanta.Koda
Yazirina tazo nan a jawabinta sai hankalin Mujahid
ya dugunzuma ainun ya dubeta cikin alamun
tsananin tsoro a lokacin da idanuwansa suka
zazzaro yace haba ya shugabata wace irin magana
kikeyi ne haka kamar wacce ta zautu,ta yaya kura
zata ce ta taro zaki da fada?Ke kanki kinsan cewa
Sarila tafi karfinmu ta kowace siga kuma indai zamu
tareta gaba da gaba cikin dakiku kadan zata gama
damu,ni ina ganin cewa baki da wani zabi wanda yafi
ki hada kai da wannan yar uwata taki Muznaira.Koda
jin wannan batu sai Yazirina ta murtuke fuskarta
cikin alamun tsananin bakin ciki a lokacin da
Mujahid yabita da kallo kawai zuciyarsa dauke da
matukar damuwa.Kawai sai yaga Yazirina ta
durfafoshi fuskarta a murtuke,al'amarin daya razana
shi kenan ainun.Tana isowa daf dashi sai ta kama
kafadunsa a karo na farko ta girgiza shi ta dube shi
cikin fushi tace,idan zaka dawo cikin haiyacinka ka
dawo amma abinda kake fada ba zai taba yiyuwa
ba,idan kuwa ka dage akan hakan saidai mu raba
hanya ni da kai,ka sani cewa tun a farkon haduwata
dakai zuciyata ta bani cewar kaine saurayi dan
baiwar da aka bani labarin cewa zai iya kubutar dani
daga sharrin Sarila,dari bisa dari zuciyata ya aminta
da hakan saboda me zaka bada mini kasa a fuska?
Koda Yazirina tazo nan a zancenta sai jikin Mujahid
yayi sanyi a lokacin ne ta saki kafadunsa ta koma
izuwa kan gado ta kwanta tana mai kallon rufin
dakin cikin tunani mai zurfi.Nan take idanunta suka
ciko da kwalla sakamakon tunowa da tayi cewa ba
kowa bane ya haddasawa mutanen duniya wannan
mummunan tashin hankalin ba face mahaifinta BOKA
SALMARA.Nan take Yazirina taji bakin ciki ya
turnuketa data kasance tsatson boka Salmara kuma
taji ta tsane shi ta tsani kanta.Nan take hawaye ya
kwararo daga cikin idanunta ya kama zuba bisa
kumatunta.Al'amarin daya karya zuciyar Mujahid
kenan yaji ya kamu da tsananin tausayinta don haka
bai san sa'adda ya taso daga kan kujerar da yake
zaune ya dawo kan gefe gadon ya zauna shima a
karon farko sai ya kama hannunta ya ruke suka
kurawa juna idanu yace,ya shugabata ki gafarceni
hakika yanzu na gane duk irin abinda kike tsoro da
tunani a cikin ranki kuma nayi miki alkawarin cewa
duk wuya duk rintsi zan cigaba da taimakonki koda
kuwa zan rasa rayuwata har izuwa lokacin da
bukatarki zata biya amma fa akwai matsaloli guda
biyu.Matsala ta farlo itace ni kaina bansan ko ni
waye ba,abin nufi shine bani da tabbacin cewa nine
wannan saurayi dan baiwa mai sa'a da rabo da zai
iya kubutar dake daga sharrin Sarila.Matsala ta biyu
itace bansan hanyar da zamu iya rabuwa da
maigidan nan lafiya ba har mu sami nasarar sace
wannan kambun sihiri dake hannunta wanda zai
taimaka mana wajen tsira daga sharrin Sarila.Koda
jin wannan batu sai Yazirina taja dogon numfashi
sannan ta zuke hannunta daga cikin na Mujahid tana
mai daka masa harara tace wanene ya baka ikon
ruke hannuna?Koda jin wannan tambaya sai shima
ya murtuke fuska yace wanene ya baki ikon kama
kafaduna dazu har da girgiza su kuma me yasa kika
bari na goyaki a bayana har nayi gudu mai tsawo
dake a lokacin da ba kya cikin haiyacinki?Baki
tambaye ni dalilin yin hakan ba sai a yanzu kawai
dana rike hannayenki.
™Abubakar Haleefah Physicist™
Koda jin wannan batu sai Yazirina ta kyalkyale da
dariya sannan ta kamo Mujahid ta rumgumeshi a
kirjinta gaba daya tace hakika yau ka burgeni dakayi
ta maza ka kawar da dukkan tsoro kuma daga yau
ka zama cikakken abokina.Lallai kafin dare ya raba
inason kayi tunani akan hanyar da zamu sami
nasarar fita daga cikin wannan gidan bayan mun
sace kambun sihiri.Ai dama sata idan ta saci sata ba
laifi bane.Koda gama fadin hakan sai Yazirina ta
janye jikinta daga cikin na Mujahid ta koma kan
gadonta ta kwanta tana mai juya masa baya,shima
saiya mike tsaye ya koma kan kujera ya zauna kuma
ya daga kansa sama ya fada sabon kogin
tunani.Wannan shine abinda ya faru tsakanin
Yazirina da Mujahid bayan sun tsallake harin Sarila
na farko sun fada hannun yar uwarta boyayyiyar
bokanya Muznaira.
*A can cikin birnin Yamein kuwa saida aka gama
wannan bakin gumurzu tsakanin Sarila da Yazirina
bayan gidaje da yawa sun rushe,mutane da yawa
sun hallaka sannan Boka Matawus dasu sarkin yaki
suka iso wajen.Koda sukaga irin mummunar barnar
da su Sarila suka aiwatar sai hankalinsu ya
dugunzuma ainun suka gane cewa lallai Sarila da
Yazirina ba kananun annoba bane.Nan take cikin
hanzari Boka Matawus ya fiddo madubin tsafinsa ya
shafeshi da hannun hagu domin yaga a inda Sarila
da Yazirina suke a sannan.Nan take yaga hoton
Sarila tana tafiya a cikin Birnin Yamein a wani
bangare daban tana waige waige da dube dube,duk
inda taje saidai kaga jama'a nata guje guje da iface
iface ana rugawa izuwa cikin gidaje ana rufe
kofofi.Babban abinda ya dagawa Boka Matawus
hankali shine hanyar da Sarila ta durfafa babu inda
zata kaita face Gidan Sarautar birnin wato inda Sarki
Ubaiyu yake.Boka Matawus ya sake shafe madubin
tsafin ko zai ga inda yaro dan baiwa yake wanda shi
suka fito nema amma sai hasken madubin tsafin
nasa ya disashe izuwa tsananin duhu.Al'amarin
dayayi matukar dugunzuma hankalonsa kenan ba
shiri ya dago kai ya dubi sarkin yaki da ragowar
dakarun dake biye dasu yace rayuwar sarki data
iyalansa na cikin mugun hadari domin can Sarila ta
nufa,yanzu kuzo muyi sauri mu koma can domin mu
kai masa dauki.Koda jin haka sai sarkin yaki Ya dubi
Boka Matawus cikin alamun firgici yace to yaya
batun yaro dan baiwar wanda shine kadai zai iya
ceto rayukan al'ummarmu da dukiyarsu?Boka
Matawus yace na kasa ganinsa a cikin madubin
tsafina,ka sani cewa bamu da lokacin neman wannan
yaro a yanzu,kuzo muyi sauri mu koma fada in ba
haka ba kuwa fadarma gaba daya zata tashi daga
aiki.Koda gama fadin hakan sai Boka Matawus ya
kada linzamon dokinsa baya ya zabureshi da gudu
izuwa ga hanyar da zata mayar dashi fada.Cikin
hanzari sarkin yaki da sauran mukarrabansa suka
rufa masa baya,nan fa suka ci gaba da yiwa
dawakansu kaimi suna tsala gudu.Aikuwa suna
isowa kofar gidan sarautar suka iske dakarun dake
gadin kofar shiga a kwance a kasa sun zama gawa
kimanin su dari uku,ita kanta kofar shiga gidan
sarautar wacce ta kasance katuwar gaske ta bakin
karfe mai matukar kauri da nauyi an jijjigeta daga
jikin gini an yarda ita kasa.Koda ganin wannan
mummunar barna sai hankalin su boka Matawus ya
dugunzuma ainun suka karawa dawakansu kaimi
suka nufi hanyar da zata kaisu fada kai tsaye.Nan fa
duk inda suka wuce basa ganin komai face
gawarwakin dakarun gidan sarautar gidan gaba daya
yayi tsit tamkar babu sauran mutum daya a raye a
cikinsa.Koda ganin wannan al'amarin sai boka
Matawus yaga bazai iya jiran dokinsa ya karaso
dashi fadar ba domin zuciyarsa bugawa takeyi da
karfi sakamakon fargabar tunanin cewa babu
mamaki tuni Sarila ta gama da sarki Ubaiyu.Bisa
wannan dalili ne Boka Matawus yayi girgiza ya bace
bat daga kan dokin nasa bai baiyana a ko ina ba sai
a cikin fadar sarki Ubaiyi.Yana baiyana yayi kicibus
da gawarwakin dakarun dake tsaron sarki da kuma
gawarwakin tsirarun fadawansa da hadimansa.Acan
kuma karagar mulki kuwa sai ya hango sarki Ubaiyu
a zaune ga wani mummunan sara a kafadarsa jini
na zuba yana numfashi sama sama Sarila na tsaye a
kansa ta daga takobinta sama tana shirin ta karasa
kashe shi.Koda yayi arba da Boka Matawus wanda
ya kasance dogon mutum mai kirar sadaukai kuma
duk jikinsa a cike yake da layu gami da guraye na
tsafi sannan kuma taga ya durfafota kai tsaye ba tare
da shakkar komai ba sai ta dan sha jinin jikinta ta
fara tunanin cewa lallai abinda yasa ta danyi
shakkarsa shine yanayin shigarsa iri daya ne dana
Boka Salmara domin shiga ce irin wadda ba zata
taba mancewa da ita ba duk da cewa tun tana
yarinya rabonta da ganin irin shigar.
Tun tana yarinya rabonta da ganin
irin shigar.Koda
ya rage saura baifi taku uku ba
tsakanin Boka
Matawus da Sarila sai ya tsaya cak a
gabanta suka
fuskanci juna ya dubeta a fusace cikin
tsananin
fushi har fuskarsa na gatsinewa
yace,wannan wane
irin haukan banza ne haka kizo kina
kashe mana
jama'armu a banza har ma sauran
kiris ki kashe
mana sarkinmu saboda kawai kin
nemi Yazirina kin
rasa?Shin baki san cewa muma
abokan gabar
Yazirina bane?Koda jin wannan batu
sai ita ma
Sarila ta fusata ta dakawa Boka
Matawus tsawa
hakan yasa yaji har saida hantar
cikinsa ta kada
amma saiya dake yaki ya nuna
tsoransa.Sarila tace
da Yazirina da dukkan sarakunan
duniya da irinku
bokaye duk abokan gabata ne tunda
nasan cewa
dukkaninku kuna son ku rigani
mallakar taswirar
dake hannun Yazirina guda biyu
domin isa kogon
Taskar Ajali.Bani da wani zabi wanda
yafi na kashe
ku gaba dayanku domin na daina
fuskantar wata
barazana.Boka Matawus yace ai kuwa
wannan
shine babban kuskuren da zaki aikata
kuwa domin
dole ne ki hada kai da wani kafin ki
sami nasarar
hallaka Yazirina har ki rabata da
wadannan
taswirori guda biyu kamar yadda ita
ma a halin
yanzu ta hada kai da wata yar uwarta
ta jini domin
ganinbayanki.Ko da jin wannan batu
sai mamaki ya
turnuke Sarila tace yanzu dama
Yazirina tana da
wata yar uwa a duniya bayan ni dana
kasance mun
sha nono daya?Boka Matawus ya
numfasa yace
kwarai kuwa.Nan take sai Matawus
yayi nuni da
hannunsa izuwa ga jikin bango sai ga
hoton Boka
Salmara ya baiyana shida mahaifiyar
Muznaira tun
daga farkon haduwarsu kawo izuwa
lokacin data
haife Muznaira har izuwa rabuwarsu
da yadda
akayi Muznaira ta zamo gawurtacciya
matsafiya har
ta gina wannan gida nata dake
karkashin kasa
kawo haduwarta dasu Yazirina.Koda
Boka Matawus
ya fuskanci hakan sai farin ciki ya
lullube shi ya
dubi Sarila yace abinda nake so dake
shine yanzu
ko kwantar da hankalinki in kaiki
masauki ki zauna
ki huta.Nayi miki alkawarin zan
taimake ki yadda
zaki kai ga samun nasarar abinda kika
sa a
gabanki cikin ruwan sanyi amma bisa
wata
yarjejeniya.Ki sani cewa gaggawa ba
zata kaiki ga
wata nasara ba face akasinta.Koda
gama fadin
hakan sai Boka Matawus ya kwalawa
wadansu
kuyangin Sarki kira.Take wadansu
kyawawan
kuyangi su uku suka shigo fadar a
guje jikinsu na
tsuma saboda tsananin tsoron
Sarila.Da zuwansu
sai suka zube kasa a gaban boka
Matawus shi
kuma saiya dubesu ya daka musu
tsawa yace ku
kwantar da hankalinku kuyi sani cewa
Sarila ba
zata taba cutar daku ba a yanzu
domin mu da ita
mun zama daya.Maza ku kaita babbar
turaka inda
aka saba saukar manyan baki ku kaita
kewaye kuyi
mata wanka sannan a gyara mata
jikinta kuma a
shirya mata abinci mai daraja.Koda jin
wannan
umarni sai kuyangin uku suka hada
baki sukace
an gama ya shugabana.Nan take
kuyangin suka
mike tsaye sukaje suka kama Sarila
tamkar wata
karamar yarinya suka fice da ita daga
cikin fadar
suka nufi wani bangare daban na
gidan sarautar ba
tare data yi musu gardama ba ko tayi
yunkurin
cutar dasu.Tafiyarsu keda wuya sai
Boka Matawus
yasa akaje aka kirawo likitan sarki
Ubaiyu cikin
gaggawa da zuwan likitan ya shiga
aikinsa ya yiwa
sarkin magani.Koda Sarki Ubaiyu ya
dawo cikin
hayyacinsa sai ya dubi Boka Matawus
cikin
murmushin karfin hali yace yakai
dirkar birnin
Yamein ina godiya a gareka bisa
ceton rayuwata
da kayi,tabbas ba don kai ba da tuni
yanzu na
zama gawa,to amma fa ka sani cewa
har yanzu
akwai sauran rina a kaba.Ta yaya kake
zaton cewa
zaka iya sarrafa wannan mahaukaciyar
Jaruma?Duk
naji maganganun da kukayi yaga
samun nasara a
kanta da kuma batun Muznaira daka
nuna mata
wanda bata san dashi ba,inda tayi
yunkurin hallaka
ka ba zaka iya tsira daga sharrinta
ba.Nasan kaga
irin mummunar barnar da tayi mana a
cikin gidan
sarautar nan

Please Login or Register in order to submit comment