Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fara taruwa a
filin gasar jarumtaka domin su
morewa idanunsu kallon yadda wannan karshen na
kambun jarumta zai kasance
tsakanin gimbiya suzaina da jarumi darusi
kafin cikar sa a daya fili ya cika makil fiye da ko yaushe
lokacin babu masakar tsinke
tunda aka fara wannan gasa bisa tarihi ba a
taba samun cikowa irin ta wannan rana ba domin
har a kan katangu da benayen gidajen jama ar gari
mutanen baja baja wani
zai samu iya raba ba komai ne ya janyo hakan
ba face za a sake fafata gumurzu a tsakanin gimbiya
suzaina da jarumi darusi
wato gawurtaccen sadauki daya kawo addinin
musulunci a kasar
bisa wannan daliline jama a sukayi ta tururuwa
daga cikin birane da kauyuka suna shigowa cikin babban
birnin
Al amin Ahmed Guyson ke magana
A wannan rana dai gimbiya suzaina da mahaifinta da wuri
suka zo fada
ba tare da bata wani lokaci ba aka buga gangan
fara gasa nan take su jarumi darusi suka shigo cikin
tsakiyar filin gasar
suka tsaya suka fuskanci yan kallo koda suzaina ta
hada ido da sarila wacce ke zaune a cikin yan kallo
tare da yazirina da kuma mujahid sai suzaina taga sarila
ta dago mata hannu tanayi mata
jinjina da murmushi
Al amarin da yayi matukar daurewa suzaina kai kenan
ta kamu da tsananin mamaki amma koda ta tuno da
irin furucin da sarila ta yi gareta bisa daukar fansar
abinda tayi mata bisa tsautsayi cewar saita tozartata a
gaban jama a sai nan
take taji ta tsani sarila ainun don haka sai ta murtuke
fuskarta ga sarila ta daka mata harara
kuma ta kauda kai ga barin kallonta a dai dai
wannan lokacine su sarila suka ga wani bakin attajiri ya
shigo cikin
filin gasar wadansu bakin dakaru na musamman na take
masa baya
fuskar attajirin cike da gemu da kasumba
kuma idonsa guda a nane yake da wani kyalle baki alamar
cewa idonsa guda ne yake da gani
gaba daya jikinsa a lullube yake da wata doguwar
alkyabba
mai daraja ko hannayensa da kafafunsa ba a gani
abin ka da mai hannu da shuni nan da nan dakarun suka
rinka
buda masa hanya yana wucewa har saida ya kusa zuwa
inda
karagar sarki take sannan dakarun sarki suka tsayar
dashi aka tuhumeshi domin a san ko waye shi dakuma
abinda ya kawoshi
dajin haka sai attajirin yace shi bafatake ne daga
can wani birni da ake kira Damar kusa da kasar misra
kuma yana fatauci kayan kyale kyale donhaka yazone
domin tallata hajarsa ga sarki
nan take akaje aka sanar da sarki wannan jawabi
lokacin da sarki yaji wannan abinda take tafe da wannan
bakon attajiri
sai sarki yace aje a gaya masa cewa ba a nan ake kawo
tallan haja
ba sai a can fada nan filin gasa ne yanzu ya zauna yayi
kallon gasar jarumta in yaso daga baya sarki zai aiko azo
dashi fada su gani
bayan sarki yayi wannan jawabi sai ya dubi hadimin
dayayiwa bayanin yace ka gayawa sarkin yaki ya zuba ido
akan wannan bakon
attajirin saoda zata iya yiwuwa cewa dan leken
asirine akan bakinmu ko mu kanmu
hadimin ya gyada kai yace angama ya shugabana shi
kuwa jarumi darusi yana tsaye a cikin
filin gasar suna masu fuskantar juna shida
gimbiya suzaina sai ya hango shigowar bakon attajiri
koda darusi ya hada idanu da attajirin sai yaji zuciyarsa
ta dan buga da karfi nan take yaji bai aminta dashi ba
duk da cewar fuskarsa cike take da gashikuma idonsa
guda a like yake
sannan akwai tazara mai dan yawa a tsakaninsu
da darusi yaga kaamar ya taba ganin fuskar wannan
attajirin
amma saiya kasa tuno a inda ya taba haduwa dashi
Guyson ko shagala boy.
Nan take dai alkalin gasa ya daga hannunsa sama kuma
ya sauke faruwar hakan keda wuya aka buga gangar
fara gasa aikuwa sai jama a suka kaure da shewa
gami da tafi da jinjina kowa na wasa gwaninsa duk da
cewa
jarumi darusi bai kasance dan gari ba amma sai ga .
Gashi masu goyon bayansa na neman yin kunnen
doki dana gimbiya suzaina
Al amin Ahmed Guyson
Lokaci guda darusi da suzaina suka zare makamansu
ita suzaina addunanta ne guda biyu shikuma
darusi takobice garkuwa kawai sai suka rugo da gudu
izuwa kan junansu suka
ruguntsume da masifaffen yaki ya zamana
cewa suna kaiwa junansu sara da suka cikin zafin nama
juriya da jarumtaka
mai matukar ban al ajabi
nan fa filin gasar ya dada rudewa da shewar jama a
sai da suzaina da darusi suka shafe sa a daya da rabi suna
mugun bakin artabu banda karar haduwar
makamansu da fitar nunfashin bakinsu da kuma karar
dake tashi a cikin filin babu wani sauti dake tashi
saboda gaba daya yan kallon sun tattara hankalinsu
a kan jaruman biyu ko motsin kirki babu mai yi
A na cikin wannan gumurzu ne yazirina ta dubi sarila tace
hakika suzaina ta cika jarumar gaske tunda koni dake
ba zamu iya shafe wannan lokaci mai tsawo ba
haka muna fafatawa da jarumi darusi face ya gama damu
sa adda sarila taji wannan batu sai tayi murmushi
sannan tace gaskiya ne suzaina jarumace ta kwatance
sai dai duk wannan jarumtakar tata ta banza ce domin
nan da cikar wani dan lokaci zata zama gawa
a nan cikin filin gasa
kuma a yau din nan zan fara samun yardar jarumi darusi
ki sani cewa a gobe sai dai a tafi da gawar suzaina izuwa
kogon Taskar Ajali
koda jin wannan batu sai mamaki ya turnuke
yazirina ta dubi sarila cikin kaduwa da dumbin mamaki
tace
me nene zai kashe suzaina kuma yaya mujahid zai baki
amincinsa?
Da jin wannan tambaya sai sarila ta bushe da
dariya tace ki zuba mini idanu kawai zakiga amsar
wadannan tambayoyi
naki daga nan inda kike zaune a dai dai wannan lokaci ne
suzaina da jarumi darusi
suka ja da baya sukayi cirko cirko suna haki saboda
gajiya domin karfi yazo daya a iya yaki ai kuwa sai
fadar ta sake kaurewa da shewa a nayi musu jinjina
kamar hadin baki sai duk su
biyun suka yarda makamansu suka gyara tsayuwarsu
sannan suka rugo da gudu suka ruguntsume da sabon
masifaffen fada suna
masu kaiwa junansu naushi da bugu da hannu
da kafa nan fa jama a suka ga wani abin Al ajabi nata
faruwa
da zarar darusi ya sami nasarar naushin suzaina sai akaga
nan take itama ta
rama da irin naushin da yayi mata
duk irin gwanintar da dayansu yayi sai aga shima
dayan yayi irin ta sak nan fa yan kallo suka rinka
cewa wannan fada shiri ne dama jaruman biyu sun tsara
yadda zasuyi gumurzun
to amma abinda ya rusawa yan kallo wannan tunani
shine dukan gaske jaruman suke yiwa juna domin har
sun hadawa junansu
jini da majina tsananin juriya da bakin naci ne yasa daya
daga cikin su ya kasa kai abokin
gwaminsa kasa
nan fa gumurzun yaki ci yaki cinyewa ya zamana cewa an
sake shafe wata
sa a daya da kusan rabi amma abinda karshen gumurzun
ke nuni shine ragas
shi kansa jarumi darusi yayi matukar mamakin yadda
akayi wannan karon karfinsa
yazo dai dai da na suzaina duk da wata dabara da yayi
kuma yayi
amfani da dukkan karfin damtsensa amma a banza
su kansu yan kallo saida suka kosa suga
karshen wannan masifaffen gumurzu sai da takai cewa
suzaina da darusi sun fara layi tamkar wadanda
suka sha giya suka bugu saboda tsananin gajiya da
galabaita
bisa ka idar wannan gasa da zarar sa a uku
ta cika ba a sami gwarzon ba za a tsayar da wasan a sauya
masa tsari koda
sarki da mahaifiyar suzaina sukaga an shiga wannan hali
sai hankalinsu
ya dugunzuma ainun saboda tsoro kada suzaina da
darusi su rasa lafiyarsu
kwatsam ba zato ba tsammani sai darusi yaga wani uban
gudan jini
bakin kirin
ya furzo waje daga cikin bakin suzaina nan take suzaina
ta durkushe kasa bisa guiwowinta cikin
matukar galabaita
cikin firgici da tsananin mamaki da midauta
darusi ya tallafo suzaina a kirjinsa ya kurma uban ihu
yana mai kwalawa likitoci kira
kafin ayi wani yunkuri sai akaga wata doguwar kibiya ta
taho da gudu zata soke
jarumi darusi amma sai sarila ta dako tsalle sama daga
cikin
yan kallo ta sha gaban darusi take kibiyar
ta soki sarila a gefen kirjinta ta hudo ta gadon bayanta
sarila ta fado kasa tim !! Ta baje a kasa sumammiya nan
fa Al amin Guyson ya rude sbd
tun farkon ganinsa da ita ya kamu da sonta ehm.
Darusi ya sake dimaucewa ya rasa inda zai tsayar da
hankalinsa a tsakanin masoyiyarsa suzaina da kuma sarila
wacce ta ceci rayuwarsa yanzu take
tabbas in ba don ta tari wannan kibiyar ba da goshinsa
kibiyar
zata shige
shikuwa sarki da dakarunsa tuni sun zare takubba
sun daga garkuwoyi suna yiwa filin gasar kawanya a
lokacin da filin gasar ya motsi jama a suka kama guje
guje da iface iface cikin firgici
nan da nan aka dauke suzaina da sarila gudu a ka shige
dasu izuwa cikin gidan sarautar
likitoci suka dukufa a kansu
sarki, darusi da sauran dakarun birnin kuwa
sai suka shiga bincike don gano makiyin da suka harbo
wannan kibiya kuma aka tsananta tsaro a cikin
birnin ya zamana cewa an kulle gaba
dayan kofofin gari ba shige ba fice aka kafa dokar kai
kawo
lokacin da su sarki suka shafe kusan rabin sa'a suna
ta kai kawo a cikin birnin suna bincike baki da mutanan
gari amma basu gano wani
mai laifi ba.
Sai hankalin sarki ya dugunzuma ainun ya dubi
darusi cikin alamun tsananin damuwa yace yakai jarumin
jarumai ka
yi sani cewa hankalina bai taba tashi ba irin yanzu ga
gimbiya can a kwance
rai a hannun Allah kuma ga sarila can ma a kwance
magashiyan wacce ta ceto rayuwarka da farko nayi
zaton cewar wannan lugudan duka da kayiwa suzaina
ne ya sata yin wannan aman bakin jini
amma daga bisani likitoci sunyi bincike sun gano cewar
guba aka bata ta sha kuma gubar tana da
tsananin karfin da take kashe mutum a cikin dakiku
kadan
nayi mamakin data kawo har i yanzu wanene
ya bata guba tasha kuma waye yake kokarin kashe ka
wannan shine abinda ya kamata mu yi kokarin ganowa
bi sa wannan daliline yanzu ni da kaina tare da
dakaru zamu rinka shiga gida gida muna bincike duk inda
mukaga
irin gubar da aka baiwa
gimbiya tasha ko kuma irin kibiyar da aka harbo maka
mun san a nan ne
makiyan suke kai yanzu ka koma can gidan
sarauta kaga halinda gimbiya take ciki kuma ka hada karfi
da yaranka da dakarun gidan sarautar ku kafara tsananta
tsaro sosai kada a bar kowa ya shiga cikin dakin gimbiya
da sarila
hatta abokiyar tafiyarku yazirina ban yarda da
ita ba kada a barta ta shiga in da suke ko wama yanzu
abin zargi ne
koda jin haka sai darusi ya dubi sarki cikin alamun
damuwa yace ya shugabana idan hakane a nima abin
zargi ne
ya kamata a bincikeni
sarki ya gyada kai yace idan har za a bincikeka
to dole ne nima a bincikeni ina mai tabbatar
maka da cewa jama ar garin nan ma sun yarda
dakai fiye da ni saboda kaine ka kawo musu addinin
gaskiya....Sarki ya gyada kai yace idan har za a
bincikeka
to dole nima a bincikeni ina mai
tabbatar maka
da cewar jama ar garinnan sun yarda
dakai fiye
da ni saboda kaine kazo da addinin
gaskiya.
Addinin da shine ya saita rayuwarsu ya
fitar
dasu daga cikin tsananin duhu ya sanya
su
a cikin haske mabaiyani'
koda gama fadin haka sai sarki ya dubi
sarkin yakinsa
yace maza muje mu fara aikin binciken
nan
nan take sarki da sarkin yaki tare da
dakaru
kimanin su dari uku suka nausa izuwa
cikin
garin shi kuwa jarumi darusi tare da
dakarunsa
sai suka ruga izuwa gidan sarautar
A cikin wani babban daki aka kwantar
da
suzaina da sarila likitoci suka dukufa
kansu
saida likitocin suka shafe sama da sa a
hudu suna
kokarin kashe dafin gubar dake cikin
suzaina
amma abu ya gagara
itama sarila an zare kibiyar da ta soke
ta a kirji
amma kuma an kasa gano irin dafin
dake
jikin kibiyar bare a bata maganin da ya
dace da
gubar don haka sai aka rinka baiwa
kowacce magunguna iri iri domin
a ceto rayuwarsu
da kyar a ka dace akan sarila ta farfado
ta dawo
cikin hayyacinta amma saboda raunin
da kibiyar
tayi mata babba ne ko mikewa zaune
kasawa tayi
All amarin suzaina kuwa numfashinta a
sarke
yake kuma kadan kadan yake fita
koda ganin haka sai
guiwoyin likitocin sukayi sanyi kuma
zuciyoyinsu ya karaya suka saddakar
da cewa
lallai suzaina ba zata tsira da rayuwarta
ba
lokacin da mahaifiyar suzaina ta ga
likitocin
sun kasa ceto rayuwar yanta sai ta
koma gefe daya
ta kama jan casbaha tana zubar da
hawaye kawai
A cikin zuciyar ta cewa take ya Allah ya
ubangijin
musulunci ka sani cewa wannan
yarinya ita
kadai gareni idan har ba wa adin nata
ya cika
ba toka tashi kafadunta
Sarila na daga kwance saita dubi
suzaina wacce
take kan gangarar mutuwasaita juyo da
kanta
da kyar ta kurawa mahaifiyar ta idanu
tana mai
muna mata alamun cewa tana son ta
fada mata
wata magana koda ganin haka sai
mahaifiyar
suzaina ta murtuke fuskarta takau da
kanta
ga barin kallonta
Ba komai ne yasa mahaifiyar suzaina
tayi haka ba face
suzaina ta bata labarin duk abinda ya
faru tsakaninsu har da
furucin da tayi na cewar
sai ta yiwa suzaina tsirara a bainar
jama a
duk da cewa taga lokacin da sarila ta
sallama rayuwarta
don ceto ta jarumi darusi sai da taji ta
tsaneta
A na cikin wannan haline jarumi darusi
ya shigo cikin
dakin a guje kuma a dimauce ko da ya
dubi inda
sarila ke kwance yaga har ta farfado
kuma ta kura
masa idanu tana murmushi sai yayi
murna
ya yunkura zaije gareta sai kuma ya
hangp
inda suzaina take numfashinta a sama
sai ya juya
ya ruga gareta amma sai sarila tayi
caraf ta ruko hannunsa
ta dubeshi lokacin da hawaye ya zubo
mata
tace kayi hakuri yakai jarumin jarumai
domin
likitoci sun kasa gano irin gubar dake
jikin
masoyiyarka ina ba don ma tana da
taurin raiba
da tuni ta sheka barzahu
na sani cewa kayi mamaki bisa ganin
na sallama
rayuwata domin ceto taka to ka sani
cewa
nadama ce tazo mini na gane kuraina
kuma ina rokonka
daka yafe miki ka karbe ni a matsayin
masoyiyarka domin a halin yanzu na
kamu da
tsananin sonka da kaunarka
Topa Guyson dai bai yarda da wannan
sonba kufa?
Idan har ka karbi soyayyata lallai zan
karbi addininka
kuma na tayaka jaddada shi a ko ina
cikin duniya
koda sarila tazo nan a zancenta sai
jarumi darusi
yayi wuf ya fisge hannunsa daga cikin
nata.
Ya ruga izuwa kan suzaina da zuwa
yaga idanunta
a wurkile kuma numfashinta na kara
sarkewa
sai hankalinsa ya dugunzuma
kawai sai ya kore dukkan likitocin dake
kanta suka koma gefe daya sannan ya
debo
ruwa a kofi ya karanta wadansu
addu'o'i na musamman
ya durawa suzaina a baki
duk wannan abu da jarumi darusi keyi
sari na kallonsa
tana yin murmushin mugunta saboda ta
tabbatar
da cewa dole ne suzaina ta mutu bata
isa ta tsallake
sharrin gubar dake jikin ta ba
a she tun a daren jiya bayan suzaina ta
baro turakar
sarki ta koma tata kafin ta kwanta saida
wata
kuyangarta ta kawo mata ruwan inibi
tasha
a cikin wannan ruwan inibi ne ka sawa
suzaina wani mugun dafi mai kisa farat
daya albarkacin addu ar da suzaina tay
ne karfin tasha ruwan inibin yasa
dafin ya tsaya a iya cikinta bai zagaya
cikin jinin taba
Ba wani bane ya zuba wannan guba a
cikin ruwan
inibi ba face SARILA da kanta kuma tayi
amfani da
Karfin sihirinta na tsafi wajan samo
gubar da kuma shiga har cikin turakar
suzaina a sirrance ba tare da kowa ya
ganta ba.
Ita kuyangar data kawo wa suzaina
ruwan inibin
bata san cewa an zuba guba a cikinsa
ba
lokacin da mahaifiyar suzaina taga
jarumi darusi
na yin wannan kokari na ceto rayuwar
gimbiya
sai ta kamu da farin ciki ta taso da sauri
daga
inda take zaune tazo kanta ta kura mata
idanu tana mai ci gaba
da addu'a
kwatsam ba zato ba tsammani sai akaji
tari ya sarke suzaina daga
nan kuma sai ta mike zaune da kanta ta
kama
kwarara amai wani irin amai ne na
tsurar
jini wanda ya kasance bakin kirin kuma
mai
kaurin gaske babu kyan gani
sai da suzaina ta cika wani akushi da
wannan
aman jinin
Sannan idanunta suka dawo dai dai
daga wurkulewar da sukayi
kuma ta dawo cikin haiyacinta koda
ganin
haka sai farin ciki ya kama darusi da
mahaifiyarta basu san
sa adda suka rungume ta ba a tare ita
kuwa sarila
bakin cikine ya dameta
taji zuciyarta na tafarfata kamar zata
kone saboda hakanta bai cinmma ruwa
ba
sotayi lallai ayau ta kashe suzaina
domin ya kasance
za a tafi kogon taskar ajali babu ita
kuma taci
gaba da yaudarar jarumi darusi a
matsayin ta kamu da
sonshi har su isa can taskar ajali ta
shammaceshi ta kasheshi
Al amarin sarki kuwa lokacin da suka
fara shiga cikin gida
tare da sarkin yakinsa da dakarunsa
suna bincike
sai da suka kusan karade birnin har
izuwa
tsakiyar dare ba tare da sun kama wani
mai laifi ba
wanda ake zargi da kaiwa jarumi darusi
hari
ko kuma wanda ya sawa suzaina guba
Lokacin dasu sarki suka iso kofar wani
gida ne
dake can bayan gari sarki yaji ya gaji
likis
har ya juya da nufin ya daina binciken a
koma
gida sai ya fara ya juya ya dubi kofar
gidan
sannan ya dubi sarkin yaki yace
wai shin wanene mai wannan gidan ne?
Sarkin yaki yace Ai gidan sarkin kasuwa
ne
wanda yake baiwa fatake haya koda jin
haka sai sarki yace a buga musu kofa
su bude mu shiga
Nan take kuwa aka cika umarnin bugun
farko aka bude
kofar saiga wannan bakon Attajiri mai
ido daya ya
zube har kas ya kwashe gaisuwa cikin
girmamawa sarki ya kama kafadunsa
ya tashe shi tsaye
sannan ya dubeshi yace
yakai wannan babban attajiri kayi hakuri
bisa tashinka da mukayi
daga barci muna kan aikin mune na
bincike domin gano
wadanda suka kaiwa jarumi darusi hari
dasu a filin gasa
da kuma wadanda suka cutar da yata
gimbiya
suzaina da guba
koda jin wannan batu sai attajirin ya ce
wannan
dakyau ya shugabana a sa dakaru su
caje ko ina
a cikin gidan nan kuma su duba dukkan
kaya na ina murna
da haka ba tare
da bata wani lokaci ba aka shige cikin
gidan
aka kama bincike
babu inda ba aduba ba a cikin gidan
hattama cikin
rijiyar saida aka yi nutso izuwa can
karkashinta
aka tabbatar da cewa babu komai a
cikinta
akwatunan da hajojin attajirin ke cike
kuwa kimanin guda dari uku
da ashirin saida aka fito da gaba dayan
kayan
cikinsu akayi musu
filla filla ama ba aga komai ba face
kayankyale kyale
masu daraja irin na sarakai
nan take sarki yayi sha awar kayan har
yayi cinikinsu yace
gobe da safe attajiri yazo fada ya karfi
kudinsa
har sarki ya yiwa attajiri sallama ya juya
zasu tafi
sai attajirin yayi gyarar murya yace ya
shugabana ina da shawara a kan
yadda za a gano masu laifi ka sani
cewa
sau tari makashinka na jikinka saboda
haka ina mai
shawartarka dakasa a caje dakin koda
da kowa a cikin
duk mutanen dake daf dakai komai
gaskiya da amanarsu kuwa
ta wannan hanyace kadai za a iya gano
wadanda sukayi wannan
sa adda attajiri yazo nan a zancensa sai
sarki
ya numfasa yace tabbas kazo mini da
shawara mai
kyau kuma lallai zanyi aiki da ita.
Al amin Ahmed guysonke magana.
Lokacin da sarki ya dawo fada ya tske
cewa suzaina
da sarila sun tsira da rayukansu har
kowacce
ta koma turakarta sai farin ciki ya
kamashi ainun
musamman da yaji cewar darusi ne ya
baiwa suzaina ruwa
wanda ya tofa addu a a cikinsa tasha ta
warke
da yake dare ya raba sosai sai sarki ya
tafi izuwa turakarsa
inda ya iske matarsa mahaifiyar suzaina
a zaune cikin farin ciki tana jiransa
da shigowarsa saita mike ta taryeshi ta
cire masa
rawaninsa da alkyabbarsa da kuma
takalminsa sannan
ta jashi izuwa kan gado suka kwanta
tana mai
dora kanta akan kirjinsa tace
yakai Abul suzaina hakika yaunaga ikon
ubangijin musulunci kuma naga wani
abu dayayi
matukar daure mini kai
koda jin wannan batu sai sarki ya kawo
gwauron numfashi
ya ajiye sannan yace ni kaina nayi
Al'ajabi matuka to amma wai shin wani
abune ya daura miki kai?
Mahaifiyar suzaina ta ce nayi matukar
mamaki bisa ganin
yadda ta sallama rayuwarta domin kare
ta jarumi darusi
da cewar alhalin yanzu ta kamu da
tsananin sonsa
har ma tana cewa itace zata maye
gurbin suzaina idan ta mutu
koda jin wannan batu sai hankalin sarki
ya tashi ainun
ya mike zaune zumbur ya yunkura zai
sauka daga kan gadon domin
ya sanya kayansa ya fice
amma sai mahaifiyar suzaina tayi wuf
ta riko hannunsa
tace lafiya? Me zakaje
kayi yanzu?
Sarki ya dubi matarsa a cikin alamun
firgici
yace jikina da zuciyata sun bani cewa
wannan
yarinyar sarila itace take da hannu a
harin da aka kawowa
jarumi darusi da kuma gubar da aka
baiwa gimbiya
ki tsaya kiyi nazari a kwakwalwarki ki
tuna cewa babu wanda ya tsani
gimbiya sama da sarila tun daga ranar
da
ta kayar da ita a gasar jarumtaka
ki tuno da duk irin furucin da tayiwa
suzaina
akan rabata da darusi
da son tozarta ta a bainar jama a
ki tuna da yadda take burin zuwa kogon
TASKAR AJALI bakya tunanin cewa ta
sallama rayuwarta ne don ceto tasa
saboda
nan gaba zai iya taimakonta wajan isa
kogon Taskar Ajali?
Lokacin da sarki yazo nan a zancensa
sai matar
tasa tayi shiri tana tunani sannan tace
to amma tayaya sarila zata iya zubawa
gimbiya
guba a cikin abincinta ko abin shanta
alhalin bata isa taje turakarta ba?
Guyson nake.
Sarki ya gyada kai yace ni ma nayi
tunani a kan hakan amma dai ai maso
abinka
ya fika dabara a gobe ne likitoci zasu
kammala
bincike a kan duk abincin da abin shan
da gimbiya
tayi amfani dasu a ranar
mahaifiyar suzaina ta sake ajiyar
numfashi tace to yaya batun wannan
kibiyar
da aka harbo domin a kashe jarumi
darusi?
Al amin Guyson nake
shinka gano wanda ya harbota ne sarki
ya girgiza kai yace bamu gano ba amma
dai har yanzu muna aiki a kan hakan
mahaifiyar suzaina tace ka tsananta
wannan bincikea cikin bakin da suka
shigo garin nan domin dan gari bashi
da kwarin
guiwar harbar darusi sai dai kuma ance
da dan gari akanci gari
koda jin wannan batu sai sarki ya koma
ya kwanta yana mai cewa
na yar da da shawararki zamu ci gaba
da bincike
domin inaji a raina cewar mai laifin nan
a cikin garin nan yayi
basaja wannan shine abinda ya faru a
gidan sarauta
Al 'amarin wannan attajiri wanda ya
siyarwa da sarki
hajojinsa kuwa bisa cewar gobe da safe
zaizo fada ya
karbi kudinsa sai bayan sarki da
dakarunsa
sun dan jima da tafiya sanan ya tara
gaba dayan yaransa
ya bushe da dariyar farin ciki yace
tabbas
shirina yana tafiya dai dai kamar yadda
na tsara
koda gama fadin hakan saiya umarci
daga daga cikin
yaran nasa ya dauke alkyabbar dake
jikinsa sai ga shi ashe hannu daya
gareshi nan take
kuma yasa lafiyayyen
hannun nasa ya daye
gemu da sajen dake kan fuskarsa kuma
ya bude
rufaffen idonsa
A she idon nasa lafiyayye ne ba wani
bane ba wannan
attajiri face SARKI DAMNASH wanda ya
fafata kazamin
yaki da JARUMI DARUSI
har darusi ya sare masa hannu guda
bayan sarki Damnash ya gama baiyana
fuskarsa da jikinsa
sai ya sake bushewa da dariyar
mugunta lokaci guda kuma ya turbune
fuskarsa ya dubi dukkanin yaran nasa
yace
kun sani cewa na batar da kamannin
nane nazo nan birnin domin na dauki
fansa a kan jarumi darusi
sannan kuma na kashe sarila da
yazirina na dauke
taswirorin dake hannunsu na isa can
kogon TASKAR AJALI na kwaso dukiyar
dake ciki wacce
da zarar na mallaketa duniya kaf data
dawo karkashin ikona
dani daku duk mun huta da wahalar
duniya har abada
don haka dolene muci gaba da jajircewa
iya ranmu
wajan ganin mun cinma burinmu
tabbas in ba don sarila ta ceci rayuwar
Darusi ba a lokacin da na harba masa
wannan
kibiya mai mugun dafi ba da tuni ya
sheka barzahu
yanzu itace zata mutu kuma bamu san
a inda ta
boye taswirarta ba
Abin tambaya anan shine menene
dalilin da yasa
sarila ta ceci rayuwar darusi?
Tabbas ruwa baya tsami banza kodai ta
kamu
da tsananin sonsa da gaske ko kuma
tana sonta yaudare
shi don amfani dashi
wajan isa kogon Taskar Ajali.
Sa adda sarki Damnashi yazo nan a
jawabinsa sai
shugaban dakarunsa ya risina a gareshi
yace
ya shugabana
yanzu dai dole ne mu dakatar da komai
har
sai mun gano halin da sarila ke ciki
walau tana raye ko ta mutu
sarki Damnashi ya numfasa yace sarila
zata iya yiwa kanta maganin dafin
wannan kibiya
domin tasan shi amma wai shin ta yaya
aka baiwa gimbiya suzaina dafi tasha
domin wannan gudan jini daya furzo
daga bakinta
akwai guba a cikinsa
yanzu dai akwai yiyuwar mutuwar
gimbiya idan kuwa ta mutu na tabbatar
da cewa komai zai koma hannun
yazrina da sarila da darusi
abu ne mai sauki a wajena domin nafi
tsoron sarila
da su saboda dukkaninsu
tafisu kaidi da makirci da kuma sanin
tuggun duniya
sai da aka shafe kwanaki uku cif a cikin
wannan birni ana bincike da neman
masu laifi
bisa dokar hana kowa shige da fice
amma ba agano komai
ba aranar kwana na ukunne da farkon
safiya
aka janye dokar kowa ya fita don
aiwatar da harkokinsa
a ranar ma sai da kasuwa taci.
Attajiri Damnashi kuwa sai a ranar
kwana na ukunne ya
sami damar isa fada don karbar kudin
kayan hajojinsa
yana isa ya iske jama a sunyi dandazo
a fadar ana jiran sarki
ya fito domin aikalan gasa su yanke
hukunci
bisa wanda ya cancanci a ba shi kambu kai nima dai
Guyson na cancanci ku
bani Kambu a wannan zauran+
koda attajiri damnashi tare da yaransa
suka shigo
cikin fadar sai suka hango jarumi darusi
tare
da gimbiya suzaina zaune a can saman
gini kusa da karagar sarki cikin hanzari
damnashi ya buya a cikin yaransa ya
sake batar da kamanninsa yayi shiga
irin ta yaran nasa saboda ya tabbatar
da cewar idan har ya kusanci darusi
suka hada idanu sai ya shaida shi.
A wannan lokaci sarila da yazirina na
zaune a gefe
daya kusa dasu darusi shikuwa mujahid
yana tsaye
a hannun hagun jarumi darusi yana ta
kalle kalle da waige waige yana lura da
duk mutanan
dake cikin fadar da kuma wadanda ke
shigowa
jarumi darusine ya bashi wannan aiki
domin kada
makiya su shammacesu su sake kawo
musu wani
harin duk da cewa an kara tsananta
tsaro a fadar an ninka yawan dakaru
sau uku
a dai dai wannan lokacine sarki ya
shige cikin fadar ai kuwa
sai kowa ya mike tsaye don girmamawa
shi har sai da sarki ya iso inda karagar
sa take
ya zauna sannan kowa ya koma kan
mazauninsa
A sannan ne jama suka fara yin kus kus
kowa na
fadin albarkacin bakinsa bisa abinda
ake zaton
zai wakana kawai sai aka ga sarki ya
mike tsaye ya fuskanci jama ayayi
gyaran murya yace.
Yaku jama ar wannan biri namu mai
albarka
kamar yadda kukaga ni da idanunku
abubuwan
da suka faru a gasar jarumta na ban
tsoro da ban
mamaki abubuwane wadanda basu
taba faruwa ba
kuma hakan ya na nuni da cewar akwai
makiyanmu
a cikinmu amma bamu san su ba
kowa ya sani cewa jarumi darusi da
gimbiya suzaina sunyi ragas a wannan
gasa babu wanda ya sami nasarar
karbar kambun jarumta daga cikinsu
bisa dokar wannan gasa idan har ta kai
da anyi kunnan
doki to dolene a sauya salon gasar
kuma a sake yin wata
gasar sabuwa
A yanzu na yanke shawarar cewa za a
sake yin wannan
gasa kuma yanayinta shine za ayi shiri
a tafi izuwa
kogon TASKAR AJALI duk jarumin da ya
iya yakar
mugayan abubuwan dake kan hanyar
zuwa
can din da kuma abubuwan dake cikin
kogon ya hallaka
su sannan ya iya dauko dukiyar dake
cikin kogon
shine ya lashe wannan gasa ta birnina
kuma shi
za a baiwa kambun jarumta na duniya
gaba daya
Ehm An ya bada Guyson za ayi wannan
gasar ba kuwa.
Amma dai bari muji cigaban labarin..
Za ayi wannan tafiya ne nan da cikar
kwana bakwai
don haka duk wanda yake da sha awar
shiga wannan gasa
to ya kai sunansa zuwa alkalan gasa
ayau din nan
kafin gari ya waye
lokacin da sarki yazo nan

Please Login or Register in order to submit comment