Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gajine
maza ka turomin abokin gwami na gaba
daga cikin wadancen jaruman uku
dajin haka sai alkalin gasa ya juya ya dubi
inda jarumi darusi yazirina da sarila ke tsaye ya dubi
yazirina yace
kece mai wasa na gaba
dajin haka sai yazirina ta dako tsalle daga
inda take tsaye tamkar an cillota daga cikin
baka ta dira a tsakiyar filin gasar ya zamana
cewa ta zarar dake tsakaninsu da gimbiya
suzaina bata wuce taku biyar ba kawai sai
ta zare takobinta ta jujjuyata tana mai sarrafa
ta cikin tsananin gwaninta take gaba dayan
jama ar dake filin suka kaure da shewa gami
da tafi saboda ba a taba ganin jarumin da ya
iya sarrafa makami ba haka
ita kuwa gimbiya suzaina saita dubi yazirina
cikin murmushi gami da kallon raini kawai
saita mayar da addunanta cikin kufensu
dake rataye a bayanta ta gyara tsayuwarta
kuma tayafito ta da hannu
koda yazirina taga suzaina tayi mata irin
wannan raini da wulakanci wato ma tafi
karfin ta yaketa da makami sai ranta ya baci
ainun ta yunkura cikin zafin nama da dukkan
karfinta kuma cikin tsananin fishi ta rugo izuwa kan
suzaina
koda ya rage saura taku biyu kacal su hadu
sai duk su biyun suka daka tsalle sama take
yazirina ta kawowa suzaina sara a wuya
da nufin ta cisge mata kai cikin bakin zafin nama
suzaina ta sunkuya a saman takobin yazirina ta sari iska
kafin yazirina ta waigo ta kawowa suzaina
wani harin tuni suzaina ta gabza wa yazrina
budu da kafarta akan kunnenta na dama.
Take akaga yazrina ta fado kasa sumammiya ko
kyakkyawan
motsi batayi ba kuma ta kife kasa rub da ciki
jini na yoyo a hancinta da bakinta
a dimauce likitoci suka rugo izuwa cikin filin gasar
suka dauke yazrina
a lokacin da gaba dayan mutanen dake filin
suka kame saboda tsananin mamakin yadda
suzaina ta yiwa sarila kwaf daya haka
ita kuwa jarumar jarumai sarila zuciyarta
ce ta kama tafarfasa kamar zata kone saboda
bakin cikin ganin abinda suzaina tayiwa yazirina don haka
kafin ma alkalin gasar ya sake shigowa
cikin filin gasar ya kira jarumi na gaba
tuni sarila ta dako tsalle a sama daga inda take tsaye
cikin shammace ta jerawa suzaina duka akan kirjinta
sau biyu kuma ta naushi fuskarta sau daya
saboda karfin naushin saida suzaina tayi taga taga
saura kiris ta fadi kasa amma sai akaga ta tsaya
cak a wannan lokacinne ta shafo lebenta taga
dan jini sakamakon yar tsagewar da yayi
koda suzaina taga jini a kan lebenta sai ta dako sufa
daga inda take tsaye ta fyalli kafafun
sarila, sarila tayi sama tayi juyi tamkar an murza
tayi katantanwa kafin ta faddo kasa tuni
suzaina ta daki kirjinta da karfin gaske
saboda karfin dukan saida tayi sama ta fice daga cikin
filin gasar gaba daya
bayanta yaje ya gwaru da katangar
gini amma sai akaga ta diro kasa bisa
kafafunta amma sai da ta furzar da gudan jini
daga bakinta kuma ta sosa kirjinta saboda
tsananin zugi da radadin da taji
Take itama ta dako sufa daga inda take tana mai
zare takobinta kafin ta diro kan suzaina tuni itama ta zare
addarta guda
ta tareta sun ruguntsume da azababben yaki.
Take ita ma sarila ta dako sufa daga inda take ta
na mai zare takobinta kafin ta diro kan suzaina tuni itama
ta zare addarta
guda ta tareta sun ruguntsume da azababben yaki
Wohoho, idan gwani da gwani suka hade kuma
jarumta ka da sadaukantaka tayi karo da
takwararta dole ne gumurzu ya zama ta shin hankali
ga dan kallo ma
ana fara wannan gumurzune hankalin yan kallo
ya dugunzuma domin take jama a suka fara guduwa
suna barin inda suke zaune a kewayen
filin gasar saboda barazanar dirar makaman jaruman
biyu a kan kujerunsu suna ragargajewa saboda tsalle
tsallensu suna
dira a ko ina tamkar kwari ko tsintsaye duk abinda
suka sara ko suka soka a filin gasar take yake rabewa
biyu ko kuma ya huje hatta sarki da jarumi
darusi saida hankalinsu ya dugunzuma bisa ganin
wannan mugun artabu da akeyi
tsakanin gimbiya suzaina da sarila
kafin cikar yan dakiku duk yan kallo
dake gaba gaba a filin gasar sun tarwatse
sun koma can baya babu shiri mutane suka
rinka kama katanga suna hayewa don su tsira
kuma saboda nacin son ganin yadda karshen
gumurzun zai kasance
saida jaruman biyu suka shafe kusan sa a guda suna ta
fafatawa
ba tare da dayansu
ya sami nasarar koda lakutar jikin daya ba
alamar cewa iya yakinsu yazo daya gami da
zafin namansu bisa dole kowannansu ya ja da baya
sukayi
cirko cirko suna haki saboda tsananin gajiya
a lokacin da fadar tayi tsit tamkar mutuwa
ta gifta kuma a lokacinne kurar da jaruman biyu suka
tayar ta fara lafawa
sai a dai dai wannan lokacine jaruma yazirina ta dawo
hayyacinta bayan
likitoci sun jima a kanta suna kokarin ceto
rayuwarta a firgice ta mike zaune zumbur
ta bangaje likitocin dake zagaye da ita ta rugo
da gudu izuwa cikin yan kallo
koda ta iso taga sarila da suzaina a tsaye suna
kallon kallo kawai kuma kowannansu a kwai
busashshen jini akan fuskarsa saita cika
da tsananin mamaki domin a zatonta yadda
suzaina tayi mata dukan farat daya haka itama
sarila za ayi mata
yazirina ta dubi jarumi darusi tace tabbas sarila
ta cika jaruma amma yaya kake ganin yadda
karshen wannan gumurzu zai kasance?
Kafin darusi ya budi baki ya bawa yazirina amsa sai kawai
yaga suzaina da
sarila sun zubar da makaman hannunsu
sun dunkule hannayensu koda ganin haka sai darusi
ya gyada kai ya dubi yazirina yace
ai yar uwarki ta tafka babban kuskure data
yarda makamanta domin yanzu ne zata gane
banbancinta da suzaina
kafin darusi ya gama rufe bakinsa tuni sara
da suzaina sun rugo izuwa kan juna sun
ruguntsume da azababben yaki suka
wanzu suna kaiwa junansu naushi da bugu da hannu da
kafa ai kuwa a na fara wannan gumurzu a karo na biyu
sai sarila ta raina kanta saboda
suzaina ta fita zafin nama da karfin damtse kafin
sarila ta naushi suzaina sau daya tuni suzaina
ta jera mata naushi uku kuma karfin naushin
nata ya ninka na sarila sau uku
duk sa adda sarila ta kare naushin suzaina da hannayenta
saitaji
hannayanta nayin mugun zugi da radadi
tamkar zasu kakkarye nan da nan suzaina ta kuntata
sarila ya zamana cewa bata iya maida martani sai kokarin
kare hari
koda aka sake dan jimawa kadan sai kare
harinma ya gagara nan fa sarila ta fara shiga
cikin mugun hali domin tuni suzaina ta fara jera
mata luguden naushi sai gani akayi tana
furzar da jini daga cikin bakinta tana yin tangadi
da layi tamkar wacce tasha giya ta budu
A na cikin hakane suzaina ta shammaci sarila
ta yi mata wani wawan dundu a gadon bayan
take sarila ta sunkuya kasa tayi ruku'u a lokacin
da taji wani irin mugun jiri ya kamata kuma
idanunta suka kama lumshewa tana gani
dishi dishi
har suzaina ta yunkura zata gabzawa sarila
naushi a fuskarta da kafarta sai ta hada idanu
da jarumi darusi
take yayi mata inkiyar kada ta bugeta kawai sai
suzaina ta fasa dukan nata tasa danyatsanta guda
ta ture ta take sarila
ta tuntsire da baya ta baje a kasa ta kasa koda mikewa
tsaye
koda ganin abinda ya faru sai jama a suka
rude da shewa ana tafi akaci gaba da yiwa
gimbiya suzaina jinjina hatta sarki sai ya mike tsaye
tare da matarsa suka rinka yiwa suzaina tafi gami da
jinjina.
( Al amin Guyson ma saida ya tafa mata )
a dai dai wannan lokaci ne alkalan gasa ya shigo cikin
filin gasar da sauri ya dubi suzaina yace shin
zaki iya wasanki na karshe ne yanzu ko kuwa
sai gobe ko anjima?
Kafin suzaina ta bude baki tabada amsa sai jarumi
darusi yayi wuce yace sai gobe da safe zan fafata
da ita yana gama fadin hakan sai jama a suka kaure da
shewa
a dai dai wannan lokacine sarila ta mike zaune
dakyar sa adda hawayen takaici ya subuto
daga cikin idanunta ita kuma yazirina saita ruga da gudu
izuwa gareta ta taimaka mata ta tasheta
tsaye ta janyeta suka fice daga cikin filin gasar tare.
Lokacin da magariba tayi sai darusi da mujahid na zaune
a cikin turakarsu
bayan darusi ya idar da sallar magariba
yana zaune yana lazimi sai ga wani hadimin sarki
ya shigo cikin turakar da sallama ya risina ga
jarumi darusi yace ya shugabana sarki yace
na shaidamaka cewa yana gaiyatarka izuwa
Dare bayan sallar isha koda jin wannan batu
sai darusi yayi murmushi ya dagawa hadimin hannu yana
mai yi masa nuni
da cewar ya amsa wannan gayyata kuma
yana nan tafe
nan take hadimin yayi musu sallama ya juya ya fita daga
turakar
fitarsa keda wuya darusi ya hattama lazimin nasa
sannan yayi addu a ya shafa ya juyo ya
fuskanci mujahid kawai sai yaga mujahid
ya daga kansa sama yana kallon rufin dakin
alamun cewa ya fada cikin kogin tunani mai zurfi
koda ganin haka sai darusi ya dafa kafadarsa take
mujahid yayi firgigit kamar
wanda ya farka daga barci ya dubi darusi cikin
alamun razana yace '' Eye me a kace? Darusi yayi dariya
yace saboda me kake damun kanka a kan
abinda bai damu da kai ba ina mai shawartarka
daka koyi yadda ake danne zuciya a lokacin
da ta kamu da son abu kamar yadda nake danne
son gimbiya suzaina a cikin raina duk da cewa
nasan tana tsananin kaunata,
koda jin wannan tambaya sai mamaki ya turnuke
mujahida yace kai kuwa yaya akayi kasan cewa tunanin
sarila nake yi?
Koda jin wannan tambaya sai jarumi darusi
yayi murmushi yace ai tatsuniyar gizo bata
.wuce ta koki duk abinda mutum yake so yana tare dashi
kada ka manta cewa tun a farkon haduwarmu daku
na gane cewa kana matukar son saril
abinda zan yi maka albishir dashi shine
mahakurci mawadacine kaci gaba da jira akwai
lokacinda sarula zata baka soyayyarta amma ba yanzu ba
koda jin wannan batu sai mujahid ya kamu
da tsananin farin ciki bai san sa adda ya rungume
darusi ba yana mai cewa yaya akayi kasan cewa
sarila zata soni a nan gaba?
Darusi yace bana duba ba na tsafi amma ina amfani da
tunani ne da kuma hangen nesa a yanzu haka son da
kake yiwa sarila yasa ka kasa karbar addinina
saboda kana tunanin cewa idan ka karbe shi bazata
taba yarda dakai ba har ta baka soyayyarta
toka sani nayi maka uzuri kuma nayi maka
alkawari akwai lokacin da zaizo komai ya daidaita
mujahid ya dubi darusi cikin alamun rashin fahimta
yace me kake nufi da cewar akwai lokacin da komai zai
dai daita
darusi ya sake yin murmushi yace wai shin
me kake ci ne na baka na zuba ka sani cewa
gaggawa aikin shaidanne zaka ga komai da idanunka
kawai kabi a sannu har jarumi darusi ya yunkura
zai mike sai mujahid ya ruko hannunsa yace
dashi ina kuma zaka tafi ka barni alhalin ni
ma ina da wata magana mai mahimmanci wacce
zan gaya maka?
Darusi yace ina son zanje masallaci ne na zauna naci gaba
da addu oina saboda ina da wadansu manyan
bukatu a gabana
wacce magana ce mai mahimmanci wacce
tun tuni baka sanar daniba?
Mujahid yayi ajiyar zuciya yace ka taka a hankali
na fahimci cewa yazirina ta kamu da sonka
kuma ita ma tana son ta karbi addininka
koda jin wannan batu darusi yayi murmushi
yace sai yanzu haka tuntuni na san da hakam
amma saboda nasan cewa ba abune da zai yiyuba
shi yasa tuntuni ban daukeshi da mahimmanci ba
darusi na gama fadin hakan sai ya mike tsaye ya fice daga
cikin dakin shikuwa mujahid
saiya bishi da kallo kawai yana mamakin irin
kwakwalwarsa da kuma basirar da Allah ya bashi.
++
++
A can ban garen masaukin su sarila kuwa bayan sunci
abinci sun sha magunguna
bisa tsamin jikinsu saboda dakuwar dasukayi
a filin gasa sai suka kishingida akan
shimfidunsu cikin tsananin gajiya tamkar zasuyi barci
amma sai
dukkaninsu idanunsu suka bushe kowacce
tayi shiru tana tunanin a cikin ranta
tsawon yan dakiku dayansu baice kala ba daga can sai
sarila taja dogon numfashi ta ajiye ta dubi yazirina
cikin alamun tsananin takaici tace a duniya ba a taba
tozarta jarumtakata ba da wulakantani kamar yadda
suzaina tayi mini
ki sani cewa a halin yanzu ina jin tsananin kiyayyarta
a cikin zuciyata fiye da yadda na tsani mtuwata
kuma na rantse da girman mahaifinmu
saina cusa mata bakin ciki da zata tafi dashi har kabarinta
koda jin wannan batu sai yazirina ta dubi sarila cikin
alamun
tsananin mamaki tace ke kuwa ta yaya zaki
sami nasarar cusawa suzaina bakin ciki alhalin
ta fiki komai ta fiki kyau ta fiki jarumtaka
gami da dukkan gata na duniya
sa adda yazirina tazo nan a zancenta
sai sarila ta bushe da dariyar mugunta lokaci guda kuma
ta hade fuskarta tace.
Al amin Guyson ke magana
idan mutum ya zame maka alakakai kana tsayawa ne kayi
tunani ka gano lagonsa suzaina bata da wani
lago face son da take yi wa jarumi darusi
daga yau zan fara kafa bacin soyayyarsa a kan darusi
kuma dole yadda zanyi na ribaceshi na rabashi da ita sai
nayi
wannan shine babban makamin da zan iya tarwatsa
rayuwar suzaina da shi ina mai tabbatar miki da cewa sai
na mallaki jarumi
darusi komai rintsi da tsanani koda kuwa sama
da kasa zata hade zan jure duk irin wulakancin
da zaiyi mini kamar yadda na wulakanta
shi a baya har sai zuciyarsa ta karaya ya kamu
da tsananin kaunata ki sani cewa ba wai sai da kyau da
kudi ko jarumtaka ba mace zata iya siye
zuciyar da namiji ba akwai hanyoyi na kissa gami da nuna
masa tsananin so da kuma sihiri wanda bana tsafi ba
akwai sirrika da dama na al ada wadanda
na gada tun iyaye da kakanni lokacin da
sarila tazo nan a jawabinta sai hankalin yazirina
ya dugunzuma ainun idanunta suka
Zazzaro cikin alamun tsananin damuwa
ta dubi sarila tace amma dai ni a ganina bai
kamata kiyi haka ba kuma ko kin aikata hakan ba
zaki yi nasara ba
dajin haka sai sarila ta dakawa yazirina tsawa ta firgita
ainun har hantar cikinta ta kada sannan sarila
ta dubeta a fusace tace kada ki daukeni
wata shasahsha ki dauka cewa bansan
abinda ke cikin rankiba
toki sani tun a farkon haduwarmu da jarumi
darusi na gane cewa kin kamu da sonsa ki kwantar
da hankalinki ni soyayya ta a gareshi bata gaskiya
bace kawai zanyi amfani da shine izuwa tsawon
dan lokaci sannan na bar miki shi idan kika kuskura
kika tona mini asiri bisa abinda nake shirin
kullawa mutuwace hukuncinki koda gama
fadin hakan sai jaruma sarila ta juyawa yazirina
baya ta rufe idanunta ta kama barci abinta
ita kuwa yazirina hankalinta ne ya dugunzuma
ainun ta rasa abinda ke mata dadi a duniya
bayan an gabatar da sallar isha i a masallaci
jama a sun fito daga cikin masallacin sai sarki ya kama
hannun jarumi darusi ya ruke ya jashi
suka tafi izuwa can turakarsa domin suci abindin dare
tare kamar yadda ya tsara lokacin da suka fara tafiya
a cikin harabar gidan sarautar sai sarki yace wai shin
menene dalilin da yasa kaki
yarda kuyi wasan karshe na wannan gasar jarumtaka
ayau dinnan ?
Koda jin wannan tambaya sai darusi ya maidawa
sarki martanin murmushi yace ya shugabana kowa
a garin nan ya san irin jarumtaka ta kuma
ansan cewa nafi suzaina iya yaki da karfin damtse
dukda cewa sa adda muka fafata a waccen gasar da kyar
na sami nasara akanta
ka tuna cewata gaji likis a lokacin da tayi wannan
gumurzu har sau uku a filin
gasa idan muka fafata na bata dama tayi nasara dole
mutane su gane cewa alfarma nayi mata amma idan
a gobe ne muka fafata dukkaninmu zamuji jiki kuma yan
kallo
zasu gamsu da dukkan sakamakon karshe na gasar
koda darusi yazo nan a jawabinsa sai
sarki yayi dariya yace tabbas Allah ya hore maka
basira da hangen nesa irinka basu da yawa
a duniya amma abinda nake so dakai shine
a gobe idan kuka fafata kada ka bata dama ta sami
nasara a kanka kai nake so ka karbi kambun
gasar daga hannunta
koda jin wannan batu sai mamaki ya turnuke
darusi yace ya shugabana me yasa kake son na karbi
wannan kambun jarumta daga hannun yarka
sarki yayi ajiyar zuciya yace
yakai wannan jarumin jarumai
ina so ka sani cewa duk abubuwan da suke
faruwa a yanzu a cikin birnin nan nawa
manyan sarakunan dake wannan nahiya da manyan
bokaye suna gani ko kuma ince suna samun
labari idan aka ga ka karbi wannan kambun
jarumtaka zukatan makiya zasu karaya su fara
tunanin cewa lallai addininka abin gasgatawa ne
musamman a nan gaba idan akaga kun shiga
cikin Kogon Taskar Ajali ka fito a raye cikin koshin lafiya
Al amin guyson ke magana
koda sarki yazo nan a zancensa sai darusi ya cika
da mamaki ya jinjinawa sarki yace tabbas
duk wanda ya rigaka kwana dole ya rigaka
tashi gashi dai yanzu saboda ka rigani zuwa duniya
ka hango mini abinda ko kadan ban yi
tunaninsa ba a cikin kwakwalwata
koda jin wannan batu sai sarki ya rungumo
darusi a jikinsa ya bushe da dariya yace
wannan gaskiya ne to amma akwai wani abu
guda danake so na gaya maka lallai kayi
tsantsan da duk masoyanka da makiyanka
domin a ko yaushe komai na iya sauyawa
sa adda jarumi darusi yaji wannan batu sai
hankalinsa ya dugunzuma yai sauri ya janye
jikinsa daga jikin na sarki ya dubeshi a firgice yace
ya shugabana me kake nufi da na kula da
masoyana da makiyana komai na iya sauyawa?
Sarki yayi murmushi sannan yace ka zamo mai hakurin
jin
amsar wannan tambaya a yanzu
ka nutsu ka yi amfani da basirarka da kwakwalwarka
domin ka gano komai saboda yin hakan shine sanin
karatun a cikin wannan duniya
wacce ta kasance babbar makaranta
koda gama fadin haka sai sarki yayi shiru bai kara cewa
uffan ba yaci
gaba da jan hannun darusi har izuwa cikin falon
turakarsa
da shigarsu cikin turakar
sai sukayi kicibis da gimbiya suzaina
a zaune bisa kan teburin cin abincin
ta caba ado na musamman ga mahaifiyarta zaune a kusa
da ita
fuskar suzaina na cike da annuri gami da
murmushi ta mike tsaye ta tarbi sarki tana
maiyi masa maraba da zuwa kuma ta ruko
hannun damansa suka taho tare izuwa kan
teburin abincin da isowarsu sai mahaifiyar
suzaina ta mike ta karbi sarki daga hannunsu tace
ku bani abina domin nan fada tace
bata kowa ba dajin haka sai suka bushe
da dariya gaba daya
jarumi darusi sai yar guntuwar dariya ya
sake ya hada idanu da suzaina sai ya hada rai
da yake suzaina ta san laifin da tayi masa ko
kadan bata damu da fishin da yake yi ba
kawai sai yaci gaba da sha aninta
batare da bata wani lokaci ba
mahaifiyar suzaina ta zubawa sarki da suzaina
abincin a kan faranti din dake gabansu
kafin a zubawa darusi sai suzaina tayi wuf
ta zuba masa nan dai kowa yayi bismilla a ka fara cin
abincin
inda jarumi darusi ya kasa daga kansa
ko sau daya ya dubi sarki da matarsa
saboda tsananin kunya kuma da kyar ma ya iya
yin loma biyu
koda sarki ya fahimci halin da jarumi darusi ke ciki
sai ya dubi matar tasa yace abincin nan
ya fita daga raina kayan
Marmari kawai nake bukata ki je ki kaimini
cikin turakata a yanzu
yana gama fadin haka sai ya mike tsaye ya nufi
cikin turakarsa cikin hanzari itama mahaifiyar
suzaina ta mike tsaye ta nufi wani dakin da ban
koda ganin haka sai shima jarumi darusi ya ajiye cokalin
da yake cin abinci ya mike tsaye da nufin ya fice daga
cikin falon amma sai suzaina tayi wuf
ta mike da sauri tasha gabansa kamar zata rungume
shi domin ta kusance shi ainun har suna iya jin
numfashin juna
....
.
ME ZAI FARU MU HADU A CIKIN LITTAFI NA TAKWAS (8)
DONJIN CIGABAN WANNAN KASAITACCEN LABARI
TASKAR AJALI
Littafi na Takwas 8
Na Abdulaziz Sani M Gini
Complet
Ebook creat by Shuraih Usman
Ebook publish by www.hausaebooks.cf
Ebook din nan yazo maku ne daga shafin www.hausaebooks.cf
Kuna ziyartar shafinmu don samun sababbin littatafai
Ga duk wanda ke bukatar ebooks nashi ya samu shiga cikin wepsite namu sai ya turo mana da littafin ta Email namu hausaebooks@gmail.com
CIKIN RAZANA DARUSI yaja da baya amma sai ta matse
shi a
jikin bango ta dubeshi tace' wallahi idan ka sake yunkurin
guduwa zan rungumeka
na kankame jikinnka
koda jin wannan batu sai ya tsaya yace don Allah kiyi
hakuri karkiyi min haka wai shin ke bakya jin kunya ne
sarki ko ummanki ta leko ta ganmu a haka?
Suzaina ta kyalkyale da dariya tace menene don an
ganmu
a rungume da juna waye bai san cewa ni dakai
masoya bane na kwarai iyayen na sun yar da da imaninka
da kuma tsoron Allan ka sun san cewa
bazakayi wani mugun abu ba a gareni wanda ya sabawa
shari'a
darusi ya murtuke fuska yace amma dai ni kin sani cewa
haramun ne mu hada jiki ni dake tunda ke ba
muharramata bace
suzaina ta sake yin dariya tace to mun hada jikinne
yanzu harda zaka fara yi min wa azi idan kana son
na matsa daga kusa dakai saika furta da bakinka
kace ka yafe mini laifin da nayi dazu a filin gasa
koda jin wannan batu sai darusi ya sake hada rai yace
ai ba a wajena zaki nemi gafara ba face a wajan Allah
saboda
shine ya hana mana nuna tsiraici saboda me kike
sanya sutura data baiyana dukkan surar jikinki?
Koda jin wannan tambaya sai suzaina ta sunkuyar da
kanta
cikin alamun takaici tace
tabbas na san na aikata zunubi kuma tun a sannan nake
ta yin istigfari amma nayi hakane domin na
karya zuciyar sarila da yar uwarta domin su gane
cewa nafi su komai kuma nayi musu nisan da ba zasu iya
kamoni ba tunda Allah ya yi mini baiwar
da basu da irinta
Wannan shine bukatar ka kamar yadda na sami
labari daga bakin abokin tafiyarka mujahid
asirrance tun kafin ayi wannan gasa burina shine
kowa ce irin bukata taka ta biya
lokacin da gimbiya suzaina tazo nan a jawabinta sai
murmushi ya subucewa jarumi darusi yace
to shi kenan na gode amma daga yau kada ki
sake aikata duk abinda kika san cewa Allah ya hana
duk da dai nasan akwai dokokin Allah da yawa
wadanda baki sani ba amma dai aikin san wadansu
kafin jarumi darusi ya gama fadin abin dake bakinsa
tuni gimbiya suzaina ta sumbaci kumatunsa
ta juya cikin sauri ta ruga izuwa cikin gida tana mai
cewa yau zanyi barci mafi dadi a dukkan kwanakin
rayuwata na duniya
caraf sai taji darusi ya kira sunanta take ta tsaya
cak amma sai taki yarda ta juyo ta fuskanceshi
saboda a zaton ta wani laifi ta aikata yanzu
kawai saiji tayi darusi yace gobe da safe idan
Allah ya kaimu mun hadu a filin gasa kada ki ragwanta
mini
ko kadan domin nima ba zan ragwanta miki ba
ko kadan duk damar da kika samu kada kiyi wasa
da ita domin so nake muyi gasa ta tsakanin da Allah
domin
na karbi wannan kambu daga hannunki ki nemi
taimakon Allah nima shi zan nema duk mai sa a
da rabo sai ya samu koda jarumi darusi yazo nan
a zancensa sai gimbiya suzaina ta kamu da tsananin
mamaki cikin kaduwa ta juya da sauri domin ta
tambayeshi dalilin wannan jajircewa da
yake son duk su biyun suyi sai kawai taga ya yi wuf ya
fice daga cikin falon yabi ta wata kofar wacce zata
kaishi can hanyar da zata kaishi inda masaukinsa yake
Al amin Ahmed guyson nake cewa.
Nan take jikin gimbiya suzaina yayi sanyi taji
kamar ta buya a wani wurin inda ba za a ganta ba
saboda kada ta halacci wannan gasa ta gobe amma
data tuna cewa rashin zuwanta gasar zai lalata tarihin
gasar ma gaba daya sai hankalinta ya dugunzuma ainun
fiye da ko yaushe
haka dai suzaina ta kama tafiya a cikin gidan sarautar ba
tare da
sanin inda ta dosa ba saboda damuwa gami da tunanin
zuci
Al amarin da ya janyo ta nufi bangaren
masaukin su jaruma sarila kenan ba tare da ta ankara ba
sai dai wannan lokaci sarila na zaune a kofar dakinsu
daga ita sai wani mayafi daurin kirji kuma ta juya
baya ne tana tsefe gashin kanta tana tasheshi da mataji
kawai sai suzaina ta bugi kujerar da sarila take zaune a kai
bata sani ba
mayafin dake jikin sarila ya cire ya fadi can gefe
daya tayi tsirara kuma gashi a lokacin kuyangin gidan
sarautar na zaune a wajan cikin tsananin dimauta
suzaina ta mike zumbur ta ruga inda mayafin sarila ya
fadi ta dauko shi ta sake
rugowa da gudu zuwa gareta da nufin ta rufe mata
jikinta kawai sai sarila ta fisge mayafin ta yi jifa
dashi sannan ta dubi suzaina a fusace cikin
tsananin kiyayya tace meye nufinki ki suturce jikina
alhalin kinyi min tsirara
a gaban bayi domin ki tozartani
koda jin wannan batu
sai suzaina ta ce ko kadan banyi niyar tozartaki ba
tsautsayine yasa nazo na doki wannan kujera saboda
bana cikin hayyacina
sakamakon halin da na shiga na tsananin tunani
koda jin wannan batu sai sarila ta bushe da dariya
har izuwa wani lokaci
bata rufe bakinta ba kuma babu alamar tanajin
kunyar tsiraicin data yi kawai sai sarila ta murtuke
fuskarta ta sake duban suzaina a cikin alamun
kiyayya mara misaltuwa a karo na biyu tace na rantse da
girman
shekaruna
sainayi ramuwar gaiya a kanki
lallai sainayi miki tunbur
a gaban dimbin mazajen garin nan domin na
kunkatar da mutuncinki da darajarki
koda jin haka sai suzaina tayi hailala tace
da izinin Ubangijin musulunci ba zaki samu wannan
dama ba koda kuwa
a cikin daji ne
Ba wai a cikin gari ba gaban al umma
sarila ta yi murmushi na mugunta tace kada ki.manta
cewa akwai
doguwar tafiya a gabanmu tunda tare
dake zamu tafi izuwa kogon TASKAR AJALI zan ga yadda
zaki iya tsallake dukkan sharrina
A dai dai wannan lokacine yazirina ta fito
daga cikin turakarta su itama tana taje gashin kanta
batare da tasan abinda ke faruwaba
koda ta hango sarila a tsaye tumbur a gaban suzaina
suna ta sa insa sai
ta ruga da gudu ta lullube jikinta ta shiga rarrashinta
tana bata baki haka dai ta janyeta da kyar suka shige
cikin turakarsu
wannan abu daya faru a tsakanin suzaina da sarila
sai daya jefa suzaina cikin tsananin damuwa da tashin
hankali
har saida tayi kuka kuma har dare ya yi nisa batayi
barciba koda
taga haka sai ta mike tsaye taje tayi alwala
sannan ta zotayi nafila raka a biyu ta shiga
rokon Allah tana mai cewa ya ubangijin komai da kowa
ka shiga tsakanin na gari da mugu ka sani
cewa bada gaiya nayiwa sarila wannan abu ba a bisa
tsautsayine amma gashi
tana son ta dauki mugun mataki a kaina ya Allah
ya ubanginin sammai da kassai ka kare ni daga
dukkan sharrinta
Aikuwa gimbiya suzaina na cikin yin wannan
Addu a ne tafara yin gyangyadi daga zaune
daga can kuma saita bingire ta kama barci batare
da tasaniba
suzaina bata farka daga barcin da takeyi ba har saida
akayi kiran sallar assalatu
saida gari ya waye sosai sannan jama a suka

Please Login or Register in order to submit comment