Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jakar guzurinta ta fiddo
wannan Allon Katako sannan ta fiddo jemammiyar
fatar ta ajiye akan tebur ta jonasu tare sai ga
Taswirar ta hadu saura kaso daya babu.Yazirina
tayi
ajiyar zuciya ta dubi Mujahid yace yanzu saura kaso daya
na wannan taswirar ya rage na hada da
wadannan biyun sannan na gano hanyar da zanbi
takai ni Taskar Ajali shin ko kasan a ina Taswira ta
ukun take?Mujahid ya gyada kai yace ta yaya za'ayi
na sami alhalin ta biyun ma sai yanzu nasan cewa
tana wajenki,abinda na sani kawai shine mai gidana
Boka Kaisu Bin Alkama ya turo ni gareki domin na
sato masa wannan jemammiyar fata.Inda ya san
cewa kina tare da wannan Allon Katako ma ai saiya
umarceni dana hado dashi.Lokacin da Mujahid yazo
nan a jawabinsa sai Yazirina ta bushe da dariya sannan ta
nutsu tace ai shi wannan Allon Katako
babu wani mahaluki dayasan cewa yana tare dani
sai
kai a yanzu sai kuma yar uwata Sarila zata zo tayi
farauta ta,inason ka saurara da kyau kaji
tambayoyin da zanyi maka yanzu kamar yadda na gaya
maka
tun a farkon haduwarmu cewa inada tambayoyi a
gareka.Kasani cewa albarkacin wadannan
tambayoyi
ne wadanda bansan amsarsu yasa na jaka a jikina
muka kasance tare har yanzu in ba don haka ba na tsani
yin kusanci da 'da namiji.Koda kuwa wanda
yayi sanadiyyar zuwana wannan duniyar ne,ina
zaune tare dakai ne bisa larura amma duk da haka
bazan yarda mu kwana a wuri daya ba kuma ko a
mafarki kada ka kuskura kabar hannunka ko
jikinka su rabi nawa.Idan hakan ta faru zaka gane
kurenka,kada kayi kokarin lekowa wannan falo a
lokacin danayi barci idan na fahimci hakan zaka
sha
wahala.Tambaya ta farko itace a ina fadar
maigidanka Boka Kaisu take?Nayi iya kokarina akan
na gano hakan na kasa,Tambaya ta biyu itace shin
ka taba ganin wani farin kambu a hannun Boka
Kaisu?Tambaya ta uku wacce itace ta karshe itace
shin zaka iya sato mini wannan farin kambu dake
hannun Boka Kaisu?Abinda nake nufi shine inason dara
taci gida,ka dade kana yiwa sauran bokaye
sata
da manyan sarakuna da manyan attajirai,wannan
karon maigidan naka nakeson ka yiwa sata.Kada
ka
kuskura kayi mini karya a cikin amsoshin da zaka bani
domin dole ne na gano karyar taka kuma idan
haka ta faru saika gwammace mutuwa da
rayuwarka.Lokacin da Jaruma Yazirina tazo nan a
cikin zancenta sai hankalin Mujahid ya dugunzuma
ainun fiye da koyaushe ya rasa abinda ke masa
dadi a duniya don haka saida ya shafe yan dakiku yana
tunani har gumi ya tsatstsafo daga cikin kansa
sannan ya dago kai ya dubi Yazirina yace,Fadar mai
gidana Boka Kaisu tana can cikin wani daji da ake
kira Darul Kinsasa a cikin yankin Birnin Kisra fiye da
shekaru talatin baya fatake suka hakura da ratsawa
ta cikin wannan daji,babu mai iya shigarsa face
Boka
Kaisu da wadanda ya lamincewa wato irinmu da
muka kasance manyan hadimansa,dangane da
tambayarki ta biyu,tabbas naga wani farin kambu a
damtsen hannun hagu na Boka Kaisu kuma wani
lokacin ma na kanga ya ciro kambun daga
hannunsa
ya kura masa idanu.A kan tambayarki ta uku kuwa
a
gaskiya bazan iya sato miki wannan kambu ba saboda
nasan irin tsananin sihirin da tsaron Boka
Kaisu yafi gaban ace wani barawo ya shiga har
cikin
fadarsa ya sami nasarar yi masa sata.Koda jin
wannan batu sai Yazirina ta bushe da dariyar farin
ciki sannan ta dubi Mujahid tace kai samari babu wani
abu wanda bazai yiyuwa ba a wannan duniya
face wanda ba'a jarraba yinsa ba.Lallai zaka rakani
izuwa fadar boka Kaisu tunda ba zaka iya yi masa
sata ba,lallai ina bukatar wannan kambu na
hannunsa domin shine abu na farko dazai iya
tserar dani daga sharrin Sarila.Sa'adda Jaruma Yazirina
taji wannan tambaya sai tayi ajiyar zuciya tace idan
har wannan kambu na hannuna da zarar Sarila ta
dira a cikin wannan duniya zai sauya kala ya koma
ja,kuma ko barci nakeyi saiya tasheni sannan zai
sanar dani a inda take da kuma tazarar dake tsakanina da
ita,abu na biyu da zai iya kareni daga
sharrin Sarila ba komai bane face wani bakon
saurayi wanda ya kasance dan baiwa mai tsananin
sa'a da rabi bisa duk abinda tasa a gabansa shidai
wannan saurayi bashi da KARFIN DAMTSE ko na
sihirin tsafi kuma ko takobi bai iya rukewa ba.Ni kuwa
yanzu babban abin fargabata shine bansan a
inda zanga wannan saurayi ba har na iya shaida shi
kuma bansan lokacin da Sarila zata baiyana ba da
kuma inda zata baiyana.Babu mamaki ma ta
baiyana
a inda nake ban sani ba ta shammaceni ta kashe ni ta
rabani da wadannan taswirori guda biyu.Lokacin
da Yazirina tazo nan a jawabinta sai Mujahid yaji
tsigar jikinsa ta tashi kuma yaji ya tsargu a cikin
zuciyarsa,ba komai ne yasa yaji ya tsargu ba face
yasan cewa shima ai bashida karfin sihiri kona
damtse sannan kuma yana da tsananin sa'a da da rabo
bisa duk abinda yasa a gabansa.Anya kuwa
bani bane wannan saurayi wanda Yazirina take
nema?A wata zuciyar kuma sai tace da Mujahid kai
dai wawa ne ta yaya zaka kasance kaine saurayin
da
taje nema alhalin tuni ta sanka,duniya ma ta sanka,kaine
mashahurin barawon daya addabi
bokaye da sarakai da kuma manyan attajirai.Mujah
id
na cikin yin wannan tunani ne Yazirina ta katse shi
tace mekake tunani?Cikin rawar murya yace babu
komai,kawai ina tunanin cewa kin jefa ni cikin TSAKA MAI
WUYA ne domin tsakanin keda
maigidana Boka Kaisu bansan wanda ya kamata na
butulcewa ba domin na tsira da rayuwata.Koda jin
wannan batu sai Yazirina ta kyakyale da dariya har
da fadowa kasa daga kan kujerar da take
zaune.Daga can kuma ™Abubakar Haleefah Physicist™
saita nutsu ta dubeshi tace kana burgeni saboda
halayenka guda biyu,na farko shine tsananin
tsoronka,ba biyu kuma shine son duniyarka.Koda
jin
haka sai Mujahid yayi murmushi yace ai komai son
duniyata ban kama farcen kafarku ba dakeda
manyan sarakunan nan hudu da kuma manyan
bokaye irin su Miagida na Boka Kaisu tunda kun
sallama rayuwarku domin kuje inda ba'a zuwa a
dawo a raye don kawai ku debo dukiyar da babu
irinta a cikin fadin wannan duniya.Yazirina tayi murmushi
tace aini dama na cancanta da debo
wannan dukiya tunda ta mahaifina ce.Koda jin
haka
sai Muhajid ya zaro idanu cikin alamun matukar
mamaki yace dama ke yar boka Salmara ce?Tabbas
na sami labarinki a wajen Boka Kaisu amma bai taba bani
labarin yar uwarki ba Sarila.Hankalinsa
gaba daya a kanki yake ba'a kan Sarila ba alhalin ta
fiki hadari.Koda jin wannan batu sai Yazirina tayi
murmushi tace ba komai bane yasa Boka Kaisu
baya
tsoron Sarila saidon yana da wannan kambun sihirin
a tare dashi,kafin ta cimmasa yasan a inda take
kuma yasan inda zai gudu ya buya shi yasa nima
nakeson na raba shi da kambun.Na yanke
shawarar
nayi kwana bakwai ne anan birnin Yamein saboda jikina
ya bani cewar nan ne birni Na farko Inda
Sarila
zata fara baiyana saboda inda Mahaifiyata ta fara
zama kenan a farkon yawon duniyarta kuma a
nanne
ta fara haduwa da mahaifina wato Boka Salmara.Lallai
inason nayi FITO na FITO nida Sarila
domin naga iyakar KARFIN DAMTSE nata da iya
yakin nata wanda ake bani tsaro dashi.Gama fadin
hakan keda wuya sai sukaji an kwankwasa musu
kofar dakin.A firgice Mujahid ya mike tsaye zumbur
ya ruga izuwa bayan Yazirina yana kokarin buya,Yazirina
tayi dariya tace to farar kura jeka ka
bude kofar ba hari aka kawo mana ba.Cikin dari
dari
Mujahid yaje ya bude kofar kawai sai yaga ashe
daya
daga cikin matan banzan ne na gidan dauke da farantin
abinci,karuwar ta dubi Mujahid cikin
murmushi da kallo irin na halikata da kwarkwasa
ta
mika masa abincin har ta juya zata tafi sai Yazirina
ta bude baki tace dawo ki shigo nan.Cikin alamin
tsananin tsoro jikinta na tsuma karuwar ta shigo cikin
dakin ta zube kasa agaban Yazirina,faruwar
hakan keda wuya sai Yazirina ta yaye mayafin data
lullube fuskarta da jikinta ta dubeshi tace meye
sunanki?Ba tare data dago kanta ba tace suna na
Siyama.Yazirina tace inason ki bude wannan abinci
kici kuma ki zauna a nan tare damu har tsawon sa'a
guda.Koda jin wannan batu sai jikin Siyama ya
kama
karkarwa sosai tamkar an tsomata a cikin ruwan
kankara,kuma sai takai hannun ta izuwa kan
kwanunkan abincin amma sai ta kasa bude
kwanukan.Koda ganin haka sai Yazirina tayi
murmushi tace tashi kiyi tafiyarki amma ki saki
jikinki kada ki kuskura ki gayawa saurayinki
abinda
ya faru yanzu tsakanina dake.Koda jin haka sai
farin ciki ya lullube Siyama ta kama godiya ta mike tsaye
da sauri ta fice daga cikin dakin tana fita sai Yazirina
ta dubi Mujahid tace saurayinta ne ya bata guba ta
zuba mana a cikin abincinmu kuma ba wani bane
saurayin nata ba face wannan katon dana fara
karyawa kuma dan leken asiri ne na shugaban dakarun
sumamen da suka kawo mana hari na
farko.Yana da kyau musan kowane uban gidan
nasa
tunda ba sarkin garin nan bane,shima sarkin
nemana yake ruwa a jallo.Tunda naga ya aiko
dakarunsa domin su kamani,abinda nakeso dakai shine
kaje ka gayawa Andalu na janye dokar dana
kafa ta shige da fice a cikin gidan,lallai idan dare ya
raba a bude kofar gidan a cigaba da harka kamar
yadda aka saba.Koda jin haka sai tsoro ya kama
Mujahid yace haba ya shugabata in kikayi haka ai
tamkar kin tona asirin inda muke ne duk masu farautarki
zasu iya riskarki a koyashe.Yazirina tace
sau tari zama a kusa inda ba'a zatonka yafi sirri
akan ka tafi nesa,sai kayi ganganci gami da saida
rai
sannan ka kan tsallake hadari,ka kwantar da
hankalinka babu abinda zai samemu domin nasan abinda
baka sani ba.Koda jin wannan batu sai
hankalin Mujahid ya dan kwanta ba tare da wata
fargaba ba sai ya juya ya sauko kasan benen yaje
ya
isar da sakon Yazirina izuwa ga Andalu kuma a
gaban mutane ya fadi sakon,Al'amarin daya baiwa kowa
mamaki kenan.Lokacin da Mujahid ya koma
sama benen saiya iske Yazirina ta sauko daga kan
kujerar ta kishingida a kasa ga jakar guzurinta
rataye a kafadunta kuma ta lumshe idanu kamar
barci takeyi.Koda ganin haka sai Mujahid ya tura
kofar falon ya rufeta ruf yasa sakata da kuba sannan
ya wuce kai tsaye izuwa cikin dakin data umarce
shi
daya shiga ya kwana a ciki.Yana shiga ya rufo
kofar
ya fada kan gado ya haye faruwar hakan keda wuya
kuwa sai barci ya saceshi nan da nan.Can sa'adda
dare ya raba sai kawai akaji wata irin iska mai karfi
ta soma kadawa iskace mai ban tsoro irin wadda
ba'a saba jinta ba domin tana dauke da wani irin
sauti mai kama da tsatstsagewar duwatsu,daga can kuma
sai sararin samaniya ta sauya launi tamakr
wata damina ne alhalin ana cikin tsakiyar
bazara.Kawai sai akaji an kwada wata irin tsawa
mai
tsananin karfi data firgita komai da kowa gami da
walkiya mai ban tsoro,duk jama'ar dake yin barci saida
suka farka a birnin na Yamein gaba
dayansu.Tsuntsaye da dabbobin dake cikin garin
da
daji suka firgice suka kama guje guje da iface iface
suna neman maboya,mutane kuwa saboda
dimaucewa basu san sa'adda suka kama shigewa cikin
karkashin gado ba da cikin rijiyoyin gidajensu
ba wasu ma suna hallaka kansu a banza.Kwatsam
sai akaji wani abu ya fara yowa kasa jif wanda
nauyinsa ya haddasa girgizar kasa a birnin gaba
daya.Karar tsawar da akayi bata sa Yazirina ta farka
daga barci ba amma dirar wannan abu sai yasa ta farka a
firgice,jakar guzurinta
™Abubakar Haleefah Physicist™
ta fara dafewa ta tabbatar da cewa tana tare da
ita,cikin hanzari ta mike tsaye ta zare takobinta ta
ruga izuwa kofar dakin da Mujahid ke kwance ta
doki kofar da kafarta.Take kofar ta balle ta fadi kasa
Mujahid ya mike zaune zumbur a dimauce ya
dubeta yace shin kema kinji muguwar tsawar da
aka
tafka kuwa yanzu?Maimakon Yazirina tace dashi
wani abu sai ta cakumi rigarsa tajashi izuwa falon sannan
ta dubeshi tace wannan tsawa da kaji ba
itace abar tsoro ba abinda ya diro kasa daga sama
ya haddasa girgizar kasa shine abin tsoron.Naji a
jikina cewa Sarila ce ta biyana zo muje mu gani da
idanunmu ko itace din.Koda jin haka sai tsoro ya
baibaye Mujahid ya dubi Yazirina yace kiyi mini rai nidai
ki barni na nemi wajen buya,koda jin haka sai
Yazirina ta dakawa Mujahid tsawa tace baka da
hankali,idan ni da kai muka buya bamu fuskanci
Sarila ba gaba dayan mutanen dake cikin gidan
nan
sai sun mutu.Dole ne muje mu tareta domin mu kare
rayukan miliyoyin jama'ar garin nan da
dukiyoyinsu,cikin mamaki Mujahid ya dubi Yazirina
yace yaya ni da ban kasance Jarumi ba zaki ce na
biki mu tari Sarila?Yazirina tace nasan cewa kai ba
jarumi bane amma ai kana da sa'a da rabo kuma
kai da bakinka ka fada mini hakan,tana gama fadin
hakan sai ta kama hannun Mujahid a karo na farko
taja shi suka fice daga cikin dakin gaba daya suka
fara kokarin saukowa kasa daga kan matattakar
benen.Ashe adaidai kofar wannan gida ne wannan
abu mai nauyi ya fado kasa kuma ba komai ne ya fado
daga saman ba face JARUMA SARILA.Inda ta
fado din saida kasar wajen ta rufta tayi rami tamkar
wani dutsen mai nauyi ya fado wajen.Sarila na
sanye
da jar riga da wando na miski matsatstsu wanda
suka bayyana kyakkyawar surar jikinta,takalman kafarta
ma dogaye ne na fata masu madauri a
kuibin
cinyoyinta dama da hagu wadana manyan Adduna
ne guda biyu a cikin kufe.Sarila ta kasance
doguwar
mace mai kyawun surar jiki da kyawun fuska a bar
kwatance amma kuma wannan kyawu nata kyan
dan
maciji ne domin inda ansan irin tsagwaron rashin
imaninta da irin zaluncinta ba za'a sami namiji dazai
kaunace ba.Lokacin da Sarila ta diro kasa daga
sararin samaniya kafafunta suka bugi kasa wajen ya
loba yayi rami kura ta turnuke wajen saita mike
tsaye ta nufi cikin gidan yan bariki,dama an bar
kofar
a bude kawai sai ta kunna kai izuwa cikin gidan.A
wannan lokaci gaba dayan mazajen gidan sun firfito
sun zazzauna a falon duk da cewa akwai sabuwar
karaya a jikin kowannensu suna ta shaye
shayensu
na giya da busa sigari,yan caca ma na sha'aninsu
tamkar Yazirina batazo ta hargitsa gidan ba a yau.Dama a
najin wannan tsawa da kuma karar
durowar Sarila sai kowa ya firta ainun maza da
mata
suka yunkura da nufin su leke waje suga abinda ya
fadi kasa sai ga Sarila ta shigo tana wani murmushi
na mugunta.Koda ganinta sai maza suka fara yin
murmushi gami dayi mata kallon raini,nan take
wani
katon saurayi mai son matan tsiya ya durfafi Sarila
yakai hannu da nufin ya taba Kirjinta.Caraf ta rike
hannun nasa ta cincika kawai sai akaga hannun
gaba daya ya cisgo daga cikin kafadarsa,jini yayi
feshi,katon ya kurma uban ihu kuma ya sulale kasa
sumamme.Koda ganin abinda ya faru sai kowa ya
girgita ainun,mazan dake wajen ma basu san
sa'adda suka fara sakin fitsari ba a wando.Saida
Sarila ta shigo tsakiyar falon ta karewa kowa kallo
sannan ta bude baki tace ina yar uwata Yazirina take?Ku
hanzarta sanar dani ko yanzun nan
dukkaninku ku zama gawa.Kafin Sarila ta gama
rufe
bakinta sai kawai taji ance gani nan idan kinason ki
karbi abinda kikazo nema a saukake ki kyale kowa
ya fice daga cikin gidan nan.Yazirina ce ta fadi hakan a
lokacin da take saukowa kasa daga kan
matattakalar benen,Mujahid na take mata baya.
Toofah!!!Nima ganin Sarila ta baiyana da yadda ta
cisgewa wannan katon hannun farat daya da
kuma
haduwarta da Yazirina yasa na dan tsorata na tsaya
ananTake saukowa kasa daga saman matattakalar
benen.Mujahid na take mata baya.Nanfa Sarila ta
kurawa Yazirina idanu suka fara kallon kallo kowacce
na nazarin yar uwarta.Sarila na tayin murmushin
mugunta a lokacin ne gaba dayan mutanen dake
gidan suka fara sulalewa suna ficewa daga cikin
gidan.Saidai Sarila ta gama nazarin Yazirina sannan
hankalinta yakai izuwa kan Mujahid,tana hada idanu
dashi sai taji zuciyarta ta buga da karfi,al'amarin
dayai matukar bata mamaki kenan domin wannan ne
karo na farko data taba jin hakan ya faru a
tsakaninta da wani 'da namiji.Kawai sai tayi sauri ta
kau da kanta ga barin kallonsa ta dubi Yazirina tace
ina taswirar dake hannunki guda biyu?Ina mai
shawartarki daki gaggauta miko mini su in ba haka
ba kuwa zaki iya rasa rayuwarki gaba daya,idan
kuma kikayi yunkurin guduwa tofa ba zaki iya bace
mini ba kuma zaki janyo na baje wannan birnin gaba
daya na kawar da duk wani abu dake da rai a
cikinsa.Koda jin wannan batu sai Yazirina tayi
murmushi tace yake yar uwata kiyi sani cewa ni a
rayuwata bansan wani abu waishi TSORO ba don
haka yana da kyau ki gane cewa ko kadan bana
shakkar ki duk da nasan cewa kin fini karfin damtse
dana sihirin tsafi.Kema kin san cewa ba zata yiyu ba
na dauki wadannan taswirori da hannuna na danka
miki ba face na jarraba sa'a ta ta samun taswirar
dake jikinki.Don haka yanzu ga taswirori guda biyu a
cikin jakar guzurina daya taswirar kuma na sani
cewa mahaifina ya zanata a kan gadon bayanki tun
kina da shekara shida a duniya,ni dake mu gwabza
mu gani wanda zai sami nasarar hada taswirorin nan
guda biyu.Koda gama fadin hakan sai Yazirina ta
gyara tsayuwarta kuma ta bude hannunta mai rike da
takobi kuma ta kara daure jakar guzurinta tamau a
jikinta.Koda ganin haka sai Sarila tayi murmushi ta
zare addunanta guda biyu kuma ta murtuke
fuska,kamar hadin baki duk su biyun sai suka rugo
da gudu suka kacame da azababben yaki ya zamana
cewa suna kaiwa junansu sara da suka cikin
tsananin zafin nama da juriya da bajinta na gaban
kwatance da matukar al'ajabi domin suna yin
wannan yaki ne da wani irin gagarumin zafin nama
tamkar jikinsu bana JINI DA TSOKA bane,nan da nan
suka tashi hankalin falon gaba daya sai gashi
Mujahid ya dimauce yana ta guje guje da boye boye
don kada su lahantashi.A duk lokacin da Sarila ta
kawo wa Yazirina sara da suka ta goce to fa duk
abinda ta samu saita raba shi gida biyu ko kuma ta
huda shi.Nan da nan ta ragargaza kujeru da teburan
falon ta farfasa dukkanin tulunan giya da
tambuloli.Ashe tun ma kafin a fara wannan
gumurzun kofar wannan gidan ya cika ya batse da
mutane mafi akasarin mutanen da suka zo wannan
wuri mutanen gari ne wadanda suka firgita
sakamakon jin tsawa da karar fadowar Sarila daga
sararin samaniya,sunzo ne domin su ga newa
idanunsu amma akwai bakin bokaye da wakilan
manyan sarakai wadanda suka zo wajen a cikin
badda kama kawai jira suke suga wadda zata yi
nasara a wannan gumurzu da ake tsakanin YAZIRINA
da SARILA suk afka mata su rabata da wadannan
taswirorin guda uku.Rashin sani yafi dare duhu inda
jama'ar da suka taru a wannan wuri suna leken
gumurzun da akeyi sun san abinda zai biyo baya da
basu kawo kansu wannan wuri ba.Koda aka shafe
kusan rabin sa'a na wannan bakin artabun ba tare
da dayansu ya sami nasarar koda lakutar jikin daya
ba sai Jaruma Sarila ta fusata ainun ta fara amfani
da karfin sihirin tsafi tayi nuni da hannunta izuwa
kan Yazirna take wata irin iska mai karfi ta taso ta
daga Yazirina sama ta makata a jikin garu.Take kan
Yazirina ya fashe jini ya zubo ta fado kasa a
galabaice,Sarila ta sake daga hannunta da nufin ta
daga Yazirina sama a karo na biyu,koda ganin
hakan zata faru sai Mujahid ya fito daga inda yake
boye ya dako tsalle ya dira a gaban Sarila ya dubeta
ya daka mata tsawa yace,kada ki kuskura ki kashe ta
domin ta fiki amfani a wajen al'umma.Koda jin
wannan batu sai mamaki ya kama Sarila har dariya
ta subuce mata ta dubi Mujahid tace kai kuwa meye
takamarka har da zaka sha gabana ka daka mini
tsawa haka?Shin baka ga yadda kowa ke tsorona
bane ko kuwa ka gaji da rayuwar duniya ne kanaso
ka tafi BARZAHU?Mujahid ya gyada kai yace yake
Sarila kiyi sani cewa ni matsoraci ne lamba
daya,amma a duk sa'adda naga za'ayi zalunci sai
naji zuciyata ta kekashe ga barin tsoron kowane irin
mahaluki walau mutum ko aljan komai girmansa da
karfinsa.Ke kina so ki mallaki wannan dukiya ne
domin kiyi mulkin zalunci a doron kasa ki wahalar
da talakawa kuma kiyi abinda ranki yake so,ni kuwa
burina shine na yi yaki da zalunci na shimfida adalci
tunda har ina kan tafarkin gaskiya nayi imani cewa
zan iya taimakon duk mai irin halina da
zuciyata.Koda jin wannan batu sai Sarila ta fusata
ainun zuciyarta ta kama tafarfsa kamar zata kone
kawai sai ta daga Addarta sama da nufin ta sare kan
Mujahid amma sai ta kasa,kawai sai ta cakumoshi
da hannu daya tayi wurgi dashi izuwa can bayanta
tamkar tayi cilli da sillan kara.Mujahid yaje ya gwaru
da bango ya fadi kasa,kafin Sarila ta kaiwa Yazirina
wani harin tuni Yazirina ta daka tsalle sama ta doki
kirjin Sarila da dukkan karfinta da kafafunta
biyu.Sarila tayi baya taga-taga kamar zata fadi kasa
amma saita tsaya kyam,al'amarin dayai matukar
razana Yazirina kenan domin komai girman kato
idan tayi masa irin wannan duka sai yayi sama ya
fado kasa ya baje amma gashi Sarila ta shanye
shi,ita kuwa Sarila mamakin daya kamata shine
Yazirina ce kadai ta taba yi mata dukan da yasa ta
motsa har taji tana neman faduwa kasa.Cikin
tsananin fishi Sarila ta dako tsalle sama
™Abubakar Haleefah Physicist™
daga inda take ta kawowa Yazirina wawan naushi a
kirji,cikin bakin zafin nama Yazirina ta kaucewa
naushin ta murgina a kasa can baya.Take hannun
Sarila ya naushi kasan falon ai kuwa sai wajen ya
burma hannunta ya lume a cikin kasa kawai sai
akaga ta zaro hannun nata ko kurjewa batayi ba,ta
sake rugowa izuwa kan Yazirina taci gaba dakai
mata mugayen naushi da bugu da hannu da kafa,in
badon Yazirina tana da bakin zafin nama ba kuma
na kaucewa hare haren nata gami da karewa da
takobin hannunta da tuni Sarila ta burma sassan
jikinta.A wannan lokaci ne hankalin Yazirina ya
DUGUNZUMA ainun domin a sannan ta tabbatar da
cewa KARFIN DAMTSEN Sarila ya ninka nata sau
goma,sakamakon naushin ginin falon da Sarila keyi
sai gidan gaba daya ya kama rugujewa da kyar ma
Mujahid ya fice daga cikin gidan sai gashi gidan
gaba daya ya baje amma Sarila da Yazirina basu
daina gumurzu ba.Nanfa bala'i kuma ya fara shafar
yan kallo domin sauran gidajen dake wajen ma sai
suka kama rushewa suna fadowa kan jama'a suna
hallaka.Nanfa birnin gaba daya ya hargitse aka kama
guje guje da iface iface saida ya zamana cewa kowa
ya cika wandonsa da iska babu wanda ya rage a
wajen face manyan bokaye da tsirarun dakaru
wakilan manyan sarakunan hudu na duniya sai
kuma Mujahid.Ana cikin wannan BAKIN ARTABU ne
Sarila ta shammaci Yazirina ta sareta da takobi akan
kirjinta daga sama.Take gurin ya dare jini yayi
tsartuwa Yazirina ta kurma uban ihu sakamakon
tsananin zafin dataji a lokacin data tayi tsalle sama
da baya ta fado kan rusasshen gini a cikin matukat
galabaita.Kawai sai Sarila ta dako tsalle sama daga
inda take ta dira a gaban Yazirina ta na mai raba
kafafunta akanta ta dubeta cikin murmushin mugunta
a lokacin da jini ya cigaba da yoyo akan kirjin
Yazirina kuma tana gani dishi dishi.Sarila ta bushe
da dariyar murna bisa ganin nasarar data samu
sannan ta dubeta tace yanzu zan karasa kashe ki na
dauke wannan jakar guzuri taki tunda taswirorin
guda biyu na ciki.Koda gama fadin hakan sai Sarila
ta daga Addarta sama da nufin ta lumawa Yazirina a
ciki kawai sai akaga Mujahid yayi wuf ya janye
Yazirina ya goyata a bayansa ya falfala da
azababben gudu izuwa cikin gari aikuwa sai suka
kasa tsere shida Sarila sannan ragowar matsafa da
wakilan manyan sarakuna suka rufa musu baya.Bisa
mamaki sai Sarila taga Mujahid yana yin wani irin
gudu na ban al'ajabi wanda yafi gaban tunaninta
domin tazarar daya bata ba ta wasa bace duk da
cewa ta sami horon gudu mai tsananin amma duk
sai ya zamo na banza.Koda taga Mujahid na neman
bacewa sai ta kara karfin gudun nata da karfin sihirin
tsafi amma duk da haka sai ta kasa cimma
Mujahid,al'amarin dayai matukar daure mata kai
kenan kuma yayi matukar bata mamaki.Nan taje ta
fara wasu wasi a cikin ranta tace anya kuwa wannan
saurayi daya taimaki Yazirina ba shi bane bakon
jarumin da aka bani labari cewa zai hanani samun
nasara akan Yazirina?Me yasa a farkon haduwata
dashi naji zuciyata ta buga da karfi?Shin na kamu
da SON sa ne ko kuwa tausayinsa naji shi yasa na
kasa kashe shi?Akan wane dalili zanji tausayinsa
alhalin ban taba jin tausayin wani bil'adama ba?Haka
Sarila taci gaba da wannan tunani tana cigaba da
falfala masifaffen gudun ta na tsafi,duk inda ta gifta
sai kaga kamar tauraruwa mai wutsiya ce ta wuce
amma duk da haka a can nesa take hango Mujahid
goye da Yazirina a bayansa wacce tuni ta dade da
suma.Haka dai aka cigaba da wannan tseren gudun
har tsawon sa'a daya da rabi har ya zamana cewa
an fice daga cikin ainihin birnini Yamein an nausa
cikin daji.Koda Mijahid ya shiga cikin wata sarkakiya
mai tsawon gaske gami da hudu sai ya bacewa
Sarila ta nemeshi sama da kasa ta rasa,ba shiri ta
tsaya cak ta kama waige waige da dube dube a
daidai wannan lokacin ne bokaye da wakilan
sarakunan suka iso duhuwar da suka ga ta shiga sai
kowannensu yayi turjiya ya tsaya yana haki gami da
tsoron shiga cikin sarkakiya.Duk da cewa Sarila tayi
nisa a cikin sarkakiyar kuma tazarar dake tsakaninta
da wadannan bokaye da wakilan sarakunan su goma
sha hudu takai taku dari da ashirin tana iya jiyo
sautin hakinsu a cikin dodon kunnenta saboda karfin
sihirinta na tsafi.Nanfa Hankalinta ya rabu biyu ta
bazama neman inda su Mujahid suka buya kuma
tana tunanin ta koma da baya inda wadannan
bokaye suke ta hallakasu tunda suma abokan
gabarta ne suna farautar abinda take nema.Har daya
daga cikin bokayen da yunkura zai kunna kai izuwa
cikin wannan sarkakiya sai wani daga cikin ragowar
yan uwan nasa uku yace kada mu kuskura mubi su
Sarila cikin wannan sarkakiya domin babu mamaki
kafin mu isa inda suke tuni Sarila ta kashe Yazirina
da abokin tafiyarta,kunga kenan tana ganinmu zata
gama damu tunda ta san cewa abindake hannunta
muke bukata,kuzo mu watse daga nan domin mu
tsira da rayuwakanmu in yaso muyi bincike a cikin
hallarar tsafinmu muga abinda ya faru tsakanin
Sarila da Yazirina sannan musan hanyar da zamu bi
mu sace taswirori uku daga hannun Sarila.Koda jin
wannan shawara sai sauran bokayen da wakilan
sarakunan hudu suka amince nan take kuwa sukayi
amfani da karfin tsafi suka bace bat daga wajen
gaba dayansu.Lokacin da Sarila ta dubi gaba da
yamma,kudu da arewa a cikin wannan duhuwa bata
ga su Mujahid ba kuma bata jiyo sautin
numfashinsu ba sai ta fara neman sawun Mujahid
amma sai taga wayam ko akamr sawun bil'dama
babu a wajen da nesa dashi.Al'amarin dayai matukar
kara rikirkita mata kwakwalwa kenan ta tambayi
kanta tace wai shin wannan bakon saurayi wane irin
shu'umi ne shi haka,tabbas na fishi karfin sihirin
tsafi da karfin damtse da iya yaki amma yaya
™Abubakar Haleefah Physicist™
akayi ya tsere mini da karfin gudu kuma ya bace
mini da gani sai kace aljani,Koda gama fadin hakan
keda wuya sai Sarila tacigaba da falfala gudun tsiya
tana neman su Mujahid har ya zamana cewa ta
kusan kure karshen

Please Login or Register in order to submit comment