Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gyada kai cikin murmushi yace
tabbas
dani za ayi wannan tafiya saboda
wannan tafiya itace
babbar jahadi na yada addinin Allah a
wannan nahiya tamu
Idan har muka yi nasara a kan tsafi to
ko wacce kasa sai sun karbi musulunci
kaga kenan ko dani za ayi wannan
tafiyar jahadi
koda sarki yazo nan a jawabinsa sai
jarumi darusi yayi murmushi yace
hakika kayi gaskiya ya shugabana
kuma kayi tunani irin wanda ban taba
zatoba
gama fadin haka keda wuya sai sarki ya
dubi
sarkin yakinsa yace ka tura da dakaru
dubu dari suje su kewaye masaukin
wannan attajiri sannan kuma abaza
wadansu dakarun yan leken
asirinmu a binciko inda yake boye a
kamashi
sarkin yaki yace an gama ya shugabana
har sarkin yaki ya juya zai tafi domin
zartar da wannan umarnin sai aka
hango mujahid
ya taho garesu a guje mujahid ya
karaso
gaban sarki yana haki sannan ya risina
yace
ya shugabana ba wani bane wannan
bakon attajirin face SARKI DAMNASHI.
Koda jin wannan batu sai mamaki ya
kama kowa
mujahid yaci gaba da bayanin duk
abinda ya faru
a cikin turakarsu sarila sannan kuma ya
kara da cewa a yanzu haka sarki
Damnashi yasa sunansa a cikin
jaruman gasar da zasu tafi zuwa kogon
taskar ajali
dajin wannan batu sai aka sake cika da
mamaki
shi kuwa sarki sai yayi murmushi yace
ba komaine
ya kawo sarki damnashi birni na ba
face
abubuwan nan biyu abu na farko shine
domin ya dauki fansa akan jarumi
Darusi
abu na biya shine yanzu yana kan
bakansa na son mallakar
dukiyar da mahaifin yazirina ya bari a
cikin TASKAR AJALI
hm lallai Sarki damnashi ya cika mai
son duniya
A halin yanzu bashi da wani amfani mu
kama sarki Damnashi mu tsare a
kurkuku
kawai mu tafi tare da shi zuwa kogon
taskar ajali
koda jin wannan batu sai gimbiya
suzaina ta dubi
sarki cikin alamun tsoro tace haba ya
abbana saboda me
zamu sake jiki da wannan shaidanin
sarki harmuyi wannan tafiya tare dashi
alhalin kasan cewa zai iya
shammatarmu ya cutar da kowa?
Kada ki damu yake yata idan har kinyi
imani da
cewa mune akan gaskiya sukuma suna
kan bata to
Insha Allahu ba zasu taba samun
galaba a kanmu ba dajin haka sai jikin
suzaina
yayi sanyi tayi shirutana mai sunkui da
kanta kas
amma sai ta sake dago kai ta dubeshi
tace wane sakamao aka samu a cikin
binciken na gano wanda ya samini guba
acikin abincina?
Koda jin wannan tambaya sai sarki yayi
yar doguwar dariya sannan yace
mun gano cewa acikin ruwan inibin da
kika sha aka sanya gubar kuma babu
hannun
hadiminki a cikin wannan al amari mun
san kowanene ya yi wannan yunkurin
na
hallakaki amma bashi da wani amfani
kisan
kowanene
a yanzu sai dai nan gaba don ha ka
kimanta da wannan batu,
Yanzu na sallami kowa a je a fara
shirye shiryen tafiyarmu
izuwa kogon Taskar Ajali
koda gama fadin haka sai sarki ya juya
ya shige cikin gidan sarautar shima
jarumi Darusi
sai ya kama hannun mujahid suka juya
zasu nufi nasu dakin amma sai suzaina
ta sha gabansa tace ya za ayi da
wadannan masu yin barcin a kan doki?
Darusi ya gyada kai cikin murmushi
yace ''
Ai hodar barki aka shaka musu don
haka kin fini
sanin abinda yakamata ayi musu
koda gama fadin hakan sai jarumi
darusi
ya sake jan mujahid sukayi tafiyarsu
tafiyarsu keda wuya sai ga wadansu
kuyangi sunzo giftawa kawai sai
suzaina ta dubi
kuyangin tace dasu su dauke sarila da
yazirina daga kan dokin su kaisu can
turakarsu
nan take kuwa kuyangin suka cika
umarni
bayan an kai sara da yazirina turakar
gimbiya suzaina an shimfidesu a kan
gadonta sai da aka dora musu wani
magani a cikin bakinsu kuma suka ci
gaba da barci har izuwa tsawon sa a
uku
da rabi sannan suka farka
a firgice suka mike zaune zumbur
domin a zatonsu zasu tsinci kansune a
daure a gaban makiya amma sai suka
tsinci kansu a cikin kasaitaccen daki
bisa
luntsumemen gado
shidai wannan daki yasha ado da kayan
kawa iri iri
masu matukar ban sha awa nan dai
sarila da yazirina suka sauko daga kan
gadon
suka kama kalle kalle sama da kasan
dakin da jikin bango
kwatsam sai suka jiyo takun sawu an
nufo cikin dakin
a tare sarila da yazirina suka yunkura
domin su zare takubbansu
amma sai suka kasa sakamakon ganin
cewa ashe gimbiya suzaina ce ta
durfafo su fuskarta cike
da annuri kawai sata wuce ta tsakiyar
su ta karasa kan gadonta ta zauna gefe
kuma
ta dora kafarta guda kan dayar ta dubi
sarila tace
in ba don na ceci rayuwarku ba da tuni
yanzu kun
dade da zama gawa yake sarila shin
har yanzu kina na a kan bakanki nason
tozarta
mutuncina a gaban jama a domin
ramuwar ga tunkudekin da nayi bisa
tsautsayi?
Sa adda sarila taji wannan tambaya
saita bushe da dariya lokaci guda
kuma ta turbune fuskarta tace kina
zaton cewa saboda kin ceci rayuwata
shikenan
kin katse gabar dake tsakaninmu?
To bara kiji idan kina son na kawar da
batun fansana saidai kiyi abu biyu abu
na farko dolene ki hakura da batun
zuwa kogon Taskar Ajali
abu na biyu kuma dolene ki fansar da
soyayyarki a gareni
ma ana ki hakura da jarumi Darusi ki
bar minshi
saboda ahalin yanzu na kamu da
tsananin sonshi
fiye da komai a cikin wannan duniya
kafin sarila ta gama fufe bakinta tuni
gimbiya suzaina ta kyalkyale da dariya
sannan
itama ta hade fuska
tace ki daina tunanin cewa zaki iya
yaudarata ki cutar dani waya gaya miki
cewa ana iya fansar da so na gaskiya
dukiya ko mulki ko mai basa iya fansar
da soyayya ta gaskiya abinda zaisa na
iya bar miki darusi ba komai bane face
mutuwa
ina ji a jikina cewar kedai har abada ba
zaki taba son darusi bisa gaskiya ba
saboda kasancewarsa musulmi
nasan yadda kika tsani musulunci da
musulmai
kuma nasan yadda kike da matukar son
duniya akan abin duniya babu abinda
ba zakiyi ba
hatta yazirina ta dake tare dake so kike
ki yaudareta
ki rabata da dukiyar mahaifinta dake
cikin taskar ajali kuma ki hallakata
tsoronki da takeji ne ya hanata
karbar addinin na sani cewa kina
matukar son mujahid kamar yadda
shima yake sonki kuma
tuni zuciyarsa tayi imani da addinin
gaskiya don
haka babu sauran kwadayin abin duniya
a ransa
zai aureki ne bisa soyayyar gaskiya
donku zauna kyi rayuwa ta farin ciki da
kwanciyar hankali shin kina son ki
mallaki
masoyin nakine ko kuwa kina son kici
gaba da bin yar uwarki
mai mugun nufi a kanki a cikin
zuciyarta?
Hm Al amin Ahmed Guyson sunana.
Lokacin da gimbiya suzaina tazo nan a
wannan zance nata
sai hawaye ya zubowa yazirina ta juya
da baya daga inda sarila ke tsaye ta
dawo dai dai gun suzaina ta tsaya
sannan ta nuna sarila da dan yatsanta
tace
tabbas ke shaidaniyace kuma azzaluma
ki tuna irin miliyoyin rayukan da kika
kashe
a wannan duniya ke kanki baki san
iyakarsu
ba dai dai da rana daya baki taba jin
tausayi ko nadamar abinda kike
aikatawa ba
kullum burinki shine dukiya
da mulki daga yau na yanke duk wata
hulda a tsakaninmu dake na dawo
bangaren gimbiya suzaina
kuma da yanzu ba zan sake kwana a
daki tare dakeba
domin babu sauran yan uwanta
tsakaninmu
ni dake kowa tasa ta fishsheshi koda
yazirina tazo nan
a zancenta sai sarila ta kama yake
gami da murmushin mugunta kawai
saita
nuna yazirina da dan yatsa tace sai
kinyi nadamar nisantata
caraf sai suzaina ta tari numfashinta
tace
yazirina ba zatayi nadamar dawowa
bangaren gaskiya ba kece zakiyi babbar
nadama a lokacin da babu damar mu
karbi tubanki
kifice mini daga cikin turakata domin
idanuwa na sun gaji da ganin fuskar
azzaluma kuma kunnuwana sun gaji da
jin maganganunki
sarila ta bushe da dariya tace shi kenan
ni daku zanga wanda a karshe zai
zubar
da hawaye tana gama fadin haka saita
juya da sauri ta fice daga cikin
turakar ita kuwa yazirina saita fada kan
kirjin suzaina ta fashe da kuka a lokacin
da suka rungume juna
daga wannan rana taci gaba da kwana
a dakin gimbiya suzaina bayan ta karbi
Addinin musulunci shi ma mujahid take
ya musulunta a cikin yan ragowar
kwanakin da suka
rage na yin tafiya izuwa kogon taskar
ajali yazirina da mujahid suka tsinci
kansu
a cikin sabuwar rayuwa ta dinbin farin
ciki
saura kwana biyu a tafi kogon taskar
ajaline yazirina da mujahid suka bukaci
a daura musu aure.
Koda jin wannan batu sai ita ma
suzaina tace
sai dai a hada da auranta da jarumi
darusi
ai kuwa sai sarki yace sam ba zaiyi
wuba sai sarki yace
samba zaiyiwuba domin mujahid ba zai
sami sukunin gabatar da babban aikin
dake gabansa ba idan nauyin aure ya
hau kansa.
Nan fa suzaina ta firgice kuma ta
dimauce ta rinka kuka
da bakin ciki dare da rana har sai da
darusi ya rarrashe
ta dukansa ya tabbatar mata da cewa
ana dawowa daga kogon Taskar Ajali
za a daura nasu auran haka dai a kayi
bikin auren yazirina da mujahid cikin
murna aka gama
da ranar tafiya kogon taskar ajali tazo
sai jama a suka yi cincirindo a fada
sarki da darusi mujahid da Sarki
Damnashi
yazirina da sarila da gimbiya suzaina
na zaune bisa ingarman dawakai
kowannansu yayi gagarumar shigar
yaki
dakarun birnin kuwa su dubu dari uku
ne sukayi hawa saboda kwadayin
samun
shahada cikin wannan gagarumar tafiya
Ba tare da bata wani lokaci ba sarki ya
wuce gaba mukarrabansa na take
masa baya suka fice daga cikin birnin
gaba daya
sarki Damnashi da sarila a can karshen
baya sun jeru
kawai sai Damnashi ya dubi sarila yace
duk kece
kika wahalar damu saboda mugun
burinki
na son kanki ke kadai in
da kin hada kai dani da yanzu mu biyar
kacal zamuje
wannan wuri mu mallaki wannan dukiya
kafin sarila ta bude baki tace da shi
wani abu sai
kawai aka hango kura ta turnuke
sararin samaniya acan gaba
koda ganin hakan sai sarki ya bayar da
umarnin a tsaya nan take aka yi cirko
cirko sannu a hankali kurar ta rinka
lafawa kuma aka rinka jiyo sautin takun
dawakai barkatai marasa adadi
jim kadan kuma sai aka fara hango
runduunoni na kasashe da yawa dake
nahiyar kowacce kasa sarkin su da
kansa yake yi musu jagora
in da ace mutun na nan a wannan
lokaci yaga miliyoyin mahayan da suka
durfafo zato zaiyi
gaba dayan mutanan duniya ne ke tafe
saboda yawansu
su jarumi Darusi basu yi motsin komai
ba har wadannan rundunoni na
miliyoyin suka iso daf dasu
A sannan ne sarki da ya dubi mahaifin
suzaina yace yakai wannan sarki na
Arnan daji
wadanda suka karbi addinin musulunci
a yanzu kayi sani cewa
ina yin
magana neh da yawun gaba dayan
sarakunan dake wannan nahiya tamu
mun sami labarin cewa jarumi Darusi
zai iya kaimu kkogon Taskar Ajali ba
tare da taswirori ukun da mai kogon ya
kirkira da dukkaninmu mun sani cewa
duk sarkin da ya mallaki wannan dukiya
ta kogon TASKAR AJALI shine zai
mallaki duniya gaba dayanta
bisa wannan daliline muka dungumo
gaba dayanmu muka taho domin
a raba gardama mai rabo a cikinmu nan
duka sai ya samu
koda jin wannan batu sai sarki ya yi
murmushi
gami da gyaran murya sannan yace
kuyi sani cewa
ni yanzu banyi imani da duk abinda
kuka fada ba
saboda haka idan mukaje can za a
baiwa kowa damar sa ya shiga cikin
kogon ya dauko Dukiyar dake ciki da
karfin
damtsensa karfin sihirinsa da dabararsa
amma bisa sharadi guda
sharadin kuwa shine idan kowa ya kasa
jarumi
darusi zai shiga ya dakko dukiyar da
taimakon
ubangijin musulunci idan har haka ta
faru to dolene
kowane sarki ya karbi addinin
musulunci
idan kuma baku yarda da wannan
sharadi ba to yanzu take zamuyi yaki
Mu kashe junanmu in yaso kasar ta tafi
can kogon ta dauko dukiyar
sa adda gimbiya suzaina taji wannan
bayani sai hankalin kowa ya
dugunzuma
aka yi tsit tamkar mutuwa ta gifta
nanfa gaba dayan mutanan kimanin su
dari da sittin suka sauko daga kan
dawakansu suka zauna suna
tattaunawa
sai da aka shafesama da sa a uku ana
mahawara
da shawarwari sannan aka yanke
shawarar a tafi
gaba daya aje can din kowa ya jarraba
sa arsa
kaico hakika tsautsayi baya wuce
ranarsa
kuma idan masifa ta tunkaro to fa babu
abinda
zai tsaidata face Allah
tun da aka durfafi hanyar zuwa kogon
Taskar Ajali aka rinka haduwa
da masifu iri iri nan fa mutane da
dawakansu
suka rinka hallaka tamkar wata
annobace ta sauko daga sama
kafin a isa can kogon na taskar ajali ya
zamana cewa saura baifi runduna arba
in ba su kansu
su jarumi darusi da suke ta neman tsari
da taimakon
Alla saida suka sha bakar wahala
amma ko mutum
daya bai mutu ba daga cikinsu
sai dai akwai wadanda suka raunana
da yawa abinda
ya daurewa kowa kai shine SARKI
DAMNASHI da sarila ko kurjewar jiki
basuyi ba
amma kafin a isa bakin kogon taskar
Ajali
gaba dayan jama ar sarki Damnashi
sun mutu saura shi kadai shi kansa
yayi mamakin yadda ya iya haye
dukkanin masifun
A kofar kogonne aka sake baiwa
kowace runduna damar
jarraba sa arsu nan fa duk rundunar da
ta shiga cikin kogon sai aji
shiru tamkar maye yaci shirwa
domin ko duriyarsu ba za a jiba
anan ma dai saida runduna ashirin da
shida ta salwanta
ya saura runduna goma sha hudu kacal
wadannan
rundunan suka karaya sukace sun
yarda darusi
ya shiga indai ya fito a raye zasu karbi
musulunci
koda jin haka sai sarila da sarki
Damnashi sukayi caraf
sukace su basu yarda ba
sai dai suyi yaki da darusi idan ya kashe
su ya shiga idan kuma su suka kashe
shi su shiga
nan take aka basu wannan dama suka
afkawa darusi
su biyu aka ruguntsume da Azababben
yaki tabbas idan kaji makaho yace
ayi wasan jifa toya taka hoge
A shie a cikin wannan tafiya sarila ta
shammaci darusi tasa an zuba masa
wani sinadari
mai la anta idanu a cikin abincinsa
yaci bai sani ba ai kuwa ana fara
wannan gumurzu ne
darusi yaji idanunsa sun daina gani
gaba daya tamkar daman can shi
makaho ne koda jin
hakan sai ya shiga rokon Allah ya na
mai cewa
ya Allah indai saboda kai zanyi wannan
aiki to ka zamo jina da ganina
wohoho nan fa jama a suka sha
mamaki da abin al ajabi da basu taba
gani ba
domin Darusi na makaho ya rinka yin
gagarumar
jarumtaka yayi ta yakar sarila da Sarki
Damnashi har
ya sami nasarar sare daya hannun na
sarki Damnashi
ya durkushe kasa yana kwarara uban
ihu
ita kuma sarila wani wawan naushi yayi
mata a kirji tayi sama ta
soke gadon bayanta a jikin wata bishiya
nan take ta zama gawa ko shurawa
batayi ba
hm sarila an zama gawa sarauniyar
makircin duniya
sai muga ta mallakar wannan dukiyar ai
+
A wannan lokaci ne darusi ya shiga
cikin kogon
TASKAR AJALI a makancan ya dade a
ciki sannan ya
fito a raye cikin koshin lafiya take gaba
daya jama ar dake wajan suka karbi
Addinin musulunci
Lokacin da aka dawo birnin su gimbiya
suzaina sai aka iske bakaken Aljanun
da sarki Damnashi a mace
gaba dayansu mutanan gari kuwa babu
abinda ya samesu cikin tsananin farin
ciki aaka daura auran JARUMIN
DUNIYA SADAUKI UBAN SADAUKAN
DUNIYA WATO JARUMI DARUSI DANA
GIMBIYA SARAUNIYAR KYAU WATO
SUZAINA.
Aka shiga shagali daga wannan rana
aka sami
zaman lafiya da kwanciyar hankali a
nahiyar
gaba daya kuma addinin musulunci yaci
gaba da yaduwa har izuwa sauran
nahiyoyi.......................................
ALHAMDULILLAH !!!
Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya
nufemu da kammala wannan littafi na
TASKAR AJALI tun daga na 1 zuwa na 9
Ni guyson nake cewa
Ku kasance da shafin http://hausaebooks.cf Don samun wasu kayatattun littatafan Yaki
TASKAR AJALI
Littafi na Tara 9
Marubucin littafin
Abdulaziz Sani M gini
Ebook creat by Shuraih Usman
Ebook publish by www.hausaebooks.cf
Ebook din nan yazo maku ne daga shafin www.hausaebooks.cf
Kuna ziyartar shafinmu don samun sababbin littatafai
Ga duk wanda ke bukatar ebooks nashi ya samu shiga cikin wepsite namu sai ya turo mana da littafin ta Email namu hausaebooks@gmail.com

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment