Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

duka nice na
shayar dasu ina
kallonsu a matsayin 'ya'yana.Koda
gama fadin hakan
sai Basma ta kurma uban ihu
sannan ta fashe da
matsanancin kuka na bakin ciki,ita
kuwa tsohuwar
sai ta shiga rarrashinta tana mai
cewa babu yadda
zakiyi da kaddarar rayuwarki tunda
baki da ikon
sauyata.Haka dai tsohuwar
tacigaba da rarrashinta
har izuwa lokacin mai dan tsawo
sannan ta shawo
kanta ta daina kukan.Daga wannan
rana kuyangin
suka ci gaba da kula da Basma ya
zamana cewa
juna biyunta ya dada Girma har
watanni tara suka
cika,da tsakiyar dare nakuda ta zo
mata kuma a
cikin dakiku kadan ta haife
santaleliyar 'yarta.Da
kwanaki bakwai suka cika aka
radawa yarinyar suna
Yazirina,nan fa Basma da
kuyancinta suka cigaba da
renon Yazirina har takai shekaru
shida a duniya
kuma tun a sannan ne aka rinka
ganin abubuwan
al'ajabi a tare da Yazirina domin
tana iya sarrafa
komai da karfin sihirin tsafi domin
komai nauyin abu
data dauke shi da hannu sai ta
daga shi sama takai
shi inda takeso ta ajiye.Tana da
shekaru shida ne
akaga wadansu zakakuron aljanu
suna zuwa suna
bata horon yaki,tun a wannan
lokaci Basma ta sanar
da Yazirina komai dangane da
rayuwarta da kuma
gagarumin aikin dake gabanta nan
gaba idan ta cika
Budurwa.Koda Yazirina taji cewar
an sameta ne bata
hanyar aure ba sai bakin ciki ya
turnuketa yayi mata
kututu a cikin ranta domin saida ta
kwana ta yini
tana kuka baci basha.A sannan ne
taji ta tsani
Basma kuma ta tsani Boka
Salmara,kai saida ma tayi
yunkurin kashe kanta da kyar
aljanun gidan da
kuyangin dake kula da ita suka
rarrasheta ta hakura
amma duk da haka saida ta kwana
uku bata yiwa
Basma magana ba,kuma bata
zuwa,Basma na zaune
a cikin turakarta ta hada kai da
guiwa tana tunani da
kuka bisa ganin yadda yar cikinta
ta tsaneta,lokaci
guda sai kawai taji an turo kofar
dakin,koda Basma
ta dago kanta sai tafa ashe
Yazirina ce ta shigo
idanunta sunyi sharkaf da
hawaye,cikin sanyin jiki
Yazirina ta karaso gaban Basma ta
durkusa a
gabanta bisa kafafunta ta sunkui
da kanta kas
tace,yake ummina kiyi mini aikin
gafara domin nayi
babban kuskure dana nuna
kiyayyara a gareki tunda
bani da kamar ki ko inaso ko
banaso ban isa na
sauyawa tuwo suna ba.Koda jin
wannan baty sai
mamaki da farinciki suka lullube
Bsma domin bata
taba zaton cewa yarinya yar
shekara shida kamar
Yazirina zatayi irin wannan tunani
ba.Nan take
Basma ta rungume Yazirina suka
fashe da kukan
farin ciki tare.Daga wannan rana
Basma da Yazirina
suka cigaba da zama cikin farin
ciki har Yazirina ta
cika shekaru goma sha biyar a
duniya.A wannan
lokaci ne kyawun surar jikinta ya
baiyana sosai
kuma ya zamana cewa ta sami
horon yaki mai
tsanani yadda tana iya tarwatsa
gungun dakarun
yaki na aljanu ma.Wata rana da
safe sai Yazirina
taga gaba daya yanayin Basma ya
sauya,alamun
cewa hankalinta a tashe yake
domin ta kasa cin
abinci kuma idanunta sun kada
sunyi jawur alamar
cewa tasha kuka a boye.Koda
ganin haka sai
hankalin Yazirina ya dugunzuma
ainun ta dubi
Basma cikin alamun tsananin
damuwa tace yake
Ummina ina dalilin sauyin yanayi
haka a tare dake
alhalin an gaya mini cewa baki da
wata damuwa a
gidan nan.Sa'adda Basma taji
wannan tambaya saita
mike tsaye daga kan gadonta
maimakon tace wano
abu sai kawai ta kama hannunta ta
jata suka fice
daga cikin turakar suka nufi wani
bangare daban na
gidan.Wani lungu suka shiga mai
zurfin gaske kuma
yana da dan duhu.Tun daga
tasowar Yazirina kawo
izuwa girmanta ko sau daya bata
taba shiga wannan
lungu ba saboda ganin cewa gaba
dayan hadiman
gidan ma bata taba ganin wanda
ya shiga ba don haka tun tana
yarinya taje tsoron
lungun bisa mamaki sai taga
Basma sai dada
kutsawa take cikin lungun ba tare
da wata fargabar
ba saida sukayi doguwar tafiya a
cikin lungun
tamkar bazasu isa karshensa har
saida Yazirina ta
kosa sannan suka iso wani daki
wanda bashi da
kofa.Da isarsu gaban dakin sai
Basma ta dafa garun
dakin da hannunta na hagu.Take
garun ya tsage
gida biyu ya bude musu hanya
suka shige ciki suna
shiga sai bangon ya koma ya
hada.Babu komai a
cikin wannan karamin daki face
akwatuna na gilashi
sama da guda miliyan daya,wata
kan wata,gaba daya
akwatunan a rufe suke kuma babu
kofa ko murfi a
jikinsa wanda za'ayi budewa ko a
zura hannu ciki
don dauko abindake ciki kowacce
akwatu na dauke
da abu guda daya ne jal mai
muhimmanci.Kai tsaye
Basma ta nufi wata akwatai mai
dauke da wani Allon
Katako da isarta gaban akwatin sai
ta dafata da
hannun hagu take akwatun ta dare
tamkar an yanka
tsakiyar tuffa.Ba tare da tsoron
komai ba Basma ta
zura hannunta cikin akwatun ta
dauko wannan allon
katako.faruwar hakan keda wuya
sai akwatun ya
bace bat tamkar bai taba wanzuwa
ba a wajen
Basma ta mikawa Yazarina allon ta
karba sannan ta
sake zura hannunta cikin aljihun
rigarta ta dauko
jemammiyar fata ta sake danka
mata tace wannan
abubuwa biyu dana baki ba komai
bane a jikinsu
face zanen taswirar izuwa taskar
ajali wanda
mahaifinki yabar miki gado amma
kiyi sani cewa ba
zasuyi amfani ba har sai kin tafi
farauta yar uwarki
Sarila kin kasheta kin kwafi
taswirar dake zane a kan
gadon bayanta kin hada da
wadannan guda biyu
dake hannunki.Kamar yadda na
gaya miki a baya
yanzu ne zaki shiga sabuwar
rayuwa ta biyu wato
zaki bar wannan daji ki shiga cikin
duniya domin
farautar Sarila ki sani cewa nice na
shayar da Sarila
don haka na dauketa tamkar yar
cikina don haka
bana son dayanku ta cutar da yar
uwarta.Ina rokonki
alfarma guda daya idan har akwai
hanyar da zakibi
ki kwafi taswirar dake kan gadon
bayan Sarila ba
tare da kin kasheta ba to kiyi
hakan.A yaune zamuyi
bankwana ni dake ki shiga cikin
duniya kuma bani
da tabbacin zamu sake saduwa
bisa wannan dalili
ne kika ga yanayina ya sauya gaba
daya domin tun
jiya nake ta faman shara kuka da
bakin ciki bisa
ganin cewa lokacin rabuwarmu
yazo.Koda Basma
tazo nan a jawabinta sai hawaye
ya zubowa Yazirina
ta rungume Basma suka fashe da
kuka tare.Saida
suka dan jima a kankame da juna
sannan Yazirina ta
janye jikinta daga cikin na Basma
suka dubi juna a
lokacin da hawaye ke sartu akan
kumatunta
tace,yake ummina kiyi sani cewa
babu maganar
sassauci ko tausayi ko kuma jin kai
tsakanina da yar
uwarta Sarila musamman idan
kikayi la'akari da
yanayin yadda halayenta zasu
kasance na rashin
tausayi da kuma zalunci.Duk
danaji ance sai ta
ninkani a karfin damtse dana
sihirin tsafi da kuma
iya yaki ni bazan ji tsoronta ba
kuma ba zan fasa
tunkararta ba ko da kuwa zan rasa
raina,saboda ni a
rayuwata babu mutumin dana
tsana sama da
azzalumi.Da wannan furuci nake yi
miki sallamar
karshe gami da bankwana amma
nayi alkawari
cewar bayan na cika burina na
dauko dukiyar
mahaifina dake can Taskar Ajali
zan dawo nan na
rabaki da wannan gida mu koma
cikin gari muci
gaba da rayuwa a lokacin da zan
zama sarauniyar
duniya.Koda gama fadin hakan sai
jaruma Yazirina
ta juya ta fice daga cikin wannan
daki tana waigen
mahaifiyarta ta su duka suna zubar
da
hawaye.Lokacin da Boka Matawus
Bin Ashshahab
yazo nan a labarin da yake baiwa
Sarki Ubaiyu sai
kowa dake cikin fadar ya kamu da
tsananin mamaki
gami da tsoro musamman sarki
Ubaiyu wanda
hankalinsa ya dugunzuma ainun
fiye da kowa.Hankalinsa ya tashi Ainun fiye da
kowa.Cikin
kaduwa sarki Ubaiyu ya dubi Boka
Matawus yace
yanzu ina dabara?Ka gaya mini cewa
idan har daya
daga cikin wadannan yan mata walau
Yazirina ko
Sarila ta sami nasarar zuwa Taskar
Ajali ta dauko
dukiyar Boka Salmara saita mulki
duniya gaba
dayanta.Gashi a yanzu mun kasa kama
Yazirina
kuma kace Sarila ta fita hadari,yanzu
shi kenan babu
matakin da zamu iya dauka domin mu
magance
wannan matsala.Koda jin wannan
tambaya sai Boka
Matawus yayi doguwar ajiyar zuciya
gami da sunkui
da kansa kas ya na tunani.Daga can
kuma saiya
dago kai ya dubi Sarki Ubaiyu cikin
alamun tsananin
damuwa sannan tace ya shugabana
akwai hanyoyi
guda biyu kacal wadanda za'a iya
amfani dasu
wajen magance wadannan yan mata
biyu wadanda
suke neman su zamewa duniya
ANNOBA.Koda yake
daya a cikinsu ta gari ce wato ita
Yazirina,ita kuwa
Sarila muguwa ce wadda a halin yanzu
bata iso nan
cikin duniya ba tana can tsibirin
Jannatul Duniya
amma daga yanzu zata iya baiyana a
koyaushe
kuma tana baiyana sai duniya gaba
daya ta san da
baiyanarta.Hanya ta farko da za'abi a
ga bayan
Sarila Da Yazirina shine dole ne manyan
sarakuna
guda hudu na kasashen da babu
kamarsu a wannan
nahiya su hada KARFI DA KARFE su
yake su su
kawar dasu daga doron kasa,kafin daya
daga cikinsu
ta hada taswirorin uku na zuwa Taskar
Ajali a
hannunta.Wannan sarakai hudu kuwa
ba wasu bane
face sarkin kasar Sin da Sarauniyar
Birnin Hindu sai
kuma Sarkin Misra da Sarkin
Kisra,kuma kowanne
sarki dole ne yayi aiki tare da babban
bokansa.Hanya ta biyu da za'a iya
ganin bayan
wadannan takadiran yan mata shine
akwai wani
bakon sarauyi dan baiwa mai tsananin
sa'a da Baiwa
shine kadai zai iya hallakasu ta hanyar
hikimar ba
wai da makami ba.Koda Boka Matawus
yazo nan a
zancensa sai ran sarki Ubaiyu ya baci
bai san
sa'adda ya dakawa boka Matawus
tsawa ba,kuma ya
mike tsaye zumbur daga kan karagarsa
ta mulki ya
dubeshi a fusace yace wannan wace
irin maganar
banza kake yi mini ne hala alhalin
kasancewa ban
san a inda wannan bakon saurayi yake
ba,ban san
ta yadda zan iya shaida shi ba kumaka
gaya mini
cewa sarakunan kasashe hudu a halin
yanzu tuni
kowannensu ya baza dakarunsa izuwa
kowanne
bangare na duniya domin suyi farautar
Yazirina da
Sarila su rabasu da taswirorin zuwa
Taskar
Ajali.Kaga kenan babu dayansu da zai
yarda a hada
kai saboda son kai da son zuciya gami
da kwadayin
duniya.Lokacin da sarki Ubaiyu yazo
nan a
jawabinsa sai Boka Matawus yace
ubangiji Kartus ya
huci zuciyarka ya shugabana kayi sani
cewa wuya
itake sawa ayi gudun dole idan lokaci
yayi halinsa
ya zamana cewa kowa yaji a jikinsa to
dole ne a
nemi mafita.A wannan lokaci ne
wadannan sarakuna
hudu zasu nemi hadin kan junansu na
dole domin
magance wannan matsala amma ba
yanzu ba ni
yanzu shawarar da zan baka itace duk
yadda zaka yi
domin ka mallaki wannan bakon saurayi
da zai
baiyana ya kasance yana tare dakai
domin idan daya
daga cikin wadannan manyan sarakuna
hudu ya
sami taswirar zuwa Taskar Ajali har
yaje ya debo
dukiyar Boka Salmara to gaba daya ku
sauran
sarakunan duniya sai kun zama
bayinsa.
TURKASHI SAI MUN HADU A CIKIN
LITTAFI NA BIYU
DON JIN CIGABAN WANNAN LABARI.
TASKAR AJALI 1
Littafi na daya 1
Na Abdulaziz Sani M gini
Ebook creat by Shuraih Usman
Ebook publish by www.hausaebooks.cf
Ebook din nan yazo maku ne daga shafin www.hausaebooks.cf
Kuna ziyarci shafinmu don samun sababbin littatafai
Ga duk wanda ke bukatar ebooks nashi ya samu shiga cikin wepsite namu sai ya turo mana da littafin ta Email namu hausaebooks@gmail.com


TASKAR AJALI
Littafi na biyu 2
Na Abdulaziz sani M gini
Ebook creat by Shuraih Usman
Ebook publish by www.hausaebooks.cf
Ebook din nan yazo maku ne daga shafin www.hausaebooks.cf
Kuna ziyarci shafinmu don samun sababbin littatafai
Ga duk wanda ke bukatar ebooks nashi ya samu shiga cikin wepsite namu sai ya turo mana da littafin ta Email namu hausaebooks@gmail.com
KODA jin wannan batu sai idanun Sarki Ubaiyu suka
zazzaro ya dubi Boka Matawus cikin razana da
firgita yace waishin a kan wane dalili zamu zamo
bawan wanda ya mallaki wannan dukiya dake Taskar
Ajali?Koda jin wannan tambaya sai Boka Matawus
yayi murmushi yace,yanzu kayi tambaya mai
matukar muhimmanci ya shugabana kayi sani cewa
daga ranar da aka sami mahalukin daya debo
waccan dukiya ta Boka Salmara dake can Taskar
Ajali ya kawota kasarsa to daga wannan rana sauran
kasashen duniya zasu shiga cikin fari,fatara da
munin talauci saboda babu wata kasa da za'a iyayin
noma a kanta face kasar garin da aka ajiye wannan
dukiya.Babu inda za'a iya siye da siyarwa face
wannan kasa,kai hatta abinci saidai a rinka
fataucinsa daga birnin da aka ajiye wannan dukiya
ana kai shi izuwa sauran kasashen duniya kuma
inda duniyar zata taru domin ta kwace dukiyar daga
hannun mai ita ba zata iya ba,kaga kenan dole ne
sauran sarakuna su zamo almajirai a gaban mai
wannan dukiya domin su tsira daga yunwa da
talauci su da jama'arsu.Ka sani cewa ko akan hanya
yan fashi basu isa su iya kwace irin dukiyar garin da
aka ajiye wannan dukiya ba ta Boka Salmara.A
takaice dai duk sarkin da ya sami nasarar debo
wannan dukiya sai ya zamo kadagaran bakin tulu
kuma saiya zama kangarau maganin gagararru.Koda
Boka Matawus yazo nan a jawabinsa sai sarki
Ubaiyu yaja dogon numfashi cikin ajiyar zuciya gami
da karayar zuciya ya dago kai ya dubi Boka Matawus
yace na baka ragamar nemo wannan bakon saurayi
dan baiwa da zai baiyana kuma sarkin yaki da
dakarunsa ne zasu taimaka maka wajen yin wannan
aiki,kudi ko nawa ake bukata zan bayar dasu don
ganin wannan aiki ya cika.Ni kam na cire raina daga
kan tunanin mallakar dukiyar Boka Salmara amma
inason lallai na mallaki wannan saurayi dan baiwa
domin ya kawar mini da duk wani mahaluki mai son
yaje ya debo wannan dukiya ya janyowa duniya
gagarumar annoba wacce take daidai da GOBARA
DAGA KOGI wacce bata da magani.Koda jin wannan
batu sai fuskar boka Matawus ta fadada da
murmushi yace tabbas yanzu kayi tunani da shawara
mafi alheri a garemu baki daya ya shugabana.Gama
fadin hakan keda wuya sai Boka Matawus ya dubi
sarkin yaki yayi masa wata inkiya a lokacin daya
juya ya nufi kofar fita daga cikin fadar.Cikin hanzari
sarki yaki da mukarrabansa suka mike tsaye da
sauri suka takewa Boka Matawus baya,wannan shine
abinda ya faru a fadar sarki Ubaiyu na birnin
Yamein.
*Al'amarin Jaruma Yazirina da Barawo Muhajid kuwa
bayan ta dafa kafadarsa sun bace bat daga wannan
wuri inda ta fafata da dakarun sumamen,basu
baiyana a ko ina ba sai wata unguwar daban dake
nesa sosai da inda akayi gumurzu kuma agefe
hanya suka bayyana inda mutane ke
wucewa.Baiyanarsu keda wuya sai Yazirina tayi sauri
ta dauko mayafi daga cikin jakarta ta guzuri ta
lullube jikinta yadda idanunta kadai ake gani,kawai
sai ta dubi Mujahid a lokacin da taga har yanzu
jikinsa bai daina bari ba domin gani yake kamar a
ko yaushe shugaban wadannan dakarun sumamen
zai iya baiyana tsulum a gabansa,ta dafa shi tace kai
matsoracin banza kwantar da hankalinka kayi sani
cewa babu wani makiyi da zai riskemu anan yanzu
ka nemo mana gidan da zamu kwana domin ni bana
son na kara yin magana da kowa kuma ban son aga
fuskata.Koda jin haka sai Mujahid yayi murmushi
yace kada ki damu ya shugabata zo muje wani wuri
dake can gaba kadan na san ida zamu sami mai
kyau.Koda gama fadin hakan sai Mujahid ya wuce
gaba ba tare da fargabar komai ba kuwa Yazirina ta
bishi a baya kai kace miji da mata ne.Yar gajeriyar
tafiya sukayi suka iso kofar wani gida mai tsananin
shiru tamkar babu kowa a cikinsa,da zuwansu sai
mujahid ya kwankwasa kofar gidan har sau
bakwai,cikin alamun fushi Yazirina ta dubi Mujahid
tace wannan wane irin shashancin banza ne haka
zakayi ta kwankwasa kofar gidan mutane haka har
sau bakwai ko kuwa kurame ne a cikin gidan.Koda
jin wannan tambaya sai Mujahid yayi murmushi yace
dadi na da dan adam kenan ya cika garaje da
mantuwa,ashe har kin manta ke da bakin ki kince
babu inda ban sani ba a cikin garin,wannan
kwankwasa kofar da kikaga nayi har sau bakwai to
inkiya ce na yiwa mai gidan domin ya gano wanda
yazo.Ai kuwa kafin mujahid ya gama rufe bakinsa
tuni sunji karar zare sakatu uku dake jikin kofar
sannan kuma sai sukaji an sanya kuba a cikin kofar
an murde har sau uku sannan aka turo kofar gidan
ta wangame sai ga wani dan gajeran mutum mai
katon ciki ya fito.Daga shi sai gajeran wando a
jikinsa iya guiwa sai wani mayafi daya rataya a
kafadarsa gashi baki ne sosai fuskarsa babu gemu
kuma kansa yasha askin kwarya molo.A hannunsa
na hagu akwai dan karamin tulu na giya yana
kwankwada kuma a cikin maye yake don haka baima
lura da Yazirina ba wacce ke tsaye a gefe daya
lullube cikin mayafi.Koda gajeran mutumin ya dubi
Mujahid saiya bushe da dariya irin ta yan giya
sannan yace kai shegen duniya lallai yau ma dawa
tayi nama kenan,ina akaje akayi aiki mai riba haka
har da akazo neman hayar gidana mai tsaada..?Koda
jin wannan tambaya sai Mujahid ya doki kafadar
mutumin yace kai Andalu tsohon kwallon
duniya,dubi bayana da kyau ka gani tare nake
da..Kafin Mujahid ya karasa abinda yakeson fadi sai
Yazirina ta tari numfashinsa tace ni matarsa ce daki
nake son ka bamu mafi kyau a cikin wannan
gida.Koda Andalu yaji sautin zazzakar muryar
Yazirina sai ya bangaje Mujahid daga gabansa ya
kura mata idanu duk da cewa gaba dayan jikinta da
fuskarta a lullube yake sannan ya juya ya dubi
Mujahid yace wai kai wane irin yaro ne DAN BAIWA
haka mai tsananin sa'a da
™Abubakar Haleefah Physicist™
rabo,ba'a taba kama ka ba a wajen yin sata ko ayi
maka rauni yanzu gashi ka auro dalleliyar mace
wacce muryarta kadai ta isa ta debe kewa koda tafi
kowace mace muni a duniya.To gaskiya dakin daya
rage babu kowa a gidan nan shine mafi tsada sai
kun bani dinare dubu uku,kafin Andalu ya gama rufe
bakinsa tuni Yazirina ta bude jakar Guzurinta ta fiddo
da kullin dinare guda,sannan tace kaimu dakin naga
yanayinsa.Batare da wata gardamar ba kuwa sai
Andalu ya ratsa ya baiwa su Yazirina hanya suka
wuce cikin sannan ya janyo kofar gidan ya rufe ya
maida sakatun kuma yasa kuba ya dada kulleta yana
mai murda kubar har sau uku kamar yadda yayi a
farko.Yazirina na shiga cikin gidan ta tsinci kanta a
cikin wani babban falo,ashe mutane ne da yawa a
zazzaune maza da mata ana ta shaye shaye na
giya,lemo iri iri wasu kuwa hayakin taba suke ta
faman busawa,kallo daya zaka yiwa gaba dayan
mutanen gidan ka gane cewa dukkaninsu yan bariki
ne muma dukkanin matan karuwai ne babu
mutuniyar kirki gaba daya a cikinsu.A gefe daya
kuma teburin yan caca ne suna tayin cacar
tasu,daga can bangaren yamma kuma sai suka
hango wasu majiya karfi mutum biyu zaune a kan
wani tebur sun hada hannaye suna gwada yar kwanji
jama'a sun kewaye su suna yi musu tafi da shewa
kowannensu ya dage iya karfinsa domin yaga ya
sami nasarar danna hannun dan uwansa izuwa
kasa.Koda Yazirina ta dubi mafi girman surar karfi
daga kartin biyu sai taji bata yarda dashi
musamman datayi la'akari da irin kallon da yayi
musu ita da Mujahid amma sai ta basar suka wuce
ta gabansu suna bin Andalu a baya yayin da suka
hau kan wata matattakalar bene suka hau can sama
inda dakunan gidan suke burjik har suka iso kofar
wani daki dake can kuryar karshe.Take Andalu ya
zaro wata kuba dake cikin aljihunsa ya mikawa
Mujahid,Mujahid na karbar kubar saiya zurata cikin
kofar ya kunna kai cikin murna.Ita kuwa Yazirina
saita waigo tana mai lekawa kasan benen,akawai sai
taga ahe gaba dayan mutanen dake kasan benen
sun tsayar da duk abinda sukeyi sun daga
kawunansu sama suna kallonsu.Koda ganin Haka sai
Yazirina tayi tsaki tace nifa babu abinda na tsana
sama da a rinka kallona,kuma babu abinda nafi so
sama da sirri,kai Andalu na wane kudin gaba dayan
dakunan gidan nan kuma nawane kudin duk giyar da
aka sha a yau da sigari zan biyaka duka yanzu
amma inason ka sallami gaba dayan mutanen dake
cikin gidan nan su fice ya kasance daga ni sai
angona domin yaune zamuyi daren farko na
AMARCINMU.Koda jin wannan batu sai mamaki ya
kama Mujahid shi kuwa Andalu tsoro ne ya kama
shi jikinsa ya hau tsuma ya dubi Yazirina cikin
alamun tsananin firgici yace kiyi mini rai yake
wannan amarya kiyi sani cewa mutanen dake cikin
gidan nan a yanzu sune mafi RASHIN IMANI a garin
nan,idan naje musu da wannan bukta taki zasu iya
cutar dani kuma keda angon naki ma ba zaku tsira
da rayuwarku ba.Koda jin haka sai Yazirina tayi
tsaki tace matsala daya ce kawai dole ne na kara
asarar kudin da zan biyaka na barnar da za'ayi maka
a yanzu,tana gama fadin hakan saita sauko kasa da
sauri daga kan matattakalar benen a lokacin da
Andalu da Mujahid sukaji cikisu ya duri ruwa don
sun tabbatar da cewar tashin hankali za'ayi.Koda
Yazirina ta gama saukowa kasan matattakalar saita
dubi gaba daya mutanen dake cikin falon tace
inason kowa ya fice daga cikin gidan nan yanzun
nan domin na karbe shi haya gaba daya,wanda duk
ya kara dakika dari da ashirin a cikin gidan nan
saidai ya fita a karye.Koda jin wannan batu sai gaba
dayan mutanen suka bushe da dariya suka rinka
yiwa Yazirina kallon mahaukaciya.Al'amarin daya
fusata Yazirina kenan jikinta ya kama tsuma a
lokacin dataji zuciyarta ta kama tafarfasa kamar zata
kone amma sai ta dake ta tsaya cak a inda
take.Koda ganin haka sai wannan narkeken kato
wanda yayi gasar karfi da wani dazu wato wanda ya
kura mata idanun nan ya mike tsaye daga kan
kujerar da yake zaune ya tunkarota.Kan Yazirina na
sunkuye ko dagowa bata yi bare ta kalleshi har ya
iso daf da ita.Ai kuwa sai ya yunkura cikin
shammace ya kawo mata wawan naushi ta gefen
fuskarta,naushi ne irin wanda duk wanda aka yiwa
shi sai an karya masa kashi,cikin zafin nama ta
kauce katon ya naushi iska.Kafin yayi wani yunkuri
ta kama hannun nasa da hannayenta biyu ta daka
akan cinyarta.Take sautin karyewar hannun nasa ya
cika falon gidan ya kurma uban ihun sakamakon
tsananin zafi da zugin da yaji ya durkushe
kasa.Koda ganin abinda ya faru sai gaba dayan
sauran mazajen dake gidan suka zare MAKAMANSU
na yaki suka rugo da gudu suka afkawa Yazirina da
nufin su gididdibata.Wohoho!abin mamaki baya
karewa a duniya lokacin da wadannan mazaje suka
afkawa Yazirina ita kadai sai aka kacame da
masifaffan yaki ya zamana cewa suna kai mata SARA
DA SUKA tana kauce dukkan hare haren nasu ba
tare data rike wani makami ba.Saita rinka gwabza
musu naushi da bugu tana bazar dasu kasa kuma
ko mutum yaje kasan bata kyaleshi face ta take
masa kafa ko hannu ya karye nan take,komai girman
kato da hannu daya take surarsa ta dokashi a kas ya
kasa mikewa tsaye.Nanfa ihun mazaje ya cika gidan
a lokacin data rinka hada musu JINI da MAJINA
kuma tana kakkaryasu.Koda sauran karuwai sukaga
irin wannan mumunar barnar da Yazirina keyi sai
suka firgice suka ruga izuwa kofar gidan domin su
bude su fice domin sun manta ma cewa tuni Andalu
ya rufe kofar.Ai kuwa suna ganin kofar a rufe sai
suka dimauce wasun su basu san sa'adda suka far
fitsari ba a tsaye wasu kuwa kuka suka kamayi
saboda tsoron kada Yazirina ta kakkaryasu kamar
yadda ta karya mazajen gidan.Duk wannan abu dake
faruwa Andalu da Mujahid
™Abubakar Haleefah Physicist™
nacan sama bene sunki yarda su sauko kasan
kawai sun zuba na mukiya suna kallon ikon
Allah,shidai Andalu saboda tsananin mamaki da
tsoro ma tuni wandonsa ya dade da jikewa da fitsari
kuma daidai da dakika daya jikinsa bai daina
karkarwa ba.A hakanne ya dubi Mujahid yace me
yasa tun farko baka gaya mini cewa matarka aljana
bace ba mutum ba,da tun a sannan zan gudu na
bar muku gidan ungo kudinku da kuka biyani dai
kuyi min rai.Koda jin wannan batu sai Mujahid yaji
dariya ta kwace masa sannan ya dubi Andalu yace
kai matata mutum ce kamar kai ba aljana bace
amma ta musamman ce.Andalu yace kai koda
mutum ce ina ganin akwai aljanu a jikinta dubi fa
yadda ta ragargaza komai da kowa dake cikin gidan
nan,a daidai wannan lokaci ne gidan yayi tsit baka
jin sautin komai face nishi da koke koken mazajen
dake kwance a kas.Wadanda gaba dayansu karyayyu
ne su kuwa sauran matan gaba dayansu sun cure a
waje daya suna ta kyarma kamar ace kyat su tsure
da gudawa,gaba daya tebura da kujerun dake falon
sun kakkarye,tulunan giya sun farfashe ko ina yayi
kaca kaca kuma babu mahalukin da yake tsaye a
falon face Jaruma Yazirina kuma duk wannan dauki
ba dadi da akayi lullubin da Yazirina tayi bai kwance
ba bare aga fuskarta ko surar jikinta.Koda Yazirina
taga ta sami wannan nasara sai ta dubi gaba dayan
karuwan tace kowacce ta dauki saurayinta ta kaishi
daki tayi jinyarsa bana son mutum daya ya fita daga
cikin gidan nan har izuwa tsawon kwanakin da
zanyi.Tana gama fadin hakan sai ta juya ta hau
matattakalar benen ta isa Inda Andalu ke tsaye kawai
sai ta fiddo kulli uku manya na dinare ta cilla masa
ya cafe tace kasa a gyara komai na gidan nan kamar
wani abu bai faru ba.Kasa tsaro ya kasance bashiga
ba fita,duk abinda ake bukata na dangane da abinci
da sauran kayan ciye ciye dana shaye shaye a kawo
wanda zai ishi kowa har tsawon kwanaki bakwai da
zanyi a garin nan.Daga yau nice shugaba a gidan
nan babu abinda za'a zartar saida izinina,aikata
sabanin hakan ranka ne fansarsa.Koda gama fadin
hakan sai Yazirina ta dubi Mujahid tayi masa
murmushi tace Angona mu kara cikin dakinmu nan
take Yazirina da Mujahid suka shige cikin wannan
daki na musamman suka banko kofa.A sannan ne
matan suka fara taimakon mazajen da Yazirina ta
kakkarya suna tashinsu tsaye suna shigar dasu cikin
dakunan gidan kuma suka shiga gyara musu karayar
jikinsu,shi kuwa Andalu tuni ya kirawo hadimansa
duka yaja musu kunne akan kada su kuskura su
fitar da labarin abinda ya faru yanzu a cikin wannan
gidan sannan ya basu kudi suka je suka siyo
abubuwan da aka lalata a gidan aka mayar dasu
tamkar wani abu bai taba faruwa ba,kuma suka je
kasuwa suka siyo kayan abinci da ababan sha isasu
gami da tulunan giya da kararen sigari.Lokacin da
Yazirina suka shiga cikin wannan daki na
musamman sai suka tsinci kansu a ciki wani dan
kayataccen falo wanda ke dauke da jan kilishi mai
taushi wanda aka shimfida a kasa gami da jajayen
kujeru da kuma jajayen labulaye.A takaice dai komai
dake cikin falon launin ja gareshi akwai dakunan
barci guda biyu a cikin falon sai kuma kewaye guda
daya.Yazirina taje ta zauna akan doguwar kujera
tana mai sauke jakar guzurinta a kusa da ita sannan
ta dubi Mujahid fuskarta a murtuke tace zaka kwana
a cikin dakin ni kuma nan falon zanyi barcina.Koda
jin wannan batu sai Mujahid ya dubeta cikin alamun
tsoro yace haba ya shugabata kin sani cewa yanzu
kin kara gaiyato mana abokan gaba sakamakon
kakkarya mazajen gidan nan da kikayi kira tara
musu gajiya.Ni gaskiya tsoro nakeji nayi nesa dake
domin bazan iya kare kaina ba.Kafin Mujahid ya
gama rufe bakinsa sai Yazirina ta tari numfashinsa
tana mai daka masa tsawa tace kada ka raina mini
hankali mana,dacan wanene yake kareka daga
dukkan irin hadarin da kake shiga a lokacin da kake
yawon satarka?Mujahid ya gyada kai yace ai wannan
karon an turo nine na sato abinda yafi komai hadari
a duniya wato Taswirar zuwa kogon Taskar Ajali
kuma masu farautar wannan Taswira guda uku
manyan bokaye ne da manyan sarakuna ababen
tsoro.Koda jin wannan batu sai Yazirina ta bushe da
dariya sannan tace ni kuwa ko kadan bana
shakkarsu amma ina shakkar wata mace yar uwata
guda daya wadda a koyaushe zata iya baiyana a
cikin wannan duniya ana kiranta da suna JARUMA
SARILA.Cikin tsananin alamun mamaki Mujahid ya
dubi yazirina yace yanz kina nufin kice akwai wata
jaruma wadda ta fiki jarumtaka da hadari a cikin
jaruman duniya?Yazirina ta gyada kai tace kwarai
kuwa kuma baiyanarta a cikin duniya daidai yake da
baiyanar GOBARA DAGA KOGI wacce babu abinda
zai iya kasheta,inda ace itace ta shigo wannan gida
yau dinnan da tuni ta kashe kowa saboda batada
tausayi ko kadan,zata rinka farautata kamar yadda
mai fama da kishi ke neman ruwan sha ba don
komai ba sai domin ta rabani da taswirar zuwa
kogon Taskar Ajali guda biyu dake hannuna.Koda jin
wannan batu sai mamaki ya sake turnuke Mujahid
yace au dama daya Taswirar ma ta biyu na
hannunki.?
Nima dai na tsaya anan saboda tsananin Al'ajabi da
mamakîn Jarumtakar Jaruma YAZIRINA.
Au dama daya Taswirar ma ta biyu tana hannunki?
Yazirina tayi murmushi ba tare da tace komai ba sai
ta zura hannunta izuwa cikin

Please Login or Register in order to submit comment