Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

murmushi ya yi kafin ya ce"Amin Diya amma fa kin cancanci fiye da haka saboda samun mace kamar ki mai ƙanƙan da kai da yarda da cewa bata sani ba tare da rumgumar sabon ilimin da aka zo mata da shi abu ne mai matuƙar wahala,ina sonki zan kuma ci gaba da sonki har ƙarshen rayuwata,Allah ya albarkaci rayuwarki da zuriya ta gari."

"Amin Habibina kuma in sha Allahu zan yi dukkanin iyawata dan ganin na zama maka mar'atus saliha dangane da fannin girki kuma zan sa nutsuwa da lura wajen ganin na girka mana abinci mai lafiya ba tare da na yi almubbaranci da shi ba."

"Ma sha Allah,haka nake son ji daga gareki Diya,koyon girki a kafafen sada zumunta sam ba laifi bane matuƙar zaka sa hankali da lura tare da ɗakko irin abincin da muka saba ci kuma daidai da aljihun maigida idan kika yi hakan faffaɗan fada zaki samu a cikin zuciyata, sannan Ni Masoyin abincin gargajiya ne,inason tuwo daga na masara har kan na dawa ya dahu ya ji wuta ta yanda da asuba zaki min ɗumame in yi sahur da shi."

Murmushi mayalwaci na yi na ce"Shiyasa ka ke kato ashe  Habibi ka ce tuwo ke gina ka."

"Sosai ma ba ki ga ku ƴan indomie generation sam baku da ƙarkon mu ba."

Murmushi na yi kafin na ce"
Tabbas amma fa ni gaskiya ban iya miyan gargajiyan nan ba sai dai in koma gida a koya min."

"Shameless to You Dear kin ji kunya da baki iya Mulka tuwo da miyan kuka mai daddawa da naman rago ba Billah,ki samu man shanu ki zuba a gefe wayaga daɗi kan daɗi."

Dariya nake hadda ƙyakyatawa sai dana sahirta sannan ya ce"gobe gidanmu zan kaiki wajen maman Kwamared ta koya miki miyan gargajiya,kin ga in kika yi sai mu zo mu sa a firiza na tabbata idan kika ga yanda ake sau ɗaya shikenan zaki iya i trust You."

Turo baki na yi gaba kafin na ce"Gurin Maman Farrah za'a je Billah ba wani maman Kwamared haka kawai kana shirin yi min ƙwace."

"To na ji gurin Mamanki ina shikenan."Ya furta hakan yan yi min kallon ƙasa-ƙasa.

Kwaɓe fuska na yi alamun shirin yin kuka ya rarrashe Ni ta cikin ƙwayar idon shi na ce"Ummm abinci ko karatun za mu yi dan na fara jin bacci."

"Karatun dear kin san muna gab da shiga halwa remain few days mu shiga goman ƙarshe dole mu tsage dantse dan ke ma ki shiga sahu kar ban kai wata shekarar ba ki zo kina kuka kina Allah sarki HABIBI."muryata ya kwaikwaya ta ƙarshen amma jin ya ambato mutuwa yasa na ce"No,No....dan Allah ka daina ambatar min mutuwa Habibi haba!"

"Aikuwa ta zama dole ba ki ji mai Allah ya ce ba ne a cikin Alkur'ani mai girma"Duba na kai kan shi cikin alamun tambaya da neman sani.

"Ce wa ya yi Kullu nafsin za'ikatul maut summa ilaina turja'un(dukkanin rai sai ta ɗanɗani zafin mutuwa kuma gare shi zamu koma.)."

"Haka ne tabbas Allah ya ba mu ikon cikawa da imani Amma na fi yi mana addu'ar samun tsawon rai mai amfani dan mu mori rayuwar aurenmu da muke burin ginata da tubali mai kyau sannan ina mana ƙwaɗayin samun Waladus-saleh ɗan da ko ba ma raye zai tuna da mu ya mana addu'a"

"To Allah ya ba mu tsawon rai mai albarka tare da ƴaƴaye na gari."

"Amin ya rabbi."miƙewa na yi cikin sanyi naje na ɗakko littattafaina na dawo muka ɗaura daga in da muka tsaya duk jikina a sanyaye haka muka tashi har muka yi bacci sam zuciyata ba daɗi duk in na tuno da ummata sai in ji gabana ya yanke ya faɗi Ras.

ABBIYN FARRAH.
Ango an shiga sabon rayuwa yayinda matsanancin kishi da kaɗaici ke tare da zuciyar Ammi na rashin shi a kusa da ita,duk da daman ita ba mai yawan ciwo ba ce amma in ya kamata ya kan yi kamar zai kasheta,to duk lokacin da ta tsinci kanta a cikin irin wannan tashin hankalin tana samun wani kulawa na musamman daga gareshi sai ga shi tana ji tana gani wata ta ƙwace mata shi ta rasa shi a gefenta yana can tare da wata  suna raya sunnar ma'aiki,gado ɗaya shimfiɗa ɗaya jikin shi tare da nata kai Subhanallahi!

Firgirgit ta farka daga cikin nannauyan  báccin da ya yi awon gaba da ita sai dai ta tashi a firgice gumi  duk ya gama jiƙa mata jiki tsabar m
Kiɗima ga uban zufan da ta haɗa wanda sam bata damu da share shi ba,  nan take ta fara ambaton Allah da neman taimakon shi saboda mummunan mafarki take akan ƙarin auren da mijinta ya yi ,Kulu ce ta faɗo cikin ɗakin bakinta ɗauke da sallama,turus ta yi dan ganin uwargiyarta a cikin wannan halin har zata juya kuma ta tsaya tuno da roƙonta da ta yi  gafara a safiyar yau akan duk abinda ta aikata a gareta na rashin kirki ta yafe mata da yardan Allah yanzu rayuwarta ba irin ta da ba ce ta canza hali,ta santa sarai a dah wanda ba ƙaramin aikinta ba ne  yanda ta shigo ta balbaleta da masifa,

"Allah ka ɗau raina in huta da ganin wannan mummunan rana"karaf sai a kunnen Kulu ta yi daurin ƙarasowa kusa da ita ta  zauna a ƙasan ƙafarta durƙushewa ta yi kafin  ta ce"Hajiya ki yi hakuri dan Allah sannan ki rungumi ƙaddarar ki da hannu bibbiyu duk da na san kishiya ko ta bubuzu ce akwai ta da zafi amma idan kika ɗakko abinda ke gabanki wanda ya fi zama da ita ɗin muhimmanci shikenan kin rabu da damuwa."

"Duniyata ba zata ƙara daɗi ba Kulu,alƙiyamata ce ta tsaya dan Mansur shine fitilar dake haskaka rayuwata kuma ya samu makwafina to me ce ce amfanin rayuwata ki faɗa min?"

"Rayuwar ki kuwa ita ke da matuƙar amfani tunda har kike neman canzata daga mummuna zuwa kyakykyawa, shin idan kika sa damuwa har hawanjini ya ƙara bigeki irin na wancan karon zuciyarki ta buga kika mutu ta ya ya zaki nemi gafarar mutanen da kika ƙuntata ma na gurin aiki da dangin mijinki?"

Shin kin san Allah ba ya laifin da ke tsakanin bawa da bawa kuwa?"

Ta girgiza kai cike da tsoron haɗuwa da Ubangijinta  cikin rashin kuzari ta kai duba kan  Kulu wacce ta cigaba"To tun wuri ki farka dan Allah baya yafewa kuma wallahi Hajiya ko akan haƙƙin Maigidan nan kadai aka kyaleki ba zaki zauna cikin kabarinki da daɗi ba dan haka ki saki ranki ki yi kishin birni ki riƙe mijinki gam-gam sai ki samu aljanna cikin sauƙi."

"Hakane Kulu na gane yanzu mai zanyi?"

Nan ta fara jero mata duk abinda ta sa Ni dangane da tarairayan miji da ba shi kulawa sannan ta yi mata hannunka mai sanda dangane da ƙarancin ilmin addinin da take fama da shi, sosai ta yi mata godiya kafin ta sallameta,tana ficewa ta fara nazarin kalaman da Kulun ta faɗa mata tare da tariyo su tamkar mai bita,dake maca ce gogaggiya wacce ta saba mu'amala da jama'a ta samo mafita in da ta ɗauki remote ta fara bibiyan tashoshi wanda ke gabatar da shirye shirye akan addini musamman cikin wannan wata na Ramadana,Afrika Tv 3 ta tsaya in da ta yi dace da wani Farin dattijo yana tafsirin Alkur'ani mai girma nan da nan ta maida hankali tana jin fassarar ayoyin Allah masu tsuma zuciya,lema-lema ta ji a saman kuncinta wanda ta tabbatar da hawaye ne ke kwarara tsabar yanda take jin wa'azin tamkar da ita ake,jiyo rahama tare da ni'imomin da Allah ya tanadar ma bayin shi masu tuba yasa ta ji wani irin ƙarfin gwiywa ya zo mata nan take ta fara hamdala,sai da aka kammala tafsirin tsaf sannan ta miƙe jin an sanya karatun Alkur'ani yasa ta ƙara volume ta shige banɗaki domin gabatar da wanka.

HAKEEMA.
Nan take na fara kakkauda kayana dake waje na kintsa su tsaf a ɗaki,zumbulelen hijabina na janyo sai jiyo hannun shi na yi cikin nawa ya riƙe hijabina gam tare da rumgumo Ni.

Kin ci jarabawar tabbas kin cinyeta duka Hakeema."

Ƙoƙarin ƙwace jikina daga nasa nake yi yaƙi bani damar hakan cikin fushi na ce"Ka cikani dan Allah Malam in wuce ba kaima ka gaji da zama da Ni ba?"na ƙarashe maganan hawaye Malale akan fuskata dan rikenin da ya yi shine abinda ya fi komai ɓata min rai,

"Ki yi hakuri kamar yanda na ce kin ci jarabawa to wallahi jarabawa ce na yi miki domin in samu mace mai sona dan Allah."Shiru na yi ina sauraron shi jin wata sabuwar maganar da ya ɓullo da ita.
Nine tilon ɗa a gidan Alhaji Bisallah,shararren ɗan kasuwar nan wanda ya shahara da arziki a garin nan namu mai albarka, sanadin arzikin mahaifina ya sa na auri mata har guda 3 suna niyyar hallakani saboda su gaji arzikin dana gada,na rabu da su bayan Allah ya tuna musu asiri dan auren gata mahaifina ya min in da aura min mata 2 rana 1,Mahaifiyata ta aura min zaɓinta itama,duka a cikin shekara guda na auri waɗannan matan kuma a cikin shekarar muka rabu sanadiyyar CCTV camerar dake maƙale a kowani lungu da saƙo na gidan saboda tsaron lafiyata.

Kallonshi nake cike da mamaki bakina sam ya gagara rufuwa sai bin lallausan fatar jikin shi nake da kallo wanda sai a lokacin ma na ankara da yanda take sheƙi ga wani lallausan gashi ya musu rumfa(gargasa),shaƙar daddaɗan turaren shi na yi wanda na sha jin ƙamshin shi a jikin ƴaƴan masu hannu da shuni na lumshe ido cikin murya sansanya na ce"Mahaifinka ya maka auren gata har mata biyu su kuma matan sun so kasheka saboda su gaji arzikin da ka Gada shin daman ana gado kafin mutuwa ne ko Mahaifin naka ya rasu ne."

Murmushi ya yi mai sanyi kafin ya zaunar da Ni a daya daga cikin kujerun dake ɗakin namu ya ce"Mahaifina tun yana raye ya raba dukiyar shi saboda sanin yanda zamu fuskanci barazana Ni da Mahaifiyata idan har ya faɗi ya mutu saboda Ni kaɗai ya haifa yana kuma da sauran mata guda uku."

"Na'am na fahimce ka."

Wannan barazana dana samu daga matayena yasa na ji na tsani mata da auren kan shi,in da iyayena suka kaɗa suka raya akan in zo da zaɓina tunda sun min nasu na nuna a bari sai na huta,sun yi matuƙar gajiya da hutun nawa in da suka bani nan da sati biyu akan in fito da mata ko kuma su min auren dole."

Meyasa suka matsu da auren naka."

Dan su ga jikokin su, wannan shi ne babban burin mahaifina a duniya saboda tarin arzikin da yake da shi amma ba shi da yawan ƴaƴa dan haka ya ɗaura burin duniya a kaina."

Na'am."Na furta hakan ina bin gemun shi da kallo wanda ya Kusan zuwa ƙirjin shi saboda yalwar shi ga shi sai sheƙi yake tabbacin yana samun gyara mai kyau dan haka ya kusa kamu 3.

"Damuwar da nake ciki na takurar Mahaifina da yanda aure ya fice min a rai yasa na samu Abokina mijin Farrah da wannan mas'alar in da ya bani shawarar yin basaja har in samo wacce ke sona domin Allah da hannu bibbiyu na karɓi shawarar shi amma sai nake tunanin ta yaya zan samu kalar wannan matar tunda ayyukan da ke gabana sun min yawa, Kwatsam sai aka gayyaci Mahaifina taro domin zuwa musabakar da kika zo na ɗaya,ranar sai ya kasance yana da mitin da wani babban kamfani dan haka yasa na wakilce shi,anan na yi gamo da ke Hakima wanda tun daga yanayin takun tafiyarki na ji kin tafi da imanina kina samun guri kika zauna kuma na ji zazzaƙar muryanki na ji ina neman ɗimaucewa,tun daga wannan ranar na jingine dukkanin wani abu mai muhimmanci wanda ya danganci kasuwancinmu na fara bibiyarki har sai da na samu duk wani bayanai da ya dangance ki,hatta kalar mijin da kike so,irin shigar sa da komai kwaikwayo na yi, sabbin ɗinki na yadi nasa aka min dan na ji labarin kina son miji mai tawadu'u da gudun duniya,ganin duk abin buƙata ya samu hakan yasa na tunkare ki,sai na sameki da sauƙin kai da iya kulawa,sam baki da kwaɗayi ke macace mai neman na kanta,na so miki a matsayin namiji mai son banza ne da hannun kutare (a dunkule)sam bana miki kyauta sai kika nuna min koda kyauta ko ba bu kina sona.

Ban ƙara sakankancewa da lamarinki ba sai da aka kawo kuɗin aure da komai na ce"ban da halin yin lefe kuma a ɗaki ɗaya za mu zauna kika bani saitin akwati da zannuwan da kike tarawa idan auren ƙaninki ya tashi ki bashi kika bani na kawo gidanku."

Tun daga nan na sallama na san ce Wa ke ɗin ta musamman ce kuma kyauta ce ke wanda Allah ya min bayan an yi aurenmu a daddafe sai na tsiro da sabon iya shege kawai dan in jaraba ki shin dan kina sana'a kina kama kuɗi ne yasa ba ki damu da babuna ba ko kuma halinki ne haka?

Nan ma sai naga kin zarce tunanin duk mai tunani dan ke ɗin samfarin matan aljanna ne a gidan duniya ke a yanda na lura da ke ba babuna kike gudu ba zamana ba sana'a shi ne babban abinda kika fi tsana.

Fagen Amana da cika alƙawari,sanin ya kamata kula da Mahaifinki da marayun kannenki tabbas kin kasance mace abin koyi ga mata uwa uba zuciya da yarda da sana'a shi ne mutuncin duk wata mace a rayuwa tabbas ina godiya ma Allah da samunki Haaakimar zuciyata,ba sai gobe ba yanzu-yanzu zan kai ki  gurin iyayena dan sun matsu su ganki.

Waya ya ɗakko daga aljihun wandonsa Iphone 15 ya kara a kunnen shi cikin ƙasaitacciyar murya ya yi magana da wanda nake zaton direbansa akan ya zo ya ɗauke mu.

Miƙewa yake da shirin yi na yi saurin janyo shi dan inada tarin tambayoyin dake ƙunshe a ƙirjina dangane da shammatata da ya yi.


Uztaz Fans how market today🤪ya kuka ga kafcen shin wani darasi kuka ɗauka daga rayuwar gidan Hakima dana uztanta,kowa dai ya san akwai kalan mazan nan masu yi ma matansu wayo musamman idan sun kasance tailoli,ko masu sana'a,sake musu komai suke yi su dogara da ɗan samuwar da suke yi dan su yi ma yaransu kayan sallah shin idan hakan ya faru dake jan wuya zaki zama kamar Hakima ko kuma zama zakiyi kiyi ta masa bauta kamar Allah ne ya aiko ki?
  Ina buƙatar ganin tarin comments ɗinku ƙarƙashin wannan post ɗin dan littafin First Ramadan with HABIBI yana gab da ƙarewa saboda gabatowar goman ƙarshe na watan Ramadan, fatan ba zaku manta da   sa Ummu jidda a cikin addu'o'inku ba Fans na gode.

*Masu kiran waya,saƙon text message both whatsapp and Facebook ina godiya sosai,jiki alhmdulillah na gode sosai Allah ya bar zumunci inayinku irin sosai ɗin nan,yanzu rashin wuta ne ke kawo min tsaiko ku jama ƴan Nefa carmandudu cikin carbi lolz*






Ummu-jidda.

FIRST RAMADAN WITH  HABIBI.

  💔Heart touching story.💔


FARIDAT HUSAIN MSHELIA (UMMU-JIDDA).

*ZAFAFA WRITERS ASSOCIATION*


https://chat.whatsapp.com/H16N47YvbD60SKUCaNRF6Z


TSARABAN RAMADAN.
*Mai Azumi*
Yana da Farin ciki guda biyu: Farin ciki a lokacin da zai sha ruwa, da farin ciki lokacin gamuwa da Ubangijin sa, kuma tabbas warin bakin me Azumi shi yafi daɗi a wurin Allah akan ƙamshin turaren Almiski.”

LAMBA NA SHA BAKWAI.
DIYAN HABIBI.
Bayan na kammala ayyukana na gida na samu nutsuwa a ɗaya daga cikin luntsuma-luntsuman kujeruna na alfarma na zauna hannuna riƙe da Zubdatul Ahkam domin yin bita,wayana ne yayi ƙara cikin hanzari na ɗauka ganin Ammina ne yasa na kara shi a kunnena bakina ɗauke da sallama,lumshe ido na yi jin yanda ta amsa min sallamar i cikin walwala alamun ta
Rungumi ƙaddararta,gaisawa muka yi sannan muka ɗan taɓa hira kaɗan wanda ya shafi lafiyarta,jin zata kashe yasa ni ƙara rarrashinta akan zamantá da kishiyarta amma bisa ga mamakina sai na ji ta ce"Farrah magana akan auren ABBIYnki daga yau a rufe shi dan Allah saboda umurnin Allah ya aikata,Ni kuma ba zan yita jayayya dangane da halal ba babban addu'a dai shi ne Allah Ya ba shi ikon yin adalci a tsakaninmu."

"Amin ya rabbi Ammi amma gaskiya kin sakko da wuri a ce Habibi ne ya yi wata mata ai sai dai ya zaɓa tsakanin Ni Ko ita Allah,Ni fa i cannot share Habibi with any Woman Billah."

Dariya sosai na bata har sai da ta tsagaita sannan ta ce"Eh lallai yaro yaro ne,to idan ya zaɓe ta kuma fa."

"Sai ya rabu da Ni amma i will make sure na kashe shi itama na zama ajalinta."

"This is the great mistake da yawancin matan wannan zamanin suke aikatawa kowacce mace burinta ta mallaki mijinta ita kaɗai alhalin Ubangiji ya fi mu sanin hikimar da yasa ya ce maza su auri mata 4 saboda maza ba su kaimu yawa ba,koma sun kaimu to duk tashin tashina na yaƙi in ana yi su ake kashewa,to shin idan ke kin samu miji asirinki ya rufu bakya yi ma ƴar'uwarki kwaɗayin samun kwatankwacin ni'imar da kike ciki."

Ina mata amma ina jin tsoro yawanci ƴanmatan yanzu babban burinsu su shiga su fitar da na gida ko a wulaƙanta wacce suka samu.

Thats is Your beleive dear ,hakan kike ma kanki fata shiyasa zai faru dake amma da'ace zaki tsarkake zuciyarki wallahi ko da wani mugun abu kishiya ta zo Allah ba zai bata nasara akan ki matuƙar kin riƙe addu'a,idan kuma har ta yi nasaran to na lokaci kaɗan ne Allah sai ya warware shi tare da baki ladan hakurin da kika aikata."

Hakane Ammi haka na ji wani malami na faɗin irin wahalar da mahaifiyar shi tasha a hannun kishiyoyinta ƙarshe Allah ya ɗaukaka ƴaƴanta,ga shi malami,a cikinsu akwai attajiri,mai muƙamin gwamnati da babban ɗan kasuwa hakan ya faru ne bayan mahaifin na su baya raye."

To kin gani dan haka ki tsarkake zuciyarki ki daina kambama kishi a cikin zuciyar ki duk da halal ne amma in ya yi yawa yana jawo bushewar zuciya da ƙeƙeshewarta daga ƙarshe ka aikata mummunan abu danasani mara amfani ya biyo baya bayan sunanka ya karaɗe duniya da hotonka liƙe a shafin kowace jarida."

Hakane Ammi Allah ya bamu ikon yaƙar zuciyarmu."

Ta amsa da "Amin,ga wani sirri na musamman da aka bani."

All ears Ammina."na furta hakan ina baza fatun kunnuwa,

"Kowani sallah idan zaki yi ki dinga roƙon Allah akan baƙin kishi da zuciyarki ke da kinji Dear and ki roƙi Allah ya mallaka miki zuciyar mijinki idan kuma ya ƙaddara miki zama da kishiya ya ba ki hakuri da juriyar danne duk abinda zai kawo miki danasani."

"In sha Allah amma Ammi na ƙarshen nan Ni........."

Common ki yi na ce kuma ki daina kambama kishin hakan ke sa mata shiga uku,ke ko miji ne kika sa a gaba da fitina da shegen dube-duben waya ai baki da sukuni balle kuma wacce zama da ita ya zama miki dole."

"To na ji."na furta hakan ina turo bakina gaba sam banda wadatacciyar walwala tunda ta ambato min kishiya tana datse kiran wata ta ƙara shigowa ganin Sarauniyar jijjida kan First Ramadan with HABIBI group ce ke ƙirana(Shamzee),

"Egiyar gari ina kika shige ne 2days."

Na koma ga Allah stop calling me with that stupid name."

Shegiya na ce do what You can banziya kawai."

Dariya na fashe da shi na ce"Allah ya shirya min ke Shamzee(Zainab ta Shamsuddeen.),Hope dai bakya azumi tunda na ji kina zagi."

Ina yi sai dai in ke zaki min breaking na shi with Your shegen iyeyen tsiya."

Annabi ne ya faɗa not Farrah so mind Your tongue.

"SAW to na ji Astagfirullah wallahi ban taɓa sa nin zagi na karya azumi ba."

Zan turo miki audio clif ɗin ta Whatsapp Habibi ya tutturo min."

Zan kuwa saurara na gode,Kin san mai yasa na kiraki?

No Shamzee

Gidan wancan ƙawar taki Uztaziyyar muka je what that her name i even forget ma Billah."

Hakeema.

Yeahhh ita,shi ne kika sa mana ita a group ga shi kina shirin janyo mana asarar manyan classic ladies dan labarin ghetto Area da muka je muka sameta da muka bayar ya janyo cecekuce a group amma fa ta iya ɗinki gaskiya,kira na yi akan ki je ki cireta if not group ya tarwatse dan we can stay with Fakiriya gaskiyan magana a group."

So what idan group ɗin ya tarwatse,talaka ba mutum ba ne da har zaku fita dan kuna amsa sunan Classic ladies,a matsayinku dana iyayenku me yasa ba zaku yi ƙoƙarin tallafa mata dan ganin kun cireta a halin da take ciki ba,

Haka ne kuma fa wallahi balle in da ta birgeni ba maula take ba hajarta ta tallata amma duk da haka bata cancanci zama a cikinmu ba maganar Allah kawai ki cireta Ni dai.

"Ba zan cireta ba because tama fiku cancanta da ta zauna a wannan group ɗin."

Hujja

Tana auren Social Uztaz the must richest guy a wannan town ɗin .

You mean da gaske ne shi muka gani zai shiga wannan ƙazantaccen gidan rannan har yana gaishe mu muna wucewa,sai da muka shiga cikin mota muka yi ribas sannan Juwairiyya ke ce min Kamar"Social Uztaz."

Na ce mai zai kawo shi wannan jujin amma Meyasa shi yin wannan basajar da matsayin shi da komai na shi.

Neman mai son shi dan Allah.

Aikuwa ya samu am happy For her yanzu kuwa zan je musu da sabon gist."

Alright mu haɗu a group zuwa dare akwai shawarar dana yanke a matsayinku na ƴaƴan masu akwai ya kamata mu kafa gidauniya domin tallafar marayu da kayan sallah,start yours now.

Me ɗin

Investigation

Akan me

Akan gidajen masu ƙaramin ƙarfi a Unguwarku dan ki tallafa musu.

Ba bu ai kin san a GRA nake.

Ok zan je unguwar su Hakeema na da zan binciko the only thing da zan roƙe ku shine ku daure ku tallafa ku bada ƙalilan Allah zai baku kasiran.

To malaman Ramadan."Kit ta kashe wayarta raina ya so sosuwa amma tuno da ɗimbin ladan da zan samu yasa na ji dole zan yi kuma insha Allahu sai marayu sun sa kayan sallah kamar yanda kowane ƴaƴa ke sawa.
  (Dan Allah makaranta littafin nan ku taimaka ma marayu da kayan abinci,kayan Sallah gwargwadon iyawarku,ku tuna kuma watarana ƴaƴanku zasu zama tamkar su kar ku yi tunanin kun bar musu dukiya mai yawa idan wata musiba ta faɗa ma dukiyar fa,idan kuma sun rayu cikin daula ba lallai ne ma su tuna da ku ba tunda baku horesu da tausayi da jinƙan na ƙasa da su ba,talakawa na cikin wani hali a ƙasar nan ku taimake su da abinci da dukkanin abin buƙata kuma Allah zai yalwata muku a sanda babu mai taimakon ku idan bashi ba,ga masu buƙatar tallafawa kuma babu hanyar taimakon ma'ana unguwannin da suke rayuwa ba mabuƙata kuna iya tuntuɓata,kar dai ku manta da har yanzu Yusuf na littafin SUN GUJE NI yana nan yana rayuwa akan keken guragu duk da yana sa ran zai miƙe in kun tallafa, Allah ya bamu abin tallafama na ƙasa da mu alfarman Annabi.)

HAKEEMA.
Miƙewa yake da shirin yi na yi saurin janyo shi dan ina da tarin tambayoyin dake ƙunshe a ƙirjina dangane da shammatata da ya yi,sai dai yanda ya ruƙunƙune Ni ya hanani furta komai dan dole na gumtse bakina tare da rumgumar shi ina shaƙar daddaɗan turaren da ke fita a jikin shi har na ji ana horn a waje,

Kafin ƙiftawar gira da bismillah zarata majiya ƙarfi suka bayyana a ƙofar ɗakin namu wanda alamu sun nuna masu tsaron lafiyar shi ne,gyara min zaman hijabin dake jikina ya yi tare da gyara min nikabin da ke jikin shi kafin ya saƙalo hannuna a cikin nasa muka fito,muna fitowa suka rufa mana baya,

Motoci ne na alfarma guda uku reras a bakin ƙofar gidan yara sun kewaye su tare da yi musu daɓa-daɓa har muka fito,

Umurtan ɗaya daga cikin masu rakiyar na shi yayi da yaga yaran nan kuɗi,dan haka ya fara yi musu rabon ƴan dubu-dubu before You know har manya sun shiga cikin sahu ganin abun bana ƙare ba ne yasa Social Uztaz ya umurce su da su shigo mu je gobe zai zo ya yi rabon kayan abinci,kayan sallah da gyara hanyar ruwa da samar da rijiyar burtsatsi da yin kwalta duk zasu biyo baya da yardan Allah dan a dan zaman da ya yi a wannan unguwar har kamuwa ya yi da zazzabin cizon sauro saboda yawan kwatoci da suka buwayi unguwar tabbas zasu ga aikin Social Uztaz soon.

Iya na hango ta fito ba ko ɗankwali alamun labari ya risketa

Please Login or Register in order to submit comment