Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kallo har zuwa minti,a tare da bugun zuciyata kowanni minti ke ƙaruwa har na shafe awa ɗaya ba amo ba labarin shi,sai kai komo nake yi tsakanin ɗakin,

Tsabar ruɗun da nake ciki yasa ko tuna ana ƙira a waya ban yi ba sai dana jiyo sautin kira daga wayar shi dake yashe akan gado sannan na tunota,

Private numba ne dan ba suna kuma an ɓoye numban hannuna na karkarwa na latsa koren da ke nuna alamun kira na manna wayar a kunnena,

Muryan mace na ji cikin siririyar murya tana kiran Mashkur cikin sanyi,gashin jikina mimmiƙewa ya yi lokaci guda na ji zufa ta karyo min"Mashkur masu gari tunda ka yi aure ka gujeni,sai dai Ni zuciyata ta gagara mancewa da kai kuma har kwanan gobe ina sonka ina fatan shigowa ata biyu in ka bani dama."

Leɓena rawa ya dinga yi na gagara ce wa uffan tsabar rudanin da nake ciki har ta gama zubarta kamar kanya ban yi ko tari ba jin tana ta "Hello,Hello."ya sa na tattaro dukkanin wani ƙarfi da ya rage min na ce"Sai dai ko a lahira idan ana aure ki aure shi amma ba a wannan duniyar da muke ciki ba sakarai shashasha kawai."

Ƙit ta kashe wayar jin muryata ina kwararo mata na maguzawa,nan take na miƙe a fusace na fita zuwa falo ina dakon jiran Mashkur ya dawo,awa biyu ya ɗauka sannan ya shigo cikin gidan hannun shi ɗauke da kaya niƙi-niƙi,ko kallo ban isheshi ba ya wuce kai tsaye zuwa madafa ya dire su,ƙara dawowa ya yi ya giftani yana niyyar wucewa zuwa waje na yi karaf na cafke ƙafafuwan shi,cike da rauni na ce"Ba in da zaka ƙara fita  HABIBI har sai ka faɗa min gurin wa ce ƴar iskan ka je,sannan wata haihuwar haram ɗin ce ta kiraka a waya tana burin mallakar ka."

Ci kanki bai ce mata ba hasalima fizge ƙafar shi ya yi ya fita yaje ya kwaso sauran kayayyakin da ke cikin Boot ɗin sa yaje ya kai su kicin ya dawo sai a sannan ya fuskance ni tare buɗe min hannayen shi biyu alamun in taho gare shi na bi shi da wani mugun kallo zuciyata na zugani akan haka kawai ya je ya gama harka da matan banza sannan ya zo ya taɓa Ni,

Kamar ya san mai nake saƙawa a cikin zuciyata  ya ce"Bana son shaiɗan ya ci gaba da samun gurbin zama a zamantakewar mu Diyah ki yaƙi zuciyarki mu shimfiɗa nagartacciyar soyayya a gidan mu dan Allah."

Maƙe kafada na yi alamun naƙi ɗin sanin shegen kafiyata ya min yawa yasa ya ƙaraso gareni tare da kama hannuna ya janyo ni har zuwa ɗakina ya kwantar da Ni kan gado tare da lulluɓa min bargo cikin raɗa ya ce min"Ki kwanta gobe za mu yi magana in sha Allah."har na yunƙura zan miƙe ya haɗa hannayen shi biyu alamun roƙo na koma na kwanta,fita ya yi ya je ya ɓallo min Paracetamol jin alamun zazzaɓi a jikina ya sa ya bani maganin dana rage raɗaɗi bacci ne ke fizgata bayan fitar shi sai dai zuciyata cike take da son jin ina Mashkur ya je bayan fitar shi sannan wata shaiɗaniyar ce jikan Mayu ke bibiyar min miji haka na yi baccin rabi-rabi tsabar ruɗun dana shiga ganin na gagara baccin yasa na hau online (Madadin tashi ta gabatar da nafilfilu,karatun Alkur'ani da addo'o'i.), sosai na shagala da duba saƙonni har na ji an fara ƙiran salla,dirowa na yi daga gadon a hankali na tafi kai tsaye zuwa banɗaki,fitowata ke da wuya na hango HABIBI tsaye ya goya hannayen shi biyu a baya yana jiran fitowata,fuskar shi a sake dan daga gani ya shirya sulhu da ni amma Ni ta bangarena sam ba sauƙi dan haka ko kallon in da yake ban yi ba na nufi closet na zaro jallabiyya na sa tare da ɗaura ɗankwalin a kaina,na zauna a bakin gado na cigaba da jujjuya wayata ina duba saƙonnina dan har yanzu zuciyata tafasa take,

Ƙarasowa ya yi daf da ƙafata ya zauna,ya fara yi min tafiyar tsutsa a saman ƙafata har zuwa kan sharaɓata,da sauri na janye ƙafar tare da matsawa gefe cikin salon shi mai narkan da zuciya ya ce"Duk fa wayon amarya sai an sha manta yarinya."

"Haka kuma duk soyayyarka da namiji sai ya ci amanar ka,kamar Ni HABIBI dan na maka laifi har ka ɗauki hannu ka dukeni hakan bai isheka ba ka kwashi ƙafa ka tafi gurin matan banza shaiɗanu haihuwar titi,ashe da man kana da su tunda ga wata la'ananniyar na kiranka har tana tambayar tunda ka yi aure shi......."

Enough dear wallahi tallahi Ni ban je gurin kowace mace ba idan kin yarda,duka dai na ɗau laifina amma ke ma matsayinki na mace bai kamata in kin ga na yi fushi ba ki dinga ɗaga muryarki a saman tawa ba saboda kin fi kowa sanin halina bana iya controlling temper na,secondly bana son zagi dan Ni a gurina cin mutunci ne na yankar ƙauna and wace ce wacce kuka yi waya da ita?

Oho maka daman can yawa ne ma da su HABIBI har da kake tambayata wacce daga ciki?


"O'o Farrah rigima." ya furta hakan cikin wasa yana Kallona ƙasa-ƙasa yana dariya,dariyar ta shi kuwa ƙara tunzurani ya yi gani nake ya raina min wayo shiyasa ya ke faɗa min haka fuskar shi ɗauke da murmushi tsabar na kira mi shi sunan masoyiyar shi shiyasa yake annashuwa,


"Inajinka na ce wacece ita?"


Ban sani ba Diyah hasalima bi ban san ina waya da kowacce mace ba tunda muke waje dake balle yanzu da na kawo ki gidana shiyasa na ke tambayar ki."

Shine kuwa ƙaryan da zaka min wanda ba zan taɓa yafewa ba Billah,kuma matuƙar baka faɗa min wacece ita ba da alaƙar dake tsakanin ku masifa da bala'i ba zai taɓa ƙarewa a tsakanin mu ba."



Haka kika ce?


Ta ɗaga mi shi kai cikin fushi ya ce"To yanzu aka fara wasan wallahi mu zuba Ni da ke mugani shege ka
ka fasa."

Fuuu haka ya fice zuciyar shi na tururi sai dai kuma ko mai ya tuna sai ya dawo tare da hangame ƙofar ɗakin cikin ɗaga murya ya ce"Ta shi muje ki tuƙa min tuwo da shi zan yi sahoor."


"Billahillazi ba uban da ya isa ya sani aikin tuwo yanzu ai ba baiwa aka kawo maka na"Ce War Farrah wacce ke cika tana batsewa har wani karkaɗa ƙafa take tsabar fitina.



To fah Fans masoyan Farrah wannan mutuniyar taku an ya ta san menene aure?



Sorry For late update Fans, ayyuka sun riƙe Ni jiya da yau amma daga gobe na zama free in sha Allah,idan na ga ruwan comments zan biya bashin pages ɗin da kuke bina lolz.







Ummu-jidda.

FIRST RAMADAN WITH  HABIBI.
  💔Heart touching story.💔


https://chat.whatsapp.com/H16N47YvbD60SKUCaNRF6Z

FARIDAT HUSAIN MSHELIA (UMMU-JIDDA).


TSARABAN RAMADAN.
*Ka zamo mai soyayya don Allah kuma kada ka cutar da wanda yake sonka don Allah.*


LAMBA NA GOMA.
DIYAN HABIBI.
"Billahillazi ba uban da ya isa ya sani aikin tuwo yanzu ai ba baiwa aka kawo maka ba"na faɗi hakan ina cika ina batsewa har wani karkaɗa ƙafa na ke yi tsabar fitinar da ke cikin zuciyata."

"Wannan ne kuma baki isa ba Farrah sai dai in aurena ne kika gaji da shi."

"Eh na gajin ka sakeni in huta."

"Kin yi kaɗan wallahi dan aurena da ke ba saki ba yaji mutu ka raba takalmin kaza sai dai in auro wacce zata koya miki yi min biyayya sau da ƙafa wataƙil......"ai ban bari ya dasa aya ba na miƙe tare da hayyaƙo mi shi ba tare da ya saurareni ba ya shiga cikin ɗakin kai tsaye ya ɗauki wayata zai fice.

Da sauri na yi kan shi zan rarume shi da  kokawa ya bini da kallon kar ki kuskura ki taɓa ni haka ina ji ina gani  ya wuce min da wayata wanda nake jin Kamar da raina ya tafi,mara mi shi baya na yi har ina haɗawa da gudu,

Kai tsaye kicin ya nufa ya tafasa ruwan shayi ya juye a flask ya haɗa duk abinda ya san yana da buƙata a kan babban tray ya fice zuwa ɗakin shi jin yunwa na murɗa min ciki ya sa ban bi ta kan wayar ba dan haka na ƙarasa shiga cikin kicin ɗin domin dafa Noodles, nema na shiga yi na ga wayam,sam na mance da kayan abincinmu na side ɗin shi, dudduba cikin buhunhunan da ya shigo da su na yi nan na ga garin masara ne dana dawa,sai gero wanda ba'a surfa ba da suga sai da daddawa da kuka da kuɓewa busasshe.

"Kuturun uban nan kayyasa lallai HABIBI bai shirya zaman aure da ni ba aradun Allah,ko ba azumi yaushe zan iya cin wannan abincin gidadawan?"sanin ba bai bani amsa yasa na fice Fuuu ina ƙwala mi shi kira.

Ko tari bai yi ba duk uban kiran da na ke ƙwala mi shi kuwa har sai da na yi  tattaki na isa ɗakin shi na tsaya akan shi na ce"Wani salon wulaƙanci ne hakan da zaka ajiye min gingima gingiman buhu sai ka ce wacce ka auro daga karkara?"

Shiru ya min ya cigaba da shan shayin shi cikin kwanciyar hankali sai tura bread yake yi yana haɗiya da ƙyar dan da abu mai laushi mai kama ciki ya so  ya yi sahur da shi tunda mun tashi tun ukun da shabiyar a ganin shi har zan iya girka mi shi naƙi,

"Noodles zan ci HABIBI ina jin yunwa"na furta hakan cikin muryan sangarta,idan kun tunka ya ɓara, jin agogon dáke ɗakin shi ya buga alamun huɗu da rabi yasa na fara hawaye dan da gaske yunwa nake ji na fitar hankali dan rabona da sa wani abu mai nauyi a cikina tun jiya da magrib,

Ganin ya miƙe yana shirin kabbara salla tamkar bai ganni ba yasa na ce"HABIBI fa magana na ke maka ka yi banza da ni dan wulaƙanci yanzu abinda zan ci a sahur  ma shirin hanani ka ke?

Sam! Sai dai ke baki isa ki ƙi bin umurnina ba ne kiyi tunanin samun farinciki daga gareni wai Farrah mai kika ɗauki aure ne?

"Rayuwar jindaɗi da samun cikakkiyar ƴancin yin duk abinda raina ke so."

"Tabbas kin yi kuskure aure bautar Allah ce kuma a cikin kowani bautar Allah dole sai ka lanƙwasa zuciyarka domin samun rabauta,ni mijinki ne wanda ya zamto shugaba a gareki ya kuma zamto dole ki yi min biyayya ga duk abinda na umurce ki matuƙar ba saɓon Allah ba ne."

"Matsalata da kai daga mun fara magana sai ka so nuna Ni ban san Allah ba to Ni dai ko meye ka bani abinci."

Nuna min trayn da kayan da yayi sahur ya yi ya kabbara sallah nan na haɗa kakkauran shayi tare da juye rabin madara na zuba Milo tare da ɗiban biredi na fara  ci a yunwa ce,sosai naci sai da naji ya kai min karo sannan na ture bayan na yi wata irin gyatsa ina mai neman kwanciya akan lallausa carpet ɗin dake Malale a ɗakin shi dan ba shan wasa na ma tean ba,

"Tashi ki ɗauro alwalla tare da kuskure baki mu yi nafila."ce war HABIBI wanda idar da sallar shi kenan,

"A'a Ni bacci nake ji."

"Ok to tashi ki zauna ba kyau daga mutum ya ci abinci ya kwanta dan yana kashe zuciya sannan kuma ya kamata ki san muhimmancin wannan watan dan haka nake son ki dage da ibada."

"A'a fa gaskiya na gaji ka barni kawai laisal matsi wala takura a addini komai sai da niyya."

Shiru ya yi kamar ba zai ɓara ba can dai ya ce"Kowani musulmi murna ya ke da shigan wannan wata domin ya nemi yafiya,shin ke bakya yi ma kanki wani tanadi ne domin samun gafarar Allah tare da roƙon alhairai ma rayuwarki ta duniya da ta lahira?"

"Ya wuce tanajin da na yi maka shekara da shekaru ina koyon girki a zahiri da online saboda kawai in ɓarje gumina a First Ramadan ɗin da zamu yi shi tare?,ko shi ba ibadan bane?"

"Wannan fannin shi daban amma mai muhimmanci ai shine raya wannan watan da ambaton Allah,zikiri,karatun Alkur'ani,yin Bacci da sunna ta tanadar ba mai sa shagala ba tare da saurare ko kallon malamai magabata domin samun kusanci da Allah."

"To ai ka gode ma Allah ma da yanzu nake cika Farillan Ni fa kaga Sallan safe Allah ko a gidanmu sai na tumu na tumulmule nake tashi in yi, sallar ishsha kuwa ba kullum nake yi ba amma darajar wannan watan ka ga ina ƙoƙarin ramakon shi da asuba."

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un,Farrah Sallar ki ke wasa da ita?

"To meye kuma da jan wani dogon salati  dan na faɗa maka gaskiya daga duniyar fa sai Kaduna.......

(Jan hankali gareku mata dangane da zage damtse cikin wannan wata mai alfarma da addu'a, yawancinmu hankalinmu ya fi karkata akan harkar girke-girke ba su damu da tsayuwar dare ba wata ma ko farillan bata cikawa,azumin kawai ake ba sallah,mu dage mu jajirce dan samu mu rabauta, Allah ya karɓi ibadunmu.)

To fah Fans an ya wannan DIYAN TAKU TA JE ISLAMIYYA kuwa?


***** **** ****
HAKEEMA.
Uztazuna taɓe baki ya yi cikin son tura min haushi ya ce

"Sai ka ce wani ɗan ki?

Shanye ɓacin ran da yake shirin cusa min na yi nace"My Noor ala Noor sannan daddaɗan albishir na taho maka da shi wanda na tabbatar da in ka ji shi yau har goyani sai ka yi."

"Kuɗi muka samu?"ya tambayeni a hanzarce har yana niyyar hantsilowa daga gado,

"Eh,A'a"

"Wace irin amsa ce haka Hakeema?"

"Idan ka bada izini tare da yardanka za'a samu kuɗin da yardan Allah amma da sharaɗi ɗaya."

"Tun kafin in jima  nina amince ai Annabi da kan shi ya ce mu nemi tsari da talauci,dan me shi talaucin zai mana kaka-gida ya hanamu morar amarcin mu yanda ya kamata."

"Saboda mun ƙi tashi mu nema yanzu kuma na samu mafita ta hanyar amfani da wayata domin tallata irin sana'ar da nake yi har ma na samu kostomomi biyu gobe za su kawo min ɗinki."

Tuni ya washe baki sai Murmushin farinciki yake kamoni ya yi ya zaunar akan cinyar shi ya ce"Ma sha Allah,barakallahu fiki."

"Amin Uztazuna."

"Da man kina da wannan hikimar kika bar mu a gantale haba Uztaziyya matar Uztazu mai halin matar Sahabbai."

Dariya ce ta ƙwace min har ina tuntsirawa dan sai yau na yarda Uztazuna mayen son kuɗi ne to amma me yasa  baya son ya nema?

"Son jiki da mutuwar zuciya"na ba kaina amsa ganin yanda ya biyoni ƙasan yana niyyar tumurmusheni yasa na ce"Sai dai wani hanzari ba gudu ba."

"Eh ina jinki Hakimar zuciyata."

Nan ma dariyar ya bani ganin naƙi tsagaitawa yasa ya haɗe fuska,da kyar na tsaida dariyar na ce"Wanda zai haɗa mana keken ɗinkin alhalin ko ficika Bama magani."

"Ba zai gagara ba gobe da sassafe zan je in yi buga-buga in samu mai haɗa mana keken nan,tabbas kin kasance Furen zuciyata,Allah ya saka miki da alhairin sa shikenan wahala taƙare mana da yardan Allah."

Take yanke na haɗa fuska na ce"Wahalar mu bata ƙare ba matuƙar ba zaka tashi ka nemi sana'a ba wallahi dan dubu 20 ba zai riƙe mu a wata ba ko ba tsuntsun soyyyarmu(Mashin)balle kuma akwai ta tana iya ƙoƙarinta wajen shanye man da kake shawagi da shi a gari."

"Haaakimar zuciyata kenan"ya kawar da wannan zancen gefe dan baya son yawan ƙorafin da nake mi shi akan sana'a.

"Ai Allah dai ya zambaɗa miki albarka, Allah kuma yasa ki fara a sa'a,yasa zamu huta  da nemanki ko har kin mance alƙawarin da kika min ne kafin Allah yasa mu mallaki juna?"


"Alƙawarin me?"na tambaye shi,


"Alƙawarin sama min sana'ar da zan dogara da kaina idan har Allah yana sa miki albarka a naki kasuwancin......"



*Saƙonninku ya ƙayatar da ni Fans, ina godiya ga ɗaukacin masoyana waɗanda suka bani goyon baya domin ci gaba da rubuta wannan littafin sannan ina mai farincikin sanar da ku zan cigaba da rubuta shi sai dai salon zai canza.*









Ummu-jidda.

FIRST RAMADAN WITH  HABIBI.
  💔Heart touching story.💔

FARIDAT HUSAIN MSHELIA (UMMU-JIDDA).



*ZAFAFA WRITERS ASSOCIATION*


https://chat.whatsapp.com/H16N47YvbD60SKUCaNRF6Z



TSARABAN RAMADAN.

*Khalid bin Walid* (RA) Ya kan ɗauki *Al-Qur-ani* ya sa kuka yana mai cewa: "Jihadi da yaƙe-yaƙe ya shagaltar damu ga barin karanta ka".
*A yau kuma ko me yake shagaltar damu ga barin karanta shi.....?*



LAMBA NA SHA ƊAYA.
HAKEEMA.
"Alƙawarin sama min sana'ar da zan dogara da kaina tunda Allah yana sa miki albarka a naki kasuwancin."

"Zan cika da yardan Allah amma sai ka koma shagon da kake saida musu littafan nan kai ma kana samo na cefane nima ina nema har mu haɗa mu tadaka."

"In sha Allah,ke dai ki ja ɗamara tare da sa himma,ki hana kan ki baccin banza mu samu kuɗin da zamu mori amarcinmu."

Murmushi kawai na yi ƙasan zuciyata kwance da takaicin halin Uztazu dan ina sane da samarin Sunna maza ne masu ƙoƙari gurin kiyaye dukkanin abinda Allah ya yi umurni da shi da Manzon shi, musamman ɓangaren neman ilimi da sana'a tabbas na san basa zaman banza, Uztazu ne kawai Allah ya jarabce ni da shi,hakan muka kwanta cikin farinciki sai wani lallaɓani yake yi abin har abin dariya da takaici saboda halin shi ne zafin rai da faɗa kuma komai kayi baka iyan masa ashe banda lamarin Naira.


DIYAN HABIBI.
"To meye kuma daga duniyar fa sai Kaduna, ka ga ka isheni da surutu alhalin Ni bacci nake ji tunda kai na lura duk training da Ammina ta bani na zama good wife bakaso tunda ga kayan girke-girken duk ka sa musu kwaɗo."

Magana yake da niyyar yi amma tsabar shiga ruɗani ya kasa ganin yanda ya zama kamar dolo ya sa na ce"Tunda baka da ta cewa ni ka ga tafiyata dan bazaka hanani gudanar da abinda na yi niyya ba ato."

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un." shine kalmar da HABIBI ya ke maimaitawa har DIYAH ta wuce shi ji ya yi jikin shi ya yi sanyi ƙalau tabbas shi ya janyo ma kan shi wannan gaggarumar matsalan da yake ciki da na ce"Sai cikakkiyar ƴar boko zan aura saboda ita ce kaɗai  macen da zata iya jiyar dani daɗi a zamantakewarmu na aure,a tunanina duk sauran mata fanko ne matuƙar baka goge a rayuwa irin ta turawa ba,sai dai sam ban taɓa tunanin bokon ne kaɗai a kan Farrah ba ko karatun Fatiha da ƙyar take karantashi daidai, Dalili kuwa ta taso ne a hannun mahaifiyar data fifita boko akan komai na rayuwarta dan daidai da karatun Sallan data iya ta koya ne da Alkur'ani mai  translation ɗin larabcin zuwa Turanci,kamar yanda ta sha faɗa min yayinda nake zuwa hira,A wata tattaunawar da muka yi da ita bayan na mata tambayoyin da suka shafi addini ce wa ta yi"Sam Mahaifiyata ne duk ta jawo min wannan matsalar saboda ta ƙi bani damar zuwa islamiyya in zauna gaban malami ya koya min karatu saboda in na yi laifi takakkiya take yi ta je har islamiyar ta masife malamin a ce warta"Bata haifa ma mai dattin hula ɗiyar da zai yi ta jibga ba."
"Dan haka ta cireni tun ina da ƙuruciya, ta sanyani a makarantar boko mai tsada wanda inna tafi tun bakwai na  safe sai huɗun yamma nake dawowa,ina dawowa kuwa na cire kaya wanka zan yi in ci abinci in hau yin assignment tare da lesson ticana,Asabar da Lahadi kuwa ranar kitso ne da bacci sam Mahaifiyata bata taɓa koya min sallah ba,na dai tashi naga Abbiy na zuwa massallaci,Ammina kuwa sam ibadar ba damunta ya yi ba sai jifa-jifa idan ma tana yin to sai dai ko a Office,a makarantar boko na koyi sallah ganin sauran ƙawayenaa musulmai da muke zuwa Salla massallacin makaranta,ina bin su muje in tsaya ƙiƙam duk abinda naga sun yi nima in yi  har dai na gaji na faɗa ma ɗaya daga cikinmu ni fa ban iya karatun Sallan  ba,jin haka sai ta yi mamaki dan ko su  basa zuwa Islamiyyar amma malami na zuwa har gida ya musu karatu, washegari ƙawart tawa ta min kyautan Alkur'ani mai fassara,idan mun yi break ta koya min Ni kuma da dare in yi bita ta hanyar amfani da karatun turancin da aka rubuta,haka na tashi in kaga a gidanmu wani wani ya yi sallah bayan Abbiy to kuwa Kulu ce mai aikinmu ita kam ina ganinta tana yi sau biyar a rana ranan weekend,da ke Ni kuma gwanar tambaya ce sai na yi ta jero mata tambaya tana faɗa min iya abinda tasani,Abbiy kuwa matuƙar yana gida yana ƙoƙarin sanyani  na yi alwala ya ce in yi sallah ya fice massallaci sam bai san ban san ya ake ibadar ba ma,kuma yanayin aikin shi yasa sam bai san bana  zuwa islamiyya ba saboda yawanci sai dare yake shigowa gida.
  (Wannan babban ƙalubale ne gareku iyaye maza damƙa ma mace ragamar gida dan kawai ta Fika hali Babban ɓaraka yake kawowa a rayuwar iyali,yana da gayen muhimmanci uba ya yi iya ƙoƙarin shi ba ya bar ragamar ma mace ita kaɗai, dangane da koyar da yara ibada shi ma iyaye suna sakaci yawanci ba ma ƙoƙarin zaunar da yaranmu mu koyar da su yanda ake karatun Salla mun bar ma malaman islamiyya wannan ragamar shiyasa ga irin su Farrah wanda mahaifiyarta ta hanata karatun addinin aka samu mishkila,ina shawartan iyaye da su rage sa soyayyar ƴaƴa a rai wanda yake hana ba ma ƴaƴa ilimi, wannan matsalar yana faruwa ne ga ƴawancin yaran masu ƙumban susa kaɗan ne daga cikin yaran Malam Shehu ke kokawa da malamai idan an daki ƴaƴansu, Allah yasa mu fi ƙarfin zuciyarmu Amin.)

Ammina wacce ta hanani  zuwa Islamiyyar kullum ta shigo cikin gida tambayarta na farko"Kin yi Assignment?na amsa da "Eh"wanda kuma ya gagareni in lesson ticana ya zo kuma ya ɗaura min a  inda na tsaya,a haka ta taso tun ƙuruciyata."Ajiyar zuciya mai ƙarfi ya sauke bayan tuno wannan labarin sannan ya fara hasko yanda haɗuwarsu da Farrah ya kasance"Mun haɗu ne a wani taron ƙarawa juna sani a wata jami'a,Farrah ta fito gaban stage ta fara zubo speech cikin ƙwarewa da har sai da maɗaukacin mazauna gurin suka tafa mata nan take ta siye zuciyata dan haka ana tashi a gurin taron  tsareta sai dai ko saurarona bata yi ba saboda jan aji,wani daɗi ne ya tsirga zuciyata dan komai nata birgeni yake ,ganin ta nufi motarta yasa nima na yi sauri na rufa mata baya,anan na san gidansu tun bata kulani inna zo har na ƙulla alaƙa da ita mai ƙarfin gaske, kasancewar bata taɓa soyáyyá ba yasa na saye zuciyarta lokaci guda, ranar da ta gabatar dani a gurin mahaifiyarta sam ban samu karɓuwaba dan a gaban idona ta ce"In gama ɗaura burin duniya a kanki amma ki rasa wanda zaki ɗakko a matsayin miji sai mai 206(Mota)."nan take Farrah ta bijire mata tare da kafewa akan tana sona kuma har aka mana maure mahaifiyarta bata taɓa so naba."

Ban fahimci zaɓen tumun dare na yi ba sai yanzu da wannan matsalar ta shiga tsakaninmu da Farrah in da ta gwada min Jahilci ne ke mata jagora a zamantakewarmu na aure amma da yardan Allah zan yi ƙoƙarin gyarata da ƙarfin soyayyar da take min,miƙewa na yi cikin sanyin jiki na fara gabatar da nafilfilu a sujjadata na ƙarshe na koka ma ubangiji akan sauyin halin matar shi.

Jin ana kiran sallah yasa na fice zuwa ɗakinta na tasheta dan ni masallaci zan wuce sai dai na sami ƙofar a garƙame in da bacci mai nauyin gaske ya yi awon gaba da ita a daidai lokacin da muminai ke neman rahamar Allah ba ita ta farka ba sai 9 na safe,duk nacina HABIBI dole na haƙura har sai da ta tashi dan kanta sannan na samu na shigo sai a sannan take Sallan asuban in da naji gabaɗaya rayuwata  ya ɓaci amma tuno da duk wanda ya kauce akwai buƙatar a janyo shi a jiki yasa na sassauta.

"Bani wayata Habibi."ce wa ta ina nufar in da yake zaune a bakin gado,

"A haka ake gaida miji dear?"yanayin yanda ya yi maganan yasa na ji wani kunya ya kamani dan haka cikin kawar da kai na ce"Good morning Habibi,fatan ka tashi lafiya?"

"Bana lafiya?"

"Meya sameka?"na furta haka ina kallon shi.

"Damuwa dear,ina jin ciwo a cikin ƙirjina,damuwa na shirin yi min illa Diyah kuma duka ke ce silah"

"Ni kuma?" na furta hakan idanuna na bisa kan shi ganin idanun  shi na sheƙi ya yi ruwa-ruwa alamun hawaye ne kwance a cikinsu ya sa na ji na karaya,

"Eh ke."

"Mai na yi maka dan Allah."

"Hana zuciyata sukuni

Please Login or Register in order to submit comment