Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shi,kuma bai yiwa ka san ubangijinka batare da ka nemi ilimi ba.




LAMBA NA SHA HUƊU.
AMMIN FARRAH.
A daren ranar suka zo shi da matar ta shi asibitin domin duba Ammina da jiki in da ta fara kokawar miƙewa zaune sai dai kash ta kasa saboda yanda jikinnata ke mata matuƙar nauyi cike da nadama ta ce"Mansur amaryan taka kenan?"

Abbiy ya ɗaga mata kai alamun "Eh."

To Ubangiji ya baku zaman lafiya mai ɗorewa.

Suka amsa da "Amin."Fashewa ta yi da kuka Zuciyarta na mata ƙona tsabar kishin da ke azalzalarta amma ciwon da Allah ya jarabeta da shi sam bata da wani kuzarin gabatar da dukkanin ƙudurin da ta yi niyyar aiwatarwa idan mijinta ya mata kishiya,

Lallai ɗan adam ba a bakin komai yake ba kuma ba zaka san da hakan ba sai Allah ya baka komai na duniya ya hanaka lafiya hawayen tausayin kanta take yi har Abbiy ya ƙaraso gaban gadon ya kama hannayenta biyu cikin son kwantar mata da hankali ganin yanda ta yi laushi yasa ya ce"Ki yi haƙuri Fatima, wannan auren ƙaddara ce da rabo dan rabon shi ya kashe mijinta dan in aureta, babban abinda nake sonki da shi ki kwantar da hankalinki ki samu lafiya alfarman Annabi da Alkur'ani zan kwatanta adalci a tsakaninku Ni dai babban burina ki canza halayya kin ji."

Da yardan Allah zan canza dan inaji a jikina ba zan ƙara rayuwa ba a duniya tunda har wata ta mallakeka,Gara in kyautata tsakanina da Allahko zan dace da aljanna.

To ai aljannar sai ya ɗaga ƙafa sannan zaki shiga ƴar'uwata ki yi hakuri sannan ki rungumi ƙaddarar ki in sha Allahu Ni ɗin alhairi ce a gareku ba zan taɓa shiga tsakanin soyayyarku da mijinki ba."Ce War Amaryan Abbiy wacce ta tattako ta ƙara so gaban gadon da Ammie ke zaune ta ja kujera ta zauna tana fuskantar Ammina fuskarta ɗauke da murmushi,

Wani sanyin daɗi ne ya shiga ratsa kowani lungu da saƙo na jikina har ban san lokacin da na furta Alhamdulillahi ba a zuciyata ashe a fili na furta hakan har yasa hankalin Abbiy da amaryan ya dawo kaina dan sam basu san ina cikin ɗakin ba saboda sun shigo ina salla idarwata kenan,

"Farrah mai kike yi anan baki koma gida kin ma mijinki abin buɗa baki ba?"

"Na je dawowa na yi Abbiy na kawo ma Ammina abincin dare shi ne Mashkur ya ce in kwana tare da ita."

"Sam ba za'a yi haka ba maza kira shi a waya ni aikin me nake yi da ɗiyata amarya zata kwana a asibiti ta bar mijinta."Ce War Amaryan Abbiy.

Ganin duk mun zura mata na mujiya mamaki shimfiɗe a fuskarmu ya sa ta ce"Maza kira min sirikin nawa ki koma gida Ni anan zan kwana da mamanki ai kin yi ƙankanta da jinya irin wannan."

Tuni asirin zuciyata ya fallasu akan fuskata dan haka na fara murmushi cikin jin kunya na fara ƙoƙarin gaisheta,

Buɗe min hannayenta biyu ta yi alamun in iso gareta da man na santa tunda daɗewa mutuniyar kirki ce ta bugawa a jarida muna haɗuwa da ita a duk wani sha'anin ahalin gidan su Abbiy,Ammi ce ta gargade Ni da daina gaisheta ko ta cire min kwankwaso tunda ta san  an so haɗata da Abbiy dan haka take kishi da ita ala dole in muna tare da ita nake kauda kai sai dai in mata sansanyar murmushi itama ta maida min da nata sansanya dan mace ce da bata son matsala,ko da naji hukuncin da Abbiy ya yanke akan Ammina jinjina mi shi na yi dan hauka ɗaya ma HABIBI na karɓi bulala to ina ga shi daya ɗauki tsawon shekaru arba'in tare da Ammi mace mai shegen mitan tsiya da faɗa,gwaliya,ƙyaliya da raina duk wanda bai kaita ba shine halayyarta,kamar yaron aikinta haka ta ɗauki Abbiy yana zaune zata aike shi ya ɗakko mata abu kuskure kaɗan zai yi mata ta balbale shi da faɗa kamar zata duke shi,ita kaɗai ce gwana a duniya duk wanda ya aikata saɓanin abinda take so ya shiga uku ai ma ya yi matuƙar ƙoƙari wallahi dan kullum cikin nasiha da faɗa mata matsayin shi a gareta yake amma ta gagara ganewa  ina da tabbacin ba dan ya mata hakan ba ba zata taɓa nadama ba (Ni kuwa na ce Allah dai ya so ta da shiriya ai ba dan yasota ba da akan kishiyar sai ta ƙara zarmewa, Allah ya shiryi mata masu irin halin Ammi ya sa kuma su yi nadama tun kafin lokacin da nadamar bata da amfani zata riske su.)

Ganin na zurfafa a cikin tunani yasa Hajiya Amina tasowa ta iso gurina ta ɗago Ni duba na kai kan Ammina wacce jikinta ya mata nauyi ta gagara miƙewa naga hawaye na zuba a idonta da sauri na ƙarasa gurinta cikin gunjin kuka na ce"Dan Allah dan Annabin shi Ammina ki cire damuwa ki rayu ko dan mu da  ƴan'uwana kin san daga Allah da Annabin shi bamu da kowa sai ke,ke ce sanyin idaniyarmu kar ki tsawwala ma kanki damuwa akan Abbiy ya ƙara aure Sunna ce ta Annabinmu,wanda ya fi kowa ma a duniya da lahira matan shi sun zauna da kishiyoyi to ina gamu?.

Still hawayen take yi bakinta sai rawa yake yi yana ɓari amma ta gagara motsa shi ta yi magana,hannun Hajiya Amina na kama na haɗa shi dana Ammina cikin kuka na ce"Ammina ga amanar abokiyar zamanki na baki haƙika na yarda da halayyarta da kyakkyawan ɗabi'unta ke ce kawai zuciyata ke taraddadin yanda zaki karɓeta Ni kam zuciyata ya natsu da ita."

Bisa ga mamaki sai na ji Ammina ta ce"Nima na karbi ƙaddarata hannu bibbiyu tabbas idan har Allah ya ƙaddara zan miƙe akan dugadugaina sabuwar Fatima ce wannan mai koyi da halayyar ɗiyar Manzon Allah da yardan Allah."

Take Abbiy ya durƙushe akan gwiywowin shi biyu ya sa fuskar shi a ƙasa ya yi ma Allah sujjuda ta godiya da farincikin ganin wannan rana na shiryuwar masoyiyar shi kuma uwar ya'yan shi,

Koda ya ɗago rungume su ya yi dukkanin su biyu yana shi musu albarka kafin aka dawo kaina Hajiya Amina tasa na kira Habibi ya zo ya ɗauke ni ,tare muka fito da Abbiy ango wanda ya bar Hajiya Amina a gurin Ammina dan su kwana a tare,

Hira mai daɗi ta dinga mata tare da bata kissoshi na manyan bayin Allah mata waɗanda suka hidimtawa addini musamman Sayyida Fatima da Mahaifiyarta Nana  Khadijah wacce dukiyarta gabaɗaya ta ba ma addinin musulunci amma hakan bai sa taƙi yi ma manzon Allah biyayya ba nan Ammina ta ji tana da burin ta ƙara rayuwa ko dan ta aikata ayyukan alhairi tare da gyara tsakaninta da mutane har bacci ya yi awon gaba da ita,

A sannan Hajiya Amina ta amsa kiran Abbiy a waya tana ɗauka ya fara yi mata ƙorafi akan yanda ta zaɓi yin daren farkonta a asibiti gurin jinyar kishiyarta ita ta bar shi shi kaɗai,

Dariya ma abin ya so bata tsofai-tsofai da su ai ita bata tunanin zasu ƙara yin wani soyayya a cikin auren su amma dai ko mene ne ta ji daɗin kulawar da ya bata dan haka ta bi shi da daɗaɗan kalamai da yasa ya ji tamkar yana rumgume da ita a hakarƙarin shi.

Habibi kuwa............

HAKEEMA.
Sakina ya yi tare da samun bakin gado ya zauna yana jirana in dawo in ba shi kuɗin cefane mu ci irish da ƙwai ,da  miyan dage-dage har mu kora da Kunun gadara da madara mai kwakwag a ciki,

Wayata na fiddota daga cikin aljihun rigar dake jikina na da7nna ma ƙanina kira,jin na ce zan bashi kuɗin mashin yasa y f jin an admin suka fara da Uztazu Ni kuwa na shige cikin daki na kwaso kayayyakin da suka kawo na zube su a tsakiyar ɗakin na fara yi ma ƙanina lissafi,

Tun daga landing har kan man keke almakashi,allura,zare stone da duk na bashi kuɗin su wanda suka kama dubu tara daidai,ɗari biyar na cira a sauran dubu ɗayan na bashi ya fice bayan na gama yi mishi bayanin kalolin da duk nakeso ƙarshe ma ya ɗauki zannuwan ya tafi da su dan kar a samu failure,

Jiyowa na yi gurin Uztazuna murmushi  akan fuskata na ce"Ka ga mun cika Sunna Noor mun karɓi amanan kayan mutane da kuɗinsu mun je za mu kashe kudin yanda ya kamata."

"Me kike nufi?",ya tambaye Ni a fusace dan ina lura da shi tun shigar mu ɗakin da ƙanina ya ke bina da kallo ƙasa-ƙasa,

Cikin sanyin murya na ce"Ina nufin na bada kuɗin kaf an je siyo min kayan aiki  Inna gama suka ciko kuɗin sai muyi amfani da shi."

"Saboda kin fi kowa rashin wayo ko saboda ke ce muguwa ta bugawa a jarida Haba Hakeema wato ainufin tun ina karatu na ke haɗiyar yawu saboda na san ke ɗin gwana ce gurin sarrafa nama,kin san duk wani hukunce-hukuncen da ake masa ya kama maggi ya yi zauyy."

Dariya na fashe da shi hadda ina ƙyakyatawa ganin yanda yake kumburi kamar zai fashe yasa na fara daidaita nutsuwata ganin hakan yasa ya ce"Ki yi ma Allah ki shiga ki fito da kuɗaɗen nan in je kasuwa da wuri dan da kunun gadaran nan nake son yin buɗa baki."

Babu su kuma ba dalilin su Noori sabo da idan kiɗa ya sauya to rawar ma canza shi a ke yi yanzu a matsayin matarka nake ba budurwan dana saba hana kaina bacci in nemi kuɗina ka zo ka cinye min su ba kullum da kayan buɗa baki,ko tausayin maraicina baka yi da yanda nake tsaye akan ƙannena dan rufa ma juna asiri kai dai kullum burinka in haɗa maka kayan daɗi ka zo ka take ciki ko ƙwandala baka bani balle in ɗan rage daga an yi magana ka ce bidi'a ne yin Ramadan basket amma Sunna ce zuwa gidanmu ka ci abincin dana siya da kuɗina ka kakkaɓe jiki ka yi gaba.

Tun muna waje baka taɓa yi min kayan sallah ba amma fa kana jiran abincin sallah na sati guda a jere batare da ko goron Sallah ka bani ba Shin ba Allah ne ya halasta kyautatawa ba a tsakanin mutane?

"Shi ne tabbas."

"Ni da ke kyautata maka shin bakajin daɗi?"

"Ina ji sosaima har ma ina alfahari da ke."

Ka san dalilin da yasa na ɗaga maka ƙafa san da muke waje?ya girgiza kai alamun A'a

To na yi hakan ne saboda a lokacin Allah bai kallafa maka ɗaukar ɗawainiyata ba kuma Ni dan na kyautata maka ba laifi ba ne sai dai kuma yanzu na tabbatar da ce wa"Na tafka babban kuskuren sabar maka da yin  komai tunda ka gagara ciyar da Ni da ɗaukar ɗawainiya........."

Na ji kuma ba gode da gori ai Bama sai kin kai da nisa ba Hakima ki ce kawai ba zaki bada kuɗin ba zan yarda sai dai ki sani bafa ki isa ki hanani bin gidajen abokai ba ina kwasar Gara fahimtum?.

Na'ammm ya Uztazul Karim.......

*Wannan shafin na rubuta shi ne ga ƴan mata masu shagwaɓa mazaje ta hanyar bugun ƙirji tun suna waje su ƙi saba ma namiji da yi musu komai sai dai su suyita hidima da saurayin kwatankwacin hakan ne ya faru da Hakima na cikin wannan labarin kuma kun ga yanda zuciyar shi ta mace sam burin shi Ita dai ta mi shi hidima da dukiyar ta,dan haka ku yi takatsantsan Allah ne ya kawo mu wani lokaci da maza ke son mace ta musu sam ban hanaku kyautatawa ba ban kuma ce mace ta zubda kimarta ta roƙa ba sai dai kar a wuce gona da iri gudun matsalar da ka iya zuwa ya dawo, Allah ya sa mu dace*



*Ban yi 2 page ba amma na yi double page a tafa min🤩💃, Allah ya karɓi ibadunmu,Barka da shan ruwa*








Ummu-jidda.

FIRST RAMADAN WITH  HABIBI.

  💔Heart touching story.💔


FARIDAT HUSAIN MSHELIA (UMMU-JIDDA).

*ZAFAFA WRITERS ASSOCIATION*

https://chat.whatsapp.com/H16N47YvbD60SKUCaNRF6Z

TSARABAN RAMADAN.
Misalin ƴan uwantaka saboda Allah, kamar misalin hannu da idanu ne, idan ido ya zubar da hawaye sai hannu ya share masa, idan kuma hannu ya ji ciwo sai idon ya zub da hawaye sabo da zafin da hannu ya ke ji.
Allah ya bamu ikon soyayya domin shi.

LAMBA NA SHA BIYAR.
DIYAN HABIBI.
Habibi kuwa tun a motar yake kwantar min da hankali dan ya san inada kyakkyawan alaka da Mahaifiyata ba matsayin uwa kawai take a gareni ba ƙawata ce wacce sam ba ma rabuwa dan haka duk abinda zai shafeta dole ya taɓani dan haka ya dinga rarrashina cikin tattausan kalamai masu sanya nutsuwa har na ji na samu ƙarfin gwiywar yi mata addu'ar samun lafiya nagartacciya.

Muna isa gida ya hanani taka ƙasa tsabar gata ya sunkuce ni zuwa ɗakin shi kamar wata ƴar baby kasancewar ba wani nauyi ke gareni ba,

Sakina ya yi a daidai saitin katifa in dana faɗa kai,nannauyan ajiyar zuciya na sauke dan sam ban yi tunanin akan abu mai laushi zan sauka ba,hararar wasa na mi shi ina ciccije leɓena alamun na ɗan ji zafi ya bini da murmushi tare da zaro harshen shi waje alamun gwalo,

Ƙoƙarin raba jikin shi da kayan da yake yi ne yasa na yi saurin runtse ido dan wani irin zafi da ake yi ga kuma rashin wadatacciyar iska a gari shiyasa daga shigowar mu yayi tunanin yin wanka,dariya ma na ba shi sosai hadda ƙyakyatawa dan haka ya dawo saitin fuskata ya fasa ƙara tare da rarumo Ni,a gigice na miƙe na yi kan shi sanin ni matsoraciya ce lamba ta ɗaya yasa ya ce"Ƙarshen runtse ido gaki gani sai in ga na jin kunya."

Murmushi kawai na yi tare da sunne kaina a jikin ƙirjin shi nan take na haifar mana da baƙon yanayi wanda muka dulmiya a cikin har sai bayan awanni biyu muka dawo hayyacinmu,

Wanka muka yi a tare,ina fitowa na shimfiɗe akan gadon tsabar gajiyar da na yi da taimakon shi da komai ya sa min kayan bacci sannan ya kunna mana kira'a nan take wani bacci mai daɗin gaske ya yi awon gaba da mu.
  Washegari a asibiti na wuni in da na samu ana samun ci gaba sosai dangane da ciwon Ammina dan a jingine da gadon na sameta tana shan kankana Hajiya Amina zaune kusa da ita tana riƙe da filet ɗin,

Sai hira suke abin gwanin ban sha'awa suna ganina Hajiya ta fara yi min oyoyo fuskarta ɗauke da murmushi a haka muka gaisa kafin na isa gurin Ammina na mata ya jiki,

Amsa min ta yi cike da kulawa sannan na samu guri na zauna ina bitar littafin addu'o'i wanda Habibi ya koya min da asuban nan,ko da muka samu keɓewa da Ammina tambayata ta yi dangane da zamana da mijina wanda na faɗa mata duk yanda muka yi a taƙaice,tabbas ta ji daɗin wannan al'amarin kuma ta yi min nasiha mai ratsa jiki wanda yasa har hawaye sai da nayi dan ina ganin kamar wasiyya take bar min tsabar yanda ta yi laushi ta ɗauki duniya ba koman komai ba da haka muka rabu zuciyata ƙunshe da farinciki canjin halayyar uwatawashegari kuwa aka sallameta muka ɗugunzuma zuwa gida in da har ɗaki na bi Hajiya Amina na yi mata godiyan karamcin da ta gwada mana yanda daga zuwanta ta yi jinyar Mahaifiyata,faɗa ta dinga yi min akan godiyan kan shi in da ta ce"Ai yi ma kaine."

Na daɗe a shashinta sannan na shiga gurin Ammina na fara tausarta,tare da nuna mata girman ƙaddara da yarda da ƙaddara mai kyau da mummuna,hawaye kawai take yi sai naji  jikina ya yi sanyi dan haka na cigaba da kwantar mata da hankali ina kuma mamakin irin wannan shiriyar da ya zo mata a lokaci guda dan da ada ne wane mutum in ji mutuwa har yaushe na isa in tunkareta da ce War su zauna lafiya da kishiya,kishiyar da taci alwashin matuƙar aka yi mata ita sai ta ƙonata da ranta in yaso duk ma abinda zai faru ya faru,tabbas da na san zata aika dan nafi kowa sanin halinta na rashin tsoro da tsayuwa akan ra'ayinta amma yanzu sau nake hango sassauci a cikin ƙwayar idonta da gangan jikinta wanda ya yi laƙwas, godiya na yi ma Allah da ya nuna min wannan rana Sannan na yabi Manzonsa ɗan daɗin Allah.
Sai dare sannan Habibi ya zo  ɗaukata bayan ya shiga gurin Ammina ya mata ya jiki, cikin sanyin murya a karon farko na rayuwarta da shi ta dinga mi shi godiya tare da damƙa amanata a gare shi tana kuma mai neman yafiyar shi akan duk kuskuren data aikata a gareshi,

Murmushi kawai yake yi cike da farinciki sannan ya ce"Uwa ai bata yi ma ɗan ta laifi Ammi, Ubangiji ya baki lafiya nagartacciya."

Ta amsa da "Amin, Allah ya muku albarka."muka haɗa baki wajen amsawa,da taga ina ta kai komo wajen shiryawa da kanta ta ƙira Kulu ta haɗa mana abinci cikin basket tunda an sha ruwa lokacin har an sauke abincin dare wanda Hajiya Amina ta aiko min da nawa na musamman,sallamarta na yi ina kallon fuskarta wacce ta yi fayau sai kallona take itama har na fita na ƙara dawowa na zo na rumgumeta a tare muka fashe da kuka kafin ta yi jarumtar ɓanɓareni daga jikinta ta yi min rakiya har gaban motar Habibi,lallaɓawa ta yi ta koma dan jikinta sam ba ƙarfi nan ta fara yin istigfari a cikin zuciyarta dan sam bata son wani mugun tunani ya zo ranta,kishingidar da ta yi anan wani nannauyan bácci ya yi awon gaba da ita.

Tun a cikin mota Habibi ya lura da yanayina da ya yi matuƙar canzawa dan haka ya sake mana ƙira'a cikin muryan Sheikh Abdullahi Abba sai bi yake yi cike da nishaɗi nan nima tawa zuciyar ta sanyaya dan haka koda muka koma gida na ware ganin haka ya  ɗaukeni  a hannu ya dinga zagaye falon da ni tamkar ya samu jaririya sai da ya gaji dan kan shi kafin ya sauke Ni yana godiya ga Allah da ya nuna mi shi wannan ranar cikin farin ciki ya ce"Tabbas mahaƙurci mawadaci sannan mai haƙuri shi zai dafa dutse har ya sha romon sa."

"Da mai ya faru?"

Da Ammina ta amshi auren mu mana,tabbas rayuwar aurenmu zai inganta tunda mun samu albarkan uwa Diyah, dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Ubangijin talikai."

Hakane alhmdulillah mun gode ma Allah da ya sa muka tama silar shiryuwan Ammi zuwa ga hanya madaidaiciya, Allah ya cigaba da zama jagoranmu a cikin kowani al'amarurruka na rayuwar mu.

Ya amsa da "Amin."ka fin y nuna min hanyar kicin alamun in yi gaba,tafiya na fara cikin saiɓi da yanga wacce ta kasance halittana,ya  dinga bina da kallo cike da sha'awa har na kai bakin ƙofa sannan na juyo cike da mamaki nake kallon shi na ce"Ya da kallona?"

"My property nake kallo Diyah."dariya ya bani amma na kanne tare da ɗaga mi shi gira ɗaya da sauri ya fara tattakowa ganin zai cimmini yasa na shige da sauri ya biyo ni da sauri,

Kyakkyawan runguma ya min ta baya kafin ya ce"Close Your eyes Dear."

Rufe idon na yi da gaske kafin ya juyar dani saitin store ɗin mu sannan ya ce"in buɗe."

Wal!haka na yi tozali da...........tamkar a mafarki 🤪💃.

HAKEEMA.
Na'ammm ya Uztazul Karim."
Ganin yanda ya wuce ni fuu kamar guguwa yasa na ce"Allah ya huci ran maigida."in kun tanka ya tanka haka ya saka kai ya fice yana cika yana batsewa ko a jikina wai an mari kakkausa hasalima miƙewa na yi a gurin har ƙanina ya kawo min kayan ɗinkin nan take na yi yanka na mamman gum a jikin kayan kafin na faka su gefe,ban ko tuna Uztazuna na fushi da Ni ba sai da lokacin shan ruwa ya yi,jin shiru bai dawo ba yasa na aika taliya yar murji ta ɗari biyu na watsa shi a tukunya,ana kiran sallah na gabatar da salla sannan na yi buɗa baki da taliyata da sansanyar ruwa na hamsin a gefe,ci na yi na ji nayi nak kafin na adana sauran wanda zan yi sahur da shi,da 3 in 1 ɗina wanda na siye shi saboda tsaro,ko da Uztazuna ya zo na wanke komai na maida shi mazaunin shi tamkar ban girka komai ba,sai bai bi takaina ba samun guri guda ya yi yana sakace da tooth pick sai gyasa yake jerowa a jajjere,daurewa na yi na je na same shi na mi shi sannu da zuwa amma ci kan ki bai ce min ba Ganin haka yasa na kama kaina na bi lafiyar gado Dan matuƙar mutun na son ƴanci to fa dole yaga vadaidai ba.
Cikin kwana biyu na hana kaina sukuni har sai da na tabbatar na musu aiki na bajinta wanda duk wanda ya gani zai yaba ina kammalawa na goge sannan na hau Whatsapp na sanar musu aikuwa a ranar suka rankayo dan sun matsu su ga kayan su babban tsoron su kar in ɓata musu zani,

Sai dai bisa ga mamakina sun yaba fiye da tunanin mai tunani nan na dinga hamdala a cikin zuciyata har suka biyani cikon kuɗina tare da min alƙawarin kawo wasu gobe idan mai duka ya kaimu.

Suna ficewa na danna ma ƙanina kira in da na bashi dubu goman cancat domin ya sayo ma kan shi yadi da sauran ƙannena mata turmin atamfa biyu domin rufa ma kanmu asiri,

Sauran kuɗin na mishi lissafin roll ɗin Milo guda dana madara milky domin in raba biyu ya kaima mahaifina sauran canjin kuma ya dawo min da shi dan in riƙe a hannuna.

Fitar shi ke da wuya sai ga Uztazu ya faɗo cikin ɗakin yana haki"Ina kuɗin ɗinkin?"

Na yi shiru saboda yanayin shi kaɗai na kalla na san ina buɗe baki ba alhairi ne zai fito daga bakina ba,

Ina miki magana kin min banza dan kin maisheni ɗan iska"ya furta hakan a fusace,

Ka yi hakuri gani na yi baka bani ajiyar kuɗi ba shiyasa ka ji na maka shiru, kuɗin ɗinki kuma tuni na aika kasuwa a sayo ma marayun ƙannena kayan zuwa idi."

Nan kika fi ƙauri wajen iya zance amma ki taimaka ma mijinki da bashi da shi kin kasa bayan kin fi kowa sanin da arzikin Nana Khadijah addinin Allah ya kafu a Makka."

Dariya kalaman shi ya bani sannan na ce"Tabbas haka ne amma ya ka ji kissar farin jakada ɗan Aminatu ɗan Abdullahi Muhammadur-rasulullahi?"

Shiru ya min dan ya san ya ɓallo ma kan shi ruwa jin ya yi shiru yasa na ce"Ba ka ji sanadin tafiya fatauci da Manzon tsira ke zuwa ma Nana Khadijah ba suka haɗu da shi ba saboda yaba ma ƙwazon shi?"

Tabbas rayuwar ma'aiki ya ishe mu yin gadara saboda ya zo mana da komai dan haka Noor ka ƙara zage dantse sam kar ka yarda Sunna ta wannan ɓangaren(Sana'a)ka samu tawaya,ko ba ka ji yanda abin koyinmu yafi kowa kula da matan shi ba ne duk da yafi kowa yafi komai?"

Na ji kuma tun kafin ki je islamiyya na san da hakan kawai ki bani kuɗi mu kwashi girki yau kamar yanda kika alƙawaranta mana."

Ban yi alƙawari ba in ma na yi na fasa dan haka ka fita ka nemo mana abin da zamuci tun kafin in ɗauki kwaƙwaran mataki a kanka.

Ki ɗauka kawai ina ganin hakan zai fi dan Ni kaina na gaji da zama dake.

Haka ka ce?

Eh nan take na fara kakkauda kayana dake waje na kintsa su tsaf a ɗaki,zumbulelen hijabina na janyo sai ........



*I AM so sorry masu jiran page ɗin safe,rashin wuta ya mana katutu wannan ma a inji na samu na sa fatan kun sha ruwa lafiya, Allah ya karɓi ibadunmu*




Ummu-jidda.

FIRST RAMADAN WITH  HABIBI.

  💔Heart touching story.💔




FARIDAT HUSAIN MSHELIA (UMMU-JIDDA).

*ZAFAFA WRITERS ASSOCIATION*

https://chat.whatsapp.com/H16N47YvbD60SKUCaNRF6Z

TSARABAN RAMADAN.
*"Kowacce rana da Allah ya halitta tana cewa:" Ya ɗan adam kayi amfani dani watakila bazaka rayu zuwa wani yinin ba, kowane dare da Allah ya halitta yana cewa: "Ya ɗan adam kayi amfani dani watakila bazaka ƙara kaiwa wani daren ba".*


LAMBA NA SHA SHIDA.
DIYAN HABIBI.
Wal!haka na yi tozali da kayan abinci tamkar a mafarki hadda buhun irish a ciki ga kiret ɗin ƙwai,cabbage, karas, green pearls da kayan marmari nan take na ruƙunƙune shi ina tsallen farinciki,

Hannuna ya kama muka taho falo na kwantar da kaina a jikin kafaɗar shi na ce"Habibi na rasa da wace irin kalma zan maka godiya ma Billah, because kana sani farinciki ta kowani fanni,fatana dai Allah ya cigaba da wanzar da soyayya da ƙauna a rayuwarmu."

Ƙayataccen

Please Login or Register in order to submit comment