Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

maganar"Yi in yi maka"ba ne yanzu,

Duk a tanajin shi sahoor zai yi da abincin DIYAN HABIBI dan haka ya ɓata rai,Ni kuwa da murna na na tarbe shi sannu da zuwa ɗauke a bakina,

Ciki-ciki ya amsa min sannan ya ce"Da fatan kin sha ruwa lafiya?"

"Alhamdulillah amma ban ci komai ba bayan ruwa."

Wani irin mugun kallo..........
   (Assalamu alaikum, wannan labarin na Hakeema jan hankali ne ga ƴanmata masu zurfafawa a kan aƙida ban yi shi dan cin fuskar wani ko wata ba,hasalima abinda idona ne ya gani na rubuta saboda haka idan ya yi daidai da rayuwar ki ko na wani ku min afuwa,A kowace aƙida da muke da su a addinin musulunci akwai nagari akwai na banza shi ne abinda nake son yin jan hankali a kai tare da nuna muhimmancin sana'a a cikin rayuwar aure Na gode.)

HABIBI.
Kuwa ya kasa zaune ya kasa tsaye sabo da ran shi in ya yi dubu ya ɓaci,sai maimaita Headline ɗin da yaga abokanan shi wanda suka yi fushi akan gayyato su buɗa baki da ya yi yake yi"MUN GA GIRKI GANIN IDON MU GURIN AMARYAR HABIBI."
  A akwatin gurin aje bayanai(Comments)kuma shaguɓe ne kala-kala ake yi ana tagging ɗin sa,ayayin da kuma posting ɗin Farrah ya karaɗe sosai media sai Yaga sun sa daga gani wannan hukuncin Kwamared ne ga Amaryarsa,nan take ya ji fushin shi na ƙara hauhawa tabbas ya ɗebo ruwan dafa kan sa ji ya yi zuciyarsa na zafi ga zagin da Farrah ta dinga aiko masa yana masa amsa kuwwa a cikin kunnen shi,jin kan shi na niyyar tarwatsewa yasa ya fara ambaton Allah sai dai tun kafin nutsuwa ya game da jikin shi yaji muryan sirikar shi tana ƙwala mi shi kira tamkar maƙoshinta zai fita MASHAKURU!

Ya yi saurin dafe kunnuwan shi tare da afkawa a cikin dogon tunani wato hukuncin da ya yanke akan Farrah shi ne har ta ƙira mara mutuncin mahaifiyarta gidan shi har ta mance ɗauki ba daɗin da aka yi tsakanin shi da ita kafin auren su dan ita sam bata so auren ba ta so Farrah ta auri mai dukiya ne ba Kwamared kamar shi ba wanda da ke riƙe da kwali ba fus tunda  ingantaccen aiki ya gagara,

Wani ƙara ƙiran sunan na shi ta yi a hassale ta ce"Mashakuru ka fito dan na san kana jina,Ka fito in rama ma ɗiyata dukan da kamata mugu azzalumi kawai,ina dalili ina mafari daga baka yarinya ka mata wannan mummunan aikin,wannan ai rashin sanin haƙƙin mace ne dan haka ka fito ka bata takardan sakinta ko kuma mu dangana lamarin da police station, kai wallahi idan ya gagara ma har Human right sai na kaika dan Ni na san mutuncin ƴata."

"Yo banda sanin darajar mace ta ya ya gandamemen kamar ka zaka zage ƙwanji ka zane min ɗiya kamar wata dabba........"bai kai ga jin ƙarashen zancen ta ba ya fara Kokawada zuciyar shi akan ya fito ko kar ya fito sai dai ɗayan ɓarin zuciyar tafi ƙarfi a kansa na ya fita ayi duk wacce ma za'ayi dan haka ya nufi bakin ƙofar ɗakin wanda Farrah ke bubbugata kamar zata karyata,

Wayar shi ce ta yi ƙara dan haka ya juya ya ɗakko shi ganin mai ƙiran yasa ya ɗaga da gaggawa a hanzarce ya ce"Abbiy ka zo ka fitar Ammin Farrah daga gidana dan Allah."

Da "To"ya amsa nan take ya ci burki ya yi baya ya dumfari gidan sirikin na shi da matuƙar sauri,

Ihun Farrah da masifar Amminta kaɗai yake jiyowa tun daga ƙofar get ɗin gidan,dan haka jikin shi na rawa har baya ganin gaban shi ya afka cikin falon kamar zai kifu, tamkar mahaukaci haka ya isa gurin Ammin Farrah ya janyo ta tare da sauke mata yatsu biyar akan ƙonanniyar fuskarta da man bilicin duk ya gama siɗewa,A firgice Farrah ta dakata daga bugun ƙofar da take yi falon ya yi tsit tamkar ruwa ya cinye ma'abota cikin shi,

Jin shirun yasa Mashkur (HABIBI)ya buɗe ƙofan ɗakin jikin shi duk a sanyaye dan tabbas ya ji ƙarar marin da sirikin shi ya sauke ma matar shi wacce takaici, mamaki da ta'ajjubin marinta da mijin da ta raina yasa tayi mutuwar tsaye sai dai ganin shigowar Mashkur ya sa......

Tabbas na ga ruwan comments da madaran ƙauna gareku masoya wannan littafin,ina roƙon mai kowa mai komai ya sa littafin ya amfanar da ni daku gaba-daya,ya sa Amaren FIRST RAMADAN WITH HABIBI su ɗau darasi,wacce bata yi haukar da farrah ta yi ba dan Allah kar ta jaraba irin kalan girke-girken banza da wofin nan ta yi na masu hankali, wacce kuma ta yi oga ya yaba sai ta ƙara ɗamara, dangane da illar zaɓen mace ko miji nagari kuma ga shi duk muna gani a cikin wannan littafi Mai albarka.




Mu je zuwa shin Ammin Farrah shaƙe HABIBI za ta yi?









Ummu-jidda.

FIRST RAMADAN WITH HABIBI.
  💔Heart touching story.💔


https://chat.whatsapp.com/LM4sMyc4lT5Jgnv9lw1vOS

FARIDAT HUSAIN MSHELIA (UMMU-JIDDA).

TSARABAN RAMADAN.
Manzon *Allah* (SAW) yana cewa:

(تسحروا فان في السحور بركة)

*“Lallai ku yi sahur saboda acikin yin sahur akwai albarka”.*

[Bukhari].

LAMBA NA BAKWAI.
HAKEEMA.
Wani irin mugun kallo Uztazuna ya bini da shi sai dai ganin yanda na langwaɓar da wuya ya sa yaji wani tausayina ya kama shi amma sai ya dake ya ce"Ittaƙillaha ya Uztaziyya ko dai dan kin ganni da Gara."

Ji na yi raina ya ɓaci amma sai na danne cikin muryan shagwaɓa na ce"To mai ka bar min da zan ci Fisabilillahi ya Uztaz ummm, har kana wani in ji tsoron Allah."

Dage kafaɗa ya yi cikin nuna halin ko in kula ya ce"Allah dai ya so ba gidana ne kaɗai ake rasa abincin ci ba har gidan Annabi an sha yin kwana da kwanaki ba'a ɗaura sanwa ba haka ma gidan Sahabbai na san baki manta da ayar da ta sauka akan Imam Ali Bin Abi Thalib ba da matar shi."

"Ban mance ba tabbas amma misalin da ka kawo na gidan ma'aiki ba sam ba haka abin yake ba,Annabin rahama mai neman na kan sa ne kuma  ayar Haƙuri da jarawabawa take nunawa wanda hatta a gidan ma'aiki an rasa abin ci amma ba dan bai je nemowa ba,na gidan Imam Ali kuwa ayar koyar da sadaukarwa da falalar ciyar da miskinai take  amma kai naka ya banbanta dan baka fita ka nema ba ma balle ka ce ka rasa kai dai kawai ka kama sana'a ya  Uztaz."ina dire maganata ban ko kalli gefen da yake ba na raɓa ta kusa da shi na shige na ɗakko faranti da cokali na duƙa na fara zuba abincin da ke cikin basket ɗin,shaƙe farantin na yi taf tare da sa Coslow ɗin a gefe kafin na buɗe kular source ɗin,anan ya yi wani irin tsalle sai ga shi a gabana ya dafe kulan,abin dariya ya so bani amma takaicin shi ya hanani darawar,

"Kawo in sa miki da kaina."

sake mi shi kular na yi yasa min yankan nama ɗaya  tare da tarfo min source ɗin akai,miƙo min filet ɗin ya yi yana janyo min hadisin raba ciki gida uku dan shi a haukar shi na yi zari(sam bai tunano yanda ya je ya take nashi cikin ba hadda riƙo extra.)

Gyara zama na yi ina cin abincin ina tuno makomar rayuwata sai dai samun matsaya akan wata shawara da zuciyata ta bani yasa na ji na gamsu dan haka murmushi ya suɓuce min,

Cin abinci nake yi ina murmushi, Uztazuna kuwa sai suɗe kwanon da ya zuba source ɗin nan yake yana zare ido,jin yanda ƙamshin miyar duk ta cika masa ciki ya sa ya miƙa hannu domin ɗakko kula,nan take wata farar takarda ta faɗo ƙasa ya yi saurin buɗeta ya ga an ya fara karantata.
"Matar Uztazu Barka da shan ruwa,ga ɗaya daga cikin girkin ƴan group ɗin first Ramadan with HABIBI nan ki ci ki ji,santi sosai mijinki yake yi hadda yin Take-away,to ya ci albarkacin ki na zubo dan ki ci,muma sai mun zo cin girkin matar Uztazu."
   Farrah Diyan Habibi.

Gumi ne ya ji yana tsatstsafo mi shi tsabar ruɗewa,karatun yake a cikin zuciyar shi amma ya fito fili dan haka ina kammala cin nawa abincin na ce"ka ji dai saƙon Farrah ko ashe ma abincin nawa ne har ka ke min rowa."

Kame-kame ya fara na sa ɗan yatsana akan bakina alamun ya yi shiru cikin murya mai sanyi na ce"Kayan Allah ai na Annabi ne Noor fatana dai zaka koma shagon da kake tsare musu littafan nan dan kar abinda zamu ci ya dinga gagarar mu dan Allah."

Tsam ya tashi ya shige ɗaki Ni kuwa na buɗe data na hau online dan fara gabatar da shirina.

GIDAN HABIBI.
Mamaki da ta'ajjubin marinta da mijin da ta raina yasa tayi mutuwar tsaye sai dai ganin shigowar Mashkur ya fito yasa ta ji ta wartsake,amma hango yanda ya haɗe girar sama da ta ƙasa ya sa ta ji ya mata kwarjini dan haka ta juyo bangaren mijina ya ce"Ka mareni a kan gaskiyata?"

Shiru ya mata tare da jan hannun Farrah dana Mashkur ya ja su zuwa cikin falon,yana isa tsakiyar falon ya sake hannun na su tare da yi musu nuni da hannu akan su zauna,

Ba musu suka zauna akan maidaidaicin carpet ɗin da ke shimfiɗe a tsakiyar falon sai dai sun bama juna matuƙar tazara saboda haushin juna da suke ji,

Me ya faru tsakaninki da mijinki Farrah har kika yi ƙiran mahaifiyarki?"

Dukan tsiya ya lakaɗa ma........."

Dakata Malama sunan ki ne Farrah"ce War Abbiy wanda ya yi saurin dakatar da Ammi wanda ta karaso cikin falon tana cika tana batsewa,

Tsit ta yi saboda ganin yanayin shi,

Ina jinki Farrah."kuka ta fashe da shi sannan ta fara shiryo ƙarya da gaskiya ta faɗa ma Mahaifinnata,

Mamanta sai gyada kai take tana ce wa"Ka ji baƙin zaluncin na shi ko"sai ta yi kwafa tana jin kamar ta tashi ta shaƙo wuyar shi ya mutu kowa ma ya huta dan takaici,

Uffan Mashkur bai ce ma har sai da Abbiy ya jeho masa tambaya da ce wa"Haka aka yi Mashkur?"bayan Farrah ta gama shimfiɗo zancenta kenan,

"A'a Abbiy kai shaida ne akan abinda ta aikata min a ranar farko na watan Ramadan idonka ya ga komai kuma ka ji hukuncin da na ce zan ɗauka."

Cike da gamsuwa ya ce"Eh hakane tabbas."

To ban ɗau hukuncin ba gata nan ka tambayeta sai........nan HABIBI ya feɗe biri har wutsiyar shi,ya faɗi sanadiyyar da yasa ya duketa Abbiy banda faɗin"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un"da yake yi yana maimaitawa ba abin da yake ce wa,

Jin Mashkur ya yi shiru alamun ya gama yasa ya ce"Tabbas ka yi hakuri ma da baka turo min ita gida ba duk kalar rashin tarbiyyar nan da ta nuna maka ka yi hakuri dan Allah,ina baka haƙuri a matsayina na mahaifinta da matsayina na uba a gareka ka yi hakuri ka ji."

Na yi Abbiy nima a yi haƙuri da ni ga hukuncin da na yanke a kanta duk a cikin fushi ne sharrin shaiɗan ne,


Ba wani sharrin shaidan Malam dan kaine babban shaiɗanin,shaiɗanu ai a ɗaure suke tunda muka shigo cikin watan Ramadana, kawai dai ka yi abinda kake so ka zalunci yarinyata,so what dan ta kai magananka social media an tattauna matsalar ku baka gode ba ma kun zama cele,ko ka san shekaru nawa Farrah ta ɗauka tana cin burin ganin ta nuna bajintar ta ga mijinta a cikin watan Ramadan?

Ita ce ta fara buɗe group a Whatsapp na FIRST RAMADAN WITH HABIBI tana kawo ma classic ladies zafafan girke-girke na gida dana ƙetare kawai dan ta gwada akan mijinta shikenan an samu mishkila shine zaka tasa min ita a gaba ka duka kamar ka samu jaka?

To ahir ɗin ka This should be the last warning da zan maka akan taɓa lafiyar ɗiyata in ka ki ji wallahi hukuma ce zata rabani da kai."

Kin ji kunya, matuƙar kunya A'isha(Ammin Farrah)saboda matuƙar haka za ki ci gaba da yi ma yaƴanki mata to tabbas baki so zaman su a gidan miji ba kuma a irin al'ada irin tamu ta bahaushe zaki bar musu abin gori ƴaƴa da jikoki,tir da irin wannan halayyar naki ta rashin kara da sanin ya kamata ke ga ƴar boko mai kokawa da ilimin addini,

So what dan ka ce haka"Ni dai na faɗa maka aure ne kuma tsakanin Farrah da Mashkur ya ƙare dukan da ya mata ya daki auren shi Billahi dan haka tashi mu je."

Ba tare da tunanin komai ba Farrah ta ce"Ina son mijina Ammi."jin haka ya sa ta fara masifa kamar zata ari baki ganin ba wanda ya kulata ya sa ta fice tana bin Farrah da mugun kallo.

"Allah ya miki albarka" shi ne kalmar da ta fito daga bakin Abbiy,HABIBI ma wani sassanyar kallo ya bini da shi wanda duk ɓacin ran da yake ciki ya ji ya wanku Ni kuwa na ce tsakanin mata da miji ai da man sai Allah,

Nasiha mai ratsa jiki ne Abbiy ya fara yi min kafin ya dawo kan HABIBI ya mi shi tashi nan take aka rufe taron da addu'a sai dai Abbiy na wucewa na shige ɗaki a guje na rufe tare da cin alwashin sai na gasa ma HABIBI aya a hannu matuƙar ina raye,bai daki banza ba.


To fah Fans kun ji wata sabuwa fa a ɗaukata mutuniyar taku ta yi hankali.








Ummu-jidda.

FIRST RAMADAN WITH  HABIBI.
  💔Heart touching story.💔


https://chat.whatsapp.com/H16N47YvbD60SKUCaNRF6Z

FARIDAT HUSAIN MSHELIA (UMMU-JIDDA).


TSARABAN RAMADAN.
*Kuskuren Musulmi Game da Azumi*
  *Shi ne yin buɗa baki da abin da Allah ya haramta kamar abin da ke sa maye, wiwi, hodar iblis, sigari, ko kuma shi sha, da sauran su.*

LAMBA NA TAKWAS.
Nasiha mai ratsa jiki ne Abbiy ya fara yi min kafin ya dawo kan HABIBI ya mi shi tashi nan take aka rufe taron da addu'a sai dai Abbiy na wucewa na shige ɗaki a guje na rufe tare da cin alwashin sai na gasa ma HABIBI aya a hannu matuƙar ina raye,bai daki banza ba.

Wayata na ɗaga na dinga jera ma Ammina ƙira amma sam bata ɗaga ba sanin na yi matuƙar ɓata mata rai tare da kunyata ta a idon su Abbiy da HABIBI ya sa na rubuta mata text message kamar haka"Ba umurninki naƙi bi ba ya Ammi face son in koyar da Mashkur darasin da bai taɓa riska ba a rayuwar shi,mace mai aji bata yaji haka kika sha faɗa min a kullu-yaumin, ƙasaitacciyar mace ita ce mai zama cikin gidanta har sai ta hora mijinta akan laifin da ya mata,tabbas Mashkur zai fuskanci hukuncin da ya fi dukan da ya mini da wanda Abbiy ya maki a kan shi,na rantse da Ubangiji sai na gwada ma shi nononki na tsotsa,Sai na gasa ma shi gyaɗa a hannu tabbas sai ya gwammace kiɗa da karatu trust me ny First love."

Tura saƙon na yi ina addu'ar Allah ya sa ta buɗe ta karanta aikuwa yana shiga ta duba,wani murmushin kashe Boss ta yi cikin zuciyarta ta ce"Tabbas ƴar halak na haifa"
Dan haka ta ji kaso cassa'in na ɓacin ran da take ciki ya tafi dan ta san Farrah will make it,she will make sure ta mi shi discipline ɗin da sai ya gwammace kiɗa da karatu dan haka ta tuɓe kayanta ta shige cikin bayi ranta fess dan ta san wacece Farrah.

HABIBI kuwa ji ya yi ƙafafun shi sun yi sanyi da buga ƙofar da DIYAN SHi ta yi dan da lalurar buƙatar matar shi ya yini ɓacin ran da ta sanya shi a ciki ya sa ya mance da damuwar shi ma, sai dai yaji wani irin soyayyarta ya mamaye jiki da ruhinshi yayinda ta ƙi bin umurnin da mahaifiyarta ta bata,ya ji ta cancanci yafiya dangane da duk wani laifi da ta aikata a gareshi,ya fahimci tarbiyyar mahaifiyarta ne a haka,ita ke ɗaurata a kan keken ɓera na koyi da rayuwar yahudawa tunda ya ga har alfahari take da yanda Diyah ta iya handling case ɗin ta ba sai da ta kai mata ƙara ba,aiki ne tuƙuru a gareshi na koyar da Diyah yanda zasu rayu cikin aure bisa ga turban addinin musulunci ya shimfiɗa dan haka kai tsaye ya koma ɗakin shi ya yi wanka tare da sa farin singelet da sabon boxer,sabuwar jallabiyya mai ruwan zuma ya ɗauro tare da zura shi a jiki a murɗaɗɗen surar shi,ya fesa turaren shi mai sanyin ƙamshi na Black oud,spare key ya ɗauka tare da dosar ƙofar ɗakin da Diyan shi take,a daidai wannan lokacin na fito daga wanka jikina duk ya yi tsami saboda bugun da nasha, sosai na gaggasa jikina tare da zura rigar bacci na ɗale kan gado ina jin zazzaɓi na niyyar kamani,ko minti biyar ban 0
yi da kwanciya ba na ji ana ƙoƙarin buɗe ƙofar da nake ciki tare da tattaɓa shi,wani munafikin murmushi ne ya suɓuce min dan na san na bar key a jikin ƙofar so duk ƙoƙarin HABIBI na son ya buɗe ƙofar sam  keyn ba zai shiga ba tunda da wani a ciki dan haka ya fara ƙwala min kira cikin murya mai sanyi,

Jin shiru ban amsa ba yasa ya ɗauka ko bacci na yi dan haka ya fara bubbuga ƙofar yanda na ke tunanin zai ji amma sai yaji ɗiff,shiru ba ko alamun mai rai na kwance a ƙarƙashin rufin ɗakin,ji ya yi ya fara gajiya dan a bukace yake da DIYANSA dan haka cikin sauri ya hau bubbuga ƙofar irin bugun haukar nan,ban san lokacin da wani munafikin murmushi ya suɓuce min ba dan haka cikin farin ciki na sakko da ƙafafuwana ƙasa dan tsabar farinciki ji na yi zazzaɓin ma ya sauka na nufi bakin ƙofar cikin azama,

Cikin kasalalliyar murya da sigar janyo hankalin shi gareni na ce"HA....BI....BI....."

"Na'am, Please open the door Diya,i need youuuuu"ya ƙara sa maganan yana jan kalmar ƙarshen cikin sigar da ke nuna a buƙace ya ke dani,

Dariyar shaƙiyanci na fashe da shi yanda nake da tabbacin zai jini ka fin na ce"Bakaji mai Ammi ta ce bane HABIBI?."

"A'ahhhh Diya dan Allah kar ki hukunta ni ta wannan fuskar zaki janyo ma kan ki fushin Allah dana Mala'iku."

Bravo!Kwamared Habibi,tabbas ka yi kyan kai daka gane hakan kai kuma dukan da kayi min kana tunanin lada Angels ɗin suka rubuta maka ne?, wannan shine ladan dukan da kayi min ai baka daki banza ba Billah."

Ji ya yi kamar ya fashe da kuka sai dai ya daure ya ce"Ok ki dafa kayanki ki ci Farrah,ba dai Ni zaki wulaƙanta a cikin wannan wata mai alfarma ba?

Na ba banza ajiyarsa dan haka na jingina da jikin ƙofar ɗakin yanda har ina iya juyo nishin wahalar da yake fesar wa amma ko a jikina dan yanda bai tausaya min a matsayina na mace ba ya dukeni she deserved such punishment daga gareni,

Zufa ce ya gama wanke mi shi jiki har yana ɗiga muryan shi yana kyarma ya ce"da man soyayyar da kika ce kina min ashe ta ƙarya ce to zan fita kuma duk in da naje na kai kaina ke kika janyo."Dan haka cikin azama na ji takun shi yana ciccira ya fita,

Komawa kan gadona na yi na lulluɓa farinciki kwance a fuskata, sai jin tashin motarsa na yi daga harabar cikin gidan ya sa na ji wani irin tashin hankali ya ziyarce ni,zumbur na miƙe jin wani irin tashin hankali ya ziyarce ni lokaci guda nan da nan na fara kaikawo tsakanin gaban gado da ƙofar ɗakin,tunanin gurin da zai je na fara yi tsabar tashin hankalin da na shiga,

Zuciya da saka kuwa ta raɗamin gurin ƴan good evening(Ƙaruwai)domin su biya mi shi buƙatar shi.

HAKEEMA.
Tsam ya tashi ya shige ɗaki Ni kuwa na buɗe data na hau online dan fara gabatar da shirina.

Group ɗin mu na FIRST RAMADAN WITH HABIBI na shiga,group ɗin da na san ya tara classic ladies masu ji da kan su na fara tallata hajata ta ɗinki,tela ce ni ta mata kuma babu wani ɗinki da za'a kawo min wanda zai iya gagarata dan haka na kwaso zafafan style daga instgram na watso shi cikin group,nan take suka ruɗe dan duk yawancin su ƴaƴan manya ne kuma mata ne masu son kece raini sam basa son aga gazawar su dan haka suka fara selecting kowacce burinta ta zaɓi daidai da kalar jikinta wanda zai fiddata,duk da ba wani faɗa aji nake da shi a group ɗin ba amma tallata musu hajata da na yi akan su kawo ɗinkin Sallah zan musu kuma duk wacce na ɓata ma kaya zan biyata tabbacin su san na san kai aikina sai duka hankalinsu ya dawo kaina take yanke na samu kostoma guda 2 suka karɓi address ɗina akan za su kawo min ɗinki in fara gwada wa a kan su kafin sauran su kawo na sallarsu,

Da man inada keken ɗinkina wanda Abba ya siya min kuma tun ina budurwa sana'ata kenan har ma inada yara yan koyon aiki,dalilin da yasa ƴan First Ramadan with HABIBI ba su Sanni da shi ba shine bayan gama candyn mu na ƙware har na fara yin na kuɗi,su kuma tun a Sakandire muka rabu suka cigaba da karatu tunda ƴaƴan masu ƙumba da susa ne Ni ce kaɗai ƴar gidan malam Shehu,

Samun waɗannan kostoma ya faranta raina matuƙa gaya kuma shawarar da zuciyata ta bani tabbas ta min aiki dan haka na fita  a group su kuwa suka ci gaba da tattauna zancen girke-girken da za su yi gobe dan su nan suka fi auki tare da bada labarin yanda mijin ke ɗoki wanda yawancin su ƙarya ne kawai suke sharara ma junansu dan a cikin su akwai wacce ko tukunya bata iya ɗaurawa ba ƴar aikinta ne ke mata komai,Ni kuwa status na koma na yi posting tare da tura ma duk group ɗin da nake ciki a Whatsapp sannan na koma Facebook na sa hotunan ɗinki tare da nuna sana'ata ma duniya cike da alfahari,nasa sunan gari da sunana,numban waya ce kawai na ɓoye gudun janyo ma kaina matsala.

Sauka na yi farinciki ɗauke a fuskata dan haka na shiga cikin ɗaki gurin Uztazuna sai dai me samun shi na yi ya cika ya yi fam kamar gasashshiyar buredin da ya ƙone,

Yana ganina ya ƙara haɗe girar sama da ta ƙasa nan da nan na ji gwiywowina sun yi sanyi akan daddaɗan albishir da na zo mi shi da shi cikin sanyi na ce"Allah ya huci ran Maigidana na barka kai kaɗai ko?"

Taɓe baki ya yi cikin son cusa min haushi ya ce.........

To fah ta Uztazu ya dai lamarin naku ne yake tafiya a baibai ko dai da sa hannun ƴan group ɗin First Ramadan with HABIBI ne ba mu sani ba?dan na ga kafi kowa baƙin jini lolz.

Ina masu goyon bayan HABIBI akan hukuncin da ya yanke i mean (Team HABIBI)Da masu goyon bayan Farrah
(Team Farrah) su waye da nasara ne a wannan page ɗin?

Mu je zuwa.




Ummu-jidda ce.

FIRST RAMADAN WITH  HABIBI.
  💔Heart touching story.💔


https://chat.whatsapp.com/H16N47YvbD60SKUCaNRF6Z

FARIDAT HUSAIN MSHELIA (UMMU-JIDDA).

TSARABAN RAMADAN.
*Kuskuren Musulmi Game da Azumi.*
Ƙirƙiro tafiya zuwa wani gari ba tare da wata buƙata ba ko wani dalili, kawai don an halartawa matafiya ajiye Azumi a halin tafiya, har ma ya kafa hujja cewa ai shi matafiyi ne, wannan kuma baya halatta.

*Allah ya karɓi Ibadunmu*




LAMBA NA TARA.
Zuciya da saka kuwa ta raɗamin gurin ƴan good evening(Ƙaruwai)ya tafi domin su biya mi shi buƙatar shi tamkar mahaukaciya haka na dawo nan take na fara kokawa da ƙofa a niyyata in buɗe in fita amma tsabar kyarma da hannuna yake yi ƙofar taƙi buɗuwa sai jujjuya mabuɗin na ke yi tamkar ƙaramar yarinya,

Can dai Allah ya bani ikon buɗe ƙofar ɗakin na fita a guje zuwa sashinshi,lalleƙa lungu da saƙon sassan na yi ban hangi ko ƙurar shi ba nan take na gasgata zancen da zuciyata ke yi na ya tafi zuwa ga biyan buƙatar shi a gurin wata mace ba Ni ba,

Kuka na fashe da shi ina jin wani irin kishi na sukata a ƙarƙashin zuciyata,nan take na fice a cikin hayyacina dan da gaske ina son HABIBI da zuciya da gangan jiki kai har ma da ruhina kuma ba na jin baƙin kishi zai iya barina in zauna da kishiya ma balle wata a waje,danasi na fara mara amfani dan da na san wannan hukuncin dana yanke zai janyo min shiga wannan halin tabbas da ban ɗauki shawarar zuciyata ba,nan na shiga tufka da warwara idona kafe a kan agogon dake manne a jikin bangon ɗakin ina bin kowani sakan da

Please Login or Register in order to submit comment