Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ma wani haske da cika daya sani,a sabon gidan mu mai kama da wata masarauta a Dubai tsabar tsaruwa muka tare in da Farrah ta fara kawo min ziyara, rumgumar juna muka yi Ni da ita hawaye kwance akan fuskar mu dukkaninmu rayuwar mu ta baya muke tunawa, Uztaz da Habibi da suka shigo hannayensu cikin na juna dariya suke mana,sai dai Hakima hawaye yaƙi barin fuskarta har sai da Uztazu ya fara yi mata nasiha cikin daddaɗan murya sannan ta shagwaɓe fuska ta ce"Naƙi yin shirun har sai ka fadamin."ta fashe da wani irin kukan tabara take jikin shi ya fara rawa a diririce ya ce"me kike son in faɗa maki?",

"Wanda ya koya maka basajar zama Uztaz." Dukkanin mu dariya muka fashe da shi dan Ni har ga Allah na ɗauka wani abin ne na daban ta ruɗa ɗan talikin nan a gaban idonmu ko kunyar Habibi bata ji ba,

Ganin tana niyyar fashe mi shi da wani kukan ya sa ya ce"Wait my lady Please kar ki  koya ma yarona rigima Ni kam,zan faɗa miki."Murmushi ta yi bayan ta bamu guri mun zazzauna haɗe da abin sha ya ce"Daman dai sunana ne Social Uztaz kamar yanda ki ka ji abokaina na ƙirana da shi saboda na tsani duk wata saɓon Allah duk da kasancewata shahararren ɗan boko dake na ƙoshi da ilimin addini yasa duk wata wayewa ta Bature na san koma bayan namu ne dan haka a komai nawa Addinin Musulunci a gaba sam ban damu da akida ba,Ni dai kowace Aƙida kake a gurina in dai kai Musulmi ne zan yi aiki da kai dan haka sunan ya samo asali ne tun daga rayuwar mu ta jami'a, dangane da basajar da na miki kuwa na Uztazanci shiga cikin su na yi na gabatar ma babban Malaminku buƙatana nan take ya yi maraba da Ni ya rungume ni hannu bibbiyu,cikin kwana uku kacal na dawo yanda zaki so Ni larabci kuwa shine course ɗin da na fara karanta a jami'a dan haka ina jin shi fiye da tunaninki."

Ma sha Allah yanzu na ji magana amma da kullum Inna tambayeka sai dai ka yita kame-kame."dariya kawai muka yi nan muka fara sabon gaisuwa bayan mun nitsa muka gabatar da ayyukan da muka gudanar da basa nan suka gani,sun yaba da ƙwazonmu da Himmarmu dan haka bizar mu na tafiya China yana fitowa na yi ma HABIBI rakiya ya je ya yi odar kekuna,kujeru da duk abinda Fashion House da gidajen marayu zai buƙata acan cikin dake maƙale a marata ya bayyana in da tashin zuciya ya hanani zaune da tsaye,murna a wajen Habibi ba'a magana bayan mun zaga gari mun gagga wajaje muka biyo jirgi muka dawo ƙasar mu ta gado.
  Alhamdulillah cikin watanni ukun aka kammala ginin har gashi yau ana bikin buɗe Fashion House da gidan marayu,taro ya yi taro in da hadda mai girma gwamna sai da ya samu halartar bikin buɗe gidan Marayu mai suna"HAMSAL ORPHANAGE AND FARRAH FOUNDATION",Sarkin garinmu shine ya zama babban baƙo,manyan attajiri da masu hannu da shuni duk sun samu halartar bude Gidan marayu da GIDAUNIYAR da Farrah ta buɗe na tallafa ma gajiyayyu,an ci an sha zuciyoyin ilahirin Ahalin mu duk sun sanyaya,masu hannu da shuni da manyan yan kasuwa sun zuba hannun jari a HAMSAL(Hakima Bisallah) FASHION HOUSE dan kara mata karfin gwiywa akan ayyukan alhairin da ta yi,mai girma gwamna ya samar da nagartattun ma'aikata ma marayu na gidan dan akwai katafaren makarantar boko tun daga matakin Nursery har zuwa Sakandire da babban makarantar addini wanda ya tara manyan malamai,sai asibiti da Ammi ta zama babban likita Hajiya Amina kuma ta zama uwar Raino mai ba yara tarbiyya saboda sanyin halinta,tabbas labarin wannan taro wanda gidajen rediyo dana jaridu har ma dana talabijin ya ja hankalin mutanen arewacin ƙasar nan musamman yanda ƴan group ɗin first Ramadan with HABIBI suka gayyato manyan jaridun online aka watsa shi a media,Hajiya Farrah da Habibinta sun zamto abin kwatance a cikin al'umma yayinda HAMSAL da mijinta suka fi ƴan siyasa farinjini.

Tammat bi hamdillahi wa husni aunihi wassalatu wassalamu ala Mustapha Abul ƙasim Muhammadur-rasullullah, Muhammadur-rasullullah wa ala Alihi wa sahbihi wajma'in.
  Ina mai godiya ga Allah da ya bani ikon kammala rubuta wannan littafi Mai albarka,

JINJINA.
*Jinjina ga ɗaukacin marubuta na hannun damana Musamman Malamaina waɗanda idan sun ga kuskurena basa sanya gurin gyara min Oga Bamai dabuwa,Malam Mubarak Saulawa,MALAM JIBRIN RANO,Sarauniyar tsokana(Hajara Oum Nass)ina godiya a gareku Allah ya ƙara muku ɗaukaka da tarin nasarori.*

*Kakata Hadiza D Auta gaisuwarki ta musamman ce saboda kin tsaya tsayin daka hadda tare min faɗa akan rubutun wannan littafin Allah ya saka miki da alhairi ya kuma bar soyáyyá a tsakanin mu tabbas kina da kishin marubuta ƴan'uwank*i.

*Jarumar jarumai.*
*Sarauniyar jarumai writers wato Maman Amatullahi tabbas kin ciri tuta kin kasance abokiya mai ƙoƙarin ƙarfafa min gwiywa a duk inda na ji rauni,ina godiya da muhimman shawarwarinki wanda tabbas ba dan ke ba da tuni na ajiye rubutun wannan littafin Allah ya raya min yarana ya kuma sa musu albarka,fagen rubutu kuwa Allah ya kara basira da ɗaukaka*

USMAN IlIYASU MAJIDAƊI.
Ka kasance ƙashin bayana mai kara min karsashi a duk lokacin da na yi niyyar kwantawa tabbas kana ɗaya daga cikin sirrin nasarata Kandenmu,Ubangiji ya azurtaka da samun mata ta gari ya jiƙan Abba da Hajiyata ya kuma yalwata maka samunka ya shirya mana kai shirin addinin musulunci alfarman wannan wata mai albarka.

Kungiyata Abar alfahari na.
Jinjina gareku gabaɗayanku,shugaba Pinky Cutie,Dotana Jidda washa,Jikalle Hilfat,sirikata Matar Sayyadi, Shalelen....,FATIMA,Laurat da saurann duk waɗanda ban ambata ba ina godiya.

MARUBUTA.
Gareku Marubuta ina godiya da karfafa gwiywarku da juriya da bibiyata duk da raunina musamman S Fulani daddyn dota,Hajara,Rukayya Ibrahim Gazawa,Qamshi and co Allah ya saka da khairan ya kuma karbi ibadanmu.

Masu share.
Musamman Hajiya Maryam da babban admin na hairan and teddys palace ina godiya ɗan'uwana,Fatima Abubakar Saje da ma wadanda ban ambata ba jazakumullah.

*First Ramadan with HABIBI group 1 and 2*
  Kun ji jarumaina,masoyana,ƙawayena masu ƙara min ƙarfin gwiywa,tabbas yawanku ya yi yawan da ba zan iya ambatar sunayenku ba dan kar ku ce na yi son kai,kun dai san kanku dotas ɗina,ƙawayena,ƴan'uwana marubuta da sauran Fans ɗin a masu hana wayata motsi saboda hira,dukka ina yinku Fisabilillah, Allah ya barku da mazajenku har a aljanna ƴanmatan dake cikin gidan kuma Allah ya baku mazaje na gari.

HADIZA AUTA PALACE.
ƁARIN ZANCE......
TAWA SOYÁYYÁ...
JARUMAI.......da dukkanin group ɗin da littafin nan ke zagayawa ina sonku fisabilillahi,ƴar garinmu ina godiya, Amarya kuma Uwargidan Abban hydar (Malama Zeenatuddeen Musa)ban mance da ke ba da addu'arku nake taƙama,Muhd Sabi'u (Jauro)ina godiya da karamcinka tare da ɗan'uwsnka Fulani Abdul Faskari Allah ya bar zumuncin dake tsakanin mu har gaban abada.

KUNE A ƘARSHE.
Masu zagina saboda na yi typing a watan Ramadan,na yafe muku dan kune tushen nasarata Allah ya shirye Ni daku gabaɗaya.

Littafin First Ramadan with HABIBI sadaukarwa ne ga ruhin mahaifina da ruhin da ke kwance a ƙasa, Mahaifiyata dake rayuwa Aban ƙasa,Allah ya ƙara mata tsawon rai da lafiya mai albarka,Mahaifina kuma Allah ya jiƙan shi ya gafarta mishi.

A dalilin AUREN JARI matata wacce na aura saboda yi ma mahaifiyata biyayya Ita da abokaina SUN GUJE NI saboda cutar lakka dana kamu da ita sai dai kuma SANADIN FACEBOOK na haɗu na dubun dubatar masoya, ITA CE SILAH(WAYAR ANDROID) da ta zamto min fitila har na yi SOYAYYA LOKACIN KULLE(SOYAYYA A LOCKDOWN)sai dai na gagara gane LAIFIN SU WAYE tsakanin BESTYN MIJINA da danginsa,duk da dana yarda da MUTUNCINA YANCINA ne da ban watsa sirrina a social Media ba da ban zama shugaba a cikin  group ɗin Amaren First Ramadan with HABIBI ba har na zamto fitilar data haska rayuwar HAMSAL,danasi ya riskeni dana yi YAWON TA ZUBAR a ƙasa mai alfarma(Saudiyya)a cikin wata mai alfarma kuma a goman ƙarshe da sunan zuwa Tahajjud duk da na san  babban zunubi ne da ba zan yafe ma kaina ba.


To masoya gani gareku ɗauke da sabon salo cikin littafina mai suna YAWON TA ZUBAR  littafi ne da ya taɓo rayuwar yara mata ƴan talle da wadanda ake safarar su  zuwa Saudiyya aikatau domin samun abin duniya.shin kin shirya mallakar naki/naka akan yan'kudi ƙalilan?
To ku tsumayeni Ranar sallah zai zo muku a matsayin Barka da Sallah masoyana, dangane da BESTYN MIJINA Book 2 shima yana nan zuwar muku da yardan Allah sai dai book 2 paid book ne,maza garzayo ka nemi na farko in baka karantaba ba domin cigaban shi na nan tafe,taku ce har kullum Ummu-jidda.





Ummu-jidda.

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment