Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da ɓacin ransa ba suka fara hasalla zuciyarsa. Ya ji ya kawo wuya. Duk da shi bai cika saurin fushi da saurin kai hannu ba irin na Mu'az ba. Amma yau dai kam yana jin Mariya ta kai shi bango.

“Na farko kin aikata min laifin fita daga gidana ba tare da izinina ba. Na biyu kin fita kin bar min ɗa a gida shi...”

Bai kai aya ba Mariya ta katse shi.

“Wai ni a kanka aka fara haihuwa? Magana ɗaya biyu sai ka sako ta ɗanka a ciki? Ai ni ma ɗana ne, ba shegensa na yo a waje ba!...”

Ba ta rufe bakinta ba ta ji sauƙar mari a kuncinta na dama. Lalle yau ta ƙure Faruk har wuya, tun da yake bai taɓa ɗaga hannunsa a kan wata mace ba, ballantana matarsa ta auren sunnu, matar tasa ma Mariya, wadda yake jin sonta har cikin ransa.

Amma abin da ta aikata yau ya sa ba zai iya yafe mata ba kamar sauran kura-kurenta na baya. Ita ce da laifi, amma ji yanda take ɗaga masa murya kamar ita ce mijin, shi kuma matar.

“Ba ki isa ba Wallahi... Mary ba ki yi wannan tasirin a zuciyata ba da zai sa ki aikata min laifi, sannan ki zo kina ɗaga min murya na ƙyaleki...”

Mariya da mamaki ya sa ta sandare ta ci gaba da kallon fuskarsa da ta sauya mata lokaci guda. Ko dai ba Faruk ɗinta ba ne?. An yama kuwa wannan mijinta ne?... Har ya gama faɗansa ya ɗauki Hilal ya bar mata falon ba ta iya yin ko da tari ba.

Cike da jin haushin da bai gama washewa a ransa ba Faruk ya kwantar da Hilal a kan gado. Ya lulluɓe shi yana jin wani abu na baƙin ciki na tokare masa maƙoshi. Gaba ɗaya ma ya rasa yanda zai yi ya huta.


MAIMUNA POV.

Yau da matsanancin ciwon baya ta tashi. Amma duk da haka sai da ta yi duk ayyukan da suka zame mata wajibi a gidan. Tana yi tana kuka, saboda yau ciwon da take ji ya fi na kullum. Ta yi doyar safe. Ta je ta siyar, sanan ta fara haɗa kunun dare. Tana tsaka da tatar hatsin da ta karɓo a wurin niƙa Auwwa ta kirata.

“Ke Maimuna!”

Da ƙyar ta iya ɗaga yalayen idonta irin na masu sickler ta kalli Auwwan. Sannan ta amsa.

“Na'am”

“Zo!”

Da ƙyar ta iya miƙewa tsaye. Tana dafe da bayanta da yake matsanancin ciwo. Ta nufi inda Auwwa ke tsaye. Auwwa ta miƙa mata dubu uku, ta kai hannu ta karɓa.

“Kasuwa za ki zo ki tafi ki siyo min doya. Na ga sauran guda ɗaya!”

A take Maimuna ta ji ruwan dake zuba a idonta ya ƙara gudu. Dan haka ta ɗaga kai ta kalli Auwwa. Yanzu idan ba'a rage mata aikin dake kanta ba ai ba a ƙara mata ba. A yanayin jinyarta kwata-kwata ba'a son su shiga damuwa ko tashin hankali, dan hakan kan iya taɓa zuciyarsu kai tsaye. Amma a gidansu sam ba'a damu da hakan ba. Ɓacin rai kullum sai Auwwa ta kasa mata a fai-fai ta ɗauka.

“Ko ba za ki je ba ne?”

Ganin Auwwan na shirin ɗaukan madoki ya sa ta yi saurin girgiza kai.

“A'a zan je”

Ta rufe leɓenta ƙwalla na ƙara sauƙo mata. Ba tare da tace komai ba ta ja siraran ƙafafunta da ba su cika ƙwari da lafiya ba ta ɗauki hijabinta. Ta saka. Sannan ta fita waje tana kallon yanda rana ta baza duniya.

Da ace tana da gata da a mashin za ta je kasuwar. Amma a halin da take ciki na magen maƙota ma ta fita muhimmanci ba za ta samu wannan gatan ba. Ba komai take hasasowa ba face nisan dake tsakanin gidansu da kasuwa.

A abin hawa ma tafiyar ba kaɗan ba ce, ballantana kuma a ƙafa. Ga kuma yanda rana ta ƙwalle a sama, kamar ba lokacin hunturu ba, duk da sanyin ya fara ja baya. Ga ciwon baya ga na ƙafa, ga kuma na jiki da na zuci.

Haka ta ci gaba da daurewa tana tafiya. Idan ta gaji sai ta samu gefen hanya ta zauna ta huta, kafin ta tashi ta ci gaba da tafiya. Da haka har ta iso titin ƙofar fada. A nan ɗin ma sai da ta zauna ta huta. Tana ta haki, ga bayanta da take jin kamar zai karye.

Kuma idan aka raba tafiyarta biyu, ba ta ɗauki kashen ɗaya ba, sai dai a kirata da kwata. Hawaye ne ya zubo mata. Ta kai hannu ta share, sannan ta raba kanta da wannan hutun na jaki kaya a ka. Ta ci gaba da jan ƙafarta da ƙyar... Har ta hau kan titi a ƙoƙarinta na tsallakawa...

A dai-dai lokacin kuma wani mummunan haɗari ya faru, a tsakiyar titin, a tsakiyar gari, a tsakiyar jama'a da ma duk wani me wucewa.

*. *. *.

Gambo ne da uban gidansa, wato me napep ɗin da yake ba shi sojan haya. Suka ɗebo wasu fasinjoji mutum biyu. Gambo ya juya ya kalli ogansa yana faɗin.

“Oga ba na jin Auwwa za ta iya bada kuɗin nan... Ba ka san Auwwa ba ne, masifar son kuɗi gareta kamar me?”

Ogan ya yi murmushi.

“To ai shikenan. Sai ka yi ta zama a haka, kana hawa napep ɗin sojan haya. Ka je ka sha baƙar wahala, ka dawo a ɗauki kuɗin da bai taka kara ya karya ba a baka a matsayin sallama!”

Gambo ya mayar da hankalinsa kan tuƙinsa. Yana nazarin maganar ogansa. A ƙalla yanzu an kai kusan shekaru biyu kenan da yake ta ƙoƙarin siyan napep tasa ta kansa. Amma babu hali, saboda yanda Auwwa ta kasa ta tsare a kan kuɗinta.

“Me napep a Gagulmari fa za ka sauƙe mu!”

Ɗaya daga cikin fasinjojin ta faɗa. Hakan ya sa ya ɗan juyo ya kalleta, sannan ya amsa.

“To Hajiya”

Ya faɗa yana juya kan napep ɗin. Dan harsun ɗan gota unguwar Gagulmarin. A kan titin ƙofar Arewa ya sauƙe su. Suka biyasu kuɗinsu, sannan suka juya kan napep ɗin zuwa ƙofar fada.

Haka suka ci gaba da hira shi da ogansa. A kan mallakar napep ɗin da ya kamata ace ya yi, yana magana yana ɗauke kai daga kan tuƙin da yake. A haka har ya buge wata yarinya dake shirin tsallaka titin ƙofar fada ba tare da ya lura ba.

Duk da ya tsorata bai sai ya kasa guduwa ba, amma kuma cikin rashin sa'a sai jama'ar dake wurin suka yi caraf suka kamasu su biyu...


HALIMA POV.

Hannu ta kai ta ɗauki jakarta. Ta rataya a kafaɗarta, saboda lokacin tashinsu aiki ya yi.

“Kairat sai gobe”

Ta yi wa ƙawarta sallama tana ɗaga mata hannu. Ita ma Kairat ɗin hannu ta ɗaga mata. Tana shirin wucewa, hirar da cashier da wata ma'aikaciya suke yi ta ɗauki hankalinta. Hakan ya sa ta tsaya tana sauraronsu.

“... Wallahi dai kam haka na ji manager ya faɗa. Wai za ayi ragin ma'aikata!”

Lokaci guda ta ji gabanta ya faɗi. Dan haka kawai zuciyarta ta raya mata cewar ita ma tana cikin waɗan da za'a sallama. Ita kuwa idan aka sallameta ina za ta je ta samu wani aikin?. Wannan ɗin ma da ya aka same shi?. Ballantana kuma ace ta rasa shi... Gabanta bai tsananta faɗuwa ba sai da ta ji cashier na faɗin.

“Kuma a yanda Amina ke faɗa min wai waɗan da suka zo a ƙarshe-ƙarshen nan za a kora!”

Ido ta zaro tana faɗin ‘Inna lillahi wa inna ialaihi raji'un’ a cikin zuciyarta. Sai ta kasa motsawa daga wurin da take. Ta ci gaba da baza ido har ta yi wani kyakkyawan gani.

Saboda a sanda idonta ya lula zuwa ƙofar shigowa ta ga sanda Mr. JJ ya shigo boutique ɗin. Gabanta ne ya sake faɗuwa. Musamman da ta tuna rabuwarsu ta jiya. Hannunta na dama da ya riƙe ta kalla, tana jin kamar har yanzu hannayensa na kan wurin... Sai ta yi saurin goge ƙwallar da ta zubo mata, sannan ta nufi hanyar fita a sace, wai duk dan kada ya ganta.


MU'AZ POV.

Tun da ya shigo boutique ɗin yake ta dube-dube ko zai ganta. Amma har ya ɗauki sweatern da ya zo dominta bai samu ganin nata ba. Har ya fara jin ba daɗi na rashin ganinta, saboda ya fara tunanin ko dai ta tafi gida ne.

Yana shirin nufar wurin cashier ya ci karo da ita tana tafiya a sukwane. Tana ganinsa ta taka birki tana ɓata fuska. Lokaci guda kuma ta juya za ta gudu. Sai dai kamar jiya, haka yau ma ya riƙo hannunta. Kuma kamar dai jiyan, yau ma sai da ta ji kamar ta yi hauka da ya riƙo mata hannu. Da ƙyar ta juyo suka haɗa ido. Sai kuma ta shiga bin kayan jikinsa da kallo.

Kamar dai yanda ta saba ganinsa ne, sanye da baƙar T-shirt, da kuma wandon kakin sojoji, sai wani baƙin boot irin nasu na sojiji. Kuma yau ma kansa ba hula. Sai sweater guda biyu da yake riƙe da su. Ta sake kallon fuskarsa tana zare hannunta daga cikin nasa.

“To wai mi ye?”

Ta tambaya tana turo baki gaba. Mu'az ya yi murmushi kawai yana kallon wannan fuskar.

“Kaya na siya a boutique ɗinku. Kuma ke nake so ki kai min mota!”

Sai ta ƙara turo baki gaba. Hawaye ko tun da ya ruƙota ta fara zubar da su.

“Ni lokacin tashi na ya yi”

“Okay. Bari in je na faɗawa oganku...”

Ya yi maganar yana shirin nufar office ɗin manager. Duk dan ya tsoratata, kuma ta tsorata ɗin, dan taku biyu kawai ya yi, ta yi saurin riƙo hannunsa ta dawo da shi baya. Ta ci gaba da ɓata fuska tana faɗin.

“To ai ba sai ka je ba... Ka je ka biya, zan kai maka motar”

Ta ƙarashe tana ɗauke kai gefe. Bai sake ce mata komai ba, ya yi murmushi ya je ya biya kuɗin, sannan ya dawo ya sameta tsaye a inda ya barta, ya danƙa mata shopping bag ɗin da aka saka masa sweatern a ciki. Sannan ya yi gaba ya barta a nan.

Halima ta ɗaga jakar da ba wani nauyi gareta ba. Tsabar isa da gadara da take cin ransa, shi ya sa zai sa marainiyar Allah ta ɗaukar masa. Ta ƙarashe tana jan tsaki a ranta.

Sannan ta bi bayansa tana kumbure-kumbere, kamar kwaɗon da ya ke shirin yin kuka. Kasancewar ta san motar tasa ya da kai tsaye ta nufi inda motar take. Ganin ƙofar driver seat a buɗe yabsa ta nufi wurin. Zaune ta gan shi a cikin motar. Amma kuma ƙafafunsa na wajen motar. A gefe ta tsaya, sannan ta miƙa masa jakar.

“Ga shi”

Ta faɗi kamar me shirin fashewa da kuka. Mu'az da tun da ta fito yake binta da kallo ya sa hannu ya karɓi jakar. Tana shirin juyawa yace.

“Ba ki ji ba”

Cike da ƙosawa Halima ta juyo, ta buga ƙafarta a ƙasa.

“Dan Allah ka ƙyaleni ranka ya daɗe. An tashi aiki, kuma gida nake son zuwa”

Sai kuma ta kai hannu ta share ƙwallar da ta zubo mata. Ta juya masa baya, ta turo baki gaba tana harɗe hannunta a ƙirji. Mu'az ya yi murmushi. Sannan ya fito daga motar, hannunsa riƙe da bag ɗin da Na'im ya saka masa chocolate da cookies a ciki. Ya zagaya ta gabanta, ya jingina a jikin motar yana ƙarewa fuskarta kallo.

“Tambayarki zan yi”

Ta masa irin wannan kallon da yake sawa ya ji kamar ya tsaga ƙirjinsa biyu, ya ciro zuciyarsa ya yar ya huta, saboda yanda bugunta yake hargitsewa.

“Ina ji”

Ta faɗa tana sauƙewa hannunta da ta rungume. Sannan ta goge hawayenta.

“Me nene sunanki?”

Sai ta dube shi.

“Ai ka sani”

Ya jinjina kai.

“Na san sunanki Halima. Cikakken sunanki nake nufi”

Sai ta ja hanci tana juya kanta gefe.

“Halima Auwal Ali Kaska”

Ya yi murmushi. Sannan ya ɗauki chocolate ɗaya ya miƙa mata. Ta kalli chocolate ɗin. Sannan ta kalle shi.

“Ki karɓa”

Ta kai hannu ta karɓa, a sanda wata tambayar take biyowa baya.

“Ina ce unguwarku?”

Yanzu ma sai da ta masa kallon tsanaki. Sannan ta amsa.

“Da a Life Camp muke ni da iyayena. Bayan Allah ya musu rasuwa kuma sai na dawo wurin kawuna a Bwari!”

Ya kuma jinjina kansa. Sannan ya bata wata chocolate ɗin. Ita ma ta karɓa tana kallonsa kawai.

“A halin yanzu kina karatu?”

Mu'az ya sake tambaya. Saboda yana so ya san wani abu da ya shafi rayuwarta, ƙila shi ne zai nuna masa hanyar da zai bi domin gano abin da idanuwanta ke faɗa masa a duk sanda nasa idon zai haɗu da nata.

“Shekaru biyu da suka wuce na kammala FCT College of Nursing Sciences, Gwagwalada. Kuma a shekarar ne Allah ya yi wa iyayena rasuwa”

Ya kuma bata wata chocolate ɗin.

“Me ya sa malamar asibiti take aiki a boutique?”

Yanzu kuma sai ta kasa amsa masa. Ta yi shiru tana kallonsa.

“Na gaji da amsa tambayoyin da ban san dalilinsu ba. Sai an jima”

Ta ƙarashe tana shirin raɓa shi ta wuce. Amma sai ya riƙo damtsen hannunta a wannan karon, ya dawo da ita. Mamaki zane a kan fuskar Halima take kallonsa. Wai shi me yake damunsa ne?. Haka kawai sai ya yi ta riƙeta?. Shi bai san me take ji ba a duk sanda zai riƙeta?.

“Gida zan tafi”

Ta faɗa tana turo baki.

“Mu je na kaiki”

Yanzu ma kallonsa ta sake yi.

“Ni ban sanka ba fa Malam JJ Ɗan Iya!”

Sunan da ta kira shi da shi ya sa ya yi dariya kaɗan.

“Ni kuma na sanki. Ki shiga mu je na kaiki”

Ta noƙe kafaɗa alamun ba za ta shiga ba. Lokaci guda Mu'az ya haɗe fuska.

“Get in, Idan ba haka ba zan mareki!. I'm running out of patience!. ”

Lokaci guda cikinta ya murɗa. Saboda ta tuna yanda ya mareta last time. Dan haka ta yi saurin ja da baya za ta sa kuka.

“Leemat ba na son gardama. With due respect. Get into the car”

Ta turo baki. Sannan ta buga ƙafa a ƙasa. Ta juya ta zagaya ɗayan ɓangaren, ta shiga gidan gaba tana hawaye. Shi ma motar ya shiga. Sannan ya miƙa mata jakar chocolate ɗin hannunsa. Ta ɗauka tana ta ɓata rai. Wanda suke hannunta ma a ciki ta sa. Ta kame kanta gefe, ta ƙi yin magana sai hawayen da take.

Shi ma bai takura da sai ta yi maganar ba. Har sai da suka iso Bawri. Sannan ya tambayeta layin gidansu a Dutsen Alhaji. Sai a sannan ne ta yi magana. Kuma suna isa ƙofar gidan ta shiga ƙoƙarin buɗewa ta fita.

“Baby girl!”

Cak ta tsaya daga shirin fitar da take. Saboda wani abu da ya faɗo a cikin kanta. A gaba ɗayan rayuwarta mahaifiyarta ce kaɗai ke kiranta da sunan. Hakan ya sa ta juyo ta kalle shi.

“Kukan na mi ye?”

Ta kai hannu ta goge ƙwalla tana ci gaba da tura baki.

“Ba kai ne ka min tsawa ba”

Kansa ya girgiza.

“Gardama kika yi. And i hate stubbornness. Amma ki yi haƙuri”

Ta ci gaba da tura baki tana kumbura shi.

“Ki haƙura da wuri, saboda kar ki sake shigo min ciki tunani ki fitineni”

Ta kuma kallonsa.

“To na haƙura. Kuma na gode”

Tana kaiwa nan ta fice daga motar. Zuciyarta cike taf da farin cikin wannan kyauta da ya mata ta chocolate da cookies. Saboda abu ne da ta daɗe ba ta sa a ido ba, ballantana har ta kai ga sha. A ɗaya ɓangaren kuma tana cike da fargabar batun rage ma'aikata da za ayi a boutique ɗinsu. Shi ma wannan batu ya hana zuciyarta sukuni. Har ta shige gidan Mu'az na kallonta yana murmushi.

“Rigima Baby girl”

Ya faɗa yana shafa gajerar sumar kansa. Yana shirin tayar da motar kiran Faruk ya shigo wayarsa. Hakan ya sa ya fasa ya ɗaga wayar.

“Kaigama what's up?”

Daga ɗayan bangaren Faruk yace.

“Yanzu Muktar ya kirani. Ya sanar min da cewa yana son ganinmu ni da kai da gaggawa!”

Mu'az ya ɗan sosa kan hancinsa yana duba agogo.

“Okay a ina zan sameka?”

“Ina gida. Ka zo ka ɗaukeni sai mu wuce headquartern”

“Okay”

Daga haka ya sauƙe wayar. Sannan ya tayar da motar ya nufi gidan Faruk.


MUKTAR POV.

Zaune yake cikin office ɗinsa. Yayin da Faruk da Mu'az ke zaune a kan kujerun dake gaban teburinsa. Tun da suka zo headuatern, suka ritsa shi da tambayoyi na me ya same shi.

Saboda ganin raunukan da suke a jikinsa. Hannunsa na hagu da yake da tabbacin ya karye ya kuwa karye ɗin. Dan yanzu haka sai da aka yi wa hannun ɗori a asibiti. Ban da sauran wuraren da suka raunatu a jikinsa.

Saboda jiya har ƙarfe sha biyu suna asibiti shi da Walid da Ali. Kuma duk da yanda likitocin suka so ya zauna a asibitin ƙi ya yi. Saboda ba ya jin zai bar abin da ya faru ya tafi a banza. Dole ne ya ɗauki matakin gaggawa, a yanzu sun kuskure wurin halaka shi, wata ƙila nan gaba Allah zai iya basu nasara.

Ba mutuwarsa ce abar tsoro a wurinsa ba. Ya san cewa ko wani mai rai ƙarshen rayuwarsa a duniya mutuwar ce. Kamar dai yanda mahaifinsa ya rasu ya bar su shi da ƙaninsa da kuma mahaifiyarsu. Abin da zai fi ƙona masa rai shi ne da zai mutu ya bar Mariya da abokin aikata kisanta a raye, suna cutar Faruk da kuma sauran al'umma...

“Mukhy!”

Mu'az ya kirashi da ɗan ƙarfi, ganin kamar tunaninsa ya yi nisa da gangar jikinsa. Hakan ya sa ya dube shi da sauri yana amsawa.

“Na'am!”

“Ina ka tafi?”

Mu'az ya tambaya yana watsa hannu a iska. Muktar ya girgiza kansa yana ɗora hannunsa a kan table ɗin dake gabansu. Ya furzar da huci kaɗan. Sannan ya dubi Faruk, ya dawo ya dubi Mu'az.

“Kaigama!”

Faruk ya gyara zama yana faɗin.

“Na'am Mukhy!”

Muktar ya kalli Mu'az.

“MJ!”

“Umm!”

Shi ma ya amsa. Muktar ya jinjina kansa. Yana son sanin ta inda zai fara musu bayani a kan wata makusanciyarsu ita ce me laifin da suka daɗe suna nema ruwa a jallo.

“Kaigama! MJ!. Ba na so na zama mutum na farko da zaisanar da ku wannan mummunan labarin!... Dan haka zai fi kyau ku kalla da idonku, kafin bayanina ya biyo baya!...”

Su dai kallonsa kawai suke da rashin fahimta. Kuma duk sun ƙagu ya faɗa musu dalilinsa na yin kiransu. Ba su ce komai ba har ya juyo musu screen ɗin laptop ɗin dake kan teburin. Sannan ya naɗe hannunsa yana kallon fuskokinsu.

A lokacin da videon ya kai ƙarshe. Ba a ce a tsakanin Faruk da Mu'az wa ya fi wani shiga shock ba. Kallon juna kawai suka yi baki a sake. Kafin Mu'az ya yi ƙarfin halin kai hannunsa ya sake kunnawa.

Tunaninsa, zuciyarsa, da duk wani abu me faɗa a ji a jikinsa na faɗin wannan ba ƙanwarsa ba ce. Wannan ba Mariya ba ce. Wannan ba ƙanwarsa da ta fi kowa acikin ƙannensa soyiwa a ransa ba ce. Sam ba ita ba ce!... Ya ma za ayi ta kasance Mariya Jibrin Gimba?.

Shi dai Faruk ba irin wannan tunanin yake ba. A kallo ɗaya da ya yi wa videon ya gane matarsa. Saboda ya santa, ya kuma san wacece ita. Amma abin da bai gane ba shi ne, me ya sa Mariya za ta sace Munira, har ta kai ga kasheta?.

Sannan wannan mutumin da suke tare da shi, waye shi?. Me zai sa matarsa da ba za ka yi tunanin idan ka sa mata hannu a baki ba za ta ciza ba ta yi kisan kai?... Yanzu har Mariya za ta iya kashe wani?. Me ya sa?. Me zai sa ta kashe Munira?. A tare suka sake kallon juna, sannan suka kalli Muktar da shi ma yake kallonsu.

“Na san kallon wannan videon zai sa tarin tambayoyi a cikin kawunanku... Tabbas wannan Mariya ce. Matarka Kaigama, ƙanwarka MJ. Kuma...”

Bai kai ga ƙarasawa ba. Mu'az ya miƙe tsaye, sannan ya shaƙo wuyansa ya miƙar da shi tsaye yana jin kamar ya kashe shi ya huta. Sai huci yake yana jin zuciyarsa na zafi.

“Yes, it is a good sentence! It's a clear and strong expression of defense and protection towards one's sister. The phrase "How dare you" is a powerful way to convey shock, anger, and disapproval. The sentence is well-structured and effectively conveys the speaker's emotions and stance.

Here are some similar sentences that convey a similar message:

"How dare you talk about my sister in that tone!?”

Ya faɗi a kausashe. Muktar bai ce komai ba, kuma bai yi yunƙurin ƙwatar kansa ba. Saboda ya san ko shi aka zo aka samu da zancen cewa Walid ya yi kisan kai zai iya shiga cikin halin. Da ƙyar Faruk ya cire hannun Mu'az a wuyan Muktar, ya ja shi baya ba tare da ya ce masa komai ba.

“I can't believe he thinks Mariya is responsible for Munira's death!... And... and!”

Ya kasa ƙarasawa yana jin idonsa na cika da ƙwalla. Amma kuma ba ta zubo ba. Har ji yake numfashinsa na shirin ɗaukewa. Ya yi shiru kawai, yana fitar da iska daga huhunsa da ƙyar, kamar me ciwon zuciya.

“Get seated”

Faɗin Faruk yana zaunar da shi a kan kujera. Zaman ya yi yana dafe kansa da ya fara sarawa. Da ma shi haka yake, daga zarar ransa ya ɓaci zai fita hayyacinsa gaba ɗaya, idan bai yi sa'a ba ma sai ya kwanta jinya.

“Ina jinka Muktar”

Faruk ya haɗe kalaman yana haɗiyar yawu da ƙyar. Saboda jin wani abu ya toshe masa maƙoshi. Shi bai faɗa cikinsa ba, kuma bai fito ta bakinsa ba. Muktar ya zauna, sannan ya ci gaba da faɗin.

“... Na samo wannan videon ne a unguwar da aka sace Munira. Na same shi ne daga wurin wani yaro da a lokacin da aka sace Munira ya yi recording videon... A lokacin da na samu vedion ban yi ƙoƙarin sanar da kowa ba face Ali mataimakina, wanda tare da shi muka je. Abin da ya ba ni mamaki shi ne a wannan ranar wani ya biyoni gida yana ƙoƙarin kasheni. Amma Allah ya taimakeni na tsira. Sai dai kuma a daren jiya Mariya da wannan mutumin na cikin videon ne suka zo har unguwar mu. Kuma na gansu, sannan su ne suka bigeni da mota. Har na samu waɗannan raunikan na jikina... Shi ya sa na ce ba zan yi ƙasa a gwuiwa wurin sanar da ku wannan gaskiyar ba!”

Faruk ya dafe kansa. Tunanin abin da ya faru tsakaninsu jiya ya dawo masa. Ke nan jiya da daddare kashe Muktar ta tafi?. Innalillahi wa inna ialaihi raji'un. Ya furta yana murza goshinsa. Mu'az kuwa bai sake cewa uffan ba. Sai yatsun hannunsa da yake murzawa idonsa na sauya kala zuwa ja.

-------------------------------

_Wato a wasu lokutan. Abubuwan da ba mu yi zato ba su ne suka cika faruwa da mu._

_Irin haka ce ta faru ga Faruk da Mu'az._

_Shin! Wani dabi ne zai ɓarke a haɗejia, tsakanin Gambo da Maimuna da kuma Auwwa?._

_Shin, wani hali kuke tunanin Halima za ta shiga idan aka sallameta a aiki?._

_Me zai faru tsakanin Mariya da Faruk?._

_Sannan Mu'az, dan shi kam ya fi Faruk fusata._

_Yaya Mariya za ta yi domin wanke kanta a idon yayanta da kuma mijinta, da ma sauran jama'ar duniya da za su sani?._

_Shin, kuna ganin cewa, kisan Munira zai zama kisa na ƙarshe da Mariya za ta aikata?. Ko za ta ci gaba da zama a ƙungiyarsu ta bayin Shaiɗan!?._

_Hummm!_

_Akwai magana. To, ga duk wanda yake son sanin amsoshin waɗannan tambayoyin, sai ya biya ₦300. Tun kafin tafiyar nan ta wuce ku._

_Kun san daga ganin tafiyar nan ba ta wasa ba ce, dan har yanzu ba mu yi komai ba. Kuma ina me muku tabbacin ba za ku yi da na sanin siyan wanna littafi ba. Kun san alƙalamin Candy akwai suger._

••• ••• •••

*Zan yi amfai da wannan damar, wurin gode muku, SALMANIANS. Kun san da cewa ku ne on top a ƙalbina. I love you like wujiga-wujiga. Ina sonku fiye da irin son da kuke min*

Ga duk wanda ya shirya dan ayi tafiyar nan da shi, zai ₦300 kacal. Ta wannan account details ɗin da zan rubuta. Idan kuma har ya zama complete document sai dai ku biya ₦500.

5487270431
Salma Isah
Moniepoint

Shaidar biya kuma via.

08130172702.

Sai na ji ku SALMANIANS.

Best regards.
*SALMA AHMAD ISAH*
*(CANDY🦋)*

2024...

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan

Please Login or Register in order to submit comment