Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zarar lokacin ya yi za mu sanar da ke. Yanzu dai abu ɗaya nake buƙata daga gareki. Shi ne gashin kansa, domin ba za mu sadaukar da jininsa ga shugabanmu shaiɗan ba ba tare da mun tsaface shi ba. Dan haka sai kin jira nan da wasu wattani!”

Duk da ba haka ta so ba ta ji daɗi. Da wannan batu ta yi wa Wahash sallama, sannan ta dawo gidanta, cikin ɗakinta. Kuma tana dira a ɗakin Hilal ya zabura ya farka, lokaci guda ya canyara kuka. Amma ko ajikinta an mintsini kakkausa. Dan bathroom ma ta shiga.

Ta je ta yi wanka ta dawo ta sauya kaya ta kwanta a kan gadon tana kallon Hilal ɗin dake kuka har zuwa lokacin. Kallonsa da ta yi ya motsa wani abu a cikin zuciyarta. Musamman ma da ta tuna cewa nan da wasu watanni za ta sadaukar da shi ga abin bautarta a yanzu, wato shaiɗan.

(Ya ilahi!)

Tausayinsa ta ji ya fara shiga zuciyarta, dan haka ta kai hannu za ta taɓa kansa. Amma sai wannan baƙin hayaƙin da ya saba rufe mata ido a duk sanda za ta tuna wani abu na soyyaya tsakaninta da Faruk ko ɗansa ya rufe idonta.

Lokaci guda hannunta na dama da ta ɗaga za ta ɗora a kan Hilal ya ƙame a saitin kan nasa. Ƙwayar idonta ta juye zuwa ja. Sannan lokaci guda fushi ya maye fuskarta. Sai ta yi saurin janye hannunta daga kansa.

Sannan ta juya masa baya tana huci kamar wadda aka ɓatawa rai. Lokaci guda idonta ya soma zubar da hawayen jini. Ta rintse idonta gam tana karanto wata addua'a tasu ta bayin shaiɗan. Har ta samu ta yi bacci.

FARUK POV.

Da misalin ƙarfe goma na dare ya fito daga banɗaki. Bayan ya watsa ruwa a jikinsa kasancewar bai jima da dawowa daga wurin aiki ba. Sanye yake da yellow plain T-shirt da baƙin sweat trouser, ƙafafunsa duka na sanye cikin baƙin sliders ɗinsa.

A hankali ya kai hannu ta taɓa sumar kansa da take a jiƙe, wadda kuma bata cika tsayi ba kasancewarsa soja ya sa ba ya tara gashi ko da ya so hakan. Shi yasa yake askin high fade tare da buzz cut.

Yana shirin kashe hasken dake ɗakinsa, idonsa ya sauƙa a kan wani hoto dake cikin kyakkyawan frame. Wanda ya ƙunshi Mu'az da Munira da kuma shi kansa. Zama ya yi a gefen gadonsa. Ta inda hoton ke aje a kan side drawer.

Ya kai hannu ya ɗauki hoton yana kallo. Gaba ɗaya su ukun na sanye cikin korayen kaya ne na sojoji, kuma sai kayan dake jikin nasu ya tuno masa da lokacin da aka ɗauki hoton. Wato ranar da suka yi passing out.

Domin NDA Kaduna (National Defense Academy Kaduna) suka fara haɗuwa da Munira a wurin training. Ƙwazonta da kuma nuna jarumtarta duk da kasancewarta mace 'yar arewa yasa suka ƙulla abota da ita. Alaƙarsu da Mu'az kuma ta fara ne tun daga secondary school. Har suka kai ga tertiary school suna tare, kuma burin kowwane a cikinsu tun a wancan lokacin shi ne zama soja.

A sanda suka kammala karatu mahaifinsa Alhaji Haruna Aminu Kaigama yana da rai. Kuma shi ne wanda ya nema musu makarantar horar da sojojin ta NDA. Kasancewar Hajiya Batula mahaifiyarsa bata da matsala da aikin da yake son yi sai ya riga Mu'az tafiya.

Saboda shi Mu'az Mummynsu bata son ya yi aikin soja. Shi ya sa sai da aka kai ruwa rana kafin ta amince ya tafi. Amma duk da haka sai ya zo ya fisu muƙami shi da Munira da suka fara zuwa a farko.

Wani abu da ya ƙarawa abotarsu ƙarfi shi ne lokacin da aka yi posting kowwane a cikinsu sai aka turasu gari ɗaya. Da haka suka ci gaba da aiki tare har zuwa lokacin da ko wanne a cikinsu ya samu ƙarin girma. Da kuma nasarorin rayuwa. Kafin komai ya tarwatse a lokaci guda.

Saurin aje frame ɗin ya yi, saboda hoton gawar Munira da ya haska a cikin idonsa. A hankali ya kwanta a kan gadonsa. Ya yi rigingine. Yana kallon p.o.p ɗin dake saman ɗakin. Hannunsa na dama ya dunƙule, sannan ya ɗora tsintsiyar hannun nasa a bisa goshinsa yana tunani.

Can kuma sai yajuyar da kansa ya kalli makwancin Mariya a da. Kafin ta nemi raba ɗaki da shi. Ya ɗauke kansa yana tuna adadin lokutan da ya mata magana kan hakan. Amma sai tace masa ita bata da lafiya.

Tun yana haƙuri har ya gaji ya daina mata maganar. Kuma babban abin da yake damunsa da ita shi ne rashin kula da Hilal da take. Kamar ba ita ta haife shi ba. A ganinsa ko da ba ita ta haifi Hilal ba in dai ya kasance ɗansa bai kamata ta masa irin ruƙon da take masa a yanzu ba. Cike da saƙe-saƙen goma da ashirin ɗin da suka haɗe masa bacci ya ɗauke shi. Amma bai kai ga barin Nigeria ba a duniyar baccin nasa kukan Hilal daga ɗakin Mariya ya tasheshi.

Ya buɗe idonsa da ƙyar. Saboda bala'in baccin dake cin idonsa. Tun da ya fara aikin soja baya jin akwai ranar da ta zo ya rama tarin bashin baccin da ake binsa. Dan a ko da yaushe a gajiye yake dawowa gida. Idan kuma an tura shi wani aiki ne ma kwana yake idonsa biyu. Wani lokacin kuma sai ya samu baccin. Amma rashin baccin yana yawan damusa.

Jin kukan Hilal ɗin ya ƙi ƙarewa ya sa ya miƙe zaune yana yin hailala. Ya saka takalmansa dake ƙasan gadon. Sannan ya fita daga nasa ɗakin ya shiga na Mariya. Ganin Hilal ɗin kwance a gefen Mariya yana kuka bai bashi mamaki ba.

Dan ya ga abin da ya fi hakan ma. Shi dai a rayuwarsa bai san Mariya wata kala ba ce. Cikin ɗakin ya ƙarasa, sannan ya kai hannu ya ɗauki yaron da yake ta kuka har da hawaye. Ganin yana gwagwiuyar hannunsa yasa ya fahimci cewa yunwa yake ji. Dan haka ya zagaya ta ɗayan ɓangaren ya tashi Mariya a bacci. Duk da bata yi nisa a baccin ba amma da ƙyar ta buɗe ido ta kalle shi.

“Mary Hilal yana ta kuka. Kuma da alama yunwa yake ji. Ki tashi ki shayar da shi.”

Mariya ta mayar da idonta ta rufe, kamar ba za ta yi magana ba, can kuma sai tace.

“Ka duba kitchen akwai kayan abincinsa sai ka dama ka ba shi idan kukan nasa ya dameka!”

Cike da takaici Faruk ya girgiza kansa yana kallon yaronsa. Ɓacin rai ya sa bai sake cewa Mariya komai ba ya fice daga ɗakin. Ya nufi kitchen da Hilal ɗin a hannunsa, kuma har zuwa lokacin bai yi shiru ba.

Shi kuma sai faman jijjiga shi yake alamun rarrashi. Da Allah ya taimake shi sai ya samu bottle ɗin Hilal ɗin akwai damammen custard a ciki. Shi ya ɗauka ya dawo ɗakinsa da shi. Ya shiga ba shi yana masa kallon tausayi.

Dan yanda yake zuƙar bakin bottle ɗin da ƙarfi zai sa ka fahimci cewa yinwa yake ji. Hilal bai kai ga shanye custard ɗin ba ya yi bacci. Cike da tausayin ɗansa Faruk ya kwantar da shi a kan gadonsa. Dan ba yau suka fara kwana tare ba. Ɗan karamin ɗa da uwarsa a raye amma ya zama kamar maraya.

Sanyin AC ya rage. Sanna ya ɗauki duvet ɗan ƙarami ya masa rufa. Kafin ya kwanta a gefensa yana kallonsa cike da so da kuma tausayi. Addu'a ya masa, shi ma ya yi, har Allah ya sa bacci ya sace shi.

MU'AZ POV.

“Mima ƙara min”

Ya faɗa yana miƙawa Mima dake serving kowa na gidan dake zaune a dinning table, kasancewar suna shirin yin karin kumallo ne. Mima ta kalli plate ɗin da ya miƙo mata. Cike da mamaki ta karɓi plate ɗin.

“Yanzu Ya Mu'az a ina zan ƙara maka wani abincin? Ji fa yanda plate ɗin ya cika da abinci, baka ci ba amma ka na neman ƙari!...”

Wani kallo ya mata yana faɗin.

“Miƙo min na coolern duka. Tun da ke baki da dabarar sauya plate!”

Mima ta aje plate ɗin tana ɓata rai. Mu'az ya miƙe ya zagaya ta inda take yana faɗin.

“Matsa ki bani wuri ko na sauya miki kammani yanzu!”

Mima ta turo baki gaba tana matsawa. Ta kalli Mummy da ke kallonsu, dan wannan faɗan nasu sun saba yinsa kullum a kan abinci. Tun ana saka musu baki har kowa ya ƙyalesu da halinsu. Cikin ƙunƙuni Mima tace.

“Mutum sai ci kamar gara!”

Mu'az dake shirin zama a kan kujerar da ya miƙe ɗazu, bayan ya sauya plate ya cika shi da abinci ya kalleta.

“Magana kika yi?”

Mima ta sosa wuyanta tana faɗin.

“A'a fa. Ni ban ce komai ba”

Ta faɗi ƙwaƙwalwarta na faɗa mata amsar da zai bata. Dan tun ba yau ba sun saba, ta riga ya haddace kalmar kamar sunanta. Mu'az ya yi ƙwafa yana jan kujerarsa, tare da zaunawa. Sannan ya furta abin da Mima ke zaton zai faɗa ɗin.

“Ƙaramar mara kunya!”

Cike da mamakin halin yayan nata Mima ta yi serving Daddy. Ita ta rasa sai zuwa yaushe za ta girma a rashin kunyar nan. Kullum a ƙarama take, daga ta masa abu zai ce mata ƙaramar mara kunya, ko yace zai sauya mata kammani. Words ɗinsa ke nan.

“Daddy zan iya ganinka a falonka?”

Faɗin Mu'az yana miƙewa tsaye. Bayan da ya tashi plate ɗin da ya cika da boiled yam da kuma egg sauce daga aiki. Idan har abinci ya yi daɗi ba za ka samu ragowarsa a plate ɗin Oga me cika aiki ba. Daddy ya dube shi.

“Maganar na buƙatar privacy?”

“Yeah Daddy”

Ya amsa yana wanke hannunsa a sink. Kafin ya juyo yana kallon Mummy dake kallonsa.

“A kan mi ye?”

Mummy ta tambaya. Kafin ya kai ga bata amsa Daddy ya amsa mata.

“Ya ce maganar tana buƙatar sirri. Idan ba haka ba ai kin san da ya faɗeta a nan ko?”

Mummy ta yi wa Mu'az kallon ban yarda da kai ba!. Kafin takalli Daddy ta taɓe baki tana juya spoon a cikin teacup ɗinta.

“Mu'azzam ka je falon ka jirani. Yanzu zan kammala na zo”

“Okay”

Ya faɗi yana nufar ƙofar falo. Fita ya yi, inda ya bi ta compound ya nufi sashin Daddy. A falon farko ya zauna yana jiran zuwan Daddy. Kuma Daddyn bai jima ba sai ga shi ya zo.

“Wace magana ce that needs privacy Mu'zzam?”

Daddy ya tambaya while sitting. Mu'az ya gyara zamansa yana faɗin.

“Daddy a kan Mariya da Faruk ne?”

Naman goshin Daddy ya tattare wuri guda cike da mamaki, sannan yace.

“Mariya da Faruk kuma? Me yake faruwa? Ko wata matsalar suka samu?”

“Ban sani ba Daddy. Amma na lura da kamar akwai matsala tsakaninsu. Na gane hakan ne ta hanyar halin damuwa da yawan tunani da Kaigama yake shiga. Kuma duk yanda na kai da bugun cikinsa dan ya faɗa min ya ƙi faɗa. Saboda mugun zurfin ciki irin nasa. Amma ni na tabbatar akwai matsala a tsakaninsa da Mariya!”

Daddy ya yi shiru yana sosa haɓarsa dake ɗauke da ɗan gajeren gemunsa irin na masu rayuwa cikin hutun nan. Can kuma ya dubi Mu'az yace.

“In dai kuwa haka ne ya kamata a ji abin da yake faruwa”

“Haka ne Daddy. Sai ka kiransu su duka, dan su zo ka ji abin da ke faruwa a tsakaninsu, wata ƙila idan kai ka tambaya za su faɗa maka. Kuma ka ga sai a sasanta su!”

Daddy ya yi murmushi yana kallonsa.

“Shi yasa nake jin alfaharin cewa bayan na mutu kai ne za ka gajeni. Saboda a bayan bauɗɗaɗɗun ɗabi'unka akwai halaye masu kyau. Haƙiƙa ka yi tunani me kyau. Allah ya maka albarka, ya kuma baka ladan zama sannadiyyar gyara sunnar fiyayyen hallita. Tun da kai ka ƙi raya sunnar!”

Mu'az ya yi murmushi yana shafa gajerar sumar kansa me ƙarfi kamar ta sauran Africans. Amma da yake tana jin gyara kuma ba ya tarata sosai sai ta yi kyau abinta.

“Daddy! Zan yi aure fa. Kawai dai ni harkar 'yan matan ce bata gabana. Bana son raini Daddy, 'yan matan yanzu kuma sun iya raini!”

(MJ ne ya faɗa. Nii dai ba ruwana!)

Daddy ya dara.

“Allah ya baka mace ta gari, sannan ya baka wadda za ta yi haƙuri da kai, ya kuma baka wadda ba za ka zalunceta ba. Sannan ya baku zuri'a ta gari!”

Mu'az ya miƙe tsaye yana murmushi.

“Oh lord of mercy!. Irin wannan addu'a haka Daddy?”

“To ai baka ce amin ba”

“Amin Daddy”

Ya amsa yana fita daga falon. Kai tsaye ya nufi sashensa dake can wani gefe da ban na gidan. Falo ɗaya ne da ɗaki sai bathroom. Tun daga falo ya cire rigar jikinsa. Dan shi da riga kamar maƙiya haka suke. Idan ka ga ya saka riga fita zai yi.

Amma muddin zai zauna a sashensa to fa ba zai sakata ba, a cewarsa wai takura shi take. Yana shiga ɗaki ya aje rigar a kan bed. Sannan ya kunna kiɗa ya yi zamansa a ɗakin.

Saboda yawan jin kiɗa ɓabi'ar sojoji ce. Bai haura mintina biyar da shigowa ɗakin ba aka kira wayarsa. Hakan ya sa ya rage sautin kiɗan. Ya ɗaga wayar yana wani haɗe rai, kamar wanda aka cewa ya sha magani ba ruwa. Kuma hakan ya samo asali ne daga ganin sunan me kiran.

Yasmin. Wata yarinya ɗaya tilo da ta nace a duniya kan shi take so. Kuma cikin wani ikon Allah sai aka yi rashin sa'a shi babu sonta a tsarin rayuwarsa. Dan yace shi bata masa ba, saboda ta cika naci da yawa.

“Yanzu abin da kake min ka kyauta Mu'az?”

Muryarta me sanyi ta fito daga cikin wayar. Ya lumshe idonsa yana murza goshinsa.

“Me na yi kuma?. Ko da yake, ai ba'a rasa nono a ruga. Da ma ni kullum me laifi ne!”

Daga ɗayan ɓangaren, Yasmin ta girgiza kanta.

“Ko kaɗan Mu'az ba haka ba ne. Ni dai kawai abu ɗaya nake so daga gareka. Kuma shi ne na kasa samunsa har yanzu. Kulawa ita ce abin da nake buƙata Mu'az. Ya kamata ka riƙa nuna cewa ina da muhimmanci a cikin rayuwarka!”

“Me ya sa zan miki ƙarya?”

Cikin rashin fahimta Yasmin tace.

“Ƙarya kuma? What do you mean?”

“Yes, ƙarya. Did you want me to be saying that i love you?. Bayan kuma a zahiri ba haka ba ne”

Ƙwalla ta zubo daga idon Yasmin.

“Mu'az!”

Ta kira cikin sanyin murya.

“Na'am”

Ya amsa.

“Ina so na tambayeka abu ɗaya”

“Faɗi, ina ji”

“Mu'az kana sona, ko a'a?”

Kai tsaye yace.

“Bana sonki Yasmin. Ban taɓa sonki ba, kuma bana tunanin fara sonki ko da a nan gaba”

Cike da baƙin ciki Yasmin ta kashe wayarta. Yana jin ta sauƙa a layi ya cilla wayar kan gado. Sannan ya ƙure Volume ɗin waƙar da yake ji hankalinsa kwance kamar tsumma a randa. Kamar ba shi ne ya gama tarwatsa zuciyar wata yanzu ba.

_Share fi sabillilah❤️_

------------------------

_I have told you that KADDARA CE! Isn't free!_
_If you want to subscribe pay ₦300 to._

5487270431
Salma Isah
Monie point

And send the evidence of payment via 08130172792.

*Daga alƙalamin Salma Ahmad Isah✍️.*
*CANDY CE🦋.*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*ƘADDARA CE!*


*©SALMA AHMAD ISAH.*
*CANDY🦋*

_ArewaBooks @SalmaAhmad_
_Wattpad @Salma_Ahmad_Isah_


*04*


*Unguwar Fantai, Haɗejia local government, Jigawa state.*

MAIMUNA POV.

Su uku ne jere a bakin titi. Kuma ko wacce a cikinsu kayan siyarwarta ne a gabanta. Ɗaya tana suyar awara, ɗaya tana soya wainar fulawa, sai kuma ita da bokitin kununta ke aje a gabanta.

Tun daga nesa ta hangi kawunta, ƙanin mahaifinta wato Kawu Barau. Duk da duhun magariba da ya fara sauƙa bai sa ta kasa gane shi ba. Baki ta washe ta miƙe tsaye tun kafin ya iso inda suke. Kuma shi ma har ya iso inda suke murmushi yake.

“Kawu ina wuni!”

“Lafiya ƙalau me sunan Hajja”

Kawu Barau ya amsa yana kallon tilon 'yar ɗan uwansa. A lokacin ya lura da hannunta na dama dake ɗauke da tabon ƙuna. Lokaci guda fara'ar kan fuskarsa ta yi balaguro.

“Me sunan Hajja ya aka yi kika ƙone?”

Maimuna ta kalli hannunta, sannan ta kalli kawu tana faɗin.

“Auwwa ce ta ƙonani rannan. Amma ai ya fara warkewa, saboda Mummynsu Maryam ta kaini asibiti, kuma har magunguna ta sai min”

Cike da tausayawa Kawu ya girgiza kansa yana faɗin.

“Wa cece kuma Mummyn su Maryam?”

“Wannan ƙawar tawa, jikar tsohon Kaigama”

“To to. Na gane, 'yar gidan Bara'atu ko?. 'Yar Alhaji Haruna Kaigama me rasuwa, ƙanwar Alhaji Bello Kaigama na yanzu!”

Maimuna ta gyaɗa masa kai.

“Amma ko ta kyauta. Allah ya biyata da gidan aljanna... Amma baki faɗawa Hajja ba?”

Ta yi saurin gyaɗa masa kai. Dan bata faɗawa kakar tata ba. Saboda a tsakanin kwanakin ba ta je gidanta ba. Kuma ko ta je ma ballale ta faɗa ba idan har ba tambaya Hajjan ta yi ba.

“To Allah ya kyauta. Ya saka miki da abin da Auwwa take miki. Ki ci gaba da haƙuri kin ji ko me sunan Hajja?. Allah na sane da ke, kuma zai kawo miki ƙarshen wannan wahalar taki. Ki ci gaba da addu'a. Kan Allah ya baki ikon cinye wannan jarabawar da yake miki”

Faɗin Kawu Barau yana lissafo 'yan kuɗaɗen da suka sa aljihunsa yin nauyi a safiyar yau. Cike da damuwa Maimuna ta gyaɗa masa kai.

“To Kawu. Inshallah zan yi”

“Karɓi wannan ba yawa. Na san magungunanki sun ƙare, dan wallahi suna raina, shi ya sa na kasa sukuni har sai da na samo kuɗin siyansu, dan na san a yanzu lokacin sanyi kin fi buƙatarsu”

Maimuna ta yi murmushi tana girgiza masa kai.

“Ai duka Mummy ta siya min har da folic acid da palludrine”

Cike da mamaki Kawu ya kalli kuɗin hannunsa, sannan ya ƙara miƙa mata.

“Duk da haka dai ki karɓa, ba zaki rasa amfanin da za su miki ba. Ko sabulu kika siya kika wanke kayanki ai kin rage”

Maimuna ta karɓi kuɗin hanu biyu, tana kallon kawunta da yalayen idanuwanta.

“Na gode Kawu. Allah ya ƙara buɗi”

Kawu ya yi murmushi. Sannan ya mata sallama ya ɗale kekensa ya nufi gida. Kasancewar tun bayan rasuwar matarsa bai sake yin wani auren ba ya sa yake zaune tare da mahaifiyarsu. A soro ya jingine kekensa, sannan ya yi sallama ya shigo cikin gidan. Inda ya iske mahaifiyarsu Hajja, zaune a tsakar gida, da alamun alwala ta yi, dan ga buta nan aje a gabanta.

“Barau an dawo?”

“Eh Hajja. Na dawo”

Hajja ta miƙe tana faɗin.

“To sannu da hanya”

“Yauwwa Hajja”

Daga haka ta shiga rumfar dake gidan, ta ɗauki hijabinta dake aje a kan sallaya. Ta saka ta tayar da sallah. Yayin da Kawu ya kama ruwa, sannan ya yi alwala ya fita masallaci.

Sanda ya dawo Hajja na zaune a nan rumfar tsakar gidan tana jan carbi. Zama ya yi a kan kujera 'yar tsugguno yana jiran ta kammala. Kuma sai da ta kammala ɗin ya faɗi abin da ke bakinsa.

“Hajja magana nake so mu yi a kan Me sunanki!”

Hajja ta aje carbin hannunta tana tattara hankalinta gare shi, jin batun magana a kan tilon jikarta.

“Me ya samu Maimunatun?”

Cikin damuwa Kawu ya tsara mata abin da Auwwa ta yi wa Maimuna, sannan ya ƙara da.

“... Ni Wallahi dan de kin ƙi ta tawa ne, tun yarinyar nan tana ƙarama na so ta dawo wurinki da zama, amma kika ce can shi ne dolenta, dan haka ba za ta dawo nan ta zauna ba, yanzu bayan talla da Auwwa ke ɗora mata har da su hukunci da wuta take mata, ya kamata mu yi wani abin a kan lamarin me sunanki Hajja. Ko da wannan cutar dake damunta aka barta ya isheta ƙaddara, ballantana a ƙara mata da izayar matar uba!”

Hajja ta ci gaba da kallonsa har ya kai aya, sannan tace.

“Barau! Ba wai na ƙi amincewa da shawararka ba ne. A'a, ni akwai abin da nake hangowa. Yanda Auwwa take da masifar son abin duniya za ta iya cinyewa wannan gidan. Bayan kuma shi ne kaɗai gadon da mahaifinsu ya bar musu ita da Gambo. Ina da tabbacin idan har Maimuna ta bar gidan nan Auwwa da ɗanta za su iya mallake mata gado. Kuma ko ba komai ɗa a gidan ubansa ya fi daraja, idan tana can ɗin ita kanta sai ta fi jin cewa a gidan ubanta take!”

Kawu ya yi shiru. Can kuma yace.

“A gaskiya Hajja ni na fara tunanin yi mata aure. Dan na lura da auren shi kaɗai ne zai kuɓutar da ita daga wanna baƙar azabar da take sha!”

Hajja ta girgiza kanta.

“Barau kenan! A auren yanzu masu lafiya ma ba auruwa suke da daɗin rai ba. Ballantana ita da take da jinya. Jinyar da iyaye ma kan guji 'ya'yansu idan suna ɗauke da ita, saboda gudun wahala, ballantana kuma miji. Kuma a irin auren yanzu ba na jin akwai wanda zai iya kula da Maimuna. Ka sani ba sai na nanata maka ba cewar cutar da Maimuna ke da ita na matuƙar bukatar kulawa. Kuma fa ni tun da nake da ita ban taɓa ji tace yau ga wani saurayi yace yana sonta ba, saboda kawai tana da sickler!”

Hajja ta ƙarasa maganarta a raunane. Saboda tausayin jikarta dake ƙara kamata. Shi dai Kawu shiru ya yi kawai, dan a zahirin gaskiya ya fara gajiya da abubuwan da Auwwa takewa 'yar ɗan uwansa. Kuma yana ganin kamar lokacin da zai ɗauki mataki ya yi.



MARIYA POV.

Zaune take a kan kujerar falo. Ta saka Hilal dake wasa a cikin car toy ɗinsa a gaba tana kallo. Kamar ta samu tv, a hankali ta ciro yatsun hannunta biyu da ta cusa a cikin gashin kanta.

Sannan ta gyara zamanta tana kallon yaron, sai kuma ta kai hannunta saitin da motar wasan nasa take. Sannan ta motsa hanun nata. Na take motar ta iyo gabanta kamar yanda ta motsa hanun nata.

Kallon yaron ta ci gaba da yi, kamar yanda shi ma yake kallonta. Sannan a hankali ta ɗaga hannunta na dama, ta saka a cikin sumar kansa me laushi, sannan ta ciro gashin kansa da mugun ƙarfi. Amma kuma ko gezau yaron bai yi ba.

Ya yi shiru kawai yana kallonta, hannunsa riƙe da rattle yana karkaɗawa. Gashin ta ɗaga tana kallo. A take ƙwayar idonta ta sauya kala zuwa ja. Sannan ta kalli Hilal, ta buɗe baki da shirin yin magana, fiƙoƙin haƙwaranta na sama suka ɗan ƙara tsayi kaɗan.

“Na gode Hilal. Saboda da ban haifeka ba da ba zan zama ta hannun daman shugaban bayin shaiɗan ba. Ina sonka!”

Ta ƙarashe tana shafa gefen fuskarsa. Shi dai kallonta yake kawai, kamar me fahimtar abin da take faɗi. Mariya ta janye hannunta daga kansa, sannan ta yi amfani da ƙarfin tsafinta ta tura car toy ɗin nasa inda take da.

Ta miƙe ta fita daga falo, ta zagaya bayan gidan, sai ta tsaya ta waiga hagu da dama, sanna ta rufe idonta, ta ɗora hannunta a bayan wuyanta, inda tambarin ƙungiyarsu ta bayin shaiɗan ke zane a wurin. Sannan ta furta.

“Mishk baksh hushk!”

Bata kai ga rufe bakinta ba wani farin matashi ya bayyana a gabanta, sanye da jajayen kaya. Idonta ta buɗe ta kalle shi, sannan ta miƙa masa gashin Hilal.

“Saƙo ne zuwa wurin Wahash!”

Matashin ya karɓi silin gashin guda ɗaya. Sannan ya kalleta.

“Saƙo zai isa ga shugaban bayin shaɗan!”

Yana gama faɗin hakan ya ɓace ɓat kamar almara. Tunawa da cewar yanzu haka ta kusa zama ta hannun daman Wahash ya sa ta yi murmushi. Sannan ta saka yatsun hannunta biyu cikin bakinta, ta fito da reza sabuwa daga ƙasan harshenta. Cike da nishaɗi ta shiga juya rezar tana murmushi.

Har ta koma falon ta zauna. Bata daɗe da zama ba wayarta ta shiga ringing, ganin Daddy ne me kiran ya sa ta ɗaga tana saita nustuwarta.

“Barka da safiya Daddy. Ina kwana!”

Ta gaida shi cikin sanyinta. Kuma cikin kamalarta dake burge kowa da ita. Daga ɗayan bangaren Daddy ya amsa sallamar, sannan ya faɗi abin da ya sa ya kirata.

“Yau da daddare ina son ganinku ke da mijinki!”

Ta tatare girarta wuri guda. Zuciyarta na raya mata ko dai Faruk ne ya je ya kai ƙararta?. Sanin zurfin ciki irin nasa ya sa ta kore wanna zargin, dan tana da yaƙinin cewa ba lalle ace ko Hajiyarsa ta sani ba ballantana Mu'az ya sani, har a je ga kan Daddy.

“To Daddy, bari na sanar da shi”

“A'a, ba sai kin yi hakan ba. Dan na faɗawa Mu'az ya sanar masa”

Ta gyaɗa kanta. Daga haka suka yi salama. Tunani barkatai a ranta. Dan ta kasa hasaso dalilin da ya sa Daddy ke son ganinta ita da Faruk.

*FCID (Force Criminal Investigation Department), Moshood Abiola Road, Garki, Abuja.*

MUKTAR POV.

“Wallahil azim da gaske nake muku yallaɓai!.

Please Login or Register in order to submit comment