Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kiran ya sa Mummy ta bi bayan kiran. Bugu uku Hajiya ta ɗauki wayar da sallama.

“Hajiya Ina wuni?”

Mummy ta gaisheta cike da girmamawa.

“Lafiya ƙalau Bara'atu!. Ya gida ya yaran?”

“Lafiyarsu ƙalau. Alhamdullilah. Ya wurin su Faruk da matarsa, Dan Adam mun yi waya da shi ɗazu”

“Faruk lafiya, amma ba lau ba Bara'atu!”

Jin hakan ya sa girar Mummy tatarewa wuri guda. Sannan tace.

“Me ya faru da shi?”

Hajiya ta girgiza kai.

“Matsalar Mariya ce ba komai ba. Duk da dai shi da kansa bai furta min hakan ba. Amma kuma ni na gane hakan tun ba yau ba!”

Mummy ta girgiza kanta.

“To ya za ayi Hajiya?. Tun da shi ba zai iya faɗar matsalarsa ba ballantana a ba shi shawara sai a taya shi da addu'a!”

Hajiya ta sauƙe numfashi.

“To... Haka ne... Allah ya dai-daita tsakani...”

Daga gaka suka ɗan taba hira, kafin suka yi sallama. Ko da Mummy ta gama abin da take a kitchen ɗin sai ta fito. Inda ta samu Maimuna da Maryam zaune a falo.

“Maimuna ya kamata ki tafi gida. Na ga lokaci ya ƙure. Kar Auwwa ta dakeki!”

Maimuna ta miƙe tsaye tana faɗin.

“To Mummy, bari na tafi!”

“Ga shi kuma yau Sadiq ba ya gari. Ballantana su raka ki shi da Maryam”

Maimuna ta girgiza kai tana faɗin.

“Ai ba komai Mummy. Zan iya tafiya Ni kaɗai”

Mummy ta jinjina kai.

“To mu kwana lafiya”

“Allah ya tashemu da alkairi”

“Amin”

Maimuna ta yi wa Maryam sallama, sannan ta fita. Tana tafiya a hanya tana tuna dalilin fitarta cikin wanna daren, kuma ba komai ya ja hakan ba face abinci da Auwwa ta hanata kamar yanda ta saba a wasu lokutan. Dan wani lokacin idan 'yan imanin na kusa ba ta hanata.

“Assalamu alaikum”

Ta yi sallama daga soron gidan. Sannan ta shiga. Gabanta ne ya soma faɗuwa tun da ta yi arba da Auwwa tsaye a tsakar gidan. Ta ƙame a gu ɗaya. Hannunta kan ƙugu tana jijjiga kamar me shirin hawa bori. Tun da ta ga haka ta san cewa yau kam ta banu.

“Daga gidan ub*n wa kike?”

Auwwa ta tambaya. Maimuna ta haɗiye yawu jikinta na rawa. Sannan tace.

“Gi... Gi... Gidan su... Maryam na je!”

“Saboda ke gaki kwaɗayayyiya ko?... Su kuma ga su dangin waliyyai, masu zuciyar tausayi?... Shi ne kika ɗauki ƙafa kika tafi gidan...”

Ta dakata tana cafkowa hannunta. A take Maimuna ta fashe da kuka. Sannan ta soma roƙon Auwwa.

“Dan Allah Auwwa ki yi haƙuri! Dan Allah! Dan Allah!..”

Auwwa ta ɗaga ɗayan hannunta da bata riƙeta da shi ba, ta doke mata baki har sai da jini ya fara fita daga bakin nata. Maimuna ta fashe da wani sabon kuka, a sanda ta ga Auwwa ta nufi gindin murhu da ita.

A gaban murhun ta durƙusar da ita, sannan ta sa wani cokali a cikin murgun, ta ɗaiko garwashi, ta ɗora a kan hannun Maimuna. Haka Maimun ta yi ta ƙwalla ƙarar azaba tana kuka tana roƙon Auwwa. Amma ko a jikinta. Ga shi su ba maƙota garesu ba bare a ji a kawo mata agaji.

“Shegiya matsiyaciya. Allah ya sa gobe ma idan na hukunta ki da abinci ki sake zuwa can ki ci!”

Maimuna ta ƙarawa kukanta sauti. Sannan ta durƙushe a wurin tana kuka me ban tausayi. Haka Auwwa ta miƙe tsaye ta tsallaketa ta wuce ɗakinta. Maimuna ta ci kukanta ta godewa Allah. Da ƙyar ta iya tashi ta shiga ɗakinta da babu bulb.

Da akwai, amma kwana nan Auwwa ta cire shi, wai za'a bawa Gambo. Saboda ɗakin da yake kwana nasu ya mutu. Haka ta zauna a cikin sauron da take iya jin kukansu a kunnenta. Da ƙyar ta janyo ledar magungunan da Mummy ta sai mata. Ta sha tana hawaye har zuwa lokacin.

Saboda wannan ƙunan da Auwwa ta mata a yau ya fi na ko yaushe. Da ƙyar ta lallaɓa ta shiga net ɗin. Tana jin yanda ƙashin bayanta yake amsawa. Saboda a kullum rana idan ta zo kwanciya sai bayanta ya amsa. Shi ya sa bata kwanciya kai tsaye, sai a daddafe.

Zaninta ta ja ta lulluɓe jikinta. Duk da yanzu sanyin ya fara ja baya, ba kamar na kwanakin baya ba. Amma da ma ita ko da sanyi ko babu sicklernta tashi take a ko wani lokaci. Har ɓarawo ya saceta ba ta daina zubar da hawaye ba.


HALIMA POV.

Kamar kullum, yau ma haka suka tashi a gidan babu ruwa ko na yin sallah ballantana na yin wanka ko girki. Tana ji tana ganin ƙananan yaran gidan zaune suna harkarsu aka sakata aikin ɗiban ruwa. Kuma ba ta isa ta musa ba, dan ya zame mata dole.

Da zunɓure-zumɓuren bakinta da komai ta fita daga gidan ɗauke da bokiti. Tana tafe tana hawayen da suka zame mata farilla. Gidan dake kusa da nasu ta shiga, sannan ta roƙi matar kan dan tana so a mata lamunin ɗiban ruwa a somon gidan. Matar bata hanata ba. Dan sun ɗan saba a zamanta a unguwar.

Sai da ta cika babbar randar gidan, sannan Mama Zulai tace ta je ta ɗebowa Jidda ruwan wanka. Wai akwai inda take son zuwa yau. Cike da baƙin ciki ta fita daga gidan. Amma ƙiwarta ta hanata ƙarasawa gidan da take shiga ɗiban ruwan. Sai ta tsaya a ƙofar gida. Jim kaɗan ta koma cikin gidan tace ai matar gidan tace ruwan ya ƙare.

“Ke maƙiwaciya ko? Ai ko za ki ga ƙiwa ganin idonki... Jidda! Jidda!”

Mama Zulai ta ƙarashe tana kiran Jidda. Jidda dake ɗakinta na ita kaɗai ta fito tana amsawa.

“Zo ki ɗibi ruwa a randa ki yi wankanki... Ke kuma idan kin ɗibi ruwan nan sai dai idan na mutu!”

A take idon Halima ya ciko da ƙwalla. Da ma kukan a kusa yake. Dan haka ta sake shi takaici na cika ranta. Tana ji tana gani 'ya'yan Mama Zulai suka dinga ɗiban ruwan suna ɓatawa. Kuma ba ta isa tace uffan ba.

Sai Mama Sadiya ce ta sa ɗaya daga cikin yaranta ƙanana ya je ya ɗibowa Halima ruwa dan ta yi wanka. Da haka Mama Sadiya ta kashe wutar kukan nata. Tana zaune yaron ya kawo mata ruwan. Sannan ta yi wanka ta shirya domin tafiya wurin aikinta.

Ko abinci bata zauna ci ba. Saboda ita yanzu ba ta jin za ta iya cin wannan busasshen ɗumamen nasu me kama da dutse. Babur ta hau, wanda ya sauƙeta a Ummul Banat boutique. Kuma shigarta cikin boutique ɗin ba wuya ta hango shi yana shigowa.

Wannan farin mugun sojan da ya sauƙe mata rabin fuska jiya. Tana ganinsa ta yi saurin ɓuya a bayan wasu kaya da akajera a cikin boutique ɗin. Dan ba ta ma son wani tsautsayi ya sake haɗata da shi, bare har ta kai ga ya sake marinta.


MU'AZ POV.

Kamar yanda ya kwanta da tunaninta haka ya tashi da shi. Har ya gama shirinsa na fita bata fita daga tunaninsa ba, da ƙyar ya iya samun sukunin cin abinci. Kuma yana gama cin abinci ya yi hanzarin fita daga gida. Kai tsaye ya nufi Ummul Banat boutique.

A sanda ya shiga wurin ya lura da cewar yanzu ma masu aikin wurin suke zuwa. Dan haka ya shiga raba idonsa a kansu, wai ko zai ga tauraruwa mai wutsiyar da ta hargitsa masa lissafi a iyaka jiya kawai. Amma bai ganta ba. Dan haka ya tsayar da ɗaya daga cikin ma'aikatan wurin, ya tambayeta.

“Dan Allah ina neman wata... Wata farar yarinya haka... Fara ce... Eh fara!”

Ya tsaya kame-kamen kammaninta. Dan gaba ɗaya ba yace ga yanda suffar jikinta take ba. Da ace yanayin idonta aka tambaye shi da ya zayyana komai game da shi, ba dan kar ya yi ƙarya ba, zai iya cewa ya san adadin yawan gashin idonta na ƙasa. Saboda su ne abin da ya fi kallo a fuskarta.

“Halima kake nema?”

Ma'aikaciyar ta tambaya. Sai ya kalleta yana tuna sanda wata ta kirata da Halima jiya. Kamar gaula, haka ya gyaɗa mata kai, sanna ya ƙara da.

“Eh, ita ce. Ya aka yi kika sani?”

Sai ya ga ta ɗan yi murmushi.

“Cry-cry baby kenan. Ai na ga sanda ka mareta jiya!”

Kamar wanda ita ma ta koɗa masa marin haka ya ji sauƙar maganarta a tsakiyar kansa. Hakan ta sa ya rintse idonsa. Kafin ya buɗe yana cilla mata tambaya.

“A ina zan ganta?”

“Bata daɗe da zuwa ba ai. Ka duba ta can, ba za ta wuce wurin ba”

Ya dubi inda ta nuna masa. Sannan ya mata godiya ya raɓata ya wuce. A hankali yake duba kayyayakin dake wurin. Har ya wuce, sai ya tsaya cak, saboda wani hoto da idonsa ya ɗauko masa. Ya dawo da baya, ya tsaya a inda ya ganta. Sannan a hankali ya kalli fusarta da ta ɓoye a tsakiyar kayan.

Suna haɗa ido Halima ta zaro nata idon. Sannan ta turo baki gaba tana shirin fashewa da kuka. Ta miƙe tsaye tana shirin fita da gudu. Kuma a lokacin ya aikata abin da bai taɓa zaton zai aikata ba. Kuma ya aikata abin da ita kanta Halima ba ta zata ba. Dan ba ta yi taku uku ba ta ji ya riƙo tsintsiyar hannunta.

Cak Halima ta tsaya. Ƙirjinta na dokawa da mugun ƙarfi. Saboda wani abu da ta ji ya sauƙa a kan fatar hannunta me tsananin taushi. Bata kai ga tantance abin da yake faruwa da ita ba ta ji ya dawo da ita baya. Sannan ya shiga janta zuwa waje.

Bata san me ya zare mata laka ba har ta kasa musa masa. Dan haka ya yi ta jan hannunta tana biye da shi har parking lot. Kallonsa kawai take, bakinta sake, hawaye kuwa tuni suka wanke mata fuska. A jikin motarsa ya tsayar da ita, sannan ya buɗe front seat. Ya zaunar da ita a cikin motar, amma kuma ƙafafunta duka biyu suna waje.

Har zuwa lokacin kallonsa kawai take tana sakewa, ashe ma jiya bata ƙare masa kallo ba. Saboda sai a yau take ganin ainahin kammanin fuskarsa da ba su bayyana gareta ba a jiyan. Fari ne sosai, yana da tsayi, kuma yana da manyan idanu. Ga wasu dogayen gashi da suka ƙawata mabuɗar idon nasa sama da ƙasa.

Ga kuma baƙin gashin girarsa da bai cika yawa ba. Kansa babu gashi sosai, sannan a fuskarsa babu gemu, sai dai ɗan siririn gashin bakinsa da babu gashi da yawa, dan sai ka yi da gaske za ka gane cewa yana da gashin bakin.

Yanda yake kallonta da fararen idanuwansa ya sa ta ji kamar ba a zaune take a kan kujerar motarsa ba. Sai ta ji kamar tana zaune a kan wani abu me tsananin laushin da ya fi gajimare. Duk sai ta ji kamar za ta narke a wurin. Ba ta dawo hayyacinta ba sai da ya miƙa mata gorar ruwa, sannan yace.

“Karɓi ki sha”

Sai ta kalli gorar. Sannan ta kalli farin hannunsa da ya riƙe gorar. Wanda yake ɗauke da fararen faratu, gakuma wani baƙin smart watch da ya saka a tsintsiyar hannunsa da ya sa farar fatar tasa ƙara haskawa da kyau a cikin safiyar.

Cikin wannan shagwaɓar da ta zame mata jiki ta ɗaga hannu ta karɓi ruwan. Sannan takai bakinta ta sha tana hawaye har zuwa lokacin. Yayin da Mu'az ya ke tsaye a kanta yana ƙare mata kallo. Shi kam ba zai ce jiya bai kalleta da kyau ba. Ya kalleta sosai, ta yanda ko da zana kammaninta za ayi idan aka tambaye shi zai iya wassafasu.

Amma wannan fuskar tata da ta shagwaɓe ce ta fi ɗaukar hankalinsa fiye da komai tattare da ita. Haka kawai ya ji ta burge shi. Yanda ta turo bakinta gaba, da yanda take ƙif-ƙifta idonta cike da zallar shagwaɓa, da kuma yanda hawaye yake zuba a kan fusarta. Kuma a hakan ya ga shatin yatsunsa huɗu a gefen fuskarta.

‘Lord have mercy!’

Ya faɗa a ranaa yana furzar da huci kaɗan.Kansa ya kawar gefe yana rintse ido. Sannan a hankali ya furzar da iska daga bakinsa. Ya buɗe idonsa sannan ya juyo ya kalleta.

“Kin ga!...”

Cak maganar da yake son fitarwa daga bakinsa ta tsaya a maƙoshinsa, saboda yanda Halima ta kalleshi da fararen idanuwanta dake zubar da ƙwalla.

“Hasbunallahu wa ni'imal wakil!”

Ya furta a iyaka kan leɓensa. Shi yanzu gaba ɗaya ma ya rasa me yake damunsa. Ko de yarinyar nan ta masa wani abin ne?... Sai ya girgiza kansa a fili yana haɗiye yawu. Ya yi gyaran murya, sannan ya ɗauke idonsa a kanta yana faɗin.

“A... Abin da na miki jiya ban kyauta ba... Shi ya sa na dawo yau dan na baki haƙuri... Ki yi haƙuri!...”

‘Kuma dan Allah kar ki sake shigo min cikin tunanina...’ Ya ƙarashe sauran maganar a zuciyarsa. Dan ba ya jin ta isa ya faɗa mata cewar jiya tunaninta ya hana shi bacci. Halima ta ci gaba da kallonsa da fararen idanuwanta da har zuwa lokacin ba su daina zubar da ƙwalla ba.

Mamakinta ɗaya, dalilin da ya sa yake bata haƙuri. Ya san cewa zai zo ya yi nadama zai mareta tun farko?. Sai ta ƙara turowa leɓenta na ƙasa gaba. Tana wani ƙif-ƙifta ido. Sannan ta shafa gefen fuskarta.

“To me ya sa ma za ka mareni jiya?. Kuma ma fa ni ba da gangan na bigeka ba. Sai da na yi ƙoƙarin kauce maka, amma ka kai ka ƙi ka kauce. Har ka san na bigeka na zuba maka ruwa a jikin rigarka... Wallahi jiya har na yi bacci ina kuka. Gefen fuskata sai zugi yake min, har ji nake kamar ba a jikina yake ba!...”

Mu'az ya yi shiru kawai yana kallon bakinta da take turowa gaba lokaci zuwa lokaci, da kuma yanda take maganar a shagwaɓe. Kafin ya kalli idonta da take kallon ƙasa da shi. Wato ita nan har damar yin ƙorafi ta samu, saboda kawai ya bata haƙuri?...

“Kuka da ma ai ke gwanarsa ce... Tun da yanzu ma ga shi nan kina yi”

Ya faɗi yana kallonta. Sai ta kalle shi ita ma. Sannan ta ɗauke kai tana ƙara tura baki gaba.

“Yanzu kin haƙura?”

Ya tambaya. Shi kansa tambayar na ba shi mamaki. Ita ma sai ta kuma kallonsa, sannan ta miƙe tsaye, hannunta riƙe da gorar ruwan da ya bata.

“Na haƙura amma ban haƙura ba!”

Ya ɗan ƙara girman idonsa cikin mamaki. Wai ta haƙura amma bata haƙura ba.

“Me ya sa kika haƙura kuma at the same time ba ki haƙura ba?”

Ta masa wani irin kallo da ya hautsina bugun zuciyarsa nan take. Sannan ta juya kanta tana kallon wani gefen... Sai tura baki take, kamar wadda aka wa dole kan sai ta yafe masa.

“Na haƙura dai”

Ta faɗa tana kallon gorar dake hannunta. Mu'az bai san sanda murmushi ya suɓuce daga kan leɓensa ba. Saboda shi haka kawai wannan abin da take yake burge shi. Yana jin ana cewa shagwaɓa, bai taɓa ganin mace me shagwaɓa ba sai yau...

A hankali ya sunkuya ya sa hannunsa a cikin motarsa ta saitin inda ta fito. Ya ɗauki chocolate. Sannan ya miƙe ya miƙa mata.

“Kina so?”

Sai ta masa irin wannan kallon na ɗazu. Sannan ya kalli chocolat ɗin.

“Ai ban sanka ba. Na sani ma ko kai ɗan yankan kai ne?”

Murmushi ya sake yi yana ɗaga kansa sama kaɗan. Sannan ya sauƙe yana faɗin.

“Ba ki ga ni soja ba ne?”

Ta kalli wandon kakin sojojin dake jikinsa. Dan daga shi sai wata baƙar T-shirt da ya sa. Ta kalli fuskarsa, wadda yanayinta kaɗai, da kuma askin kansa zai sa ta gane cewa shi sojan ne, amma sai ta girgiza kai.

“Ai akwai sojojin gona”

“Ni ba ɗaya daga cikinsu ba ne”

“Me cece shaidarka?”

Ta tambaya tana kafe shi da ido. Ya kuma yin murmushi yana girgiza kansa, sanna ya sa hannunsa ya kamo nata da bata riƙe gorar ruwan da shi ba. Ya saka mata chocolat ɗin a ciki, kuma ba tare da ya saki hannun nata ba ya kalleta yana faɗin.

“Ki daina jayyaya Leemat. Ba na son gardama na san kin yarda da ni, tun da har kika yarda kika sha ruwan da na baki. Dan haka ki karɓi wannan ma. Kyauta ce daga MJ zuwa Leemat! Sunana Mu'az... Wata ƙila hakan zai amfaneki wata rana”

Tun da ya riƙo hannunta Halima ke kellon fuskarsa. Saboda ita ta kasa gane wannan wani kalar mutum ne. Haka kawai sai ya yi ta riƙe mata hannu ba da son ranta ba?. Saboda ƙarfin hali biyan ba shi da ɗan kishiya?.

Kuma ita amfanin ne sunansa zai mata. Ai tun jiya take fatan kada Allah ya sa ta sake haɗuwa da shi, yanzun ma tsautsayi ne. Kuma tana fatan kada Allah ya sake nuna mata shi har ta koma gare shi. Hannunta dake kan nasa ta janye tana goge ƙwallar idonta. Sannan ba tare da tace masa komai ba ta juya ta nufi hanyar shiga cikin boutique ɗin.

Sai da ta shige ciki sannan Mu'az ya yi dariya. Haka kawai halinta na saurin kuka da langwami da kuma shagwaɓa suka saka shi cikin nishaɗi. Motarsa ya shiga ya tayar ya bar boutique ɗin. Kuma har ya isa barrack bai daina dariyar abin da Halima ta yi masa ba.

Cike da farin ciki Halima ta buɗe ledar chocolate ɗin da MJ ya bata. Saboda tun tana ƙarama Allah ya ɗora mata ƙaunar chocolate. Kuma iyayenta na sai mata chocolate ɗin sosai. Yanzu kuma da ruwa ya ƙarewa ɗan kada ta manta rabonta da shan chocolate ɗin.

Bite na fako da ta yi sai da ya sa ta ji ta kamar a wata duniya. Saboda ta yi matuƙar kewar chocolate fiye da yanda za'a iya kwatantawa. Lokaci guda ta yi murmushi. Saboda ta tuna da yanda mahaifinta yake yawan kawo mata chocolate.

“Allah ya ji ƙanka Daddy”

Ta faɗa a fili. Tana tuna duk wani kyakkyawan abu da ya gabata a rayuwata.

“Ke Halima! Zaman me kike a nan da ba za ki zo ki kama aiki ba?”

Ta juyo muryar Boss ɗinsu a bayanta. Da sauri ta sauƙa daga kan kujerar da take. Tana zare ido kamar wadda ta yi wa sarki ƙarya.

“Ki zo ki fara aikinki. Ga wasu can sun zo siyan kaya suna neman wanda zai taya su zaɓa!”

Ta gyaɗa kai da sauri tana nufar hanyar wurin da Boss ɗin ya nuna mata.

_________________

_Daɗina da gobe saurin zuwa😂_

_Salmanians!_

_Da alama Sir MJ dodon abinci ya haɗu da gamonsa_

_Share fi sabillilah❤️_

*Daga alƙalamin Salma Ahmad Isah✍️.*
*CANDY CE🦋.*

--------------------
_Kada a manta da biyan kuɗin littafi. Coz free pages sun kusa ƙarewa. To subscribe pay ₦300 to._

5487270431
Salma Isah
Monie point.

And send the evidence of payment via.

08130172702

#Candy
#SalmaAhmadIsah
°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*ƘADDARA CE!*


*©SALMA AHMAD ISAH.*
*CANDY🦋*

_ArewaBooks @SalmaAhmad_
_Wattpad @Salma_Ahmad_Isah_


*09*

MUKTAR POV.

Kamar yanda suka yi alƙawarin komawa bincike layin BB hotel sun koma ɗin. Amma a wanan karon da shirinsu suka tafi, ta yanda ko da za'a kawo musu hari za su iya kare kansu. Amma kuma rasa makama ya sa shi da Ali yin cirko-cirko a cikin layin da Munira ta bi sanda motar nan ta biyota. Saboda tun da suka shigo ba su ga wani me tallah ko me abin siyarwa ba. Hatta da masu wucewa sai dai ka gansu jifa-jifa.

Shi ya sa ya faɗawa kansa cewar dole ne ma a sace mutum a wannan layin, saboda babu zirga-zirga a layin. Sai dai idan har Allah ya hukunta faruwar abu a lokaci, to ba makawa sai ya faru. Dan har sun riga sun cire rai da samun wani abu. Sai Allah ya jefo da dalilin tonuwar asirin da suka daɗe da son ya tonu. Saboda a sanda suke da niyyar juyawa su koma inda suka fito. Muktar ya yi arba da wata mabaraciya ta shigo layin. Hakan ya sa ya yi wa Ali magana kan ya tsaya.

Tsayawar suka yi. Kuma a kan idonsu matar ta tsaya a jikin wata bishiya. Ta shimfiɗa buhu, ta zauna a kai, sana ta aje wani kwano a gabanta ta fara barar da ta saba yi kullum a layin. Muktar bai san sanda murmushi ya suɓuce masa ba.

“Ali mu je”

Yace kawai. Sannan ya nufi wurin matar. Ali ya bi bayansa kamar kullum, zuwa jikin bishiyar da matar ke zaune a ƙarkashinta. Har ƙasa suka durƙusa suka gaisheta. Sannan Muktar ya fara tambayarta.

“Iya. Mu jami'an 'yan sanda ne. Kuma muna bincike a kan ɓatan wata matashiya. A cikin binciken mu mun yi karo da wani bayani da yace an ga sanda ita wadda aka sace ɗin ta shigo layin nan. Dan haka muke so mu tambayeki ko kin ga sanda ta shigo!”

Iya me bara ta jinjina kai. Sannan tace.

“To yaro, faɗa min rana da kuma lokacin da aka ga ta biyo ta nan ɗin. Idan zai iyu ma ku faɗa min har da kalar tufafin jikinta. Saboda idan har nan layin ta iyo to tabbas zan ganta. Dan ni nan da kuka ganni kullum nan nake zama ina bara, sai dai idan da magariba ko da sassafe ta shigo layin. To shi ne dai ba zan sani ba!”

“To Iya. Yanzu za'a iya kaiwa kimanin wata ɗaya da kwanaki da faruwar abin. Kuma ranar asabat ne da yamma. Sannan tana sanye da jallabiya kalar ruwan goro. Haka fara ce, me ɗan siririn jiki!”

Muktar na kaiwa aya Iya me Bara na buɗe bakinta.

“Ƙwarai kuwa yara. Na ga sanda ta wuce ta nan. Kuma ka ga can...”

Ta ɗan yi fasali tana nuna musu ƙofar wani gida, Muktar da Ali suka juya suka kalli gidan, sannan suka sake kallonta a tare, sanda ta ci gaba da faɗin.

“... A ƙofar gidan can wata baƙar mota ta tsaya. Wasu mutum biyu mace da na miji da baƙaƙen kaya suka fito daga ciki, sannan suka ɗauketa suka jefa cikin motar!... Ni kuma ganin hakan ya sa na tsorata, shi ya sa na yi gum da bakina ban taɓa faɗawa kowa ba”

“To iya shin kin iya ganin fuskokin waɗan da suka ɗauketa?”

Muktar ya tambaya da sauri. Iya me bara ta girgiza kanta.

“A'a. Ban gani ba. Amma ranar da aka saceta akwai wani matashi ɗan can gidan da shi ma ya ga sanda suka saceta, kuma har hoto me motsi ya ɗauke su a wayarsa. Da yace zai faɗawa 'yan sanda, amma sai mahaifinsa ya hana shi!”

Muktar da Ali suka dubi juna. Sannan suka jinjina kai a tare.

“Iya me nene sunan matashin?”

“Audil”

Iya ta amsa. Yanda ta kira sunan Audil ɗin instead of Abdul ya sa su yin dariya. Kafin Muktar ya ɗebo kuɗi ya bata. Har suka bar wurin tana saka musu albarka. A ƙofar gidan da ta nuna musu suka tsaya. Ali ya yi sallama. Sannan suka tsaya jiran fitowar masu gidan.

Da farko mahaifin Abdul ɗin ne ya fito. Sai da suka masa bayanin abin da ke tafe da su, sannan ya kira Abdul ɗin. Ya saka su a gaba yana son ganin abin da zai faru. Dan ko sama da ƙasa za su haɗe ba zai bari su tafi da ɗansa headquarter ba. Idan videon suke son kallo shi bai hana ya nuna musu ba. Za ma su iya turawa a nasu wayoyin, amma su tafi da ɗansa shi ne abin da ba zai lamunta ba.

“Abdul. Idan har ka san kana da videon nan a wayarka. Ka daure ka nuna mana. Saboda idan har ba ka nuna mana ba rayuwar sauran al'ummar gari tana cikin haɗari!”

Abdul da ya sunkuyar da kansa ya ɗago ya kali babansa. Wanda ya harɗe hannaye a ƙirji yana kallon kowa cikinsu. Sannan ya kalle su.

“Idan da akwai a wayarka ka nuna musu. Ni ban hana ba, amma fa daga nan babu inda za ka ƙara ɗaga ƙafarka. Ba zan bari ka tafi ko ina ba Wallahi!”

Faɗin baban Abdul. Kuma kalamansa suka sa Abdul ya sa hannu a aljihun wandon jikinsa. Ya ɗauko wayarsa ya cire password. Sannan ya nemo videon a inda ya ɓoye. Ya kunna, ya miƙawa Muktar.

Muktar ya karɓi wayar da dukkan zumuɗin duniya. A zatonsa zai ga abin da zai kawo ƙarshen matsalar ne. Bai sani ba cewa yanzu ne ma matsalar za ta soma. Saboda tonuwar asirin makashin ba ya nufin zuwan ƙarshen matsalar. Sai dai ma ya zama wani sabon mafarin tarin matsaloli.

Da farko da ya ga videon da fuskar macen dake cikinsu bai yarda ba. Sai da ya dawo da shi baya ya sake kalla, ya sake sakewa, wai dan ya tabbatar da abin da yake gani ko gaskiya ne. Duk da sau ɗaya ya taɓa ganin matar Faruk ya ganeta. Saboda kwanaki da yake ta neman layin Faruk ɗin ba ya samu ya sa

Please Login or Register in order to submit comment