Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba.

Da Daddy ya sallame su ma ta riga shi fita daga falon na Daddy. Ta wuce sashin Mummy, yayin da shi kuma ya tsaya a wurin Mu'az dake compound. Sun daɗe a gidan. Kafin suka yiwa kowa sallama suka tafi.

Faruk ya ɗauka cewa Mariya ta ji nasihar Daddy, ta kuma ɗauketa kamar yanda Daddyn ke fata, amma sai ya ga saɓanin haka. Dan suna komawa gida ta wuce ɗakinta ɗauke da Hilal a hanunta, wanda ya yi bacci. A mamakance ya bita da kallo har ta shige ɗakin. Ji ya yi yau ba zai iya turewa ba kamar yanda ya saba, dan haka ya bita ɗakin dan ya mata magana. A bakin gado ya sameta tana kwantar da Hilal.

“Mariya”

Ya kira sunanta. Ta juyo ta kalleshi.

“Na ɗauka cewar ko da laifi na miki, za ki yafe min saboda nasihar da Daddy ya mana ɗazu. Na ɗauka cewar ko da kina jin haushina ne za ki sauƙo saboda maganar Daddy... Amma kuma kin tabbatar min da ba haka ba ne, tun da har kika dawo ɗakinki a maimakon nawa.”

Mariya ta yi shiru tana kallonsa. Wai da shi haka yake zaton tana da sauƙin kai?. Ai ko ya yaudari kansa da zuciyarsa. A ta waje ne jama'a ke mata kallon me sauƙin kai, amma a ta ciki sam Mariya bata da taushin zuciya.

“Faruk! A gaskiya ba na jin zan sake haɗa ɗaki da kai. Ballantana har na haɗa shimfiɗa da kai... Wannan a baya ne, ban da yanzu!”

Ta yi maganar tana juya masa baya, tare da nufar barthroom. Amma sai ya riƙo hannunta ya dawo da ita baya. Ta kalli hannunta da ya riƙe, sannan ya kalli fuskarsa.

“Faruk! Are you trying to hurt me?”

Ta tambaya a mamakance. Faruk ya kalli hannunta da ya matse. Da sauri ya saki hannun nata, sannan yace.

“Mariya, look, I don't want to hurt you or cause you any harm. I just want to know if you've stopped loving me. Just be honest with me!... A farkon aurenmu ba haka muke zaune ba. There is love and care. Me ya sa komai ya sauya yanzu? Could you explain to me why?”

Ko gezau ba ta yi ba ballantana ta ba shi amsa. Jin haka ya sa Faruk ya ɗora yatsun hannunsa biyu a kan karan hancinsa ya rintse ido. Sannan ya buɗe idonsa.

“Mariya!. Idan sona kika daina ya kamata ki faɗa min. Ni kuma a shirye nake domin sawwaƙe miki, da ace mun ci gaba da yin irin wannan zaman da za mu riƙa cutar da junanmu!...”

Jin yana batun rabuwa ya sa Mariya ta saka ƙwayar idonta cikin nasa. Sannan a hankali bakinta ya motsa cikin faɗin wata kalma. A take ƙwayar idonta ta sauya kala zuwa ja.

Wani irin jiri Faruk ya ji ya kwashe shi. Hakan ya sa ya yi saurin dafe kansa yana yin baya. Idonsa ya rintse gam, sannan ya buɗe yana jin wani irin juyawa da kansa yake. Juyowa ya yi ya kalli Mariya dake tsaye. A take ya ji tunaninsa ya birki ce. Sai ya kasa tuna sanda ya shigo ɗakinta. Ya kasa tuna maganar da yake, kamar kuma wani abu yake nema a wurin wani.

“Mary!”

Ya kira yana kallonta.

“Papi lafiyarka ƙalau?”

Sai ya sauƙe hannunsa daga kansa yana kallon ɗakin kamar baƙonsa. Gaba ɗaya ya kasa tuna abin da ya faru a ɗakin.

“Me nake yi a nan?”

Wani irin makirin murmushi ta yi na gefen baki. Sana ta nufe shi, ta tsaya a gabansa ta yanda har suna musayar numfashi.

“Baka da lafiya Papi. Mu je na kaika ɗakinka”

Ta faɗi tana kama hannunsa na dama. Sannan ta shiga jansa zuwa waje. Kuma bai musa mata ba. Ya bi bayanta yana son tuna abin da ya kai shi ɗakinta. Amma ya kasa tunawa. Har ɗakinsa ta kai shi. Sannan ta zaunar da shi a bakin gado. Ta ɗauki ruwa ta bashi ya sha, har zuwa lokacin bai fita daga cikin ruɗanin da ya shiga ba.

“Ba na so ka cika zurfafawa a tunani. Dan haka ka kwanta ka huta”

Ta faɗa tana shafa sumar kansa. Yanzu ma bai musa mata ba. Kansa kawai ya gyaɗa sannan ya kwanta a kan gadon ba tare da ya sauya kayan da ya fita da su ba. Ba ta bar ɗakin ba sai da ta tabbatar da ya yi bacci. Sannan ta sumbaci goshinsa, ta miƙe ta fita.

A yanzu ba ta shirya rabuwa da Faruk ba, saboda har yanzu tana sonsa, kuma bata jin za ta iya rabuwa da shi, sai dai idan har shugaban bayin shaiɗan ya buƙaci ta sadaukar da shi ne. To a nan fa ba makawa za ta bayar da shi. Amma yanzu dai kama bata shirya ba.

(Aikin ɓirr! In ji tusa🧐)

*Daga alƙalamin Salma Ahmad Isah✍️.*
*CANDY CE🦋.*

_Share fi sabillilah❤️_

------------------------
_A halin yanzu mun yi rabin free pages, dan haka sai ku shirya domin fara biyan kuɗin littafi, tun da idan baku manta ba na ce muku isn't free._

_Ga duk wanda ya shirya biya, sai ya biya ₦300 to_

5487270431
Salma Isah
Monie point FCMB

Shaidar biya kuma ta wannan numbern wayar.

08130172702.

Ku tabbatar wannan tafiyar bata wuce ku ba, dan har yanzu ba ayi komai ba a tafiyar.

#Candy
°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*ƘADDARA CE!*


*©SALMA AHMAD ISAH.*
*CANDY🦋*

_ArewaBooks @SalmaAhmad_
_Wattpad @Salma_Ahmad_Isah_


*06*


*BB paradise hotel.*

MUKTAR POV.

Muktar da abokin aikinsa ne tsaye a gaban ginin hotel ɗin ‘BB paradise’. Binciken hanyar da Munira ta bi a sanda ta fito daga ginin hotel ɗin shi ne ya sa suka buga uban sammako.

“Sir!”

Muktar ya juyo ya kalli Ali, abokin aikin nasa da ya kirashi.

“Me zai hana mu binciki CCTV camera footage ɗin wancan super market ɗin?. Ina ga kamar za mu iya samun wani abu”

Muktar ya ɗaga kai ya kalli super market ɗin dake opposite da hotel ɗin. Kafin ya duba CCTV cameras ɗinsu dake saƙale a gaban ginin. Ba tare da yace komai ba ya nufi titi da nufin tsallakawa. Ali ya bi bayansa har zuwa cikin super market ɗin. Ko da suka shiga sai suka iske cewa babu ma'aikata sai masu aikin share wurin.

“Barkanku da aiki”

Mutum biyun dake aiki a wurin suka amsa.

“Dan Allah zan iya ganin ma'aikatan wurin nan?”

Suka dubi juna a tare. Kafin suka kuma dubansu.

“Eh Abubakar manager ne kaɗai ya zo”

Muktar ya gyaɗa kansa.

“To ko zan iya ganin shi managern?”

Suka kuma diban juna. Alamun dai basu yarda da su ba. Kuma su Muktar ɗin sun gane hakan.

“Mu jami'an 'yan sanda ne... Za ku iya yarda da mu”

Muktar ya faɗa yana nuna musu ID card ɗinsa. Sai a lokacin suka ɗan yarda da su kaɗan. Kuma da haka ɗaya daga cikinsu ya juya ya nufi ƙofar wani office. Jim kaɗan ya dawo tare da wani mutum, wanda da alama shi ne Abubakar managern.

“Salamu alaikum”

Faɗin Muktar yana miƙa masa hannu alamun su gaisa. Abubakar ya amsa yana miƙa masa nasa hannun suka gaisa, kafin suka gaisa da Ali. Sai ya ci gaba da kallonsu cikin rashin sani.

“Ko zan iya sanin dalilinku na son ganina?”

Ya tambayi tambayar dake rubuce a kan fuskarsa. Muktar ya yi murmushi.

“Mu jami'an 'yan sanda ne. Kuma muna bincike a kan wani kisa da aka yi wata ɗaya da ya wuce. Binciken mu ne ya biyo ta kan super market ɗinku. Amma fa ba wai abin ɗaga hankali ba ne, taimakonku kawai muke buƙata!”

“Allah ya sa za mu iya”

“Da yardar Allah ma za ku iya. A ranar da aka rasa victim ɗin kafin a tsinci gawarta ta ziyarci wannan hotel ɗin dake opposite da super market ɗinku. Kuma da muka duba footage na ranar da ta ɓata ba mu samu komai ba. Hasali ma an goge duk wani footage na ranar. Dan haka muke buƙatar taimakonku. Ta hanyar nuna mana footage ɗin ranar da ta ɓata daga CCTV Cameras ɗinku!”

Manager ya yi shiru kawai. Kamar ya yarda kamar kar ya yarda, kuma ba komai ya sa ya ji kamar kada ya yarda ba face jin batun ɓata da kisan kai.

“Kaga Abubakar Sadik. Taimakon da za ka mana a wannan case ɗin shi zai sa mu iya kama mai laifin da ya kasheta. Idan har baka taimaka mana ba. Makashin zai ci gaba da yawo a cikin gari, kuma cikin kwanciyar hankali, tunanin cewa ya aikata wani kisa ba tare da an kamashi ba zai ƙara ba shi access na ƙara kashe wani. Kaga hakan ya bawa aikinsa damar ci gaba... Babu wanda ya san gobe, wata ƙila sai ka ga har ya faɗi kan wani naka!”

Jikin manager ya yi sanyi. Kuma kalaman Muktar na hikima sun taɓa zuciyarsa. Dan haka ya gyaɗa kansa. Sannan yace su biyo shi zuwa CCTV control room.

Shi da kansa ya binciko musu footage ɗin ranar da aka yi kisan. Kuma cikin taimakon Allah sai suka samu abin da suke so. Dan tun daga kan zuwan Mubarak hotel ɗin, da zuwan Munira duk sun gani. Kuma har fitar Munira daga hotel ɗin sun gani. Sannan a cikin footage ɗin suka ga wata baƙar mota ta fito daga hotel ɗin, ta bi bayan Munira. Footage ɗin na zuwa nan ya tsaya...

“Daga wannan camerar ta 08 babu wata a gaba?”

Muktar ya tambaya. Manager ya gyaɗa kai.

“Eh, daga wannan babu wata camera!”

Muktar ya gyaɗa kansa. Sannan suka yi wa Abubakar godiya suka fita daga super market ɗin. Jikin motarsu suka koma. Inda Muktar ya tsaya a jikin motar yana nazari. Ganin ya yi shiru ya sa Ali faɗin.

“Sir! Yanzu mi ye abin yi na gaba?”

“Dole muna buƙatar sanin mutanen cikin motar nan. Sannan bayanai a kan motar, da kuma wuri na gaba da Munira ta je bayan hotel ɗin nan...”

Ya ja fasali yana saka hannayensa cikin aljihun wandonsa. Sannan ya juya ya kalli hanyar da suka ga Munira ta bi a footage ɗin da suka kalla.

“Wata ƙila waccan kwanar ta kusa da me lemon can ta shiga. Wata ƙila kuma ta miƙe hayar nan ne har zuwa wurin da suka saceta. Wata ƙila kuma tun a sanda ta fito daga hotel ɗin nan suka saceta. Zargin ya taru ya min yawa Ali. Komai zai iya faru”

Ya dakata yana rage girman idonsa. A lokacin da wata mata ta tsaya kusa da mai lemon da yake kan wata kwana.

“Ali! Mu je”

Yana faɗin hakan ya soma tafiya. Ali ya bi bayansa ba tare da neman ba'asi ba. A gaban rumfar me lemon suka tsaya. Sai da suka gaisa da shi sannan Muktar yace.

“Baba akwai wani abu da ya faru wata ɗaya da ya wuce. Ban sani ba ko idan na maka tambaya a kai za ka iya tunawa!”

Tsoho me lemo yace.

“Eh to yaro. Yi tambayarka, idan na iya tunawa in amsa maka, idan kuma na gaza sai a ɗau haƙuri”

“Allah ya baka ikon tunawa Baba. Wata ɗaya da ya wuce. A wata ranar asabat, da misalin ƙarfe shida na yammaci. Akwai wata matashiya, fara me ɗan siririn jiki, da ta zo wucewa ta nan hanyar!?”

Baba mai lemo ya yi shiru yana son ya tuna. Can kuma sai yace.

“Wani kalar kaya ne a jikinta?”

“Baba tana sanye da abaya ruwan goro!”

Ali ya amsa masa. Baba ya kuma yin shiru, can kuma sai ya gyaɗa kai.

“Ƙwarai kuwa da gaske, na gano, lokacin da ta zo ta wuce ina zaune a nan. Har nake cewa wata ƙila wani mugun abin ne ya biyota...”

Muktar ya yi murmushi.

“Yauwwa Baba. To ko za ka iya tunawa da inda ta yi bayan ta wuce ta nan ɗin?”

“Ƙwarai zan iya tunawa. Dan har ta ƙulewa ganina idona na kanta. Saboda na ga kamar akwai wata baƙar mota dake bibiyarta.”

Tsabar jin daɗi yasa Muktar zama kusa da baba. Sannan yace.

“Haka nake son ji Baba. To nuna min ta inda ta bi”

Baba ya juya bayansa, sannan ya nuna musu layin dake bayansa.

“Ta nan haka ta bi. Kuma har ta ɓace min baƙar motar nan na binta”

Muktar ya gyaɗa kansa. Sannan ya miƙe tsaye. Ya miƙawa baba Hannu suka kuma gaisawa. Ya masa godiya. Suka juya zuwa wurin motocinsu. Yana shirin shiga motar ya tsinkayo muryar Ali cikin faɗin.

“Sir ya kamata mu shiga layin mu bincika ko akwai wanda ya ga sanda aka ɗauketa”

Ba tare da ya juyo ba ya yi murmushi. Sannan yace.

“Ka ɗan juya bayanka ta ɓarin hagu. Akwai wani matashi a kan mashin da yake amsa wayar ƙarya tun sanda motarmu ta tsaya a nan. Ɗa leƙen asiri ne. Idan muka ce za mu shiga layin a yanzu akwai matsala. Ni da kai ne kawai, kuma mu duka ba mu da bindiga. So sarkin yawa ya fi sarkin ƙarfi. Yanzu mu koma headquarter. Next time za mu haɗe da shi!”

Yana gama faɗin hakan ya buɗe motarsa ya shiga ciki. Ali ya juya ya kalli matashin dake waya yana satar kallonsu. Kuma ba tare da yace komai ba shi ma ya zagaya ta ɗayan ɓangaren ya shiga motar ya ja suka bar wurin.

*No.42, Inuwa Wada crescent, Utako, Abuja.*

*08:32 na safe.*

FARUK POV.

Kasancewar yau an tashi da yayyafi ya sa daddaɗar iskar dake haɗe da sanyin ruwan saman a aka yi yake kaɗa curtains ɗin dake ɗakin. Iskar da ta ɗan ƙara ƙarfi ce tasa windown ɗakin ya buɗe. Sannan iskar ta kaɗa labulen da yake a saitin inda gadon ɗakin yake.

Sanyin iskar ya busa a kan fatar jikinsa. Hakan ya sa ya motsa ƙafafunsa dake cikin takalmi. Kafin ya rintse idonsa dake rufe, saboda wani ciwo da kansa ya fara lokaci guda. Hannunsa na dama ya ɗaga ya ɗora a kansa. Sannan ya ja iska ta bakinsa cike da jin zafin ciwon kan.

A hankali ya buɗe idonsa. Sannan ya rufe, ya kuma buɗewa, ganin gari ya yi haske ya sa ya yi saurin miƙewa zaune. Ya dafe kansa dake masa ɗan karen ciwo. Da ƙyar ya miƙe tsaye ya shiga banɗaki. Bayan wani lokaci ya fito. Ya yi sallahr asuba da ta wuce shi. Bayan ya idar bai miƙe daga kan dardumar ba sai da ya yi ta jero istigfar.

Saboda rashin yin sallahr a kan kari. Haka ya zauna a kan dardumar yana nazarin da bai san na miye ba. Har yanzu yana jin kamar akwai abin da ya manta, kamar akwai wani abu da aka goge daga cikin tunaninsa. Amma kuma ya kasa tuna miye. Jin an buɗe ƙofar ɗakin ya sa ya ɗaga kansa ya kalli Mariya da ta shigo. Ganinsa cikin wannan yanayin da ya kwana da shi a jiya ya sa ta yi miskilin murmushi.

“Sai yanzu ka farka?”

Ya kalleta. Amma bai ce mata komai ba. Dan ji ya yi bakinsa ya yi nauyi, ga kansa da yake sarawa.

“Ya Mu'az ya zo yana waje. Yace ya jika shiru ba ka je barrack ba, kuma ya kira wayarka baka ɗaga ba, shi yasa ya zo!”

Da ƙyar ya iya miƙewa tsaye. Sannan ya sa hannu ya cire rigar jikinsa yana faɗin.

“Ki ce masa ina zuwa!”

Mariya ta juya kai, sannan ta fita daga ɗakin. Ta dawo ƙasa. Idan ta bar Mu'az da Hilal zaune suna wasa. Ganin ta fito ita kaɗai ya sa Mu'az ya ɗaga kai ya kalleta.

“Yana ina?”

Ta zauna a kan kujera tana faɗin.

“Wanka zai yi. Amma yace yana zuwa”

Mu'az ya gyaɗa kai, sannan yace.

“Me ya same shi wai?”

“Kwana ya yi da ciwon kai, shi yasa ya makara”

Ya kuma gyaɗa kansa yana ɗaga Hilal. Suka ci gaba da wasa da Hilal ɗin, har zuwa sanda Faruk ya sauƙo sanye da kayan aikinsa, wato kakin sojoji. Kana ganinsa ka ga wanda ba ya cikin nutsuwa, ko kuma mara lafiya.

“Kaigama!”

Mu'az ya kira yana miƙewa tsaye, yana riƙe da Hilal. Faruk ya ɗan yi murmushi yana lumshe idonsa da kalarsa ta sauya. Sannan ya buɗe shi a kan Hilal.

“Idan kan naka bai daina ciwo ba za ka iya komawa ka huta”

Faruk ya girgiza kansa.

“A'a. Zan iya zuwa barrack. Mu je kawai”

“Kuma fita za ka yi ba tare da ka ci abinci ba?”

Mariya dake gefe ta faɗi. Hakan ya sa suka dubeta a tare.

“Yanzu na makara. Ki aje min abincin dare kawai”

Faɗin Faruk.

“A'a ka zauna ka ci abincika kawai”

Cewar Mu'az.

“Bana jin cin abincin ne. Mu je kawai, zan ci abincin a barrack”

Mu'az ya jijina kansa, sannan ya miƙawa Mariya Hilal. Suka mata sallama suka fita a motar Mu'az. Suna tafiya a hanya Ƙaddara tasa Mu'az tsayawa a wani boutique me sunan ‘UMMUL BANAT BOUTIQUE’. A sanda motar ta yi parking a harabar boutique ɗin Faruk ya ɗaga kansa ya karanta sunan boutique ɗin. Sannan ya kalli Mu'az yana faɗin.

“MJ me za mu yi a nan?”

Mu'az na cire seat belt ya amsa da.

“Na'im ne yace na sai masa sweater”

“Okay mu je”

Ya faɗa yana buɗe ƙofar motar. A tare suka nufi ƙofar shiga boutique ɗin. Boutique ɗin da ƙaddarar Mu'az ke zaune a ciki. Boutique ɗin da zuwansa cikinsa zai sauya rayuwarsa gaba ɗaya.

Kamar yanda Na'im ya wassafa masa yanayin sweatern da yake so ita ya ɗauko masa har guda biyu. Rigunan na riƙe a hannunsa suka nufi wurin cashier. Ya juya kansa yana yi wa Faruk magana. Ya ji ya ci karo da mutum. Kuma a lokaci guda abinda ke hannun mutumin da sukayi karon, wanda yake da tabbacin ya fishi tsayi ya zube a jikin rigarsa.

A lokaci guda zuciyarsa ta tafarfasa har ta fara shirin ƙonewa. Hakan ya sa ba tare da ya duba da wa ya ci karo baya ɗaga hannunsa da bai riƙe rigar da shi ba, ya sharara wa budurwar dake tsaye a gabansa mari.

Wata iriyar ƙamewa ta yi. Ta saki kofin ruwan dake hannunta, wanda ruwan cikin ya zube a jikin rigarsa. Sannan ta ɗora hannunta na dama a kan kuncinta. A take hawaye suka soma zubowa daga raunannun idanuwanta. Da ƙyar ta iya ɗaga idonta ta saka su cikin nasa.

Kuma shi ma sai a lokacin ya samu damar kallonta. Wata farar matashiya ce, da a shekaru ba za ta ɗara Mima ba. Hawayen da suka wanke mata fuska ya sa ya ga fuskar tata har wani ƙyalli take. Sanye take da farar Oxford shirt. Da kuma baƙar straight skirt. Ta yafa baƙin veil a kanta. Kuma ya lura da kamar kayan su ne wanda masu aikin wurin suke sakawa.

Ƙwayar idonta dake rawa a kan fuskarsa, da kuma hawayen da ya taru a cikin idonta da yake ƙyalle saboda hasken fitilun wurin yasa ya ji kamar yana nitsewa cikin wani abu me kama da gajimare. Akwai rauni, haɗe da neman taimako a cikin idonta. Sannan ya ga fata da kuma sa rai a cikinsu. Yanayin yanda ta turo fatar bakinta ta ƙasa zai sa ka san cewa shagwaɓɓaɓɓiya ce tun tana da ƙarancin shekaru, ko kuma wadda gata ya yi wa yawa.

“Mu'az!”

Faruk ya kira yana taɓa kafaɗarta.

“Humm!”

Ya amsa kamar wanda ya dawo daga WATA DUNIYA. Ya kalli Faruk, sannan ya sake kallon budurwar dake tsaye a gabansa har zuwa lokacin. Tana dafe da kuncinta. Ga hawayen da take zubarwa, sannan bakinta da ta turo cikin shagwaɓa yana rawa kaɗan. ‘Oh lord have mercy!’ Ya faɗi a zuciyarsa.

“Wai me ya faru ne?”

Faruk ya tambaya. Amma sai Mu'az ya kasa magana. Ya ci gaba da kallonta. Har zuwa sanda wata murya ta kira sunan.

“Halima!”

Daga bayansa. Hakan ya sa ya juya, yayin da ita kuma budurwar me suna Halima ta kalli Kairat ƙawarta da ta kirata. Dan haka sai ta sauƙe hannunta daga kan fuskarta. Ta sunkuyar da kanta ƙasa, ta raɓa Mu'az ta wuce wurin Kairat.

“MJ!”

Faruk ya kuma kira. Mu'az ya juyo ya kalle shi. Sai kuma ya kalli rigunan da yake riƙe da su, haka kawai ya aje rigunan a kan wasu kaya. Ya nufi hayar fita. Kai a kulle Faruk ya bi bayansa. Dan shi sam bai ga tahowar yarinyar ba, ballantana ya ga sanda suka yi karo da Mu'az ɗin.

“Me ya faru wai?”

Kairat ta tambayi Halima da har zuwa lokacin bata daina hawaye ba. Sai ta juyo mata da ɓarin fuskarta na dama. Inda shatin hannun mutumin da ya mareta ya fito har guda huɗu. Wurin har ya yi ja. Ya kuma kumbura.

“Na shiga uku? Wai wancan sojan ne ya mareki haka?”

Kairat ta tambaya tana zaro ido. Tare da kama gefen fuskar ƙawarta tana ganin yanda wurin da aka mareta ya yi ja. Cike da shagwaɓar da ta zame mata jiki Halima ta gyaɗa kai tana goge ƙwalla. Sannan cikin murya me sanyi tace.

“Haka kawai bawan Allahn nan ya sharara min mari, wai dan na bige shi. Kuma fa sai da na kauce masa, shi ne bai kula ba!”

“To Allah ya saka miki. Ya hana masa sukuni saboda marainiyar Allah da ya cutar!”

Kamar an kunna famfo haka ta ci gaba da zubar da ƙwalla. Kuma da ma ita can haka take. Abu kaɗan kan iya sakata kuka, ballantana yanzu da ta sha mari. Har zuciyarta ta jawa wannan azzalumin sojan Allah ya isa ta fi sau dubu.


MARIYA POV.

Kukan Hilal da ya cika ɗakinta ne yada ta ja dogon tsaki. Sannan ta juyo ta kalle shi. Yanayin zaman da ya yi kaɗai ya sa ta gane cewa bayan gari ya yi a cikin diapers ɗin dake jikinsa. Wani tsakin ta ja, sannan ta ci gaba da latsa wayarta hankali kwance. Kukan nasa da ya ci gaba da tashi ya sa ta kalle shi a hasalle, sannan ta daka masa tsawar da za ka dafa ƙur'an kan cewa ba ita ta yita ba.

“Ka rufe min bakinka a wurin!”

Amma bai yi shirun ba. Sai kukan nasa da ya ƙarawa volume. Wani dogon tsakin ta kuma ja. Sannan ta miƙe tsaye ta fita daga ɗakin, ta kulle ƙofar ɗakin. In yaso ya je can ya yi ta yi shi kaɗai.

Tana taka stairs tattoo ɗin dake bayan wuyanta ya soma haske. Hakan ya sa ta ƙame a wuri ɗaya. Domin ta san kira ne daga shugaban bayin shiaɗan. Bata raba ɗayan biyu ba suffar Wahash ta bayyana a tsakiyar falo. Hakan yasa ta sauƙa ƙasa da gudu. Sannan ta yi saurin zubewa a ƙasa, ta yi wa shugaban bayin shaiɗan sujjada.

“Giram gareka Wash. Duk wani shugaba da ba kai da shaiɗan ba ba a kan gaskiya yake ba!”

(A'uzubillah!)

Wahash ya sa hannu ya ɗago da ita, ya miƙar da ita a kan ƙafafunta. Amma kanta a ƙasa cike da girmamawa irin tasu ta 'yan wahala a duniya.

“Rezor!”

Wahash ya kira. Hakan ya sa ta ɗaga idonta ta kalli fuskarsa.

“Mijinki da ɗan uwanki, da kuma wani jami'in ɗan sanda na shirin haƙa ramin binne kansu!”

Cike da rashin fahimta tace.

“Ban gane ba shugaban bayin shaiɗan!”

Wahash ya juya bayansa. Sannan ya yi taku biyu gaba. Ya ɗan juyo kaɗan ya kalleta.

“Duk da na sa a goge duk wata shida da za ta nuna cewar ke kika kashe Munira da kuma Danesh sai da suka yi ƙoƙarin zaƙulo wani abin. Yanzu haka shi ɗan sandan da suka ɗora a kan aikin yana ta binciken gano wanda ya kashe Danesh da Munira, domin kuwa duk sun gane cewa makasan nasu mutum ɗaya ne ko biyu. Ko ma sama da haka, kuma da alama suna daf da cimma gano ki. Ganoki kuma yana nufin gane ƙungiyar jajayen bayin shaiɗan!...”

Mariya ta girgiza kanta da sauri, sannan ta tsaya avbayan Wahash tana faɗin.

“Yanzu wani mataki aka ɗauka a kansu... Da ace asirin ƙungiya ya tonu tadalilina gwanda a kawar da mijina da kuma ɗan uwana. Idan har asirin ƙungiya ya tonu ina zan saka kaina Wahash?!”

Wahash ya girgiza kansa, sannan ya juyo suka fuskanci juna.

“Mijinki da ɗan uwanki ba su ya kamata mu kashe a yanzu ba. Shi wannan ɗan sandan me sunan Muktar shi ne babban haɗarinmu a yanzu. Dan haka shi ne wanda za mu fara kawarwa a duniya”

Ba tare da ta nemi sanin waye ɗan sandan ba tace.

”Ina fatan yin hakan ya kawo ƙarshen wannan tsinannen binciken da aka fara. Da dukkan goyon bayana na amince da hakan Wahash!”

Wahash ya gyaɗa kansa. Sannan ya lumshe idonsa, cikin ƙasa da sakanni ya ɓace a falon. Mariya ta ja dogon tsaki tana jin haushin Mu'az da Faruk a lokaci guda. Ta lura da kamar suna so su daƙile mata son kasancewarta ta hannun daman Wahash. Amma ba komai, idan har suka ci gaba da ƙoƙarin tono ramin za ta sa a binne su ciki.

_Share fi sabillilah❤️_

*Daga alƙalamin Salma Ahmad Isah✍️.*
*CANDY CE🦋.*

--------------------
_Kada a manta da biyan kuɗin littafi. Dan free pages sun kusa ƙarewa. To subscribe pay ₦300 to._

5487270431
Salma Isah
Monie point.

And send the evidence of payment via.

08130172702

#Candy
°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*ƘADDARA CE!*




Please Login or Register in order to submit comment