Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Wallahi ba ni na kashe Munira ba!”

Faɗin Mubarak saurayin Munira. Yayin da yake zaune a cikin ɗakin tuhuma na headquartern. Muktar da ya sa shi a gaba da tambayoyi, ya harɗe hannayensa a ƙirji, yana daga tsaye a kan Mubarak ɗin da tsoro ya sauyawa kamanni.

“Ni ma ban ce ka kasheta ba. Amma me ya kaika hotel ɗin a waccan ranar, da har ka tura mata saƙo ta wata lambar da ba taka ba?”

Mubarak ya haɗiye miyau. Sanna yace.

“Eh, na... Na tura mata da saƙo ne saboda ina so mu tattauna wata magana ni da ita!”

“Amma me ya sa ka tura nata saƙo da baƙuwar lamba, saɓanin wadda ka saba amfani da ita!”

A tsorace yace.

“Sati biyu kafin lokacin aka sace min wayata a Almart farm. Kasancewar ba ni ne wanda ya yi rigistern waccan layin nawa ba ya sa na jinkirta yin welcome back. A maimakon na zauna haka sai na siyi wani sabo na fara amfani da shi!”

“Me ya sa ka zaɓi haɗuwa da ita a hotel. Saɓanin gidansu ko wani wurin da ban”

“Da... Dama... Da dama!”

Suna haɗa ido da Muktar ya ji cikinsa ya saki ƙarar tsoro. Ganin yana kame-kame ya sa Muktar ya saki hannayensa. Sannan ya ɗora su a kan table ɗin dake wurin.

“Zai fi maka kyau ka sanar da ni komai. Tun kafin nasa a kaika ɗakin horo. Dan wallahi ka ji na rantse idan ka je can ba za ka fito da kammaninka na asali ba!”

A take Mubarak ya soma hawaye, ya haɗiye miyau ya fi sau ƙirgen yatsunsa. Ganin babu sarki sai Allah ya sa ya buɗe baki ya faɗi gaskiya.

“Ƙwarai. Na kirata hotel ne saboda ina so mu sasanta wata matsala da ta shiga tsakanina da ita. Bayan ta zo sai na nemi da ta bani kanta. Hakan ya sa muka yi wani sabon faɗan da ita. Har ta bar hotel ɗin ranta a ɓace yake. Amma daga wannan ban san komai ba yallaɓai...”

Ya kai ƙarshe yana fashewa da kuka me sauti.

*

“Duk abubuwan da ya faɗa gaskiya ne. Saboda na sa an yi bincike a Almart farm, inda yace an sace masa wayar, kuma masu gadin wurin sun tabbatar da hakan. Dan sun ce a lokacin da aka rasa wayar su ya fara sanarwa... Shi ya sa tun farko ni ban yi zarginsa da kashe Munira ba. Tun bayan sanda muka gano cewa shi ne wanda ya aiko mata da saƙo kan ta zo ta same shi a hotel ɗin!”

Muktar ya korowa Faruk dake jiransa a office tun ɗazu bayanin, bayan da ya baro ɗakin tuhuma. Faruk ya sauƙe numfashi. Yana jin ko ina na duniyarsa na ƙara cika da hargitsi. A gida Mariya da matsalolinta, a waje kuma damuwar mutuwar Munira.

“So yanzu me nene mataki na gaba?”

Muktar ya sauƙe numfashi, sannan ya ɗora hannayensa a kan table ɗin da ya raba tsakiyarsu da Faruk ɗin.

“Duk wani CCTV camera footage na hotel ɗin an goge shi. Hakan ke nuna cewa wanda ya aikata kisan ya iya takunsa. Amma kuma duk da haka ya tafka wani kuskure da zai iya sawa mu kama shi cikin sauƙi!”

Cike da zaƙuwa Faruk yace.

“Wani kuskure ya aikata?”

“Duk yanda mai laifi zai yi wurin binne laifinsa a ƙarƙarshin ƙasa yana kuskurewa ta wata hanyar. To haka shi ma wannan ya kuskure. Domin akwai ɗaya daga cikin masu aiki a hotel ɗin da muka tambaya, ta sanar mana da cewa ta ga sanda Munira ta fito daga ɗakin da Mubarak ya kama. Amma kuma kafin ta kai ga sauƙa ƙasa ta tsaya a ƙofar ɗaki me lamba 24. Sannan ita matar tana zargin cewa akwai abin da Munira ta ga a ɗaki me lamba 24, wanda zai iya zama sanadiyyar mutuwarta!”

Girar Faruk na tattarewa wuri guda ya furta.

“Ban gane ba Muktar!”

Muktar ya jinjina kansa.

“A ranar da Munira suka haɗu da Mubarak aka kashe wani ba'indiye a cikin hotel ɗin, me sunan Danesh Kumar. Danesh Kumar shi ne mutumin da ya kama ɗaki me lamba 24. Idan har za ka iya zurfafa tunaninka. Za ka iya gane alaƙar zance na da kuma mutuwar Danesh!”

Faruk ya yi shiru. Can kuma yace.

“Idan na fahimta dai-dai, wata ƙila a sanda Munira ta baro ɗakin da Mubarak ya kama ta ga sanda aka kashe Danesh, ko kuma ta ga masu kisan, ko kuma ta ma san wanda ya yi kisan, shi ya sa ita ma aka bita aka kasheta!”

“Wanna shi ne abin da bake so ka gane”

“Amma abin tambayar a nan shi ne. Me ya sa makashin ko makasan ba su kasheta a nan cikin hotel ɗin ba, sai da suka bari ta fita, sannan kuma suka bita suka saceta. Sai kuma kirana da ta yi a waccan ranar, kafin su saceta!”

“Idan za ka iya tunawa tun farko na sanar maka da cewa masu gadin hotel ɗin sun sanar mana da cewa Munira ta bar hotel ɗin. Kuma a ƙafa, saɓanin sanda ta shigo wurin da mota, ka ga wannan ma zai ƙara tabbatar mana da cewa lallai akwai abin da ta gani. Shi ya sa ta ruɗe har ta manta da motarta da ta je wurin da ita. Kuma wata ƙila makashin yana ganin idan har ya kasheta a hotel ɗin asirinsa zai iya tonuwa. Shi ya sa ya zaɓi ya barta ta fita daga hotel ɗin, domin ya kauda tunanin jami'an tsaro kan alaƙar kisan Danesh da na Munira. Kuma ya zaɓi sace ma duk akan wannan dalilin. Batun kiranka kuma zai iya kasancewa ta gane makashin na bibiyarta, shi ya sa ta kiraka dan neman taimako!... Amma duk da haka akwai lauje cikin naɗi! Sai dai na maka alƙawarin gano shi nan ba da jimawa ba abokina!”

Faruk ya sa hannayensa duk biyu ya shafa fuskarsa zuwa ƙeyarsa. Ya furzar da iska yana jin kansa na ƙara dulmiyewa cikin kogin matsaloli.

“Yanzu abin da za mu yi nagaba shi ne gano ainahin inda aka saceta. Kuma za mu iya gane hakan ta hanyar wayarta. Dan a lokacin da ta kiraka aka saceta!”

Faruk ya gyaɗa kansa. Kafin ya miƙe ya bawa Muktar hannu suka gaisa, haka ya bar headquartern da nauyin zuciya, ya nufi barrack.

MU'AZ POV.

“Shigo!”

Ya bada umarnin bayan da aka ƙwanƙwasa ƙofar office ɗinsa. Kansa ya ɗaga ya kalli me shigowar.

“Sir!”

Sojan da ya shigo ya faɗi yana sara masa da hannunsa na hagu. Mu'az ya aje pen ɗin dake riƙe a hannunsa yana kallonsa.

“Dismiss!”

Sojan ya sauƙe hannunsa.

“Barka da safiya sir”

“Barka. Eze me ya sa jiya baka je duty ba?”

Ya tambaya yana shafa fatar bakinsa. Sargent Chiku Eze ya washe baki, sannan ya yi taku biyu zuwa jikin table ɗin Mu'az, ya aje masa containerr da ya shigo da ita. Mu'az ya kalli containerr, sannan ya kalli Eze. Da ido ya masa alama da wannan fa?. Eze ya sosa ƙeya yana faɗin.

“Eh Sir. Grilled fish and potato ne matana ya girka maka!”

Mu'az ya yi murmushi. Wai shi za'a bawa cin hanci da abinci. Sai ya sauƙe hannunsa a kan bakinsa, sannan ya kai hannu ya buɗe containern. Ba tare da tunanin komai ba ya fara cin abincin. Yau abinci ne fa, ai ba yaƙi ci ba.

“Oh lord of mercy! Matarka ta iya girki Eze!”

Ya faɗi yana kai loma. Eze ya yi 'yar dariya, ganin dabarar kawowa oga cin hancin abinci ta yi aiki. Dan shi kam baka isa ka siye shi da kuɗi ba. Ko da ace shi ba shi da kuɗi kowa ya san irin arziƙin mahaifinsa. Kasancewar ɗan kasuwa ne, kuma tsohon ministern kuɗi a Nigeria.

Sai da Mu'az ya kusa cinyewa, sannan ya miƙe tsaye, hannunsa riƙe da containerr. Ya nufi Eze dake tsaye har zuwa lokacin. Sai ya dafa kafaɗarsa suka fita zuwa wajen office ɗin. Kuma har zuwa lokacin yana cin abincin.

“Eze me ya sa jiya baka zo aiki ba?”

Ya kuma dawo masa da tambayar ɗazu. Lokaci guda yanayin fuskar Eze ya sauya daga fara'a zuwa mamaki da tsoro.

“Sir... Sir da ma. Matana ne ba shi da lafiya”

Mu'az ya kai loma yana gyaɗa kai.

“Na fahimta. Amma kuma ya aka yi matarka ta yi girki yau. Ita da bata da lafiya. Ko dan manta da wanan batun, ai lafiya ta Allah ce, haka ma jinya, zai iya ɗorawa kowa ya kuma sauƙe masa s sanda ya so, haka ne ba?”

Ya tambaya yana ɗage masa gira. A tsorace Eze ya gyaɗa kansa.

“Eh haka ne. To amma me ya sa baka sanar ba. Ai ya kamata ace ka sanar da mu. Yanda matarka ta iya girki irin wannan ai ya kamata ace na je na dubata!”

Eze ya kuma haɗiye miyau. Sannan yace.

“Sir! Sir”

“Ya isa. Na san haka kawai ka ƙi zuwa duty. Kuma wannan abincin bai isa ya hanani sakawa a maka hukunci ba. Dan haka ka je wurin lieutenant Bala, ka ce na ce a maka bulala hamsin!”

A take Eze ya fara rawar tsoro, hawaye suka zibo masa.

“Sir dan Allah ka yi haƙuri. Na tuba Sir, ba zan sake ba!”

“Hamsin ta yi yawa. Tun da ka haɗani da Allah ka je a maka talatin. Idan ka kuskura ka sake magana kuma zan sa a ninka maka ita, daga talatin zuwa wasu masu kamarta sau uku. Na san ka iya lissafi!”

Eze ya ja bakinsa ya yi shiru. Ya sara masa a tsorace, sannan ya juya ya fita daga sashen office ɗin nasa. Mu'az na tsaye a ƙofar office ɗinsa yana cin abinci Faruk ya shigo.

“Yanzu ba za ka iya haƙuri ka ci a zaune ba MJ?”

Mu'az ya kalle shi yana cusa loma a bakinsa. Kafin ya miƙa masa containern.

“Za ka ci ne?. Amma fa kayan haram ne, cin hancinsa aka kawo min!”

Faruk ya yi murmushi yana girgiza kai.

“A ci daɗi lafiya. Ni ba na ci”

Ya faɗi yana shirin wucewa, amma sai Mu'az ya dakatar da shi.

“Daddy yace yau yana son ganinku a gida kai da Mariya!”

Cak Faruk ya tsaya. Sannan ya juyo ya kalle shi.

“Fatan dai ba wani abin ne ya faru ba?”

Mu'az ya girgiza kansa alamun bai sani ba.

“To Allah ya kaimu an jima ɗin. Zamu zo”

“Sai kun zo”

Mu'az ya faɗi yana shiga office ɗinsa. A kan table ya aje containern da ya cinye abin ciki tas. Sannan ya shiga banɗaki ya wanke hannunsa da bakinsa. A sanda ya dawo cikin office ɗin ya ja ya tsaya yana kallon Yasmin da bai ji shigowarta ba. Yasmin na ganinsa ta miƙe tsaye.

“We need to talk MJ!”

“Bani da wannan lokacin Yamin. Na sha faɗa miki cewar kada ki sake zuwa office ɗina. Bana tattauna abubuwan da suka shafi rayuwata a office, ki bari idan na koma gida sai ki zo mu yi magana!”

Ya kai ƙarshe yana zaunawa a kan kujera. Takaici ya sa Yasmin cewa.

“A nan nake so mu yi maganar, saboda bana jin za mu sake haɗuwa bayan yau!”

“Mutuwa za ki yi ke nan?. Yasmin bai kamata ki kashe kanki a kan wanda bai damu da ke ba!”

Yasmin ta kai hannu ta goge ƙwallar da ta zubo mata.

“Ko kaɗan ban taɓa tunanin kashe kaina ba, domin kuwa da ace zan yi hakan da na yi tuntuni. Nan da next week zan tafi Cairo, zan je na ƙarasa makarantar da soyyayarka ta hanani ƙarasaww!”

Mu'az ya yi dariya.

“Da kuwa kin taimaki kanki”

Yasmin ta kuma goge ƙwalla.

“Mu'az ya kamata ka ji tsoron Allah. Ko da kaɗan ne ya kamata ka nuna kulawa ga wanda yake sonka...”

Ya nuna kansa yana faɗin.

“Ni? Ni kuma me na yi bawan Allah?”

“A'a, ba ka yi komai ba, ni ce wadda ta yi kuskuren fara sonka, har ina zaton cewa wata rana kai ma za ka fara sona. Ashe na aikata babban kuskure. Mu'az ina maka addu'ar Allah ya ɗora maka son da zai wahalar da kai. Allah ya sakawa zuciyarka son da zai sa ka yi ƙoƙarin kashe kanka. Allah ya sa maka son wadda za ta hana rayuwarka sukuni, Allah ya saka maka son da zai gana maka kwatankwacin azabar da ka bani. Allah ya ɗora maka son da zai sa ka ga fari ka ce baƙi ne. Wata ƙila a lokacin za ka fahimci irin abin da nake ji. Bana maka addu'ar fara son wadda ba ta sonka, dan nasan yanda raɗaɗin son ma so wani yake. Na barka lafiya!”

Ta ƙarashe tana ɗaukan jakarta da ta aje a kan table sanda ta shigo office ɗin. Kuma har ta fice Mu'az bai ce mata ƙala ba. Dan shi yana farin cikin ficewa daga rayuwarsa da za ta yi. Kuma ko kaɗan bai sa a ransa cewa addu'o'inta za su bishi ba. Tun da ya san shi bai zalunceta ba.

_Share fi sabillilah❤️_

*Daga alƙalamin Salma Ahmad Isah✍️.*
*CANDY CE🦋.*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*ƘADDARA CE!*


*©SALMA AHMAD ISAH.*
*CANDY🦋*

_ArewaBooks @SalmaAhmad_
_Wattpad @Salma_Ahmad_Isah_



*05*

MAIMUNA POV.

Yau ba kamar kullum da ta saba siyar da kunu duka ba. An samu ragowar wanda ba'a siya ba. Kuma ga shi har ƙarfe goma kunun bai ƙare ba. Dan haka ta kamo hanyar gida tana hasaso yanda za su kwashe da Auwwa.

“Maimuna!”

Ta ji an kira daga bayanta. Hakan ya sa ta juya dan ganin me kiran kafin ta kai ga amsawa. Ganin Abba ne, ɗaya daga cikin abokan Gambo ya sa ta amsa.

“Na'am”

Ta tsaya tana kallonsa. Har ya ƙaraso inda take. Duk da ba haske sosai a inda suke tana iya ganin fara'ar da yake ta yi.

“Har an dawo daga tallar ne?”

Ta gyaɗa kai tana son sanin dalilin da ya sa yake mata magana. Bayan da ba ya mata magana.

“Kin siyar da kunun duka?”

Ta girgiza kai.

“To yanzu ya za ki yi da wannan muguwar matar?. Na ga idan ba ki siyar ba dukanki take”

Sai ta yi shiru tana ƙare masa kallo.

“Ko ba za ta dakeki ba?”

Ta kuma girgiza kanta. Sai ya sa hannu a aljihun wandon jikinsa, ya zaro kuɗin da ya kai dubu biyu, ya miƙa mata.

“Ga shi idan kin je ki bata. Na san wannan zai hana ta dakeki!”

Maimuna ta kalli kuɗin, sannan ta kalli fuskarsa.

“Idan har ka bani wannan kuɗin ne dan Allah. Allah ya baka kadan niyya, kuma na gode. Idan kuma ka bani ne da wata manufa mummuna. Allah ya mayar maka da kayarka kanka. Kuma ina so ka san cewa duka ba ya kisa!”

Tana gama faɗin hakan ta ja siraran ƙafafunta ta yi gaba. Abin da Abba ya yi bai bata mamaki ba. Saboda Allah ne kaɗai ya san adadin samarin da suka so lalata rayuwarta. Samari da dama sun sha cewa suna sonta, amma ita ta san ba soyyayar gaskiya ba ce.

Ƙawayenta na makaranta sun faɗa mata cewar a halin rayuwar yanzu babu namijin da zai iya aureta, saboda tana da sickler. Duk wanda zai zo yace yana sonta raina mata hankali kawai zai yi. Kuma ita ma ta yarda da wannan batun nasu, shi ya sa bata sa a ka ba, in ji ɓarawon tagiya.

Bata takurawa kanta cewar sai ta yi aure ba. Tun da ta kammala secondary school bata sake sakawa kanta wani buri ba. Saboda ita ma secondary school ɗin da ƙyar da fama Auwwa ta barta ta ƙarasa. Shi ya sa ta ture ko wani irin buri da ta san tana da shi. Ta fawallawa sarkin sammai da ƙassai duka lamuranta. Kuma ta san zai kawo mata ƙarshen wahalar nan da take sha.

“Salamu alaikum”

Ta yi sallama daga soron gidan. Jin muryoyi uku sun amsa sallamar ya sa ta fahimci cewa ba Auwwa ba ce kaɗai a gidan. Ilai kuwa, kusan su huɗu ta samu a tsakar gida. Kuma ta san su waye, ƙannen Auwwan ne daga cikin gari.

“Anti Kubura ina wuninku!”

Ta gaishe su tana tsuggunawa. Ciki-ciki suka amsa. Kuma ita bata damu ba, dan idan da sabo ta saba. Tana shirin miƙewa Auwwa ta dakatar a ita da faɗin.

“In ji dai kunu bai ƙare ba?”

Ta sauƙe ajiyar zuciyar kwanciyar hankali. Dan ta san tun da su Kubura suka zo su za'a bawa sauran kunun. Da ace ba su zo ba kuwa yau da ta yabawa aya zaƙinta a hannun Auwwa. Da sauri ta gyaɗa kai tana aje bokitin.

“Akwai saura”

“Shiga kitchen ki ɗauko kofuna ki zubawa su Kubura!”

“To”

Maimuna ta amsa da sauri. Sannan ta miƙe ta shiga ɗan ƙaramin kitchen ɗin gidan. Ta ɗauko kofuna huɗu. Ta zube kunun da ya yi saura a bokitinta, ta miƙawa ƙannen Auwwa.

Daga nan ta shiga banɗaki ta ɗauro alwala. Sannan ta shiga ɗakinta ta yi sallah. Ta fito ta zauna tana jin yunwa, a gefe guda kuma tana jin tsoron tambayar Auwwa abinci.

“Ub*n miye za ki zo ki zauna ki samu a gaba kina jin zancen da muke?”

Auwwa ta faɗi cike da hantara. Maimuna ta sinne kai tana faɗin.

“Yun... Yunwa nake ji!”

“Saboda ub*nki ne yake kawowa abincin da zan girka ai dole ki ce min kina jin yunwa. To na yi na bawa 'yan uwana sun cinye... Sai a tashi a kaini gaba”

Ta sunkuyar da kanta, ƙwalla na taruwa mata a cikin ido. Kafin ta miƙe ta fita daga gidan. Da ta rasa inda za ta je sai ta nufi unguwar Chadi a cikin wannan daren. Dan ba ta son ta cika kaiwa Mummyn su Maryam matsalolinta. Jiki da jini, wata rana za ta iya gajiyawa da ita. Dan haka gwanda ta je wurin dolenta, wato gidan kakarta.

Da yake tsakanin unguwar Fantai da Chadi ba nisa sai bata sha wahala wurin isa ba. Tun daga soro ta fara shagwaɓe fuska, dan ta san ta zo inda za'a share mata hawaye. Sallamar ma a shagwaɓe ta yi, ta shiga cikin gidan tana wani bubbuga ƙafa a ƙasa.

“Wani irin iskanci ne kuma wannan Maimuna?”

Hajja dake zaune a cikin ɗakinta ta tambaya. Maimuna ta ƙarasa cikin ɗakin tana turo baki gaba.

“Hajja”

Ta kira tana zama kusa da kakarta. Hajja ta dubi jikar tata cike da tausayawa.

“Na'am mai sunana”

“Hajja yunwa nake ji. Rabona da abinci tun safe”

Ta faɗi a shagwaɓe tana shafa cikinta. Hajja ta girgiza kanta.

“Jeki ki ɗiba abincin a cikin cooler. Yana nan a rumfa”

“Da yawa fa zan ɗiba”

“Ɗibi wanda zai isheki”

Ta miƙe ta fita da murnarta. Ta ɗauki kwano ta zubo tuwon shinkafa da miyar taushen da Hajja ta girka. Ta buɗe ɗan ƙaramin fridge ɗin Hajjan, ta ɗauki pure water. Ta dawo ɗakin ta zauna. Ta shiga ci tana bawa Hajja labarin abin da ya faru da ita yau, ciki har da haɗuwarta da Abba.

“To yanzu Maimuna. Da kika masa haka, idan kuma da gaske yake yana sonki fa?”

Maimuna ta dakata daga kai loma bakinta. Ta mayar da abincin da ta ɗebo cikin kwano. Sannan ta kalli Hajja.

“Hajja ban bari ya kai ga furta min hakan ba. Saboda na san ba zai min soyyaya tsakaninsa da Allah ba. A irin halin da nake ciki bana jin akwai namijin da zai soni”

Hajja ta girgiza kai.

“Ba komai Maimuna ƙaddara ce!. Ki ci gaba da haƙuri, Allah ya san da ke. Kuma zai kawo miki sauyin rayuwa”

Maimuna bata sake cewa komai ba. Har ta kamalla cin tuwonta. Ta fito da kwanon waje. Ta wanke hannunta ta dawo ta zauna kusa da Hajja.

“Ina Kawu ne? Tun da na shigo ban ji motsinsa ba”

“Ya tafi jajantawa Alhaji Babangida. Saboda asarar da ya yi a satin nan.”

Maimuna ta gyaɗa kai.

“Ah, Maimuna. Duba cikin jakar can tawa, za ki ga leda ki ɗauko”

Cewar Hajja. Maimuna ta miƙe ta nufi jakar. Sannan ta buɗe ta ɗauko ledar dake ciki. Ta dawo kusa da Hajja ta zauna.

“Hajja ga ledar”

Hajja ta karɓa ta buɗe, sannan ta fito da hijabai biyu dake ciki, da abonaki, da kuma audugar mata.

“Gasu nan. Duka naki ne na sai miki a bakin asibiti. Na san yanzu sanyi ya shigo, kina buƙatar abonaki... Kuma idan za ki tafi zan baki kwaki da ƙanzo. Ki ɓoye a ɗakinki idan kin koma. Duk ranar da Auwwa za ta hanaki abinci sai ki ɗauka ki ci”

Maimuna ta yi murmushi ta kwanta a jikin kakarta.

“Ina sonki Hajja”

Hajja na murmushi ta shafa kan gudaliyar jikarta.

“Allah ya ji ƙan Muhammadu da Asabe (iyayen Maimuna).”

“Amin Hajja”

Ta amsa tana jin kewarsu, duk kuwa da kaf cikinsu babu wanda ta sani. Sai dai a hoto ko ta ji labarinsu.


FARUK POV.

Tsaye ya yi a ƙofar ɗakin Mariya yana kallonta. Yayin da take yafa mayafi a kanta. Alamun ta shirya tsaf domin ziyartar gidansu. Idonsa ya zarce kan Hilal dake zaune a kan gado. A hankali ya saki handle ɗin ƙofar ya shiga ciki. Kallo ɗaya Mariya ta masa ta ɗauke kai. Shi kuma bai ma kalleta ba, Hilal kawai ya ɗauka, sai a sannan ya kalleta.

“Kin gama shiryawa ne?”

“Umm”

Amsarta ta fito a taƙaice kamar kullum. Kansa kawai ya gyaɗa, sannan ya nufi ƙofa yana faɗin.

“Ina jiranki a mota”

Sannan ya fita daga ɗakin. Kai tsaye ya sauƙa ƙasa, ya shige motarsa dake parking lot. Ya zauna a ciki, tare da zaunar da Hilal a kan cinyarsa. Yana jiran fitowar Mariya.

Ido kawai ya tsira mata a sanda ta fito daga ƙofar falo. Saboda kalar kwalliyar da ta yi. Wata kyakkyawar atamfa ce da ya sai mata a Khadeeja Candy store a jikinta. Atamfar me ratsin orange ta bala'in dacewa da fatar jikinta da take wani abu tsakani fari da baƙi.

Ta yafa wani orange gyale, fuskarta babu wata kwalliya ta a zo a gani. Amma she looks perfect. Murmushi ya yi yana binta da kallo har ta shiga cikin motar. Har ga Allah shi kam yana son matarsa. Kuma duk abin da take masa yana dannewa saboda darajar yayanta da ta mahaifinta, da kuma son da yake mata. Da ma an ce so hana ganin laifi.

“Mu je?”

Ta faɗi ganin bai ja motar ba har bayan da ta shiga. Idonsa ya ɗauke daga kanta, sannan ya tayar da motar ya fita daga gidan, gidan Hajiyarsu suka fara zuwa, kafin su nufi gidan su Mariyar.

A falo suka iske Hajiyarsa zaune tana cin abincin dare. A falon suka zauna, suka gaisheta cike da girmamawa. Har ta karɓi Hilal tana masa wasa. Kafin suka mata sallama suka fita a kan za su je gidan su Mariya ne.

Sai da suka fita daga falo ta janye idonta a kansu. Ta girgiza kai, halin damuwar auren ɗan nata na bata mamaki. Ba sai an faɗa ba, ta san cewa Faruk ba ya jin daɗin zama da Mariya.

Duk kuwa da bai taɓa faɗa mata ba, saboda ta san halin zurfin ciki irin nasa. Amma ko makaho ya shafa zai gane hakan. Sai dai kuma ita a matsayinta na uwa bai kamata ta saka musu baki a cikin al'amarin aurensu ba tare da sun sakota a ciki ba.

“Wa alaikassalam!”

Ta amsa sallamar ɗanta Adamu, yayan Faruk, kuma ƙanin Bara'atu 'yarta ta fari dake aure a mahaifarsu wato Haɗejia. Asalin mahaifinsu Alhaji Haruna haifaffen garin Hadejia ne. Wanda ya gaji sarautar Kaigaman Haɗejia tun daga kakkaninsa.

Kuma yana da mata biyu. Hajiya Ruƙayya ita ce matarsa ta fako, wadda ta haifa masa yara uku maza, wanda a yanzu babbansu Muhammad Bello shi ne yake riƙe da sarautar ta Kaigama. Hajiya Aisha, wato mahaifiyar su Faruk ita ce matarsa ta biyu. Wadda ta haifa masa yara uku, Bara'atu ita ce ta farko, sai kuma Adamu, sannan Faruk.

Kasancewar harkokin kasuwancinsa yana yinsu ne a garin Abuja ya sa ita Hajiya Aisha ya dawo da ita nan garin Abuja. Yayin da matarsa ta farko da yaranta ke gidansa na garin Haɗejia. Karatu ne ya sa Bara'atu ta koma Haɗejia. Kuma da Allah ya sa rabonta a can yake sai Allah ya haɗata da mijinta a can ɗin.

Wanda suka yi aure har suka hayyayafa, kafin Allah ya masa rasuwa, amma duk da haka bata bar garin Haɗejia ba, saboda aikinta da kuma yaranta da 'yan uwanta da suke can. Adamu kuma yana da mata ɗaya. Wadda yake zaune da ita a nan garin Abuja da yaransa biyu.


MARIYA POV.

Durƙushe suke ita da Faruk a gaban Daddy. Wanda ke musu nasihar hannunka me sanda. A nasihar tasa bai fito yace akwai ɗaya daga cikinsu da ya zo ya kawo ƙarar ɗan uwansa ba. Kuma bai nuna cewa ya san akwai matsala a tsakaninsu ba.

Ya yi amfani da hikima irin tasu ta manya. Wurin ganin ya nusar da su kurakuransu cikin ruwan sanyi. Tun da babu wanda ya san abin da ke tsakaninsu. Ko da Daddy ya kai ƙarshe sai Faruk yace inshallah za'a kiyaye. Mariya kuwa bata ce komai ba. Kuma da ma ba za ta ce ɗin

Please Login or Register in order to submit comment