Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

*©SALMA AHMAD ISAH.*
*CANDY🦋*

_ArewaBooks @SalmaAhmad_
_Wattpad @Salma_Ahmad_Isah_


*07*


*Unguwar Dutsen Alhaji, Bwari, Abuja.*

*Da misalin 08:20 na dare.*


HALIMA POV.

Mai mashin ɗin da ya ɗaukota tun daga Ummul Banat boutique, wato wurin da take aiki ya tsaya a ƙofar gidan kawunta. Ƙanin mahaifinta, wanda take kira da Kawu Sani. Sauƙa ta yi daga kan mashin ɗin. Sannan ta ɗauko kuɗin mai mashin ɗin ta ba shi.

Ta juyo ta kalli ƙaramin gidan da ya fi ko wani gida nuna halin rashi a layin. Bakinta ɗauke da sallama ta shiga gidan. A tsakiyar gidan ta taka birki. Ta shiga kallon jama'ar gidan dake kaikawo. Duk yawan mutanen gidan, an rasa wanda zai amsa mata sallama sai Mama Sadiya. Wato matar Kawu Sani ta farko.

Ba tare da tace ko ta yi komai ba ta wuce ɗakin 'yan matan gidan. Su huɗu ta samu zazzaune a ɗakin suna sabgarsu. Sallama kawai ta yi ta shiga cikin ɗakin. Kai tsaye ta wuce wurin da take aje kayanta, wato kusa da katifarta ta kwana. Jakarta ta sauƙe. Sannan ta zauna a bakin katifar tata tana jin yunwar dake cikinta na ƙara girmama.

“Halima!”

Zaliha 'yar Mama Sadiya ta farko ta kira sunanta. Hakan ya sa ta juyo ta kalleta.

“Me yake damunki?”

Ta shagwaɓe fuska kamar yadda ta saba. Sannan ta nuna mata gefen fuskarta.

“Dubi ki ga abin da wani mugun soja ya min yau a boutique. Wai dan kawai mun yi karo fa shi ruwan da yake hannuna ya zube a jikinsa. Shi ne ya sharara min mari! Wallahi yanzu haka ma wurin ciwo yake min. Ji nake kamar ya karya min ƙashin fuska !”

Ta ƙarashe ƙwallar shagwaɓa na zubo mata. Ta turo baki gaba. Tana jin kamar ta fashe da kuka. Da ace lokacin iyayenta na raye ne da yanzu wannan abin da ya mata ya sa ta kwanta jinya. Saboda a wancan lokacin ita 'yar gata ce. Shagwaɓiɓiyyar iyarta da babanta, saboda har suka koma ga mahaliccinsu ita kaɗai ce 'yarsu.

Mahaifinta Alhaji Auwal Kaska ɗan kasuwa ne me arziƙi dai-dai gwargwado. Matarsa ɗaya, haka kuma 'yarsa ɗaya. Kasancewar tun bayan da aka haifi Halima ba su sake samun wani ɗan ba sai suka shagwaɓata. Gata babu kalar wanda ba su yi mata ba. Shi ya sa ta taso a shagwaɓe.

Domin ko me ta nema za ta samu. Ba ta san babu ba. Shi ya sa a sanda Allah ya yi wa iyayenta rasuwa a lokaci guda ta shiga halin ha'u'la'i. Ba'a samu kanta ba sai bayan kwana arba'in da rasuwarsu. Kuma daga lokacin ne ƙalubalen rayuwarta ya fara. Saboda kaf cikin dangin mahaifiyarta babu wanda ya yi ƙoƙarin ɗaukanta dan ya riƙeta. Kowa yana gudun wahala. A cikin dangin mahaifin nata ma da ƙyar aka samu Kawu sani yace zai riƙeta.

Saboda a lokacin an raba gado, dan daga ita sai shi ne kaɗai suka ci gadon mahaifinta. A sanda ta dawo wurinsa ya lallaɓata da daɗin baki ya ƙwace duk wani abu da aka mallaka mata ya cinye. Sai da kuɗaɗe da kadarorinta na hannunsa suka ƙare sannan ta fara fuskantar taskun rayuwa a gidansa. Dan gaba ɗaya Kawu Sani rikiɗewa ya yi ya sauya mata. A farkon zuwanta gidan ba ta cin abinci ɗaya da sauran iyalansa.

Saboda ita ba ta saba da cin abinci mara kyau da daɗi ba, shi kuma taƙonsa ya sa gidansa babu kyakkyawan abinci. Amma bayan kuɗaɗen sun ƙare sai ita ma ta dawo tana cin abinci ɗaya da na yaran gidan. Sai kuma tsangwamar da matar Kawu Sani ta farko wato Mama Zulai ke mata. Aikin wahala babu wanda ba ta sakata, kowa na gidan ya rainta. Shi ya sa gaba ɗaya ta tsani rayuwar gidan. Idan ta tuna da yankan ƙaunar da mutuwar iyayenta ta mata.

A rayuwar Kawu Sani, idan kana da kuɗi kai ne mutum. Shi ya sa gaba ɗaya 'ya'yansa mata suke fita domin nemo masa kuɗi. Wasu ma ta hanyar da bata dace ba suke samowa kuɗin. Amma shi bai damu ba, in har za'a kawo masa kuɗi to su bi kowace hanya ma. To Halima bata shiga tara ba sai da Kawu Sani ya bijiro mata da zancen dole ta fara fita neman kuɗi kamar sauran 'ya'yansa. A lokacin ta sha kuka sosai, duk da da ma can ita kuka ba ya mata wahala.

Sai dai ta riga tasa a ranta cewa ba za ta taɓa yin abin da su Jidda babbar 'yar Mama Zulai ke yi ba, na bin maza domin samun kuɗi. Shi ya sa ta naimi taimakon Zaliha kan ta tayata naiman aiki. Shi ne har ta samu aiki a Ummul Banat boutique. To da wannan aikin ne take samun kuɗin da take bawa kawu Sani, dan ta samu ta zauna a gidansa. Amma duk da haka ba ta da kwanciyar hankali, saboda masifar Mama Zulai ba ta barinta ta huta.

“Ayya. Sannu, kuma wurin ya yi ja sosai, bari in shafa miki man zafi!”

Faɗin Zaliha cikin tausayawa. Halima ta gyaɗa kai tana jin tausayin kanta, saboda yanzu haka ma kanta ciwo yake. Zaliha ta miƙe ta nufi jakarta ta kaya, ta ɗauko man zafin. Sannan ta dawo ta zauna kusa da Halima, ta shafa mata a gefen fuskar tata da ya kumbura.

“Kin yi sallah?”

Zaliha ta tambaya. Halima ta gyaɗa mata kai a shagwaɓe.

“To Mama ta kusa gama girki, idan ta gama sai na zubo mana mu ci”

Ta kuma gyaɗa kai, sanna ta kwanta tana jin kanta na ƙara mata ciwo. Idonta ta lumshe, fuskar wannan mugun sojan ta shigo cikin tunaninta, dan haka ta yi saurin buɗe idonta gabanta na faɗuwa. Dan haka kawai take ganinsa kamar wani dodo. Ƙwafa ta yi, sannan ta cije leɓenta na kasa. Ta juya kwanciyarta tana ja masa Allah ya isa.

“Insha Allah ba za ka samu sukuni ba tun da ka ɗaga hannunka ka mareni. Mugu me jar fuska kawai... Banza ƙatoto!”

Ta faɗi a zahiri, zuciyata na zafi da abin da ya mata. Kamar daga sama ta ji Mama Zulai na ƙwala mata kira.

“Ke Halima!. Halima!”

Idonta ta rintse. Ko wani ɗan ƙaniyar ne ya faɗawa wannan masiffafiyar matar ta dawo?. Miƙewa ta yi zane, tana faɗawa zuciyarta cewa yanzu za'a haɗata da wani aikin. Ba'a barta ta huta da gajiyar da ta kwaso a wurin aiki ba, an zo za'a ƙara mata da wani aikin.

Tana tura baki gaba tana shagwaɓe fuska ta ɗaga labulen ɗakin da suke ciki, tana amsa kiran 'yan farautar da Mama Zulai ke mata. Tsaye ta hangeta a bakin rumfar da ake girki a gidan. Ta haɗe girar sama da ta ƙasa, tana mata wani kallon tara saura kwata.

“Ub*n me kika shiga yi a ɗakin?. Bayan kin san cewa yau girki na ne?”

‘Aikin ƙaniya na shiga yi a ɗakin. Masifaffiya kawai! Ni na saki yin girkin dole?, Da za ki zo ki takurawa rayuwar marainiyar Allah?. Muguwa Azzaluma’

Ta yi maganar duka a zuciyarta. A fili kuma sai wani tsuke baki take tana rau-rau da ido. Tana wani karkata kai, wai duk dan a ji tausayinta. Amma ta san ba za'a ji tausayi nata ba. Tana yi ne kawai dan ya zame mata jiki.

“Ki fito ki zo ki ƙarasa tuƙa tuwon nan... Kuma in kin gama ki rabawa yara... Mtsuww!”

Mama Zulai ta ƙarashe da tsaki. Sannan ta juya zuwa ɗakinta. Jiki a saɓule Halima ta fito daga ɗakin. Tana tafe hawaye na mata zuba. Tana shirin zama a gaban murhun dake ɗauke da tukunya lamba goma. Mama Sadiya ta fito daga ɗakinta tana faɗin.

“A'a me sunana. Ta shi ki je ki kwanta ki huta. Ni zan tuƙa tuwon!”

Halima ta girgiza kai. Sannan ta zauna a kan kujera tana faɗin.

“Ba komai Mama. Zan yi”

“Da dai kin kawo na tuƙa”

“Ai ba yawa, yanzu zan tuƙa”

Da haka ta ɗauki doguwar muciyar tuƙin tuwon da ta kusa kaiwa tsawonta. Sannan ta saka a cikin buɗaɗɗiyar tukunyar. Ta fara ɗiban garin dawar dake gefe tana zubawa a cikin tukunyar. Sai da ta gama tuƙe tuwon, sannan ta shiga rabawa yaran gidan a tray. Ba ita ta koma ɗaki ba sai da ta tabbatar da ta rabawa kowa nasa. Sannan ta koma ɗaki ta kwanta. Tana hawayen da suka zame mata jiki tun shekaru uku baya.

“Halima tashi mu ci tuwo”

Faɗin Zaliha tana aje musu tray ɗin tuwon da ta saka masa miyar kukar da Mama Zulai ta yi. Halima ta miƙe zaune, tana sharar ƙwalla. Ita fa a rayuwa ba ta san cewa mutane na cin dawa ba sai a gidan Kawu Sani. A rayuwarta ta baya ta ɗauka cewa doki kawai ake bawa dawa.

Ashe ita ma za ta wayi gari ta girka tuwon dawa, har ma ta ci shi dan maganin yunwa. Kamar yanda ta saba cin ko wani abincin gidan dan kashe yunwa yau ma haka ta ci. Saboda da ace ita take ɗaukan albashinta ba ta ga dalilin da zai sa ta ci wannan abincin ba.

Amma ita ko da wuƙa za'a ɗora a wuyanta ace nawa ne albashinta ba ta sani ba. Ko kalarsu ba ta gani, daga an yi albashi Kawu Sani yake zuwa ya karɓa da kansa. Tsakaninta da shi kawai shi ne kuɗin abin hawa.

Gaba ɗaya yau zuciyarta ta fi ko yaushe jagulewa. Na farko abin da Wannan koɗɗaɗen mugun sojan ya mata. Na biyu ga kumatunta da take jinsa kamar ba a jikinta yake ba. Sai kuma wannan tuwon da take cinsa a dole. Dan cusawa kawai take. Amma sam bakinta babu wani ɗanɗano.


*Efab metropolis Estate, Gwarinfa, Abuja.*

*10:18 na dare.*


MUKTAR POV.

Motar Ali ce ta yi parking a ƙofar gidan. Sannan a hankali ƙofar dake gefen driver ta buɗe. Ya fito daga cikin motar, sannan ya rage tsayinsa ya leƙa kansa ƙasan windown. Yana kallon Ali dake cikin motar.

“Gobe ka zo ka ɗaukeni da misalin karfe takwas!”

“Okay sir!”

Ali ya amsa.

“Sai da safe!”

“Sai da safe sir”

Daga haka ya miƙe, sanna ya juya ya nufi gate ɗin gidansu. Motarsa da Ali ke ja na barin wurin aka haske shi da fitilar babur. Hakan ya sa ya kare fuskarsa da hannunsa ɗaya. Sannan ya juyo yana son ganin mashin ɗin. Amma kuma yanda me mashin ɗin ya haske shi ya sa bai iya ganin mashin ɗin ballantana me shi.

A lokaci guda tunaninsa ya hasko masa lokacin da ya lura da wani me mashin da yake bibiyarsu. Sai ya yi murmushi, sannan ya juya bayansa yana sauƙe hannunsa da ya rufe fuskarsa da shi. Sannan hankali kwance ya ƙwanƙwasa ƙaramar ƙofar shiga gidansu.

Ganin haka ya sa me mashin ɗin ya tako mashin ɗin nasa da gudu. Ya iyo kan Muktar da shi. Sai dai kafin ya kai ga isa inda yake har me gadin gidan ya buɗe ƙofar, shi kuma Muktar sai ya yi amfani da wannan damar ya faɗa cikin gidan da sauri. Sanna ya datse ƙofar gidan.

“Yallaɓai lafiya?”

Me gadin da ya buɗe masa ƙofar ya tambaya. Amma Muktar bai amsa shi ba. Sai wayarsa da ya zaro ya aikawa da Ali kira.

“Hello Ali. Idan baka yi nisa ba ina so ka dawo da gaggawa. Wannan mutumin na kan mashin ne ya biyoni har gida ina so ka dawo ka tare min shi!”

Ya faɗi bayan da Ali ya ɗaga kiran.

“Okay sir”

Ali ya amsa daga cikin wayar. Muktar ya kashe wayar, sannan ya sauƙeta daga kunnensa. Ya ƙara matsawa jikin gate ɗin ya leƙa. Sai ya ga har yanzu mashin ɗin na nan. Ya dawo baya yana kaikawo. Shi ko me gadi ya sa shi a gaba yana kallo, dan ya kasa gane abin da yake faruwa.

Yana tsaye a wurin ya ji dirin motarsa da Ali ya dawo da ita. Hakan ya sa ya buɗe ƙofar da sauri ya fita. Amma sai ya ga me mashin ɗin ya tayar da shi ya ja shi da gudu. Kuma shi ma Alin sai ya bi bayansa da mota. Yana tsaye a wurin Ali ya dawo. Kuma tun da ya ga Alin ya dawo shi kaɗai ya san cewa bai samu damar kama shi ba.

“Sir ya kufce mana”

Faɗin Ali da ya fito daga mota. Ba tare da yace komai ba ya gyaɗa kansa. Sannan ya sallami Ali ya koma cikin gidan. Ya tsaya a wurin me gadi tare da faɗa masa cewar.

“Duk wanda ya zo kada ka kuskura ka buɗe masa gate ɗin nan.!”

Me gadi ya gyaɗa kai cike da bin umarni. Dan tun da ya ji haka to akwai matsala. Daga wannan umarnin Muktar ya juya ya nufi cikin gidan. A ƙofar shiga falo ya cire takalman ƙafarsa, sannan ya buɗe ƙofar falon ya sa kai, bakinsa ɗauke da sallama. Mahaifiyarsa da kuma ƙaninsa dake zaune a falon ne suka amsa masa. Kuma a tare suka dube shi.

“Ya Mukhy sannu da zuwa”

Ya yi murmushi yana kallon ƙaninsa.

“Sannu Walid... Karatu ake ne?”

Ya tambaya yana kallon littatafan dake gaban Walid ɗin. A lokaci guda kuma yana zama kusa da mahaifyarsa.

“Eh, muna da test on monday”

“To Allah ya taimaka... Mama ina wuni”

Ya ƙarashe yana gaida mahaifiyarsu. Mama ta amsa da murmushi.

“Lafiya Muktar. An dawo ke nan?”

“Eh Wallahi... Bari na je na ɗan watsa ruwa na zo na ci abinci”

Ya faɗa yana miƙewa tsaye.

“To sai ka fito”

Ya gyaɗa kansa. Sannan ya nufi corridorn dake ƙunshe da ɗakunansu shi da Walid. Ɗakinsa ya shiga. Kuma ya na shiga ya kulle ƙofar ɗakin. Sannan ya zaro wayarsa ya aikawa Kaigama ƙira. Bugu uku ya ɗaga da sallama.

“Wa alaikassalam. Kaigama!”

Daga ɗayan ɓangaren Faruk ya amsa.

“Na'am Mukhy... Fatan dai lafiya?”

“Lafiya, amma ba lau ba...”

Nan ya kwashe kaf abin da ya faru tun daga ranar da ya je BB hotel domin bincike har zuwa kan wanda ya faru yau. Ya zauna a bakin gadonsa yana ƙarawa da.

“... Duk yanda aka yi wannan mai laifin ba mutum ɗaya ba ne. Wata ƙila su biyu ne, ko uku, ko huɗu. Ko kuma ƙungiya garesu. Kuma ina da tabbacin suna da ƙarfin ikon yin duk abinda suke so. Saboda idan ba haka ba babu ta inda za ayi su shigo unguwarmu. Ka san yanda matakan tsaro suke da tsauri a nan. Ammz abin yana bani mamaki!”

Faruk ya sauƙe numfashi. Sannan yace.

“Mukhy! Idan har kana ganin wannan case ɗin zai iya shafar personal life ɗinka zai fi kyau ka aje shi. Ni da MJ za mu iya ƙarasa shi!”

Muktar ya girgiza kansa.

“Kaigama. A baya ban sanka ba, amma wannan binciken shi ne ya haɗani da kai. Kuma tun da na fara wannan binciken ba na jin zan aje shi ba tare da na kai ƙarshensa ba. Idan har zan ji tsoron abin da zai same ni ko ahalina a kan aikina to me ya sa zan fara?. Da ma can na riga na saba da irin wannan abin... So dan haka ba na so ka saka kanka a cikin damuwa, zan ci gaba da bincike a kan wannan case ɗin har sai na kama me laifin nan!...”

Faruk ya yi murmushi.

“Na gode sosai Muktar. Allah ya saka da alkairi”

“Kada ka damu. Da yardar Allah mun kusa kaiwa ƙarshen wannan binciken. Duk wani ci gaban da aka samu i will give you a touch!”

“Na gode sosai. Sai da safe”

“Okay sai da safe”

Muktar ya aje wayar, sannan ya shafa kansa. Ya yi shiru yana nazari, bisa ga dukkan alamu wanna case ɗin ba ƙarami ba ne kamar yanda suke tunani. Dan haka yana buƙatar faɗaɗa tunaninsa domin kaiwa ƙarshensa. Daga haka ya miƙe tsaye, sannan ya shiga barthroom dan ya watsa ruwa a jikinsa.

*No.53, off Justice Clara Ogunbiyi street, Asokoro, Abuja.*

MIMA POV.

Ita da wata cousin sisternsu ne zaune a falo suna gulmar Mu'az. Mima ta dage tana shararowa budurwar me suna Zulaihat labarin kalar cin abinci irin na Mu'az.

“... Kin ga fa waccan layyar haka bawan Allahnan ya cinye rabin ragon da ya yanka tun a ranar farko!”

Zulaihat ta zare ido cikin faɗin.

“Rabin rago fa Mima? Ban da sharri dai!”

Mima ta taɓe baki.

“Wallahi da gaske nake. Kin san ai ba zan miki ƙarya ba. Kin san Anti Maryama ce ta zo ta tayamu suya waccan layyar. To in faɗa miki Ya Mu'az zuwa ya yi compound ya aje kujera, ya hau ya zauna yana aika Na'im ya je ya ɗebo masa idan an soya. Ana soyawa yana ci, kan ki ce me har naman ya faɗa. Haka Anti Maryama ta yi ta mamakin ƙarewar naman. Da aka tambayi Gogan ina nama sai yace ai shi ya cinye kayansa. Anti Maryama har da cewa an yakuwa Mu'az mutum ne?”

Zulaihat ta kwashe da dariya Mima na tayata.

“Wallahi. Ai wannan mutumin da kika ganshi kura ma haka ta ga ta ƙyale a kan cin nama. Ya Mu'az? Humm!”

Bata kai ga rufe bakinta ba, Mu'az ɗin ya buɗe ƙofar falo ya shigo. Saurin gimtse bakinta ta yi. Ta shiga zara ido tana faɗin ta shiga uku a ranta. Dan ta ɗauka cewa ya ji abin da tace, idan kuwa har ya ji ai yau sai ɗan buzunta a gidan nan.

Amma kuma sai ta ga ko kallonta bai yi ba har ya zauna a kan sofa. Hakan ya sa ta gane cewa bai ji abin da tace ba. Ajiyar zuciya ta yi, dan ta san da ace ya ji babu abin da zai hana ya lakaɗa mata na jaki. Saboda Mu'az bai iya kauda kai a kan laifi ba. Daga zarar an masa yake mayar da martani.

Amma kuma ba shi da ruƙo. Dan daga zarar ka masa laifi ya amayar da abinda ka masa zai manta, mintuna kaɗan za ka ga ya dawo yana maka magana da kansa. Kuma da ma yawancin mutum mafaɗaci haka yake.

A sace ta ci gaba da kallonsa. Har ta lura da kamar akwai abin da yake damunsa. Ta riga da ta san halin yayanta. Abu ne mawuyaci ya ganta zaune a falo bai mata magana ba. Ko da ko ita bata fara masa maganar ba, ko tsokanarta ne zai yi.

“Ya Mu'az ina wuni”

Zulaihat ta gaida shi. Sai ya juyo ya kallesu da mamaki. Dan shi a sanda ya shigo kwata-kwata tunaninsa bai ba shi cewar akwai wani ɗan adam a falon ba.

Kuma ba komai ya ja hakan ba face wani halin damuwa da zuciyarsa ta shiga yau kaɗai. Gaba ɗaya tun bayan abin da ya faru a Ummul Banat boutique ya rasa nutsuwarsa. Zuciyarsa da gangar jikinsa na faɗa masa cewar ya aikata ba dai-dai ba.

Amma kuma ƙwaƙwalwarsa ta kasa yarda da hakan. Gaba ɗaya shi ji yake cewar bai aikata ba dai-dai ba, tun farko wa yace ta buge shi, har ta zuba masa ruwa a jikinsa?. Sai dai kuma wani sashi na zuciyarsa na faɗa masa cewar ya aikata kuskuren marinta. Bai kamata ace tashin farko ya mareta ba, ya kamata ace sai da ya tambayi ba'asi tukkuna.

Amma ya zai yi?. Zuciyarsa ce a kusa, abu kaɗan ke sawa ya harzuƙa, kuma shi daga ya fusata yake mayar da martani. Ture wannan tunanin dake damun kansa ya yi, sana ya amsa gaisuwar Zulaihat.

“Lafiya Zulaihat... Ya gida?”

“Gida lafiya”

Ta amsa tana satar kallon idon Mima da har yanzu a tsorace take. Kuma ba ta ƙara razana ba sai da Mu'az ɗin ya kalleta.

“Mima ina Mummy?”

Ta haɗiyi yawu, sannan ta amsa masa da sauri.

“Tana ɗakinta”

“Me aka dafa yau?”

Ya kuma tambaya.

“Tuwo aka yi. Amma Mummy tasa na dafa maka jollof ɗin couscous”

“Kin saka nama ko kifi?”

Ta ɗan kalli Zulaihat, dariya na son kufce mata. Sannan ta kalle shi tana amsawa.

“Eh. Na saka maka catfish”

“Zuba min Please”

“To”

Ta faɗa tana miƙewa, sannan ta nufi kitchen. A lokacin Na'im ya sauƙo daga sama. Kuma yana sauƙowa ya yi kan Mu'az.

“Ya Mu'az ka siyo min sweatern?”

Na'im ya tambaya yana zaunawa kusa da shi. Maganar sweater ta tuno masa da yanda aka yi ya aje sweatern. Lokaci guda hoton ya taho haɗe da na fuskarta, da kuma na idanuwanta da ya fi kalla a fuskar tata. Maimakon yace wani abu sai ya dafe kansa yana faɗin.

“Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un!”

Na'im ya taɓa shi.

“Baka da lafiya ne Ya Mu'az?”

Sai ya girgiza kansa yana ɗagowa da shi. Sannan ya ƙaƙalo murmushi.

“Lafiyata ƙalau. Na manta da siyan sweatern ne. Amma gobe inshallah zan siyo maka!”

Yana faɗin hakan ya miƙe tsaye, ya nufi hanyar fita daga falon. Mima da ta fito daga kitchen, hannunta riƙe da plate ɗin abincinsa tace.

“Ya Mu'az ga abincin!”

Sai ya juyo ya kalleta. Ba tare da ya ce komai ba ya nufeta, sannan ya karɓi plate ɗin. Ya juya ya fita daga part ɗin Mummy ba tare da yacewa kowa komai ba. Har ya fice su Mima ba su daina mamakin abin da ya hana shi sukuni ba.

A falon part ɗinsa ya zauna, ya saka abincin da ya karɓa a wurin Mima a gaba yana kallo. Ya kasa ci, kuma ya rasa yanda zai yi da shi. Can kuma sai ya ja wani dogon tsaki.

Haba mana. Ya za ayi wata yarinya ta shigo tunaninsa ta takurawa rayuwarsa, ta hana shi sukuni haka kawai dan ya mareta?. Mutum nawa ya mara a kan sun masa laifi?. Sai ita da aka ƙerata da gwal?. Za ta takurawa tunaninsa?. Idan har ta sake shigo masa tunani sai ya je har Ummul Banat boutique ɗin ya hukuntata.

Da wannan maganar da zuciyarsa ta raɗa masa ya samu sukunin cin abinci. Har ya taso ya koma ɗaki. Ya cire rigar jikinsa ya kwanta a kan gado. Ya kashe wuta da niyyar yin bacci. Amma sai baccin yace ai ba su yi yarjejeniya da shi kan zai ɗauke shi a wannan lokacin ba. Tunaninta kuma ya ƙara dawo masa. Idanuwanta da suke ƙyallin ƙwallar da take zubarwa sun fi komai takura masa.

Hannu ya kai ya ɗauki pillow ya danne kansa da shi, wai ko za ta fice masa a cikin tunani. Amma Wallahi ba ta fita ba. Daga ƙarshe ma sai ya miƙe zaune a kan gadon, sannan ya dafe kansa yana faɗin.

“Ya isa Mu'az. Ya isa!”

Ya faɗawa kansa yana shafa saitin zuciyarsa. Sannan ya ƙara da.

“Babu abin da ya haɗa hanyarka da ta waccan yarinyar. But she's innocent!...”

Wani zancen ya shigo cikin wani. Sai ya rintse idonsa yana furta.

“Oh lord of mercy. Na shiga uku ni Mu'azzam!”

Ya buɗe idonsa. Sannan ya sauƙa daga kan gadon. Ya shiga bayi, ya yi wani sabon wankan, wai ko zai samu yarinyar ta fita daga kansa. Ko da ya dawo ɗakin ya kwanta ba ta sauya zani ba.

Daga ƙarshe sai ya miƙe ya zauna a tsakiyar gadon ya shiga yin salatin annabi. Wata ƙila Allah ya dube shi ya kawo masa ɗauki. A ranar bai yi bacci ba sai da ya sa a ransa cewar zai je ya bata haƙuri, kuma ya amin ce cewar ya aikata mata ba dai-dai ba.

Zuciyarsa ma sai da ta raya masa cewa wata ƙila ma mayya ce. Shi ya sa ta hana shi baccin dare. Amma dai ko ma aljana ce zai je ya bata haƙuri, in ya so ta ci kanta ta sha baƙin ruwa.

°°° °°° °°°

_Humm Humm Humm_

_Garin daɗin kowa ya kama da wuta. In ji Malam Tsalha mijin me Koko.😂._

_Da alama Halima da Kairat sun yi addu'a a bakin 'yan amin._

_Sir MJ dodon abinci ya kasa sukuni saboda kuskuren da ya aikata mata_

_Wai ni ina Maimuna ne?_

_To a yi dai mu gani_

_Share fi sabillilah❤️_

*Daga alƙalamin Salma Ahmad Isah✍️.*
*CANDY CE🦋.*

--------------------
_Kada a manta da biyan kuɗin littafi. Free pages sun kusa ƙarewa. To subscribe pay ₦300 to._

5487270431
Salma Isah
Monie point.

And send the evidence of payment via.

08130172702

#Candy
#SalmaAhmadIsah
°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*ƘADDARA CE!*


*©SALMA AHMAD ISAH.*
*CANDY🦋*

_ArewaBooks @SalmaAhmad_
_Wattpad @Salma_Ahmad_Isah_


*08*

*Unguwar Fanisau, Haɗejia local government, Jigawa state.*

“Maryam! Maryam! Maryam ke!”

Mummy dake cikin kitchen ta ƙwalawa Maryam dake zaune da Maimuna a falo kira.

“Na'am Mummy”

Maryam ta amsa tana nufar kitchen ɗin. Ta tsaya a ƙofar kitchen ɗin, sannan ta leƙa kanta ciki.

“Mummy ga ni”

“Tsabar iskanci kina ji ana kirana amma ba za ki iya kawo min wayar ba?”

Maryam ta ɗan yi dariya irin ta marasa gaskiya ta na sosa kai.

“Yanzu za ki je ki ɗauko min wayar ne? Ko tsayuwa za ki ci gaba da yi a nan har Mahadi ya bayyana?”

Da sauri Maryam ta dawo falo, inda Maimuna ke zaune tana cin abinci. Ta ɗauki wayar Mummu dake chargy. Sannan ta kai mata wayar ta dawo ta zauna a wurin Maimuna. Ganin mahaifiyarta ce mai

Please Login or Register in order to submit comment