Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

*SHALELEN ALHAZAWA*

*Writing and story*

*By*

*Asmeetar Hydar*


(Asma'u Ayuba)


*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*


*BISMILLAHIR RAHMANIN RAHIM*

*Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, tsira da aminci su ƙara tabbata ga shugabanmu Annabi muhammad s a w, yau ma kamar kullum na ƙara kawo muku shahararren book ɗina me taken Shalelen Alhazawa, ina fatar za ku bibiyeni domin jin yanda zata kasance, ban yi wannan littafin dan na ci zarafin wani/wata ba duk wanda ya yi daidai da rayuwarsa to akasi ne, ban yarda a juya min book ta kowacce suffa ba, idan kunne ya ji jiki ya tsira, kar wanda ya yi gangancin ɗora min book a Website ko You tube ba tare da izini na ba, idan aka yi hakan za ka iya ganin sammaci daga kotu dan haka a kiyaye, ni ce ta ku har kullum Asmeetar Hydar marubuciyar littafin
Gidan Mulki
Mayaudari. Littafin Shalelen Alhazawa akwai faɗakarwa ilmantarwa gami da nishaɗantarwa uwa uba al'ajabi, ku dai ku bibiyeni domin jin yanda zata kasance*


*08082589590*




P. 1




Tun da ta fara ratsa unguwarsu take rufe hanci saboda warin da ke tashi, kayan jikinta kawai idan ka gani zaka ce ɗiyar wani hamshaƙin me kuɗi ce, kaya ne na alfarma zai kai kimanin dubu ɗari biyu, handbang da takalman ƙafarta kuwa sun kai dubu ɗari, wayar hannunta ƙirar iphone 13promax ce, tafiya take cikin iya taku da karairaya har ta fito daga unguwar tasu, sai da ta yi tafiya me nisa kafin ta shiga wata unguwar, daga nesa wata bugaggar mota ce da alama ita ake jira.

A gadarance ta ƙaraso tana sakin murmushi, ba tare da wata fargaba ba ta shige motar tana mai rufe ƙofa.

Alhajin da ke ciki kuwa zai kai kimanin shekaru arba'in, haƙoran makka biyu ne a bakinsa, washe baki ya yi kafin ya ce "Barka da zuwa Zinariyar mata"

Ɗan gyara zaman mayafin jikinta ta yi wanda sai cikakkun ƴaƴan masu kuɗi zasu iya saka shi ta ce "Thanks love am very tied tun safe muke abu ɗaya, waɗannan talakawan kullum cikin yi musu kyauta ake, yau Dad ɗina be samu damar zuwa ba shine fa ya ce na wakilce shi" Ta faɗa tana fari da ido.

"Eyyeh gaskiya akwai gajiya amma be kamata Dad ya turo kyakykyawar mace kamar ki irin wannan unguwar ba, but ina Driver ne?"

Da sauri ta katse shi da faɗin "No ai bana buƙatar Driver because ba kowa nake son ya san ko ni wacece ba"

"Okay zamu iya tafiya ko?"

"Yes we can go dan ina son mu yi sauri mu dawo kafin Dad ya dawo gida, ya tafi Meeting a ƙasar Dubai yau zai su shigo".


Gyaɗa kai Alhajin ya yi alamar gamsuwa tare da kunna mota yana mai barin unguwar.

Wani haɗaɗɗen Hotel suka nufa wanda sai manyan masu kuɗi ne zasu iya shigar sa, ɗagewa Gate ɗin ya yi sama, Alhajin kuwa ya danna hancin motarsa a ciki, Najmeer kam tun lokacin da aka shigo ta ƙara haɗe fuska tamkar ɗiyar shugaban ƙasa, a mota ta tsaya shi kuwa ya shige daga ciki domin biyan kuɗin room ɗin da zasu sheƙe ayarsu, mintuna uku ya ɗauka kafin ya fito yana sakin murmushi.

A tare suka nufi ɗakin tana rungume a jikinsa, wani ƙayataccen room ne wanda ya gaji da haɗuwa, mayafin da ke jikinta ta ɗora kan makeken bed ɗin da ke baje a ɗakin tana mai fara yaye kayan da ke jikinta, Alhajin kuwa ya zuba mata ido kamar zai haɗiye ta ganin yanda shape ɗinta ya fito sosai, daga saman ƙugunta zuwa ƙasa ya buɗe, can bayan mazaunanta ya ɗago sosai gwanin sha'awa, cikinta ya shafe har ya hana cibiyarta fitowa, a hankali ta juya tana mai girgiza jigidar da ke ɗaure a ƙugunta, wani mugun numfashi Alhajin ya ja wanda ya yi sanadiyar faɗawarsa kan bed be san lokaci ba, tun da Allah ya halicce sa be taɓa ganin mace me kyan diri irin na Najmeer ba, rigar jikinta ta fara cirewa tana faɗin "Ka haɗa mun ruwan wanka ina son na shiga" Kamar wani Dolo haka Alhajin ya shige toilet ɗin yana mai juyowa dan ko kaɗan baya son ɗauke idanunsa daga barin kallonta.

Sai da ta gama sauke duk kayan da ke jikinta kafin ta zauna kan bed tana mai ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, gashin kanta da ke yawo har ƙarshen bayanta ne ta ɗaure dan yana takura mata, baƙi ne sosai me laushi ga wani ƙamshin da ke tashi tamkar an yi ɓarin turaren gashi a kai, na shanunta kuwa sun ɗago sama ƙyam gwanin sha'awa, su ba girma ba kuma ba ƙaranci ba masu masifar kyau da jan hankali, Najmeer fara ce sol wanda haskenta me ɗaukar ido ne, macece me kyau wadda duk unguwarsu ake kwatance da ita, a iya binciken da aka yi babu wata macen da ta kai ta kyau a duk faɗin unguwarsu, kyawunta na ƙara mata farin jini gurin maza musamman manyan Alhazawa, bata harka da yara ko talakawa, idan ka ganta tare da namiji tabbata hamshaƙin me kuɗi ne, ƙwarjinta ma baya bari wasu mazan tunkararta, idanuwanta manya ne masu kyau da ɗaukar hankali, ƙwayar idon nata kuwa blue ne siɗik shiyasa wasu ke cewa ba mutum ba ce, wasu ma suna faɗin Aljana ce shiyasa kyawunta ya yi yawa, bakinta ɗan ƙarami ne me ɗauke da pink lips haƙoranta kuwa sirara masu haske, a tsakiya sun raba kaɗan sai haƙoran suka ƙara kyau tamkar ita ta jerewa kanta, hancinta dogo ne daga sama har ƙasan shi, gashin girarta baƙi siɗik ga yawa har ya kwanta ƙasan idanuwanta, Namjeer macece wadda ta haɗa duk wani abun da cikakken namiji me ji da kansa ke buƙata, kayan da take bugawa sun wuce ɗiyar sarkin garin Jos ta saka su, Najmeer yarinya ce ƴar shekaru goma sha bakwai wadda kana ganinta ka san yarinya ce amma yanayin jikinta zaka iya cewa ta fi hakan, domin duk wasu halittu na jikinta sun fito tamkar ita ta tsarawa kanta, cikakkiyar shuwa'arab ce me ji da tsagwaron kyau da kwarjini gaban manyan mutane, iyayenta sun rasu tun tana da shekaru uku a duniya, tana zaune tare da Kakarta ta gefen Mahaifiyarta wadda suke kira da Mamu, iyayen Najmeer kuwa ita ce kaɗai ƴarsu a duniya daga ita basu sake samun haihuwa ba, bayan shekara uku da samun Najmeer Mahaifiyarta me suna Maryam ta rasu sakamakon ciyon cikin da ya kama ta, ko wata ɗaya bata yi da rasuwa ba gobara ta kama gidansu Mahaifinta Malan Bala da sauran jama'ar gidansu Allah ya yi musu rasuwa, itama Najmeer ɗin da ƙyar aka samu damar ceton rayuwarta, ta yi saukar Alqur'an tana da shekaru takwas a duniya, ta yi haddarta lokacin da ta cika shekaru goma sha biyar, batun makarantar boko kuwa babu shi dan Primary kawai ta yi ta daina zuwa, babu yanda Mamu bata yi ba dan ta koma makaranta amma abin ya gagara, rana ɗaya ta daina zuwa islamiyar ma gaba ɗaya, a kullum za ta fita tun safe sai dare take dawowa, tun Mamu Kakarta na kuka da damuwa har ta daina, Mamu ce kawai ke haƙuri da ita dan babu yanda ta iya, duk ƴan Uwan Mahaifinta sun ce kar ta sake zuwa gidansu tun da ta zama karuwa, kasancewar Najmeer akwai zuciya ne ya sa ta janye ƙafarta daga gidan, amma duk da haka suna zuwa dan cin arziƙinta, tun tasowar Najmeer bata da ƙawa ko ɗaya a cewarta bata son munafurci, duk mutanen da ke unguwar sun san wacece ita, inhar za'a yi kwatance idan ba ka ce Shalelen Alhazawa ba babu wanda zai gane, duk ƴan unguwar da sunan da suke kiranta kenan, rashin jin maganarta kuwa sai ƙaruwa yake dan wasu lokutun ma a waje take kwana.



Miƙewa ta yi daga inda take zaune tare buɗe Handbang ta ciro wata farar leda tana sakin murmushi, Frigd ɗin da ke gefe ta buɗe tana mai ɗauko Drink ta zuba a Cup, da sauri ta maida kallonta kan Alhajin da ya fito daga toilet fuskarsa na kallonta, cikin basira da ƙwarewa ta zuba maganin kamar guda uku tana sakar masa murmushin da ya tashi ɗimauta shi, gaba ɗaya hankalinsa na kanta be san wainar da take toyawa ba, a hankali ta ɗaga Cup ɗin tana mai nufar inda yake, wani irin juyi ta yi wanda ya ƙara firgita shi, "Ga wannan ka ɗan taɓa kafin na fito wanka My sweet Guy". Najmeer ta faɗa cikin zazzaƙar muryarta, karɓar Cup ɗin ya yi yana mai kaiwa baki, sai da ya sha sosai kafin ya ce "Thank you Baby Girl am waiting for you, and this your kayan marmari" Ya ƙarasa maganar yana shafa bayanta, sai da ya ja mugun numfashi jin wani mahaukacin laushi ya shige sa.

Ba tare da Najmeer ta ce komi ba ta shige toilet bakinta ɗauke da addu'ar shiga.

Sai da ta kai kusan mintuna talatin a ciki kafin ta fito ɗaure da tawul, kwance ta sami Alhajin yana sharar bacci harda sakin nunshari kamar gandamemen ƙato, a fili ta ce "Gud job" Mintuna biyar ya ɗauketa gurin shiryawa, sai da ta duba gaba ɗaya ɗakin da kyau dan ta san wasu Hotels ana saka Camera a ɗakunan mutane, sosai ta duba tare da tabbatar da ba bu Camera ko ɗaya, a gaggauce ta fara bincika aljihun kayansa, ai kuwa sai ga kuɗaɗe masu yawa, tattara kuɗin ta yi ta zube cikin Handbag ɗinta, wayarsa da ke gefe ta ɗauka tana mai danna wasu pin, cikin ƙanƙanin lokaci ta cire security sannan ta yiwa kanta tranfer na 10million, kayansa kuwa a leda ta zuba takalmansa ma haka, babu abin da ta bar masa face wayarsa, shima dan kar a yi bincike akai ne, hatta gajeran wandonsa sai da ta ɗauka, cikin hanzari ta goge alert tana mai barin Hotel ɗin.



Sai da ta yi nisa da tafiya kafin ta tari adaidaita, kwatance ta masa har unguwarsu, a bakin layi ta ce ya ajeta, sannan ta biya sa kuɗi tana mai nufar hanyar gidansu, har me adaidaita zai juya ta yi saurin dakatar da shi tana faɗin "Bawan Allah tsaya, ga wannan kayan idan zasu yi maka" Kayan Alhajin ta miƙa masa, cikin murna me adaidaita ya karɓa yana ta zuba mata godiya, ita kuwa ta wuce ba tare da ta amsa masa ba.

Bakinta ɗauke da sallama ta shigo gidan, a tsakar gida ta sami Mamu na jan carbi, kallo ɗaya ta yi mata ta ɗauke kai, Najmeer na murmushi ta ƙaraso tana mai zama kusa da ita "Allah ya sa dai ba laifi na yi ba, Mamu wannan hararar ta mecece?"

Ƙara haɗe fuska Mamu ta yi "Najmeer.....Najmeer.....Najmeer......., sau nawa na kiraki?"

"Sau uku" Namjeer ta amsa tana kallonta.

"Na gaji da halinki, na gaji da maganganun mutane, ke ce kullum yawo cikin gari, meyesa baza ki tausaya min ba, ko zagin da mutane ke min idan na fita bakya gani ki daina wannan yawon iskancin"

Turo baki Najmeer ta yi har da matso ƙwallan ƙarya, "Wai ke Mamu meye matsalarki da karuwancin da nake yi, duk wannan fa dan ke nake yin sa, idan ban fita na samo mana ba Uban wa zai ciyar da mu?"

"Ubanki zai ciyar da mu, marar kunyar yarinya wato fitsarar taki za ki fara ko? tom bari idan Kawunki ya zo sai na faɗa masa cewar Karuwancin da ki ke zuwa saboda ni ki ke yi".

Kawu Jamilu Ƙani ne ga Mahaifin Najmeer Uwa ɗaya Uba ɗaya su uku ne dama, shine Autansu, Namjeer na masifar tsoronsa, shi kaɗai ne wanda take shayi a halin yanzu, a duk lokacin da ta haɗu da shi to fa yanzu zata rasa natsuwarta, dan tsananin tsoronsa.


A ɗan tsorace Namjeer ta ce "Kinga Mamu duk abin be kai haka ba, ke wace irin tsohuwa ce iyeeee? ni zan shiga daga ciki bacci nake ji"

Ba tare da ta saurari abin da Mamu zata faɗa ba ta shige ɗakinta tana turo ƙofa.

Ko mintuna biyu masu kyau bata yi da shiga ɗaki ba suka ji sallamar Kawu hannunsa ɗauke da leda, bayan sun gaisa da Mamu ne ya ce "Ina yarinyar nan ne? Allah ya sa bata fita yawon iskancin nata ba" Duk da cewar Mamu ta ji zafin abin da ya ce amma sai ta yi murmushin yaƙe, "Najmeer na daga ciki ai yau babu inda ta tafi" Duk abin da suke faɗi tana jinsu sai ma ƙara lafewar da ta yi dan kar ya ce a kira ta.

Ledar Goron ya miƙawa Mamu yana faɗin "Nikam ya batun Jabir ɗan gidan Malan Bukar da na ce zan haɗa shi aure da Najmeer ko ita ce ta hana shi zuwa zance?"

"Imban da abinka Jamilu ni menene nawa a ciki? tana ɗaka ai ka sameta sai ku yi magana" Ɗakin Kawu ya nufa yana mai ɓata fuska shi ala dole Mamu ta gasa masa magana.

Ya jima a ɗakin wanda har Mamu ta kasa haƙuri ta kira sa, duk da hakan sai da ya ƙara sama da mintuna biyar kafin ya fito fuskarsa a ɗaure, ko sallamar arziƙi be yiwa Mamu ba ya fice daga gidan, sheshsheƙar kukan Najmeer ne ya sa Mamu nufar ɗakin a kiɗime dan babu abin da ta tsana kamar ganin kukan Jikanyar tata. Najmeer na ganin Mamu ta shigo, ta yi saurin tasowa daga kwancen da take ta faɗa jikinta tare da sakin kuka me cin rai, cikin kukan take faɗin "Mamu dan Allah kar ki bari Kawu ya aura min Jabir, wallahi bana son shi, yanzu kamar ni zan auri namiji irin Jabir wanda ko Boko be yi ba, kuma ba wayayye ba haba dan Allah" Jin yanda ta ƙarasa maganar ne ya ba Mamu dariya, tureta daga jikinta ta yi "Yooo yau naga ja'irar yarinya, ke Bokon ki ka yi ne? ai da wannan taɓarar da ki ke gwara a aura miki shi ku je can ku ƙarata" Ƙara rushewa da kuka Najmeer ta yi "Ai kuwa ba zan aure shi ba, ke Mamu kinga na yi miki kalar macen da zata auri talaka, kalleni da kyau cikakkar mace amma a rasa wanda za'a haɗani da shi sai Jabir"

"Ke ni rabani da zancen banza, in kinso ki auri ɗan Sarki ba me kuɗi ba, mtsssss" Mamu ta faɗa tana barin ɗakin, ita ko Najmeer ta shiga mitar maganar har aka kira sallar magrib, alwala ta haɗo tare da yin sallah, ta jima a zaune tana karatun Alqur'an har aka kira isha, dama sun yi da wani Alhaji kan cewa zasu haɗu bayan sallar isha, sai da ta gama sallah kafin ta shirya cikin wando iyakarsa cinya, sai Top me gajeren hannu milk Colour kasancewar wandon Blue ne, wasu uban takalma sawu ciki masu masifar kyau ta saka Milk kalar rigar jikinta, sai gashin kanta da ta ɗaure daga baya ya zuba har ƙugunta yana rito, hula ta ɗora a kai tana mai juyi cike da salo, sai da ta tabbatar cewa komi ya yi need kafin ta yi wankan turarukka masu mahaukacin ƙamshi, a tsakar gidan ta sami Mamu na ƙoƙarin shiga ɗakinta, da sauri ta koma da baya har Mamu ta shige ɗaki, Najmeer na ganin haka ta fice daga gidan, a tsarinta bata bayar da Numbern wayarta balle a kira ta, idan ka haɗu da ita a hanya zata faɗa maka inda zaku haɗu kuma da lokacin da zaku haɗu, asalima bata yawan anfani da wayarta.

Kamar yanda suka aje da Alhajin kuwa haka aka yi, wata hamshaƙiyar unguwar da ke can bayan layi Namjeer ta ce masa idan ya zo ya tsaya, dan haka ta nufi can cikin tafiyarta me masifar jan hankali, ba sabon abu ba ne ganin Najmeer cikin irin wannan shigar, dan duk ƴan unguwarsu sun san ita ce macen da ke fita tamkar ba musulma ba, tun ana gulmace-gulmace har ta kai idan suka ganta sai dai ka ji ana faɗin, Shalelen Alhazawa-Shalelen Alhazawa, ita kuwa Najmeer idan tana cikin nishaɗi zaka ga ta fitar da kuɗaɗe tana watsa musu tamkar wadda bata san zafinsu ba.

Tun da ta fara ratsa titin layinsu mutane ke kallonta har ta fice gaba ɗaya, wani farin hankacif ɗan ƙarami da ke hannunta ne ta saka bayan aljihun wandonta.

Motoci uku ne bugaggu masu masifar kyau, daga waje masu tsaronsa ne kusan su biyar majiya ƙarfi, wani irin yawu Najmeer ta haɗa jin yanda gabanta ke faɗuwa, cikin ƙarfin hali ta ƙaraso gurin, tun kafin su tare ta Alhajin ya fito daga motar yana mai sakin murmushi tare da ware hannayensa alamun ta zo gare shi, cike da iya barikanci Najmeer ta nufesa tana mai shigewa jikinsa, masu tsaronsa kuwa baya suka basu cikin girmamawa, "Baby kin haɗu sosai, wallahi ko a matan larabawa sai an bincika"

"My Alhaj banda matan larabawa, a barni a Jos ma kawai is okay"

Najmeer ta faɗa tana shafo tsakiyar bayansa, wani irin shiɗewa Alhajin ya kuma yi, "Baby faɗa min account numberki"

Dama abin da Najmeer ke son ji kenan, a makirce ta zayyano masa, sai da ya gama tura mata kafin ya ce "Mu shiga daga ciki ko? na tura miki 50million ba yawa, amma tun da muna tare za ki ci arziƙi Baby" Ɗan taɓe baki Najmeer ta yi "Okay but ina zamu nufa yanzu?"

"Gidana zamu tafi, akwai wani gida a can Area 1, wanda nake zuwa dan hutawa" Ba tare da jin tsoron komi ba Najmeer ta shige motar, masu tsaron kuwa suka rufe ƙofa suna mai shiga sauran motocin, cikin ƙanƙanin lokaci suka bar unguwar.



A gafen Mamu kuwa ganin har tara na neman bugawa amma Najmeer bata fito ta ci abinci ba ne yasa ta nufi ɗakinta amma wayam ba kowa, gaba ɗaya gidan ta duba ba bu Najmeer ba bu alamunta, ƙamshin turaren da ta ji ne ya tabbatar mata cewar Najmeer ta yi abin da ta saba.

Jikin Mamu a sanyeye ta koma ɗaki, duk idauwanta sun ciko da ƙwalla a fili ta ce "Haƙiƙa Najmeer kin ɗauko hanyar da baza ta ɓulle miki ba, tun da ki ka san ciyon kanki har zuwa yanzu kullum sai kin sakani kuka, yanzu me zan faɗawa iyayenki idan muka tashi a gaban Ubangiji? na tabbata cewa a halin yanzu mutane suna ɗaukar cewa na sakar miki jiki kin lalace saboda ke marainiya ce, Allah ya kare ki a duk inda ki ke kuma Allah ya shiryeki".
Mamu ta ƙarasa maganar tana mai share ƙwallan da ke zubo mata kamar an buɗe pampo.



Su Namjeer kam a wani tangamemen gida suka shiga wanda ya gaji da haɗuwa, kasancewar Namjeer ta saba shiga manya-manyan gidajen Alhazawa ne ya sa take ganin wannan gidan ma ba komi ba ne, ɗakinsa suka nufa Najmeer na gefensa ya rungumota ta baya, har rawa jikinsa ke yi tsabagen jaraba, dan ba ƙaramin tafiya da iamaninsa ta yi ba.

Tamkar aljannar duniya haka ɗakin ya tsaru, komi na ɗakin da Gold aka yi shi, hatta bed ɗin na Gold ne barin ma ƙofofin gidan, hasken ɗakin da ya gauraye ne yasa Alhajin ƙara zubawa Najmeer ido, a ransa ya ce tabbas Allah ya zuba halitta a anan, wannan ƙwayar idon nata tamkar zinari, ajiyar zuciyar da Najmeer ta sauke ne ya sa shi dawowa daga duniyar tunanin da ya shiga, cikin ƙasaita ta nufi Frigd ɗin da ke ɗakin ta ɗauko drinks da Cup, kamar wani soko haka Alhajin ya miƙe tare da karɓar kayan da ke hannunta "Baby ai wannan aikin ba irin na mata kamar ki ba ne, let me help you with it, amma ba bu abin da ki ke son ci kuwa?"

Zama kan bed Najmeer ta yi, ta ɗauki mintuna biyu kafin ta ce "Akwai Shawarma?"

"Yes akwai Shawarma" Alhajin ya faɗa yana latsa wata ƙararrawa, ɗaya daga cikin masu aikin ce ta shigo bakinta ɗauke da sallama, kallon Namjeer ta yi tana mai mamakin ganin ƙaramar yarinya kamar wannan tare da Dattijo irin me gidanta, tsawar da Najmeer ta daka mata ne yasa matashiyar matar da zata kai shekaru talatin razana cikin tsananin tsoro, a fusace Najmeer ta miƙe tana mai ɗauketa da mahaukacin mari, "Ke dabba jaka me ki ke kallo? kinga na yi kama da wadda za ki zubawa ido kamar wata tsohuwar mayya, tom bari na ba ki amsar abin da ki ke son sani, kallon da ki ke mun ya nuna cewar kina son sanin meya kawoni gidannan ko?"

A hankali ta koma tana mai zama kan cinyar Alhajin cikin iya barikanci ta shafo gefen fuskarsa tana faɗin "Ni Karuwa ce, cikakkiyar ƴar tasha me zaman kanta, idan kuma da abin da ki ke son sani za ki iya faɗa mun" Jikin matashiyar na ƙyarma ta ce "Allah ya ba ki haƙuri insha Allah hakan baza ta ƙara faruwa ba, Sir me ka ke da buƙata?" Ta ƙarasa maganar tana kallon me gidanta.

"Shawarma za ki kawo mata na ba ki minti ɗaya" Cikin biyayya ƴar aikin ta fice tana mai rufo ƙofar, ko cikakken minti ɗayan bata yi ba ta dawo hannunta ɗauke da plate, a gaban Najmeer ta aje sannan ta fice daga ɗakin, har yanzu Najmeer na kan cinyarsa sai yamusta fuska take, cike da makirci ta ce "Ka haɗa mun ruwan wanka kafin na gama" Tun kafin ta gama magana Alhajin ya miƙe dan cika umarni, ita kuwa ta fara cin Shawarmar tana lumshe ido saboda daɗin da ke ratsa ta.


A haka Alhajin ya fito ya sameta, ko kallon inda yake bata yi ba ta cigaba da abin

Please Login or Register in order to submit comment